RUKUNAN MUSULUNCI

أركان الإسلام بلغة الهوسا

بسم الله الرحمن الرحيم

DA SUNAN ALLAH MAI YAWAN RAHAMA MAI MATU{AR JIN {AI

Yabo da godiya duka na Allah ne, salati da salami su tabbata ga Annabin da babu wani annabi bayansa, Annabinmu Muhammadu ]an Abdullahi.

Bayan haka, ha}i}a ya]a ilimummukan addini yana da tasiri mai }arfin gaske cikin bayyana ha}i}anin musulunci da tabbatar da ginshi}ansa da ma ciyar da al'umma gaba cikin rayuwarta. Wannan babbar manufa kuwa ita ce manufar da jami'ar Musulunci ta Madina take kai gwauro ta kai mari domin ganin an cin mata gwargwadon iko, ta hanyar da'awa da karantarwa.

A cikin nasa }o}arin na ganin an cin ma wannan burin, sashin nazarin binciken ilimi na jami'ar ya }ir}iro aikace-aikace daban-daban masu manufa a fagen na ilimi, wanda daga cikinsu har da akwai wasu tsararrun rubuce-rubuce kan musulunci da kyawawan siffofinsa, da nufin ya]a su domin kwa]ayinsa na yi wa 'ya'yan wannan al'umma ta musulunci guzuri mafi aminci kuma mafi inganci a ilimin musulunci; ta ~angaren a}ida da ~angaren shari'a.

To wannan rubutun ma da muke gabatarwa game da "Rukunan Musulunci" ]aya ne daga cikin tsare-tsaren wannan sashi; domin shi ne ya gayyaci malaman da suka rubuta shi -daga cikin malaman wannan jami'a- sannan kuma ya ]ora wa 'yan kwamitin ilimi da ke }ar}ashinsa da su yi bitar rubutun wa]ancan malaman gami da gyara shi da kuma tsara shi har  ya fito cikin surar da ta dace da manufofin wannan sashe, tare da mai da kai sosai wajen ha]a kowacce mas'ala da dalilanta. Manufar wannan rubutu dai a wajen sashen ilimi ba wata manufa ba ce illa sau}a}awa 'ya'yan musulmi hanyar samun ilimin addini mai amfani, wannan shi ya sa ya nemi a fassara masa wa]annan littattafan zuwa harasa daban-daban na duniya; domin ya]a su da kuma sa su cikin gizo-gizon sadarwa ta duniya (wato internet).

To muna dai ro}on Allah Mai girma da ]aukaka Ya saka wa hukumar Masarautar larabawa ta Saudiya mafi alherin sakamako kuma mafi cikarsa saboda }o}arin da take yi wajen yi wa musulunci hidima da ya]a shi da kuma kare shi, da kuma irin abin da wannan jami'a take samu daga wajenta na kulawa da taimakawa.

Muna kuma ro}on Allah Mai yawan albarka da ]aukaka da Ya amfanar da mutane da wannan littafi, Ya kuma datar da mu wajen buga sauran aikace-aikacen ilimi na wannan sashe don baiwarSa da karamcinSa Ma]aukaki, kuma muna ro}onSa da Ya datar da mu baki ]aya zuwa ga aikata abubuwan da Yake so kuma Yake yarda da su, Ya kuma sa mu daga cikin masu kira zuwa ga shiriya tare da taimakawa gaskiya.

Allah Ya }ara salati da salami da albarka ga BawanSa, AnnabinSa Muhammadu tare da 'yan gidansa da sahabbansa baki ]aya.

SASHEN BINCIKEN ILIMI


 Rukuni Na Farko: Shaidawa Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai Allah, Kuma Muhammadu Manzon Allah ne

Wa]annan kalmomin shahada guda biyu, sune kofar shiga musulunci, sune kuma rukuninsa mafi girma, kuma ba a yin hukunci da musulusncin mutum, sai da furuci da su, da kuma aiki da abin da suka }unsa, da wannan ne kuma kafiri yake zama musulmi.

 1-Ma’anar kalmar shahada:

Ma’anar shaidawa da cewa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi ne yin furuci da ita tare da  sanin ma’anarta, da kuma yin aiki da abin da ta }unsa, zahiri da ba]ini, malamai sun ha]u akan cewa furuci da kalmar shahada, ba tare da sanin ma’anarta ko yin aiki da abin da ta }unsa ba, ba shi da amfani, kai sai  dai ma ta zama hujja a kansa, kuma ma’anar (La Ilaha Illallah) shi ne babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi ka]ai matsarkaki ma]aukaki. 

Rukunan wannan kalmar (shahada) sune: (korewa da tabbatarwa), wato kore ha}}in bauta daga wanin Allah, kuma tabbatar da shi ga Allah shi ka]ai ba shi da abokin tarayya. Haka kuma wannan kalmar ta }unshi kafircewa [agutu (shi ne dukkannin abin da ake bauta masa wanda ba Allah Ma]aukaki ba, ko da kuwa ya kasance mutum ne (tare da yardarsa da bautar da ake masa), ko dutse, ko bishiya, ko son zuciya, ko sha’awa), da nuna masa }iyayya da yin kubuta daga gare shi.Wanda ya fa]i wannan kalmar (shahada da bakinsa) amma bai kafircewa abubuwan da ake bauta musu wanin Allah ba (a aikace), to tamkar bai fa]eta ba.

Allah Ma]aukaki ya ce:

]  وَإِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ لا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الرَّحْمَنُ الرَّحِيمُ[ [البقرة:163]

“Kuma abin bautarku abin bauta ne guda ]aya. Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Mai rahama Mai jin }ai”.(Ba}ara: 163).

Kuma Ma]aukaki ya ce:

] لا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ قَدْ تَبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنَ الْغَيِّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِنْ بِاللَّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى لا انْفِصَامَ لَهَا وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ  [[البقرة: 256]

“Babu tilastawa game da (shiga) addinin (musulunci), ha}i}a shiriya ta bayyana daga ~ata, saboda haka wanda ya kafirce wa [agutu kuma ya yi imani da Allah, to ha}i}a ya ri}i igiya amintacciya, (wadda) ba ta yankewa. Allah kuwa Mai ji ne, Masani ne”. (Ba}ara: 256)

Kuma kalmar (Ilah) tana nufin abin bautawa da gaskiya, duk wanda ya kudurci cewa abin da ake nufi da kalmar (Ilah) shi ne: Mai halitta, Mai arzutawa, ko Wanda yake da ikon kirkira, kuma ya kudurci cewa yin imani da wannan kawai zai wadatar, ba tare da ka]aita Allah da ibada ba, to ha}ika fa]in kalmar (La Ilaha Illallahu) ba za ta amfane shi ba, a nan duniya wajen shiga Musulunci, kuma a Lahira ba zata kubutar da shi ba daga azaba madawwamiya.

Allah Ma]aukaki ya ce:

  قُلْ مَنْ يَرْزُقُكُمْ مِنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ أَمَّنْ يَمْلِكُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَمَنْ يُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ الْمَيِّتَ مِنَ الْحَيِّ وَمَنْ يُدَبِّرُ الْأَمْرَ فَسَيَقُولُونَ اللَّهُ فَقُلْ أَفَلا تَتَّقُونَ[  [يونس:31]  

“Ka ce (da su): “Wane ne yake arzuta ku daga sama da }asa? ko kuma wane ne yake mallakar ji da gani?, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wane ne kuma yake tsara al’amura?” To za su ce: “Allah ne”. To ka ce (da su): yanzu ba za ku ji tsoronsa ba?” (Yunus: 31).

Allah Ma]aukaki ya ce:

]أَمَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَأَنْزَلَ لَكُمْ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَنْبَتْنَا بِهِ حَدَائِقَ ذَاتَ بَهْجَةٍ مَا كَانَ لَكُمْ أَنْ تُنْبِتُوا شَجَرَهَا أَإِلَهٌ مَعَ اللَّهِ بَلْ هُمْ قَوْمٌ يَعْدِلُونَ[ [النمل:60]

 “Ko wane ne ya halicci sammai da }assai, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan (da wannan ruwan) muka tsirar da (shukokin) gonaki masu }ayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba?, shin akwai wani abin bautawa tare da Allah, A’a, su dai mutane ne da suke kauce wa (gaskiya). (Naml: 60).

Kuma Allah Ma]aukaki ya ce:

]وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ مَنْ خَلَقَهُمْ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ فَأَنَّى يُؤْفَكُونَ[ [الزخرف:87]

“Kuma lallai idan ka tambayesu, “Wane ne ya halicce su?, Lallai za su ce: “Allah ne” To, yaya ake juyar da su (daga bauta wa Allah)?” (Zukhruf: 87).

 Sharru]an Kalmar Tauhidi:

1.                      Sanin ma’anarta (wajen korewa da tabbatarwa), sani wanda ya ke kore jahilci, wato sanin cewa kalmar tauhidi, tana nufin kore bauta daga wanin Allah, da kuma tabbatar da ita ga Allah shi ka]ai, ba shi da abokin tarayya, kuma babu wani da ya cancance ta sai shi.

2.                      Ya}ini mai kore shakku, wannan kuwa shi ne mutum ya yi furuci da ita, alhali zuciyarsa tana mai nutsuwa da ita, tana mai yin yakini da abin da ta }unsa, yakini wanda yake yankakke.

3.                      Kar~a mai kore watsi da ita, wato mutum ya kar~i dukkannin abubuwan da wannan kalmar ta }unsa, da zuciyarsa da harshensa, sai ya gaskata labaran (da Allah da Manzonsa su ka ambata), ya bi umarni, kuma ya nisanci hani, ba zai kuma tinkari nassosin (Al}ura’ni da hadisi) ba ya yi watsi da su ko ya yi musu ta’awili.

4.                      Mi}a wuya wanda yake kore bijirewa, wannan kuwa shi ne  mutum ya mi}a wuya ga abin da wannan kalmar ta }unsa a fili da a ~oye.

5.                      Gaskatawa mai kore }aryatawa, wannan kuwa shi ne bawa ya fa]eta da gaske a cikin zuciyarsa, ta yadda abin da ke cikin zuciyarsa zai da ce da abin da yake furtawa da harshensa, zahirinsa kuma ya da ce da ba]ininsa.

Wanda ya yi furuci da kalmar shahada da harshensa, amma ya musanta abin da ta }unsa da zuciyarsa, To ,ha}i}a wannan ba zai amfane shi ba, halinsa daidai yake da halin munafikai wa]anda harsunansu ke furuci da abin da ba ya cikin zukatansu.

6.      Ikhlasi (tsarkakewa) wanda yake kore shirka, wannan kuwa shi ne bawa ya tantance aikinsa na ibada da nagartacciyar niyya, daga dukkannin abubuwan da suke da dangantaka da shirka.

Allah Ma]aukaki ya ce:

]وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ[ [البينة: 5]

“Ba a kuma umarce su ba sai don su bautawa Allah, suna masu tsarkake addini gare shi, masu karkata zuwa ga addinin gaskiya” (Bayyina:5).

7.    So mai kore }iyayya, wannan kuwa zai kasance ne idan bawa ya so wannan kalmar da abin da ta }unsa, da masu fa]inta wa]anda suke lazimtar sharru]anta, ya kuma nuna }iyayya ga duk wani abu da kan iya warware wannan. Kuma alamar hakan ita ce  bawa ya gabatar da son Allah (a kan komai) ko da ya sa~awa son zuciyarsa, da nuna }iyayya ga dukkan abin da Allah ya }i, ko da son zuciyarsa ta karkata zuwa gare shi, kuma da }aunar wanda yake }aunar Allah da Manzonsa, da yin gaba da wanda yake gaba da Allah da Manzonsa.

Allah Ma]aukaki ya ce:

]قَدْ كَانَتْ لَكُمْ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ فِي إِبْرَاهِيمَ وَالَّذِينَ مَعَهُ إِذْ قَالُوا لِقَوْمِهِمْ إِنَّا بُرَآءُ مِنْكُمْ وَمِمَّا تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ كَفَرْنَا بِكُمْ وَبَدَا بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمُ الْعَدَاوَةُ وَالْبَغْضَاءُ أَبَداً حَتَّى تُؤْمِنُوا بِاللَّهِ وَحْدَهُ[ [الممتحنة: 4]

“Ha}i}a kyakkyawan abin koyi ya kasance a gare ku game da (Annabi) Ibrahim da wa]anda suke tare da shi, lokacin da suka ce da mutanensu, “Ha}i}a mu babu ruwanmu da ku, da kuma abin da kuke bauta wa koma bayan Allah, mun kafirce muku, kuma }iyayya da gaba sun bayyana tsakaninmu da ku har abada, sai sanda kuka yi imani da Allah shi ka]ai) (Mumtahana:4).

Kuma Allah  Ma]aukaki ya ce:

]  وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَتَّخِذُ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَنْدَاداً يُحِبُّونَهُمْ كَحُبِّ اللَّهِ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَشَدُّ حُبّاً لِلَّهِ [ [البقرة: 165]

“Kuma akwai wasu mutane da ke ri}on abokan tarayya koma bayan Allah, suna son su kamar son Allah, (amma) kuma wa]anda suka yi imani sun fi tsananin son Allah” (Ba}ara:165).

Wanda ya fa]i (La Ilaha Illallahu) da ikhlasi da ya}ini, kuma ya kubuta daga babbar shirka da }arama, kuma ya kubuta daga bidi’o’i da zunubai, to ha}i}a ya samu shiriya a duniya, da aminci daga azaba, wuta  kuma ta haramta a gare shi.

Kuma ya wajaba a kan bawa ya cika wa]annan sharru]a, wato ya zamanto suna tare da bawa wajen ayyukansa, kuma ya lazimce su, ba tilas ba ne sai ya haddace su da ka.

Wannan kalma mai girma (La Ilaha Illallahu) ita ce Tauhidul Uluhiyya (ka]aita Allah da bauta), Tauhidul Uluhiyya kuma shi ne mafi muhimmancin nau’oin Tauhidi, wanda a kansa ne sa~ani ya auku tsakanin Annabawa da mutanensu, domin tabbatar da shi ne kuma aka aiko da Manzonni, kamar yadda Allah Ma]aukaki ya ce:

]وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولاً أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ[ [النحل: 36]

 “Ha}i}a mun aiko manzo a cikin kowace al’uma cewa: “ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci [agutu” (Nahl: 36).

Kuma Allah Ma]aukaki ya ce:

]وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ مِنْ رَسُولٍ إِلاّ نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لا إِلَهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ[  [الأنبياء: 25]

“Kuma ba wani manzo da muka aiko gabaninka face sai mun yi masa wahayi cewa: babu wani abin bauta wa sai Ni, to sai ku bauta Mini” (Anbiya: 25).

Duk sanda aka ambaci kalmar tauhidi kawai, abin nufi shi ne Tauhidul Uluhiyya.

Ma’anarsa:

 Tauhidul Uluhiyya shi ne tabbatar da cewa lallai Allah shi ne abin bauta a bisa dukkannin halittarsa, da ka]aita shi da bauta shi ka]ai ba shi da abokin tarayya.

Sunayensa:

Ana kiran wannan nau’i na tauhidi da Tauhidul Uluhiyya ko Ilahiyya domin an gina shi a kan tsarkake tsananin so ga Allah shi }adai. Kuma an kira shi da wa]annan sunaye masu zuwa:

1-                     Tauhidul ibada: domin an gina shi a kan tsarkake ibada ga Allah shi }adai.

2-                     Tauhidul irada: domin an gina shi a kan neman yardar Allah da ayyuka.

3-                     Tauhidul }as’d: domin an gina shi a kan tsarkake niyya wadda za ta kai ga tsarkake ibada ga Allah shi }adai.

4-                     Taihidul ]alab: domin an gina shi a kan tsarkake neman (biyan bukata) daga Allah Ma]aukaki.

5-                     Tauhidul amal: domin an gina shi a kan tsarkake ayyuka ga Allah Ma]aukaki.

Hukuncinsa:

Tuhidul Uluhiyya wato ka]aita Allah cikin bauta; farilla ce a kan bayi, ba za su shiga musulunci ba sai da shi, kuma ba za su tsira daga wuta ba, sai da }udurce shi da yin aiki da abin da ya }unsa, kuma shi ne farkon abinda ya ke wajaba a kan bawa (balagagge mai hankali)  }udurce shi da aikata shi, kuma shi ne farkon abin da yake wajaba wajen kira zuwa ga tafarkin Allah da karantarwa, ba kamar yadda wasu suke ganin wanin haka ba. Kuma dalili a kan farlancinsa shi ne yin umarni da shi a cikin Al}ur’ani da sunna, kuma kasancewar  lallai Allah ya halicci halitta kuma ya saukar da littatttafai saboda shi.

Allah Ma]aukaki ya ce:

] قُلْ إِنَّمَا أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ اللَّهَ وَلا أُشْرِكَ بِهِ إِلَيْهِ أَدْعُو وَإِلَيْهِ مَآبِ[ [الرعد: 36]

“Ni dai an umarce ni ne kawai in bauta wa Allah, kada kuma in tara wani abu da Shi, kuma zuwa gare Shi kawai nake kira, kuma zuwa gare Shi ne kawai makomata take” (Ra’ad: 36).

Kuma ya ce:

]وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْأِنْسَ إِلاّ لِيَعْبُدُونِ[ [الذاريات :56]

“Ban kuma halicci mutane da aljanu ba sai don su bauta Mini” (Zariyat: 56).

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce wa Mu’az Allah ya yarda da shi:

»إنك تأتي قوما من أهل الكتاب فليكن أول ما تدعوهم إليه شهادة أن لا إله إلا الله، فإن هم أطاعوك لذلك فأعلمهم أن الله افترض عليهم خمس صلوات في كل يوم وليلة؛ فإن هم أطاعوك لذلك فأعلمهم أن الله افترض عليهم صدقة تؤخذ من أغنيائهم فترد على فقرائهم…« أخرجه البخاري ومسلم

 “Ha}i}a za ka je wurin wasu mutane ne daga cikin ma’abotan littafi, saboda haka shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ya kasance farkon abin da zaka kira su zuwa gare shi, idan suka yi maka biyayya a kan haka, to ka sanar da su cewa Allah ya farlanta musu salloli biyar cikin ko wane yini da darensa, idan suka yi maka biyayya a kan haka, to ka sanar da su cewa Allah ya farlanta musu zakka wadda za a kar~a daga mawadatansu a baiwa matalautansu…” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Tauhidul Uluhiyya shi ne mafificin ayyuka a kowane hali, kuma shi ne mafi girman ayyuka wajen kankare zunubai. Ha}i}a Bukhari da Muslim sun ruwaito daga hadisin Itban Allah ya yarda da shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»فإن الله حرم النار على من قال لا إله إلا الله يبتغي بذلك وجه الله«

 “Lallai Allah ya haramta shigar wuta ga wanda ya fa]i La Ilaha Illallahu yana neman yardar Allah da haka”.

 Ha]uwar Manzonni A Kan Kalmar Tauhidi:

Dukkannin Manzonni sun ha]u a kan kiran mutanensu zuwa ga kalmar (La Ilaha Illallahu), da tsorotar da su daga kauda kai daga gareta kamar yadda Al}ur’ani mai girma ya bayyana haka cikin ayoyi da dama, Allah Ma]aukaki ya ce:

]وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ مِنْ رَسُولٍ إِلاَّ نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لا إِلَهَ إِلاَّ أَنَا فَاعْبُدُونِ[ [الانبياء:25]

“Kuma ba wani manzo da muka aiko gabaninka face mun yi masa wahayi cewa: babu wani abin bauta wa sai Ni, to sai ku bauta Mini” (Anbiya: 25).

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya buga misali game da ha]uwar Manzonni wajen kira zuwa ga kalmar (La Ilaha Illallahu), yayin da ya bayyana cewa su Manzonni ‘yanuwa ne daga uba ]aya, amma uwaye dabam – daban, kuma addininsu ]aya ne, wato asalin addininsu ]aya, shi ne Tauhidi, ko da rassan shari’o’insu sun bambanta; kamar yadda ‘yaya su kan bambanta wajen uwayensu amma ubansu ]aya.

 Ma’anar Shaidawa Lallai Muhmmadu Manzon Allah ne:

Ma’anar shaidawa lallai (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne shi ne a yi masa biyayya cikin abin da ya umarta, da gaskatashi a kan abin da ya ba da labari, da nisantar abin da ya hana kuma ya yi tsawa a kansa, kuma ba za a bautawa Allah ba sai da abin da ya shar’anta.

 Tabbatar Da Shaidawa Lallai Muhammadu Manzon Allah ne:

Shaidawa lallai (Annabi) Muhammdu Manzon Allah ne tana tabbata ne da yin imani da cikakken ya}inin cewa lallai (Annabi) Muhammdu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bawan Allah ne kuma Manzonsa ne ya aiko shi zuwa ga Aljanu da mutane gaba ]ayansu, kuma lallai shi ne cikamakin Annabawa da Manzonni, kuma shi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bawa ne makusanci a gurin Allah ba shi da komai daga siffofin Allah, kuma (wannan shaidar tana tabbata ne) da yi masa biyayya da girmama umarninsa da haninsa, da lazimtar sunnarsa a baki, a aikace, kuma a }udurce. Allah ya ce:

]قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعا[ [الأعراف: 158]

“Ka ce: ya ku mutane lallai ni Manzon Allah ne zuwa gare ku gaba ]aya” (A’araf: 158).

Kuma ya ce:

]وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا كَافَّةً لِلنَّاسِ بَشِيراً وَنَذِيراً[ [سـبأ: 28]

“Ba mu kuma aiko ka ba face zuwa ga mutane baki ]aya, kana mai garga]i da bushara” (Saba’a: 28).

Kuma ya ce:

]مَا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَا أَحَدٍ مِنْ رِجَالِكُمْ وَلَكِنْ رَسُولَ اللَّهِ وَخَاتَمَ النَّبِيِّينَ[ [الأحزاب:40]

(Annabi) Muhammadu bai kasance uban ]aya daga mazajenku ba, sai dai (shi) Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa” (Ahzab: 40).

Kuma ya ce:

]قُلْ سُبْحَانَ رَبِّي هَلْ كُنْتُ إِلاَّ بَشَراً رَسُولاً[ [الإسراء: 93]

“Ka ce tsarki ya tabbata ga Uabangijina, ni ba kowa ba ne face mutum kuma Manzo” (Isra’i : 93).

Wannan (tabbatar da shaidawa Annabi Muhammadu ManzonAllah) ya }unshi al’amura kamar haka:

Na farko: yarda da Manzoncinsa da }udurceshi a ~oye cikin zuci.

Na biyu: yin furuci da haka da harshe a bayyane.

Na uku: koyi da shi da yin aiki da abin da ya zo da shi na gaskiya, da barin abin da ya hana na }arya. Allah Ma]aukaki ya ce:

]َفَآمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ النَّبِيِّ الْأُمِّيِّ الَّذِي يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَكَلِمَاتِهِ وَاتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ[ [الأعراف: 158]

“Sai ku yi imani da Allah da Manzonsa, Annabi Ummiyyi([1]) wanda yake imani da Allah da kalmominsa, kuma ku bi shi don ku shiriya” (A’araf: 158).

Na hu]u: gaskatashi a kan dukkan abin da ya ba da labarinsa.

Na biyar: Mutum ya so shi sama da son kansa da dukiyarsa da ]ansa da mahaifinsa da mutane baki ]aya; domin shi Manzon Allah ne, kuma ha}i}a sonsa yana daga cikin son Allah, da so saboda Allah

Ha}i}anin son Manzon Allah shi ne yi masa biyayya wajen bin umarninsa da nisantar haninsa da taimakonsa da jibintarsa. Allah ya ce:

]قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ[ [آل عمران: 31]

“Ka ce: idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, sai Allah ya so ku, ya kuma gafarta muku” (Ali Imran: 31).

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»لا يؤمن أحدكم حتى أكون أحب إليه من والده وولده والناس أجمعين«

[ayanku ba ya zama mumini har sai ya soni fiye da mahaifinsa da ]ansa da mutane gaba ]aya” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi daga hadisin Anas Allah ya yarda da shi.

 Kuma Allah Ma]aukaki ya ce:

]فَالَّذِينَ آمَنُوا بِهِ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَاتَّبَعُوا النُّورَ الَّذِي أُنْزِلَ مَعَهُ أُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ[ [الأعراف: 157]

“Saboda haka wa]anda suka yi imani da shi, suka kuma girmama shi, suka kuma taimake shi, suka kuma bi hasken da aka saukar a tare da shi, to wa]annan su ne marabauta”. (A’araf: 157).

Na shida: }udurce cewa sunnarsa asali ce ga shari’ar musulunci, kuma ita sunnar kamar Al}ur’ni mai girma take (wajen dogoro da aiki da ita), saboda haka ba a sa~a mata domin hankali ya ci karo da ita.

Na bakwai: yin aiki da sunnarsa da gabatar da maganarsa a kan maganar kowa, da mi}a wuya zuwa gare shi, da yin hukunci da shari’arsa da yarda da ita. Allah Ma]aukaki ya ce:

]فَلا وَرَبِّكَ لا يُؤْمِنُونَ حَتَّى يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيْنَهُمْ ثُمَّ لا يَجِدُوا فِي أَنْفُسِهِمْ حَرَجاً مِمَّا قَضَيْتَ وَيُسَلِّمُوا تَسْلِيماً[ [النساء: 65]

“Na rantse da girman Ubangijinka ba za su yi imani ba, har sai sun sanyaka mai hukunci game da abin da ya faru a tsakaninsu, sannan kuma ba su sami wata }unci ba a zukatansu game da abin da ka hukunta, su kuma mi}a wuya gaba ]aya” (Nisa’: 65).

 4- Falalar Kalmomin Shahada:

Kalmar tauhidi tana da falala mai girma, nassosi daga Al}ur’ani da sunna sun bayyana hakan, daga ciki akwai:

1- Ita ce rukuni na farko daga rukunan musulunci; ita ce asalin addini kuma tushensa; ita ce kuma abu na farko da bawa zai musulunta da shi; da ita ce kuma sammai da }assai suka tsaya.

2- {a]aita Allah, da yin hukunci da shari’ar annabinsa (Muhammadu) tsira da amicin Allah su tabbata a gare shi za su tattaru idan aka tabbatar da ita.

3- Ita sababi ne na kare jini da dukiya, wanda ya fa]eta za ta zame masa sanadiyar kiyaye jininsa da dukiyarsa.

4- Ha}i}a fa]in (La Ilaha Illallahu) shi ne mafificin ayyuka a kowane hali; kuma mafi girmansu wajen kankare zunubai, da wajen sanya ma’aunai su yi nauyi a ranar }iyama; itace sababin shiga Aljanna da tsira daga wuta, inda za a aza sammai bakwai da }assai bakwai a hannun ma’auni, kuma a aza La Ilaha Illallahu a ]ayan hannun da La Ilaha Illallahu ta rinjayesu.

Muslim ya ruwaito daga Ubada daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi:

»من شهد أن لا إله إلا الله وأن محمدا عبده ورسوله حرم الله عليه النار«

“Wanda ya shaida babu abin bautawa da  gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawansa ne; kuma Manzonsa ne, to Allah zai haramta wuta a gare shi”.

5- Ha}i}a zikiri da addu’a da yabo sun tattaru a cikinta, ta }unshi kuma addu’ar ibada, da addu’ar ro}o, itace kuma mafi yawa kuma mafi sau}in samuwa daga cikin nau’o’in zikiri, ita ce kyakkyawar kalma, amintacciyar igiya, kuma kalmar ikhlasi, da ita ne kuma sammai da }assai suka tsaya, saboda ita ne aka halicci halitta, aka aiko da Manzonni, aka saukar da littattafai, kuma domin kammalata ne aka shar’anta sunnoni da farillai, don ita ne kuma aka zare takubban yaki, saboda haka wanda ya fa]eta kuma ya yi aiki da ita da gaske, da ikhlasi, da yarda, da so, Allah zai shigar  da shi Aljanna kowane irin ya kasance a kai.

*  *  *


 Rukuni Na Biyu: Salla

Ana ]aukar salla a matsayin ibadar da tafi kowace ibada girman sha’ani, wadda kuma dalilanta suka bayyana fiye da sauran. Musulunci ya damu ta ita, ya kuma ba ta kulawa matuka, don haka ya bayyana falalarta da matsayinta tsakanin sauran ibadu, ha}i}a ita ce kuma abin sadarwa tsakanin bawa da ubangijinsa; yadda ta hanyarta biyayyar bawa ga umarnin ubangijinsa za ta bayyana.

 1-Ma’anarta:

Ma’anarta a cikin harshen larabci: tana ba da ma’anar (addu’a). Ta zo da wannan ma’anar a cikin fa]in Allah Ma]aukaki:

]وَصَلِّ عَلَيْهِمْ إِنَّ صَلاتَكَ سَكَنٌ[ [التوبة: 103]

“Kuma ka yi musu addu’a. Ha}i}a addu’arka kwanciyar rai ne a gare su” (Tauba : 103).

Ma’anarta a wajen malaman shari’a: ita ce wata ibada wadda ta }unshi wasu zantuttuka, da ayyuka ke~a~~u kuma wadda ake bu]eta da kabbara kuma a rufeta da sallama.

Abin da ake nufi da zantuttuka: sune kabbara, karatun Al}ur’ani, tasbihi, addu’a, da makamancin haka.

Abin da ake nufi da ayyuka: sune tsayuwa, ruku’i, sujada, zama, da makamancin haka.

 2-Muhimmancinta A Gurin Annabawa Da Manzonni Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare su

Salla tana daga cikin ibadu da aka shar’anta cikin addinan Allah da suka gabaci aikowar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Dubi dai yadda  Annabi Ibrahim tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake rokon Ubangijinsa ya sanya shi da zuriyarsa su zama masu tsai da ita (inda yake cewa):

]رَبِّ اجْعَلْنِي مُقِيمَ الصَّلاةِ وَمِنْ ذُرِّيَّتِي[ [إبراهيم:40]

“Ya Ubangiji, ka sanya ni in zama mai tsai da salla da kuma zuriyata” (Ibrahim: 40).

Annabi Isma’il tsira da amincin Allah su tabbta a gare shi ya kasance yana umartar iyalinsa da yin salla (Allah ya ce game da shi) :

]َوَكَانَ يَأْمُرُ أَهْلَهُ بِالصَّلاةِ وَالزَّكَاة[ [مريم: 55]

“Kuma ya kasance yana umartar iyalinsa da (tsai da) salla, da kuma (ba da) zakka” (Maryam: 55).

Kuma yayin da yake zantawa da (annabi) Musa tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi Allah Ma]aukaki ya ce:

]إِنَّنِي أَنَا اللَّهُ لا إِلَهَ إِلاَّ أَنَا فَاعْبُدْنِي وَأَقِمِ الصَّلاةَ لِذِكْرِي[ [طـه:14]

“Ha}i}a Ni ne Allah, babu wani abin bautawa in ba Ni ba, sai ka bauta Mini, kuma ka tsai da salla don ambato Na” ([aha:14).

Kuma Allah ya yi wasiyya da ita ga annabinsa Isa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cikin fa]insa:

]وَجَعَلَنِي مُبَارَكاً أَيْنَ مَا كُنْتُ وَأَوْصَانِي بِالصَّلاةِ وَالزَّكَاةِ مَا دُمْتُ حَيّاً[ [مريم:31]

“Ya kuma sanya ni mai albarka a duk inda nake, kuma ya umarce ni da yin salla da kuma ba da zakka matu}ar ina da rai’ (Maryam: 31).

Ha}i}a Allah ya farlanta salla ga Annabinmu Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a sama daren Isra’i da Mi’iraji, kuma a farkon farlantata ta kasance salloli hamsin, sannan Allah ya sau}a}ata zuwa salloli biyar, a aikace salloli biyar; a wajen lada salloli hamsin suke..

Salloli biyar din sune: Alfijir, Azahar, La’asar, Magariba, Isha. Kuma lamari ya tabbata a kan haka da ha]uwar musulmi.

 3- Dalilan Shar’antata

Shar’anta salla ya tabbata ne da dalilai masu yawa, daga ciki:

Na farko daga Al}ur’ani:

1-    Fa]in Allah Ma]aukaki:

] وَأَقِيمُوا الصَّلاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ[ [البقرة: 43]

“Kuma ku tsai da salla, kuma ku ba da zakka” (Ba}ara: 43).

2- Da kuma fa]insa:

]إِنَّ الصَّلاةَ كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَاباً مَوْقُوتاً[[النساء: 103]

“Ha}i}a salla ta kasance farilla ce a kan muminai mai }ayyadaddun lokuta” (Nisa’: 103).

3-    Da fa]insa:

]وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ[ [البينة:5]

(Ba a kuma umarce su ba sai don su bautawa Allah, suna masu tsarkake addini gare shi, masu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla su ba da zakka) (Bayyina:5).

Na biyu daga Sunnar Manzon Allah:

1- Hadisin Ibnu Umar Allah ya yarda da su Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»بني الإسلام على خمس: شهادة أن لا إله إلا الله، وأن محمدا رسول الله، وإقام الصلاة، وإيتاء الزكاة، وحج البيت، وصوم رمضان« متفق عليه

“An gina musulunci a kan rukunai guda biyar: shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, da tsai da sallah, da ba da zakka, da ziyartan ]akin Allah, da azumtan Ramadana” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

2- Hadisin Umar ]an Kha]]ab Allah ya yarda da shi, a cikinsa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»الإسلام أن تشهد أن لا إله إلا الله وأن محمدا رسول الله صلى الله عليه وسلم، وتقيم الصلاة، وتؤتي الزكاة، وتصوم رمضان، وتحج البيت إن استطعت إليه سبيلا…« رواه مسلم

“Musulunci shi ne ka shaida  babu abin butawa da gaskiya sai Allah, lallai kuma (Annabi) Muhammadu ManzonAllah ne, ka tsa ida salla, ka bada zakka, ka yi azumin Ramadana, ka ziyarci ]akin Allah idan ka samu ikon zuwa gare shi…” Muslim ne ya ruwaito shi.

3- Hadisin Ibnu Abbas Allah ya yarda da su  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya aiki Mu’az zuwa Yaman sai ya ce da shi:

»ادعهم إلى شهادة أن لا إله إلا الله وأن محمدا رسول الله، فإن هم أطاعوا لذلك فأعلمهم أن الله افترض عليهم خمس صلوات في كل يوم وليلة…« متفق عليه

 “Ka kirasu zuwa ga shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma lallai Muhammadu ManzonAllah ne, idan suka yarda da haka, to ka sanar da su lallai cewa Allah ya farlanta musu salloli biyar cikin kowane wuni da darensa…” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Na uku Ha]uwar Musulmi:

 Dukkan musulmi sun ha]u a kan shar’anta salloli biyar, sun kuma ha]u a kan su din nan farillai ne daga cikin farillan musulunci.

 4- Hikimar Shar’antata:

An shar’anta  salla ne domin wasu hikimomi da asirai, zai yiwu ayi nuni ga wasunsu kamar haka:

1-    tabbatar da bautantakar bawa ga Allah Ma]aukaki, da kuma cewa lallai shi mallakarsa ne. Da wannan sallar ce mutum zai rika jin shi bawa ne na Allah, kuma zai rayu koyaushe yana mai kusantar mahaliccinsa Mai tsarki Mai ]aukaka.

2-    Salla za ta sanya mai yinta ya rayu yana mai }arfin ala}a da Allah, kuma mai yawan ambatonsa.

3-    Salla tana hana mai yinta ga barin alfahsha, da abin }i, tana kuma daga cikin sabubban (da suke) tsarkake bawa  daga zunubai.

Ha}i}a hadisin Jabir ]an Abdullahi Allah ya yarda da su ya nuna hakan, (Jabir) ya ce: ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»مثل الصلوات كمثل نهر جار غمر على باب أحدكم يغتسل منه كل يوم خمس مرات« رواه مسلم

 “Misalin salloli (wajen tsarkake bawa) kamar }orama ce mai yawan ruwa mai gudana a kofar ]ayanku, yana wanka daga gareta sau biyar a kowace rana” Muslim  ne ya ruwaito shi.

4-    Salla nutsuwace ga zuciya, hutu ne ga rai kuma ita ce mai kubutar da ran daga masifun da suke gur~ata masa lamari su; shi ya sa salla ta kasance abin farin ciki ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Ya kasance kuma yana fakewa da ita idan wani abin damuwa ko abin bakin ciki ya same shi, har ya kasance yana cewa Bilal:

»يا بلال أرحنا بالصلاة« أخرجه أحمد

“Ya kai Bilal ka hutar da mu da ita (salla) Ahmad ne ya ruwaito shi.

 5-Wanda Salla Take Wajaba A Kansa:

Salla tana wajaba ne a kan kowane musulmi balagagge mai hankali na miji ko mace, ba ta wajaba a kan kafiri, wato ba za a neme shi da yin ta ba a duniya; domin ba ta inganta daga gare shi tare da kafircinsa, sai dai kuma za a azabtar da shi a kanta a Lahira; domin yana da damar ya musulunta ya aiwatar da ita amma bai yi ba. Dalili akan haka fa]in Ma]aukaki:

]مَا سَلَكَكُمْ فِي سَقَرَ  قَالُوا لَمْ نَكُ مِنَ الْمُصَلِّينَ  وَلَمْ نَكُ نُطْعِمُ الْمِسْكِينَ  وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ الْخَائِضِينَ وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوْمِ الدِّينِ  حَتَّى أَتَانَا الْيَقِينُ[ [المدثر: 42-47]

(Su ce musu) “Me ya shigar da ku cikin Sa}ar? Suka ce: Ba mu kasance a cikin masu yin salla ba. Kuma ba mu kasance muna ciyar da miskinai ba. Kuma mun kasance muna kutsawa (cikin ~arna) tare da masu kutsawa. Kuma mun kasance muna }aryata ranar sakayya. Har mutuwa ta zo mana” (Muddatthir: 42- 47).

Kuma ba ta wajaba a kan yaro; saboda shari’a bata hau kansa ba, haka kuma ba ta wajaba a kan mahaukaci, ko mace mai haila ko mai jinin biki; domin shari’a ta ]auke wajabcinta a kansu sanadiyar kari (na jini) mai hana yinta.

Yana kuma wajaba a kan waliyyin yaro ko yarinya da ya umarcesu da yin salla idan sun isa shekaru bakwai, ya kuma yi musu duka a kanta idan sun isa shekaru goma, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, har su saba da yinta, kuma su kwa]aitu a kanta.

 6-Hukuncin Mai Barin Salla:

Wanda ya bar salla ha}i}a ya kafirta kafirci mai fitarwa daga addini, yana daga cikin wa]anda suka yi ridda  daga addinin musulunci; domin ya sa~awa Allah da barin abin da ya farlanta masa, saboda haka za a umarce shi da yin tuba, idan ya tuba ya koma yana tsai da ita, to yana nan a kan addininsa, idan kuma bai yi haka ba, to ya zama murtaddi (wanda ya fita daga addini) ba ya halatta a yi masa wanka, ko likafani, ko sallar gawa, ko binne shi a ma}abartar musulmi; domin shi baya daga cikinsu.

 7-Sharru]anta:

1-    Musulunci.

2-    Hankali.

3-    Bambancewa.

4-    Shigar lokaci.

5-    [aura niyya.

6-    Fuskantar al}ibla.

7-    Suturta al’aura. Alaurar miji daga cibiya zuwa gwiwa, amma ita mace dukkan jikinta al’aurace sai fuskarta da tafin hannayenta a cikin salla.

8-    Gusar da najasa daga rigar mai salla, da jikinsa, da kuma gurin da zai yi salla.

9-    Kauda kari, hakan kuma ya }unshi: yin alwala, da wankar janaba.

 8- Lokutanta:

1- Azahar: lokacinta yana farawa ne daga zawali (karkatar rana daga tsakiyar sama zuwa bangaren yamma) har zuwa lokacin da inuwar kowane abu za ta kasance kamarsa.

2- La’asar: lokacinta yana farawa ne daga fitar lokacin azahar har zuwa lokacin da inuwar kowane abu za ta  ru~anya, kuma wannan shi ne lokacin da rana za ta ka]a.

3- Magariba: lokacinta yana farawa ne daga fa]uwar rana har zuwa lokacin da jan shafa}i zai faku, (shafaki) shi ne ja da yake biyo fa]uwar rana.

4- Isha: lokacinta yana shiga ne daga fitar lokacin magariba har zuwa rabin dare.

5- Alfijir: lokacinta yana  farawa ne daga ketowar alfijir na biyu har zuwa fitowar rana.

Kuma dalili a kan haka (lokutan da aka ambata) shi ne hadisin Abdullahi Ibnu Amru Allah ya yarda da su cewa lallai ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»وقت الظهر إذا زالت الشمس وكان ظل الرجل كطوله ما لم يحضر العصر، ووقت العصر ما لم تصفر الشمس، ووقت صلاة المغرب ما لم يغب الشفق، ووقت صلاة العشاء إلى نصف الليل الأوسط، ووقت صلاة الصبح من طلوع الفجر ما لم تطلع الشمس، فإذا طلعت الشمس فأمسك عن الصلاة…« رواه مسلم

“Lokacin Azahar (yana shiga ne) idan rana ta gota, inuwar mutum kuma tana  daidai da tsawonsa, har zuwa shigowar lokacin La’asar, lokacin La’asar kuma yana farawa ne daga karshen lokacin Azahar har zuwa lokacin  da rana za ta ka]a, lokacin sallar magariba kuma yana farawa ne daga fa]uwar rana har zuwa fakuwar shafa}i, lokacin sallar Isha kuma yana farawa ne daga fitar lokacin Magariba har zuwa rabin dare na farko, lokacin sallar Asuba kuma yana farawa ne da ketowar alfijir har zuwa fitowar rana, idan rana ta fito ka kame ga barin salla..” Muslim ne ya ruwaito shi.

 9- Adadin Raka’o’inta:

Adadin raka’o’i na dukkanin sallolin farilla raka’a goma sha- bakwai ne, kamar haka:

1-Azahar: raka’a hu]u.

2-La’asar: raka’a hu]u.

3-Magariba: raka’a uku.

4-Isha: raka’a hu]u.

5-Asuba: raka’a biyu.

Wanda ya yi }ari a kan wa]annan raka’o’i, ko ya yi ragi da gan-gan to sallarsa ta ~aci, idan kuma ya kasance ya aikata hakan ne da mantuwa sai ya riske shi da sujadar mantuwa.

Wannan adadi da aka lissafa ban da sallar matafiyi, domin shi matafiyi an so masa ya yi }asaru, ya ta}aita salla mai raka’a hu]u zuwa raka’a biyu, ya kuma wajaba a kan musulmi ya sallaci wa]annan salloli biyar a cikin lokutan da aka }ayyade musu, ba ya halatta ya jinkirtasu sai da wani uzuri na shari’a, kamar barci, mantuwa, da kuma tafiya, wanda ya yi bacci ko ya yi mantuwa har lokacin wata salla ya wuce, to sai ya yi ta duk sanda ya tuna da ita.

 10- Farillanta:

1-Tsayuwa.

2-Kabbarar harama.

3-karatun Fatiha.

4-Yin ruku’i.

5-Dagowa daga ruku’i.

6-Yin sujada akan ga~o~i bakwai([2]).

7-Zama bayan sujada (ta farko a kowace raka’a).

8-Tahiyya ta karshe.

9-Zama saboda tahiyya ta karshe.

10-Nutsuwa cikin wa]annan farillai.

11-Jeranta wa]annan farillai.

12-Yin sallama.

 11- Wajibanta:

Wajiban salla guda takwas ne:

1- Dukkan kabbarori da ake yin su wajen kaura daga wani aiki zuwa wani aiki ban da kabbarar harama.

2- Fa]in: سمع الله لمن حمده (Sami Allahu liman Hamidah) “Allah ya ji wanda ya yaba masa”, fa]in wannan wajibi ne a kan liman da mai yin salla shi ka]ai, amma mai bin liman ba zai fa]e shi ba([3]).

3- Fa]in:   ربنا ولك الحمد  (Rabbana Walakal Hamd) “ya Ubangijinmu dukkan yabo ya tabbata gareka”.

Fa]in wannan wajibi ne a kan dukkanin mai  yin salla: liman,da mai bin sa, da mai yin salla shi ka]ai.

4- Fa]in: سبحان ربي العظيم  (Subhana Rabbiyal Azeem(

“tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma” a cikin ruku’i.

5- Fa]in:  سبحان ربي الأعلى  (Subhana Rabbiyal A’ala) “tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi ]aukaka” a cikin sujada.

6- Fa]in:  رب اغفر لي (Rabbig fir lee) “ya Ubangiji ka gafarta mini” tsakanin sujada ta farko da ta biyu.

7- Tahiya ta farko, ya ce:

التحيات لله والصلوات والطيبات، السلام عليك أيها النبي ورحمة الله وبركاته، السلام علينا وعلى عباد الله الصالحين، أشهد أن لا إله إلا الله وأشهد أن محمدا عبده ورسوله

 (Attahiyatu lillahi, Wassalawatu Wa]]ayyibatu, Assalamu Alaika Ayyuhan Nabiyyu Wa rahmatullahi Wa barakatuhu, Assalamu Alaina Wa ala Ibadillahis Saliheen Ashhadu An la Ilaha Illallahu, Wa ashhadu Anna Muhammadan Abduhu Wa rasuluhu).

“Dukkan nau’in ban girma ya tabbata ga Allah, da kuma salloli da kyawawan kalmomi. Aminci ya tabbata gare ka ya Annabi, da rahamar Allah da albarkatunsa. Aminci ya tabbata gare mu, da kuma ga bayin Allah salihai. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne”.

 Ko kuma ya fa]i makamancin haka daga cikin lafuza daban-daban na tahiya da suka zo a cikin sunna.

8- Zama domin tahiya ta farko.

Duk wanda ya bar wajibi da gan-gan sallarsa ta ~aci, amma wanda ya bartshi saboda jahilci, ko mantuwa sai ya yi sujadar mantuwa.

 13 - Sallar Jama’a:

Ya wajaba a kan musulmi ya sallaci salloli biyar din nan tare da jama’ar musulmi a masallaci; don ya samu yardar Allah Ma]aukaki, ya kuma samu lada daga gare shi tsarki ya tabbata gare shi.

Salla cikin jama’a ta fi sallar mutum shi ka]ai da daraja ashirin da bakwai, (ya tabbata) a cikin hadisin Ibnu Umar Allah ya yarda da su lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»صلاة الجماعة أفضل من صلاة الفذ بسبع وعشرين درجة« متفق عليه

“Salla cikin jama’a ta fi sallar mutum shi ka]ai da daraja ashirin da bakwai” Bukhari da muslim ne suka ruwaito shi.

Amma mace musulma sallarta a cikin gidanta ta fi falala a kan sallarta tare da jama’a.

13- Abubuwan Da Suke |ata Salla:

Salla ta kan ~aci da ]ayan wa]annan abubuwa masu zuwa:

1- Ci da sha da gan- gan; domin malamai sun ha]u a kan cewa lallai duk wanda ya ci ko ya sha da gan- gan, to ramuwa ta wajaba a kan sa.

2- Magana da gan- gan ba don gyara salla ba; dalili a kan haka hadisin Zay’d  ]an Ar}am Allah ya yarda da shi ya ruwaito, ya ce:

»كنا نتكلم في الصلاة، يكلم الرجل منا صاحبه وهو إلى جنبه في الصلاة حتى نزلت:] وَقُومُوا لِلَّهِ قَانِتِينَ[ [البقرة: 238]، فأمرنا بالسكوت ونهينا عن الكلام« رواه البخاري ومسلم

“Mun kasance muna magana cikin salla, ]ayanmu yana magana da wanda yake gefensa cikin salla, har aya ta sauka:

“Ku tsayu saboda Allah kuna masu biyayya” (Ba}ara: 238), Sai aka umarce mu da yin shiru, aka kuma hana mu yin magana” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

 Haka kuma kalmar malamai ta ha]u a kan cewa lallai wanda ya yi magana cikin sallarsa da gan- gan alhali ba ya nufin gyaran sallarsa, to sallarsa ta ~aci.

3- Motsi mai yawa da gan- gan, (motsi mai yawa kuma shi ne duk wani motsin da idan wani ya gan shi yana yi zai zaci ba a cikin salla yake ba).

4-Barin wani rukuni ko shara]i da gan- gan ba tare da wani uzuri ba, kamar yin salla ba tare da tsarki ba, ko yin salla ba tare da fuskantar al}ibla ba; saboda hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito cewa lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce wa bakauyen da (ya yi salla) bai kyautata sallarsa ba:

»ارجع فصل فإنك لم تصل«

“Ka koma ka yi salla domin baka yi salla ba”.

5- Dariya cikin salla; hakan kuma saboda kalmar malamai ta ha]u a kan ~acin salla da dariya.

 14- Lokutan Da Aka Hana Yin Salla:

1-    Bayan sallar asuba har sai rana ta daga.

2-    Lokacin da rana za ta daidaita a tsakiyar sama.

3-    Bayan sallar La’asar har sai rana ta fa]i.

Ha}i}a hadisin ﷻ‬}ba ]an Amir Allah ya yarda da shi ya nuna cewa an }i yin salla a wa]annan lokuta, (ﷻ‬}ba) ya ce:

»ثلاث ساعات كان رسول الله صلى الله عليه وسلم ينهانا أن نصلي فيهن وأن نقبر فيهن موتانا، حين تطلع الشمس بازغة حتى ترتفع، وحين يقوم قائم الظهيرة حتى تميل الشمس، وحين تَضَيَّف الشمس للغروب حتى تغرب« رواه مسلم

“Lokuta guda uku Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana hana mu mu yi salla a cikinsu, ko mu binne mamatanmu a cikinsu: lokacin da rana take fara fitowa har sai ta daga, da lokacin da inuwa take tsayawa daidai (ba ta karkata zuwa bangaren yamma ko gabas ba) har sai rana ta gota (daga tsakiyar sama), da lokacin da rana take  karkata (domin ta fa]i) har sai ta fa]i” Muslim ne ya ruwaito shi.

Da kuma hadisin Abi Sa’id Alkhudri Allah ya yarda da shi lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»لا صلاة بعد صلاة العصر حتى تغرب الشمس، ولا صلاة بعد صلاة الفجر حتى تطلع الشمس« متفق عليه

 “Ba a yin salla bayan sallar La’asar har sai rana ta fa]i, ba a yin salla kuma bayan sallar Asuba har sai rana ta fito”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

 15- Siffar Salla A Dunkule:

Wajibi ne a kan musulmi ya yi koyi da ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; saboda fa]insa:

»صلوا كما رأيتموني أصلي« رواه البخاري

 “Ku yi salla kamar  yadda kuka ganni ina yi” Bukhari ne ya ruwaito shi.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya tashi yin salla yana tsayawa gaban Allah tsarki ya tabbata gare shi da ]aukaka,  ya ]aura niyya a cikin zuciyarsa. Ba a kar~o daga Annabi cewa yana furuci da niyya ba. Sannan ya yi kabbara yana mai cewa:   الله أكبر(Allahu Akbar) “Allah ne mafi girma” ya  ]aga hannayensa   (tare da kabbarar) daidai da kafadarsa, a wani lokacin kuma yana ]agasu daidai da fatar kunne, ya kuma ]ora hannayensa a kan kirjinsa  hannunsa na dama yana kan na hagu, sai ya yi wata addu’a daga cikin addu’o’in da ake bu]e salla da su, daga cikinsu:

سبحانك اللهم وبحمدك، تبارك اسمك، وتعالى جدك، ولا إله غيرك

(Subhanakalla Humma Wabihamdik Tabarakasmuk Wa ta’ala jadduk Wa la’ilaha Gairuk)

“Tsarki ya tabbata gareka ya Allah, tare da yabo gareka. Albarkatun sunanka sun yawaita, Mulkinka da girmanka sun ]aukaka; babu abin bautawa da gaskiya ba kai ba”.

 Sannan ya karanta Fatiha da wata sura, sai ya yi kabbara yana mai daga hannayensa sai ya yi ruku’i, yana kuma mai daidaita bayansa a cikin ruku’insa, yadda ko da za a ]orawa bayan nasa kwarya cike da ruwa, ruwan ba zai zuba ba, kuma yana fa]in: سبحان ربي العظيم      (Subhana Rabbiyal Azeem) sau uku, sai kuma ya dago daga ruku’in yana mai cewa: سمع الله لمن حمده ربنا ولك الحمد  (Sami Allahu liman Hamidah, Rabbana Wa lakal Hamd) yana mai daga hannayensa har ya daidaita, sannan ya yi kabbara ya yi sujada, idan ya yi sujada sai ya nisantar da hannayensa daga sassan jikiknsa har yadda za a iya ganin hammatarsa. Yana kuma tabbatar da goshinsa da hancinsa da tafin hannayensa da gwiwowinsa da yatsun kafafuwansa har su taba }asa yana mai cewa:) سبحان ربي الأعلى Subhan Rabbiyal A’la) sau uku, sannan ya yi kabbara ya zauna a kan kafarsa ta hagu yana mai kafa kafarsa ta dama, yana mai fuskantar da yatsunta zuwa al}ibla, yana mai cewa a wannan zaman:

رب اغفر لي وارحمني واجبرني وارفعني واهدني وعافني وارزقني

 (Rabbig firli Warhamni Wajburni Warfa’ni Wahdini Wa afini Warzu}ni)

“Ya Allah ka gafarta mini, ka ji }ai na, ka wadata ni, ka ]aukaka ni, ka shirye ni, ka ba ni lafiya da tsira daga masifu, ka arzuta ni”.

 Sannan ya yi kabbar ya yi sujada sai kuma ya tashi ga raka’a ta biyu.

Haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake aikatawa a kowace raka’a. Idan kuma ya zauna zaman tahiya ta farko bayan raka’a ta biyu sai ya karanta tahiya (kamar yadda ya gabata), sannan ya tashi yana mai kabbara yana mai daga hannayensa (wannan shi ne wuri na hu]u da Annabi yake daga hannayensa), idan ya zauna domin yin tahiya ta karshe a raka’a ta uku ta magariba ko a raka’a ta hu]u ta Azahar da La’asar da Isha sai ya zauna a kan mazauninsa na hagu, ya fitar da kafarsa ta hagu ta karkashin }waurinsa na dama, kuma ya kafa kafarsa ta dama yana mai fuskantar da yatsunta zuwa al}ibla, ya kuma tara yatsun tafinsa na dama, ba tare da ya ha]a da manuniya ba, domin ita zai mikar da ita ne don ya yi nuni da ita ko ya motsata, yana mai dubinta da idanunsa. Ya karanta tahiya kuma ya }ara da salati ga Manzon Allah wato ya ce:

اللهم صل على محمد وعلى آل محمد، كما صليت على آل إبراهيم إنك حميد مجيد، وبارك على محمد وعلى آل محمد كما باركت على آل إبراهيم إنك حميد مجيد

(Allahumma Salli Ala Muhammadin Wa ala Ali Muhammadin Kama Sallaita Ala ali Ibrahim Innaka Hameedun Majeed, Wa barik Ala Muhammadin Wa Ala ali Muhammadin Kama Barakta Ala ali Ibrahim Innaka Hameedun Majeed).

“Ya Allah ka yi salati ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi salati ga alayen Ibrahimu, lallai kai abin yabo ne, Mai girma. Kuma ka yi albarka ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga alayen  Ibrahimu, lallai kai abin yabo ne, Mai girma”.

 Idan ya gama tahiya sai ya yi sallama ga damansa da hagunsa ya ce: السلام عليكم ورحمة الله، السلام عليكم ورحمة الله(Assalamu Alaikum Warahmatullah, Assalamu Alaikum Warahmatullah)  har aga kumatunsa (yayin da yake sallama ga damansa da hagunsa).

Ha}i}a an bayyana wannan siffar (da aka ambata) a cikin hadisai da dama da aka ruwaito daga ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Wa]annan abubuwa da aka bayyana wasu ne daga cikin hukunce–hukuncen salla wadda ingantuwar sauran ayyuka sun rataya ne a kanta, saboda ita salla idan ta inganta sauran ayyuka na bawa za su inganta, idan kuma ta ~aci haka nan sauran ayyukan za su ~aci, kuma sallar itace farkon abin da za a yiwa bawa hisabi a kanta a ranar }iyama, idan ya yi ta cikakkiya, to ya rabauta da yardar Allah ma]aukaki, idan kuma ya rage wani abu daga cikinta, to ya halaka. Har wala yau ita salla tana hana aikata alfahasha da abin }i, saboda haka salla tana tsarkake ran ]an adam daga abubuwan da za su tunku]a shi zuwa ga aikata muggan ayyuka, har ran ya tsarkaka kuma ya kubuta daga ayyukan assha.

*  *  *


 Rukuni Na uku: Zakka

 1- Ma’anarta:

Ma’anar zakka a cikin harshen larabci ita ce : bun}asa da }aruwa, tana kuma ]aukar ma’anar yabo, da tsarkakewa, da  gyara. An kuma kira dukiyar da aka fitar ]in da zakka; domin tana kara albarkar dukiya, tana kuma tsarkake mutum (daga zunubai) da samun gafarar Allah.

Ma’anarta a wajen malaman shari’a: itace wani ha}}i da yake wajaba a cikin wata dukiya ke~a~~iya, ga wasu jama’a ke~a~~u, a  wani lokaci ke~a~~e.

 2- Matsayinta Da Hikimar Shar’antata:

Zakka ]aya ce daga cikin rukunan musulunci guda biyar, ita kuma abokiyar salla ce (tare da salla aka ambacesu) a wurare dayawa a cikin littafin Allah, daga cikinsu, akwai fa]in Allah Ma]aukaki:

]وَأَقِيمُوا الصَّلاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ[ [البقرة: 43]

“Kuma ku tsai da salla, kuma ku ba da zakka” (Ba}ara: 43).

Da fa]insa:

]وَيُقِيمُوا الصَّلاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ[ [البينة:5]

“Kuma su tsai da salla, kuma su ba da zakka” (Bayyina: 5).

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»بني الإسلام على خمس…« وذكر منها: »إيتاء الزكاة« متفق عليه من حديث ابن عمر رضي الله عنهما

 “An gina musulunci a kan rukunai guda biyar…” ya ambaci daga cikinsu “ba da zakka” Bukhari da  Muslim ne suka ruwaito shi daga  hadisin Ibnu Umar Allah ya yarda da su.

Allah ya shar’anta zakka ne domin tsarkake rayukan mutane daga rowa da ha]ama, domin kuma taimakon matalauta da mabukata, domin kuma tsarkake dukiya da ha~aka ta, da sanya  mata albarka, da kareta daga masifu da barna, (an kuma shar’antata) domin samar da abubuwa na amfani masu gamewa wa]anda rayuwar al’uma da jin da]insu ba ya yiwa sai da su. Ha}i}a Allah ya ambaci hikimar ba da zakka a cikin littafinsa inda ya ce:

]خُذْ مِنْ أَمْوَالِهِمْ صَدَقَةً تُطَهِّرُهُمْ وَتُزَكِّيهِمْ بِهَا[ [التوبة: 103]

“Ka kar~i sadaka daga dukiyoyinsu da za ka tsarkake su kuma ka wanke su da ita” (Tauba: 103).

 3- Hukuncinta:

Zakka farillace a kan kowane musulmi da ya mallaki nisabi([4]) na dukiya da sharru]anta, har ma yaro da mahaukaci tana wajaba a kansu, waliyyinsu ne zai fitar a madadinsu, wanda ya musanta wajabacinta da gan-gan alhali yana sane da hakan, ha}i}a ya kafirta, wanda kuma ya hanata don rowa da sakaci, za a dauke shi a matsayin fasi}i, wanda ya aikata wani zunubi mai girma daga cikin manyan zunubai, idan kuma ya mutu a kan haka, to lamarinsa yana ga Allah wato ko dai ya gafarta masa, ko kuma ya azabtar da shi  in ya so; saboda fa]in Allah Ma]aukaki:

]إِنَّ اللَّهَ لا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ[ [النساء: 48]

“Ha}i}a Allah ba ya gafarta a yi tarayya da Shi (amma) kuma yana gafarta wanin wannan ga wanda ya so” (Nisa’: 48).

Kuma za a kar~i  zakkar daga gare shi, sannan kuma a ladabtar da shi; domin ya aikata haram.

Ha}i}a Allah tsarki da ]aukaka sun tabbata a gare shi ya yi tanadin azaba ga mai hana zakka da fa]insa:

]وَالَّذِينَ يَكْنِزُونَ الذَّهَبَ وَالْفِضَّةَ وَلا يُنْفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَبَشِّرْهُمْ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ  يَوْمَ يُحْمَى عَلَيْهَا فِي نَارِ جَهَنَّمَ فَتُكْوَى بِهَا جِبَاهُهُمْ وَجُنُوبُهُمْ وَظُهُورُهُمْ هَذَا مَا كَنَزْتُمْ لانْفُسِكُمْ فَذُوقُوا مَا كُنْتُمْ تَكْنِزُونَ[ [التوبة: 34- 35]

“Wa]anda kuma suke ~oye zinariya da azurfa, ba sa kuma fitar da hakkin Allah daga cikinsu, to sai ka yi musu  albishir da azaba mai ra]a]i. Ranar da za a narka su (zinariya da azurfa) cikin wutar jahannama, sai a yi wa goshinsu da kwibinsu da bayansu lalas da ita, (a ce da su): Wannan shi ne abin da kuka ~oye wa kanku, sai ku ]an]ana sakamakon abin da kuka kasance kuna ~oyewa” (Tauba: 34- 35).

Kuma an kar~o daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi ya ce: ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»ما من صاحب كنز لا يؤدي زكاته إلا أحمي عليه في نار جهنم، فيجعل صفائح، فيكوى بها جنباه وجبينه حتى يحكم الله بين عباده في يوم كان مقداره خمسين ألف سنة ثم يرى سبيله إما إلى الجنة وإما إلى النار…« الحديث متفق عليه وهذا لفظ مسلم

“Babu wani ma’abocin taska da ba ya ba da zakkarta face an narka ta a cikin wutar Jahannama, sai a mulmulata a yi wa kwibinsa da goshinsa lalas da ita, har (ranar da) Allah zai hukunta tsakanin bayinsa (wato) ranar da gwargwadonta shekaru dubu hamsin, sannan zai ga hanyarsa ko dai zuwa Aljanna ko kuma zuwa wuta…” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi, lafazinsa kuma na Muslim ne.

 4- Sharru]anta:

Sharru]an zakka guda biyar ne:

1-    Musulunci, zakka ba ta wajaba a kan kafiri.

2-    ‘Yanci, ba ta wajaba a cikin dukiyar bawa a wurin mafi yawan malamai, haka kuma ba ta wajaba a kan mukatabi([5]); domin shi bawa ne muddin dai akwai ko da dirhami ]aya da ya saura a kansa.    

3-    Mallakar nisabi, idan dukiya ta kasa nisabi to babu zakka a cikinta.

4-    Cikakken mallaka, zakka ba ta wajaba a cikin bashin fansa (wanda yake kan bawa mai fansar kansa), haka kuma ba ta wajaba a cikin kason riba na wanda ya ba da dukiyarsa ga wani yana kasuwanci da ita har sai an raba ribar, haka kuma ba ta wajaba a cikin bashin da yake kan wanda ba shi da halin biya har sai mai shi ya samu ya karba. Babu zakka a cikin dukiyar wa}afi wadda aka takaitata a kan gudanar da aikin alheri da kyautatawa, kamar dukiyar da aka tanada domin jihadi, ko masallatai, da matalauta, da makamancin haka.

5-    Cikar shekara, zakka ba ta wajaba a cikin dukiya har sai shekara ta zagayo, amma ban da amfanin gona, kamar }wayoyi da ‘ya‘yan itatuwa  wadda zakka take wajaba a cikinsu, irin wannan dukiyar ana fidda zakkarta ne a lokacin da aka girbeta; domin fa]in Allah Ma]aukaki:

]وَآتُوا حَقَّهُ يَوْمَ حَصَادِهِ[ [الأنعام:141]

“Kuma ku fitar da zakkarsa ranar girbinsa” (An’am: 141).

Ma’adanai da rikazi([6]) hukuncinsu shi ne hukuncin amfanin gona; domin kasancewarsu dukiya ce da aka samu daga cikin }asa.

‘Ya‘yan dabbobin da ake kiwonsu, cikar shekarar iyayen ita ce cikar shekararsu, haka kuma ribar dukiyar kasuwanci cikar shekarar asalin jari ita ce cikar shekararta, saboda haka sai ya ha]a ‘ya‘yan da iyayensu,  haka kuma ribar da asalin jarin ya fidda zakkarsu, idan iyayen sun cika shekara, ko asalin jarin ya cika shekara.

 Balaga da hankali ba shara]i ne ba  a cikin zakka, saboda haka tana wajaba a cikin dukiyar yaro da mahaukaci a wurin mafi yawan ma’abota ilmi.

5- Dukiyoyin Da Zakka Take Wajaba A Cikinsu:

Zakka tana wajaba ne a cikin nau’i biyar na dukiya:

Na farko: zinariya da azurfa da ake amfani da su a matsayin samani, haka kuma da takardun ku]i da ake amfani da su a madadinsu.

Kuma gwargwadan abin da ake fitarwa na zakkar shi ne kashi ]aya bisa hu]u na daga kashi ]aya bisa goma (kashi ]aya daga cikin arba’in na dukiya) wannan kuma ya yi daidai da (2.5%) wato biyu da rabi daga cikin ]ari. Zakka ba ta wajaba a cikinsu har sai sun cika shekara, kuma sun isa nisabi.

Kuma nisabin zinariya shi ne mis}ali ashirin, kuma nauyin  misa}ali ya yi daidai da gram (4.25), saboda haka nisabin zinariya ya kama gram (85).

Nisabin azurfa kuma ya kama dirhami ]ari biyu, kuma nauyin dirhami ya yi daidai da gram (2.975), saboda haka nisabin Azurfa ya kama gram (595).

Amma takardun ku]i na zamani nisabinsu shi ne }imarsu ta zama daidai da }imar gram (85) daga zinariya, ko gram (595) daga azurfa a lokacin da ake so a fitar da zakkarsu yayin da suka cika shekara; saboda haka nisabinsu yakan bambanta gwargwadon yadda karfinsu na sayayya yake bambanta  idan aka kwatantasu da nisabin zinariya ko azurfa, idan takardan ku]in da mutum ya mallaka ya kai gwaragwadon da zai iya sayen nisabin zinariya (gram:85) ko azurfa (gram: 595)  ko fiye da haka, to zakka ta wajaba a cikinsa, ba a la’akari da bambantar sunayen takardun ku]a]en da ake amfani da su, saboda haka  Naira, Riayl, Dinar, Frank, Dola, da makamancinsu duk hukuncinsu ]aya ne, muddin }imarsu ta kai gwargwadon da aka ambata, haka nan ba a la’akari da bambantar siffofinsu, wato ku]i ne na takarda  ko kuma  tsaba, da makamancinsu dukkansu hukuncinsu ]aya ne. Abu ne sananne cewa farashin ku]a]en da ake amfani da su yana bambanta daga lokaci zuwa wani lokaci, saboda haka wajibi ne a kan mai fidda zakka ya lura da }imar kudinsa lokacin da zakka ta wajaba a cikinsa, shi ne lokacin da  ku]in da yake hannunsa yake cika shekara.

Abin da kuma ya karu a kan nisabi za a fidda zakkarsa ne gwargawdon yadda ya karu, dalilin haka hadisin Ali Allah ya yarda da shi ya ce: ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»إذا كانت لك مائتا درهم وحال عليها الحول ففيها خمسة دراهم، وليس عليك شيء حتى يكون لك عشرون دينارا وحال عليها الحول ففيها نصف دينار، فما زاد فبحساب ذلك، وليس في مال زكاة حتى يحول عليه الحول« رواه أبو داود وهو حديث حسن

“Idan kana da dirhami ]ari biyu, kuma suka cika shekara zakkarsu dirhami biyar ne, kuma babu komai a kanka  har sai ka mallaki dinari ashirin, kuma sun cika shekara, to zakkarsu rabin dinari, abin da ya karu a kan haka sai akwatanta shi da haka a fidda zakkarsa, zakka ba ta wajaba a cikin dukiya har sai shekara ta kewayo” Abu Dawud ne ya ruwaito shi, kuma hadisi ne hasan (mai kyau).

Gwalagwalai na mata idan  sun kasance an tanada su ne domin ajiya ko ba da shi haya to zakka ta wajaba a cikinsu babu sa~ani a kan haka, idan kuma ya kasance an tanade su ne domin amfani da su to magana mafi rinjaye daga cikin maganganun malamai  shi ne zakka tana wajaba a cikinsu; saboda dalilai masu gamewa da suka zo a kan wajabcin zakkar zinariya da azurfa, kuma saboda hadisin da Abu Dawud, da Nasa’i, da Tirmizi suka ruwaito daga Amru Ibnu Shua’aib daga babansa daga kakansa Allah ya yarda da su cewa:

»أن امرأة أتت النبي صلى الله عليه وسلم ومعها ابنة لها وفي يد ابنتها مسكتان غليظتان من ذهب، فقال لها: أتعطين زكاة هذا؟ قالت: لا، قال: أيسرك أن يسورك الله بهما يوم القيامة سوارين من نار، فخلعتهما فألقتهما إلى النبي صلى الله عليه وسلم وقالت: هما لله ورسوله« رواه أبو داود والنسائي والترمذي

“Wata mace ta zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, tare da ‘yarta, kuma a hannun ‘yartata akwai awarwaraye guda biyu na zianariya masu kauri, sai Annabi ya ce mata: “shin kina ba da zakkar wannan?”, ta ce: a’a, ya ce: “shin zai faranta miki rai Allah ya sa miki awarwaraye na wuta (a sanadiyar awarwarayen nan na hannun ‘yarki) ranar gobe }iyama”, sai ta jefasu ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ta ce: “na ba da su ga Allah da Manzonsa”.

Haka kuma Abu Dawud da waninsa sun ruwaito daga A’isha Allah  ya yarda da ita ta ce:

عن عائشة رضي الله عنها قالت: » دخل علي رسول الله صلى الله عليه وسلم فرأى في يدي فتحات من ورق، فقال: ما هذا يا عائشة؟ فقلت: صنعتهن أتزين لك يا رسول الله، قال: أتؤدين زكاتهن؟ قلت: لا، أو ما شاء الله، قال: هو حسبك من النار«رواه أبو داود وغيره

 “Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya shigo mini sai ya ga zobba na azurfa a hannayena sai ya ce: “mene ne wannan ya ke A’isha?”, sai na ce: na sa su ne domin in yi maka ado ya Manzon Allah. Sai ya ce: “shin kina fidda zakkarsu?”, na ce: a’a, ko abin da Allah ya so, ya ce: “wannan ya isa ga azabar wuta”.

Amma ma’adanai  da abubuwan da ba da zinariya aka kera su ba, kamar duwatsu masu alfarma da Lu’ulu’u babu zakka a cikin su a wurin dukkannin malamai, sai dai idan sun kasance ana kasuwanci da su, sai a fidda zakkarsu kamar yadda ake fidda zakkar sauran kayayyaki na kasuwanci.

Na biyu: Dabbobi:

Dabbobin da ake fidda zakkkarsu su ne: rakuma, shanu, da tumaki da awaki, zakka kuma tana wajaba ne a cikinsu idan sun kasance suna kiwo, wato su zama suna fita kiwo a mafi yawan lokuta na shekara; domin mafi yawa  daidai yake da duka wajen hukunci, kuma dalili a kan haka (dabbobin su zama na kiwo) fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»في كل إبل سائمة صدقة« رواه أحمد وأبو داود والنسائي

 “Zakka tana wajaba a cikin  dukkanin  ru}uma masu kiwo”. Ahmad ne da Abu Dawud da Nasa’i suka ruwaito shi, haka kuma da fa]insa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»في صدقة الغنم في سائمتها« رواه البخاري

“Zakka tana wajaba a cikin tumaki da awaki masu kiwo” Bukhari ne ya ruwaito shi.

Kuma ya zamana sun cika nisabi, kuma shekara ta kewayo.


 Ga kuma bayanin nisabin dabbobi kamar haka:

Nau’i

Gwargwadon Nisabi

Gwargwadon Da Yake Wajaba

daga

zuwa

RA{UMA

5

9

akuya

10

14

awaki biyu

15

19

awaki uku

20

24

awaki hu]u

25

35

Bintu Makhad([7]) wadda ta cika shekaru biyu

36

45

Bintu Labun([8]) wadda ta cika shekaru biyu

46

60

Hi}}a([9]) wadda ta cika shekaru uku

61

75

Jaza’a wadda ta cika shekaru hu]u

76

90

Bintu Labun biyu

91

120

Hi}}a biyu

Abin da ya karu a kan: 120

A cikin kowane ru}uma arba’in za a fidda Bintu Labun, kuma a cikin kowane ru}uma hamsin za a fidda Hi}}a, wannan a wurin mafi yawan malamai kenan

SHANU

30

39

Tabi ko Tabi’a([10]) wa]anda suka cika shekara

40

59

Musinna wadda ta cika shekara

60

69

Tabi’a  biyu

70

79

Tabi da Musinna

Abin da ya karu akan: 79

A ko wa]anne shanu talatin za a fidda Tabi kuma a kowane shanu arba’in za a fidda Musinna

TUMAKI

DA

AWAKI

40

120

akuya \ tinkiya

121

200

awaki \ tumaki  biyu

201

300

Awaki \tumaki uku

Abin da ya karu a kan: 300

A kowane awaki \ tumaki ]ari za a fidda ]aya   

 Dalili a kan haka, hadisin Anas Allah ya yarda da shi lallai sayyidina Abubakar ya aika masa da wannan takardar - yayin da ya aike shi zuwa garin Bahrain -:

»بسم الله الرحمن الرحيم، هذه فريضة الصدقة التي فرض رسول الله صلى الله عليه وسلم على المسلمين والتي أمر الله بها رسوله، فمن سئلها من المسلمين على وجهها فليعطها ومن سئل فوقها فلا يعط، في أربع وعشرين من الإبل فما دون من الغنم من كل خمس شاة، فإذا بلغت خمسا وعشرين إلى خمس وثلاثين ففيها بنت مخاض أنثى، فإذا بلغت ستا وثلاثين إلى خمس وأربعين ففيها بنت لبون أنثى، فإذا بلغت ستا وأربعين إلى ستين ففيها حقة طروقة الجمل، فإذا بلغت واحدة وستين إلى خمس وسبعين ففيها جذعة، فإذا بلغت – يعني ستا وسبعين – إلى تسعين ففيها بنتا لبون، فإذا بلغت إحدى وتسعين إلى عشرين ومائة ففيها حقتان طروقتا الجمل، فإذا زادت على عشرين ومائة ففي كل أربعين بنت لبون، وفي كل خمسين حقة، ومن لم يكن معه إلا أربع من الإبل فليس فيها صدقة  إلا أن يشاء ربها، فإذا بلغت خمسا من الإبل ففيها شاة، وفي صدقة الغنم في سائمتها إذا كانت أربعين إلى عشرين ومائة شاة، فإذا زادت على عشرين ومائة إلى مائتين شاتان، فإذا زادت على مائتين إلى ثلاثمائة ففيها ثلاث، فإذا زادت على ثلاثمائة ففي كل مائة شاة، فإذا كانت سائمة الرجل ناقصة من أربعين شاة شاة واحدة فليس فيها صدقة إلا أن يشاء ربها« رواه البخاري

 “Da sunan Allah Mai rahama Mai jin }ai, wannan (bayanin) zakka  ta farilla  ce wadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare  shi ya bayyanata ga musulmi, wadda kuma Allah ya yiwa manzonsa umarni da ita, saboda haka  duk wanda aka neme shi daga cikin musulmi da ya ba da zakka kamar yadda Annabi ya bayyana, to ya bayar, wanda kuma aka neme shi da ya ba da sama da abin da aka bayyana, to kada ya bayar, abin da ya kama daga  ra}uma biyar zuwa ashirin da hu]u za a fidda a ko wa]anne rukuma biyar akuya ]aya, idan sun kai ashirin da biyar zuwa talatin da biyar za a fidda Bintu makhad, idan sun kai talatin da shida zuwa arba’in da biyar za a fidda Bintu labun, idan sun kai arba’in da shida zuwa sittin za a fidda Hi}}a wadda ta isa na miji ya take ta, idan sun kai sittin da ]aya zuwa saba’in da biyar za a fidda Jaza’a, idan sun kai saba’in da shida zuwa tis’in za a fidda Bintu labun biyu, idan sun kai tis’in da ]aya zuwa ]ari da ashirin  za a fidda Hi}}a biyu, idan sun karu a kan ]ari da ashirin a ko wa]anne arba’in za a fidda Bintu labun, kuma a ko wa]anne hamsin Hi}}a. Wanda kuma bai mallaki sama da ru}uma hu]u ba babu zakka a cikinsu sai dai idan ya so (ya yi sadaka), idan suka kai biyar za a fidda akuya. Awaki da tumaki kuma wa]anda suke kiwo idan sun kai arba’in  har zuwa ]ari da ashirin za a fidda akuya, idan sun karu a kan haka har zuwa ]ari biyu za a fidda awaki biyu, idan sun karu a kan ]ari biyu har zuwa ]ari uku za a fidda awaki uku, idan sun karu a kan haka a cikin kowacce ]ari za a fidda akuya, idan kuma awakin sun kasa arba’in ko da akuya ]aya ce to babu zakka a cikin su sai dai idan mutum ya so (ya yi sadaka) Bukhari ne ya ruwaito shi.

Wani dalilin kuma shi ne hadisin Mu’az Allah ya yarda da shi cewa:

حديث معاذ رضي الله عنه: »أن النبي صلى الله عليه وسلم بعثه إلى اليمن فأمره أن يأخذ من كل ثلاثين بقرة تبيعا أو تبيعة، وفي كل أربعين مسنة« رواه أحمد وأصحاب السنن.

“Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aike shi zuwa Yaman sai ya umarce shi da ya ]auki Tabi ko Tabi’a daga cikin shanu talatin, kuma a kowane arba’in Musinna”, Ahmad ne da ma’abotan litattafan sunna suka ruwaito shi.

Abin da dabbobin kiwo suka haifa za a ha]a su ne da iyayen a lissafasu idan iyayen sun kai nisabi, idan kuma iyayen ba za su iya cika nisabi ba, sai idan an ha]a su da ‘ya‘yan, sai a bari har shekara ta kewayo daga ranar  da gaba ]ayansu suka cika nisabi.

Idan kuma  ya zamana an yi tanadin dabbobin ne domin kasuwanci, to sai a fidda zakkarsu kamar yadda ake fidda zakkar sauran kayayyakin kasuwanci, idan kuma an tanadesu ne domin yin amfani da su ko kiwatasu a gidaje  to babu zakka a cikinsu; saboda hadisin Abu Huraira Allah ya yarda shi:

»ليس على المسلم في عبده ولا فرسه صدقة« رواه البخاري ومسلم

 “Babu zakka a kan musulmi game da bawansa ko dokinsa” ([11]) Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Na uku: Amfanin Gona (shuke-shuke Da ‘Ya‘yan Itace):

Zakka tana wajaba a cikinsu idan sun kai nisabi a wurin mafi yawan malamai, nisabin kuma a wurinsu was}i biyar ne; saboda fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi:

»ليس فيما دون خمسة أوسق صدقة« رواه البخاري ومسلم

 “Babu zakka a cikin abin da bai kai was}i biyar ba” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Was}i kuma shi ne: sa’i sittin, saboda haka gwargwadon nisabi kai sa’i ]ari uku, wanda kuma nauyinsa ya kai kusan  kilo gram: (652,800) na kyakkyawar alkama.

  Shuke-shuke da ‘ya‘yan itatuwa ana ba da zakkarsu ne a ranar da aka girbesu, ba shara]i ba ne su cika shekara; saboda fa]in Allah Ma]aukaki:

]َوَآتُوا حَقَّهُ يَوْمَ حَصَادِه[ [الأنعام:141]

“Kuma ku fitar da zakkarsa ranar girbinsa” (An’am: 141).

Kuma gwargwadon abin da ake fitarwa shi ne kashi ]aya bisa goma dangane da abin da aka shayar ba tare da dawainiya ba, abin da kuma aka yi dawainiyar shayar da shi ana fitar da rabin kashi ]aya bisa goma; saboda fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»فيما سقت السماء والأنهار والعيون أو كان عثريا العشر، وفيما سقي بالسواني أو النضح نصف العشر« أخرجه البخاري

“Abin da aka shayar da shi da ruwan sama, ko da ruwan }oramu, ko da idanuwan ruwa, ko yakasance yana shan ruwan da ya taru a karkashinsa, za a fidda kashi ]aya bisa goma, abin da kuma aka shayar da shi da dabba, ko da guga za a fidda rabin kashi ]aya bisa goma”, Bukhari ne ya ruwaito shi. 

Na hu]u: Kayan Kasuwanci

Kayan kasuwanci shi ne dukkanin abin da musulmi ya tanade shi domin kasuwanci daga kowane  nau’i yake, kuma shi ne mafi gamewa fa]in dukiyoyin da ake fidda zakkarsu. Zakka tana wajaba ne a cikinsa idan ya kai nisabi, abin da kuma ake la’akari da shi anan shi ne }imarsa ta zama ta kai nisabin zinariya ko azurfa, wato }imar dinari ashirin na zinariya (gram: 85), ko }imar dirhami ]ari biyu na azurfa (gram: 595), sai a duba a }imanta shi da abin da ya fi amfani ga matalauta, zinariya ko azurfa. Kuma ba a la’akari da }imar kayayyakin lokacin da aka sayesu, abin lura shi ne }imarsu lokacin da ake fidda zakkarsu bayan sun cika shekara.

Gwargwadon abin da ake fitarwa kuma shi ne kashi ]aya bisa hu]u na daga kashi ]aya bisa goma na dukkannin }imar, kuma ribar kayan kasuwanci za a ha]a ta ne a lokacin fidda zakka da uwar jari, idan uwar jarin ta cika shekara, ba a  jira har sai ribar ta cika wata shekara, amma idan uwar jarin ta kasance ba za ta isa nisabi ba sai idan an ha]a ta da ribar, to sai a bari wata shekara ta kewayo daga lokacin da dukkkanninsu suka cika nisabi sannan a fidda zakkarsu.

Na biyar: Ma’adanai Da Rikazi

a – Ma’adanai: sune abubuwan da ba }asa ba ne kuma ba tsiro ba, da ake samunsu  a cikin }asa daga cikin abubuwa masu }ima da aka haliccesu a cikinta. Kamar zinariya, azurfa, karfe, tagulla, ya}utu, man fetur, da makamancinsu. Zakka kuma tana wajaba ne a cikinsu saboda gamewar fa]in Allah Ma]aukaki:

]يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَنْفِقُوا مِنْ طَيِّبَاتِ مَا كَسَبْتُمْ وَمِمَّا أَخْرَجْنَا لَكُمْ مِنَ الْأَرْضِ[ [البقرة:267]

“Ya ku wa]anda suka yi imani, ku ciyar daga tsarkakan abin da kuka tsuwurwurta da kuma abin da Muka fitar muku daga }asa” (Ba}ara: 267).

Babu shakka kuma ma’adanai suna daga cikin abubuwan da Allah Ma]aukaki ya fitar da su daga cikin }asa saboda mu.

Mafi yawan malamai sun tafi a kan cewa zakka ba ta wajaba a cikin ma’adanai sai idan sun kai nisabi, abin da kuma za a fitar shi ne kashi ]aya bisa hu]u na daga kashi ]aya bisa goma domin an }iyastasu ne a kan zakkar zinariya da azurfa. Kuma za a fidda zakkarsu ne lokacin da aka samesu, ba shara]i ba ne su cika shekara.

b – Rikazi: shi ne abin da aka samu a cikin }asa daga cikin abubuwan da aka binnesu a lokacin jahiliyya (zamanin da ya gabaci musulunci), ko abubuwan da wasu kafirai da suka gabata suka binne ko da ba a lokacin jahiliyya ba,  a daular musulunci  suka rayu, ko a daular kafirai masu ya}i da musulmi, ko wa]anda suke zaman lafiya da su,  yana da kuma wata alama ta kafirci, kamar: sunayensu, sunayen sarakunansu, hotunansu, gicceyensu (cross), ko hotunan gumakansu.

Amma idan ya kasance yana da wata alama ta musulunci kamar: sunan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sunan khalifar musulmi, ko ayar Al}ur’ani mai girma, to wannan tsintuwa ce, idan kuma ya kasance ba shi da wata alama kamar: kwanuka, gwalagwalai na ado, ko narkakkiyar zinariya ko azurfa to wannan shi ma tsintuwa ce, ba a mallakarta sai idan an nemi mai ita ba a samu ba; domin dukiyar musulmi ce ba a san sanda ta fita daga mallakarsa ba.

Abin da yake wajaba a cikn rikazi shi ne kashi ]aya bisa biyar; saboda hadisin Abu Huraira lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»وفي الركاز الخمس«

 “Kashi ]aya bisa biyar na wajaba a cikin rikazi”.

Kuma kashi ]aya bisa biyar din nan yana wajaba ne a cikin wanda yake da yawa da wanda ba shi da yawa a wurin mafi yawan malamai, kuma a wurinsu hanyoyin da ake sarrafashi sune hanyoyin da ake sarrafa fai’i,([12]) abin da ya saura kuma na wanda ya samu ne a wurin dukkannin malamai; domin sayyidina Umar Allah ya yarda da shi haka ya hukunta yayin da wani mutum ya samu rikazi sai ya kar~i kashi ]aya bisa biyar ya ba shi sauran.

6- Hanyoyi Sarrafa Zakka:

Wa]anda ya halatta a ba su zakka su takwas ne:

 1 – Fa}irai: sune wa]anda ba sa samun abin da za su rayu da shi, ko abin da suke samun baya isarsu, to wa]annan za a ba su abin da zai ishesu shekara cikakkiya.

2 – Miskinai: sune wa]anda suke samun rabin  abin da zai ishesu rayuwa ko sama da haka. Bisa ga wannan fassarar su wa]annan halinsu ya fi halin fa}irai kyautatuwa, to su kuma za a ba su cikon abin da zai ishesu shekara cikakkiya.

3 – Masu aiki a kanta: sune wa]anda suke tara zakka daga mutane, kuma suke kiyayeta suke rabawa wa]anda suka cancanta da umarnin shugaba, to wa]annan za a ba su daga zakka gwargwadon ladan akinsu.

4 – Wa]anda ake jawo hankulansu:  wa]annan sun kasu kashi biyu: kafirai da musulmi:

- Kafirai: shi kafiri za a ba shi zakka ne idan ana fatan musuluntarsa, ko kuma ana ganin idan aka ba shi ana sa ran za a kauda sharrinsa daga musulmi, ko makamancin haka.

- Musulmi: shi kuma musulmi za a ba shi zakka ne domin karfafa musuluncinsa, ko don fatan musuluntar ire–irensa, ko makamancin haka.

5 – ‘Yanta bayi: sune bayin da suka yi yarjejeniya da masu gidajensu bisa wani gwargwado na ku]i idan suka bayar za su ‘yantasu, amma suka kasa samar da wannan ku]in, sai a ba su abin da za su fanshi kawunansu da shi, su  daga cikin zakka su fita daga cikin bauta. Wasu malamai kuma sun tafi a kan cewa ya halatta mutum ya sayi bayi da zakka domin ya ‘yantasu.

6 – Wa]anda bashi ya kewaye: sune wa]anda ake binsu bashi, sun kuma kasu kashi biyu: wanda ya ci bashi don kansa, da wanda ya ci bashi don waninsa:

Wanda ya ci bashi don kansa: shi ne wanda ya ci bashi domin bukatu na kansa, kuma ba shi da ikon biya, sai a ba shi abin da zai biya bashinsa da shi daga cikin zakka.

Wanda ya ci bashi don waninsa: shi ne wanda ya ci ba shi domin sulhunta tsakanin wasu, sai a bashi abin da zai taimaka masa ya biya bashin daga cikin zakka ko da ya kasance mawadaci ne.

7- Hanyar Allah: abin da ake nufi da wannan shi ne jihadi. Wa]anda suka fita jihadi don sa kai, wa]anda  ba su da albashi daga baitul mal, za a ba su wani abu daga cikin zakka.

8- [an tafarki: shi ne matafiyi wanda guzurinsa ya yanke  ba shi da abin da zai maida shi garinsa, sai a ba shi daga cikin zakka abin da zai agaza masa ya koma garinsa.

Allah Ma]aukaki ya ambaci wa]annan nau’o’i a cikin fa]insa:

] إِنَّمَا الصَّدَقَاتُ لِلْفُقَرَاءِ وَالْمَسَاكِينِ وَالْعَامِلِينَ عَلَيْهَا وَالْمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمْ وَفِي الرِّقَابِ وَالْغَارِمِينَ وَفِي سَبِيلِ اللَّهِ وَابْنِ السَّبِيلِ فَرِيضَةً مِنَ اللَّهِ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ[ [التوبة:60]

“Ita zakka ana ba da ita ne kawai ga matalauta da miskinai da ma’aikatanta da wa]anda ake jawo hankulansu (zuwa ga musulunci) da kuma game da ‘yanta bayi, da wa]anda bashi ya kewaye, da kuma wajen jihadi saboda Allah da matafiyi (wanda guzurinsa ya yanke). Wannan (hukunci) farilla ce daga Allah. Allah kuwa Masani ne Mai hikima” (Tauba: 60).

7- Zakkar Kono (Fidda Kai):

a – Hikimar Shar’antata:

An shar’anta zakkar kono ne domin tsarkake mai azumi daga maganganun banza da kwarkwasa, domin kuma ciyar da miskinai da wadatar da su ga barin ro}o a ranar salla. Dalili a kan haka hadisin Ibnu Abbas Allah ya yarda da su ya ce:

»فرض رسول الله صلى الله عليه وسلم زكاة الفطر طهرة للصائم من اللغو والرفث وطعمة للمساكين« رواه أبو داود وابن ماجه

 “Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya farlanta zakkar bu]a baki domin tsarkake mai azumi daga maganganun banza da kwarkwasa, domin kuma ciyar da miskinai” Abu Dawud ne da Ibnu Majah suka ruwaito shi.

b – Hukuncinta:

Zakkar kono farillace a kan kowane musulmi da musulma, babba da }arami, ]a da bawa; dalilin haka hadisin Ibnu Umar Allah ya yarda da su ya ce:

»فرض رسول الله صلى الله عليه وسلم زكاة الفطر من رمضان صاعا من تمر أو صاعا من شعير على العبد والحر، والذكر والأنثى، والصغير والكبير من المسلمين، وأمر بها أن تؤدى قبل خروج الناس إلى الصلاة« متفق عليه

 “ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya farlanta zakkar bu]a baki na azumin ramadana sa’i na dabino, ko sa’i na sha’ir, a kan bawa da ]a, na miji da mace, }arami da babba daga cikin musulmi, ya kuma umartci a fitar da zakkar kafin mutane su fita salla” Bukhari da  muslim ne suka ruwaito shi. Kuma ana so a fitar da ita a madadin ]an tayi.

Wajibi ne kuma musulmi ya fitar da ita a madadin kansa da wa]anda ciyar da su take kansa, kamar matarsa da danginsa makusanta. Zakkar kono ba ta wajaba sai a kan wanda ya mallaki fiye da abin da zai ciyar da kansa da iyalansa a ranar salla da ]arenta.

c- Gwargwadon Abin Da Ake Fitarwa:

Abin da ake fitarwa shi ne sa’i ]aya daga mafi yawan abincin gari kamar: alkama, gero, dawa, sha’ir, dabino, zabib (bushesshen inab), cikwi, shinkafa, masara, (da sauransu). Sa’i ]aya kuwa ya yi daidai da kusan kilo gram (2,176).

Baya halatta kuma a fitar da }ima a wurin mafi yawan malamai; domin hakan ya sa~awa abin da ManzonAllah ya umarta, kuma ya sa~awa aikin sahabai Allah ya yarda da su.

d – Lokacin da ake fitar da ita

Lokacin da ake fitar da zakkar bu]a baki lokuta biyu ne: lokacin da ya halatta a fitar da ita shi ne kafin idi da kwana ]aya ko biyu, da lokacin da ya fi falala kuwa shi ne daga ketowar alfijir a ranar idi har zuwa kafin sallar idi, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarni da a fitar da ita kafin mutane su fita salla, ba ya halatta a jinkirtar da ita har zuwa bayan salla, idan ko ya jinkirtar da ita to abin da ya fitar sadaka ce daga cikin sadakoki (ba zakkar kono ba ce), ya kuma aikata zunubi da wannan jinkirin.

e – Hanyoyin Da Ake Sarrafata

Za a bayar da ita ne ga fa}irai da miskinai; domin su ne suka cancanceta fiye da waninsu.

*  *  *


Rukuni Na Hu]u: Azumin Watan Ramadan

1 – Ma’anarsa:

Ma’anar azumi a harshen larabci: kamewa (ga barin wani abu) kowane iri yake.

Ma’anarsa a shari’ance: shi ne kamewa ga barin abubuwa masu karya azumi daga ketowar alfijir na biyu([13]) har zuwa faduwar rana.

2 – Hukuncinsa

Azumin watan ramadana ]aya ne daga cikin rukunan musulunci da tuwasunsa masu girma; dalilin haka fa]in Allah Ma]aukaki:

] يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ[ [البقرة، : 183]

“Ya ku wa]anda suka yi imani, an wajabta azumi a kanku, kamar yadda aka wajabta shi a kan wa]anda suke gabaninku, don ku ji tsoron Allaha” (Ba}ara: 183).

Kuma Ibnu Umar Allah ya yarda shi ya ruwaito ya ce: ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»بني الإسلام على خمس: شهادة أن لا إله إلا الله وأن محمدا رسول الله، وإقام الصلاة، وإيتاء الزكاة، وصوم رمضان، وحج بيت الله« متفق عليه

“An gina musulunci a kan rukunai guda biyar: shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu ManzonAllah ne, da tsai da salla, da ba da zakka, da azumtar ramadana, da zuwa ]akin Allah” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Kuma an farlanta azumin ramadana ne a kan al’umar musulmi  a cikin shekara ta biyu na hijira.

3 – Falalarsa Da Hikimar Shar’antashi:

Watan ramadan lokaci ne mai girma na ]a’a ga Allah, samun damar isarsa ni’ima ce babba kuma falala ce daga Allah mai daraja, yana yiwa wanda ya so falala daga cikin bayinsa; domin kyawawan ayyukansu su karu, a kuma ]aga darajarsu, a shafe miyagun ayyukkansu, dangantakarsu da mahaliccinsu mai girma mai ]aukaka kuma ta karfafa, domin ya rubuta musu lada mai girma, da sakamako mai yawa, su kuma samu yardarsa, zukatansu kuma su cika da tsoronsa.

Daga cikin falalarsa:

1- Fa]in Allah tsarki da ]aukaka sun tabbata a gare shi:

] شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدىً لِلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِنَ الْهُدَى وَالْفُرْقَانِ فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَنْ كَانَ مَرِيضاً أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَى مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ[ [البقرة: 185]

(Wannan shi ne) watan azumi wanda aka saukar da al}ur’ani a cikinsa, don shiriya ga mutane da (hujjoji) mabayyana na shiriya da rarrabewa (tsakanin }arya da gaskiya). Wanda ya halarci watan daga cikin ku, to sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance marar lafiya ko a cikin tafiya sai ya biya adadin wasu kwanakin (daidai yawan wa]anda ya sha). Allah yana nufin sau}i ne a gare ku, kuma ba ya nufin tsanani gare ku, domin ku cika adadin kwanakin, domin kuma ku girmama Allah  a bisa  abin da ya shirye ku, ko kwa gode wa (ni’imominsa) (Ba}ara: 185).

2 – Hadisin da Abu Huraira Allah ya yarda da shi ya ruwaito ya ce: ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»من صام رمضان إيمانا واحتسابا غفر له ما تقدم من ذنبه« متفق عليه

 “Wanda ya yi azumin ramadan yana mai imani yana kuma mai neman lada, to za a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

3 – Abu Huraira ya kuma ruwaito wani hadisin ya ce: ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»… يضاعف الحسنة عشر أمثالها إلى سبعمائة ضعف، قال الله عز وجل: إلا الصوم، فإنه لي وأنا أجزي به، يدع شهوته وطعامه من أجلي، للصائم فرحتان فرحة عند فطره وفرحة عند لقاء ربه، ولخلوف فيه أطيب عند الله من ريح المسك« رواه البخاري ومسلم واللفظ له

 “Allah yana ru~anya kyakkyawan aiki sau goma har zuwa ]ari bakwai, Allah mabuwayi mai girma ya ce: “ban da azumi; domin azumi nawa ne, kuma ni ne zan yi sakayya a kansa; (domin bawa na) ya bar sha’awarsa da abincinsa saboda ni, mai azumi yana da farin ciki biyu: farin ciki lokacin bu]a bakinsa, da farin ciki lokacin gamuwa da Ubangijinsa, warin bakin mai azumi ya fi almiski kamshi a gurin Allah” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi, lafazin kuma na Muslim ne.

4 – Kar~ar addu’ar mai azumi, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»للصائم عند فطره دعوة لا ترد« رواه ابن ماجه

 “Ba a mayar da addu’ar mai azumi a lokacin bu]a bakinsa” Ibnu majah ne ya ruwaito shi.

Saboda haka ya kamata musulmi ya kwa]aitu ya yi amfani da lokacin bu]e bakinsa ya roki Ubangijnsa, akwai fatan ya da ce da wani furji na daga rahamar Allah Mai girma Mai ]aukaka; domin ya samu arzikin duniya da lahira.

5 – Allah ya ke~ewa masu azumi wata kofa daga cikin kofofin Aljanna; domin girmamasu da bambantasu daga waninsu, babu wanda zai shiga ta  wannan kofar sai masu azumi. An kar~o daga Sahl ]an Sa’ad Allah ya yarda shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»إن في الجنة بابا يقال له الريان، فإذا كان يوم القيامة قيل: أين الصائمون، فإذا دخلوا أغلق عليهم فلم يدخل منه أحد« متفق عليه

“Lallai akwai wata kofa a cikin Aljanna da ake kiranta (Al rayyan), idan ranar kiyama ta kasance sai a ce: ina masu azumi? (sai a bu]e musu su shiga), idan suka shiga sai a rufe, daga nan kuma babu wanda zai shiga ta wannan kofar” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

6 – Azumi zai yi wa mai yinsa ceto. An kar~o daga Abdullahi ]an Amru ]an Al’as Allah ya yarda da su ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»الصيام والقرآن يشفعان للعبد يوم القيامة، يقول الصيام أي رب منعته من الطعام والشهوة فشفعني فيه، ويقول القرآن: منعته النوم بالليل فشفعني فيه، قال: فيشفعان« رواه أحمد

“Azumi da Al}ur’ani za su yi wa bawa ceto a ranar kiyama, sai azumi ya ce: ya Ubangiji na hana shi abinci da sha’awa, ka kar~i cetona a kansa, Al}ur’ani kuma ya ce: na hana shi barci cikin dare ka kar~i cetona a kansa, sai Allah ya kar~i cetonsu” Ahmad ne ya ruwaito shi.

7 – Azumi yana sa musulmi ya saba da ha}uri,da juriya; domin azumi yana sa shi ya bar abubuwanda yake so da sha’awowinsa, ya kuma fi karfin son ransa.

4 – Sharru]an Wajabcinsa:

Malamai sun ha]u a kan cewa azumi yana wajaba ne a kan kowane musulmi balagagge, mai hankali, mai lafiya, mazauni, yana kuma wajaba a kan mace idan ta kasance tana cikin tsarki ba ta haila ko jinin biki.

5 – Ladubbansa

1 - Nisantar yi da wasu da kai-kawo, da sauran abubuwan da Allah Ma]aukaki ya haramta, saboda haka wajibi ne a kan musulmi ya kame harshensa ga barin abubuwan da aka haramta, kuma ya kiyaye shi ga barin afkawa mutuncin wasu, Annabi tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»من لم يدع قول الزور والعمل به فليس لله حاجة في أن يدع طعامه وشرابه« رواه البخاري

“Wanda bai bar maganar zur da aiki da ita ba, to Allah ba shi bu}atuwa ga barin cinsa da shansa”([14]) Bukhari ne ya ruwaito shi.

2 – Ka da ya bar abincin sahur, saboda abincin sahur yana taimakawa mai azumi ya samu karfin yin azumi, sai ya wuni yana cikin raha, ya kuma yi ayyukansa cikin nisha]i da kazar-kazar, ha}i}a Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwa]aitar a kan haka da fa]insa:

»السحور أكله بركة، فلا تدعوه ولو أن يجرع أحدكم جرعة من ماء، فإن الله عز وجل وملائكته يصلون على المتسحرين« رواه أحمد

“Cin abincin sahur yana da albarka, saboda haka ka da ku bar shi, ko da ]ayanku zai ]an kurbi ruwa ne; domin Allah mai girma mai ]aukaka yana tsarkake masu yin sahur, Mala’ikunsa kuma suna yi musu addu’a” Ahmad ne ya ruwaito shi.

3 – Ya gaggauta bu]a baki bayan ya tabbatar da faduwar rana, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»لا يزال الناس بخير ما عجلوا الفطر« متفق عليه

 “Mutane ba za su gushe ba suna cikin alheri muddin sun gaggauta bu]a baki” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

4 – Ya kwadaitu a kan bu]a baki da lubiyar dabino ko dabino; domin hakan yana daga sunna, Anas Allah ya yarda shi ya ce:

»كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يفطر قبل أن يصلي على رطبات، فإن لم تكن رطبات فتمرات، فإن لم تكن حسا حسوات من ماء« رواه أبو داود

 “Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana bu]a baki da lubiyar dabino kafin ya yi salla, idan kuma bai samu lubiyar dabino ba, sai ya bu]e da dabino, idan bai samu dabino ba, sai ya kwankwadi ruwa” Abu Dawud ne ya ruwaito shi.

5 – Yawaita karatun Al}ur’ani, da ambaton Allah Ma]aukaki, da gode masa da yaba masa, da yin sadaka da kyautatawa mutane, da yawaita nafilfilu da wasunsu daga cikin ayyuka kyawawa, dalilin haka hadisin da Ibnu Abbas ya ruwaito Allah ya yarda su ya ce:

»كان رسول الله صلى الله عليه وسلم أجود الناس بالخير، وكان أجود ما يكون في رمضان حين يلقاه جبريل، وكان يلقاه في كل ليلة من رمضان، فيدارسه القرآن، فلرسول الله صلى الله عليه وسلم حين يلقاه جبريل أجود من الريح المرسلة« روه البخاري ومسلم

 “Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance  ya fi kowa yin kyauta, ya kuma fiye yin kyauta a cikin watan Ramadan yayin da Mala’ika Jibrilu yake gamuwa da shi, Mala’ika Jibrilu ya kasance yana gamuwa da shi a kowane dare na watan Ramadan, sannan ya yi masa darasu, kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana kyauta yayin da Jibrilu yake gamuwa da shi fiye da iskar da ake aikowa gabanin ruwan sama”([15]) Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

6 – Abubuwan Da ke |ata Azumi:

1 – Ci da sha da rana da gan-gan, haka kuma da sauran abubuwa masu karya azumi kamar: allurai masu ciyarwa, ko shan magunguna, domin su ma daidai suke da ci da sha wajen hukunci, amma fitar da jini mara yawa daga jiki, irin jinin da ake ]auka domin gwada lafiya, wannan ba shi da tasiri wajen karya azumi.

2 – Jima’i da rana, yana ~ata azumi, kuma wajibi ne a kan wanda ya aikata haka ya tuba zuwa ga Allah Ma]aukaki domin ya keta hurumin wannan watan, kuma zai rama azumin wannan ranar da ya yi jima’i a cikinsa, kaffara kuma ta wajaba a kansa, sai ya ‘yanta bawa, idan bai samu ba sai ya yi azumin wata biyu a jere, idan bai iya ba sai ya ciyar da miskinai sittin,  ya baiwa kowane miskini rabin sa’i na alkama ko waninsa daga cikin abincin mutanen garin, dalili a kan haka hadisin Abu Huraira Allah ya yarda da shi ya ce:

»بينما نحن جلوس عند النبي صلى الله عليه وسلم إذ جاءه رجل، فقال: يا رسول الله هلكت، قال: مالك؟ قال: وقعت على امرأتي وأنا صائم، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: هل تجد رقبة تعتقها؟ قال: لا. قال: فهل تستطيع أن تصوم شهرين متتابعين؟ قال: لا. قال: فهل تجد إطعام ستين مسكينا؟ قال: لا. قال: فمكث عند النبي صلى الله عليه وسلم فبينما نحن على ذلك أتي النبي صلى الله عليه وسلم بعرق فيه تمر –والعرق المكتل-، قال: أين السائل؟ قال: أنا، قال: خذ هذا فتصدق به، فقال الرجل: على أفقر مني يا رسول الله، فوالله ما بين لا بتيها يريد الحرتين- أهل بيت أفقر من أهل بيتي، فضحك النبي صلى الله عليه وسلم حتى بدت أنيابه، ثم قال: أطعمه أهلك« رواه البخاري ومسلم

“ Wani lokaci muna zaune a wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai wani mutum ya zo masa, sai ya ce: ya Manzon Allah na halaka, sai Annabi ya ce da shi: me ya sameka?, sai ya ce: na sadu da iyalina ne ina azumi, sai Manzon Allah ya ce: shin kana da bawan da za ka ‘yanta?, ya ce: ba ni da shi, ya ce masa: to za ka iya ka yi azumin wata biyu a jere?, ya ce: a’a, ya ce: to za ka iya ciyar da miskinai sittin?, ya ce: a’a, sai ya zauna yana saurarawa, muna cikin haka sai aka kawowa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dabino cikin mangala, sai Annabi ya ce: ina mai tambayar?, sai mutumin ya ce: ga ni, sai ya ce: ka ]auki wannan  ka ba da shi sadaka, sai mutumin ya ce: shin akwai wanda ya fi ni talauci da zan ba shi?, na rantse da Allah babu a tsakanin labar([16]) Madina ta yammacinta da ta gabashinta wasu mutane da suka fi ni bukata, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi dariya har fi}o}insa suka bayyana, sannan ya ce: ka ciyar da shi iyalinka” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

3 – fitar da maniyyi a sanadiyar sumbatar mace ko shafarta, ko istimna’i([17]), ko don maimata kallo, idan ya yi maniyyi a sanadiyar ]aya daga cikin wa]annan abubuwa azuminsa ya ~aci, ramuwa ta kama shi, kuma zai kame ~akinsa a sauran lokaci na ranar, amma babu kaffara a kansa, sai dai ya wajaba a gare shi ya nuna nadamarsa ya tuba, ya nemi gafara ga Allah, ya kuma nisanci duk wani abu da kan iya motsa sha’awarsa, amma idan yana barci ne sai ya yi mafarki ya kuma yi maniyyi, to wannan ba zai yi wani tasiri ba a kan azuminsa, kuma babu komai a kansa, sai wanka.

4 – Yin amai da gan–gan, amma abin da ya fita ba da sonsa ba babu komai a kansa ba zai yi tasiri ba a kan azuminsa, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»من ذرعه القيء فليس عليه قضاء، ومن استقاء عمدا فليقض« رواه أبو داود والترمذي

“Wanda amai ya rinjaye shi babu ramuwa a kansa, wanda kuma ya yi amai da gan–gan, sai ya rama” Abu Daud ne da Tirmizi suka ruwaito shi.

5 – Jinin haila ko jinin biki, a farkon rana suka zo ko a karshensa, ko da dabda faduwar rana ne.

Abin da ya fi ga mai azumi shi ne kada ya yi kaho; domin kada ya bijirowa abin da zai ~ata azuminsa, kada kuma ya bayar da jininsa sai da larurar agazawa mara lafiya da makamancinsa. Amma fitar jini a sanadiyyar ha~o ko tari ko cire hakori da makamancinsu ba su da tasiri a kan azumi.

7 – Sauran Hukunce–Hukuncen Azumi

1 – Azumin ramadan yana wajaba ne da ganin wata, saboda fa]in Ma]aukaki:

]فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ[ [البقرة: 185]

“Wanda ya halarci watan daga cikin ku, to sai ya azumce shi” (Ba}ara: 185).

Kuma ganin musulmi ]aya ga wata ya wadatar, saboda hadisin da Ibnu Umar Allah ya yarda su ya ruwaito ya ce:

»تراءى الناس الهلال فأخبرت رسول الله صلى الله عليه وسلم أني رأيت فصام وأمر الناس بصيامه« رواه أبو داود والدارمي وغيرهما

“Mutane sun nemi ganin wata sai na baiwa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi labari cewa na ga wata, sai ya yi azumi ya kuma umarci mutane su yi azumi” Abu Dawud ne da Darimi da waninsu suka ruwaito shi.

Sha’anin azumi a kowace }asa ya dogara ne a kan hukuncin shugaban }asar, idan ya hukunta za a yi azumi ko ba za a yi ba ya wajaba a yi masa ]a’a, idan kuma shugaban ya kasance ba musulmi ba ne, sai a yi aiki da hukuncin da cibiyar musulmi na }asar da makamancinta (kamar majalisan malamai)  suka yanke domin ha]a kan musulmi.

Kuma ya halatta a yi amfani da na’urori na hangen nesa wajen ganin wata, ba ya halatta a dogara da lissafin falaki da ganin taurari wajen tabbatar da fara watan azumi ko bu]a baki, abin dogaro shi ne ganin wata, kamar yadda Allah Ma]aukaki ya ce:

]فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ[[البقرة: 185]

“Wanda ya halarci watan daga cikin ku, to sai ya azumce shi” (Ba}ara: 185).

Wanda ya halicci watan ramadan ya wajaba a gare shi ya yi azumi, rana ta yi tsawo ko ba ta yi ba.

Abin da ake la’akari da shi wajen fara azumi a kowane gari shi ne ganin wata a mafitartsa, bisa ga magana mafi rinjaye daga cikin maganganun malamai, domin malamai sun ha]u a kan cewa mafitar jirajiran wata suna  bambanta (a tsakanin garuruwa masu nesa da juna), wannan abu ne sananne da baya bukatan nazari. Dalilin kasancewar ganin wata shi ne abin la’akari fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»صوموا لرؤيته وأفطروا لرؤيته، فإن غم عليكم فأكملوا شعبان ثلاثين يوما« أخرجه البخاري ومسلم

“Ku yi azumi idan kuka ga wata, kuma ku yi salla  idan kuka gan shi, idan girgije (ko makamancinsa) suka hanaku ganinsa sai ku cika Sha’aban kwana talatin” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

2 -  Ya wajaba a kan mai azumi ya ]aura niyyar yin azumi tun cikin dare; domin fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»إنما الأعمال بالنيات، وإنما لكل امرئ ما نوى« متفق عليه

“Ayyuka suna inganta ne kawai da niyya, kuma kowane mutum abin da ya yi niyya ne kawai zai samu” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Kuma saboda fa]insa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»من لم يجمع الصيام قبل الفجر فلا صيام له« أخرجه أحمد وأبو داود والترمذي والنسائي من حديث حفصة - رضي الله عنها -

“Wanda bai tara niyyar yin azumi ba kafin }etowar alfijir, to ba shi da azumi” Ahmad ne da Abu Daud da Tirmizi da Nasa’i suka ruwaito shi daga hadisin Hafsa Allah ya yarda da ita.

3 – Ba ya halatta ga kowa ya bar azumi ko ya karya shi tsawon watan azumi, sai idan ya kasance yana da wani uzuri, kamar: mara lafiya, ko matafiyi, ko mace mai haila, ko mai jinin bi}i, ko mai ciki, ko mai shayarwa, Allah Ma]aukaki ya ce:

] فَمَنْ كَانَ مِنْكُمْ مَرِيضاً أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ[ [البقرة: 184]

“Wanda kuwa ya kasance ba shi da lafiya daga cikinku, ko kuwa yana cikin tafiya, (ya sha azumi) sai ya cika adadin abin da ya sha daga baya”

Mara lafiyan da azumi zai wahalar da shi, ba zai iya barin ci da sha ba, kuma zai cutu da yin azumi ya halatta a gare shi ya bar azumi sannan ya rama kwanakin da ya sha.

Kuma mace mai ciki da mai shayarwa idan suka jiwa kawunansu tsoro, sai su bar azumi, kuma ramuwa ta wajaba a gare su, da ha]uwar malamai; domin suna matsayin mara lafiya wanda ya ke jiwa kansa tsoro.

Hakanan idan suka tsoracewa kawunansu da ‘ya‘yansu, ko kuma ‘ya‘yansu ka]ai, sai su bar azumi, kuma ramuwa ta wajaba a gare su, saboda hadisin Anas daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»إن الله وضع عن المسافر نصف الصلاة والصوم، وعن الحبلى والمرضع« رواه النسائي وابن خزيمة وهو حديث حسن

 “Ha}i}a Allah ya ]aukewa matafiyi rabin salla da rabin azumi, haka nan ma ya ]aukewa mace mai ciki da mai shayarwa” Nasa’i ne da Ibnu Khuzaima suka ruwaito shi, kuma wannan hadisi ne hasan (mai kyau).

Amma tsoho da tsohuwa masu shekaru an yi musu rangwame su bar azumi idan azumin zai wahalar da su matsananciyar wahala, kuma ya  wajaba a gare su su ciyar da miskini ]aya a madadin kowane wuni, saboda hadisin da Bukhari ya ruwaito daga A]a’ cewa ya ji Ibnu Abbas Allah ya yarda da shi yana karanta (ayar):

] وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ[ [البقرة: 184]

“Kuma akwai fansa ta ciyar da miskini a kan wa]anda suka sha tare da ikon yin sa (da }yar) (Ba}ara: 184).

Sai Ibnu Abbas ya ce:

»ليست منسوخة هي للشيخ الكبير والمرأة الكبيرة لا يستطيعان أن يصوما فيطعمان مكان كل يوم مسكينا«

“Ba a shafe hukuncin wannan ayar ba, ayar ta shafi tsoho ne da tsohuwa wa]anda ba za su iya azumi ba, za su ciyar da miskini ]aya a madadin kowace rana”.

4 – Tafiya tana daga cikin uzururruka da suke halatta barin azumi, domin hadisin Anas Allah ya yarda shi:

»كنا نسافر مع النبي صلى الله عليه وسلم، فلم يعب الصائم على المفطر ولا المفطر على الصائم« متفق عليه

“Mun kasance muna tafiya tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, mai azumi ba ya ga laifin mara azumi, hakanan mara azumi ba ya ga laifin mai azumi” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

* * *


 Rukuni Na biyar: Hajji

 1 – Ma’anarsa

Ma’anar hajji a cikin harshen larabci shi ne: nufi, ana cewa: (fulan hajjana) ma’ana: wane ya nufemu ya iso wurinmu.

Ma’anarsa a shari’ance  shi ne: nufin makka domin aiwatar da wata ibada da wata siffa na musamman, a wani lokaci }ayyadadde, da  wasu sharru]a }ayyadaddu.

 2 – Hukuncinsa

Ha}i}a al’umar musulmi sun ha]u a kan wajabcin hajji a kan wanda yake da iko sau ]aya a rayuwarsa, haka nan kuma sun ha]u a kan kasancewarsa ]aya daga cikin rukunan musulunci guda biyar, Allah Ma]aukaki ya ce:

]وَلِلَّهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ الْبَيْتِ مَنِ اسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلاً وَمَنْ كَفَرَ فَإِنَّ اللَّهَ غَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ[ [آل عمران: 97]

“Kuma Allah ya ]ora hajjintar ]akin (Ka’aba) a kan mutane ga wanda ya sami ikon zuwa gare shi” (Ali Imran: 97).

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»بني الإسلام على خمس: شهادة أن لا إله إلا الله وأن محمدا رسول الله وإقام الصلاة، وإيتاء الزكاة، وصوم رمضان، وحج بيت الله« متفق عليه

“An gina musulunci a kan rukunai biyar: shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, lallai kuma Muhammadu Manzon Allah ne, da tsai da salla, da ba da zakka, da azumin ramadan, da zuwa ]akin Allah” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Kuma ya ce a hajjin bankwana:

»يا أيها الناس إن الله قد فرض عليكم حج البيت فحجوا« رواه مسلم

“Ya ku mutane ha}i}a Allah ya farlanta muku hajji, saboda haka ku yi hajji” Muslim ne ya ruwaito shi.

3 – Falalarsa Da Hikimar Shar’anta shi

Ha}i}a dalilai masu yawa sun zo a kan haka, daga cikinsu fa]in allah Ma]aukaki:

]وَأَذِّنْ فِي النَّاسِ بِالْحَجِّ يَأْتُوكَ رِجَالاً وَعَلَى كُلِّ ضَامِرٍ يَأْتِينَ مِنْ كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍ لِيَشْهَدُوا مَنَافِعَ لَهُمْ وَيَذْكُرُوا اسْمَ اللَّهِ فِي أَيَّامٍ مَعْلُومَاتٍ عَلَى مَا رَزَقَهُمْ مِنْ بَهِيمَةِ الْأَنْعَامِ[ [الحج: 27- 28]

“Kuma ka yi shela cikin mutane saboda yin Hajji, za su zo maka suna masu tafiya a }asa da kuma kan kowane ra}umi, za su zo maka daga kowane lungu mai nisa. Domin su halarci abubuwa na amfani a gare su, kuma su ambaci sunan Allah a cikin kwanaki sanannu a kan abin da muka arzuta su da shi na dabbobin jin da]i” (Hajj: 27 – 28).

Hajji ya }unshi amfanunnuka masu girma na duniya da lahira ga musulmi baki ]aya, domin za a ga cewa ayyuka na ibada iri-iri sun tattaru a cikinsa, kamar: ]awafi, Safa da Sarwa, tsayuwar arfa, kwanan Muzdalifa, jifa, kwanan kwanakin mina, aske gashin kai, da yawan ambaton allah, don neman kusanci ga allah, da kaskantar da kai  da komawa gare shi; saboda haka ne ma hajji ya kasance ]aya daga cikin mafi girman sabubba na kankare zunubi, da shiga Aljanna.

An kar~o daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi ya ce: na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:

»من حج هذا البيت فلم يرفث ولم يفسق رجع من ذنوبه كيوم ولدته أمه« رواه البخاري ومسلم

“Wanda ya yi hajji, bai yi jima’i ba, bai kuma yi fasikanci ba, zai koma ya zama ba shi da zunubi kamar ranar da mahaifiyar shi ta haife shi” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

An kuma kar~o daga Abu Huraira cewa lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»العمرة إلى العمرة كفارة لما بينهما، والحج المبرور ليس له جزاء إلا الجنة« رواه البخاري ومسلم

 “Umra zuwa umra suna kankare zunuban da suke tsakaninsu, hajji nagartacce kuma ba shi da wani lada sai Aljanna” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

 An kuma kar~o daga gare shi Allah ya yarda da shi ya ce:

»سئل رسول الله صلى الله عليه وسلم أي الأعمال أفضل؟ قال: إيمان بالله ورسوله، قيل: ثم ماذا؟ قال: جهاد في سبيل الله، قيل: ثم ماذا؟ قال: حج مبرور« متفق عليه

 “An tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanne aiki ne ya fi falala? Sai ya ce: “imani da Allah da Manzonsa” sai aka ce: sai me kuma? Sai ya ce: “yin jihadi saboda Allah” sai aka ce: sai me kuma? Sai ya ce: “hajji nagartacce” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

An kuma karbo daga Abdullahi ]an Mas’ud Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»تابعوا بين الحج والعمرة، فإنهما ينفيان الفقر والذنوب كما ينفي الكير خبث الحديد والذهب والفضة، وليس للحجة المبرورة ثواب إلا الجنة« رواه الترمذي وقال حديث حسن صحيح

“Ku yawaita hajji da umra, domin su suna kore talauci kamar yadda zugazugi yake gusar da dattin karfe da zinariya da azurfa, hajji nagartacce kuma ba shi da wani lada sai Aljanna” Tirmizi ne ya ruwaito shi, ya ce kuma: hadisi ne kyakkyawa ingantacce.

Daga cikin amfanunnuka na hajji ha]uwar musulmi daga kowane lungu mai nisa, a wurin da yake shi ne wurin da Allah ya fi so, da sanin junansu, da taimakon junansu a kan aikin alheri da tsoron Allah, da daidaituwarsu wajen zantuttuka da zikiri, da ayyuka. Wannan wata tarbiya ce ga musulmi domin su ha]a kai su ha]u a kan a}ida da ibada, su kuma ha]u a kan manufa ]aya, da hanyar cimmata. Da wannan ha]uwar ta su ne za a iya samun sanin junan da kusanci da kulawa da juna, kamar yadda Allah ya ce:

]يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرٍ وَأُنْثَى وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوباً وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ[ [الحجرات: 13]

“Ya ku mutane, ha}i}a mu muka halicce ku daga na miji da mace, muka kuma sanya ku }ungiya-}ungiya da }abilu (daban-daban) don ku san juna, ha}i}a mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah, ha}i}a Allah Masani ne, Mai sani ne da ba]ininku” (Hujurat: 13).

 4 – Sharru]an Wajabcinsa:

a- Babu sa~ani tsakanin malamai cewa lallai hajji yana wajaba ne da sharru]a biyar: musulunci, hankali, balaga, ‘yanci, da iko.

Amma ita mace shara]in wajabcin hajji a kanta –bayan wa]anda suka gabata- shi ne samun muharrami([18]) a cikin tafiya zuwa hajji, dalilin haka fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin hadisin Abu Huraira Allah ya yarda shi:

»لا يحل لامرأة تؤمن بالله واليوم الآخر أن تسافر مسيرة يوم إلا ومعها ذو محرم« متفق عليه

“Ba ya halatta ga matar da ta yi imani da Allah da ranar lahira ta yi tafiyar wuni, sai da muharraminta a tare da ita” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Ha}i}a malaman fikihu sun kasa wa]annan sharru]a kashi uku:

Na farko: shara]in wajabci da inganci, wa]annan kuma su ne musulunci da hankali, saboda haka hajji ba ya wajaba a kan kafiri da mahaukaci, kuma ba ya inganta daga gare su idan suka yi, domin ibada ba ta hau kansu ba.

Na biyu: shara]in wajabci da wadatarwa, wa]annan su ne balaga da ‘yanci. Su ba shara]i ba ne na inganci, idan yaro da bawa su ka yi hajji, hajjinsu ya inganta amma kuma ba ya wadatarwa ga hajjin farilla.

Na uku: shara]in wajabci, wannan shi ne iko, idan wanda ba shi da iko ya yi hajji cikin }unci da wahala, ya yi tafiya ba tare da guzuri ko abin hawa ba hajjinsa ya inganta.

 b- Hukuncin Yin Hajji A Madadin Wani:

 Babu sa~ani tsakanin malamai cewa wanda ya mutu kafin ya samu damar yin hajji, hajji ya sauka daga kansa, wanda kuma ya mutu bayan ya samu damar yin hajji bai yi ba har ya mutu, shin hajji yana sauka daga kansa ko kuwa ba ya sauka?

Ingantacciyar magana  -in sha Allahu ta’ala- shi ne hajji ba ya sauka daga kansa, ya wajaba a kan magadansa su yi masa hajji daga cikin dukiyarsa, ya yi wasiyya da haka ko bai yi ba, domin wannan wani wajibi ne da ya tabbata a kansa kamar bashi daidai-wa-daida, dalilin haka hadisin Ibnu Abbas Allah ya yarda da su cewa wata mata ta yi bakance za ta yi aikin hajji sai ta rasu, sai ]an uwanta ya zo wajen Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tambaye shi a kan haka, sai Annabi ya ce masa:

»أرأيت لو كان على أختك دين أكنت قاضيه؟ قال: نعم، قال: فاقضوا الله فهو أحق بالوفاء« رواه النسائي

 “Ka ba ni labari idan da za a ce akwai bashi a kan ‘yar uwarka shin zaka biya?, ya ce: zan biya, sai Annabi ya ce: “ku biya wa Allah bashinsa domin shi ne ya fi cancanta da a cika masa hakkinsa” Nasa’i ne ya ruwaito shi.

 c- Wanda Bai Yiwa Kansa Hajji ba Shin Zai yi wa Waninsa?

Ingantacciyar magana ita ce ba zai yiwa waninsa hajji ba matsawar bai yi wa kansa tun farko ba, dalilin haka shi ne mashahurin hadisin nan cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji wani mutum yana cewa:

»لبيك عن شبرمة، قال: من شبرمة؟ قال: أخ لي أو قريب لي، فقال عليه الصلاة والسلام: حججت عن نفسك؟ قال: لا، قال: حج عن نفسك ثم عن شبرمة« رواه أحمد وأبو داود وابن ماجه والبيهقي وصححه

 “Labbaika an Shubruma (na kar~a maka a madadin Shubruma), Annabi ya ce: “wane ne Shubruma?”, ya ce: ]an uwana ne ko makusancina, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata  gare shi ya ce: “ka yi hajjin kanka?” Ya ce: ban yi ba, sai ya ce masa: “ka yiwa kanka sanna ka yiwa Shubruma”. Ahmad ne da Abu Dawud da Ibnu Majah, da Baiha}i suka ruwaito shi. Baiha}i ya inganta shi.

Ingantacciyar magana kuma ita ce ya halatta a yi hajji a madadin gajiyayye wanda ba shi da karfin zuwa hajji; dalilin haka hadisin Fadul ]an Abbas Allah ya yarda su, a cikinsa:

»أن امرأة من خثعم قالت: يا رسول الله إن فريضة الله على عباده في الحج أدركت أبي شيخا كبيرا لا يثبت على الراحلة أفأحج عنه؟ قال: نعم« وذلك في حجة الوداع. متفق عليه واللفظ للبخاري

“Wata mace daga (kabilar) Khas’am ta ce: ya Manzon Allah, ha}i}a hajji na farilla da Allah ya ]orawa bayinsa ya riski mahaifina alhali yana tsoho ba zai iya zama a kan dabba ba, shin ya halatta in yi masa hajji? Annabi ya ce: “ya halatta” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Wannan hadisin kuma ya kasance ne a hajjin bankwana.

 d- Shin wajabcin hajji a bisa gaggawa ya ke ko za a iya a jinkirta shi?

  Magana mafi rinjaye daga cikin maganganun malamai -in sha Allahu ta’ala- ita ce hajji yana wajaba a bisa gaggawa duk sanda sharru]ansa suka cika; dalilin haka shi ne gamewar fa]in Allah:

]وَلِلَّهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ الْبَيْتِ مَنِ اسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلاً[ [آل عمران: 97]

“Kuma Allah ya ]ora hajjintar ]akin (Ka’aba) a kan mutane ga wanda ya sami ikon zuwa gare shi” (Ali Imran: 97).

Da kuma fa]insa:

]وَأَتِمُّوا الْحَجَّ وَالْعُمْرَةَ لِلَّهِ[ [البقرة: 196]

“Kuma ku cika (ayyukan) Hajji da Umra saboda Allah” (Ba}ara: 196).

Ha}i}a ya zo a cikin hadisin Ibnu Abbas Allah ya yarda da su, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»تعجلوا إلى الحج - يعني الفريضة -، فإن أحدكم لا يدري ما يعرض له« رواه أبو داود وأحمد والحاكم وصححه

“Ku gaggauta zuwa aikin hajji (na farilla); domin ]ayanku bai san abin da zai bijiro masa ba” Ahmad ne da Abu Dawud da Hakim suka ruwaito shi, kuma Hakim ya inganta shi.

 5 – Rukunan Hajji:

Rukanan hajji guda hu]u ne:

1-    Yin harama.

2-    Tsayuwar Arfa.

3-    [awafin ifa]a.

4-    Sa’ayi tsakanin  Safa da Marwa.

Saboda haka hajji ba ya cika sai da wa]annan rukunan.

 Rukuni Na farko: Yin Harama

Ma’anarsa: Abin da ake nufi da yin harama shi ne niyyar shiga cikin aikin hajji ko umra.

Mi}atinsa: mi}ati na yin harama nau’i biyu ne: mikati na lokaci, da kuma mikati na wuri.

Mi}ati na lokaci: shi ne watannin Shawwal, zul }a’ada, da (goma ga) zul hijja, wa]anda  Allah ya ce game da su:

]الْحَجُّ أَشْهُرٌ مَعْلُومَاتٌ[ [البقرة: 197]

(lokacin) Hajji watanni ne sanannu” (Ba}ara: 197).

Mi}ati na wuri: su ne iyakokin da bai halatta  ba ga maniyyaci ya ketaresu ya zarce zuwa Makka ba tare da ya yi niyya ba, wa]annan iyakoki su biyar ne:

1-     Zul Hulaifa: ana kiransa a yau (A’bar Ali) kuma shi ne mikatin mutanen Madina, tsakaninsa da makka nisan kilo mita (336) mil (224).

2-     Aljuhfa: wani gari ne tsakaninsa da Bahrul Ahmar nisan kilo mita (10), kuma tsakaninsa da Makka nisan kilo mita (180), mil (120), shi ne mikatin mutanen Masar da Sham, da Moroko (da kasashen da suke makwabtaka da ita) da kasashen Afrika ta yamma, da mutanen Spain da Rom. Amma a yanzu mutane suna niyya ne a wurin da ake kira (Rabig) domin yana daura da Juhfa.

3-     Yalamlam: ana kiransa a yau (Al sa’adiyya). Wani dutse ne daga cikin duwatsun Tihama, tsakaninsa da Makka nisan kilo mita(72) mil (48), kuma shi ne mikatin mutanen Yaman da Jawa (Indunisia) da India, da Sin (China).

4-     {arnul Manazil: ana kiransa a yau (Al Sail Al kabir), tsakaninsa da Makka nisan kilo mita (72), mil (48), kuma shi ne mi}atin mutanen Naj’d da Ta’if.

5-     Zatu Ir’}: ana kiransa a yau (Al ]ariba), an kuma kira shi da wannan ne; domin akwai ir’} (karamin dutse) a cikinsa, tsakaninsa da Makka nisan kilo mita (72) mil (48), kuma shi ne mikatin mutanen gabas da Ira}, da Iran.

Wa]annan su ne mikati na lokaci da ba ya halatta ga maniyacci da aikin hajji ko umra ya ketaresu ya zarce zuwa Makka ba tare da ya yi niyya ba.

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyanasu, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Ibnu Abbas Allah ya yarda su inda ya ce:

»وقت رسول الله صلى الله عليه وسلم لأهل المدينة ذا الحليفة، ولأهل الشام الجحفة، ولأهل نجد قرن المنازل، ولأهل اليمن يلملم هن لهن ولمن أتى عليهن من غير أهلهن ممن أراد الحج أوالعمرة، ومن كان دون ذلك فمن حيث أنشأ حتى أهل مكة من مكة«متفق عليه

“Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya }ayyade Zul hulaifa (ya zama mi}ati) ga mutanen Madina, Aljuhfa ga mutanen Sham, {arnul Manzil ga mutanen Naj’d, Yalamlam ga mutanen Yaman, su din nan mikati ne na mutanen wa]annan wurare, da wanda ya bi ta kansu ba daga mutanen wuraren ba, wanda ya yi niyya da hajji ko umra, wanda kuma yake zaune tsakanin Makka da mikati, muhallinsa shi ne mikatinsa, hakan nan  mutanen Makka su ma za su yi harama cikin garin Makka” Bukahri da Muslim ne suka ruwaito shi. 

Kuma Muslim ya ruwaito daga hadisin Jabir Allah ya yarda da shi:

»مهل أهل العراق ذات عرق«

“Mikatin mutanen Ira} Zatu Ir’}”.

Wanda kuma bai  biyo ta wani mikati ba a kan hanyarsa, sai ya yi niyya idan ya zo daidai da mikati mafi kusa zuwa gare shi, haka nan wanda ya hau jirgin sama zai yi niyya idan ya zo daidai da mikati, bai halatta ba ya jinkirta harama har ya sauka a filin jirgin sama na Jidda kamar yadda wasu maniyyata suke yi; domin Jidda ba mikati ba ne sai ga mutanen da suke zaune a cikinta, ko kuma wanda ya shigo cikinta ba shi da niyyar aikin hajji ko umra, sai daga baya ya so ya yi niyya, to ya hallatta ya yi niyya cikin Jidda, amma ban da wa]annan duk wanda ya yi niyya a cikin Jidda ha}i}a ya bar wajibi, wato yin harama a mikati, fidiya ta kama shi.

Hakanan kuma wanda ya ketare mikati ba tare da harama ba ya wajaba ya koma mikatin ya yi niyya, idan bai koma ba sai ya yi niyya daga inda yake to fidiya ta hau kansa, sai ya yanka akuya, ko ya ]auki kashi ]aya bisa bakwai na rakumi ko sa, ya rabawa miskinan harami, shi ba zai ci ba daga abin da ya yanka ]in.

Siffar Yin Harama:

Mustahabbi ne yin shiri domin yin harama da wanka da tsafta da gusar da gashin da ake son gusar da shi, da shafa turare a jiki, na miji kuma ya cire ]inkakken kaya, ya sa gyauto da mayafi farare masu tsafta.

Magana mafi inganci daga cikin maganganun malamai harama ba ta da wata salla ta musamman([19]), sai dai idan maniyyaci ya dace da lokacin sallar farilla zai yi niyya bayan salla; saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbara a gare shi ya yi niyya ne bayan salla. Sannan kuma an ba shi zabi ya yi niyya da ]ayan nau’o’in hajii guda uku: tammatu’i, kirani, ifradi.

Tamattu’i: shi ne mutum ya yi niyyar umra a cikin watannin hajji, bayan ya gama ]awafinsa da sa’ayinsa, kuma ya yi aski, sai ya jira zuwa ranar takwas ga wata, sai ya yi niyyar aikin hajji a ranar takwas ga watan Zul hijja, a wannan shekara.

{irani: shi ne maniyyaci ya yi harama da umra da aikin hajji a lokaci ]aya, ko kuma ya yi harama da umra sai daga baya ya shigar da aikin hajji a cikinta kafin ya fara ]awafin umra.

Ifradi: shi ne maniyyaci ya yi harama da aikin hajji shi ka]ai, ya kuma zauna cikin haraminsa har ya gama aikin hajjinsa.

Kuma mai Tamattu’i da mai {irani akwai hadaya a kansu idan su ba mutanen Makka ba ne.

An kuma yi sa~ani game da mafi falalar wa]annan nau’o’in aikin hajji, amma abin da wasu bijiman malamai suka tafi akai shi ne tamattu’i ya fi falala.

Idan maniyyaci ya yi harama da ]ayan wa]annan nau’o’in sai ya fara talbiya da zarar ya yi harama, sai ya ce:

لَبَّيْكَ اللَّهُمَّ لَبَّيْكَ لَبَّيْكَ لا شَرِيكَ لَكَ لَبَّيْكَ إِنَّ الْحَمْدَ وَالنِّعْمَةَ لَكَ وَالْمُلْكَ لا شَرِيكَ لَكَ

(Labbaikalla Humma Labbaik Labbaika La Sharika Laka Labbaik Innal Hamda Wanni’imata Laka Walmul’k La Sharika Lak).

“Na amsa maka ya Allah, na amsa maka. Ba ka da abokin tarayya na amsa maka. Tabbas godiya da ni’ima da mulki duk sun tabbata gare ka. Ba ka da abokin tarayya”.

Ana son maniyyaci ya yawaita talbiya, namiji kuma ya rika daukaka muryarsa da ita.

 Abubuwan Da Aka Haramtawa Maniyyaci

Akwai abubuwa guda tara da aka haramtawa maniyyaci ya  aikatasu idan ya yi harama, ga su nan kamar haka:

1- Gusar da kowane irin gashi da ke jikinsa ta hanyar aski ko waninsa; saboda fa]in Allah Ma]aukaki:

] وَلا تَحْلِقُوا رُؤُوسَكُمْ حَتَّى يَبْلُغَ الْهَدْيُ مَحِلَّهُ[ [البقرة: 196]

“Kuma kada ku aske kawunanku har sai hadaya ta kai wurinta” (Ba}ara: 196).

2- Yanke farce; domin yanke farce hanya ce ta jin da]i da walwala, saboda haka zai ]auki hukuncin gusar da gashi, sai in da wani uzuri, to ya halatta ya yanke, kamar yadda ya halatta ya yi aski saboda wani uzuri.

3- Rufe kai; saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana mai harama ya nada rawani, haka kuma saboda fa]insa a kan mai haraman nan da dabbarsa ta jefar da shi wuyansa ta karye kuma ya rasu:

»ولا تخمروا رأسه فإنه يبعث يوم القيامة ملبيا« رواه البخاري ومسلم من حديث ابن عباس –رضي الله عنهما-

“Ka da ku rufe kansa, domin za a tayar da shi a ranar }iyama yana talbiya” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi daga hadisin Ibnu Abbas Allah ya yarda su. Ibnu Umar ya kasance yana cewa:

»إحرام الرجل في رأسه وإحرام المرأة في وجهها« رواه البيهقي بإسناد جيد

“Haramar na miji a kansa take, haramar mace kuma a fuskarta take”. (wato na miji ba ya rufe kansa mace kuma ba ta rufe fuskarta). Baiha}i ne ya ruwaito shi da isnadi mai kyau.

4- Sa ]inkakkun tufafi da khuffi (sawu ciki) ga namiji; dalilin haka hadisin Abdullahi Ibnu Umar Allah ya yarda da su ya ce: an tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi mene ne mai harama ya halatta ya sa? Sai ya ce:

»لا يلبس المحرم القميص ولا العمامة ولا البرانس ولا السروايل ولا ثوبا مسه ورس ولا زعفران، ولا الخفين إلا أن لا يجد نعلين فليقطعهما حتى يكونا أسفل من الكعبين« رواه البخاري ومسلم

“Mai harama ba ya halatta ya sa riga ko rawani, ko burnus ([20]), ko wando, ko rigan da War’s ([21]) ko zafaran suka taba shi, ko khuffi (sawu ciki) sai idan bai samu fa]e (salifa) ba, sai ya yanke khuffinsa kasa da idon sawu” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

5- Shafa turare; domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin hadisin Safwan ]an Ya’ala ]an Umayya:

»لأن النبي صلى الله عليه وسلم أمر رجلا في حديث صفوان بن يعلى بن أمية بغسل الطيب« رواه البخاري ومسلم

 “Ya umarci wani mutum ya wanke turaren da ke jikinsa” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Kuma ya ce a kan mai harama nan da dabbarsa ta jefar da shi wuyansa ya karye ya rasu:

»لاَ تُحَنِّطُوهُ« رواه البخاري ومسلم، ولمسلم:»ولا تمسوه بطيب«

“kada ku shafa masa turare” Bukhari da Musim ne suka ruwaito shi daga hadisin Ibnu abbas.

Ya haramta ga mai harama bayan ya yi harama ya shafawa jikinsa ko kowace ga~a ta jikinsa turare; dalilin haka shi ne hadisin Ibnu Umar wanda ya gabata.

6- Farautar namun daji; saboda fa]in Allah Ma]aukaki:

] يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لا تَقْتُلُوا الصَّيْدَ وَأَنْتُمْ حُرُمٌ[ [المائدة:95]

“Ya ku wa]anda suka yi imani kada ku kashe abin farauta alhali kuna cikin harama” (Ma’ida: 95).

Farautar naman daji ba ta halatta ko da bai kashe shi ko ya ji masa rauni ba; saboda fa]in Allah:

]وَحُرِّمَ عَلَيْكُمْ صَيْدُ الْبَرِّ مَا دُمْتُمْ حُرُما[ [المائدة: 96]

“Kuma an haramta muku farautar naman daji matu}ar kuna cikin harama” (Ma’ida: 96).

7- [aura aure: mai harama baya aure, kuma baya aurar da waninsa a matsayin waliyyi ko wakili; dalilin haka hadisin Usman Allah ya yarda shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»لاَ يَنْكِحُ الْمُحْرِمُ وَلاَ يُنْكِحُ وَلاَ يَخْطُبُ« رواه مسلم

“Mai harama ba ya aure, baya aurarwa, baya kuma neman aure” Muslim ne ya ruwaito shi.

8- Jima’i; saboda fa]in Allah Ma]aukaki:

] فَمَنْ فَرَضَ فِيهِنَّ الْحَجَّ فَلا رَفَثَ[ [البقرة: 197]

“Wanda ya yi niyyar Hajji a cikinsu (watannin Hajji), to babu saduwa da mace” (Ba}ara: 197).

Ibnu Abbas Allah ya yarda su ya ce: (rafathu) shi ne jima’i; domin fa]in Allah:

]أُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ الصِّيَامِ الرَّفَثُ إِلَى نِسَائِكُمْ[ [البقرة:187]

“An halatta muku tarawa da matanku a daren azumi” (Ba}ara: 187).

Ma’anar rafasu cikin wannan ayar shi ne jima’i.

9- Saduwa da mace ban da jima’i ta hanyar sumbata, ko shafa, ko kallo na sha’awa; domin kallo na sha’awa yana kaiwa ga jima’i saboda haka ya zama haram.

Mace hukuncinta daidai yake da na miji cikin abubuwan da aka haramtawa mai harama, sai dai ita mace ta bambanta da na miji a wasu abubuwa, ita mace haraminta a fuskarta yake ba ya halatta ta rufe fuskarta da burku’i ko ni}abi ([22]) ko waninsu, ya kuma haramta a gareta ta sanya safar hannu; dalilin haka shi ne hadisin Ibnu Umar Allah ya yarda da su daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a cikinsa:

»وَلاَ تَنْتَقِبُ الْمَرْأَةُ الْمُحْرِمَةُ وَلاَ تَلْبَسُ الْقُفَّازَيْنِ« رواه البخاري

“Mace mai harama bai halatta ba ta sa nikabi a fuskarta, haka nan kuma bai halatta ba ta sanya safar hannu” Bukhari ne ya ruwaito shi.

Ibnu Umar kuma ya ce:

»إِحْرَامُ الْمَرْأَةِ فِي وَجْهِهَا« رواه البيهقي بإسناد جيد

“Haramar mace a fuskarta take”. Baiha}i ne ya ruwaito shi da isnadi mai kyau.

Hakanan kuma A’isha Allah ya yarda da ita ta ce:

»كَانَ الرُّكْبَانُ يَمُرُّونَ بِنَا وَنَحْنُ مَعَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى الله ُعَلَيْهِ وَسَلَّمْ مُحْرِمَاتٌ فَإِذَا حَاذُواْ  بِنَا سَدَلَتْ إِحْدَانَا جِلْبَابَهَا مِنْ رَأْسِهَا فَإِذَا جَاوَزْنَا كَشَفْنَاهُ« رواه أبو داود وابن ماجه وأحمد بإسناد حسن.

“Mutane ayari-ayari suna riskanmu suna wuce mu kuma muna cikin harama tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, idan suka zo daidai da inda muke, sai ]ayanmu ta kusantar da mayafinta daga kanta ta rufe fuskarta, idan suka wuce sai mu yaye shi” Abu Daud ne da Ibnu Maja da Ahmad suka ruwaito shi da isnadi mai kyau. 

Abin da bai halatta ga na miji ba, baya halatta ga mace kamar: gusar da gashi, yanke farce, farauta, da makamancinsu; domin ita ma ta shiga cikin umarnin da akayi, sai dai ita mace ba a hanata ba sanya ]inkakkun tufafi da khuffi (sawu ciki) da rufe kai.

 Rukuni Na biyu: Tsayuwar Arfa

Dalilin haka shi ne fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»الحج عرفة« رواه أحمد وأصحاب السنن

“Tsayuwar arfa ita ce (}ashin bayan) aikin hajji” Ahmad ne da Ma’abotan sunan suka ruwaito shi.

Rukuni Na uku: [awafin Ifa]a

Dalilin haka shi ne fa]in Allah Ma]aukaki:

] وَلْيَطَّوَّفُوا بِالْبَيْتِ الْعَتِيقِ[ [الحج: 29]

“Kuma su yi ]awafi a ]aki da]a]]e (na Ka’aba) (Hajj: 29).

Rukuni Na Hu]u: Sa’ayi

Dalilin haka fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»اسْعَوْا فَإِنَّ الله َكَتَبَ عَلَيْكُمُ السَّعْيَ« رواه الإمام أحمد والبيهقي

“Ku yi sa’ayi; domin Allah ya wajabta muku sa’ayi” Imam Ahmad ne da Baiha}i suka ruwaito shi.

 6 – Wajiban Aikin Hajji

          Wajiban aikin hajji bakwai ne, ga su nan kamar haka:

1-    Yin harama daga mikati.

2-    Tsayuwar arfa har zuwa fa]uwar rana ga wanda ya samu tsayuwar rana.

3-    Kwanan Muzdalifa.

4-    Kwanan kwanakin Mina (daren sha-]aya da sha-biyu da sha-uku.

5-    Jifa.

6-    Aski da saisaye.

7-    [awafin bankwana.

 7 – Siffar Aikin Hajji

1- Sunna ce ga wanda yake so ya yi harama ya yi wanka kamar yadda yake wankan janaba, ya shafawa jikinsa turare kamar kansa da gemunsa, ya sa gyauto da mayafi farare. Amma ita mace za ta iya sa irin tufar da take so da shara]in ka da ta zama tufa ce da za ta nuna adonta da ita.

2- Sannan idan ya zo mi}ati sai ya yi harama bayan sallar farilla idan ya dace da lokacin sallar farilla, idan kuma ba lokacin salla ba ne sai ya sallaci raka’a biyu da niyyar sunnar alwala ba da niyyar sunnar harama ba; domin bai tabbata ba daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa za a yi wata salla ta musamman domin yin harama.

3- Bayan ya idar da salla sai ya yi niyyar shiga cikin aikin hajji ko umra. Idan Tamattu’i yake so sai y ce:

لَبَّيْكَ اللَّهُمَّ عُمْرَة

(Labbaikalla Humma Umra)

          “Ya Allah na amsa maka da umra” idan kuma da Ifradi yake so ya yi niyya, sai ya ce:

لَبَّيْكَ اللَّهُمَّ حَجًّا

(Labbaikalla Humma Hajjan)

“Ya Allah na amsa maka da hajji”, idan kuma da }irani yake so ya yi niyya sai ya ce:

لَبَّيْكَ اللَّهُمَّ حَجًّا فِي عُمْرَةٍ

(Labbaikalla Humma hajjan fi umra)

“Ya Allah na amsa maka da hajji cikin umra”.

 Kuma ana so na miji ya fa]i wa]annan lafuza na harama a bayyane, amma ita mace ana so ta fa]esu a ~oye, kuma sunna ce mai harama ya yawaita talbiya.

4- Idan ya isa Makka zai fara ne da ]awafi, daga Hajarul Aswad kuma zai fara ]awafinsa, ya sanya Ka’aba a hagunsa, sai ya fuskanci Hajarul Aswad ya sumbace shi ko ya shafa shi da hannunsa na dama idan hakan ya sau}a}a ba tare da haddasa cunkoso ba, idan kuma bai samu damar haka ba, sai ya yi nuni zuwa gare shi da hannunsa ya yi kabbara, ya kuma ce:

اللهم إيمانا بك وتصديقا بكتابك ووفاء بعهدك واتباعا بسنة نبيك صلى الله عليه وسلم

(Allahumma Imanan Bika Wa tasdi}an Bikitabika Wa wafa’an Bi’ahdika Wattiba’an Bisunnati Nabiyyika Sallallahu Alaihi Wa sallam)

“Ya Ubangiji (na fara wannan aikin ne) don imani da Kai, da gaskata littafinka, da cika al}awarinka, da koyi da sunnar Annabinka tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi”

Sai ya kewaya sau bakwai, idan ya zo wajen Rukunul Yamani zai shafa shi da hannunsa, amma ba zai sumbace shi ba ko hannunsa.

Yana daga cikin sunnonin ]awafi yin sassarfa ga na miji a kewaye ukun farko na ]awaful }udum (]awafin isowa), dalilin haka shi ne hadisin Ibnu Umar wanda Bukhari da Musulim suka ruwaito shi:

»كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا طاف الطواف الأول خب ثلاثا ومشى أربعا«

“Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya zo yin ]awafi na farko yana sassarfa a kewaye ukun farko, sannan ya yi tafiya a  hankali cikin sauran”

Daga sunnonin ]awafi kuma akwai id]iba’i wato ya bu]e kafa]arsa ta dama ya sanya tsakiyar mayafinsa a karkashin hamatarsa ya rufe kafa]arsa ta hagu; daililin haka shi ne hadisin Ibnu Abbas Allah ya yarda da su ya ce:

»اضطبع رسول الله صلى الله عليه وسلم هو وأصحابه ورملوا ثلاثة أشواط«

“Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabbansa sun bu]e kafa]unsu (na dama) kuma sun yi sassarfa a kewaye uku”.

Kuma zai yi addu’a cikin ]awafinsa irin addu’ar da ya ke so, cikin }as}antar da kai, tare da kuma zuciyarsa tana halarto ma’anar abin da yake fa]i, kuma tsakanin Rukunul Yamani da Hajarul Aswad zai ce:

]رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي الْآخِرَةِ حَسَنَةً وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ[ [البقرة:201]

“Ya Ubangijinmu ka ba mu kyakkyawa a duniya, da kyakkyawa a lahira, kuma ka kiyashe mu da azabar wuta” (Ba}ara: 201).

{ayyade kowane kewaye da wasu addu’o’i na musamman bidi’a ce; ba shi da wani asali daga sunnar annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

[awafi nau’i uku ne: ]awaful ifa]a, ]awafin isowa, da kuma ]awafin bankwana. Na farkon rukuni ne, na biyun sunna ce, na ukun kuma wajibi ne bisa magana mafi rinjaye.

5- Idan ya gama ]awafi sai ya sallaci raka’a biyu bayan Ma}amu Ibrahim. Zai iya ya tsayawa ko da nesa da shi ne, zai karanta fatiha da (}ul ya ayyuhal kafirun)  a raka’ar farko a ta biyu kuma fatiha da (}ul huwallahu), sunna ce kuma ya sassautasu kamar yadda sunna ta zo da shi.

6- Sannan kuma zai yi sa’ayi tsakanin Dutsen Safa da Dutsen Marwa zagaye bakwai, zai fara ne da Safa ya }arasa a Marwa, idan ya fuskanci Safa bayan ya  kusanta da shi  sunna ce ya karanta:

]إِنَّ الصَّفَا وَالْمَرْوَةَ مِنْ شَعَائِرِ اللَّهِ فَمَنْ حَجَّ الْبَيْتَ أَوِ اعْتَمَرَ فَلا جُنَاحَ عَلَيْهِ أَنْ يَطَّوَّفَ بِهِمَا وَمَنْ تَطَوَّعَ خَيْراً فَإِنَّ اللَّهَ شَاكِرٌ عَلِيمٌ[ [البقرة: 158]

“Ha}i}a dutsen Safa da Marwa suna daga cikin alamomin da Allah ya sanya na addininsa, wanda ya yi niyyar Hajji ko Umra, to babu laifi a kansa ya yi sa’ayi a tsakaninsu. Kuma wanda ya }ara yin wani aikin alheri, to Ha}i}a Allah mai godiya ne, Masani” (Ba}ara: 158).

Ya kuma ce:

أبدأ بما بدأ الله به

(Abda’u Bima Bada Allahu Bihi)

“Zan farawa da abin da Allah ya fara da shi”.

Sannan zai hau kan Safa ya fuskanci al}ibla ya ]aga hannayensa ya ce:

الله أكبر الله أكبر الله أكبر لا إله إلا الله وحده لا شريك له له الملك وله الحمد يحي ويميت وهو على كل شيء قدير لا إله إلا الله وحده أنجز وعده ونصر عبده وهزم الأحزاب وحده

(Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akabar, La Ilaha Illallahu Wahdahu La Sharika Lahu, Lahul Mulku Walahul Hamdu, Wahuwa Ala Kulli Shai’in {adir, La Ilaha Illallahu Wahdah, Anjaza Wa’adahu, Wanasara Abdahu, Wahazamal Ahazaba Wahdahu).

“Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma. Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah shi ka]ai, ba shi da abokin tarayya. Mulki ya tabbata gare shi, kuma yabo ya tabbata gare shi, yana rayawa kuma yana kashewa, kuma shi mai iko ne a kan komai. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi ka]ai, ya gaskata al}awarinsa, ya taimaki bawansa, ya ruguza rundunonin kafirai, shi ka]ai”.

Sannan ya yi addu’a ya roki abin da yake so na alherin duniya da lahira. Zai kuma maimata wannan zikirin da aka ambata sau uku, yana yin addu’a bayan kowane karo.

Sannan ya sauko daga kan safa ya nufi Marwa, sunna ce ga na miji ya yi gudu-gudu tsakanin alamomin nan koraye guda biyu, in ya samu damar haka ba tare da ya cutar da wani ba, idan ya kai ga dutsen Marwa sai ya hau kansa ya fuskanci al}ibla ya ]aga hannayensa ya yi zikiri da addu’a kamar yadda ya aikata a kan Safa. (Tahowarsa daga Safa zuwa Marwa a matsayin ]aya yake, haka kuma komawarsa zuwa Safa a matsayin }idaya ]aya yake).

 Kuma babu komai idan ya yi wannan addu’ar (mai zuwa); domin ta tabbata daga Ibnu Umar da Ibnu Mas’ud Allah ya yarda da su:

رب اغفر وارحم إنك أنت الأعز والأكرم

(Rabbig fir Warham Innaka Antal A’azzul Akram)

“Ya Ubangiji ka gafarta mini, kuma ka ji }ai na; domin kai ne mafi buwaya mafi karamci”.

Ana so ya kasance cikin tsarki, idan kuma ya yi sa’ayin ba tare da tsarki ba ya wadatar, haka nan ma mace mai haila idan ta yi sa’ayi ya wadatar; domin yin tsarki ba shara]i ba ne cikin sa’ayi.

7-Idan ya gama sa’ayinsa sai ya yi saisaye idan tammatu’i yake yi, kuma na miji zai yi saisayen ne yadda zai game dukkannin gashin kansa, mace kuma za ta bi tsawon gashin kanta ta yanke karshensa gwargwadon tsawon ga~ar ]an yatsa. Da haka nan ya gama umrarsa sai ya cire haraminsa ya zauna cikin kayansa na gida. Idan kuma {irani yake yi ko Ifradi sai ya zauna cikin haraminsa har zuwa ranar salla goma ga watan Zul hijja, a lokacin ne zai fita daga haraminsa bayan ya yi jifa.

8- A ranar (Tarwiya) takwas ga watan Zul hijja mai Tamattu’i zai yi harama da aikin hajji a lokacin hantsi a masaukinsa, haka mutanen Makka su ma za su yi harama daga gidajensu, ya yi tsafta ya yi wanka ya sa turare ya sa ihraminsa, ya ce:

لبيك اللهم حجا

(Labbaikalla Humma Hajjan)

Ba sunna ba ne ya tafi masallacin harami don ya yi harama a cikinsa; domin hakan bai zo ba daga Annabi tsira da amicin Allah su tabbata a gare shi, bai kuma umarci sahabbansa da shi ba gwargwadon iya sanimu. Ya zo cikin Bukhari da Muslim daga hadisin Jabir ]an Abdullahi Allah ya yarda da su cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da su:

»أقيموا حلالا حتى إذا كان يوم التروية فأهلوا بالحج…«

“Ku yi zamanku ba cikin ihrami ba har zuwa ranar Tarwiya, sai ku yi harama da aikin hajji”. Muslim kuma ya ruwaito daga Jabir ya ce:

»أمرنا رسول الله صلى الله عليه وسلم لما أهللنا أن نحرم إذا توجهنا إلى منى فأهللنا من الأبطح«

“Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarcemu  yayin da muka yi shirin harama da mu yi harama idan muka nufi Mina, sai muka yi harama daga Ab]ah([23])(domin shi ne masaukinsu).

9- Ana so maniyyaci ya fita Mina ya yi sallar Azahar, La’asar, Magariba, da Isha’i }asaru, kowace a lokacinta, ana so kuma ya kwana a Mina daren Arfa; saboda hadisin da Muslim ya ruwaito daga Jabir.

10-  Idan rana ta fito a ranar Arfa (tara ga watan zul hijja) ya ta fi Arfa, ana so ya sauka a Namira ([24]) har zuwa zawali in hakan ya sau}a}a; domin haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aikata, idan kuma hakan bai samu ba sai ya zarce zuwa Arfa kai tsaye, idan rana ta kauce sai ya ha]a sallar Azahar da La’asar ya yi su a lokaci ]aya }asaru kowace raka’a biyu. Sannan ya fara tsayuwar Arfa. Abin da ya fi falala shi ne ya sanya Dutsen Al Rahma tsakaninsa da al}ibla idan ya samu dama, idan kuma bai samu dama ba ya tsaya a inda yake ya fuskanci al}ibla. Ana so ya shagala da zikiri, ya yi iya kokarinsa wajen kaskantar da kai da yin addu’a da karatun Al}ur’ani, yana mai ]aga hannayensa; dalilin haka hadisin Usama ya ce:

»كنت رديف النبي صلى الله عليه وسلم بعرفات فرفع يديه يدعو فمالت به ناقته فسقط خطامها فتناول خطامها بإحدى يديه وهو رافع يده الأخرى« رواه النسائي

“Na kasance Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya goya ni a kan taguwarsa sai ya ]aga hannayensa yana addu’a, sai taguwarsa ta karkata sai linzaminta ya fa]i, sai ya mika hannunsa ya dauka, alhali yana ]age da ]ayan hannun nasa” Nasa’i ne ya ruwaito shi. Ya zo kuma a cikin Muslim:

»ولم يزل واقفا يدعو حتى غابت الشمس وذهبت الصفرة«

“Bai gushe ba yana tsaye yana addu’a har rana ta fa]i, ]an jan launin kuma ya tafi”.

Adduar ranar Arfa ita ce mafificiyar addu’a; Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi y ce:

»خير الدعاء دعاء يوم عرفة، وخير ما قلت أنا والنبيون من قبلي: لا إله إلا الله وحده لا شريك له له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير« رواه مسلم

 “Mafificiyar addu’a ita ce addu’ar ranar Arfa, kuma mafificin abin da na fa]a da Annabawa gabanina:

لا إله إلا الله وحده لا شريك له له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير« رواه مسلم

          “Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi ka]ai. Mulki ya tabbata gare shi, kuma yabo ya tabbata gare shi. Kuma shi mai iko ne a kan komai” Muslim ne ya ruwaito shi.

Ya kuma nuna a fili bukatuwarsa zuwa ga Allah, da karayarsa, ka da ya bari wannan dama mai girma da dimbin lada ta kubce masa; Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»ما من يوم أكثر من أن يعتق الله فيه عبدا من النار من يوم عرفة، وإنه ليدنو ثم يباهي بهم الملائكة، فيقول: ما أراد هؤلاء« رواه مسلم.

“Ba bu ranar da Allah ya fi ‘yanta bayi daga wuta kamar ranar Arfa, Allah yana kusantowa sannan ya yiwa  Mala’iku alfahari da bayinsa ya ce: menene wa]annan suke nema” Muslim ne ya ruwaito shi.

Tsayuwar Arfa rukuni ne na hajji, kuma wajibi a tsaya har zuwa fa]uwar rana, ya wajaba a kan alhaji ya tabbatar da cewa ya tsaya a cikin iyakar Arfa; domin da yawa daga cikin mahajjata suna sakaci suna tsayawa waje da iyakar Arfa, to wa]annan ba su da hajji.

11-  Idan rana ta fa]i sai ya tafi Muzdalifa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali; saboda fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

»أيها  الناس السكينة السكينة« رواه مسلم

“Ya ku matane ku nutsu, ku nutsu”. Muslim ne ya ruwaito shi.

Idan ya isa Muzdalifa sai ya yi sallar Magariba da Isha’i, zai jinkirta Magariba zuwa lokacin Isha’i ya ha]asu ya yi su a lokaci ]aya, Magariba raka’a uku, Isha’i raka’a biyu. Kuma sunna ce ga mahajjaci ya bar  sallar Magariba sai ya zo Muzdalifa don koyi da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai idan ya ji tsoron fitan lokacin Isha’i sai ya yi su a ko ina.

Zai kuma kwana. Ba sunna ba ce ya raya daren da salla ko waninta; domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai yi haka ba, dalili kuwa hadisin da Muslim ya ruwaito daga Jabir ]an Abdullahi Allah ya yarda da shi cewa:

»أن النبي صلى الله عليه وسلم أتى المزدلفة فصلى بها المغرب والعشاء بأذان وإقامتين ولم يسبح بينهما شيئا ثم اضطجع حتى طلع الفجر«

 “Annabi tsira da aminin Allah su tabbata a gare shi ya isa Muzdalifa sai ya yi sallar Magariba da Isha’i da kiran salla ]aya, da i}ama biyu, bai kuma yi nafila ba tsakaninsu, sannan ya kwanta har alfijir ya keto”.

Ya halatta ga masu uzuri da raunana su dunguma daga Muzdalifa zuwa Mina idan dare ya raba, wata kuma ya bace daga sararin sama, domin su yi jifa, amma wanda ba shi da rauni, kuma baya tare da mai rauni zai kwanta har sai alfijir ya keto. Abin da da yawa daga cikin mutane suke yi na gaggauta zuwa jifa a farkon dare domin neman sau}i ya sa~awa shiriyar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Idan alhaji ya yi sallar Asuba a Muzdalifa sai ya tsaya a Mash’arul Haram (dutsen da ke filin Muzdalifa) ya fuskanci al}ibla ya ]aga hannayensa ya yi addu’a ya kuma yawaita yin addu’ar, har gari ya faifaye. Kuma duk inda ya tsaya daga filin Muzdalifa ya wadatar; saboda fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

        »وقفت هاهنا وجمع كلها موقف«رواه مسلم

“Anan na tsaya kuma dukkannin filin Muzdalifa wurin tsayuwa ne” Muslim ne ya ruwaito shi.

12-  Sannan mahajjata za su tafi Mina kafin fitowar rana su jefi Jamratul A}aba (ita ce wadda ta fi kusa da Makka) da tsakwankwani bakwai, kowace tsakuwa girmanta da Ka]an ta ]ara girman }wayar Himmas ([25]). Malamai kuma sun ha]u a kan cewa ya halatta a jefi Jamrar daga kowane gefe, amma mafi falala shi ne ya sanya Ka’aba ga hagunsa Mina ga damansa; dalilin haka shi ne hadisin Ibnu Mas’ud Allah ya yarda da shi cewa (shi Ibnu Mas’ud) ya kai ga babban Jamra, ya kuma sanya Ka’aba ga hagunsa, Mina kuma ga damansa, ya yi jifa da tsakwankwani bakwai, sai ya ce:

»هكذا رمى الذي أنزل عليه سورة البقرة«

“Wanda aka saukar masa suratul Ba}ara haka ya yi jifa” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Ba ya halatta ayi jifa da manyan tsakwankwani, ko khuffi, ko takalma. Kuma mahajjaci zai yanke talbiya yayin jifan Jamratul A}aba.

Kuma sunna ce mahajjaci ya gabatar da jifa, sannan ya yanka hadayarsa idan Tamattu’i ya yi ko {irani, sannan ya yi aski ko saisaye, aski ya fi falala ga namiji; saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ro}awa masu aski rahama da gafara sau uku, ga masu saisaye kuma sau ]aya, kamar yadda Bukhari da Muslim suka ruwaito. Sannan zai tafi Ka’aba domin ya yi ]awafin Ifa]a.

Dalilin haka shi ne hadisin Jabir ]an Abdullahi Allah ya yarda da shi wanda Muslim ya ruwaito shi:

»أن النبي صلى الله عليه سلم أتى الجمرة التي عند الشجرة فرماها بسبع حصيات يكبر مع كل حصاة منها، مثل حصى الحذف، رمى من بطن الوادي ثم انصرف إلى المنحر فنحر ثم ركب رسول الله صلى الله عليه وسلم فأفاض إلى البيت فصلى بمكة الظهر«

“Lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya zo ga Jamrar da take wurin bishiya sai ya jefeta da tsakwankwani bakwai, yana cikin kwarin da ke wurin,  yana kabbara tare da kowace tsakuwa, kuma kowace girmanta kamar tsakuwar ballere, sannan ya tafi wajen yanka ya yi yanka, sannan ya hau dabbarsa ya dunguma zuwa Ka’aba (ya yi ]awafi da sa’ayi) ya yi sallar Azahar a Makka”.

Wanda ya kaddamar da ]ayan wa]annan ayyuka guda hu]u (jifa, yanka, aski ko saisayi, da ]awafi) a kan sauran ya wadatar babu komai a kansa; dalilin haka hadisin Abdullahi ]an Amru Allah ya yarda da shi a hajjin bankwana:

»وقف رسول الله صلى الله صلى الله عليه وسلم والناس يسألونه، فما سئل رسول الله صلى الله عليه وسلم يومئذ عن شيء قدم أو أخر إلا قال: افعل ولا حرج«. رواه الشيخان.

“Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsaya, sai mutane suka zo suna tambayarsa. Ba a tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba a wannan rana (goma ga wata) a kan wani aiki da aka gabatar ko aka jinkirta face  ya ce: ka aikata babu komai” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Idan kuma ya kasance mai Tamattu’i ne, sai ya yi sa’ayi bayan ya gama ]awafi; domin sa’ayi na farko da ya yi na umra ne, saboda haka ya wajaba a gare shi ya yi sa’ayin hajji, in kuma ya kasance mai Ifradi ne ko mai {irani idan ya riga ya yi sa’ayi bayan ]awafin isowa, to ba zai maimata sa’ayi ba; saboda fa]in Jabir Allah ya yarda da shi:

»لم يطف النبي صلى الله عليه وسلم ولا أصحابه بين الصفا والمروة إلا طوافا واحدا طوافه الأول« رواه مسلم

“Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabbansa ba su yi sa’ayi ba tsakanin Safa da Marwa sai  sau ]aya, sa’ayinsu na farko” (domin {irani suka yi). Muslim ne ya ruwaito shi.

13-  Ayyamul Tashri} (ranakun hasken wata) sha-]aya, sha-biyu, da sha-uku ga watan Zul hijja, ranaku ne na jifa ga wanda bai gaggauta ya bar Mina ba, amma wanda yake so ya yi gaggawa ya bar Mina zai yi jifa ranakun sha-]aya da sha-biyu, saboda fa]in Allah Ma]aukaki:

]وَاذْكُرُوا اللَّهَ فِي أَيَّامٍ مَعْدُودَاتٍ فَمَنْ تَعَجَّلَ فِي يَوْمَيْنِ فَلا إِثْمَ عَلَيْهِ وَمَنْ تَأَخَّرَ فَلا إِثْمَ عَلَيْهِ لِمَنِ اتَّقَى[ [البقرة: 203]

“Kuma ku ambaci Allah a cikin }idayayyun ranaku, kuma wanda ya yi gaggawar (barin Mina) cikin kwana biyu, to babu laifi a kansa, wanda kuma ya jinkirta (shi ma) babu laifi a kansa, (an halatta wannan za~in ne) ga wanda ya ji tsoron Allah, ku ji tsoron Allah, kuma ku sani zuwa gare shi ne za a tattara ku” (Ba}ara: 203).

Kuma mahajjaci zai fara ne da jifan }aramar Jamra wadda ta fi kusa da masallacin Khaif, sannan ta tsakiya, sannan Jamratul A}aba, kowace da tsakwankwani bakwai, zai yi kabbara tare da kowace tsakuwa. Sunna ce kuma idan ya yi jifan }aramar Jamra ya tsaya ya fuskanci al}ibla ya sanyata ga hagunsa ya yi addu’a mai tsawo, haka nan kuma zai yi idan ya jefi ta tsakiya, sai dai ita zai sanyata ne ga damansa, amma Jamratul A}aba ba zai yi addu’a bayan ya jefeta

Kuma lokacin jifa yana farawa ne bayan zawali; dalilin haka hadisin Ibnu Abbas Allah ya yarda da su ya ce:

»كنا نتحين فإذا زالت الشمس رمينا« رواه البخاري

“Mun kasance muna jiran lokacin jifa ya yi, idan rana ta kauce daga tsakiyar sama sai mu je mu yi jifa” Bukhari ne ya ruwaito shi.

Malamai kuma sun ha]u a kan cewa karshen lokacin jifa na ranakun Tashri} shi ne fa]uwar rana a ranar sha-uku ga watan Zul hijja, wanda bai samu ya yi jifa ba har rana ta fa]i, to ba shi da damar jifa, yanka ta kama shi.

14-  Mahajjaci zai kwana ne a Mina daren sha-]aya, da sha-biyu, idan rana ta fa]i a ranar sha-biyu ga wata alhali bai samu ya fita daga Mina ba, ya wajaba a gare shi ya tsaya ya kwana ya yi jifa a ranar sha-uku.

Idan mahajjaci ya yi shirin barin Makka zuwa }asarsa, ba ya halatta ya fita daga Makka har sai ya yi ]awafin bankwana, domin ]awafin bankwana wajibi ne a wurin mafi yawan malamai, sai dai yana sauka daga kan mace mai haila; dalilin haka  shi ne hadisin Ibnu Abbas Allah ya yarda da su Manzon tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

»لا ينفرن أحد حتى يكون آخر عهده بالبيت« وفي رواية: »إلا أنه خفف عن المرأة الحائض« رواه مالك وأصله في صحيح مسلم

“Kada ]ayanku ya fita daga Makka har sai ya yi ]awafin bankwana”, a wata riwayar: “sai dai ya yi rangwame ga mace mai haila” Imam Malik ne ya ruwaito shi, asalinsa kuma yana cikin Sahih Muslim.

Mafi yawan malamai sun tafi a kan cewa ]awafin ifada yana wadatarwa ga ]awafin bankwana, ga wanda ya jinkirta shi zuwa lokacin tafiyarsa, idan ya shigar da niyyar ]awafin bankwana a cikinsa.

15-  Ana so ga wanda zai koma }asarsa bayan aikin hajji ya fa]i abin da Ibnu Umar Allah ya yarda da su ya ruwaito cewa: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya kama hanyar dawowa daga wani ya}i ko aikin hajji ko umra, yana kabbara idan ya hau tudu, sannan ya ce:

» لا إله إلا الله وحده لا شريك له له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير، آيبون تائبون لربنا حامدون، صدق الله وعده ونصر عبده، وهزم الأحزاب وحده«

“Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi ka]ai. Mulki ya tabbata gare shi, kuma yabo ya tabbata gare shi. Kuma shi mai iko ne a kan komai. Mu masu komawa, masu tuba, masu bauta, masu godiya ne. Allah ya gaskata al}awarinsa, ya taimaki bawansa, ya ruguza rundunonin kafirai shi ka]ai”.

* * *([1])   Ummiyyi: shi ne wanda ba ya karatu da rubutu.(Al jami’ Li Ahkamil }ur’an 7/ 284) ]Mai fassara[.

([2])   Sune: goshi tare da hanci, tafin hannaye biyu, gwiwowi biyu, da }arshen kafafuwa. ]Mai fassara[.

([3])   Wannan shi ne abin da mafi yawan malamai suka tafi akai. ]Mai fassara[.

([4])   Gwargwado wanda sai idan dukiya ta kai shi zakka take wajaba a cikinta. ]Mai fassara[

([5])   Bawan da ya yi yarjejeniya da mai gidansa a kan zai ‘yanta shi idan ya ba shi wani gwargwado na dukiya a cikin wani lokaci da za su }ayyade. (Al Nihaya 4/148) ]Mai fassara[.

([6])   Bayaninsa zai zo a nan gaba shafi ( 59).

([7])     Bintu Makhad: ‘yar mai ciki, ita ce wadda ta shiga shekara ta biyu, an kirata da wannan sunan ne; domin mahaifiyarta  ta kai lokacin da za ta yi ciki, ko da ba ta da ciki. (Al Nihaya 4/306).

([8])   Bintu Labun: ‘yar mai nono, ita ce wadda ta cika shekara biyu, ta shiga ta uku, an kirata da wannan sunan ne; domin a wannan lokacin mahafiyarta ta haihu tana da nono (Al Nihaya 4/228).

([9])   Hi}}a: ita ce wadda ta shiga shekara ta hu]u, kuma ta isa na miji ya taketa (Al Nihaya 1/415).

([10])   Tabi’a da Tabi: ‘ya’yan saniya da suka cika shekara (]an dalo). (Al Nihaya 1/179).

([11])   Fuskar kafa hujja da wannan hadisi alhali yana magana ne akan bawa da doki, shi ne ganin cewa hikimar da ta sa ba a wajabta zakka game da su ba; domin ana mallakansu ne ba don kasuwanci ba, shi bawa ana mallakarsa ne don yin hidima, doki kuma don hawa, haka ma idan mutum ya mallaki dabbobi ba don kasuwanci ba, to babu zakka a cikinsu. Duba (Sharhul Nawawi Ala Muslim 7/58) ]Bayanin mai fassara[.

([12])   Fai’i: shi ne dukiyar kafirai wadda  musulmi suka mallaka ba tare da ya}i ba (Al Nihaya 3/482). ]Mai fassara[.

([13])   Alfijir nau’i biyu ne: alfijir na farko: shi ne lokacin da wani haske siriri yake fitowa ya mike ya yi sama, ba tare da ya kwanta ba, shi wannan ba a la’akari da shi wajen azumi ko salla.

Alfijir na biyu: shi ne lokacin da haske mai kwanciya yake bazuwa a sararin samaniya, wannan shi ne ake la’akari da shi wajen azumi da salla. duba (Al Mugni 2/30) ]Bayanin mai fassara[.

([14])   Abin da ake nufi a nan shi ne bayanin girman munin wannan aiki, amma ba ya nuna cewa idan ya bar maganan zur Allah zai bu}atu  ga azuminsa. (Taw]ihul Ahkam 3/155) ]Mai fassara[

([15])   Abin nufi a nan shi ne ruwan da yake sauka bayan iskar; domin alherinsa zai shafi kowa mara hali da mai hali, haka Manzon Allah ma kyautarsa tana shafar kowa da kowa fiye da ma ruwan sama. (Fathul Bari 4116/) ]Bayanin mai fassara[.

([16])   Laba: }asa wadda tana ]auke da }ananan ba}a}en duwatsu, Ana ce mata kuma: harra. (Al nihaya 1/365)

([17])      Istimna’i: shi ne fitar da maniyyi ta hanyar wasa da zakari da hannu ko waninsa.(Bayanin mai fassara).

([18])   Muharramin mace: shi ne wanda ya haramta a gare shi ya aureta har abada kamar ubanta, ]anta, ]an uwanta, baffanta, kawunta, ]an ]an uwanta ko ‘yar uwarta, haka kuma wa]annan da aka ambata daga bangaren shayarwa, da kuma mahaifin mijinta da ]an mijinta. (Ihkamul Ahkam 2/56) ]Bayanin mai fassara[.

([19])   Amma wanda ya samu kansa a Zul Hulaifa mikatin mutanen Madina ana so ya sallaci rak’a biyu, saboda albarkar wurin ba don harama ba; dalilin haka shi ne fa]in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: “Mala’ika Jibrilu ya zo mini sai ya ce: ka yi salla a wannan kwari mai albarka (Wadil Akik) kuma ka ce: umra a cikin hajji” Bukhari ne ya ruwaito shi. (Bayanin mai fassara).

([20])   Burnus: riga da hula a li}e da ita (‘yar Moroko). (Al Nihaya 1/122).

([21])  wani tsiro ne ruwan ]orawa ake rini da shi. (Al Nihaya 5\173) ]Mai fassara[.

([22])   Burku’i da ni}abi abubuwa ne da mace take rufe fuskarta da su, sai dai shi ni}abin tana barin kwarmin idonta a bu]e. (Al Nihaya 5/103) ]mai fassara[.

([23])   Suna ne na magudanar ruwa a kwararon Makka. (Al Nihaya 1/134). Yanzu ana kiransa Muhassab, (Mai fassara)

([24])  Namira: shi ne karshen iyakar harami daga bangaren Muzdalifa, kuma (Wadi Urana) ne ya raba shi da iyakar Arfa. ]Mai fassara[.

([25])   Himmas: wani nau’i ne na kwayoyi ya yi kama da gangala amma bai kai  girmansa ba. (mai fassara).