HUKUNCE-HUKUNCEN ’RANTSUWA’ A MUSULUNCI ()

Malan Aliyu Muhammad Sadisu

Yayi Magana ne akan HUKUNCE-HUKUNCEN ’RANTSUWA’ A MUSULUNCI ,da sauran mas alolinsa

  |

  HUKUNCE-HUKUNCEN 'RANTSUWA' A MUSULUNCI

  [Hausa هوسا-]

  Malan Aliyu Muhammad Sadisu

  2014 - 1435

  الإيمان في الإسلام

  [Hausa هوسا-]

  الشيخ : علي محمد السادس

  2014 - 1435

  HUKUNCE-HUKUNCEN 'RANTSUWA' A MUSULUNCI !


  Gabatarwa : Dasunan Allah Mai yawan rahama maiyawai jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a wannan karon za mu karkata akalar mu zuwa wani bangaran daban na rayuwa , wannanan bangaran kuwa shi ne na Rantsuwa! Domin mu ga yadda musulunci ya tsara mana wannan al'amari, kuma wannan zai dada nuna mana cewa musulunci yana da ruwa-da-tsaki cikin dukkanin al'amurammu, a wannan karon bayanai za su zo game da yadda ake rantsuwa da kuma hukuncin ta da yadda halin wanda ya yi rantsuwar zai kasance da kuma abinda zai biyo baya bayan mutum ya kasa a binda ya yi rantsuwar a kan shi cewa zai yi ko kuma ba zai yi ba, da kuma matsayin rantsuwar mu ta yau da kullum, da dai sauran bayanai da suka shafe mu, muna rokon Allah da sunayan shi kyawawa da suffofin shi madaukaka da ya yi mana jagora amin.


  Tabbatuwar Rantsuwa a shara'a: Lalle rantsuwa ta tabbata a Littafin Allah Mai tsarki Alkur'ani da kuma Hadisan Ma'aikin Allah da Ijma'in malamai akan haka. Amma a alkur'ani Allah yana cewa "Allah ba zai kama ku da rantsuwar wargi ba sai dai zai kama ku da abin da ku ka kudurce na rantsuwa" Ma'ida, aya ta : 89, kuma Allah mai gaima da daukaka ya umarci Annabin shi a wurare uku cikin Alkur'ani mai girma akan ya yi Rantsuwa, Allah yake cewa " Kuma suna neman labarinka akan al'amarin gaskiya ne kuwa? Ka ce : Eh, na rantse da Ubangiji na lalle tabbas gaskiya ne" Suratu Yunus, aya ta 53. wuri na biyu kuma Allah yana cewa "Kace :A'a, na rantse da Ubangiji na sai ta zo muku" Suratu Saba'I, aya ta 3, wuri na uku cikin Suratut-Taghabun aya ta 7, Allah yana cewa "Kace :A'a, ina rantsuwa da Ubangiji na lalle sai an tayar da ku". Wadan nan sune wurare uku da Allah ya umarci Annabin shi Annabin tsira da ya yi wa wadannan kafiran rantsuwa akan lallefa alkiyama zata zo, dubi sabo da tsananin karyatawar su da aukuwar ranar sakamako sai da Allah ya umarci Manzan shi da ya yi musu rantsuwa har a wurare uku, lalle wannan yana nuna mana halaccin yin rantsuwa idan bukatar hakan ta auku, haka namma ya tabbata Ma'aikin Allah yana cewa "Lalle ni ina rantsewa da Allah – in Allah ya yarda – ba zan yi wata rantsuwa ba sannan in ga sabanin haka shi ne mafi alheri face sai na aikata abinda yake shi ne mafi alheri na warware rantsuwa ta" Bukhari da Muslim suka ruwaito, wannan shi ma ya dada fito mana da tabbatuwar rantsuwa domin Ma'aikin Allah yana yi, kuma yana dada nuna mana halaccin warware rantsuwa idan daga baya mutum ya fahimci hakan shi ne mafi alheri ba wai ya toge akan rantsuwar shi ya fake da ita da an bashi baki yace 'ai na rantse' domin Allah ya hana mutun ya sanya rantsuwar shi ta zama wani shamaki tsakanin shi da aikata ayyuka na alheri kamar sadarda zumunci ko taimakon mabukaci Allah yana cewa "Kada ku sanya Rantsuwa da Allah ta zama wani shamaki don ku ki yin aikin alheri kuma ku ki yin takawa kuma ku ki yin sulhu tsakanin mutane" Suratul-Bakara domin akwai mutane masu yin irin wannan dabi'ar nan da nan zai yi rantsuwa domin da ance ya yi hakuri sai yace ai na rantse. Kuma malamai sun yi Ijma'I akan tabbatuwar rantsuwa a musulunci.


  Hukuncin Rantsuwa: A salin Magana yin rantsuwa halas ne idan bukatar hakan ta taso, koda yake yana zama wajibi a wani lokaci, ba mutum ya mayar da ita ako da yaushe ba domin wani mutumin kuma muddin zai yi maga daya ko biyu sai ya yi rantsuwa har a wayi gari rantsuwar ba komai bace awurin shi to irin wannan halin musulunci bai yarda da shi ba ya kyamace shi domin ya hana a yarda da mai yin irin wannan rantsuwar Allah yana cewa "Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, wulakantacce." Suratul-Kalam, aya ta 10.
  Da wa ake rantsewa? Ana rantsewa da Allah mahalicci ne kadai, dudda cewa shi Allah madaukakin sarki yana da ikon ya rantse da dukkan abinda ya ga dama babu wanda zai ce da shi damme (Tsarki ya tabbata ga Allah) saboda haka Allah ya rantse da abubuwa da yawa Kamar rayuwar Manzan Allah kamar rana da wata da dare da sama d.s, ba ya halatta a rantse da dukkanin wani abin halitta, akan haka ba ya halatta da sama ko kasa ko mala'ika ko wani annibi daga cikin Annabawan Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su ko da kabari ko da kwarankwatsa wasu suce tannatsa ko gajimare ko ma dai meye, Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya riski Umar Dan Khaddab a cikin ayarin matafiya yana rantsewa da iyayan shi, nan danan Ma'aikin Allah ya kira su ya ce "Lalle kusaurara hakika Allah yana hana ku da ku rantse da iyayan ku, kuma dukkanin wanda ya kasance zai yi rantsuwa to ya rantse da Allah ko kuma ya yi shiru" Bukhari ya ruwaito shi a hadisi na 679 da 6646 Muslim a hadisi na 1646 Abu-Dauda hadisi na 3249 Tirmizi 1534 duk wadannan malaman sun ruwaito wannan hadisin cikin littafan su. To idan mutum ya rantse da wanda ba Allah ba ya rantsuwar take? Amsa anan ita ce: al'amarin yana da fuskoki biyu, fuska ta farko idan ya yi hakan akan rashin sani sai yanzu ya sami bayani to wannan ana fatan Allah ba zai kama shi da wannan laifi ba, fuska ta biyu ita ce mutum ya aikata hakan yana sane to abubuwan da za su biyo baya za su zama kamar haka: abu na farko ya sabawa Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma kowa ya san irin danyan laifin dake cikin sabawa Ma'aikin Allah domin ana jin tsoron kada mutum ya samu kan shi ba cikin mabiya ma'aikin Allah ba ranar Alkiyama Allah ya tsaremu, abu na biyu ya aikata laifi mai zaman kanshi domin yana daga cikin laifuffukan dake sa zuciya ta yi tsatsa, abu na uku rantsuwar bata kulluba (ma'ana ba rantsuwa bace) sabo da haka ya zama dole ai hattara daga irin wadannan al'amurra da kuma neman gafarar Allah, Allah ya gafarta mana amin.


  Karkasuwar Rantsuwa: Anan malamai sukan karkasa rantuwa zuwa kashi-kashi, zamu ambaci kashi uku da hukunce-hukuncensu daga cikin kasha-kashan rantsuwar domin galibi wadannan ukun su mukafi cudanya da su lokacin yin rantsuwa Allah ya bamu sa'a amin.


  Kashi Na Farko: Rantsuwar wargi. Wannan ita ce rantsuwar da malai suke kiran ta Yaminul-Laghwi. Malaman sun karawa juna sani wurin me ake nufi da Rantsuwar wargi ko yasasshiyar Rantsuwa? Wasu suka ce :Ita ce irin rantsuwar dake guda a bakuna ba tare da angudurta nufin rantsuwar a zuciya ba, kamar: Wallahi ba haka bane, ko Wallahi haka ne. wasu kuma suka ce ita ce: rantsuwar da mutum ya kan yi akan tabbas abinda ya rantse a kan shi daidai ne sai daga baya abin ya bayyana ba haka bane, misali: ka hango wani mutum daga nesa sai ka rantse da Allah waccan mutumin wane ne, domin ka kalli tsawon shi da tafiyar shi da komai na shi, sai bayan ya matso kusa sai ya bayyana ba shi dinne ba, wannan ko yakan auku sosai(akwai lokacin da naje sakkwato zuwa na nafarko kenan akaita maraba da ni ana cewa Aliyu ka zaka sai nake ta mamaki ashe a inda na sauka din akwai wani ya yi tafiya shima sunan shi Aliyu wai mun yi kama sosai) wadannan nau'uka biya na rantsuwa mukan sami kammu a ciki kwarai da gaske, to irin wannan rantsuwar tana da Kaffara? Irin wannan rantsuwar bata da wata kaffara domin Allah bai kama wanda ya yi ta da laifi kamar yadda Allah ya ke cewa "Allah ba ya kama ku da laifi saboda yasasshiyar rantsuwowin ku." Suratul-Bakara, aya ta :225. (wato rantsuwar wargi) kamar yadda bayanin ta ya gabata.


  Kashi Na biyu :Rantsuwa mai halakarwa. Wannan kashi na biyu da zamu yi bayanin shi yanzu shi ne malamai suke kiran shi Al-Yaminul-Ghamus, wato rantsuwa me halakarwa. Wannan ita ce: Rantsuwar da mutum zai yi ta akan karya domin cin hakkin wani. Wannan zai nuna mana dukkan wata rantsuwa akan karya da mutum zai yi domin ai anfani da wannan rantsuwar a bashi hakkin wani ko aba wani hakkin wani ita ce ake Magana a yanzu, misali:Mutum ne yake so ya dirkake fegin wani ko gona koma dai menene ya tsaya tsayin-daka da rantsuwa domin a bashi wannan fegen ko wannar gonar, ko kuma ya kira wani ya rantse a matsayin sheda domin a bashi shi kuma wanin ya rantse. To me nene hukuncin haka? Abinda ya kamata a sani dukkan wani hukunci da alkali ya yanke a kotu baya halatta haram ko ya haramta halal, saboda haka idan alkali ya yi iyakar binciken shi ya zamana abinda ya binciko shi ne wannan fegi naka ne alhali ba naka bane kotu ta dauka ta baka akan abinda ta dogara da shi na shaidu to wannan hukunci baya halatta wannan fegi a wurin Allah wanda yake masanin boye da sarari. Abu na biyu kuma irin wannan rantsuwa ba'a mata kaffara domin ta wuce haka bala'inta ya kai bala'I, ita dai kan sai idan mutum ya tuba yayi nadama ya kuma ci gaba da neman gafara wurin Allah ya kuma yi niyyar ba zai sake aikata wannan mummunan aiki ba ya kuma mayarwa me kaya kayan shi ya kuma ci gaba da istigfari muna fatan Allah ya yafe mishi, amma irin wannan rantsuwa ai ba maganar kaffara dirkashi! Ah, idan kaffara kawai zata biya ba sai mutum ya kamfato makudan kudi ba ya zo ya rantse in an bashi ya je ya dauki abinda bai kai dubu goma ba ya yi kaffara da su shikenan ya sha. Saboda irin girman da wannan rantsuwar take da shi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabba a gare shi ya ke cewa "Dukkan wanda ya yanki hakkin wani mutum musulmi da rantsuwar shi to hakika Allah ya wajabta mishi wuta kuma ya haramta mishi Aljanna" Muslim ya ruwaito shi, kallaci irin narkon azabar da Ma'aikin Allah ya yi bayanin ta cikin wannan hadisin ka kuma kalli yadda ake fafutukar aga antara koma ta halin kaka ne Allah ya sawwake, abin la'akari anan shi ne da Ma'aikin Allah ya :'Hakkin mutum musulmi' ba ana nufin na wanda ba musulmi ba ya halatta a'a na dai musulmi shi ne bala'in ya fi, Allah ya kare mu da kariyar shi amnin summa amin summa amin.


  Kashi Na uku ; Rantsuwar da ake wa Kaffara. Wannan ita ce malamai suke kira; Yaminul-Kaffara wato rantsuwar da idan mutum ya warware ta (wato karya ta) zai yi kaffara, wannan ita ce dukkan rantsuwar da mutum ya yi da Allah akan zai ai kata abu kaza sai kuma ya fasa aikatawa, ko ya rantse ba zai aikata ba sai kuma daga baya ya zo ya aikata. Sai dai malamai suna anbaton sharudda uku kafin hakan, sharadi na farko ya zama ya kudurce rantsuwar azuciyar shi ya yi niyya kenan, domin idan ba haka ba ta zama ya sasshiyar rantsuwa ke nan wacce bayanin ta ya gabata wacce ba za ai mata kaffara ba, sharadi na biyu ya zama alokacin yin rantsuwar baice 'In Allah ya yarda ba' domin idan ya ce In Allah ya yarda kuma ya fadi hakan ne har zuci ba iya fatar baki ba sannan bai sami damar aiwatar da abinda ya yi rantsuwa akan shi ba wannan ma ba wata kaffara akan shi, sai dai kamar yadda aka ambata ya zamana ya ce hakan harzuciyar shi ba kawai mutum ya fadi iya fatar baki ba. sharadi na uku ya zama ya hada rantsuwar da In Allah ya yarda (wato In sha Allah) amma idan sai da ya yi rantsuwar sannan daga baya ya ce in Allah ya yarda to wannan bazata kange shi daga kaffara ba idan ya warware rantsuwar. Wadanan su ne sharuddan da malamai suke ambatawa da suke kare mutum daga yin kaffara. To amma idan mutum ya rantse ce ba zai aikata abu kaza ba sai ya aikata da mantuwa ya hukuncin shi? Idan har akan mantuwa ya aikata babu wani abu a kan shi domin Allah baya kama wanda ya aikata hakan da mantuwa sai dai idan da ganganci ne domin muna yin addu'a lokacin karanta amar-Rasulu muna cewa"Ya Allah Ubangijimmu ! kada ka kama mu da abinda mukai da mantuwa ko mukai kuskure" Suratul-Bakara, aya ta karshe, kuma ya tabbata a hadisi ruwayar Muslim cewa Allah ya ce "Hakika na aikata"(ma'ana ya karba mana addu'ar). Saboda haka dukkan mutumin da ya yi rantsuwa akan ba zai yi abu kaza ba sai kuma ya aikata da mantuwa to babu wata kaffara akan shi, har ma da mutumin da ya rantse ba zai yi kaza ba ko kuma ya rantse sai ya yi kaza, sai aka tilasta shi da karfin tsiya to shima babu komai akan shi misali ya rantse ba zai shiga gidan wane ba sai aka sami samari majiya karfi suka dauke shi cancakat suka sa shi cikin gidan ko kuma ya rantse ba zai fita ba aka sa samarin suka fitar da shi da karfin bala'I ko kuma suka zane shi ko ma suka ce za su kasha shi, shi ma babu wata kaffara akan shi, dalili kuwa shi ne fadar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi "An yafe wa al'ummata Kuskure da Mantuwa da Dukkan abinda aka tilasta su akai" (dud da cewa malaman hadisi suna maganganu kan wannan hadisin) sai dai akwai ayar suratun-Nahli aya ta 106 fadin Allah mai girma da daukaka "Dukkan wanda ya kafirce ma Allah bayan ya yi imani (da Allah din) sai dai kawai wanda aka tilasta shi…" shi ne malamai suke cewa atilasta mutum ya kafirce wa Allah amma Allah ya ce bai kafurta ba balle a tilastawa mutum ya warwre rantsuwar shi?.


  Me ke sa mutum ya fita daga Rantsuwar shi? Abubuwan da suke san ya mutum ya fita daga rantsuwar da ya yi dayan abubuwa uku ne. abu na farko: ya aikata abinda ya rantse zai aikata, ko ya ki aikata abinda ya rantse ba zai aikata ba. abu na biyu: yin dogaciya wato ya fadi In sha Allahu a lokacin da ya yi rantsuwar kamar yadda bayanai suka gabata. Abu na uku kaffara, bayanai na nan na zuwa kan kaffara in Allah ya yarda. Wadan nan abubuwa uku su suke sa mutum ya fita daga rantsuwar da ya yi. Yanzu zamu kawo wadansu misalai na rantsuwa da sukan yawaitu a bakunan mutane muji hukuncin su.


  Idan Mutum ya ce in har na auri wance ta saku. Idan mutum ya yi irin wannan maganar sai kuma Allah cikin ikon shi ya kaddari auren to ya sani fa bata sakuba domin Ma'aikin Allah ya ce "Babu alwashi ga Dan-adam cikin abinda ba ya mallaka, kuma babu 'yantawa cikin abinda baya mallaka, kuma babu saki ga Dan-adam cikin dukkanin abinda baya mallaka" Tirmizi ya ruwaito ya kuma ce hadisi ne kyakkyawa.
  Idan mutum ya Rantse ba zai sayar ba ko ba zai aurar ba. ida mutum ya yi irin wannan rantsuwar sai kuma ya zo ya aurar ko ya zo ya sayar to zai yi kaffara sai dai idan mijin da aka aurarwa ya ki karba(ma'ana ya ce bai aura ba) ko wanda aka sayarwa ya ce bai saya ba to anan ba wata kaffara akan shi, zamu da kata akan wadannan misalai guda biyu har idan akwai tambaya sai a tuntuba kamar yadda aka saba. Yan zu zamu shiga Magana akan :


  Kaffara: ita ce dayan abubuwa uku da mutum zai kubutar da rantsuwar shi da su kamar yadda bayani ya gabata (Ma'ana karya rantsuwa) kuma kada a sha'afa aduk lokacin da ya yi rantsuwa ba zai aikata abu kaza ba sai ya fahimci cewa ya aikata din shine mafi alheri to ya aikata din shi ya fi sai ya yi kaffara kada ya makalkale da cewa ai ya riga ya yi rantsuwa kamar dai yadda bayanai suka gabata, anan musulunci abubuwa uku ya bayyana da cewa sune ake yin kaffara da su(wato karya rantsuwa) wadannan abubuwa kuwa su ne: Ciyarwa, Tufatarwa da 'Yantawa, wadannan abubuwa uku anbaiwa mutum zabi ya zabi wanda yaga dama ya yi kaffara da shi kamar tadda bayanan ko wanne zai zo filla-filla daki-daki in Allah ya yarda sai dai idan bai sami dama ba daga cikin wadannan abubuwa uku sai ya yi Azumini kwana uku. Wadannan abubuwa su ne ake karya rantsuwa da su, amma wata wacce ba wannan ba to ba'a yarda da ita ba kamar ace wai mutum ya kama kaza da ranta ya gatsa wuyanta ko kuma ace akwai wasu gidage su kadai ne suka san yadda ake karya rantsuwa, koda yake galibin irin wannan al'ada tana faruwa ne akan wadanda suke rantsuwa da taurari ko gajimare ko kwarankwatsa abubuwan da akai bayani baya halatta ai rantsuwa da su. Yin kaffara ta hanyar
  Ciyarwa : wannan hanya ita ce hanya ta farko daga cikin hanyoyi uku da musulunci ya baiwa mutum zabi domin yin wannan kaffarar, ita wannan ciyarwar mai kaffara zai yi ta ne ga mutane goma miskinai, wato zai ciyar da miskinai goma kuma zai ciyar da sune tsakatakiyar abin da yake ciyar da iyalan shi kamar yadda Allah ya yi bayani cikin Suratul-Ma'ida aya ta 89, shi dai miskini malamai suke ta bayanin shi, shi ne a kullum yana fafutukar abin da za'a ci na ranar wanda inda za'a kwana ana marka-marka zai iya shiga tasku Allah ya sawwake, anan sai muhaimci wanda shara'a take nufi da miskini ba naka-sasshe ba, wato gurhu ko makaho dadai sauran su wadannan ba sune miskinai da shara'a take nufi ba domin zaka iya samun wani naka-sasshen gidaje yake da su ake mishi haya wani kuma mashina sabo da haka ba lalle bane dukkun naka-sasshe ya zama wanda zai shiga cikin wadannan miskinan goma ba, sannan za'a ba kowanne miskini irin abinda ake fitarwa a zakkar kono (zakkar da ake yi bayan kammala azumin Ramadana Fiddakai) idan mutum ya baiwa miskinai goma wannan to ya kammala kaffarar shi. To yanzu ya halatta mutum ya girka abinci ya kira su su ci? Eh, ya halatta hakan ya makada abinci a gidan shi sannan ya gayyato su su zo, sai dai zai yi hakanne a abincin rana dana dare wato sau biyu kenan, kuma ba zai ciyar da wanda ciyar da shi ta zama dole a kan shi ba. kuma kamar yadda bayani ya gabata zai ciyar da tsaka-tsakiyar abinda yake ciyar da iyalan shi ne wato idan gidan shi daga shinkafa-da-miya sai dafa-dika jibi kuma tuwon shinkafa doya sakwara samonbita taliya kuskus, kaga wanna ba zai debo gero ko kaura ya ce wai zai bayar da ita a matsayin kaffara.


  Tufatarwa : wannan ko ita ce hanya ta biyu wurin yin kaffarar rantsuwa idan ita mutum ya zaba, ita tufatarwar mai kaffara zai tufatar da mutane goma ne ciccif kamar yadda mai ciyarwa ya ciyar da mutane goman, kuma tufatarwar ta na kasancewane tsakatsakiyar yadda mutum yake wa iyalan shi, sabo da haka sai ya dunkawa kowanne mutum riga da wando cikakke yadi kuma kamar yadda akai bayani tsaka-tsakiyar yadda yakewa iyalan shi, lalle kan musulunci ya dauki matakai da yawa domin kauda fatara domin wadannan mutane goma da akai musu wannan dinki ai an agaza musu, wannan shi ne takaitaccan bayani kan abinda ya shafi kaffara ta hanyar tufatarwa.


  'Yanta Baiwa/Bawa: wannan shine wani zabin da musulunci ya bai wa dukkan mutumin da kaffarar Rantsuwa ta kama shi na ya 'yanta Baiwa mumina ko Bawa mummuni wato daga bawa shima ya zama da. Sai dai sharadin da musulunci ya sa shi ne ya zama mummni wato ba zai wadatar ba idan mutum ya 'yanta wanda ba musulmi ba kenan haka kuma malamai suka ce kada ta zama nakasassa kamar yana neman kai da ita kamar makauniya ko gurgu da dai abinda yake nakasa ce bayyananniya, kaga wannan yana daga cikin manyan-manyan hanyoyin da musulunci ya bi domin hana yaduwar bautar da mutane kamar yadda Ma'aikin Allah yake cewa "Babu wani mutum musulmi da zai 'yanta mutum musulmi face sai(shi wanda aka 'yanta din) ko wacce gaba ta zama 'yantar da shi(wanda ya 'yantardin) daga wuta har al'aura da al'aura" Bukhari ya ruwaito shi 2517,6715da Muslim hadisi na 1509.


  Azumin kwanaki uku: idan mai yin kaffara bai sami daya daga cikin abubuwa ukunnan ba to sai ya koma zuwa ga yin azumin kunaki uku, rashin samun nashi zai iya kasancewa kodai bai da halin yin wadannan abubuwa ukun saboda babu dudda da cewa malamai sun yi bayanin cewa idan dai zai sami abinda zai ragu bayan abinci kwana guda to ba zai yi azumi ba, koda yake samun wanda baida halin kwata-kwata wata kila ya yi wahala saboda mawuyaci a rasa wadansu 'yankadarori kodai kiwo ko wayar hannu ko dai wata 'yarkadara da ba larura ba ce a rayuwa da mutum zai sargafar da ita domin yin wannan kaffarar, ko kuma yana da halin amma kwata-kwata bai sami miskinin da zai ba ba saboda kowa mawadaci ne wai! to amma idan mutum ya mallaki abinda zai ishe shi yin kaffara amma kuma ana bin shi bashi kwatankwacin abinda ya mallaka din kuma ana bukata ya biya kurkusa kamar Zakkar kono(Zakatul-Fitir) to wannan ba zai yi kaffara da wadan can abubuwa uku ba sai dai ya yi azumi. Idan ba shi da abinda zai yi kaffara da shi a yanzu amma yana saran shugowar wasu kudi bada dadewa to malamai sun yi maganganu biyu wasu sukace ya yi azumi domin bashi da shi a yanzun, Magana ta biyu kuma zai saurara yaga zuwan su sai ya yi kaffarar da su domin ba wani lokaci aka ajiye ba kamar sallah idan mutum bai sami ruwa ba domin tana da lokacin ta. Idan mutum ya fara yin azumi saboda bai sami sarari ba sai da ya fara ya yi daya ko biyu sai kuma ya samu wani budi anan bai zama tilas ya koma dayan wadann can abubuwa uku ba. Allah sarkin iko, Idan lokacin da mutum ya yi rantsuwa yana da abin hannun shi amma yanzu lokacin da zai yi kaffara babu kuma shikenan sai ya yi abinda ya ke da ikon shi a lokacin, ko kuma lokaci yana talakan shi tukuf, amma sai gashi lokacin da zai yi kaffarar yana da abin hannun shi shikenan sai ya yi dayan wadan can abubuwa uku da aka anbata, abin la'akari a nan shi ne halin da mutum ya ke ciki lokacin yin kaffarar ba lokacin da ya yi rantsuwar ba.
  Idan mutum ya rasu kafin ya fitar da kaffara, malamai sun yi maganganu kamar haka: za'a fitar da kaffarar daga uwar dukiyar tun kafin a raba gado domin ai hakkin Allah ne kuma hakkin Allah shi ne mafi cancantar abin da za'a biya, wasu kuma suka ce za'a fitar ne idan bai wuce daya bisa uku ba (wato kamar wasiyya ke nan).
  Kammalawa: daga dukkanin bayanan da suka gabata ya bayyana a fili yadda musulunci ya kula da rantsuwa domin munga irin yadda ya bata kulawa sosai ta yadda Allah ya saukar da ayoyi a cikin Alkur'ani mai girma domin fayyace wadannan hukunce-hukunce, Sannan kuma Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabba a gare shi ya isar kuma ya yi bayanin abinda Allah ya saukar sannan malamai basu yi kasa agwiwa ba suka suka rubuta babi-babi acikin littafan su, a wannan makala ta mu mun yi anfani da Tafsirin Kurdubi a a ya ta 89 cikin suratul Ma'ida hakana da Tafsiri Adhwa'ul-Bayan da kuma littafin Al-Mughni na Ibnu Kudamah juzu'I na 13, kuma mun yi anfani da wadan su littafan amma wadannan kusan sune jigo a wannan Kasida.

  Rbutawa :

  Malan Aliyu Muhammad Sadisu