RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI ()

Malan Aliyu Muhammad Sadisu

Yayi Magana akan RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI ,da wajibine ga kowace mace musulma tasansu

  |

  RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI

  [Hausa هوسا-]

  Malan Aliyu Muhammad Sadisu

  2014 - 1435

  الطلاق وأحكام العدة في الإسلام

  [Hausa هوسا-]

  الشيخ : علي محمد السادس

  2014 - 1435

  RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI:

  Gabatarwa:Da sunan Allah Maiyawan rahama Mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halitar Allah Annabi Muhammad, da SahabbanSa da Iyalan gidanSa amin. A wannan karan zamu gudanar da bayani ne kan yadda Addinin musulunci ya tsara yadda za'a gudanar da saki, batare da ancutar da Mata ko miji ba muddindai anbi wannan tsarin. Da zaran ance saki sai gaban namiji ko mace ya fadi, ko menene dalili? Musulunci bai shara'anta sakiba don cutar da wani ban gare, asalima musulunci ya shar'anta hakanne don ceto su daga muwuyacin hali, yana daga cikin rahamar musulunci tabbatar da saki, domin yana daga cikin mizar musulunci bai yadda a cutar da kowa ba, saboda haka idan akace a zauna babu maganar cewar akwai rabuwa ga duk wanda yaga anzalince shi kuma ya yi iyakar hakurin da zai iya yi, to wannan zai ba abokin zamanshi cewar shimafa yana da gata a musulunci, da yawa akan sami na miji yana dandanawa iyalin shi azaba, to yanzu sai kace yaya?, ko kuma matar tana gasawa maigidanta aya a hannu, to ananfa dole ne asa ido domin tabbas wani na matukar cutar da dan'uwansa kuma asan wanna mataki za'a dauka, amma musulunci tuni ya dauki matakai daba-daban domin shawo kan al'amarin tun kafin yakai ga rabuwa.Kandagarkin da musulunci ya yi.  Lalle ne musulunci ya yi kandagarki don hana rabuwar aure, ta yadda ya umarci dangin miji dana mata dasu tura wakilai guda-daga daga kowane bangare na miji da mata a lokacin da suka ga cewa lalle ka akwai sabani tsakanin wance da wane, su wadannan wakilai zasu nazarci dukkan bangarorin biyu su kuma yi kokarin daidaita al'amarin. Allah yana cewa " Idan kuka ji tsoron sabanin dake tsakanin su (miji da mata) to ku tura wani mai hukunci daga dangin sa da kuma mai hukunci daga danginta, muddin sukai nufin gyara to Allah zai daidaita tsakanisu"! Suratun-Nisa'I, aya ta :35. sanan Allah yana cewa adai cikin wannan Surar a aya ta 128 " Sulhu dai shine mafi alheri" sabo da haka a wannan bayani ya nuna mana lalle musulunci ya kula da dukkanin bangarori biyu (mata da miji), domin ganin kada rabuwa ta auku, saboda haka yana da 'yau mutun ya iya daurewa akan wani hakkinshi ya dan sassauto domin ganin ansami daidaituwa, domin daidaituwa ta fi rabuwa muddin ba akan asabawa Allah da Ma'aikinShi bane. Sauda da yawa mata sunyi hakuri da wani hakkinnasu kamar yadda mazan suma sukai hakuri da nasu domin ganin aure ya tabbata, masu iya Magana na cewa 'Tsakanin harshe da hakorima ana sabawa' wai 'zo muzauna zo musaba' saudayawa wadansu abubuwan basukai atada jijiyar wuya ba sai kaga za'a ba hammata iska, Allah ya sawwake.  Adadin Saki!


  Idan Allah ya kaddari sai an rabu tofa ba makawa sai hakan ya faru, to amma ya addinin musulunci ya tsara yadda sakin zai kasance? Kafin zuwan addinin musulunci mutanan jahiliyya sun kasance suna sakin mata yadda suka dama
  ba wani adadi, sannan idan mijin ya ga ta kusa kamma idda sai ya dawo da ita, wannan ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, yazamana suna azabtar da mata akan wannan mummunar al'ada, sai mace ta zauna shekara-da- shekaru ita ba mai mijiba kuma ba kuma mara mijiba, domin idan ya saketa ta kusa kamala idda sai ya dawo da ita, idan aka dan kwana biyu sai ya sake sakinta, da musulunci ya zo sai yai wa tufkar hanci, domin gallazawa mata a irin wannan bai kamata ba, musulunci yace ' Sakin da zai yiwu ai komai akanshi karo biyu ne' Suratul-Bakara, aya ta :229. anan sai aka nuna mana mutun zai iya sakin medakinshi kuma ya iya yin kome karo biyu, anan wata hikima ta musulunci sai yace saki sau biyu, domin ya nuna maka cewa abin da akafi so shine kayi daya sannan kasake yin dayan domin idan kai biyun lokaci guda tofa damarka ta kome daya ce ba biyuba, sabo da haka har idan ya zama ba makawa to sai kai dayan domin wata damarkace ka ajema kanka. Idan kai kake da laifi zaka gane idan kuma ita ce zata fadaka, idan ba hakaba sai ka kara gudan wani lokaci ya zama biyu kenan, to daga nan sai kowa ya shiga taitayinshi ya kuma kula da hakkokin da musulunci ya dora akan kowannensu domin ana kara saki na uku to ba kome ba biko sai kuma wani jikon, domin sai ta kammala idda ba kuma a gidanshi ba, sannan sai ta auri wani mijin ya dan-daneta ta dan-daneshi tasu ta hadasu sun rabu ko ya rasu sannan ya fito cikin 'yan-takara, dirkashi! Domin Allah maigirma da daukaka yana cewa " To idanfa ya saketa (saki na uku) bata halatta a gareshi hassaita auri wani mijin da ban" Suratul-Bakara, aya ta : 230. Kuma bayani ya tabbata daga Ma'akin Allah cewa saisun dan-dani juna. idan kai laka'ari ai anbashi damar yabi a hankali amma yai gaggawa, zaka ga wani duka biyun yake yi lokaci guda wani ukumma kwata-kwata kenan (malam mai gaba daya) sannan ya zo yana neman wai malamai su yi mishi fatawar yiwuwar dawo da ita, dankari!. Yanzudai saki ya auku to menene abinyi?
  Idda

  Idan sakin da akai bai wuce daya ko biyuba to matar zatai iddar ta ne a dakinta, bai halatta miji ya fitar da ita daga dakin, balle har ya watso mata kayan ta waje ko ya dakko mota akwashe mata kayanta, ko kuma ita tace ai tana da gidan ubanta bari ta tafi da dai sauran irin wadannan kazaman maganganu da musulunci bai amince da su ba, Allah Yana cewa " Kada ku fitar da su daga dakunan su, su kuma kada su fita sai dai idan sunzo da wata alfasha bayyananniya, dukkan wadannan dokokin Allah ne kada ku ketare su, dukkan wanda ya ketare dokokin Allah tofa hakika ya zalinci kanshi" Suratut-Talaq, aya ta :1, to anan zakaga lalle irin yadda ake gudanar da rabuwar aure hakika abin yana bukatar gyara sosai wannan fa gamu musulmai da muka yadda da dokokin da Allah ya dora mana, ya Allah ka yafe mana, kuma ya Allah kada ka kamamu da abinda wawayencikimmu suka aikata, amin. Me cece hikimar yin hakan mace tai idda a cikin dakinta? Hikimar Idda a dakin aure.  Lalle ne dukkan abinda Allah madaukakin Sarki ya tsara mana akwai hikimomi da alherai masu yawa agaremu munsani ko bamu sani ba, kuma ba'a dora mana cewa dole sai munsan hikimar hakan kafin mu ai watar da abida aka umarce mu. Tabbas mutuminda ya rabu da medakinshi ta hanyar saki yada ko biyu, matar shi ce fa , domin inka lura ai ba zaka bar wani ya zo zawarciba, inkuma ka rasu a wannan lokacin kafin ta kamma idda zata gajeka, kuma zatai maka takaba (kamar yadda ya gaba a makalarmu metaken Takaba a musulunci) to anan tunda tana Idda a gidanka zaka dawo da ita aduk lokacin da kaso ba tare da ansake daura aureba domin bata kamala Iddaba, kuma ba saika ta tuttura masu bikoba, wannan shi ne ma'anar fadin Allah daya ke cewa "Baka sani ba ana fatan Allah ya kawo wani sabon al'amari" Suratut-Talaq, aya ta :1, to amma sai wannan damar da Maigirma da daukaka ya bamu itama ana wasa da ita, bayan da mutun ya sabawa Mahaliccin shi sannan matar tana nema ta gagareshi, galibi kuma alokacin ba wacce yake so inba itaba, dabara kaga tana neman ta karewa kada. Saidai kamar yadda ishara ta gabata a baya matar da zatai idda a dakinta itace matar da saki daya ko biyu ya rabasu amma matar da saki ukune nan ba magar yin idda a dakinta, saigida!. Saidai akwai abin tanbaya anan shin akowanne lokaci ya halatta mutun ya rabu da medakin shi?.


  Lokotan Saki da musulunci ya amince da su.  Anan nake ceawa lalle yana daga cikin irin gatan da musulunci ya nuna mana cewa ba'a sakin mace lokacin da take cikin al'ada. Kuma idan mutun ya aiwatar da sakin ta saku kuma dole ya mayar da ita cikin matanshi, inyaki kuma alkali ya hukunta shi, sabo da Sayyidina Umar Allah ya kara masa yarda ya tambayi Ma'aikin Allah Tsirada amincin Allah su tabbata agareshi, cewa danshi Abdullahi ya saki matar tana ckin al'ada. Sai Ma'aikin Allah ya umarci Sayyidina Umar daya umarci dannashi Abdullahi ya dawo da ita, sannan tana karkashinshi hassai ta kammala wannan al'adar ta sakeyin wata ta kammala sannan in yaga yiwuwar ya saketa sai ya saketadin, kuma aka lissafa wannan sakin cikin sakinna shi, Bukhari ya ruwaito wannan hadisin kuma shine hadisi na : 4908, 5252 ,5253 da Muslim. To idan mutun ya saki matarshi shikenen ba dai za'a raba kirki da itaba, ma'ana bata cikin matan da za'ai karba-karban girki da su, to haka za'a kyaleta? A'a za'a bata :


  Kwabo kashewa.  Yana daga cikin hakkin dukkar matar da mijinta ya saketa da ya bata kwabon batarwa, wannan shine malamai suke kira Mut'atuttalaq, domin zata sai sabulu omo katin waya da dai sauransu, musulunci bai kayyade gwargwadon nawa za'a bayarba saidai ya fadi a wurare da dama kowa zaiyine daidai karfinshi, sabo da haka mutumin da yake da damar yaba wacce ya saka Naira dubu 40, misali sai yabata N 10,000, wannan bai yiba sai ya cika ko ta kaishi koto, haka kuma mutumin da bashi da karfin haka baya taba halatta a tilasta mishi sai ya bayar da hakan, musulunci cewa yayi kowa daidai karfin shi, Allah yana cewa cikin Suratul-Bakara aya ta :236 "Kuma ku jiyar da su dadi, me yalwa gwargwadon karfinshi, kuma mara yalwar arzikima gwargwadonshi" ayoyi akan baiwa matar da aka saka kudin kashewa sun memetu a wannan surar aya ta :241 da Suratul-Ahzab,aya ta :28 data 49, duk wadannan suna daga cikin dinbin ayoyin Alkur'ani mai girma da suke ceto mata daga cikin bakin kangin da suka sami kansu a tsarin da bana musulunci ba. kasancewar al'amarin rabuwar aure ba haka yake sakakaba. Kamar yadda alokacin daurin auren saida aka sami shaidu to hakama lokacin rabuwar saida musulunci yabada umarnin.
  Shaidawa Dattijai biyu  Abin sanine cewar Dattijai yana nuna mutanan kwarai mutane masu mutunci masu yawan shekaru ko masu matsakaicin shekarune muddin sunkai shekarun girma da sanin ya kamata, saboda haka musulunci yabada umarni shaidawa akalla Dittijai biyu domin tabbatar da saki nawa akai kuma nawa ya rage, amma inba hakaba sai aita gardaddami akan nawa ya auku kuma nawa ya ragedin, Allah Maigirama da daukaka yana cewa " Kuma ku shaidawa Adilai biyu daga cikinku, ku tsayar da shaidar domin Allah" Suratut-Talaq, aya ta:2. to kan lalle akwai kulawar musulunci cikin dukkanin motsi da juyi da Dan-adam yake yi, ya Allah ka tabbatar damu akan wannan addini naka amin.


  Kome \ Biko.


  Kome kamar yadda bayanai suka gabata yana kasancewa ne lokacin da mutum ya rabu da medakinshi ta sanadiyyar saki daya ko biyu, anan mutun ke kokawar yaga ya mayar da matarshi, amma idan ya kasance sakin saki ukune to kan ai ba maganar biko balle kome. Shi wannan al'amari na kome yana faruwane kafin matar ta kammala Idda, amma idan ta kammala Idda tofa saidai da sabon aure tunda sakin baikai ukuba, amma indai ya kai uku to sai ta yi sabon aure, saboda haka tunda saki dayane ko biyu kuma ta kammala idda bai dawo da itaba to yanzu sai ya fito cikin 'yan-takara, idan Allah ya sa ya kai labari to idan kuma ya sha kaye sai hakuri. Amma idan bata kammala Iddaba to mijin shi ke da damar ya mayar da ita ba tare da wani ya yi kaka gida cikin lamarinba muddindai sunyi nufin gyara(wato miji da mata) Allah Maigirma da daukaka yana cewa "Kuma mazajansu sune mafi cancantar su mayar da su (matansu) matukar sunyi nufin gyara" Suratul-Bakara, aya ta : 228, wannan shike nuna cewa duk lokacin da miji ya mayar da matar muddin akwai nufin gyara babu wani ta koma kawai.
  KammalawaDaga dukkanin bayanan da suka gabata bayanai sun bayyana karara na gata da jinkai da musulunci ya yi mana, domin babu wani tsari a duniya da yake da irin wannan al'amari filla-filla ya fayyace tsakanin zare-da-abawa, musammamama mata, domin zakaga duk wani tsari da ba musulunci ba to bautar dasu yake kai tsaye ko a fakaice, amma lalle musulunci ya yi mata gata saidai idan ta jahilceshi wannako babbar cuta ce, Allah ya tsaremu amin.


  Gabatarwa:Bayanda a kasidar data gabata mukai

  takaitaccan bayani kan yadda musulunci ya tsara yadda ya kamata rabuwar aure ta kasance, da kuma yadda ya baiwa ko wanne bangare na ma'aurata 'yancinshi, da kuma yadda bayanai suka gabanata na cewa babu wani tsari da yayiwa mabiyanshi irin wannan tsarin inba musulunci ba. to ayau za muyi bayani abinda Allah Maigirma da daukaka ya sawwake mana na yadda Idda kuma zata kasance bayan anyi saki ko anrasu Allah yai mana jagora amin, asha karatu lafiya.
  Kadan daga Hikimomin Idda.  Yana daga cikin hikimomin da Allah ya sanya cikin Idda kada adauki dan-wani gida akai wani gidan, domin idan mutun ya rabu da maidakinshi takan yiwu a wannan makon ansami juna-biyu, idan tai aure batare da yin iddaba bayan kwana biyu ko uku ko makamantansu da sakinta shikenan ta tauki dan-mijinta na farko ta kai gidan mijinta na biyu wanda yake wannan bakaramin zunubi bane da barna a harkokin zamantakewarmu, saboda haka musulunci ya tabbatar da cewa ba zatai aure na biyuba sai antabbatar da bata da juna biyu saboda haka aka shar'anta takaba, saidai kawai idan aka saketa kafin asadu to awannan lokacin babu wata Idda da zatayi, kamar yadda bayanai zasu zo nan gaba kadan idan Allah ya yarda. Haka kuma yana daga cikin Shar'anata Idda fatan bijin ya maida ita matar ta shi kafin ta kammala iddar idan sakin baikai ukuba, kamar yadda bayani ya gabata a makalar farko inda muka kawo fadin Allah Maigirma da daukaka " Baka saniba ana fatan Allah ya aiwatar da wani al'amari" Suratut-Talaq, aya ta 1, domin ba din da iddarba da shikenan kana sakinta yau gobe sai wani ya aura taimaka Fintinkau. Kazalika yana daga cikin manufofin yin Idda juyayin megidanta daya rasu ko dako basu taba saduwaba, kamar yadda bayani ya gabata arubummu metaken "Takaba a Musulunci". Saboda haka ko iyanan muka dakata kasan Allah Maigirma da taukaka ya sanya hikimomi masu tarin yawa cikin Idda, munsan su duka ko bamu sansu ba. Allah mungode maka.


  Karkasuwar Idda a musulunci.  Idda ta kasu kashi biyu a musulunci, wato Iddar mamaci wacce muke ce mata takaba, da kuma Iddar Saki. Itadai iddar mamaci\Takaba mungudanar da bayanai akanta, saboda haka awannan karon bayanai zasu kasance ne kan "Iddar Saki"! Allah yai mana jagora amin,
  Karkasuwar mata

  Da farko yana dakyau mufahimci cewa mata sun kasu kashi-kashi lokacin da
  zasu rabu da mazajansu, saboda haka ko dole iddarsu tasha ban-ban, anan zamu fahimci mutun zai iya rabuwa da matanshi biyu ko uku lokaci guda amma wata ta riga wata kamma Idda. Yanzu ga kasha-kashannasu :


  (1) Mace me juna biyu : Alokacin da mutun ya rabu da medakinshi tana da juna biyu to ita Iddarta itace ta sauke abindake cikinta, ma'ana inda zai saketa da karfe 5:00 na yamma sai ta haihu karfe 5:20 na yammar shikenan ta kammala iddarta inta sami wanda zata aura aranar ya yi sai adaura auren da 6:00 na yammer. Yanzu ya zama dan-kallo, saidai kawai idan ya kuru Allah ya taimakeshi saki daya ne ko biyu, sai ya bogo fasta ya shiga cikin 'yan-takara wata kila ya samu ya kai labari. Allah yana cewa " Kuma wadanda suke da juna-biyu to lokacin (kammala Iddarsu shi ne ) su sauke abinda suke dauke dashi" Suratu-Talaq, aya ta :4, hakanan kuma inda zasu rabu juna biyunnata bai huce wata dayaba saidai ta haife abinda take dauke dashi, kamar yadda wannan bayanin ya gabata a ' Takaba a Musulunci' mun dan fadada bayanai a lokacin.


  (2) Mace meganin Al'ada. Itakuma matar da take ganin al'adarta iddarta itace samun tsarki uku, saboda haka idan mutun ya rabu da maidakin shi, iddarta itace ta yi tsarki uku, shi kuwa tsarki uku ya sha ban-ban da wata uku, domin mace zata iya tsarki a kwanakin da suke kasa da wats uku, haka kuma zata iya iya tsarki uku a watannin da suke sama da haka, akwai matar da ashekara sau daya take yin al'ada to kaga wannan iddarta zata tasamma shekaru kenan. Allah yana cewa " Dukkani matan da aka sakesu zasu zauna da karankansu (suna jiran) tsarki uku" Suratul-Bakara, aya ta: 228 Idan kuma tana cikin lissafa al'ada sai ya bayyana tana da juna-biyu, to anan iddarta zata koma iddar mai juna biyu saitai zaman haihuwa (Allah ya sauke ta lafiya amin).


  (3) Mace mara ganin al'ada. Matan da basa ganin al'ada sun kasu kashi biyu, kashi na farko: basagin al'adane saboda yarinta ma'ana batakai lokacin al'adaba gashi mijinta ya rabu da ita, sai kashi na biyu :wadanda basa ganin al'ada saboda tsufansu don sun wuce lokacin al'ada. To wadannan matan da basa ganin al'ada ko saboda karancin shekaru ko kuma saboda angirma, iddarsu itace su lissafa wata uku. Alllah Madaukakin sarki yana cewa " Kuma matayen da suka debe tsammani daga al'ada daga matanku idan abin ya rikice musu to iddarsu itace wata uku, da kuma ma wadanda basu fara ba" Suratut-Talaq, aya ta :4.


  (4) Macan da ka rabuda ita kafin Tarewa. Ita matar da aka rabu da ita kafin su san junansu ita da mijin, babu wata idda da zata yi, kawai inta sami wani alokacin sai adaura aure, (sabanin rasuwa idan rasuwa mijin ya yi kafin su tare za tai takaba). Domin Allah yana cewa " Ya ku wadanda sukai Imani, idan kuka auri mata mummunai sannan kuka sake tun kafin ku sadu da su, ba ku da wata idda a kansu (matan) da za su yi" Suratul-Ahzab, aya ta :49.
  Kammalawa. Ina fatan cikin wannan dan takaitaccan bayanan da suka gabata sun dan warware mana madansu al'amurran da suka shafi Idda, da kuma irin yadda musulunci ya haskaka mana rayuwarmu. Ni ina bada shawara ga dukkan wanda wadansu al'amurran addini suka shamasa kai, da kada yai kasa agwiwa ya garzaya makaranta ya yi tanbaya, masu iya maga suce 'Tambaya mabudin ilimi, amma azauna haka ko unkula gaskiya ba zai haifadda Da me ido ba, kuma wadansu hakkokinshi da damar da musulunci ya bashi ba zai sansu ba. Allah yai mana jagora kuma ya tabbar da dugadugammu kan wannan addin amin.

  Rbutawa :

  Malan Aliyu Muhammad Sadisu