TAFARKIN SUNNAH ()

abdallah bin muhammed al gunaiman

 

TAFARKIN SUNNAH tattaunawa ta ruwan sanyi tsakanin ibnu taimiyyah da ‘yan shi’ar zamaninsa

|

 TAFARKIN SUNNAH

tattaunawa ta ruwan sanyi tsakanin

 ibnu taimiyyah da ‘yan shi’ar zamaninsa

Wanda Ya Taqaita Shi A Larabce

SHEIKH ABDALLAH AL-GUNAIMAN

FASSARA DA YAXAWA

CIBIYAR AHLUL-BAITI DA SAHABBAI TA NAJERIYA

97, Titin Ahmadu Bello, Sokoto, Najeriya

www.ahlulbaity.com

 Kwamitin Fassara

Dr. Muhammad Mansur Ibrahim

Na Cibiyar Yaxa Addinin Musulinci Ta Jami’ar Usmanu Xan Fodiyo, Sakkwato kuma Darektan Cibiyar Ahlulbaiti da Sahabbai

 Shugaba

Dr. Ibrahim Bello Na Kolejin Ilimi Ta Shehu Shagari Da Ke Sokoto.

Ya Rasu A Lokacin Da Yake Cikin Aikin. Allah Ya Jiqan Sa.

 Memba

Mal. Aminu Ibrahim Maru Na Hukumar Jaridu Ta Jihar Sokoto

Digiri a sashen Hausa

 Memba

Mal. Usmanu Sarkin Vurmin Jabo Na Kolejin Sarkin Musulmi Abubakar Ta Sokoto.

Digiri a ilimin addinin musulunci

 Memba

Aliyu Rufa’i Gusau

Na Ma’aikatar Lamurran Addini Ta JIhar Zamfara

Yana da babbar takardar shaidar qwarewa a fannin ilimin addini daga jami’ar Afirika ta duniya da ke Sudan, da diploma a kolejin fasaha da kimiyya ta Sokoto. Ya kusa kammala digirinsa a fannin Hausa.

 Sakatare

Kwamitin Bita

Sokoto Bureau Of Translation,

Federal Housing Estate, Runjin Sambo, Sokoto.

Tare Da:

Dr. Muhammad Mansur Ibrahim

Darektan Cibiyar Ahlulbaiti da Sahabbai

Da Aliyu Rufa’i Gusau

Na Ma’aikatar Lamurran Addini Ta Jihar Zamfara

Da ta fassara aikin tas sanya

A daka, a dafa, a saka kwanna

 Kowa ya ci yara har manya

 Aliyu Rufa’i Gusau

 GABATARWAR CIBIYAR AHLUL-BAITI DA SAHABBAI

 Godiya ta tabbata ga Allah wanda aikin alheri ba ya kammala sai da taimakonsa. Muna godiya a gare shi bisa taimakon da ya yi mana na kammala wannan aiki mai tarin albarka.

 Babbar manufar da aka kafa wannan cibiya a kanta ita ce, bayyana gaskiyar Allah game da kyakkyawar dangantakar da ta wanzu a tsakanin Ahlul-Baiti, iyalan gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma Sahabbai, wato almajiransa. Babu shakka sanin wannan kyakkyawar dangantaka na qara mana sanin qoqarin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wajen shiryar da al’ummarsa, da nasarorin da ya samu a cikin aikin da Allah ya xora ma sa na yin tarbiyyar jama’arsa. Kamar yadda Allah ya ce:

ﭽ لَقَدۡ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَىٰٰٰٰٰٰٰٰ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذۡ بَعَثَ فِيهِمۡ رَسُولٗا مِنۡ أَنفُسِهِمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِهِۦ وَيُزَكِّيهِمۡ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلُ لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ ١٦٤ ﭼ آل عمران: ١٦٤

Haqiqa Allah ya yi baiwa a kan muminai a lokacin da ya tayar da manzo a cikinsu, daga kawunansu, yana karanta ma su ayoyin Allah, yana tsarkake su, yana ilmantar da su littafin (Alqur’ani) da Hikima (Sunnah), kodayake sun kasance a cikin bayyanannen vata gabanin haka. Ali Imran: 164.

 Tsarkake su da Allah ya xora wa Manzo yi, shi ne tarbiyyarsu. Don haka duk wata suka ga tarbiyyar tasu to, suka ce ga Manzon Allah xin kansa. Kuma ma dai Alqur’ani ya ba mu tabbacin wanzuwar so da qauna da rahama a tsakaninsu. Kamar in da Allah yake cewa:

ﭽ مُّحَمَّدٞ رَّسُولُ ٱللَّهِۚ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ أَشِدَّآءُ عَلَىٰٰٰٰٰٰٰٰ ٱلۡكُفَّارِ رُحَمَآءُ ﭛﭼ الفتح: ٢٩

Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma waxanda ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu jinqayi a tsakanin junansu. Al-Fathi: 29

Da kuma in da yake cewa:

ﭽ هُوَ ٱلَّذِيٓ أَيَّدَكَ بِنَصۡرِهِۦ وَبِٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٦٢ وَأَلَّفَ بَيۡنَ ﭡ ﭼ الأنفال: ٦٢ – ٦٣

(Allah) shi ne wanda ya qarfafe ka da taimakonsa da kuma muminai. Kuma ya haxa zukatansu. Al-Anfal: 62-63.

Wannan cibiya ta samu littafin nan na Shehun musulunci Ibnu Taimiyyah daidai da wannan manufa, domin ya bayyana gaskiyar wannan al’amari ta hanyar hujjoji bayyanannu masu qwari.

Wannan Littafi

 Babu shakka Ibnu Taimiyyah ya yi bajimin qoqari a cikin wannan littafi, kamar yadda ya saba yi a sauran littafansa waxanda suke matsayin taurari a samaniyar ilimin addini. Muna kyautata zaton cewa, babu mai hankali da basira da zai karanta wannan littafi face ya amfana da shi ta fuskar gano bakin zaren duk abubuwan da ake taqaddama a kansu kan matsayin Sunnah da Shi’ah a addini. Malamin ya sanya haquri da juriya kamar yadda ya sa ilimi da basira a cikin mayar da martanin abubuwan da ‘yan Shi’ah suke faxa a kan Sahabbai. Ya yi shi ta hanyar tattaunawa yana mai mayar da martani a tsanake kan littafin da jagoran ‘yan Shi’ar zamaninsa Ibnul Muxahhir ya wallafa mai suna Minhajul Karamati Fi Isbatil Imamati. Malamin ya bi littafin daki-daki yana tattaunawa a kan dalilan da aka kawo.

 Da yawan mutane sukan yi zaton cewa, ‘yan Shi’ah na riqe da hujjoji ko aqalla shubhohi masu qarfi, waxanda ke da wahalar tunkuxewa in ba ga malamai ba. Amma wanda ya karanta wannan littafi take zai gano lamarin ba haka yake ba. Domin kuwa mawallafin ya tabbatar a aikace cewa, ba su da wata hujja ko guda qwaqqwara. Bil hasili ma, duk a cikin qungiyoyin da ke jingina kansu ga musulunci babu marasa hujja irinsu. Domin su ne waxanda duk hujjar da suka kafa, da an dube ta da kyau ana iya amfani da ita wajen hujjace su. Ya kuma ba da haske game da dabarun da suka cancanta mai tattaunawa da su ya bi don lurar da su gaskiya. Kamar in da ya ke cewa:

To, a wajen jayayya, idan musulmi ya tattauna da Kirista ba zai iya faxin wani abu game da Isa Alaihis Salamu ba face gaskiya. Amma in kana son ka fito da jahilcin Kirista da rashin hujjarsa, to, sai ka qaddara jayayyar a tsakanin sa da Bayahude, ka koma gefe ka saurare shi. Idan har Kirista ba zai iya kare Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba, to, duk zargin da ya yi masa zai tarar Bayahude yana yi wa Annabi Isah Alaihis Salamu irinsa. Kuma duk hujjar da zai kawo don ya kare Annabi Isah Alaihis Salamu wannan hujjar ta fi kare Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama daga shi nasa zargin. Saboda haka, in zargin da Bayahude yake yi wa Annabi Isah Alaihis Salamu qarya ne, to, zargin Kirista ga Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi zama qarya.

To, wannan shi ne abin da ke tsakanin Ahlus-Sunnah da ‘yan-sha-biyu ga lamarin Abubakar da Ali. Xan Shi’ar ba zai iya tabbatar da imanin Ali ba, da cewa shi xan aljanna ne, ballantana ya tabbatar da shugabancinsa sai fa in ya tabbatar da haka ga Abubakar da Umaru da Usmanu.

Don in ba haka ba duk lokacin da ya so ya tabbatar da wata daraja ga Ali, to, dalilai ba sa taimaka masa, kamar yadda in Kirista ya so ya tabbatar da annabcin Isa Alaihis Salamu ba zai iya ba sai in ya yarda da annabcin Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama, domin dalilai ba za su taimake shi ba.

Bisa ga haka, idan ka tattauna da wani daga cikin ‘yan-sha-biyu, to, qaddara masa tattaunawar tsakanin sa da Harijawa masu kafirta Ali da Nasibawa masu fasiqantar da shi. Harijawa sun tafi a kan cewa, Ali azzalumi ne, mai neman duniya, wanda ya nemi halifanci da qarfi, ya yaqi mutane a kansa. A garin haka kuwa ya kashe dubun dubatar musulmi, abin da ya hana cin nasarar mulkinsa. Ya kuma kasa samun abin da yake so na kevanta da mulki, sai magoya bayansa suka dare masa, suka yaqe shi har daga qarshe suka kashe shi.

To, ka ga wannan magana in qarya ce, to, ba shakka maganar xan Shi’ar a game da Abubakar da Umar ta fi ta zama qarya. In kuma har maganar xan Shi’ar a game da Abubakar da Umar daidai ne, kuma magana ce ta gaskiya, to, lalle ko maganar Harijawa a kan Ali ta fi cancantar zama gaskiya.[1]

Wannan littafi ya karva sunansa bisa gaskiya, domin mawallafin ya shimfixa qa’idodi masu tarin yawa a cikinsa, masu kuma amfani, waxanda ke bayyana tafarkin Ahlus-Sunnah a cikin sha’anin ilimi da aqida. Dubi waxannan haskakan maganganu nasa a matsayin misalai:

Ita dai magana duk wanda zai yi ta, wajibi ne ya yi ta akan ilimi da adalci, musamman in ta shafi mutuncin wani mutum musulmi kowane iri ne. Ba daidai ba ne a yi ta a kan jahilci da zalunci, kamar yadda ‘yan bidi’a ke yi a ko’ina. Dubi yadda ‘yan-sha-biyu ke bijirowa da mutane masu kusanci da juna ta fuskar girma da xaukaka, da zamansu waliyyan Allah, amma sai su raba su; wasu su ce ma’asumai ne da ko rafkanwa xayansu ba ya yi. Sauran kuma su ce masu fajirai ne ko fasiqai ko kafirai. Kai tsaye kana iya gane jahilcinsu da taqin saqar maganarsu. Kamar Bayahude ne ko Kirista, duk sadda xayansu ya buqaci tabbatar da annabcin Musa ko Isah Alahimas Salam, tare da yin suka ga annabcin Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama, ba zai iya ba, don nan take jahilcinsa da taqin saqar maganarsa zasu fito fili.

Da yawa cikin mabiyan Ali da na Usman na da ra’ayin cewa, Ali na da hannu cikin wannan juyin mulki da ya kai ga kashe Usman. Waxannan sun ce Ali na da hannu don ba su son Usman. Suna son su ce ko Ali ma ba ya sonsa. Waxancan su kuma sun ce Ali na da hannu don ba su son Alin. Suna son su shafa masa kashin kaji. Amma mafi yawan musulmi sun san qarya vangaroran biyu ke yi.[2]

Kasancewar Malam Sa’alabi na cikin malaman da ke amsa sunan Sunnah kawai bai isa hujja akan karva duk maganarsa ko da kuwa tana zancen darajar halifa Abubakar ne, sai fa in an tabbatar da ingancinta. Kamar dai xan Shi’ar yana son ne ya ce, ga wani malami nan daga cikinku na kafa muku hujja da shi, don ya faxi abin da ya zo daidai da ra’ayina. To, ai Ahlus-Sunnah gaskiya suke bi ba malamai ba. To, ta ya ya ruwayar fataken dare, mai maqoshin kolo a ruwaya, wanda ke yaki-halas yaki-haram; da sahihi da la’ifi duk hajarsa ce take zama hujja a kanmu?[3]

Kasancewar ana samun qarya da gaskiya da yawa a cikin riwayoyi, ya sa dole a koma ga ma’abuta ilimin hadisi, a matsayinsu na rariya uwar tata a fagen, don a rarrabe tsakanin garin taba da na gero. Kamar yadda ake komawa ga malaman Nahawu don banbancewa a tsakanin Nahawun larabawa da na Ajamawa. Da kuma yadda ake komawa ga malaman Lugga, don tantance abin da yake mallakar luggar da wanda ba mallakarta ba. Da kuma yadda ake tuntuvar malaman waqa da na Xibbu akan abin da ya shafe su. Kowane “Allazi” daga cikin ilimi, da nashi “Amanu” da aka san shi da shi. Wani ko “kafaru” ake samu gare shi. To, malaman Hadisi su ne mafiya girman daraja a kan sauran malamai. Su ne kuma mafiya gaskiya da xaukakar matsayi, da kishin addini.[4]

Gaba xayan qungiyoyin musulunci sun yarda da cewa, duk wanda ya yi imani da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wajibi ne ya yi wa hakan rakiya da tsare dokoki. Idan kuwa ba haka ba, gobe lahira kashinsa ya bushe Annabi na ji na gani. Akwai daga cikin Shi’ah ‘yan sha biyu da ke cewa, da zaran mutum ya so sayyidina Ali Raliyallahu Anhu a zuci to, yana iya aikata duk abin da ya ga dama don ya fi qarfin zunubi. A kan haka kenan, babu wata buqata ta samun wani shugaba ma’asumi a yau, don samun wata falala, domin son da suke ma Ali Raliyallahu Anhu a cewarsu, ya ishe su shinge.[5]

A cikin lumana, Ibnu Taimiyyah ya warware duk shubhohin da malaman Shi’ah ke kafa hujja da su. Babu zagi babu cin mutunci. Duba waxannan maganganun nasa alal misali:

Da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi nufin naxa Ali Raliyallahu Anhu a matsayin Yarima mai jiran gado, waxannan Sahabbai uku ba zasu musa masa ba. Da kuma qaddarar Allah za ta sa su yi masa musu, da sauran Sahabbai sun shawo kansu. Don gaba xayansu ba su saba da savawa ko bari a sava wa umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Ba ka ganin aqalla kashi xaya cikin uku na musulmi sun tallafa ma Ali a wajen yaqar da ya yi ma Mu’awiyah alhalin ba shi da wani nassi da ya sa shi yin haka? Ya kake zato da Ali na da nassi na zama halifa tun farko, amma waxancan suka amshe masa? Nawa ne daga cikin Sahabbai za su mara masa baya a wannan hali?[6]

Idan ‘yan Shi’ah suka ce, Ali Raliyallahu Anhu bai tava sujada ga gunki ba, saboda ya karvi musulunci tun bai balaga ba. Kuma haka bayan ya musuluntar ma bai yi ba, tunda musulmi ne. Sai mu ce ma su, ai babu wani abin alfahari a cikin wannan. Tunda kowane musulmi haka yake. Da ma shari’a ba ta hau kan yaro ba, balle. Idan kuwa suka ce: A’a, ba muna magana ne a kan bayan musuluntarsa ba, muna yi ne kan kafin haka. To, sai mu ce masu: Wannan kuma sanin gaibu sai Allah. Mu dai ba mu san wannan magana ba. Kuma shi xan Shi’ar da ke faxar wannan magana ba ya daga cikin mutanen da ake shiga xaka da zancensu.[7]

Mun yafe wa xan Shi’ar qaryar ijma’i da ya yi. Muna so ya tabbatar mana da maganar ta hanya xaya ingantancciya. Domin wadda Sa’alabi ya ambata mai rauni ce. A cikinta akwai mazajen da ba a yarda da su ba. Balle daxa wanda xan magazili ya riwaito, wanda shi rauninsa ya vaci matuqa. Hadissan da ya tattara a cikin littafinsa, ko kurtu a makarantar ilimin hadisi ya san cewa qaryayyaki ne kawai aka kitsa. To, isnadin nan guda xaya rak ingantacce da muke nema gare shi muna son ya qunshe wannan magana da waccan.[8]

 Shi dai Ibnu Taimiyyah bai tsayar da martaninsa kawai ga wannan xan taliki da yake tattaunawa da shi ba. A’a, ya fuskanci addinin Shi’ar ne ga baki xayansa ya kai masa hari da makaman hujjoji. Saurari abin da yake cewa:

Duk da yake shi wannan xan Shi’ar sawun varawo ne ya taka; ko da aka haife shi shehunansa sun riga sun yamutsa hazo a fagen tarihin musulunci. Shi kuma da ya zo sai kawai ya hau ba tare da ya tankaxe ya rairaye ba, balle ya kai ga tsagwaron gaskiyar da ma'abuta ilimi manya da qanana suka sani a yanke.[9]

Mawallafin ya kasance a cikin hattara sosai game da qarairayin da aka jingina ga Ali don a bajintar da shi. A irin waxannan wurare in babu cikakkiyar hattara sai a shiga rigar mutuncin Alin, wanda kuma ba shi ne manufa ba. Yi nazarin in da yake cewa:

Amma cewar da xan Shi’ar yayi Ali Raliyallahu Anhu bai tava bugun wani abu da takobinsa ba face ya gama da shi. Ba mu da masaniya akan ingancin wannan magana ko rashin ingancinta. Babu wata riwaya ingantatta a hannunmu da za mu iya rosa wannan da ita. Amma da za’a sami wani mutum shi kuma ya ce Khalidu ne da Zubairu da Bara’u xan Malik da Abu Dujanata da Abu Xalhata da makamantansu waxanda ba su tava bugun wani abu da takobinsu ba face sun gama da shi, ka ga an yi kunnen doki kenan. Musamman da yake kasancewar irin su Khalidu xin, da shi Bara’u mafi shahara da wannan irin jaruntaka kamar yadda masana tarihi za su iya faxa. Don kuwa har an riwaito cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Khalidu wani takobi ne daga cikin takubban Allah, wanda Allah ya zare a kan mushrikai”.

Babu wanda zai ji wani qaiqayi ko ya yi wani kokwanto, idan aka ce, wanda Manzon Allah ya siffanta da kasancewa takobin Allah, ba ya saran abu face ya gama da shi. Aka kuma taras da cewa Khalidun nan ya kashe kafirai ba adadi a fagen fama. Kuma har ya koma ga Allah bai tava gudu daga wurin yaqi ba. Wannan magana ta fi qanshin gaskiya, da an jingina ta gare shi.[10]

 Ka ga a nan ya yi qoqarin fidda kansa ga abin da babu da tabbaci a cikinsa. A wurare da dama zaka iske ya yi irin wannan. Kamar in da mawallafin wancan littafin ya ce, wai Abubakar ya nemi a yi ma sa murabus, kuma wai, wannan ya nuna daman can shi bai cancanta ba. Sai Ibnu Taimiyyah ya ce:

Kamata ya yi marubucin ya bayyana ingancin wannan magana. Idan kuwa ba zai iya ba, to ya sani ba duk abin da aka riwaito ne gaskiya ba. Kuma saqar duk da aka kitsa a kan zance da bai inganta ba, ita ma hakan.

Abu na biyu: Idan ta tabbata cewa, Abubakar Raliyallahu Anhu ya faxi wannan magana, babu mai ikon ce masa don me? Domin kuwa babu wani dalili da zai hana a yi masa murabus xin matuqar ya nemi hakan don wani dalili na qashin kansa. Mu dai ba mu da wata masaniya a kan ya nemi murabus ko bai nema ba, balle mu ga wurin vata lokaci a kan wannan batu.[11]

 Mawallafin ya wofintar da jimillar hajar ta ‘yan-sha-biyu, mafi yawan lokuta a cikin ruwan sanyi. Amma ya kan xan tsananta harshe a wani wurin. Kamar in da yake cewa:

A kan haka ne jahilcinsu da zaluncinsu suka gagari yawun alqalami siffantawa. Domin sun kasance suna godogo da riwayoyin qarya da ruxaxxun lafuzza da mummunan qiyasi, suna kuma ji da iqrarin cewa riwayoyi ne na gaskiya, kai mutawatirai ma. Kuma lafuzzan can nasu nassosa ne qwarara, ga su sarai. Kuma duk hujjar da suka bari ta hankali, hujja ce gar.[12]

 Haka dai mawallafin ya ci gaba da fexe gaskiyar Allah qarara dangane da lamarinsu:

Wannan feshin qarya ba wani abu ne ba a wurin waxannan mutane, domin kuwa jini da tsokarsu da qarya suka tofo. Hakan ta sa kodayaushe suke qoqarin musanta abin da duniya ta gama tabbatar da kasancewarsa gaskiya, tare da qoqarin tabbatar da abin da duniya da lahira an yarda da kasancewarsa toka.[13]

Ya dai kai matsaya ta qarshe a kansu ne in da ya ce:

Babu wata qungiya ta ‘yan bidi’a da za a ce gara ‘yan-sha-biyu da su.[14]

Wani lokacin kuma ya kan shaci fushi don kishin kariyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ko iyalansa da Sahabbansa daga cin mutuncin da ‘yan-sha-biyun suka yi ma su. Mafi nauyin maganar da ya furta a cikin wannan littafi ita ce maganar da ya yi a kan wautar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ‘yan Shi’ah ke yi cewa wai, ya yi gudun hijira tare da Abubakar Raliyallahu Anhu don bai san shi maqiyinsa ne ba:

Ka ga dole ne duk wanda zai riqa a matsayin aboki a cikin irin wannan tafiya ya kasance soyayyarsa da shi ta shafe ta kowa. Hakan kuwa ta tabbata, don ya nuna masa irin baqin cikin da yake ciki a kan halin da ya shiga. Amma kuma sai duk hakan ta zama busar iska; ya kasance yana qiyayya da shi a zuci? Bayan kuma shi ya sakankance har ga Allah cewa, shi masoyinsa ne?

Ko shakka babu, babu wanda zai yi wannan zavin tumun dare sai mafi wauta da jahilcin mutane. Allah kuwa ya qasqanta duk wanda ya jingina irin wannan wauta da jahilci ga Manzonsa, kuma mafi cikar halittarsa ga hankali da ilimi da gogewa.[15]

Aikinmu a Cikin Wannan Littafi

Littafin da muka dogara da shi a wannan aiki shi ne taqaitaccen Minhajus Sunnah na larabci, wanda Sheikh Abdallah Al-Gunaiman, wani malami mai koyar da Tauhidi a masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi. Wanda kuma aka buga shi a maxaba’ar Darus Siddiq da ke San’a’a ta qasar Yaman, a shekarar 1426H/2005M. Malamin ya bi sawun Imamuz Zahabi ne wajen taqaita littafin na Ibnu Taimiyyah akan abin da ya shafi aqidar Shi’ah ita kaxai.

A haqiqanin gaskiya ba fassara ce kaxai aikin da muka yi wa wannan littafi ba. Domin kuwa mun duba zubin littafin da tsarin tafiyarsa da kanun bayanansa duk mun yi gyara mai ma’ana a cikinsu. A wasu lokutan mukan buqaci koma ma asalin littafin na Ibnu Taimiyyah mai sifili takwas don tantance tushen maganar da yadda aka faxe ta, ko don cike wani givi da aka bari.

Game da fassara xin ita kanta, mun bi tsarin da muka saba da shi a wannan cibiya na lizimtar bayar da ma’anar magana kamar yadda mai ita ya faxe ta ba tare da qari ko ragi ba. Mukan kuma yi qoqarin kusantar da ma’anar ga mai karatun Hausa, ta hanyar lulluve ta da nau’oin adon magana da irin namu salo na Hausawa a maimakon lizimtar kalimomin da marubucin ya yi amfani kawai da su da larabci. A duk lokacin da mawallafin ya bayyana qwarewarsa a harshen larabci sai mu kuma mu bayyana tamu qwarewa a harshenmu na Hausa; sai mu haxiye maganar tasa, mu fito da ita da namu salo kamar daxai ba fassara ce muke yi ba. Wannan ita malamai suka sani da suna Fassara mai ‘yanci. Bari mu xan ba da ‘yan misalai ga masu karatu waxanda suka san harsunan biyu don gane muhimmancin bin wannan tsari da muka yi.

Ibnu Taimiyyah ya ce:

وإذا قام الدليل القطعي على ثبوت إمامتهم، لم يكن علينا أن نجيب عن الشبه المفصلة، كما أن علينا أن نجيب عما يعارضه من الشبه السوفسطائية. وليس لأحد أن يدفع ما علم يقينا بالظن.

Ga yadda muka fassara shi:

Da zarar kuwa irin wannan dalili yankakke ya tabbata, a kan dacewar halifofin da shugabancin, kamar yadda ya tabbata a wurinmu, to, babu buqatar sai mun ci dugadugan sauran qyaleqyalin da suka yi wa qaryar. Tsayawa bayar da amsa a kan waxannan wofintattun Shubuhohi, bayan an rosa ginshiqansu, vata lokaci ne. Babu wani mutum da ke iya rosa masaniyar da aka sakankance da ita, alhali makamin da ke hannunsa sungumin ragga ne kawai.[16]

Sai kuma in da ya ce:

الجواب من وجوه: أحدها: قد تقدم بيان بطلان كل ما دل على أنه إمام معصوم قبل الثلاثة. الثاني: أن النصوص إنما دلت على خلافة الثلاثة قبله. الثالث: أن يقال: الإجماع المعلوم حجة قطعية لا سمعية، لا سيما مع النصوص الكثيرة الموافقة له، فلو قدر ورود خبر يخالف الإجماع كان باطلا: إما لكون الرسول لم يقله، وإما لكونه لا دلالة فيه. الرابع: أنه يمتنع تعارض النص المعلوم والإجماع المعلوم، فإن كليهما حجة قطعية، والقطعيات لا يجوز تعارضها لوجوب وجود مدلولاتها، فلو تعارضت لزم الجمع بين النقيضين. وقد دل الإجماع المعلوم والنص المعلوم على خلافة الصديق رضي الله عنه وبطلان غيرهما، ونص الرافضة مما نحن نعلم كذبه بالاضطرار، وعلى كذبه أدلة كثيرة.

Ga yadda muka fassara maganar:

Mun riga mun warware duk wata magana da ke cewa, dole ne Ali ya zama halifa kafin halifofi uku da suka gabace shi. Domin kuwa gaba xayan nassosan da suka tuzgo akan shugabanci na tabbatar da halifancinsu ne kafin shi. Kuma amon ijma’i akan haka ya game duniya. Hujja ne kuma yankakka, ba naji-naji ba. Musamman kuma da aka sami nassosa da dama suka mara masa baya. Da wani labari zai tuzgo ya tunni wannan ijma’i, to, sai a tuhumce shi don ya tabbata zakka. Lalle ne kuma a qarshe a taras cewa, labarin qanzon kurege ne.

A qa’ida, ba ta yiwuwa ingantaccen nassi ya ci karo da lafiyayyen ijma’i. domin kuwa ko wanne daga cikinsu hujja ce yankakka. Su kuwa yankakkun hujjoji, amanar da ke tsattsage da cikannansu ta dalilai da ke tabbatar da ingancinsu ba ta bari su yi kabra da juna. Da wata ‘yar hayaniya za ta faru tsakaninsu sai dai a sasanta su amma ba dai rabuwa ba.[17]

 Ga kuma wata magana tasa in da yake mayar da martani a kan wata falala da suka ce ta cancantar da Ali zama halifan farko. Ita ce wai, tauraro ya sauko qasa saboda shi. Ga abin da ya ce da larabci:

لم ينقض قط كوكب إلى الأرض بمكة ولا بالمدينة، ولا غيرهما. ولما بعث رسول الله صلى الله عليه وسلم كثر الرمي بالشهب، ومع هذا فلم ينزل كوكب إلى الأرض. وهذا ليس من الخوارق التي تعرف في العالم، بل هو من الخوارق التي لا يعرف مثلها في العالم، ولا يروي مثل هذا إلا من هو من أوقح الناس، وأجرئهم على الكذب، وأقلهم حياء ودينا. ولا يروج إلا على من هو من أجهل الناس وأحمقهم وأقلهم معرفة وعلما.

Ga yadda muka fassara ta:

Babu inda tarihi ya nuna tauraro ya tava faxowa qasa a Makka ko Madina, ko wasu garuruwa kusa da su. Eh, gaskiya ne, lokacin da aka aiko Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ana yawaita jifa da taurari. Amma duk da haka ba a samu cewa, tauraro ya tava saukowa qasa ba. Da hakan ta zama wani abu na keta hankali, kuma sananne a duniya. Hasali ma kai! Wani abu ne da bai tava faruwa a faxin duniya ba, balle ya zama abin kakabi. Kuma babu ma wanda irin wannan labari zai riqa fitowa bakinsa sai mafi wauta daga cikin mutane, wanda kuma ya ce wa musailamu cas, saboda cikar rashin kunya da wasa da addini. Kamar kuma yadda babu wanda zai saurare shi, balle har ya yarda da shi, sai mafi jahilci da wauta daga cikin mutane, wanda wayewarsa da ilimin addini ba ta cika cikin cokali ba.[18]

Muna fatar samar da wannan littafi a cikin harshen Hausa ya kasance babbar gudunmawa ga yunqurin da ake yi na yaxa Sunnah da warware rikittan da aka tayar a cikin tarihin magabata.

 RAYUWAR IBNU TAIMIYYAH[19]

Wane ne Ibnu Taimiyyah?

 Sunansa Ahmad xan Abdulhalimu xan Abdussalami xan Abdullahi xan Haliru xan Muhammadu xan Haliru xan Aliyu xan Abdullahi. Ya shahara da sunan Ibnu Taimiyyah saboda kakarsa da ake kira Taimiyyah. Ana kuma ce ma sa “Majduddini”. Sannan ana ce ma sa “Numairi” saboda shi xan qabilar Banu Numairi ne. Ana ce ma sa kuma “Harrani” saboda Harrana ne garin da aka haife shi. Sannan ana ce ma sa “Dimashqi” saboda a garin Dimashqa ne ya girma, ya yi karatu.

Asalinsa

 Ibnu Taimiyyah xan asalin qasar Turkiyyah ne. Don an haife shi a garin Harrana wadda take arewa maso gabascin qasar ta Turkiyyah. An haife shi ne a ranar litinin 10 ga watan Rabi’ul Awwal 661H. Amma bayan shekaru shida sai iyayensa suka yi hijira daga qasar zuwa qasar Siriya in da suka sauka a babban birnin Dimashqa, hedikwatar Sham. Dalilin hijirar tasu kuwa shi ne kauce ma fitinar ‘yan Tattar waxanda suka auka ma garuruwan musulmi suka yawaita varna da zubar da jinainan bayin Allah ba li ba la.

 Game da mahaifansa kuwa, shi xan gidan malanta ne. Domin ya sami kansa a tsakanin iyaye da kakanni da ‘yan’uwa ma’abuta karatu. A lokacin da zasu yi hijira kuwa babu abin da ya wahalar da su kamar littafai da ke tare da su masu xinbin yawa, ga su kuma suna gudun maqiya. Ba domin kiyayewar Allah ba ma ba zasu tsira da rayukansu zuwa Sham ba.

 Isarsu qasar Sham ke da wuya mahaifin Ibnu Taimiyyah Shihabuddini ya fara koyarwa da wa’azi a babban masallacin Jum’ah na Dimashqa wanda ake kira Al-Jami’ul A’azam masallaci mafi girma. Daman shi fitaccen malamin furu’a ne a mazahabar Hambaliyyah. Nan take aka shugabantar da shi ga babbar makarantar hadisin nan da aka sani Darul Hadis As-Sukkariyyah, aka kuma ba shi gida a cikin makarantar in da nan ne xansa Ibnu Taimiyyah ya girma.

 Kafin haka, kakan Ibnu Taimiyyah Majduddini sanannen malami ne da ya yi wallafe-wallafe a fannin hadisi da Usulul Fiqhi. Shi ne mawallafin littafin nan na Muntaqal Akhbar wanda Imamus Shaukani ya yi wa sharhi a cikin Naulul Auxar.

 Haka ma baffansa Fakhruddini, malami ne fitacce da ya wallafa babban littafin Tafsirin Alqur’ani. Shi ne kuma wanda ya gaji Ibnul Jauzi a kujerarsa ta karantarwa da babban mimbarinsa na Bagadaza. Kuma Ibnu Taimiyyah ya yi karatu a wurinsa.

Tashinsa da Iliminsa

 Ibnu Taimiyyah ya tashi a gidan ilimi kamar yadda muka gani. Ya kammala hardar Alqur’ani a cikin quruciya. Sannan ya kula da sanin ilimoman Fiqihu da Hadisi da Tafsiri da Arabiyyah. Ya soma karantarwa da fatawa da rubuta littafai da tattaunawa da malamai Munazara tun bai wuce shekaru ashirin ba. Koda ya cika shekaru talatin an fara yi masa laqabin Mujtahidi kuma “Mai raya Sunnah”.

 Yana da matuqar wuya a iya sifaita baiwar da Allah ya yi wa Ibnu Taimiyyah ta fuskar ilimi. Masu ba da labarinsa na ganin kasawarsu wajen bayyana irin hikimomin da ke tattare da shi ta wannan haujin. An lisafta malaman da ya gurfana a gabansu don xaukar karatu aka tarar sun zarce malamai xari biyu. Akwai kuma littafan da ya karanta su sau da yawa a wurare daban-daban kamar Musnad na Imamu Ahmad.

 Game da nasa littafai shi kuma, Ibnu Taimiyyah ya wallafa sama da littafai hamsin a fannona daban-daban na addini, banda qananan wallafe-wallafensa da aka tara cikin Majmu’ul Fatawa mai sifili talatin da bakwai. Ya ishi mai karatu misali abin al’ajabi cewa, duk da yake Ibnu Taimiyyah bai wallafa Tafsirin Alqur’ani ba, amma malamai daga bisani sun wallafa shi daga cikin littafansa. Ma’ana an tattara wuraren da ya yi sharhi akan ayoyin Alqur’ani daga cikin littafansa a tsakankanin maganganunsa da kafa hujjojinsa, sai ga shi an samu kusan kammalallen Tafsiri mai Mujalladi huxu.

Mujaddadi Ibnu Taimiyyah

 Muna iya cewa, Allah gwanin sarki ya tashi Ibnu Taimiyyah ne a wani lokaci da buqatar irinsa ta yawaita. Don kuwa a wancan lokaci al’umma tana fama da matsaloli da rikitta da tashin hankula na ciki da na waje. Daga cikin gida musulmi na fama da rabuwar kai, da yawaitar qungiyoyi da yaxuwar bidi’ah da raunin ilimin furu’a. Ga kuma lalacin da ya yaxu a cikin jama’a da zaluncin sarakuna da kwaxayin malamai. Tsibbace-tsibbace da bokanci da duba sun zama gama-gari a cikin al’umma. Daga waje kuma ‘yan mishan sun kai ma musulmi farmaki, ‘yan Shi’ah masu kiran kansu Faximawa sun haxa kai da su. Sannan ga Tattar sun shelanta mummunan faxa da musulunci da musulmi a duk in da suke a wancan lokaci.

 Shaihun musulunci ya fuskanci duka waxannan matsaloli da nufin magance su. Ya kuma samu taimakon Allah matuqa a wajen cimma wannan gurin nasa. Ga shi kuma Allah ya ba shi makamai da ya wuyata a samu wanda ya yi tarayya da shi a dukansu. Mutum ne da aka sifaita shi da kaifin basira da qarfin qwaqwalwa, har wasu ma na ganin bai tava sanin abu ya manta da shi ba. Yana da qarfin tuna ayoyin Alqur’ani da nassosan hadissai da maganganun malamai na kowane fanni. Don haka ya kasance mai kaifin hujja wadda take yanke wuyan abokin gaba nan take. Ga shi kuma jarumi da ba ya tsoron ko-ta-kwana. Don haka ba ya da ja da baya ga abin da ya sa gaba. Sannan yana da kwarjini a idon jama’a da kyawawan xabi’u da suka daxa soyar da shi ga mutane. Ga shi mutum mai kishin gaskiya da qoqarin yaxa ta. Haxa da halinsa na gudun duniya da rashin kula da jin daxinta. Irin wannan malami Allah ya xora shi a kan kyakkyawar hanya irin ta Annabawa wane irin canji kake tsammanin al’umma ba za ta ci moriyarsa ba ta hanyarsa?

 Xan Taimiyyah nan take ya rurrusa aqidun da suka zame ma musulunci tsutsar goro ta hanyar rubuce-rubucensa da wa’azozansa da karantarwarsa. Ya kece raini a wajen wargaza aqidun Yahudawa da na ‘Yan mishan. Ya yi faxa da qungiyoyi mabiyan son zuciya irin mulhidai da zindiqai da ‘yan Shi’ah da waxanda suka wuce wuri a Sufanci. Ya yi kira ga koma ma littafin Allah da Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba tare da ta’assubanci ga wani mutum ko qungiya ko mazhaba ba.

 Sa’annan ya kira sarakuna da talakawa zuwa ga yaqar kafirai waxanda suka keta hurumin musulmi, musamman dai Tattar. Ya kuma fita ya yi yaqi a matsayin xaya daga cikin sojoji.

 Tare da haka kuma Ibnu Taimiyyah ya kafa wata makaranta da Allah ya yawaita almajiranta tun daga wancan zamani har zuwa yau, kuma tana ci gaba da bunqasa har a naxe qasa. Wannan makaranta tasa tana mutunta magabatan Sahabbai da Tabi’ai da waxanda suka biyo bayansu, da shugabannin mazhabobi, tana kuma la’akari da ra’ayoyansu da fatawoyinsu baki xaya. Tana kuma rinjayar da nassi ingantacce idan ya zo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan maganar kowa kome darajarsa. Wannan makaranta dai tana da xaruruwan littafai da dubaiban malamai a cikinta. Dukkaninsu suna jingina kansu ga Sunnah da biyar magabata ba ga shi Ibnu Taimiyyah xin ba.

Jarabawar Da Ibnu Taimiyyah ya Gamu da Ita

 Yana da wuya Allah ya xaukaka wani bawansa ba tare da ya gamu da wasu jarabawoyi ba a rayuwarsa. Wannan ita ce sunnar Allah ga Annabawa da malamai mutanen kirki.

 Shehun musulunci ya gamu da jarabawoyi da dama a sakamakon jihadinsa na makami da na alqalami waxanda suka dagula ma sa jin daxin rayuwa. Zamu faxi wasu daga cikinsu a taqaice kamar yadda suka zo a tarihinsa daga littattafai da dama.

 A shekarar 696H ya gamu da qyashin abokan tafiya, malamai, waxanda suka xauki littafinsa Al-Fatwal Hamawiyyah suka kai qararsa da shi a wurin mahukunta. Sun bi duk hanyoyin da suke iyawa wajen murxa maganarsa da ba ta irin ma’anar da suke so su jingina ma sa. A wannan lokaci sarki Saifuddin Jagan ya goyi bayan Ibnu Taimiyyah, ya kuma husata da waxanda suka kafa adawa da shi. Don haka wannan jarrabawa ba ta daxe ba ta kuranye.

 A shekarar 705H lokacin da farin jinin Ibnu Taimiyyah ya gama bayyana, bayan an ga rawar da ya taka a yaqin da aka yi da Tattar, har kuma ya samu kusanci da hukuma abin da ya ba shi damar sa a kawar da wasu varnace-varnace. Nan take sai qurjin hasada ya sake vallewa a zukatan wasu malamai daga cikin sufaye. Sai wani malami da ake kira Nasrul Mambiji da wani malami bamalike ana ce ma sa Ibnu Makhluf suka tafi hedikwatar sarauta da ke qasar Masar suka kai qarar Ibnu Taimiyyah suna tuhumar sa da gurvata aqidun jama’a. Suka kafa hujja da littafinsa na Al-Aqidatul Wasixiyyah. A nan ma sarki ya ba da umurni aka zaunar da shi tare da manyan malamai in da aka karance littafin nasa, daga qarshe kuma aka barrantar da shi daga sava ma magabata. Sai ma a wannan karon ya samu takardar yabo daga Sarkin Musulmi.

 Wata xaya bayan faruwar wannan, sai waxannan malaman suka sa sarki ya rubuta ma sa wata takarda ana neman sa da zuwa Misra don ya bayyana a gaban sarki. A wannan karon da tuhumar yana neman sarauta! An dai zaunar da shi a gaban Ibnu Makhluf don ya yanke ma sa hukunci, abin da xan Taimiyyan ya qi yarda da shi, kasancewar shi ne abokin husumar da ya kai qararsa. Shehul Islami sai da ya share wata goma sha biyu cur a gidan kaso kafin a nemi ya fita, in da shi kuma ya qi fita ya ce, sai an bayyana ma sa laifinsa. Daga qarshe ya fita daga kurkukun bayan ya cika wata goma sha biyar da sati biyu bisa ga nacewar wani basaraken garinsu.

 Wata bakwai bayan fitowarsa sai aka sake mayar da shi a cikin watan Shawwal na 707H saboda ya ci gaba da zama a Masar mutane na amfana da shi. A wannan karon sai ya kasance mutane suna tururuwa a gidan kaso don gaishe shi da yin fatawa a wurinsa, abin da ya daxa cinna wutar gaba a tsakaninsa da waxanda ke biyar sa da baqar yadiya.

 Bayan fitowarsa ma, xan Taimiyyah bai fasa abin da yake yi na karantarwa da fallasa miyagun aqidu ba. Wannan ya sa aka xauke shi daga Alqahira zuwa Iskandariyyah da nufin ya haxu da ‘yan dabar garin su kashe shi. Ana haka ne sai aka samu canjin gwamnati lokacin da sarki Muhammad xan Qalawun ya sake koma ma kujerar sarauta sai ya mayar da Shehul Islami zuwa hedikwatar ta Masar. Daga nan kuma suka fita a shekarar 712H da nufin yaqar kafiran Tattar, sai Allah ya mayar da maqiyan garuruwansu ba tare da an yi yaqi ba. Don haka, sai Ibnu Taimiyyah ya koma gida Sham, in da ya haxu da tarbo wanda ba a tava ganin irinsa ba, bayan ya yi shekara bakwai da sati bakwai a qasar Masar tun wancan kiran da aka yi ma sa.

 Ko bayan komawarsa gida Shehul Islami ya ci gaba da samun matsaloli da malamai masu qaramin sani da taurin kai. Kamar yadda suka yi cah a kansa wai don ya ce, in mutum ya yi rantsuwar saki kaffara kawai zai yi, aurensa na nan. Haka ma don cewar da ya yi saki uku na komawa xaya idan an yi su zama guda. Waxannan malamai ba su samu sukuni ba sai da suka sa aka hana shi fatawa a shekarar 719H.

 A shekara ta 720H aka sake iza qeyar babban malamin zuwa gidan kaso in da ya share wata biyar da kwana goma sha takwas.

 A shekara ta 726H wasu alqalai sun tsoma bakinsu a cikin rikicin Ibnu Taimiyyah da maqiyansa, in da aka wallafa wata fatawa ta qarya aka jingina ta gare shi, wai ya haramta ziyarar qabarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da na sauran Annabawa. Alhalin shi kuwa ya rarrabe tsakanin ziyararsu ne ita kaxai da kuma haxa ta da yin tafiyayya. Ya labarta savanin magabata a kanta, sannan ya nuna karkata ga hanawa idan ya kasance an yi tafiyayya saboda ita. Ya kuma bayyana hujjojinsa na ingantattun hadissai. Wannan rikicin ma dai sai da ya sake mayar da wannan bawan Allah a gidan maza, in da ya samu damar da ya yawaita wallafe-wallafe gami da bautar Allah Ta’ala.

 A shekara ta 728H aka fitar da duk littafan da ke tare da shi da alqalumma da tawadar da aka samu a wurinsa, saboda wani malami da ake kira Ikhna’i ya kai qarar sa, don ya yi ma sa raddi, kuma wai ya jahiltar da shi. A nan ya zama dole Ibnu Taimiyyah ya haqura ya duqufa ga zikiri da sallah da karatun Alqur’ani da yake waxannan suna a kansa tun zamanin quruciya.

Rasuwarsa

 Allah ya karvi ransa a gidan maza na birnin Dimashqa yana da shekaru 67 waxanda suke cike da karantarwa da haquri da jihadi. Ya rasu kafin wayuwar garin litinin 20 ga watan Zul Qi’ida 728H.

 Bai yi aure ba ballantana ya bar zuri’a. Bai kuma tava furta kalima xaya da take nuna rashin sha’awarsa ga auren ba. To, ko me ya hana shi cin moriyar wannan Sunnah? Sanin gaibu sai Allah.

Littafan da Aka Duba Don ba da Tarihinsa

Al’Uqudud Durriyyati Min Manaqibi Shaihil Islami Ibni Taimiyyati na Muhammad xan Ahmad xan Abdulhadi, tahaqiqin Muhammad Hamid Al-Faqi, bugun Darul Katib Al-Arabi.

Al’A’alamul Aliyyati na Bazzar, tahaqiqin Zuhair Shawish, bugun Al-Maktabul Islami, Beirut, Lebanon.

A’ayanul Asri na Ibnu Aibak As-Safadi, tahaqiqin Ali Abu Zaidah da wasu, bugun Darul Fikri, Beirut, Lebanon.

Ad-Durar Al-Kaminatu Fi A’ayanil Mi’ati As-Saminti, na Hafiz Ibnu Hajar Al-Asqalani, tahaqiqin Sayyid Jad Alhaq, bugun Jami’ar Ummul Qura, makka, Saudi Arabia.

Buhus An-Nadwatil Alamiyyati An Shaihil Islami Ibni Taimiyyati, tahaqiqin Muqtada Hasan, bugun Dar As-Sami’i.

Da’awatu Shaikhil Islami Ibni Taimiyyata Wa Asaruha Fil Harakatil Islamiyyatil Mu’asirati, na Salahuddin Maqbul, bugun Majma’ul Buhusil Ilmiyyati, New Delhi, India 1412H/1992M.

Dhailu Xabaqatil Hanabilati, na Hafiz Ibnu Rajab Al-Hambali, tahaqiqin Muhammad Hamid Al-Faqi, bugun Darul Ma’arifati, Beirut, Lebanon.

Shajaratuz- Zahab Fi Akhbari Man Zahab, na Ibnul Imadi Al-Hambali, bugun Darul Fikri, Beirut, Lebanon.

Shaikhul Islami Wa Juhuduhu Fi Ilmil Hadis, na Firiwa’i, bugun Darul Asimati.

Husulul Ma’amul Min Kalami Shaikhil Islami Ibni Taimiyyata Fi Ilmil Usul, na Abdurrahman xan Abdullahi Al-Amir, bugun Darul Waxan, Riyadh, Saudi Arabia, 1423H/2002M.

Ibnu Taimiyyah: Hayatuhu Wa Asruhu, na Imam Muhammad Abu Zuhrata, bugun darul Fikril Arabi, Alqahira, masar. 1898H/1974M.

 Godiya

 Wannan aiki ya xauki tsawon shekaru da dama, amma a wannan shekara da muke cikinta ta Hijirar 1429 ya daxa kankama sosai. Kuma a tsakkiyar aikin ne Allah ya karvi xaya daga cikin masu himma a aikin, shi ne Dr. Ibrahim Bello wanda ya ba da lokacinsa da kuzarinsa sosai don ganin nasarar aikin, sai dai ajali ya riske shi tun bai ko gama kabbarar harama a cikin aikin ba. Muna roqon Allah ya isar da ladarsa ta wannan aikin don ta zamo haske a cikin qabarinsa, ya kuma tara mu da shi a Darus-Salami.

 Ya zama tilas a kan wannan cibiya bayan godiya ga Allah, ta yi kevantacciyar godiya ga kwamitin da ya yi aikin na fassara, musamman sakatarensa Alhaji Aliyu Rufa’i wanda himmarsa a aikin ta zarce ta kowa. Ya kuma ba da gudunmawa mai tarin yawa a wajen fassarar ita kanta, sannan ya taimaka ainun a wajen bitar da ta share sama da watanni uku. Haka kuma qwarewarsa a sanin qa’idojin rubutun Hausa ta taimaka mana matuqa. Ba mu da wata sakayya a gare shi sai addu’a; Allah ya sa aikin ya zamo sanadin tsira. Sai kuma Mal. Aminu Ibrahim Maru da Sheikh Usman Sarkin Vurmin Jabo waxanda da su ne aka aza harsashin aikin tun da farko. Muna roqon Allah ya yi musu sakayya kyakkyawa.

 Sai cibiyar fassara da take Runjin Sambo a qarqashin jagorancin Dr. Tahir Muhammad Argungu. Su ma muna godiya a kan nasu qoqari.

 Gudunmawar masu saka aikin a cikin na’ura mai qwaqwalwa ita ma ba abar mantawa ce ba. Waxannan sun haxa da Al-Irshad Computers na Mal. Aminu Mustafa Digar Agyare da Aliyu Kambaza Business Centre da ke kan titin Amir Yahaya duk a nan Sokoto.

 A can kuma qasar Masar in da aka buga littafin Alhaji Uba Ahmad Ibrahim, wakilin gidan rediyon doce-belle ne ya yi tsaye don ganin aikin ya tafi daidai bisa haruffan Hausa, da kuma daidaita ayoyin Alqur’ani bisa haruffan xab’i na birnin Madina. Allah ya saka ma su ga baki xaya da mafificin alherinsa.

 Wannan gabatarwa ba za ta kammala ba sai mun miqa godiya ga jagororin wannan Cibiya da waxanda ke taimaka ma ta ta fuskoki daban-daban. Allah ya ba kowa ladar qoqarinsa, ya kuma xora mu bisa shiriya a cikin zantukanmu da ayyukanmu.

 Daga qarshe ina miqa godiya tare da yabawa ga uwargidana Mamar Mu’azzam a kan bitar da ta yi wa littafin daga bisani, da gyare-gyaren da ta yi masu ma’ana.[20]

 Allah ya daxa tsira da aminci ga shugabanmu Muhammadu da iyalansa da Sahabbansa baki xaya. Alhamdu Lillah.

 Baban Ramlatu,

 Muhammad Mansur Ibrahim

 Sokoto.

 24 ga Rajab 1429H (26-07-2008M)

 GABATARWAR SHEIKH GUNAIMAN

Wanda Ya Taqaita Littafin

Yabo da godiya Sun tabbata ga Allah Mai girma, mai rinjayar da gaskiya a kan qarya, wanda ya ce:

﴿بَل نَقذِفُ بِٱلحَقِّ عَلَى ٱلبَطِلِ فَيَدمَغُهُ فَإِذَا هُوَ زَاهِق وَلَكُمُ ٱلوَيلُ مِمَّا تَصِفُونَ١٨﴾ الأنبياء: ١٨

A’a, muna jefa gaskiya a kan qarya, sai (qarya) ta koma halakakka. Kuma bone ya tabbata a gare ku saboda abin da kuke Siffantawa[21].

﴿وَقُل جَاءَ ٱلحَقُّ وَزَهَقَ ٱلبَطِلُ إِنَّ ٱلبَطِلَ كَانَ زَهُوقا٨١﴾ الإسراء: ٨١

Kuma ka ce: “Gaskiya ta zo, kuma qarya ta lalace. Haqiqa, qarya ta kasance lalatacciya.[22]

﴿قُل جَاءَ ٱلحَقُّ وَمَا يُبدِئُ ٱلبَطِلُ وَمَا يُعِيدُ٤٩﴾ سبأ: ٤٩

Ka ce, “Gaskiya ta zo, kuma qarya, ba ta iya fara (kome). Kuma ba ta iya mayarwa[23]

Ina gode masa, godiya mai albarka. Ina shedawa babu abin bauta da cancanta sai Allah shi kaxai ba ya da abokin tarayya. Kuma Annabi Muhammadu bawansa ne, Manzonsa. Ya aiko shi da shirIya da addini na gaskiya don ya rinjayar da shi a kan sauran addinai. Ko maqiya sun qi ko sun so.

 Bayan haka, babu shakka, wannan littafi Minhajus Sunnah na daga cikin manyan Littafan da shahararren malamin nan Ahmadu xan Abdulhalimi xan Abdussalami, wanda aka fi sani da “Ibnu Taimiyyah” ya wallafa, wanda a cikinsa ya xaura sirdin fafata yaqi da qarya, ya tarwatsa gungun maqaryata da karnukan farautarsu, ya kuma taimaki gaskiya. Wannan shi ya qarfafa buqatar da ke akwai musamman ga matasa musulmi, da su tunkari wannan littafi don cin moriyar abin da ya qunsa.

Wannan bukata ta fi qarfafa a wannan lokaci, inda annobar Shi’ah ta barbazu, ta kai caffa a wasu garuruwan musulmi. A wasu wuraren ma, ta yaga ta ciza, ta saki dafinta. Ta yaudari waxanda suka jahilci lamarinta, ta hanyar shigar burtu. Babu Shakka wannan littafe waraka ne ga wanda ya kamu da rashin lafiyar Shi’ah.

 Wani abin al’ajabi shi ne, inda za ka taras da cewa, dukan qungiyoyin bidi’ah, vacewarsu ba ta yi zurfin ta mabiya Shi’ah ba, waxanda ke tinqaho da ci gaban sarkin baka. Kullum suna qara kutsawa cikin duhun dajin vata, amma suna ganin sun fi kowa shiriya, bayan suna yaqar masoyan Allah da Manzonsa. Littafansu sun cika har sun batse da zage-zage da la’antar manya-manyan bayin Allah; ba su kunyar kafirta manyan Sahabbai irinsu Abubakar da Umar da Usmanu Allah ya yarda da su ballantana qananansu. Sun kuma yi haka ne kawai saboda Sahabban nan sun bice wutar tsafi, suka rugurguza gumakan Farisa.

 Duk wanda ya buxe shafukan littafan ‘yan Shi’ah, zai ga yadda suka cika su fal da riwayoyin kafirta Sahabbai Raliyallahu Anhum. Su a wajensu yin haka ya zama tamkar ibada, har ma suna raya cewa wanda bai shiga sahunsu ba, ya zama abincin wuta. A cikin Littafinsu Al Wafi sun ce, wai, Allah ba zai karvi aikin wanda ba mabiyi Shi’ah ba, kome kyawon sa. Haka kuma a wani Littafi Alkafi mai muhimanci ainun a wurinsu, sun bayyana baqar adawarsu ga musulunci, da ma wanda ya zo da musuluncin gaba xaya.

 A wautar mabiya Shi’ah, sun ce, Allah ya saukar da Alqur’ani ne domin ya bayyana abubuwa guda biyu kawai. Na farko shi ne, nuna matsayin Ali Raliyallahu Anhu ta hanyar bayyana darajarsa da ta iyalansa. Na biyu kuma shi ne, aibanta Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da fallasa su. Wannan shi ne ya kai su ga tuhumar cewa, mafi yawan sassan Alqur’ani mai girma sun halaka ta hannun Sahhabai Allah ya yarda da su.

 Dukan tunaninsu da harkokin addininsu sun dogara kacokan a kan qarya, wadda suke zuqa ma limamansu. Sun cika shafa wa Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kashin kaji, ta inda har sun jingina su ga munafunci. Sai dai mu, muna sane cewa, sara da sassaqa ba su hana gamji toho. Allah wadaran ‘yan Shi’ah, ya cika su da tsoro, ya kunyata su, gami da ‘yan kanzaginsu.

Kodayake asalin wannan littafi ya qunshi bayanai iri-iri na martani ga masu aqidar Shi’ah da masu kore qaddara da masu falsafa, na zavar wa kaina kevantuwa ga abin da ya shafi Shi’ah kawai, saboda irin kariyar da ke tattare a wannan vangare ga abin da ya shafi tsarin shugabanci, da alfarmar Sahabbai da kuma mutuncin uwayen muminai (Matan Annabi, Sallallahu Alaihi Wasallama).

 Ban shigar da kalma ko xaya ba ta qashin kaina a cikin wannan aiki, dalili da cewa, mawallafin littafin (Ibnu Taimiyyah) bai bar wata kafa ta yin haka ba. Ya riga ya xinke shi da hujjoji masu qarfi. Allah ya saka masa da alheri, ya sa mu yi tarayya da shi a cikin ladar wannan gagarumin qoqari nasa, Amin.

 Allah shi ne mafificin wanda ake roqo. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Muhammadu xan Abdullahi da iyalan gidansa da Sahabbansa.

 0.1 GABATARWAR IBNU TAIMIYYAH

Shehul- Islami Ibnu Taimiyyah ya ce:

Yabo da godiya su tabbata ga Allah Mai girma da xaukaka. Wanda Ya ce:

﴿كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّة وَحِدَة فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ ٱلكِتَبَ بِٱلحَقِّ لِيَحكُمَ بَينَ ٱلنَّاسِ فِيمَا ٱختَلَفُواْ فِيهِ وَمَا ٱختَلَفَ فِيهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ أُوتُوهُ مِن بَعدِ مَا جَاءَتهُمُ ٱلبَيِّنَتُ بَغيَا بَينَهُم فَهَدَى ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِمَا ٱختَلَفُواْ فِيهِ مِنَ ٱلحَقِّ بِإِذنِهِ وَٱللَّهُ يَهدِي مَن يَشَاءُ إِلَى صِرَط مُّستَقِيمٍ٢١٣﴾ البقرة: ٢١٣:

Mutane sun kasance qungiya xaya (a kan gaskiya. Daga bisani sai suka yi savani, wasu suka bi gaskiya, wasu suka bi vata) sai Allah Ya aiki Annabawa suna masu bayar da bishara kuma masu gargaxi. Kuma ya saukar da Littafi da gaskiya tare da su. Domin (Littafin) ya yi hukunci a tsakanin mutane, a cikin abin da suka sava wa juna a ciki; kuma babu waxanda ya sava a cikinsa, face waxanda aka bai wa shi daga bayan hujjoji bayyanannu sun je musu, domin zalunci a tsakanin su. Sai Allah ya shiryar da waxanda suka yi imani ga abin da suka sava a cikinsa na gaskiya da izininsa. Kuma Allah yana shiryar da wanda yake so, zuwa ga hanya madaidaciya[24].

 Na shaida babu abin bauta da cancanta sai Allah shi kaxai, ba ya da abokin tarayya, kamar yadda ya shedi kansa da cewa;

﴿شَهِدَ ٱللَّهُ أَنَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ وَٱلمَلَئِكَةُ وَأُوْلُواْ ٱلعِلمِ قَائِمَا بِٱلقِسطِ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ ٱلعَزِيزُ ٱلحَكِيمُ١٨﴾ آل عمران: ١٨

Allah ya sheda cewa, haqiqa, babu abin bautawa da cancanta face shi. Su ma mala’ikku da ma’abuta ilimi sun shedi haka. Yana tsaye da adalci. Babu abin bautawa face shi, mabuwayi, mai hikima.[25]

Kuma na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne, Manzonsa. Cikamakon Annabawa, wanda Allah ya sifanta shi da cewa;

﴿لَقَد جَاءَكُم رَسُول مِّن أَنفُسِكُم عَزِيزٌ عَلَيهِ مَا عَنِتُّم حَرِيصٌ عَلَيكُم بِٱلمُؤمِنِينَ رَءُوف رَّحِيم١٢٨﴾ التوبة: ١٢٨

Haqiqa Manzo daga cikinku ya je muku. Ba ya son duk abin da ke wahalar da ku. Mai kwaxayi ne ga (shiriyar) ku Mai tausayi ne, mai jinqai ga muminai”[26]

 Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Bayan haka;

Wasu ‘yan’uwa Ahlus-Sunnah Sun isko ni da littafin Minhajul karamati fi Ma’arifatil Imamati na wani malamin Shi’ah, inda ya ke tallar hajarsa ta Shi’anci, tun ma ba a fadar sarakuna ba.

Littafin ya samu karvuwa ga mafi yawan waxanda ba su fahimci addini ba. Kuma ya samu taimakon qungiyar Shi’ah ta Baxiniyyah, mavarnata. Waxanda suka samo tushe daga malaman falsafar Yahudanci, ta Sabi’awa, waxanda ba su ganin kan kowa da gashi. Sun fanxare ma tafarkin Annabawa, sun juya ma musulunci baya, suka mayar da addini zavi son ka. Ba haka ba ma, lamarin addini a wajensu yana da matsayi irin na jam’iyyar siyasa, wadda a ke da zavin shiga da fita a kowane lokaci. Ita kuwa annabta a idanunsu, wata hanyar holewa ce kawai da kyautata zaman duniya.

 Wane mutum! Ire-iren waxannan marubuta fa da daxewa sun watsu a sassa na duniya, inda jahilci ya barbazu sakamakon qamfar malamai masana shari’a, masu tumbuke shukar vata da aka dasa cikin al’umma. Mabiya Shi’ah sun qware wajen lavewa ga sabara su harbi barewa, musamman wajen aqidar qaryata Manzanci a fa kaice. Bugu da qari kuma sun halaka mutane masu ximbin yawa ta hanyar yaudara.

 Qungiyoyin Shi’ah da na Jahamiyya su ne manya –manyan qofofin shigowar nau’ukan varna da damfara, musamman waxanda aka shigar cikinsunayen Allah da Siffofinsa da Littafansa. Kamar yadda aka samo tabbacin hakan daga limaman qungiyoyin Karramiyyah da Baxiniyyah da sauran tarkacen zindiqai.

 Shi wanda ya kawo min littafin, ya shaida mini cewa, suna amfani ne da littafin wajen yaxa gurvatacciyar aqida, musamman a gidajen masu mulki da masarautu. Za a iya tabbatar da haka, lura da cewa marubucinsa ya rubuta shi ne musamman ya aika shi ga sarki Khudabandah. A nan ne waxanda suka isko ni da littafin suka nemi in yi fashin baqi game da varnar da ke cikinsa. Saboda a ceto bayin Allah a kuma fallasa maqaryata. Sai na amsa musu da cewa, ai wannan littafi hujja ne a wajen masu shi, kodayake a cikin asiri sun jahilci cewa, babu komi cikin sa, sai shirme da maganganu marasa kan gado.

Abin da ya kyautu mu fayyace a nan shi ne, a gane cewa, su dalilai sun rarrabu ne zuwa gida biyu. Akwai dalilai na tsintsar Ilimi kuma akwai na kaifin hankali. Abin kaico shi ne, su mabiya Shi’ah, idan ka lura da ra’ayinsu da kyau za ka san cewa, sun vace vari. Domin sun rasa ilimi da hankali gaba xaya. Sun yi zo-zo zo da waxanda Allah Ya sifanta da cewarsa

Kuma suka ce: “Da mun zamo muna saurare ko muna da hankali da ba mu kasance a cikin ‘yan sa’ira ba.[27]

 Rubuce- rubucensu sun cika sun batse da qissoshi da labaran cin qanzon kurege, ga su kuma da wauta kamar xiyan fari. Sun goge wajen mayar da fari baqi a sashen riwaito hadisi, ba ruwan su da tacewa tsakanin maruwaici maqaryaci da wanda ba shi ba. Ba su dogara da komi ba face zato da an-yi-an-ce. Ga su da biyar ra’ayoyin malamansu a makance. Kuma suna jin cewa, wannan hanya da suke a kai itace a’ala, musamman a fagen kafa dalili. Wannan irin hali shi ya kai su har suka fantsama, suka faxa cikin jerin gwanon Mu’utazilawa da masu kore qaddara. Kamar yadda a wani lokacin kuma sai a tsince su a tashoshin Mujassimah da Jabariyyah. Wani abin al’ajabi da mamaki a nan shi ne, duk da irin zurfin vacewar waxannan qungiyoyi da aka zayyano, ‘yan Shi’ah sun zarce su nesa ba kusa ba a fagen rashin fahimtar lamurra. Wanda hakan ya sa malamai suka haxu a kan cewa, qungiyarsu ta fi kowace qungiya dolanci da jahilci. Sun tafka varnar da Allah ne kawai ya san iyakacinta a cikin al’umma.

Qungiyoyin Isma’iliyyah da Nusairiyyah da Baxiniyyah da Yahudawa da Kirista, manya- manyan arna da zindiqai, duk ta qofar Shi’anci suka samu hanyar barbaza varna a cikin musulunci bayan sun rinjayi wasu garuruwan musulmi, ta hanyar zubar da jini da kwashe dukiyoyinsu. Hasali ma duk qasar musulmin da masifar yaqi ta faxa ma, za ka taras da cewa, hakan ya faru ne bayan qullin qawancen makirci tsakanin kafirai da mabiya Shi’ah. Misalin faruwar irin wannan ba ya lissafuwa a duniya.

 Dalilin wannan qazamin qawance nasu, ba ya rasa nasaba da cewa tun asalatan, Shi’ah ta fito ne daga cikin tsatson zindiqai da munafukai, da suka bayyana a zamanin Sarkin Musulmi Aliyu xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu. Babbar aniyarsu ita ce faxa da Musulunci. Wannan shi ya sa Aliyu Raliyallahu Anhu ya hanzarta xaukar qwaqqwaran matakin wargaza gungunsu, ta hanyar lallasa musu nau’ukan azaba iri- iri, bayan da ya fahimci cewa, tsawa da gargaxi ba su bishe su. Ya yi amfani da bulala, ya koma yana qona su da wuta. Da lamarinsu ya vaci sai ya zaro takobinsa ya tunkare su cikin hanzari a fusace. Daga nan suka ce, qafa me na ci ban ba ki ba. Suka kama gudu ba waiwaye.

 Dalilin da ya sa Sarkin Musulmi Aliyu xan Abu Xalib Allah ya yarda da shi ya xaukar wa mabiya Shi’ah wannan mataki shi ne, saboda faifayewar su a wajen yabonsa, inda suka fifita shi sama da darajar halifa Abubakar Raliyallahu Anhu da Sarkin Musulmi Umar xan Haxxabi Raliyallahu Anhu wanda shi a wajensa bai tava fifita kansa a kan waxannan Sahabbai ba. Abin da ma ya tabbata daga wajensa shi ne, an ji shi da bakinsa yana cewa: “Abubakar ne ya fi kowa girman daraja a cikin wannan al’umma, sannan Umar, in ban da Manzonta”. Imamul Buhari a cikin ingantaccen littafinsa ya riwaito cewa, muhammadu xan Hanafiyya xan Ali Raliyallahu Anhu ya tambayi babansa cewa, wane ne mafifici daga cikin Sahabbai? Sai wancan jawabi ya zama amsa ga wannan tambaya.

 Wannan shi ne dalilin da ya sa malaman farko ba su yi savani ba a kan fifikon Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma a kan sauran al’umma. Wajen da suka yi muhawara kawai shi ne, tsakanin Aliyu da Usmanu yardar Allah ta tabbata a gare su, wane ne ba wane ne ba? Abin mamaki wai, kare da tallar tsire, tarihi ya nuna cewa, malaman Shi’ah na farko-farko, kai! har ma da na baya- bayansu an ji su suna fifita Abubakar Raliyallahu Anhu a kan sauran Sahabbai. Abdul Jabbar Al hamadani ya cirato daga littafin Tathbitun Nubuwah cewa; Abul qasim Al balakhi a cikin raddin da ya yi wa xan Rawandi ya ce, wani ya tambayi Shariku xan Abdullahi cewa; wa ya fi matsayi a tsakanin Abubakar da Ali? Sai ya kada baki da hanzari ya ce, Abubakar mana. Sai mai tambayar a cikin mamaki ya ce; “Kai da kanka ke faxin haka?” “To, ina amfanin kusancin ka ga Ali?”. “Ai duk wanda bai yarda da cewa wannan magana haka take ba, to ba shi ba Ali”. in ji Malam Shariku. Ya ci gaba da cewa, na rantse da Allah, watarana na ga Aliyu Raliyallahu Anhu da idanuna ya hau kan mimbari yana huxuba, ya na cewa, ku saurara, ku sani cewa mafi alheri daga cikin wannan al’umma bayan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne Abubakar sannan Umar yardar Allah ta tabbata a gare su. Kana ganin cewa zai kyautu a yi biris da wannan magana tasa? Na rantse da Allah, Aliyu Raliyallahu Anhu ko alama ba maqaryaci ba ne.

 Zango Na Xaya

‘Yan Shi’ah da Aqidunsu

 1.0 Malamai ku Bayyana Gaskiya

Duk lokacin da mabiya suka fara la’antar magabata, bayyanar da ilimi ya zama tilas. A lokacin da aka isko ni da wannan littafi wanda malamin Shi’ah ya rubuta aka kuma neme ni da mayar masa da martani, da yake, ba a ce ma maci dambu ya sha ruwa, sai na feqe alqalami kuma na jawo tawwada na shiga rubutu, ina mai fatattakar varna da vatan da suke neman bazawa, domin kange muminai daga faxawa cikin tarkonsu. Rashin yin hakan kuma, yana sa ‘yan barandar, karkatattu su zaci ko kasawa aka yi. Shi ya sa na himmatu ga rubuta abin da ya sawwaqa don cika alqawarin nan da Allah ya riqa ga malamai, domin tabbatar da adalci da ba da shaida domin Allah. Kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki ya ce;

﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُونُواْ قَوَّمِينَ بِٱلقِسطِ شُهَدَاءَ لِلَّهِ وَلَو عَلَى أَنفُسِكُم أَوِ ٱلوَلِدَينِ وَٱلأَقرَبِينَ إِن يَكُن غَنِيًّا أَو فَقِيرا فَٱللَّهُ أَولَى بِهِمَا فَلَا تَتَّبِعُواْ ٱلهَوَى أَن تَعدِلُواْ وَإِن تَلوُاْ أَو تُعرِضُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعمَلُونَ خَبِيرا١٣٥﴾ النساء: ١٣٥

Ya ku waxanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayuwa da adalci, masu shaida saboda Allah, kuma ko da a kan kawunanku ne, ko mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida ko ake shaida a kansa) ya kasance mawadaci ko matalauci. To Allah ne mafi cancanta da al’amarinsu. Saboda haka kada ku bibiyi son zuciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, ko kuwa kuka kau da kai, to lalle ne, Allah ya kasance Masani ga Abin da kuke aikatawa[28]

 A cikin wannan aya an yi amfani da kalmar Layyu wadda ke nufin canzar da shaida da kuma kalmar I’rad; voye shaida da rashin bayyanar da ita, wanda dukan yin haka laifi ne da bijire ma gaskiya, wanda zai jefa mutane ga ramin halaka.

 Babu shakka Allah ya yi umurni da abi gaskiya, a fayyace lamurra kamar yadda suke. Ya kuma yi hani daga yin qarya da kwana- kwana ko munaqisa ga abin da ya zama tilas ne a fitar da shi fili. Hadisi ya zo a cikin Buhari da Muslimu cewa; Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce “Masu cinikayya suna da zavi matuqar suna tare. Idan suka yi gaskiya sai a sanya albarka cikin cinikinsu. Idan kuwa suka yi qarya suka voye aibi sai a shafe albarkar cikinsu”.[29]

Wane mutum! Wannan fa game da ciniki kenan, ballantana ga voye Ilimi musamman irin lokacin da bidiar la’antar magabatan wannan al’umma ta bayyana. Ai ko alama, ba zai kyautu ba aji shiru kamar an aiki bawa garinsu. Bayani ya zo cikin wani hadisi cewa; “Duk sadda ‘yan bayan wannan al’umma suka la’anci magabatansu, dole ne masu ilimi su yi magana. Wanda ya voye ilimi a wannan lokaci, dai dai ya ke da wanda ya voye abin da Allah ya saukar wa Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama”.[30] Abin kulawa a nan shi ne, su fa jama’ar farko na wannan al’umma, su suka yi tsayuwar gwamin jaki a kan ganin cewa wannan addini ya samu kafuwa da yaxuwa a duniya baki xayanta. Don haka, duk wata suka da aka yi gare su ta na komawa ne kai tsaye ga addinin musulunci. Wannan kuwa shi ne ummul-haba’isin bijire ma abin da Allah ya aiko Manzonni da Annabawa da shi. Dama kuma shi ne matuqar gurin ‘yan Shi’ah; watsa gubar aqidar Shi’ancinsu a sassan duniya. Dabarun da suke yi kuwa domin su cimma nasara ga wannan baqar anniya tasu shi ne, sukan rava ne su zagayo ta bayan manyan kangararrun mutane maqiya addinin Allah. Sai su kai farmaki ga wuraren da suka fahimci cewa, musulmi suna da rauni, sai su baje kolinsu a wannan nahiya. Kaico! Abin tausayi da juyayi, shi ne irin yadda ‘yan Shi’ah ke ribantar wasu ta hanyar amfani da shubuhohi na jahilci da biyar son rai waxanda su ne manyan sinadarai ga kowane irin vata. Allah ya kiyashe mu. Allah Ta’ala Ya ce:

﴿وَٱلنَّجمِ إِذَا هَوَى١ مَا ضَلَّ صَاحِبُكُم وَمَا غَوَى٢ وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلهَوَى٣ إِن هُوَ إِلَّا وَحي يُوحَى٤﴾ النجم: ١ - ٤

Ina rantsuwa da tauraron, a lokacin da ya faku. Ma’abucinku bai vata ba. Kuma bai qetare haddi ba. Kuma ba ya yin magana daga son zuciyarsa. (maganarsa) ba ta zamo ba face wahayi ne da ake aikowa”.[31]

 A nan ka ga sai Allah ya yabi Manzonsa yabo na musamman, ta hanyar tsarkake shi daga vata da halaka. Vata kuwa a nan, tana nufin jahilci. A yayin da halaka ke nufin biyar son zuciya. Kamar yadda Allah Mabuwayi ya ce:

﴿إِنَّا عَرَضنَا ٱلأَمَانَةَ عَلَى ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ وَٱلجِبَالِ فَأَبَينَ أَن يَحمِلنَهَا وَأَشفَقنَ مِنهَا وَحَمَلَهَا ٱلإِنسَنُ إِنَّهُ كَانَ ظَلُوما جَهُولا٧٢﴾ الأحزاب: ٧٢

Kuma mutum ya xauke (amana). Lalle shi (mutum) ya kasance mai yawan zalunci, mai yawan jahilci”.[32]

 Wannan aya ta fayyace sarai cewa, azzalumi halakakke ne, a inda shi kuma jahili vatacce ne, in ba wanda Allah ya yi wa gyaxar dogo ta hanyar tuba ba.

 Na’am Wannan ba shakka shi ne halin ‘yan bidi’a waxanda suka nisanta kansu daga littafin Allah da sunnar Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata gare shi. Ba su biyar komi in ba zato ba da abin da rayukansu ke so.[33] Qungiyoyin vata a wajensu ne jahilci da zalunci suka yanke cibiya, tun ma ba mafiya lalaci daga cikinsu ba, ina nufin ‘yan Shi’ah. Abin da ya kai su ga wannan matsayi kuwa shi ne, kai wa matuqa da suka yi wajen bayyana mummunar qiyayya ga manyan masoya Allah watau Sahabbai, muhajiruna da Ansaru. Allah ya yarda da su da duk waxanda suka bibiyi hanyarsu da kyautatawa.

 Wani abin lura a nan shi ne, abu ne sananne cewa, ‘yan Shi’ah suna da qwaqqwarar hulxa da taimakekeniya a tsakanin su da kafirai da munafukai daga cikin Yahudawa da Kiristoci da Majusawa maqiya musulunci, da sauran fanxararrun qungiyoyi irinsu Nusairiyyah da Isma’iliyyah. Kuma kowa ya san cewa, sai hali ya zo daidai ake qulla abota. Ma’aunin gano wannan matsayi nasu kuwa abu ne mai sauqi. Za ka taras da su a duk lokacin da wani savani ya abku tsakanin Muminai da Kafirai suna gaugawar kai xauqi da agaji na musamman ga abokan faxan musulmi, kamar dai yadda aka sha ganin hakan a fayafayin tarihin duniya.

Sun tallafa wa maqiya musulunci na qasar Turkiyya a kan musulmin qasashen Khurasana da Iraqi da Jazira da kuma qasar Sham. Sun kai gagarumin taimako ga Kiristoci, aka yaqi Musulmi a qasar Sham da Masar da sauran qasashe, kuma hakan ta sha faruwa a lokuta daban- daban. Ai ko ka san ba zai yiwu musulmi su manta da irin wannan ta’asar ba. Da yawa-yawan ta’addancinsu ya abku ne a qarni na huxu da na bakwai, lokacin da kafiran Turkawa suka kutsa cikin garuruwan musulmi suka kashe adadi mai ximbin yawa, waxanda Allah ne kaxai masanin iyakar su. To, a wannan lokaci ‘yan Shi’ah sun taka rawa wadda babu waiwaye cikinta inda aka tursasa musulmi aka ci zarafinsu ainun, duk saboda gudummuwar shugabannin sharri na mabiya Shi’ah. wannan shi ne dalilin da ya sa ake yi musu suna da karnukan farautar Yahudawa.[34]

 1.1 Zumuntar Shi’ah da Yahudawa da Nasara

Minhajul Karamah Fi Ma’arifatul Imamah, shi ne sunan littafin da nake baka labari a fasalin da ya gabata, wanda marubucin Shi’ah ya Wallafa. Ni dai a ganina da an ba littafin sunan Minhajun Nadamah da ya fi dacewa. Yadda abin yake shi ne, kamar mutum ne mai datti, qazami, Bamaguje mabiyi shexan, amma ya rinqa lissafa kansa daga cikin tsarkakan bayin Allah. Ai ka ga wannan abu ne mai nisa. Babu shakka zuciyar da ke cike da qyamar manyan-manyan waliyan Allah ita ce zuciya mafi muni da qazancewa a cikin halittun da ke bayan qasa. Bayan Annabawan Allah kuwa babu mahalukin da darajarsa ta yi ko kusa da ta Sahabbai. Wannan shi ne dalilin da ya sa Allah ya hana a ba kowa ganima a bayansu sai masu cewa;

﴿وَٱلَّذِينَ جَاءُو مِن بَعدِهِم يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱغفِر لَنَا وَلِإِخوَنِنَا ٱلَّذِينَ سَبَقُونَا بِٱلإِيمَنِ وَلَا تَجعَل فِي قُلُوبِنَا غِلّا لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوف رَّحِيمٌ١٠﴾ الحشر: ١٠

Ya Ubangijinmi! Ka yi gafara a gare mu, da kuma ga ‘yan’uwanmu waxanda suka riga mu yin imani. Kada ka sanya wani qulli a cikin zukatanmu ga waxanda suka yi imani, Ya Ubangijinmu! Haqiqa, kai ne Mai tausayi, mai jin qai.

Duba sarai malam ka gani, Shi’anci da Yahudanci sun yi kunnen doki wajen biyar son rai. In kuwa gefen faifayewa ne da kuma kantar jahilci, tsakaninsu da kiristoci ba a san gwani ba. Wannan ita ce haqiqanin shaidar da mutane suka bayar a kansu.

 Malaman garin Kufa su suka fi kowa sani da tantance halayyar mabiya Shi’ah, saboda can ne tushenta. Bari mu ji wani malami daga cikinsu abin da yake cewa: “Duk a faxin duniya ba wanda ya fi Shi’ah sakarci. Kamar mujiya suke a duniyar tsuntsaye ko kuma jakkai a sashen dabbobi. Wallahi sun sha neman in fesa qarya a kan sayyidina Aliyu Raliyallahu Anhu wai don in qara bayyana darajarsa. Inda na yi haka ko to, da shirye suke su cika gidana da zinari da azurfa. Amma kash! Ni ba irin mai yin haka ne ba”[35]. In ji malam Sha’abi.

 Haka ne. Wani malami ma mai suna Baban Hafsa wanda aka fi sani da Ibnu Shahin[36] a cikin littafinsa mai suna Alluxfu Fis- Sunnati ruwitowa ya yi daga Imamus Sha’abi cewa: “Kashedinku da qungiyoyin bidi’a, musamman mabiya Shi’ah, waxanda suka shiga musulunci da qafar hagu; ba su shige shi saboda Allah ba, sai don huce haushi ga Musulmi. Wannan Shi ne babban dalilin da ya harzuqa sayyidina Ali har ya sa aka hura wuta aka rura ta sosai, ya ce a kama su xaya bayan xaya a rinqa jefawa a cikinta. Daga nan ya yunqura ya kai ma wasunsu xauki da hargagi, suka firgita. Suka cika wandunansu da iska, gudun fanfalaqi ya same su ba ji ba gani. Amma gwanin tsalle da nuna qwarewa cikin gudu a wannan rana Abdullahi xan Saba’i, ya tsira da rayuwarsa inda ya samu mafaka a Sabat ta qasar Iran, ya ko ci gaba da fesa gubarsa a can. Haka shi ma Abdullahi xan Yasaru da ya samu tserewa bai ci burki ba sai garin Khazar.

 Su dai Mabiya Shi’ah, rashin lafiyarsu guda ce da ta Yahudawa. Bari mu hawar da su kan teburin misali ka ga yadda abin ya ke:

1.1.2 Jadawalin Zumuntar Shi’anci Da Yahudanci

Yahudawa Sun Ce

Babu maganar Jihadi sai ranar da Dujjal ya bayyana, kuma Allah ya aiko shi da takobi daga sama.

Ba wanda ya cancanci shugabanci sai zauri’ar Annabi Dawuda Alaihis Salamu.

Suna jinkirin sallar magariba sai bayan fitowar taurari.

Suna bauxe ma alqibla wurin yin sallah.

Suna rufe idanunsu wurin ibada.

Idda ba dole ba ce ga mata a wurin su.

Sun karkatar da ma’anar littafin At- Taurah.

An wajabta salloli 50 a kansu kowane wuni.

Suna birkice sallama ga musulmi su ce, Assamu madadin Assalamu suna roqon mutuwa ga musulmi.

Sun haramta ma kansu wasu nau’oin kifaye guda biyu; Tarwaxa ba Buku.

Ba su yin shafa a kan safa.

Sun halalta ma kan su cin dukiyar kowa in ba wasu-wasu ba. Kamar yadda Allah ya labarta mana cikin Alqur’ani.

Wajen yin sujada suna yin dungure. Wato, suna aza gefen goshi.

Ba su zuwa sujada kai tsaye sai sun fara wani irin sunkuyar da kai.

Suna qiyayya da mala’ika Jibrilu Alaihis Salamu.

‘Yan Shi’ah Sun Ce

Babu maganar Jihadi sai ranar da Mahadinsu ya bayyana, kuma sai sun ji anyi shela daga sama.

Ba wanda ya cancanci shugabanci sai Ali Raliyallahu Anhu da zuriyarsa.

Suna jinkirin sallar magariba sai bayan fitowar taurari[37]

Suna bauxe ma alqibla wurin yin sallah

Suna rufe idanu wurin sallah

Idda ba dole ba ce ga mata a wurin su.

Sun karkatar da ma’anar littafin Alqur’ani.

Su ma sun ce, salloli 50 aka wajabta masu kowace rana.

Su ma dai haka xin suke yi.

Su ma ‘yan Shi’ah sun ce, duk kifaye sun yi magana da Ali in ban da waxannan biyu. Don haka ba su cin su.

Su ma ‘yan Shi’ah haka.

‘Yan Shi’ah ma suna ganin cewa, dukiyar kowa halas ce gare su in dai ba xan Shi’ah ba ne.

Su ma ‘yan Shi’ah suna yin irin wannan sujada.

Su ma ‘yan Shi’ah haka suke yi.

A wajensu mala’ika Jibrilu ya yi kure wajen kawo ma Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama manzanci maimakon Ali. Don haka su ma suna adawa da shi.

Aqidun Shi’ah ba da na Yahudawa kawai suka yi kama ba. Wasu aqidun nasu kama suke yi da na Kiristoci. Dubi auren ‘yan mishan, mine ne ba jin daxi kawai ba, tun da ko sadaki ba sa bayarwa? A gefe xaya kalli auren mutu’ar Shi’ah, ai ka ga biri ya yi kama da mutum ko?

Idan ka kalli wata fuska sai ka ga gara ma Yahudawa da Kirista a kan ‘yan Shi’ah. Domin kuwa duk Bayahuden da ka tambaya wane ne ya fi daraja a cikin mutane? Zai ce maka: “Sahabban Annabi Musa Alaihis Salamu”. Tambayi Kirista irin wannan tambaya, shi kuma zai ce maka: “Sahabban Annabi Isa Alaihis Salamu”. A yayin da idan ka tambayi xan Shi’ah, su wane ne suka fi kowa qasqanci a bayan qasa? Sai ya ce maka: “Sahabban Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama.

A lokacin da Allah mai girma da xaukaka ya ba da umurni a nema wa magabatan musulmi gafara, a lokacin su ‘yan Shi’ah ke cika bakinsu da zagi na fitar arziki da cin zarafi gare su, ba kunya ba tsoron Allah. Don mi ba za a zare takobi a nufe su ba, daga nan har ranar da Allah zai naxe qasa? Allah ya tarwatsa gungunsu ya watse haxin kansu. Kamar yadda Allah ya ce:

﴿ كُلَّمَا أَوقَدُواْ نَارا لِّلحَربِ أَطفَأَهَا ٱللَّهُ ﴾ المائدة: ٦٤

Kuma kodayaushe suka hura wata wutar yaqi, sai Allah ya bice ta”[38].

 Waxannan jawabai da aka jiyo haka su ke. Domin kuwa dimun sun yi kama da duk abin da ya sifanta su da shi.

 Sun yi fatar gurvata musulunci kamar Yadda Bulus xan Yusha’u wani basarake daga cikin Yahudawa ya rikirkita addinin Kiristanci. Duk da sallah suka yi ba ta zuwa ko ina don ba a amsarta. Bayani ya gabata cewa, Aliyu Raliyallahu Anhu sai da ya tarwatsa gungunsu har ma ya kai ga azabtar da su da wuta, lokacin da su Abdullahi xan Saba’i da Abubakar Al-Kurus suka yi gudun da muka faxa a xazu. Su ne kuma dai waxanda suka faifaye har suka Allantar da Aliyu wanda har ta kai yake cewa, a waqe:

Yayin da har lamarin wajensu ya kumbura

Sai nayyi gwami nak kirawo Qambara

Yad dinga jejjefa su xai-xai-xai ciki

Domin musulmi dagga nan su yi hattara

 1.2 Mafarin Sunan ‘Yan Shi’ah “Rafilah”

Sanannen suna ne ga ‘yan Shi’ah da aka kira su da shi “Rafilah”. Asalin sunan kuwa shi ne, saboda a farkon lamarinsu sun kasance masu biyyaya ga imaminsu Zaidu xan Aliyu xan Husaini, amma daga baya sai suka wancakalar da shi suka yi watsi da lamarinsa. Wannan kuwa ya faru ne a lokacin mulkin Hisham wajejan shekara ta 121 bayan hijira. Kalmar Raflu mai ma’anar wancakalarwa ita ce ta bi su har aka san su da suna ‘yan Shi’ah.

Farkon al’amarin Shi’ah ta rabu ne zuwa gida biyu: Rafilah da kuma Zaidiyyawa, a lokacin yunqurin juyin mulkin da suka ingiza Zaidu xan Aliyu xan Husaini ya yi, a qarshe kuma suka dare masa.

Tarihin wannan suna na Rafilah ya samo asali ne bayan da suka tambayi Zaidu xin matsayin sayyidina Abubakar da Umar a wurinsa. Shi kuma sai ya faxi kyakkyawar magana game da su. Daga nan sai suka bijire masa suka ba shi baya don su nuna masa rashin jin daxinsu game da yabon da ya yi wa manyan Sahabban. A nan ne sai ya ce; Rafaltumu ni? Kun watsar da ni? Sai sunan kuwa na Rafila ya bi su har lahira. Su kuwa sauran waxanda suka zauna tare da shi sai mutane suka ba su sunan Zaidiyyawa saboda jivintar lamarinsa da suka yi. Har kwanan gobe kuwa Zaidiyyawa na makokin kashe shi a daidai itaciyar da aka tsire shi, sun ma mayar da wurin wajen yin bauta safe da marece.

Da haka suka kafu a matsayin qungiya mai aqidodi daban-daban da suka haxa da; rabke salloli a yi su lokaci guda har koyaushe ba tare da lalura ba. Ba su yin sallah sai a lokuta guda uku,[39] wannan kuwa duk saboda kamanta kansu da Yahudawa.

 A cewarsu, sakin aure ba ta yadda zai tabbata sai an kafa shaidu. Kuma duk wanda ba xaya daga cikinsu ba najasa ne. Ba su cin yankan kowa sai nasu. Sun ce duk da ruwan da musulmi ya yi amfani da su, ya zama najasa. Idan kuma ya ci abinci a cikin wani kwano ko akushi dole ne sai an wanke kafin xan Shi’ah ya ci a cikinsa. Duk sun xauko waxannan xabi’oi da aqidoji daga Yahudawa, musamman Samirawa, qungiyar Yahudawa mafi muni. Kuma a kan wannan dalili ne da yawan mutane ke kiran mabiya Shi’ah da sunan Samirawa. Manufa a nan ita ce, kamar yadda Samirawa suka bar addinin Yahudanci haka Shi’ah suka bar addinin musulunci.

 Sun qware ga munafucci, wato Taqiyya kenan. Ga kuma sharri kamar Yahudawan asali.

 1.3 Wautar ‘Yan Shi’ah

 Akwai Labarun wauta da soki burutsu tattare da Shi’ah. Kaxan daga cikinsu su ne; Akwai wata rijiya wadda Zaidu bn Aliyu xan Husaini ya gina, shi ne aka samu wani sashe na mabiya suka haramta ma kansu shan ruwan rijiyar don qiyayya ga Zaidu, sun mance da cewa Annanbi Sallallahu Alaihi Wasallama da kansa tare da Sahhabbansa Allah ya yarda da su, sun kasance suna shan ruwan rijiyoyin da kafirai suka gina ballantana rijiyar da wani musulmi ya gina. Kuma akwai wasu daga cikinsu da ba su cin taura, wai don kawai a qasar Sham ake samun ta inda magoya bayan sayyidina Mu’awiyah suka fi yawa. Alhali kuwa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da kansa yana cin abincin da aka shigo da shi daga qasashen qetare. Ko da kuwa qasashen kafirai ne. Kamar yadda yake sanya tufafin da asalinsu kafirai ne suka xunka su.

 Haka kuma ‘yan Shi’a sukan canfa lamba goma, suna matuqar qyamar ta, ta yadda ko gida za su gina ba za su yarda yawan xakunansa ya zamo goma ba. To, ko a masallatansu ma, ba su yin ginshiqai guda goma. Dalili kuwa, shi ne tsananin qyamar da suke yi wa Sahabbai guda goma da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masu bushara da aljanna.

 Dubi hadisin da ya zo cikin Sahihu Muslim riwayar Jabir Allah ya yarda da shi, cewa watarana wani hadimin Haxibu xan Abu Balta’ata ya ce; “Ya Manzon Allah! na rantse da Allah sai Haxibu ya shiga wuta”. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa, ka sha qarya. Saboda Haxibu ya halarci yaqin Badar da Hudaibiyya.[40]

 To, me ya yi zafi wanda ya sa mabiya Shi’ah suke adawa da waxannan manyan bayin Allah, in ba kaxan daga cikinsu ba? Yanzu Mu ma jingine zancen Sahabbai a gefe, bari mu ba da wani misali, mu qaddara cewa yanzu haka akwai wasu gogaggun qafirai guda goma a duniyarmu ta yau, me zai zama dalilin camfa adadin yawansu har a ce ana qyamar amfani da shi idan ba tsagwaron jahilci ba? Ai Allah ya ambaci cewa:

﴿وَكَانَ فِي ٱلمَدِينَةِ تِسعَةُ رَهط يُفسِدُونَ فِي ٱلأَرضِ وَلَا يُصلِحُونَ٤٨﴾ النمل: ٤٨

Kuma waxansu jam’a (Su) tara sun kasance a cikin birnin, suna yin varna kuma ba su kyautatawa.[41]

Shi kenan sai ya zama dole a camfa lamba tara (9), a qaurace ma yin amfani da duk wani abu da ke da dangantaka da ita, hujja da cewa tarihi ya labarta samuwar wasu ‘yan daba guda tara masu varna a cikin birni a wani lokaci da ya gabata? Idan kuwa har wannan ba aikin hankali ne ba, to ya za a yi qaurace wa lamba goma (10) ya zama aikin hankali? Ai ita lamba goma xin ma, Allah ya faxe ta a wurare da yawa a cikin Alqur’ani Mai girma kuma ta fuska kyakkyawa. Kamar in da Allah ya ce;

﴿ فَمَن لَّم يَجِد فَصِيَامُ ثَلَثَةِ أَيَّام فِي ٱلحَجِّ وَسَبعَةٍ إِذَا رَجَعتُم تِلكَ عَشَرَة كَامِلَة ﴾

البقرة: ١٩٦

Sa’an nan wanda bai samu ba, sai azumin yini uku a cikin hajji da bakwai idan kun koma, sun zama goma kenan cikakku[42].

 Wannan game da hukunce-hukuncen hajji kenan. Game da lamarin Annabi Musa Alaihis Salamu kuwa, sai Allah ya ce;

﴿وَوَعَدنَا مُوسَى ثَلَثِينَ لَيلَة وَأَتمَمنَهَا بِعَشر فَتَمَّ مِيقَتُ رَبِّهِ أَربَعِينَ لَيلَة وَقَالَ مُوسَى لِأَخِيهِ هَرُونَ ٱخلُفنِي فِي قَومِي وَأَصلِح وَلَا تَتَّبِع سَبِيلَ ٱلمُفسِدِينَ١٤٢﴾ الأعراف: ١٤٢

Kuma muka yi wa’adi ga Musa da darare talatin, kuma muka cika su da wasu goma, sai miqatin Ubangijinsa ya cika dare arba’in.[43]

 Kai! Ba ma fa sai an tafi da nisa ba, duba farkon Walfajri ka ga abin da Allah ya ce:

﴿وَٱلفَجرِ١ وَلَيَالٍ عَشر٢﴾ الفجر: ١ - ٢

Ina rantsuwa da alfijir da darare goma (na farkon watan Muharram).

A cikin Sahihul Buhari, Hadisi ya tabbatar da cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance yana I’itikafi cikin kwanaki goma na qarshen Ramalana har ranar da ya bar duniya”.[44]

 Game da daren Lailatul qadari kuwa, ga abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ku Lalube ta cikin ranaku goma na qarshen Ramalana”.[45]

 Ga kuma wani hadisin da ya ce: “Babu kwanakin da aikin alheri ya fi soyuwa a wurin Allah cikinsu fiye da kwanaki goma (yana nufin na farkon watan Muharram).[46]

 Waxannan bayanai da Makamantansu suna da yawan da sun fi qarfin qididdiga.

 Wani halin kwan-gaba-kwan-baya da bankaurar mabiya Shi’ah shi ne, lale marhabin da suke yi da lamba tara (9) saboda ximauta da makanta har sun mance da cewa cikin waxancan Sahabbai goma da ba su son a ce an yi wa bushara da aljanna, guda tara ne suke qyama. Ga shi kuma lamba tara (9) ta zo ne a matsayin zargi, da bayanin adadin ‘yan daba kamar yadda ya gabata. To, ya kenan?

 Kada a manta cewa, sun qaurace ma sunan Abubakar da Umar da Usmanu kuma ba su qaunar duk wani mai sha’awar su, saboda tsananin qiyayya da masu su na asali. Alhali kuwa ko da a ce waxannan mutane sun zama ‘yan gaba-gaba ga ayyukan kafirci a duniya, ba wai gaba-gaba a wajen taimakon Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba, wannan ba ya zama dalilin qaurace ma sunayensu. Ai a cikin Sahabbai akwai mai suna Walidu wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ma addu’a cewa: “Ya Allah ka kuvutar da Walidu”.[47] Ko ka manta da Walidu xan Mugirata na daga cikin manya manyan masu adawa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, wanda har shaguve Alqur’ani ya yi game da shi a Suratul Muddassir?

 Akwai mai suna Amiru a cikin Sahabbai kamar yadda akwai mai irin wannan suna cikin mushrikai. Haka ma Khalidu da Hishamu da Uqbatu, kai! Har da sunan Aliyu akwai masu irin sa a cikin kafirai, kamar Aliyu xan Umayyata xan Khalafu, kafiri, gamji sai sara.

 Tambaya a nan ita ce, wa ya tava cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci Sahabbai da su qaurace ma waxannan sunaye, wai saboda dangantakarsu da wani kafiri? Idan kuwa babu ita ce amsar, to, ina dalilin qyama da qaurace ma sunayen manyan Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama?

 A cewarsu wai, Sahabban munafukai ne. Shi ne dalilin da ya sa suke qyamar su. Assha! Magana ta yi muni. Amma kada ku manta da matsayin Aliyu Allah ya yarda da shi a wajenku. Ba kun ce shi ma’asumi ba ne wanda ba ya kure gaba xaya? To, ai ba a ga ya nuna qyamarsa ga xaya daga cikin waxannan manyan waliyai ba. Hasali ma, ya girmama su. Kai! Har ma shi da kansa ya sanya wa wasu daga cikin ‘ya’yansa sunayensu.

Gaskiyar lamari dai, musulunci bai hana amfani da sunan duk da bai sava ma Shari’a ba, ko da ko an ambaci wani kafiri da shi. Kuma kangare ma wannan tafarki ba komi ba ne face fito na fito da shari’ar Musulunci. Sunayen Aliyu da Ja’afaru da Hasan da Husaini da suke yawan sa wa, ai ba tabbaci ne cewa duk masu waxannan suna masoya ne ga waxanda ke da sunayen na asali ba.

 A wata Sabuwa kuma suna da wata xabi’ar ta wauta, inda suke sammako da maraici a gindin wani dutse mai kogo da ke garin Samarrah. Su kan yi tamatela suna jiran bayyanar Mahadinsu wanda suke da aqidar yana cikin dutsen. Kuma sun tanadar masa ingarman doki taka-hau don da ya bayyana ya garzaya da su zuwa aljannar duniya. Sun girke wani mutum a daidai wurin mai qatuwar murya yana qwalla kira a kai-a kai yana cewa fito maza fito maza Ya Maulana! Sannan wani babban abin da ke xaure kai shi ne yadda suke zagaye wannan bagire xauke da makamai tsoron wai kada a hargage su. Sannan sai su ayyana mutum guda wanda jiddadun za a same shi a tsaye a wannan wuri riqe da makami duk da Sallah babu ruwansa da ita don kada hankalinsa ya xauku har Mahadi ya vullo ba da saninsa ba.

A lokacin da duk suka yi ma wannan wuri nisa kuwa, sai su rinqa fuskantar dabra da wajen suna qwala ihu da kiraye-kiraye cikin gaugawa, wanda babu buqatar yin hakan da a ce gaskiya ne wannan mahadin yana raye. Kuma har Allah ya umurce shi da fitowa. To, ka ga daman ai Allah Subhanahu WaTa’ala ya ce:

﴿ ذَلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُم لَهُ ٱلمُلكُ وَٱلَّذِينَ تَدعُونَ مِن دُونِهِ مَا يَملِكُونَ مِن قِطمِيرٍ١٣﴾ فاطر: ١٣

Wannan Shi ne Allah, Ubangijinku gare shi Mulki yake, kuma waxannan da kuke kira waninsa ba su mallakar ko fatar gurtsun dabino. Idan kun kira su ba za su ji kiranku ba, kuma ko sun jiya, ba za su karva muku. Kuma a Ranar qiyama za su kafirce wa shirkinku, kuma babu Mai ba ka labari kamar wanda ya sani.[48]

 Wannan ya nuna gara ma ‘yan bautar gumaka, waxanda duk da rashin ji da ganinsa amma ga shi gabansu suna kallo, savanin masu zaman jiran gawon shanu.

 Idan wani xan Shi’ah ya bugi qirjin cewa shi, babu mai xauke shi daga ra’ayinsa na yarda da samuwar Mahadin nasu, to, ai maganarsa ba ta da banbanci da ta ‘yan bautar gumaka da suke cewa, babu mai raba su da ra’ayinsu na cewa tabbas gumukansu za su cece su wurin Allah. Kuma ha kanshi ne dalilin da ya sa suka dage kai da fata suna bauta masu. Da waxannan da waxancan duk ja buge man, saboda jirgin halaka guda ya xauko su, zai kuma sauka da su tashar wahala.

Abin la’akari a nan shi ne, duk da wanda ya riqi mala’iku da Annabawa matsayin ababen bauta bai fita daga zargi da fushin Allah ba, balle wanda ya ciccivi wani mahalukin da ba ma ko xuriyarsa. Duba min gaba ka gani wai makaho ya so tsegumi.

Bugu da qari, har karvar umurni da hani suke yi daga wurin wannan hadarin kaka da Allah bai halitta ba ta hannun malumansu. Alhalin ko Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

﴿ٱتَّخَذُواْ أَحبَارَهُم وَرُهبَنَهُم أَربَابا مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَٱلمَسِيحَ ٱبنَ مَريَمَ وَمَا أُمِرُواْ إِلَّا لِيَعبُدُواْ إِلَها وَحِدا لَّا إِلَهَ إِلَّا هُوَ سُبحَنَهُ عَمَّا يُشرِكُونَ٣١﴾ التوبة: ٣١

Sun riqi Malamansu (Yahudawa) da Ruhubanawansu (Nasara) ababen bauta, baicin Allah, Kuma sun riqi Masihu xan Maryama (haka). Alhalin ba a umurce su ba face su bauta Ubangiji guda. Babu abin bauta wa face shi. Tsarkinsa ya tabbata daga abin da suke yin Shirka da shi.[49]

 Kuma hadisi ya zo a cikin Tirmizi da waninsa, daga Adiyyu xan Hatimu Allah ya yarda da shi ya ce: “Ya Manzon Allah! Ba fa bauta musu su ke yi ba”. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ba suna halalta musu haram ba, kuma suna haramta masu halal, su yi xa’a gare su? To, bautar da suke yi masu kenan”.

 A nan idan ka dubi lamarin ‘yan Shi’ah za ka taras da su suna jingina hukunce-hukuncen halattawa da haramtawa ga Imaminsu da suka kira Mahadi, wanda bayani ya gabata cewa, sam babu samuwarsa kuma ko da abin da suka jingina ma Imamin ya ci karo da Alqur’ani da sunna da ijma’in malamai su ba ruwansu. Wautarsu ba ta tsaya a nan ba, ta kai su ga liqa ta ga Imamin nasu duk wata matsala da suka qirqira maras tushe. Qarshe kuma su ce, tafi maganar kowa.

 Za a same su suna hanzari wajen misalta waxanda suke qiyayya da su da dabbobi. Wani lokacin ma sukan xauki matakin gana wa dabbar azaba, wai don xebe ta kaicin maqiyansu. Misali, sukan kamo akuya sai su xaure ta, su rinqa tsigar gashinta qarfi da yaji, wai sun ci zarafin Aisha. Kaico!

Wani lokaci kuma sukan samo salka su tsatstsageta da kakide (dasqararren mai). Daga nan sai su zaro wuqa su tsaga cikin salkar, sai kakiden ya bultso sai su rinqa riganganto wajen shan man, suna yi suna Santi, suna cewa, wai jinin Umar Raliyallahu Anhu ne suke sha. Ba wannan kaxai ba, sukan bushi iska a wani karon, su kamo jakuna biyu, su raxa wa xaya sunan Abubakar, xayan kuma sunan Umar, su ce, me za su yi in ba lallasa musu azabar duniya ba?

Wannan ya sa watarana da wani sarki ya lura da irin wannan xanyen aiki nasu ya sa aka ciyo kwalarsu, aka tungume su aka xaure ya rinqa gwada masu nau’ukan azaba, a cikin izgili, yana cewa Abubakar da Umar ne ya ke son sai ya ga baya gare su.

 Wasu ‘yan Shi’ah kuwa karnuka suke kamowa su basu sunayen halifofin can guda biyu da muka ambata. Suna kiran su suna zagi da tsinuwa suna xebe musu albarka. Wani daga cikinsu kuwa ko karensa ba ya son a jingina ma sunayen waxannan bayin Allah. Wanda ko duk ya kuskura ya yi haka, to, faxa ya gama qulluwa a tsakankinsu, ya rinqa kururuwa da kumfar baki kenan, wai don mi ake ambatar karensa da sunan ‘yan wuta?!.

 Akwai wani gogaggen kafiri wanda ya kashe Sarkin Musulmi Umaru xan Haxxabi har lahira, ana ce masa, Abu Lu’uluata, Bamajuse. Su kuwa wasu ‘yan Shi’ah shi suke matuqar girmamawa saboda a ganinsu ya yi namijin qwazo da ya kamata a so shi, a kuma jinjina masa saboda shi.

Harwayau, daga cikinsu akwai masu zuwa maqarbarta su zavi wasu qaburburan da ko kakanninsu ba su san waxanda ke kwance a cikinsu ba. Amma duk da haka, sai su zagaye su, su gina dogayen hasumiyoyi a kansu, kuma su rinqa kai musu ziyara lokaci-lokaci. Kai! Wani lokaci ma har da shirya bukukuwa a wurin, da sunan wai qaburburan Ahlul-baiti ne suke girmamawa. Wataqila ma qaburburan wasu manyan maqiya musulunci ne, amma da yake sun ximauce, sun makance gane ha kan zai wuyata gare su.

 Bari a ba da wani gajeren bayani domin masu hankali. Idan aka yi la’akari da waccan aika-aikar mabiya Shi’ah ta azabtar da wasu dabbobi da sunan waxannan Sahabbai sai a ga iyakar wauta sun yi ta. Xauki misalin abin da yake qunshe a cikin kundin tarihin duniya, in da aka zayyana sunayen wasu qeqasassun kafirai irin su Fir’auna da Abu Lahabi da Abu jahali wawa, yanzu yana yiwuwa saboda son musuluncinmu da qyamar matsayinsu, sai mu kamo wasu dabbobi bayin Allah mu ayyana ma kowace dabba sunan xaya daga cikinsu, sannan mu rinqa koxa masu azaba?

A tsarin Shari’ar musulunci, duk da gawar kafiri ba a yarda da tozarta ta ba bayan an kashe shi. Saboda muradin musulunci shi ne ya dakatar da cutar kafirin, kuma ta hanyar kashe shi wannan buqatar ta biya. A kan yi masa haka ne kawai in ya kasance shi ya fara yi wa wani musulmi haka.

An samu ingantaccen hadisi cikin Sahihu Muslim daga Buraidah Allah ya yarda da shi ya ce: “A duk lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zai tura rundunar yaqi yakan umurci shugaban rundunar da cewa, ya ji tsoron Allah a karan kansa da kuma jama’arsa. Daga nan kuma ya qara da cewa, ku yi yaqi saboda Allah, ku yaqi wanda duk ya kafirce ma Allah, kada ku ci gululi, kuma kada kuyi yaudara. Sannan ku kuma nisanci Musla, wato, wulaqanta gawa. Kada kuma ku kashe qananan yara.[50]

A Wani bayani mai kama da wannan, yazo a cikin littafan Sunan cewa, Manzon Allah sallahu alaihi wasallam ya kasance yana horon mutane da yin sadaqa, kuma yana tsawatar su game da yin Musula.

 A nan, ya bayyana a fili cewa yin Musula ga kafirai bayan mutuwarsu, wulaqanci ne ga halittar Allah. Kuma Shari’a ba ta goyi bayan aiwatar da haka ba, tattare da kasancewarsa kafiri. Kenan su waxancan manyan Sahabbai Allah ya yarda da su, waxanda ‘yan-sha-biyu ke aibatawa tare da nuna qiyayya gare su, ko da a ce tun farko su ba musulmi ba ne, to, wannan ba zai zama lasisin wulaqantar da gawarsu ba ta hanyar duka ko tsage sashen jiki ko tsigar gashin gawar, balle maganar azabtar da wata dabba da sunansu. Wannan bai ko taso ba tattare da cewa azabtarwar ba za ta kai ga jikin Sahabban ba.

Daga cikin shiriritarsu, suna shirya bukukuwan baqin ciki da koke- koken tuna rasuwar malamansu, da wasu mutane. Tabbas wannan na nuna cewa sun jahilci haramcin kukan mutuwa da bukukuwan makokin a addinin musulunci. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wanda ya mari fuska, ya keci wuyan riga, ya yi hargowar jahiliyya, to ba shi tare da mu”. [51]A wani hadisin kuwa cewa ya yi “Na barrantar da kaina daga mace mai aske kanta da mai hargowa a lokacin faruwar wata musiba, da kuma mace mai kece tufafinta” [52]. A wani wurin kuma ya ce: "Ana azabtar da mamaci saboda kukan da ake fasa masa.” [53]

 Za ka ga ‘yan Shi’ah sun fi kowa aikata ayyukan jahiliyyah, kamar marin fuska, da keta tufafi, da iface-iface. Duka wai don tuna wata tsohuwar musiba. Kuma baka tava jin sun yi wa wani daga cikin bayin Allah da aka yi wa kisan zalunci daga cikin Annabawa da Waliyyai ko qyasham ba. Abin da yake nuna maka cewa, ko Husainin ma dai a lava ga sabara ne a harbi barewa. In ba haka ba, me ya sa ko mahaifin nasa ba sa yi masa kuka? Ashe ba kisan sharri ne shi ma aka yi masa ba? Ba sai mun tambaye su ba game da Usmanu xan Affana wanda aka yi wa kisan gila yana a matsayin halifan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kuma cikin birnin Manzo yana rungume da Alqur’ani ba. Ba za mu tambaye su don me ba su yi masa kuka ba, domin mun riga mun san matsayinsu a kansa. Amma dai duk mai hankali ya gani a tarihi irin musibar da ta cimma musulmi a sakamakon kisan Usman, ba a tava ganin aukuwar irin ta ba ko a lokacin da aka kashe Husaini. Amma waxannan musibun sun wuce. To, mine ne na tashintashina?

 Abin da ‘yan Shi’ah ke yi xin nan kuwa babban dalili ne a kan wautarsu. Domin babu wani mai kiran kansa musulmi da ke yin irin wannan xabi’a in ba su ba. Wautarsu ba a nan ta tsaya ba. Yanzu haka dai wasu daga cikinsu ba su qona wata itaciya da ake kiya Xarfa’u wai don sun ji an ce jinin Husaini ya zuba ga reta! To, in banda wauta wa ya ce ba a qona itace idan wani jini ya zuba a kansa? Kuma ma shin wannan iccen shi ne yake har yanzu a cikin dazuzzuka? Irin waxannan abubuwa na wauta a cikinsu suna da yawa. Kuma tun farkon vullar Shi’ah a zamanin Tabi’ai ake hikaito irin waxannan labaran game da su, ga su ko har yau ba su bari ba.

 Don mu yi masu adalci, dole ne a nan mu faxi cewa, ba dukkan ayyukan wauta da ‘yan Shi’ah ke yi suka kevanta da ‘yan-sha-biyu ba. A’a, wasunsu an fi sanin su ne a wajen sauran qungiyoyin Shi’ah, musamman dai Gulatu. Haka kuma wasu abubuwan da jahilan ‘yan Shi’ah ke qudurtawa, malamansu ba su fatawa da su, kamar haramta cin naman raqumi, da kuma cewa sharaxi ne sai mace ta yarda da saki kafin ya tabbata.

1.4 Shaidar Malamai a Kan ‘Yan Shi’ah

A baya an ambaci wani littafi mai suna Minhajul-Karamati. Amma a haqiqanin gaskiya kamata ya yi sunan nasa ya kasance Minhajun- Nadamati. Domin kuwa nadama littafin ya qunsa ba karama ba. A cikin rubutun, marubucin ya bi sawun malamansa ne a duniyar Shi’ah irin su Mufid da alamjiransa kamar Xusi da ire-irensa.

 Irin waxannan rubuce-rubuce na ‘yan-sha-biyu ba abin da ke cikinsu sai qarya, irin wadda ke nuna su a fili, a matsayin manyan-manyan jahilai a sararin Subhana. Taqama kawai suke yi da harkar ilimi da nazari, amma abin ba haka yake ba. A haqiqa, idan kana neman mutane marasa kan gado, ga kuma qarfin hali a fagen qin ba nazari haqqinsa, to, da zarar ka yi kicivis da xayansu, to, haqarka ta cimma ruwa. Duk abin da suka dogara a kansa za ka taras ruvavve ne, da ya kamata a saka kwandon shara.

 Malamansu naji da faxi, ba su da hanya qwaqqwara ta karvar riwaya sai ga azurakan mutane irin su: Abu Mikhnaf Luxu xan Yahya da su Kalbi, waxanda ma’abuta ilimi suka bada shedar cewa, shahararrun maqaryata ne su. Masana sirrin riwayoyin hadisi kuma, sun ba da shaidar cewa, ‘yan shi’a na daga cikin manyan maqaryata a duniya.

Malam Razi Baban Hatim ya riwaito daga Malik wanda aka tambaya game da matsayin ‘yan Shi’ah sai ya ce: “Ba a shiga batun su, kashedinka da karvar maganarsu, don gwanayen qarya ne su”. Baban Hatim kuma ya riwaito daga Imamus Shafi’i cewa: “Ban tava ganin maqaryatan mutane irin ‘yan Shi’ah ba”. Shi kuwa mashahurin malamin nan Yazidu xan Haruna cewa ya yi: “Ana iya karvar riwayar kowane xan bidi’a idan ba ya tallar ta, amma banda ‘yan Shi’ah, saboda maqaryata ne”.

Haka shi ma Malam Shariku, alqalin Kufa, wanda ya zauna da su, ya kuma san su sarai, kai, yana ma cikin almajiran sayyidina Ali ga shaidar da ya bayar a kansu: “Ana iya karvar ilimi a wajen kowa banda ‘yan Shi’ah. Saboda sun iya qera hadisan qarya, kuma sun xauki yin ha kan wata hanya ta shiga Aljanna”.

 Haka kuma Malam Sulaimanu xan Mahrana wanda aka fi sani da A’amash yana cewa: “Qarya a wajen ‘yan Shi’ah ba bakin komai take ba. Babu mamaki ka ji su suna yaxa cewa sun kama wani malami na Allah da wata, saboda tsabar qazafi”.

 Waxannan bayanai babu za’ida a cikinsu. Duba su a cikin Al –Ibanatul–Kubra na Ibnu Baxxata. Shi ma Abul–Qasim Al-Xabari ya riwaito cewa Imamus-Shafi’i ya ce: “Ban ga waxanda suka zarce ‘yan Shi’ah iya qarya ba a duk cikin qungiyoyin bidi’a baki xaya”.

Saqon da ake son a iyar a nan shi ne, malamai na duniya kaf sun fayyace cewa, ‘yan Shi’a su ne limaman maqaryata. Kuma har tinqaho suke yi da wannan matsayi. Suna cewa, mu addininmu duk taqiyyah ne. suna nufin halalta wa kansu fesa qarya a duk sadda suka ga dama. Wannan kuwa ba wani abin mamaki ba ne ga wanda ya san asalinsu.

 Tattare da haka kuma sai ka ga suna zungurar magabatan wannan al'umma da cewa wai, gaba xaya sun yi ridda; sun bar lemar Musulunci.

Da 'yan Shi’ah suna da ganewa sun fi kowa cancantar waxannan sifoffin da suke jingina wa zavavvin bayin Allah. Saboda a duk lokacin da mutum ya tashi neman waxanda suke ridda da munafucci da zarar ya ci karo da gungun 'yan Shi’ah haqarsa ta cimma ruwa. Idan kuma a na son gano gaskiyar wannan zance, mutum ya yi nazari, game da rassan Shi’ah irinsu Galiyyah, da Nusairiyyah da Isma'iliyah. Duk wanda ya leqa ciki da wajensu, zai ga abin mamaki, kuma cikinsa zai xuri ruwa, ya juyo a firgice saboda gigita da tsoro game da zurfin tavarvarewar lamarinsu.

 A sashen hukunce-hukuncen shari’ah ‘yan Shi’ah suna dogara ne kacokan ga riwayoyi waxanda aka ce an naqalto su ne daga Ahlulbaiti duk da yake mafi yawan riwayoyin na qarya ne. Su kuwa ba su iya tantancewa tsakanin ingantaccen Hadisi daga mai rauni ba. Idan ma an saki kari cewa, Hadisan da ake riwaito masu ingantattu ne, to, ba su kai ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Amma sai suka gina wasu harsasai guda uku na shirme don su tabbatar da dacewar su karvi waxannan riwayoyin. Waxannan harsasan sun haxa da; cewa, kowanne daga cikin Ahlulbaiti ma'asumi ne; yana kafaxa-da-kafaxa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Na biyu kuma wai, duk abin da zai faxi tsararre ne. Na uku kuma duk abin da Ahlulbaiti suka yi ijma'i a kansa ya zama hujja. Kuma faxar xayansu ba ta kasancewa sai in sun yi ijma’i akan abu.

 Waxannan abubuwa su ne tubalan da suka gina karvar riwayoyinsu a kai. Idan aka lura da kyau, su, ba su xauki Alqur’ani mai girma da muhimmanci ba, balle ya zama tushen da suke dogara a kansa. Haka ma Hadisi, to, balle kuma ijma'i ko qiyasi.

Maganar hankali da qiyasi a wurin ‘yan Shi’ah yana ta'allaqa ne ga rubuce-rubucen Mu'utazilawa waxanda a wani gefen sun xara 'yan Shi’ah hankali. Abin da ke nuna maka haka, shi ne, mu’utazilawa basu tava yin suka ga halifancin Abubakar da Umar da Usmanu Allah ya yarda da su ba. Magabatansu suna fifita Abubakar da Umar a kan sauran Sahabbai. Su kuwa 'yan bayansu sun kame baki ba su ce komai ba. Amma an samu kaxan da suka fifita Aliyu Raliyallahu Anhu a kan sauran Sahabbai Raliyallahu Anhu a nan ne ra'ayinsu ya zo xaya ba banbanci da na Zaidiyyah tare da cewa ba su yi ja-in-ja ga halifancin waxanda suka gabaci Aliyu xin ba. Harwayau wani sashe na Mu'tazilawa sun yi qawance da Zaidiyyah a gefen maganar Adalci da Imamah da fifita Ali a kan Usman.

 1.5 Wai Imamah Ita Ce Tushen Addini!

 ‘Yan-sha-biyu sun tafi a kan cewa, idan ana magana game da tushe da asalin addini, to, shugabanci na gaba ga komai. Mai littafin da muke magana a kansa ya ce, muhimmancin littafin nasa yana da girma saboda yana qunshe da bayanin manyan mas'aloli waxanda suka shafi hukunce-hukuncen addini da kuma sha'anin shugabanci, wanda ta hanyarsa ake kai wa ga daraja maxaukakiya don kasancewar sa xaya daga rukunan Imanin da ake samun shiga Aljanna da tsira daga dukan fushin Allah. A kan haka ne ma a cewarsa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wanda duk mutuwa ta riske shi ba a qarqashin wani shugaba ba, to, ya yi mutuwar jahiliyyah”.

 Marubucin ya nemi kusanci da rubuta littafin nasa ne zuwa ga wanda ya kira shi Sarkin Sarakuna Ulijayo Khudabandah, bayan ya yi masa yabo wanda ya wuce iyaka. Sannan ya sa masa suna "Minhajul Karamati Fi Ma'arifatil Imamati". Ya kuma yi masa tsarin fasali-fasali kamar haka:

·    Fasali na Xaya: Bayanin Mazhabobi game da wannan mas’ala.

·    Fasali na Biyu: Wajibi ne abi ra'ayin Shi’ah ‘yan-sha-biyuh ga wannan mas'ala.

·    Fasali na Uku: Dalilai masu tabbatar da shugabancin Aliyu Raliyallahu Anhu bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

·    Fasali na Huxu: Bayani a kan Imamai goma sha biyu.

·    Fasali na biyar: Kakkausan suka game da shugabancin Abubakar da Umar da Usman Raliyallahu Anhum.

Tun a karon farko maganarsa cewa, shugabanci shi ne tushe, kuma shi ne mafi girman mas'ala cikin lamurran addini a wajen Musulmi, wannan zancen banza ne. Kuma yarda da hakan kafirci ne. Domin yin Imani da Allah da Manzonsa na gaba ga sha’anin shugabanci. Wannan shi ne abin da Malaman Shi’a da kansu suka yi ijma'i a kansa balantana Malaman Sunnah. Wannan kuma abu ne da ya zama tilas kowa ya sani. Babban Misali shi ne Kalmar Shahada wadda ita ce babbar qofar shiga musulunci. Kuma a kanta ne aka yi xauki ba daxin duk da ya gudana a tsakanin musulmi da waxanda ba musulmi ba.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “An umurce ni da in yaqi mutane har sai sun sheda babu wanda ya cancanci bauta sai Allah. Su kuma shaida cewa, ni Manzon Allah ne. Su kuma tsayar da sallah, su ba da zakkah. Idan suka yi haka, sun kare jinainansu da dukiyoyinsu sai da dalili.

Haka kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce:

﴿فَإِذَا ٱنسَلَخَ ٱلأَشهُرُ ٱلحُرُمُ فَٱقتُلُواْ ٱلمُشرِكِينَ حَيثُ وَجَدتُّمُوهُم وَخُذُوهُم وَٱحصُرُوهُم وَٱقعُدُواْ لَهُم كُلَّ مَرصَد فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوةَ فَخَلُّواْ سَبِيلَهُم إِنَّ ٱللَّهَ غَفُور رَّحِيم٥﴾ التوبة: ٥

Kuma idan watanni masu alfarma suka shige to, ku yaqi Mushrikai inda duk kuka same su, kuma ku kama su ku zaune musu dukkan madakata. To, idan sun tuba, kuma suka tsayar da Sallah, kuma suka bayar da zakka, to, ku sakar musu da hanyarsu. Haqiqa, Allah mai gafara ne, mai jinqai. Suratut Taubah: 5

Kuma a lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya naxa Aliyu Raliyallahu Anhu a matsayin kwamanda zuwa Haibara, farkon abin da ya umurce shi da shi, shi ne ya fara kiran mutane zuwa ga Imani da Allah da Manzonsa. Ka ga a nan bai ce masa ya kira su ga imani da shugabanci ba. Sa'annan a duk lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya samu rinjaye a kan wasu kafirai, farkon abin da yake shimfixa masu shi ne Imani da Allah da Manzonsa.Wannan ita ce hanyar kiyaye alfarmar jini da dukiya. Wannan ya zo daidai da faxar Allah Maxaukakin Sarki:

 ﴿فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوةَ فَإِخوَنُكُم فِي ٱلدِّينِ وَنُفَصِّلُ ٱلأيَتِ لِقَوم يَعلَمُونَ١١﴾ التوبة: ١١

Sa'anan idan sun tuba kuma suka tsayar da Sallah, kuma suka bayar da zakka, to ‘yan’uwanku ne a cikin addini. Suratut Taubah: 11

 Dubi yadda Allah a nan ya ambace su a matsayin ‘yan’uwa a addini dalili da tubar da suka yi. Kuma a duk lokacin da wasu suka rungumi musulunci a hannun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ba tare da wata-wata ba yakan karve su a cikin farin ciki hannu biyu-biyu ba tare da an tsaya bincike, ko nuna masu wani matsayi ba game da lamarin shugabanci. Bugu da qari, babu ko samatar samun wani Hadisi ko bayani wanda ke nuna buqatar yin hakan ga duk wanda ya karvi musulunci.

A zahiri wannan ya nuna babu hanyar da za a zagayo cikin Musulunci har a iya nuna cewa mas'alar shugabanci ita ce mafi zama a'ala a gefen girma da muhimmanci. Idan kuwa a lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yake raye lamarin shugabancin bai zama wani rukuni da saninsa yake wajibi ba, wane ne ya isa daga baya ya lizimtar da shi a matsayin rukunin addini?

 Wata tambaya muhimmiya a nan ita ce, ashe akwai wasu mutane mafiya xaukaka da daraja fiye da jama'ar da suka rayu da Imaninsu tare da mafificin halitta Sallallahu Alaihi Wasallama? Domin kuwa ya aka yi su ba su xauki wannan mas’ala da girma ba? Ba su fahimta ba ne, sai ku a yanzu kuka samu fahimta?

 Abin da ya kyautu a gane a nan shi ne, ko da an xauka cewa sha'anin shugabanci da matsayinsa zai yiwu ya canza salo daga zamani zuwa wani, to, xaukar sa a matsayin mafificin abu katovara ce ta kai tsaye. Domin kuwa babu lokacin da ya kamata shugabanci ya yi qima da alkadari kamar zamaninsa Sallallahu Alaihi Wasallama. idan ko har ba a bashi wannan matsayi ba a zamaninsa, to, ya ko za a yi ya samu wannan matsayi daga baya?

 Amma abin da yake tabbas shi ne, ita mas'alar Imani da Allah da Manzonsa, a kowane zamani ko yanayi ita ce mafi muhimmanci a musulunci. Don haka, duk wanda ya iya shata wani lokaci da cewa shugabanci a cikinsa ya shiga gaban komi har Imani da Allah, to ya shigar da kansa a cikin sarqaqiya.

 To, idan ma haka ne, cewa shugabanci shi ne tushe mafi girma a musulunci, ya aka yi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har ya bar duniya bai bayyana haka ba, kamar yadda ya bayyana matsayin Imani da Allah da ranar Lahira da Sallah da Azumi da Zakka da Ayyukan Hajji?! Kuma dukan waxannan abubuwa babu wani nassi wanda ya kusanci kwatanta su da matsayin shugabanci.

 Idan kuma ‘yan Shi’ah suka dage a kan cewa lalle sha'anin shugabanci shi ne mafi muhimmanci har a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wai saboda ganin cewa shi Annabin ne da kansa yake shugaba kuma Manzo a lokaci guda, sai mu ce, to, saurari waxannan bayanan:

Bayani Na Xaya:

 Ko da wannan ya inganta, to, ba zai yiwu a ce, shugabanci ne a gaban sahun sauran lamurran addini ba, sai dai ko a ce, a wasu lokuta yana da qarfin matsayi. To, kuma a lokacin da ya fi kowane daraja ba ta zama mafi muhimmanci ba, to, yaushe za ta zama?

Bayani Na Biyu:

 Har abada imani da Allah da gasgata manzanni ya fi maganar shugabanci qarfi. Wannan ita ce aqidar musulmi.

Bayani Na Uku:

 In da haka ne, da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi gaggawar sanar da al’ummarsa kamar yadda ya bayyana masu sauran addini.

 1.6 Wane Shugabanci ne ya fi?

Shi wannan xan Shi’ar da ya tafi a kan cewar shugabanci shi ne lamari mafi muhimmanci ga addini muna bin sa bashin bayani. Shin yana nufin cewa shugabancin Imamansu goma sha biyu ne? Ko kuwa kowanne daga cikinsu shugabancinsa a zamaninsa? Ko dai yana nufin yarda da mas’alar baki xayanta? Ko kuma yana nufin wata ma’ana ce ta daban?

Idan yana nufin shugabancin sha biyu ne da suke cewa, to, ai a zamanin Sahabbai da Tabi’ai ba a san shi ba. Kuma ma su kansu ‘yan Shi’ar cewa suka yi ba a sanin kowane Imami sai na gaba da shi ya ayyana shi. To, ya imani da abin da yake haka ke zama wajibi ballantana mafi girman wajibai?

In kuma yana nufin imani ne da kowane Imami a lokacin bayyanarsa, to, kenan tun daga shekara ta 260H har zuwa yau kuma har abada imani da voyayyen Mahadin da ba a tava gani ko aka ji xuriyarsa ba, ya fi imani da Allah da Manzonsa?

In ko ya ce, a’a, shi fa yana maganar yarda da shugabanci ne a dunqule. Sai mu ce, wane irin dunqulallen abu ne wannan da ya zarce imani da Allah da Manzonsa, kuma ya fi sallah da azumi da zakkah da hajji? Ku dai sake tunani!

In ko kuna da wata ma’ana da kuke nufi, to, ku bayyana muna ita!

 Bayan wannan ana iya tsokaci ga wani vangare mai qarfi ainun wajen ruguza wancan tunani, tsokacin shi ne, kasancewar ba a wajabta ma mutane biyayya ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba saboda kawai yana a matsayin shugaba, amma an wajabta haka ne saboda matsayinsa na Manzon Allah zuwa ga mutanen duniya baki xaya. Wannan shi ne matsayin da har qasa ta naxe ba zai canza ba. Kuma shi ne babban dalilin da ya sa xa'a zuwa gare shi a cikin kowane zamani ta zama tilas ga waxanda suka rayu tare da shi da waxanda suka zo bayan rayuwarsa.

Bayanai da dama ne za su iya qarfafa abin da ya gabata. Domin akwai yanayin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zai yi umurni ko ya zartar da hukunci ga wani mutum guda ko wasu mutane, amma duk da haka sai hukuncin ya zarce ya shafi kowa da kowa. Kamar dai a lokacin da ya gargaxi wasu daga cikin Sahabbansa Allah ya yarda da su inda ya ce musu: “Kada ku rigaye ni yin ruku'i da Sujada”. Ka ga wannan hukuncin bai tsaya a kan waxancan jama'a kawai ba. A madadin haka, hukuncin ya shafi duk wani masallaci da ke koyi da liman a halin yin Sallah.

Haka kuma a wani lokaci wani ya yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tambaya game da aikin Hajji cewa, na gabatar da yin aski kafin yin jifa a cikin rashin sani. Sai ya amsa masa da cewa: “Jifarka ta yi daidai”. To, shi ma wannan hukunci irin wancan ne; bai tsaya a kan mai tambayar kawai ba, a'a. Duk wanda ya sami kansa cikin irin wannan hali babu laifi a kansa.

Ga kuma qarin wani misali wanda a lokacin da jinin Haila ya riski uwar muminai Aisha Raliyallahu Anhu alhali tana cikin harama da Umrah, sai ya ce mata: “Ki ci gaba da sauran ayyukanki na Hajji, xawafi ne kawai ba zaki yi ba”. Ire-iren waxannan misalai su ke nuna banbancin da ke tsakanin biyayyar da ake yi wa Annabawa, da irin wadda ake ma Sarakuna da shugabannin siyasa a kowane zamani.

 A gefen halifofin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuwa, musamman waxanda suka biyo bayan wafatinsa, ba su banbanta ba daga wakillansa na zamanin rayuwarsa, a inda za ka tarar cewa, da zarar wani wakili ya ba da umurni, xa'a a gare shi ta zama wajibi. Dalili kuwa shi ne, umurnin nasa tamkar na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne. Allah Maxaukakin Sarki ya ce:

 ﴿وَمَا مُحَمَّدٌ إِلَّا رَسُول قَد خَلَت مِن قَبلِهِ ٱلرُّسُلُ أَفَإِيْن مَّاتَ أَو قُتِلَ ٱنقَلَبتُم عَلَى أَعقَبِكُم وَمَن يَنقَلِب عَلَى عَقِبَيهِ فَلَن يَضُرَّ ٱللَّهَ شَيا وَسَيَجزِي ٱللَّهُ ٱلشَّكِرِينَ١٤٤﴾ آل عمران: ١٤٤

Kuma Muhammadu bai zama ba face Manzo, Lalle ne Manzanni sun shuxe a gabaninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, za ku juya a kan dugaduganku? To, wanda ya juya a kan dugadugansa, ba zai cuci Allah da kome ba. Kuma Allah zai saka wa masu godiya.

 Wannan ayar ta fayyace cewa, mutuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba za ta dakatar da matsayinsa na Manzo ba. Amma yanzu da zarar wani basarake ko shugaba ya wuntsile ya mutu, sai a xauki muqaminsa a naxa wa wani domin shi an rufe nasa faifan, ya gama nasa ya yi kenan.

 Haqiqa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya isar da Mazanci, ya kiyaye amana tare da shimfixa adalci, ya baza nasiha cikin al'umma, ya taimaki addinin Allah da gaske, kuma ya kafu ga bautar Allah. Haka lamarinsa ya kasance har ya koma ga Mahaliccinsa. Wannan Shi ya sa xa'a gare shi ta zama dole, yana raye ko bayan wafatinsa. Domin bayan rasuwarsa addinin Musulunci bai buqaci wani ragi ko qari ba, kuma wannan shi ne musabbabin zaburar Sahabbai Allah ya yarda da su wajen tattara Al-qur'ani mai girma a waje xaya.

 Amma kuma duk da haka, wani na iya shan iska ya ce, ai shi Annabin da kansa ya zama shugaba ne kawai a halin da yake raye, domin kuwa bayan rasuwarsa shugabanci ya koma ne a wuyan wani wanda ba shi ba. Mu kuma sai mu ce masa, kana so ne ka ce bayan rasuwarsa akwai mutumin da ake yi wa biyayya kamar yadda ake yi masa? Idan wannan ita ce manufarka, ai kuwa kowa ya sheda cewa wannan maganar wofi ce. Idan kuma yana so ne ya ce, yana nufin bayan wucewarsa an samu wakilinsa wajen zartas da lamurran da suka shafi umurni da haninsa, sai a ce da shi wannan ba baquwar magana ba ce, saboda ko a lokacin da yake raye ba baqon abu ba ne cewa, yana wakilta wani musamman lokacin da zai yi wata tafiya.

In aka ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya umartar wani bayan rasuwarsa, amma lokacin rayuwarsa yana yin haka. Sai mu ce, umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ya bayar a lokacin rayuwarsa yana wajaba a yi masa xa'a ga wanda ya ji shi kai tsaye, da wanda maganar ta kai gare shi daga baya. Daman ko ai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wanda duk ya halarci maganata ya isar da ita ga wanda bai halarta ba. sau da yawa wanda aka isar wa da saqo yakan fi wanda ya isar kiyaye saqon".

 In an ce lokacin da yake raye yana hukunci a kan hukunce-hukunce na musamman, misalinsa shi ne; ba wani mutum kyauta, da zartar da haddi a kan wani mutum, da aika wasu sanannun mayaqa zuwa wani wuri. Sai a ce haka yake. Yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama xa'a wajibi ne ga abubuwan da ke kama da haka har ranar qiyama, savanin shugabanni. kodayake mai yiwuwa kafa dalili a kan abin da ya yi kama da wannan, zai iya wuyata. Kamar yadda ilimin abu na voyuwa ga wanda bai halarci abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa ba.

Wanda ya halarci abu shi ya fi sanin abin da Manzo ya faxa, kuma ya fi wanda bai halarta ba fahimta, kodayake ana iya samun waxansu da aka isar da saqon gare su, su fi waxanda suka ji maganarsa kiyaye umurnisa. Wannan fifikon tsakanin mutane yana da nasaba da sanin umurni ko hanin da Manzo ya yi ne kawai. Amma ba shi da wata alaqa da fifikon wajabcin yi wa Manzo xa'a.

 Babu banbanci tsakanin wajabcin yi wa shugabanni xa'a a rayuwar Manzo, da yi masu ita bayan rasuwarsa. Wajabcin yi masa xa’ar ya game duk bayi bai xaya. Kodayake ana samun banbanci wajen hanyar isar da saqon, jinsa da fahimtar sa, wasu na samun saqon manzo game da wani lamari, wasu kuma su sami wani saqon nasa wanda wasu ba su samu ba. Saboda haka mutanen farko na fahimtar wani lamari nasa wanda mutane na biyu Ba su fahimta ba. Duk wanda ya yi umurni da abin da Manzo ya yi umurni da shi, to, ya wajaba a yi masa xa'a don biyayya ga Allah da Manzonsa, ba don xa'a ga wanda ya yi umurnin ba.

 Idan mutane nada shugaba mai qarfi wanda ke umurni da abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi umurni da shi, kuma yake hukunci da irin hukuncinsa, to, lamurransu za su daidaita. Saboda haka ba ya halalta a sa wani shugaba ba shi ba. Ba ya yiwuwa a samu wani mutum kamar sa bayan wucewar sa, ana dai samun wanda ya yi kusa da shi, wanda ya fi cancanta ya zama mai maye wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, saboda ya fi kusanci ga yin umurni da abin da Manzo yake umurni da shi da kuma hani ga abin da Manzo ya yi hani da shi.

Sanannen abu ne cewa, ba a cika yin xa'a ba ga umurninsa a mafi yawan lokuta sai in ya kasance mai cikakken qarfi da ikon da zai tilasta ma jama’a yin xa'a. Don haka dole ne ya kasance ya samu waxanda suka saxaukar da rayukansu don tabbatar da an yi masa xa'a. Addini dai dukansa xa'a ne ga Allah da Manzonsa. Duk wanda ya yi wa Manzon Allah xa'a to ya yi wa Allah xa'a.

 Addinin Musulunci ko bayan rasuwar Manzo, yana nan a matsayinsa na xa'a ga Allah da Manzonsa. Xa'a ga shugabanni a cikin abin da Shari'ah ta ce ayi musu xa'a, shi ma xa'a ne ga Allah da Manzonsa.

 Wannan ne ya sa tushen addini shi ne gasgata cewa, babu wanda ya cancanci bauta in ba Allah ba, da kuma cewa Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama Manzon Allah ne.

 Idan Shi’a ‘yan-sha-biyu sun ce: Hankali ya nuna wajabcin shugabanci, amma bai nuna Manzanci ba. Saboda haka shugabanci ya fi muhimmanci ta wannan fuskar. Sai a ce masu: to, ai ba gaba xayan malamai ne suka yarda da cewa, hankali na wajabta wani abu ba. To, in ma mun yarda da waxanda suka ce hankali na wajabta haka, sai mu ce abin da hankali ke wajabtawa na al'amarin shugabanci, kaxan ne cikin al’amurra na hankali. Don ko ai hankali ya yarda da kaxaita Allah da bauta, kamar yadda ya yarda da faxin gaskiya, adalci da makamantansu.

 Haka kuma, duk wanda ta tabbata wurinsa cewa Muhammadu Manzon Allah ne, kuma ta tabbata cewa yi masa xa'a wajibi ne a kansa, ya kuma yi iyakar qoqarinsa wurin yin masa xa'a gwargwadon iko, Tabbas wannan zai shiga aljanna bai da buqata zuwa ga matsalar shugabanci. Duk ko wanda ya ce mai irin wannan ingantattar aqida ba zai shiga Aljanna ba, to, yana ban hannun makaho da nassoshin Al-qur'ani. Don ko sanannen abu a musulunci shi ne cewa, Allah ya wajabtar da Aljanna ga wanda ya yi imani da Allah da Manzo kuma ya yi musu xa’a.

Allah Maxaukakin Sarki ya ce:

﴿وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنعَمَ ٱللَّهُ عَلَيهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَاءِ وَٱلصَّلِحِينَ وَحَسُنَ أُوْلَئِكَ رَفِيقا٦٩﴾ النساء: ٦٩

Duk wanda ya yi wa Allah xa'a da Manzonsa waxannan suna tare da waxanda Allah ya yi ma ni'ima na daga cikin Manzanni da Shahidai da Salihai. Waxannan abokan arziki. Suratun-Nisa'i: 13

 Shi dai Mahadin naku, mutane ba su da hanyar sanin sa, kuma ba hanyar sanin abin da yake umurni da shi da abin da yake hani da shi, da labaran da yake bayarwa. Idan mutum ba zai sami tsira ba sai ya yi wa irin wannan Mahadin naku xa’a, duk da yake ba a iya sanin me yake umurni kuma me yake hani, kenan babu wanda zai kai ga hanyar tsira.

 In sun ce abin ba haka yake ba, domin idan Mahadin ya bayyana zai ba da umurnin a yi abin da ‘yan Shi’ar sha biyu suke a kai. Sai a ce: to babu buqatar kasancewarsa kenan. Domin abin da ‘yan Shi’ah ke a kai sananne ne ko da shi Mahadin ko babu shi. Daga nan za a san cewa, babu buqata ga samuwarsa. Kuma xa'a ga Allah ba ta rataya a kansa ba, balle samun tsira. Anan ne muke cewa, ba shi halasta iqirarin shugabancin irin wannan mutum, ballantana a ce wajibi ne a yarda da shi a matsayin haka. Wannan abu ne da yake bayyane ga wanda ya yi tunani amma 'yan Shi’ah sun fi kowa jahilci don ba su tunani.

 A kan haka, babu dalilin da zai sa 'yan Shi’ah su rataya tsirar halittar Allah a kan wannan aqida ta Mahadi. Musamman da yake yau da gobe ta tabbatar da kasancewar ta tatsuniya.

 Idan kuwa har suka nace a kan haka, to, lalle ne xayan abubuwa biyu zai tabbata. Wato maganarsu ta zama qarya muraran bisa hujjojin da muka gabatar. Ko kuma kamar suna cewa ne Allah Maxaukakin Sarki ya haramta wa bayinsa samun rahamarsa, qarshe kuma zai tattara su ya zuba wuta. Idan kuwa har haka ta tabbata to, su ne farkon waxanda suka tave, waxanda kuma za a azabtar, don ba su da wata masaniya da komai daga Mahadin nasu balle su nemi tsira. Iyakar abin da suka sani ‘yan riwayoyi ne daga malamansu da ba su taka kara sun karya ba dangane da shi.

 In ko har wani xan Shi’a ya ce mana ya riwaito wani abu daga wurin wannan Mahadin to, tabbas shi maqaryaci ne.

 Na ga wasu Malaman Shi’ah kamar Ibnul-Udi Al-hilli yana cewa: “Idan ‘yan Shi’ah suka yi savani game da wani abu a kan ra’ayi biyu, to, duk ra’ayin da ba a san mai shi ba shi ne gaskiya, don kuwa Mahadinmu yana a cikin sa”.

 Wannan ita ce magaryar tuqewa ta jahilci da vata. Domin ko me zai hana in har akwai Mahadin ya zan yana cikin masu xaya ra’ayin, amma ba a faxe shi ba don ba a gan shi ba balle aji ra’ayinsa?

 Asalin da ‘yan-sha-biyu suka gina addininsu a kai shi ne, abin da ba a sani ba da abin da babu shi. Suna zaton cewa, wannan shugaban nasu akwai shi kuma ba ya kuskure, alhali kuwa ba a san inda yake ba, kuma babu shi, da kuma shi samamme ne wanda ba ya kuskure, su ma sun yarda cewa, ba a iya sanin umurninsa da haninsa, tun da ba a ganin shi.

 A kan haka babu yadda ‘yan-sha-biyu za su yi su tabbatar mana da wanzuwar wannan Mahadi balle shugabancinsa. Dalili kuwa shi ne shugaba, wato Imami, na karva wannan suna ne, a lokacin da ake iya saduwa da shi, ya kuma yi umurni a bi, ko dole. Idan kuwa haka ta faskara, to, duk wata hanya da za a bi don tabbatar da wanzuwar sa waqa ce kawai da baqar wahala. Kuma gaba xayan malaman Shi’ah ba su musun haka. Domin sun tafi tare da malaman da suka yarda da cewa, hankali na iya sanin abu mai kyau da mummuna.

 In waxannan Shi’a ‘yan-sha-biyu suka ce, imaninmu da wannan ma'asumi da ake jira kamar imanin da ‘yan xariqa ke yi ne, game da Ilyasu, da Khadir, da Gausi da Quxubi da mutanen gaibi, waxanda ba a tabbatar da samuwarsa ba balle a san abin da suke umurni da hani. Duk wanda ya yarda da mutanen da aka ambata xin nan ba zai qi yarda da samuwar Mahadinmu ba.

 To, bari mu ba ku amsa ta fuskoki kamar haka:

Fuska Ta Farko: Ai sani ne baku yi ba, imami da xayan waxannan mutane da aka ambata, ba wajibi ne a kan xaya daga cikin Malaman Musulunci, da qungiyoyin Sunnah ba. Duk wanda ko aka samu daga cikinsu yana jin cewa, imanin da mutanen wajibi ne, ko har ma yake wajabta hakan a kan mabiyansa, to, shi da ‘yan Shi’ah uwarsu xaya ubansu xaya. Musamman da zai rataya hakancan da kammaluwar imanin xayan su da Allah.

Fuska Ta Biyu: Duk malaman musulmi da shugabaninsu sun haxa a kan cewa, sanin wajibban addini da mustahabbansa ba su rataya akan gasganta samuwar mutanen da aka ambata ba. Duk kuwa wanda ya zaci haka daga cikin ‘yan xariqa da wasunsu to, tabbas jahili ne kuma vatacce. Ka ga a nan sun banbanta da ‘yan Shi’ah da ke ganin cewa, ba addini ga wanda bai gasgata samuwar Mahadinsu ba.

 Sannan kuma lafuzzan da su ‘yan xariqu ke amfani da su irin, Gausi da Quxubi da Autadu da Abdalu da sauransu, ba wanda ya riwaito su daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ko Sahabbansa da isnadi tsaftatacce. Gara ma dai kalmar Abdalu da aka samu wasu magabata sun yi amfani da ita, duk da yake hadisin da aka riwaito akan ta mai rauni ne. Mun yi magana mai warkarwa game da wannan a wani littafe ba wannan ba.

 1.7 Tsakanin Shi’anci da Sufanci

Fuska Ta Uku: Wannan matsayi na Shi’ah ‘yan-sha-biyu ya yi daidai da na sufaye, waxanda ke da aqidar cewa manyan waliyyansu, wato Gausi ko Quxubi su ke shiryar da mutane a duniya. Haka kuma a cewarsu, babu wani alheri da zai sami wani mutum sai da sani da kuma izininsu. Kai! Hasali ma sun san zahirin mutane da baxininsu, na farko da na qarshe. Irin wannan aqida kuwa, duk musulmin duniya na qwarai sun haxu a kan cewa, vata ce. Domin kuwa ba ta da banbanci da aqidar Kiristoci a wannan babin. Saboda kamar suna cewa ne akwai wani mai tarayya da Allah a cikin ayyukan da ya kevanta da su.

 Kamar yadda wasunsu ke cewa game da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da wasu shaihunansu, wai ilimin xaya daga cikinsu da ikonsa daidai su ke da na Allah Ta’ala.

 Cikinsu akwai wanda ke danganta wa xayan mutanen nan abin da ke iya yiwuwa ga Annabawa da muminai mutanen kirki kamar faruwar wata karama ko kasancewar xayansu idan ya yi addu’a ana karva, da kashefi, wato a sanar da wani bawan Allah wani abin da ya faku ga sauran mutane. Waxanda ke jingina samuwar waxannan karamomi ga mutane rayayyu kuma sanannu ai sun fi kusa da gaskiya bisa ga masu danganta su ga wanda Allah bai halicce shi ba.

 1.8 Zancen Khadir Da Ilyasu

Fuska Ta Huxu: Gaskiyar magana ita ce, abin da Malamai masu zurfin bincike suke a kansa, cewa Ilyasu da Khadir sun mutu kamar yadda kowane mahaluki yake mutuwa. Kuma babu wanda Allah ya sanya a tsakanin sa da bayinsa ko ya wakilta shi wajen halittawa ko azurtawa ko shiryarwa ko bada nasara da makamantan su. Ko da Manzanni aikinsu bai wuce na isar da saqo ba.

 1.9 Mu Koma Kan Maganar Imamah

Game da maganar Imamah dai, wato shugabancin sha biyun da ‘yan Shi’a suka naxa, ba mu gan shi a Alqur’ani ba. Alhalin kuwa Alqur’anin cike ya ke da bayanin duk abin da musulmi ke da buqatar sanin sa, kamar sanin sunayen Allah da tauhidinsa da siffofinsa, da ayoyinsa da Mala’ikunsa da littaffansa da Manzanninsa da ranar Alqiyama. Ga kuma sauran bayanai da suka haxa da labarai masu qarfafa imani, da umurni da hani. To, duk waxannan abubuwan ‘yan Shi’ah sun ce ba su kai muhimmancin shugabancin sha biyu ba. To, ina yake a Alqur’ani?

 Haka kuma Allah Ta’ala ya rataya samun tsira akan abubuwa ga shi ko shugabancin irin na Shi’ah baya cikinsu. Allah Ta’ala na cewa:

﴿وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنعَمَ ٱللَّهُ عَلَيهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَاءِ وَٱلصَّلِحِينَ وَحَسُنَ أُوْلَئِكَ رَفِيقا٦٩﴾ النساء: ٦٩

Duk wanda ya yi wa Allah da Manzonsa xa’a to waxannan na tare da Annabawa da Siddiqai da Salihai, to tarayya da waxannan ya kyautatu. Suratun-Nisa: 69

Kuma Allah ya ce:

﴿ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُ يُدخِلهُ جَنَّت تَجرِي مِن تَحتِهَا ٱلأَنهَرُ خَلِدِينَ فِيهَا وَذَلِكَ ٱلفَوزُ ٱلعَظِيمُ١٣﴾ النساء: ١٣

Kuma duk wanda ya yi wa Allah da Manzonsa xa’a Allah zai shigar da shi aljannar da qoramu ke gudana a qarqashin ta, suna madawwama a ciki. Wancan shi ne babban rabo. Suratun Nisa’i:13.

Kuma Allah na cewa:

﴿وَمَن يَعصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُ يُدخِلهُ نَارًا خَلِدا فِيهَا وَلَهُ عَذَاب مُّهِين١٤﴾ النساء: ١٤

Kuma duk wanda ya sava wa Allah da Manzonsa, kuma ya qetare iyakokinsa, Allah zai shigar da shi wuta, ya na mai dawwama a cikin ta. Kuma ya na da azaba mai qasqantarwa. Suratun Nisa’i: 14.

 In ko wani ya ce: Ai shugabanci irin na Shi’ah shi ma yana cikin xa’a ga Allah da Manzonsa. Sai mu ce masa: Ya za a yi shugabanci ya zarce Sallah da Zakka da Azumi da Hajji da sauran ta fuskar muhimmanci, sannan Allah ya faxe su ya wofintar da shi?

 In an ce: Ba shi yiwuwa mu yi xa’a ga Manzo in ba mu yi xa’a ga shugaba ba saboda shi ya san shari’ah. Sai mu ce: wannan ita ce aqidar ‘yan-sha-biyu. Amma ba su da hujja ko ‘yar qarama ce akanta. Domin sannannen abu ne cewa Alqur’ani bai yi nuni da wannan ba kamar yadda ya bayyana sauran assullan addini. Ya gabata cewa, wannan shugaban da su ke rayawa, ba wanda ya amfana da wannan shugabancinsa, kuma dama abubuwan da Manzanni suka zo da su ba a buqatar shugabannin Shi’ah don saninsu.

 1.10 Asalin Addini a Wurin ‘yan-sha-biyu

Asullan addini a wajen su huxu ne: Tauhidi, adalci, Annabci da shugabanci. Kuma Shugabanci shi ne na qarshe. A cikin Tauhidi ne sukan shigar da aqidarsu ta kore siffofin Allah da ya sa ma kansa da kuma cewa, Alqur’ani halittar Allah ne, ba maganarsa ba. Haka kuma a nan ne suke cewa, ba a ganin Allah a Lahira.

A cikin rukuninsu na biyu, wato adalci sukan shigar da qaryata qaddara, da kuma cewa Allah ba zai iya shiryar da wanda ya so ba ko ya vatar da wanda ya so. Ba lalle ne kuma abin da ya so ya faru ba, ko abin da bai so ba ya qi faruwa.

Abin da muka sani game da ‘yan Shi’ah shi ne, ba su cewa, Allah na da iko akan komai, ba su kuma cewa abin da Allah ya so ne ke kasancewa. Amma dai Tauhidi da Adalci da Annabci duk suna gaba ga shugabanci. To yaushe ne suka dawo suka sanya shugabanci ya zama mafi xaukaka da muhimmanci akan komai?

 Sannan kuma, sun nuna cewa shugabanci wajibi ne don kasancewar sa mai sadarwa zuwa ga wajibbai. To yaya hanyar da ke kai mutum riskuwar maqasudi ke zama mafi xaukaka da muhimmaci a kan abin da ke maqasudin?

 1.11 Takin Saqar ‘Yan Shi’ah

Farkon tuqa da warwarar da Shi’ah ‘yan-sha-biyu suka yi a wannan babi, shi ne irin yadda suka xauki mas’alar shugabanci, a matsayin abu mafi xaukaka da girma a addinin musulunci. Qarshe kuma sai suka dawo suka tsira wata wofintattar aqida game da shi. Wato qudurce samuwar wani shugaba a baxini, kuma ma’asumi, wanda kuma luxufi ne gare su a cikin al’amurransu na addini da duniya. Alhali kuwa babu shi ba alamarsa. Haka kuwa na tabbatar da kasancewar su mafi zama nesa daga wannan luxufi tattare da kasancewar sa babban gurinsu.

 A maimakon haka, sai suka wayi gari suna xa’a ga kafirai da azzalumai don neman biyan buqatunsu, tunda waccan hanyar ta toshe. A qarshe kuma suka tave; ba su ga tsuntsu ba su ga tarko.

 A dunqule Allah Ta’ala ya rataya samun maslahohin lahira da na duniya a kan shugabanni, duk xai ne shin mun ce shugabanci ne abu mafi muhimmanci ko a’a. Su dai Shi’ah ‘yan-sha-biyu sun fi kowa nisa daga samar da wannan maslahar, da kuma alherin da suka ce ana nema, kamar yadda su ke rayuwa.

 Abu na biyu kuma shi ne, cewar da suka yi shi wannan ma’asumi a matsayinsa na shugaba, kasancewarsa samamme zata taimaka wa mabiyansa akan aikata abubuwan alheri na wajibi da nisantar munana daidai da yadda yake umurnin su. Ka ga bisa wannan iqirari, kamata ya yi a taras da ‘yan-sha-biyu sun fi kowa riqe addini hannu bi-biyu, tunda Mahadin can nasu na nan raye. Amma sai al’amarin ya kasance ba haka ba; aka wayi gari suka zama kurar baya.

 Bayan wannan kuma suka ce, ba kowa ba ne wannan ma’asumi illa Ali. Shi ne kawai ya karva wannan suna daga cikin Sahabbai. Saboda haka shi ya fi kowa cancanta da ya jivinci al’amurran musulmi bayan wucewar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kai tsaye. Kuma ma wai, kan malamai ya haxu a kan haka. Suka kuma qara da cewa shi Alin, ya zavi Alhasan ya gade shi, shi kuma ya zavi Alhusaini. Bisa wannan tsari har aka kai ga wannan Mahadi da ake dako.

 Ka ga duk wanda ya ji wannan magana sai ya zaci cewa ‘yan-sha-biyu na da cikakkar masaniya da al’amarin Mahadin nasu. Wato ko dai ya kasance sun tava sa shi a ido, ko wani wanda ya sa shi. Ko ko a’a, suna da wani kundi da ke qunshe da maganganunsa na horo da hani, ko wani abu mai kama da haka. Amma abin mamaki da na tambayi wani daga cikinsu a kan haka, sai ya karva man da cewa ba su da ko xaya daga cikin waxannan abubuwa. Ka ga a haka sun tabbata ashararu; waxanda basu jin kunyar yin amai su lashe.

 Bayan wannan kuma, duk wanda ya kalli abin da idon basira zai fahimci irin kantar jahilcin da ke damun waxannan mutane. Domin kuwa a zahiri, aqidar dakon bayyanar wasu dokoki da hukunce-hukunce a hannun Mahadin nasu na nuna cewa abin da ke hannunsu na dokoki, waxanda suka samu ga malamansu ba gaskiya ba ne. Idan kuwa har suna jin gaskiya ne, to, tabbas babu wata fa’ida a cikin bayyanar Mahadin, ko da hakan za ta yiwu.

 Ka ga a haka ma, har gara masu aqidar cewa Khadir na nan raye da su, domin ko akwai masu raya ganin sa har ma su riwaito wasu nasihohi daga wurin shi duk da yake ingancin hakan abu ne mai wuya. Amma duk da haka gara su da ‘yan-sha-biyu. Kai! Ba waxannan kawai ba, babu wata qungiya ta ‘yan bidi’a da za a ce gara ‘yan-sha-biyu da ita.

 1.12 Daga Gani Sai Kai ya Kumbura?!

A bayyane take cewa, a aqidar wannan xan sha biyu, yin zamani xaya da wannan Mahadi nasu da suke jira, ko da kuwa bai bayyana ba ta ishi wanda ya yi imani da shi dalili na samun tsira. Wato a ma daina haqilo akan rashin bayyanarsa.

To, ka ga wannan magana ko kare ba ya ci ba. Domin kuwa, masaniya da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ko yin zamani xaya da shi, ko yarda da an yi shi ba tare da amincewa da abin da ya zo da shi balle ya aikata ba, ba ya sa mutum ya samu rahamar Allah. Ka kuwa san ko waye Annabi, kuma ko waye wannan Mahadi da suke waqa.

Gaba xayan qungiyoyin musulunci sun yarda da cewa, duk wanda ya yi imani da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wajibi ne ya yi wa hakan rakiya da tsare dokoki. Idan kuwa ba haka ba, gobe lahira kashinsa ya bushe Annabi na ji na gani.

Akwai daga cikin Shi’ah ‘yan-sha-biyu da ke cewa, da zaran mutum ya so sayyidina Ali Raliyallahu Anhu a zuci to, yana iya aikata duk abin da ya ga dama don ya fi qarfin zunubi. A kan haka kenan, babu wata buqata ta samun wani shugaba ma’asumi a yau, don samun wata falala, domin son da suke ma Ali Raliyallahu Anhu a cewarsu, ya ishe su shinge.

 1.13 Shugabanci ba ya Cikin Rukunan Addini

 Xan Shi’ar ya ce, duk wanda bai yi imani da kasancewar mas’alar shugabanci rukuni daga cikin rukunan addini ba, to, babu shi babu tabbata cikin aljanna; ko ya shige ta ana koro shi.

 Martaninmu a kan wannan magana shi ne, Allah Maxaukakin Sarki ya zayyana siffofin muminai a cikin Alqur’ani, amma bai faxi maganar shugabanci a cikinsu ba. Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai ambace shi ba a cikin bayanan imani da rukunansa waxanda ya naqalto daga bakin Jibrilu Alaihis Salamu a cikin sanannen hadisin nan da Nawawi ya kawo a cikin Arba’una. Hadisin kuwa hujja ce karvavviya ga dukkan musulmi na qwarai.

 Idan kuwa har ‘yan-sha-biyu suka qi yarda da wannan hadisi a matsayin hujjarmu, tattare da su ma suna kafa mana hujja da hadisan da basu kama qafar wannan ba, muna kuma qin karva. To, ga waxancan ayoyi da muka yi masu nuni da su a farko, su nuna mana inda Allah ya umarci muminai da yin imani da wani abu wai shi Imamah balle abu ya zama fitina. Allah Ta’ala na cewa:

﴿إِنَّمَا ٱلمُؤمِنُونَ ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَت قُلُوبُهُم وَإِذَا تُلِيَت عَلَيهِم ءَايَتُهُ زَادَتهُم إِيمَنا وَعَلَى رَبِّهِم يَتَوَكَّلُونَ٢ ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوةَ وَمِمَّا رَزَقنَهُم يُنفِقُونَ٣ أُوْلَئِكَ هُمُ ٱلمُؤمِنُونَ حَقّا لَّهُم دَرَجَتٌ عِندَ رَبِّهِم وَمَغفِرَة وَرِزق كَرِيم٤﴾ الأنفال: ٢ - ٤

Muminai kawai su ne waxanda in a kira sunan Allah zuciyarsu na girgiza in aka karanta masu ayoyin Allah imaninsu na qaruwa kuma suna dogaro akan Allah). Waxanda ke tsaida Sallah kuma suna ciyarwa daga abin da mu ka arzitta su da shi, waxannan su ne muminai na haqiqa, suna da xaukaka qwarai wurin Allah da gafara da arziki mai yawa) Al-anfal 2-4.

 Allah ya sheda cewa masu sifofin da ya ambata suna da imani amma bai ambaci shugabanci ba. Kuma Allah Ta’ala yana cewa:

﴿إِنَّمَا ٱلمُؤمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ثُمَّ لَم يَرتَابُواْ وَجَهَدُواْ بِأَموَلِهِم وَأَنفُسِهِم فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أُوْلَئِكَ هُمُ ٱلصَّدِقُونَ١٥﴾ الحجرات: ١٥

Waxanda dai suka yi imani su ne waxanda na yi imani da Allah da Manzonsa sannan ba su yi qwanqwanto ba suka kuma yi jihadi da kuxaxensu da rayukansu a tafarken Allah to waxannan su ne masu gaskiya) Al-hujurat 15.

 Sai Allah ya sa (masu waxannan sifofi) cikin masu ingantancen imani ba tare da ambaton shugabanci ba.

 Bayan waxannan ayoyi kuma, tarihi ya tabbatar da cewa, babu lokacin da wani ya zo karvar musulunci daga wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama aka samu ya lissafa masa Imamah daga cikin rukunan imani. Ka kuwa san ba ta yuwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya voye wa al’ummarsa wani abu na addini. Tunda kuwa har bai yi haka ba, ka ga ashe qarya ce kawai ‘yan-sha-biyu ke yi.

 To, kuma koda ‘yan-sha-biyu za su yarda da rashin makama a nan, su ce, a’a, ai mas’alar Imamah na qunshe ne a cikin nassosa; ba qarara take ba, ta yadda sai an duba sannu a gan ta. Har yau dai basu tsira ba. Domin kuwa ko da haka ne, to, matsayin matsalar bai wuce kasancewa wani reshe na addini amma ba asali ba.

 Wata tuqa da warwara kuma, da yin ban hannun makaho da gaskiya, a cikin lamarin ‘yan-sha-biyu shi ne, cewar da wannan wakili nasu ya yi wai, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, duk wanda ya mutu bai san imamin zamaninsa ba, to, ya yi mutuwa irin ta jahiliyyah.

 To, kafin mu je ko ina dai, wannan hadisi ba gaskiya ba ne. don ko su ‘yan-sha-biyun ba su iya yin bayanin yadda suka samo shi balle ingancinsa.

 Tabbas, akwai ingantaccen hadisi mai kama da wannan, wanda Muslimu ya riwaito daga Nafi’u. sai dai hujja ne a kansu. Bari ka ji yadda abin ya ke:

 Nafi’u ya ce, Abdullahi xan Umar ya zo wurin Abdullahi xan Muxi’u lokacin da aka samu taqaddama tsakanin mutanen Madina da sarki mai ci a wancan lokacin, wato, Yazidu xan Mu’awiyah har suka yi niyyar yi masa tawaye da barazanar cire mubaya’arsa daga wuyansa. A nan ne Ibnu Umar ya zo wurin Abdullahi xan Muxi’u wanda shi ne jagoran wannan fitinar, sai xan Muxi’u ya ce, ku ba shi matashi, sai shi kuma Ibnu Umar ya karva da cewa, Ni ban zo da nufin zama ba, na dai zo ne in sheda maka abin da na ji da kunnuwana daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sa’ad da yake cewa: Duk wanda ya cire hannu daga xa’a ran gamon sa da Allah ba shi da hujja. Kuma wanda duk ya mutu ba tare da ya yi wa shugaban musulmi mubaya’a ba, to, ya mutu mutuwa irin ta jahiliyyah.

 Wannan ya nuna rashin halalcin fita daga xa’ar shugaba musulmi wanda ya tabbata. Haka kuma wanda ya qi bin shugaba na musulunci shi ne zai yi mutuwar jahiliyyah. Kowa ya sani kuwa cewa, ‘yan-sha-biyu sun fi kowa sava ma shugabannin musulunci.

 Da ‘yan-sha-biyu sun san tsiyar da suke yi, da ko wancan gurvataccen hadisin nasu ba su kafa hujja da shi ba. Domin kuwa shi ma turmuza hancinsu yake yi. Saboda xabi’u irin na jahiliyyah sun haxa har da yaqi a kan ‘yan gidanci. Babu ko wanda ya kai su wannan xabi’ar. To, kuma ko a hakan Alqur’ani da Sunnah ba su kafirta mai irin wannan xabi’a ba balle wanda bai kai shi ba. Dubi waxannan hadisai:

 Ya zo a ciki Sahihi Muslim ta hanyar Abu Hurairata ya ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk wanda ya fita daga xa'a, kuma ya bar jama'ar musulmi sannan ya mutu, to, ya mutu mutuwa irin ta jahiliyyah.

 Ya kuma zo a cikin Buhari da Muslimu ta hanyar Abdullahi xan Abbas Raliyallahu Anhu. Daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk wanda ya ga shugabansa na da wani abin da ya ke qi to, ya yi haquri duk da haka. Lalle wanda ya fito yaqi da Sarkin Musulmi kwatankwacin taqa xaya, kuma ya mutu, to, ya mutu ne irin mutuwar jahiliyyah.

 Ka ga qarara waxannan xabi’u da suka tabbata ga ‘yan-sha-biyun Shi’ah sun bayyana su xin ne suke mutuwar jahiliyyah ma damar suka gamu da Allah ba su tuba ba.

 Haka kuma idan aka yi la’akari da kasancewar babu wanda ya san Mahadin can na ‘yan-sha-biyu daga cikinsu balle wani umurni ko hani nasa tun da ya faku ne tun yana xan shekara biyu ko uku lokacin da ya shiga rijiyar Samarra. Yau kuwa a cewar su shekaru kusan xari huxu kenan.[54] Ka ga kenan ashe su ne waxanda basu san imaminsu ba. Wato, da za a qaddara kasancewar wancan hadisi ingantacce, to, su ne waxanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi wa bushara da mutuwa irin ta jahiliyyah.

 Amma kuma a kula “Sanin shugaban zamani” ba ya nufin sanin shanu ko alama, ana nufin dai sani irin wanda zai ba mabiyan sa cikakkar damar yi masa xa’a da kasancewa tsintsiya maxaurinki xaya. Wato, irin abin da mutanen jahiliyyah suka rasa kafin aiko manzo.

 Harwayau dai a kan maganar shugabanci. Siffofin da suka tabbata ga Mahadin ‘yan-sha-biyu, na rashin bayyana ga jama’a balle a yi masa xa’a, sun tabbatar da cewa shi ba shugaba ba ne a ma’aunin shari’ar musulunci. Dalili kuwa shi ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi umurni ne kawai da yin xa’a ga shugabannin da ke tare da jama’arsu. Ko su ma a kan abin da bai sava wa Allah ba. Bayan haka kuma ya hore su da haxin kai. Ka ga a cikin wannan magana akwai abin da ke tabbatar da cewa, shugaba a musulunci ba ma’asumi ba ne. don haka aka ce kada a yi masa xa’a idan ya kauce hanya.

 Kai! Ko tunanin da ‘yan-sha-biyu ke da shi na cewa, wai saboda kasancewar shugabanci abu mafi daraja a addini ne aka ga Sahabbai rana a kansa bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ba gaskiya ba ne. ba a gan su a rana ba, sun dai qara wa juna sani ne kawai akan mas’alar, kamar yadda suka yi a kan wasu mas’aloli da suka fi ta muhimmanci. Idan dai har ‘yan-sha-biyu na neman lokacin da aka ga Sahabbai rana, to, shi ne lokacin halifancin Ali Raliyallahu Anhu.

 Abin da ya faru lokacin naxa Abubakar Raliyallahu Anhu a Saqifa, da halifofi biyu na bayansa, sunansa shawarwari in har ana son gaskiya. Kuma ba a tashi taron ba sai da kowa ya fahimci juna a cikinsu.

 1.14 Ina Nassin Yake?

 Qare waccan magana kuma ke da wuya sai xan sha biyun ya jeranto sunayen Imaman nan da suke cewa su goma sha biyu. Kuma ya qara da cewa, wai, Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama bai bar duniya ba sai da ya bayyana su a matsayin waxanda za su gade shi. Kuma wai har da cewa, duk Ahlus-Sunnah sun yarda da haka. To, ina ma nassin ya ke ballantana wani daga cikin Ahlus-Sunnah ya karvi wannan magana, to, balle kuma a ce duka?!

 1.15 Zaven Siddiqu Nassi ne ko Shawara?

A wurin xan sha biyu, halifancin Abubakar naxin mutane ne ba na Allah ba. Tunda wai, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai bar wasiccin ya gade shi ba. Kuma wai, wannan shi ne abin da Ahlus-Sunnah suke a kai.

To, abin da za mu ce a nan shi ne, lalle a cikin Ahlus-Sunnah akwai masu ra’ayin cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi wasicci da wani ya hau kujerarsa ba. Amma kuma tattare da haka, sanannen abu ne cewa, akwai wata jama’a daga cikinsu, da ke da ra’ayin cewa, halifancin Abubakar abu ne da aka yi bisa ga umurnin Allah da Manzonsa, wato nassi. Akwai maganganu masu yawa a kan haka a mazhabar Ahmad da wasu mazhabobi.

Alqali Abu Ya’ala da wasu malamai, sun ambaci riwayoyi biyu daga Imamu Ahmad a kan wannan lamari:

Riwaya ta farko na cewa, halifancin Abubakar ya tabbata ne nassance; ta hanyar wasu hadisai. Kuma a kan wannan fahimta ne wasu malaman hadisi da Mu’utazilawa da Ash’ariyyawa suke. Shi ma Abu Ya’ala ita ce fahimtarsa. A yayin da riwaya ta biyu kuma ke cewa, a’a, halifancin nasa ya dai tabbata ne ta hanyar ijtihadi. Wannan kuwa shi ne abin da Hasanul Basri da wasu malaman hadisi su ke.

Akwai hadisai da dama da ke tabbatar da waxannan riwayoyi kamar hadissan da malam xan Hamidu ya kafa hujja da su, daga cikinsu har da hadisin da Buhari ya riwaito daga Jubairu xan Mux’imu cewa: “Wata macce ta zo wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya umurce ta da zuwa ta dawo. Sai ita kuma ta tambaye shi da cewa, idan ban taras da kai ba fa? Sai ya karva mata da cewa: “Sai ki nemi Abubakar”. Sai kuma hadisin rubuta wasiyyar da Annabi ya yi quduri a lokacin jinyarsa.

 Hadisi na biyu shi ne wanda Huzaifa xan Yamani ya riwaito cewa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ku yi koyi da biyun nan da ke zuwa bayana; Abubakar da Umar”.

Hadisi na uku daga Abu Hurairata Allah ya qara masa yarda ya ce: Na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “A lokacin da nake barci sai na ga wata guga a kan rijiya, sai na xibi ruwa daga cikin abin da Allah Subhanahu WaTa’ala ya sawwaqe mini. Sannan xan Abu Quhafata (Abubakar) ya xauki gugar ya xebo sau xaya ko biyu. Akwai rauni a cikin xibarsa, Allah ya gafarta masa rauninsa. Sannan guga ta koma hannun Umar xan Haxxabi, ban ga wani gwani mai xiba irin tasa ba. Har sai da mutane suka qoshi da ruwan suka zauna a wurin”. Buhari ya riwaito shi.

 Hadisi na uku daga Abdurrahman xan Abu Bakarata daga babansa ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama watarana ya ce: “Wane ne daga cikinku ya yi mafarki?” Sai na ce: “Na yi mafarkin na ga kamar sikeli na reto daga sama. Sai aka auna ka da Abubakar sai ka rinjaye shi . Sannan aka auna Abubakar da Umar sai Abubakar ya rinjaye shi. Sannan sai aka auna Umar da Usman sai Umar ya rinjaye shi. Daga nan sai aka xauke sikelin”. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mafarkinka na nuni ga halifanci irin na annabta da za a yi. Bayan sa kuwa Allah zai ba da mulki ga wanda ya so”.

 Hadisi na Huxu: Daga Jabir Al-Ansari ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wani mutumin kirki a yau ya yi mafarkin an rataya Abubakar gare ni. An kuma rataya Umar ga Abubakar. Shi kuma Umar sai aka rataya masa Usman”. Jabir Raliyallahu Anhu ya ce: “Mutumin kirkin nan da ya yi mafarkin ba wani ba ne face Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Ratayar kuma abin da take nufi shi ne gadon junansu da za su yi xaya bayan xaya”. Abu Dawuda ya riwaito shi.

 Hadisi na Biyar: Daga Nana Aisha Raliyallahu Anha cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya shiga wurin ta ranar da ya fara rashin lafiya. Ya ce: “Ki kira mani babanki da xan’uwanki, in rubuta wa Abubakar saqo”. Sannan kuma dai sai ya ce: “Ai Allah da Musulmi za su qi karvar kowa sai Abubakar”. A wani lafazi na hadisin “Saboda haka, kada kowa ya sa ransa”.

In ka haxa waxannan hadissai da dukkan riwayoyi ingantattu da suka nuna gabatar da Abubakar ya ba da Sallah, zaka aminta cewa, tabbatattar magana dai ita ce, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi nuni ga mutane cewa, Abubakar ne mai maye gurbinsa. Ya kuma yi musu ishara zuwa ga haka da abubuwa masu yawa da suka haxa da maganganunsa da ayyukansa. Kuma ya so ya rubuta wannan don ya zama wasiccin da za a zartas bayansa amma Allah bai nufa ba saboda wata hikimar da Maxaukakin Sarki yake nufi ta karantar da mu yin shawara a tsakaninmu ga al’amurranmu.

 Malam Ibnu Hazam ya kafa hujja a kan ingancin halifancin Abubakar da cewa, muhajirai da Allah ya kira su masu gaskiya su ne suka ba shi wannan suna. Allah Subhanahu WaTa’ala ya ce game da su:

﴿لِلفُقَرَاءِ ٱلمُهَجِرِينَ ٱلَّذِينَ أُخرِجُواْ مِن دِيَرِهِم وَأَموَلِهِم يَبتَغُونَ فَضلا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضوَنا وَيَنصُرُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُ أُوْلَئِكَ هُمُ ٱلصَّدِقُونَ٨﴾ الحشر: ٨

(Arzikin qasa) na matalautan muhajirai ne waxanda aka fitar da su daga gidajensu da kuxaxensu suna neman falalar Allah da Manzonsa. To, waxannan su ne masu gaskiya) Al-Hasr 8.

 Ibnu Hazam, daga cikin masu ra’ayin cewa, halifancin Abubakar ya tabbata ne da nassi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kare wannan ra’ayin nasu da hujjoji masu qarfi. Kuma ya ce, ba shi yiwuwa Sahabbai su haxu a kan ce masa Halifa in babu wani nassi a kan haka. Daga cikin hadissan da ya kafa hujja da su har da, hadisin matar da ta ce ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama idan ban same ka ba ya zan yi? Sai ya ce, ki je wurin Abubakar. Da kuma hadisin A’ishah Raliyallahu Anha wanda Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce mata: “Na so in aika ma babanki da xan’uwanki su zo don in bar masu saqo a rubuce don kada mutane su yi savani, wani ya ce, ni ne na fi cancanta, ko wani mai guri ya yi guri. Amma kuma Allah da Manzonsa da muminai duk Abubakar suka zava”.

Ibnu Hazam harwayau, ya mayar da martani a kan sauran hujjojin da malaman da ke xaya vangaren suka yi amfani da su. Kamar maganar da sayyidina Umar Raliyallahu Anhu ya yi cewa; “In na zavi halifa a bayana to, wanda ya fi ni ma ya yi haka”. Yana nufin Abubakar. “In kuma ban sa wani ba, to, kuma wanda ya fi ni ya tafi bai sa kowa ba”. Yana nufin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Sai kuma hadisin nana Aisha Allah ya qara mata yarda cewa, an tambaye ta, shin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zai sa wani ya maye gurbinsa wane ne zai sa?

Waxannan hadisai duk da yake suna nuna cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai ayyana wani tsayayyen shugaba a bayansa ba, amma malam Ibnu Hazam ya ce, ba shi yiwuwa su keta ijma'in da Sahabbai suka yi. Domin ba su yi qarfin da za su iya yin haka ba duk da ingancinsu.

 Idan har an qaddara gaskiya ne cewa, Manzo ya faxi wanda zai gade shi, to, ko a haka ma ‘yan-sha-biyu ba su da hujja. Domin Rawandiyawa daga cikinsu na ganin cewa, Abbas ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bar nassi a kan zai gaje shi, ba Ali ba. Alqali Abu Ya'ala ya qara haske a kan wannan maganar, inda ya faxi cewa, wasu ‘yan Rawandiyyah na ganin bayan Abbas ‘ya’ya da jikokinsa ne za su ci gaba da halifanci har ranar tashin qiyama. Kuma wai, in ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma sannan nassin da ya faxi haka wai ba a fayyace yake ba. Waxannan ra’ayoyan biyu sun yi hannun riga da ra’ayoya biyu na ‘yan-sha-biyu da kuma Jarudiyawa daga cikin Shi’ah. Su dai Jarudiyawa, savanin ‘yan-sha-biyu, ganin suke yi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxi shugabancin Ali amma ba qarara ba. Ya dai bayyana sifofin da ba a same su ga kowa ba sai Ali.

 Abin nufi dai a nan, shi ne cewa, kowane daga cikin waxannan bayin Allah guda uku; Abubakar da Abbas da Ali an samu masu raya cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bar nassi a kansu. Kuma cewa, ya bar nassi a kan Abubakar shi ne ya xara sauran ra’ayoyan qarfi ta fuskar hujja da kuma karvuwa a wurin malamai, duk da yake a mafi rinjayen zance babu nassin ga ko xaya.

 Alamu masu yawa sun nuna cewa, Abubakar ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zava, kuma Sahabbai sun fahimci haka. Don haka ne ma Umar Raliyallahu Anhu ya ce, a cikin huxubar da ya yi gaban Muhajiruna da Ansaru: “Babu wanda mutane ke so daga cikinmu kamar Abubakar” Buhari da Muslim. Bisa wannan dalili ne gaba xayansu suka yi wa Abubakar bai’a, in ban da Sa’adu xan Ubadata, a sakamakon sha’awar da yake da ita ga matsayin. Amma kuma daga baya ya yi mubaya’ar.

 Muhajiruna sun yi wa Abubakar wannan mubaya’a ne a kan sanin da suka yi na cewa, Allah da Manzonsa shi suka fifita. Ka ga a haka ta tabbata cewa, halifancin nasa ya tabbata ne ta hanyoyi ingantattu.

 1.16 Halifofi Shiryayyu

 Xan sha biyu ya ce, wai, Umar Raliyallahu Anhu ne kawai da wasu mutane guda huxu suka tabbatar da naxin Abubakar Raliyallahu Anhu a matsayin halifa. Kuma wai, wannan magana haka take har wurin Ahlus-Sunnah don daga gare su ne ya riwaito ta.

 To, muna sanar da shi cewa, babu wani Ahlus-Sunnah da ke da wannan fahimta. Duk da yake ba mu musun cewa, akwai wasu daga cikin zaqaquran magana, wato Ahlul-Kalam, da ke ganin cewa, a duk lokacin da aka samu mutum huxu sun goya ma mutum xaya baya to, yana iya zama halifa. Wasu kuma suka ce, mutum biyu dai. Wasu ma suka ce, kai ko xaya ya samu bukata ta biya.

 Amma ra’ayin Ahlus-Sunnah a kan wannan magana shi ne, shugabanci na qulluwa ne idan masu qarfin iko da faxa a ji waxanda xa’arsu ga shugaba ke sa a kai ga maqasudi, suka yi wa mutum mubaya’ah.

 Xan sha biyun ya ci gaba da cewa; Usmanu xan Affan ya zama halifa ne da umurnin da Umar ya bayar ga mutane shida yana xaya daga cikinsu, sai wasunsu suka zave shi.

 To, harwayau dai, ba zaven da waxannan qwarorin jama’a suka yi wa Usmanu ne ya ba shi damar zama halifa ba. Ko alama, mubaya’ar dai da gaba xayan musulmi a wannan lokaci suka yi masa ce ta ba shi wannan dama. Kuma tarihi ya tabbatar da cewa, babu mutum xaya da bai yi masa wannan mubaya’a ba.

 Imamu Ahmadu xan Hambali ma cewa ya yi, ba a tava irin mubaya’ar da aka yi wa Usman ba ta fuskar samun haxin kan kowa da kowa da rashin samun jayayya. Mubaya’ar kuwa ta tabbata ne a lokacin da sauran ‘yan kwamitinsu su biyu; Abdurrahman xan Aufu da Ali suka yi masa mubaya’a a masallaci, sauran jama’a suka rufa masu baya.

Kafin haka kuwa, Abdurrahman xan Aufu ya xauki tsawon kwana uku ba tare da ya ko samu isasshen bacci ba, don shagaltuwa da neman shawarar jama’a da xaukar ra’ayin Sahabbai. Kai, har ma sai da ya nemi jin ta bakin matan aure da qananan yara kafin ya cimma waccan matsaya da suka xora mutane a kan ta, shi da Ali.

 A qarshe kuma suka tabbatar wa jama’a cewa, sun xora Usmanu a kan wannan matsayi ba don tsoro ko kwaxayin wani abu ba. Bisa wannan dalili da yawa daga magabata irin su malam Ayyub As-Sukhtiyani suka tafi a kan cewa, duk wanda ya fifita Ali Raliyallahu Anhu a kan Usmanu bai raga wa Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Domin su a nasu fiqihu Usmanu na gaba gare shi, ittifaqan.

Daga nan kuma sai xan sha biyun ya ce: “Shi ko halifancin Ali Raliyallahu Anhu ya tabbata ne sakamakon mubaya’ar da gaba xayan jama’a suka yi masa, savanin halifofi uku da suka gabace shi.

Wannan magana ko alama ba gaskiya ba ce. Tarihin musulunci ya tabbatar da cewa, yadda kan musulmi ya haxu a kan yi wa Sahabban can uku mubaya’a ya fi yadda ya haxu a kan yi wa Ali ita, nesa ba kusa ba. Wannan ta fuskar yawan jama’a kenan. To, ko ta fuskar girma da xaukaka, waxanda suka haxu a kan bai’ar tasu sun yi wa waxanda suka haxu a tasa fintinqau. Don kuwa a wancan zamanin akwai manya-manyan Sahabbai waxanda ba a samu irin su ba a lokacin mubaya’ar Ali don sun rasu ko ba su nan. Ga kuma waxanda suka murje idanu daga cikin mutanen kirki suka qi yi wa Ali mubaya’a saboda wasu shubhohi da suka gitta masu. Abin da bai faru ba a lokacin da aka naxa halifofi uku na farko. Domin naxin na Ali ya zo a wani lokaci na hatsaniya da tashin hankali da kuma girgizar zukata a kan kisan gilar da aka yi wa halifan da ya gabace shi. Har ma ana raxe-raxin cewa, ko cikin waxanda suka yi mubaya’ar, wasu tilasta su aka yi da kaifin takobi.

To, amma in ban da Sa'adu da muka faxa, wa aka tava jin xuriyar ya yi gunguni game da zaven Abubakar, balle qin yin mubaya’a? Shi ma kuma ya zo ya yi daga baya, bai bixi wata fitina ko tada zaune tsaye ba. Musamman da yake an tunatar da shi faxar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, wannan halifanci abu ne na Quraishawa, kuma duk mutanensa sun miqa wuya babu wata jayayya. Kamar yadda wasu suka ce Ali ya yi jinkirin mubaya’a shi ma ga Abubakar sai daga bisani sannan ya yi.

Xan sha biyun yana iya cewa, Ahlus-Sunnah ma sun yarda da cewa, mutane ne suka yi ma halifofi uku mubaya’a ba nassi ne ya tabbatar da ita ba. Sai mu ce, babu shakka Ahlus-Sunnah sun yarda da zancen da Manzo Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a kan halifofi shiryayyu, da kuma cewa, lokacinsu zai miqa har shekaru talatin. Don haka, Ali yana a cikinsu. Al'umma kuwa ta haxu a kan shugabancin Sahabban nan uku, kuma sun samu cimma maqasudin shugabanci, don sun yaqi kafirai, sun ci qasashe da dama. Amma a lokacin halifancin Ali ko kafiri xaya ba a yaqa ba, balle a ci wani gari. Abin da ya faru dai kawai shi ne yaqi a tsakanin musulmi.

 Bisa ga haka, muna fahimtar cewa, nassoshin da ‘yan-sha-biyu ke raya cewa akwai game da Ali, da waxanda Rawandiyyawa ke cewa akwai a kan Abbas duk ba su da tushe, kuma ba su sa wanin su ya zamo halifa ba. Shi dai Ali ya zamo halifa da zaven da aka yi masa bayan wafatin sayyidina Usman.

 Xan sha biyun ya ci gaba da cewa, wai, Ahlus-Sunnah sun yi savani bayan mutuwar Ali, kuma rabu biyu; sashensu suka naxa Al-Hassan a yayin da xaya sashen suka zavi Mu'awiyah.

 Amsa ita ce: Ahlus-Sunnah ba su yi jayayya cikin wannan ba. Abin da dai ya faru shi ne, mutanen Iraqi sun yi wa Hassan mubaya'a a matsayin magadin babansa. Mutanen Sham kuwa daman tare suke da Mu'awiyah, kuma bayan mutuwar Ali sai suka shelanta shi a matsayin Sarkin Musulmi.

 Xan sha biyun ya ci gaba da cewa: Sannan aka sa shugabancin cikin gidan Banu Umayyata, bayansu kuma sai suka mayar da ita gidan Banul Abbas.

 Amsarmu ita ce: Ahlus-Sunnah ba su ce, xayan gidajen nan biyu shi ya cancanci shugabanci ba. Kuma su, ba su ce dole a yi masu xa'a ba ga duk abin da suka yi umurni da shi.

Abin da Ahlus-Sunnah ke yi shi ne, suna faxin abin da ya gudana. Kuma suna umurni da abin da ya wajaba, suna kafa shedu da abin da ya auku, suna umurni da abin da Allah da Manzonsa suka yi umurni da shi. Suna cewa, waxannan su ne suka yi shugabanci, kuma sun kasance suna da qarfi da iko, suna kuma iya samar da maqasudin shugabanci, kamar zartar da haddi, da raba kuxaxe, da zaven alqalai, da naxa hakimai da gwamnoni, da xaukar mayaqa tare da aika su wuraren jihadi, da tsayar da Hajji da Sallolin Idi da na Juma'a, da sauran abubuwan da suka wajaba a kan shugaba.

Ahlus-Sunnah kuma harwayau, suna cewa, ba ya halasta a yi wa xayan waxannan da na'ibansu xa'a a cikin savon Allah. Amma ana bin su wajen aikata abubuwan da suke xa'a ne ga Allah Subhanahu WaTa’ala. Sai a fita yaqar kafirai tare da su, a yi sallar juma'a da ta Idi a bayansu ko na wakilansu, a yi hajji a qarqashin jagorancinsu, a taimaka masu a wurin umurni da kyakkyawa da hani daga mummuna, da makamantansu.

 Abin da aka sani ne cewar mutane ba su gyaruwa sai da shugabanni. Kuma samun sarakuna tsayayyu ko da azzalumai ne ya fi alheri a kan barin mutane kara-zube. Kamar yadda ake cewa, shekaru sittin da shugaba azzalumi ya fi dare xaya ba tare da shugaba ba.[55]

 An riwaito daga Ali Raliyallahu Anhu ya ce: “Ba makawa ya kasance mutane na da shugabanni, masu tsoron Allah ne ko Fajirai” Aka ce masa: “Mun san hikimar da ke cikin samun shugaba mai tsoron Allah. To, wanda bai tsoronsa fa?” Sai ya karva masu da cewa: “Ana tsare lafiyar hanya da shi, a tsayar da haddodin Allah, a yaqi magabta tare shi, a kuma raba ganima da shi”. Ali xan Ma'abadu ya ambaci wannan a littafin Axxa'atu Wal-Ma'asiyatu.

 To, duk wanda ya yi shugabanci kowane iri ne, shugabancinsa ya fi alfanu ga musulmi a kan shugabancin wanda babu shi, kamar Mahadin can na ‘yan Shi’ah. Wanda har yanzu suna nan suna ta jiran sa, ba kuwa zai bayyana ba har a naxe qasa. Babu wata maslaha da yardarsu da shugabancin nasa ta haifar ga lamurran duniya ko na addini illa kafewa a kan miyagun aqidu, da haifar da fitina tsakanin musulmi, da vata lokaci.

 Mutane ba su iya zama lokaci ko xan kaxan ba tare da shugaba ba. Kai lamurransu ma vaci suke yi. To, yaya za su gyaru in ba su da shugaba sai wanda ba a sani ba, ba a kuma san abin da yake faxa ba, bai iya aikata kome dangane da shugabanci, kai dai wannan da babu shi fa!?

Amma iyayensa ba su kasance suna da qarfi da iko ba na zama shugabanni. Malamai daga cikinsu suna da shugabanci na ilimi kamar fannin hadisi da fatawa da makamantansu, amma ba su da shugabanci irin na siyasa. Saboda haka suka kasa shugabanci ko da ko sun fi cancanta ko ba su fi ba.

Duk dai yadda abin ya ke, za a tarar cewa, ba a ba su ikon shugabanci ba, kuma ba a shugabantar da su ba. Kuma bai yiwuwa a kai ga maqasudin shugabanci da su tunda ba su da qarfi da iko. Ko da mumini ya yi musu xa’a to ba za a kai ga maslahohin da ake samu idan aka yi wa shugabanni xa’a kamar jihadin maqiya da ba masu haqqi haqqinsu da tsaida haddoda.

To, in wani ya ce: Lalle wasu daga cikin waxannan limaman na Shi’ah na da qarfi da ikon da ke iya samar da maqasudin shugabanci, to sai mu ce wannan dai girman kai ne da qin gaskiya.

Da lamarin ya kasance haka da ba a sami wanda ya yi jayayya da su har ya karve mulki ya hana wa kowa ba. In kuma ya ce: Su ne shugabanni don su ya wajabta su yi shugabanci, kuma mutane sun sava ma Allah saboda qin shugabantar da su.

To, wannan daidai yake da wani ya ce: Wane ya kamata ya zama alqali amma ba a yi masa ba, amma an zalunce shi an hana masa alqalanci. Na san wataqila su ce, wannan ba zata hana su karva sunansu na shugabanni, waxanda Allah ya zava ba. Kuma waxancan mutane da suka qi shugabantar da su, tabbas azzalumai ne. sun kuma savi Allah a haka.

A nan sai mu gaya masu cewa, koda ya zama wajibi a shugabantar da su, ba za a yi laifi wa Allah idan ba a yi haka ba, sai idan hakan ta kasance da gangan. Wannan shi ne musulunci. Ai Umar xan Abdulaziz ya so ya shugabantar da Qasim xan Muhammad jikan Abubakar Siddiq saboda yarda da cancantarsa, amma masu qarfi daga cikin banu Umayyata suka taka masa burki. Kun ga wannan ba laifinsa ba ne.

Duk wanda bai yi zalunci ba, kuma bai taimaka ga yin sa ba, ba laifin da ke hawa kansa. Sanannen abu ne cewa, masu tsoron Allah ba su taimakon shugabanni sai ga abubuwan alheri da tsoron Allah. Ba su taimakawa ga savo da qetare iyaka.

Abin da Ahlus-Sunnah suka yi imani da shi a wannan babi shi ne: Ya kamata a shugabantar da wanda ya fi cancanta in ya yiwu. Wasu daga cikinsu ma na jin yin haka wajibi ne. Wasu kuma suka ce mustahabbi ne dai. Sannan duk wanda ya bar wanda ya fi cancanta kuma yana da iko to shi azzalumi ne. Amma wanda ya kasa shugabantar da mafifici ga shi ko yana son haka, to yana da uzuri a wurin Allah da mutane. A qarshe kuma za su yi xa’a ga wanda Allah ya ba shugabanci domin babu abun da ke faruwa sai da iko da yardarsa. Yana kuma canza abin da duk ya so, a lokacin da ya so. Wannan idan mun qaddara ingancin wancan nassi da ‘yan Shi’ah ke da’awa kenan.

Balle ma bai inganta ba, ko alama. Babu abin da ma mafarkin ha kan zai kawo illa ruxani. Domin kuwa duk mai imani da hankali, ba ya musun cewa, Allah Ta’ala ya san gobe. Ka ga a haka ba zai umurci bayinsa da shugabantar da wanda ba zai iya tabbatar da maqasudin shugabanci ba. Duk ma wanda ke da irin wannan hasashe da hangen nesa daga cikin mutane, a kan wasu mutane biyu da ke qarqashinsa, lalle zai yi umurni ne kawai da shugabantar da wanda buqata ke iya biya da shi. Wannan shi ne irin abin da ya faru a kan halifofi uku na farko da na huxu. Al’amarin kuwa hukunci ne na Allah. Duk ko wanda ya qi yarda da shi, to, da shi yake jayayya.

Iyakar abin da Ahlus-Sunnah ke son tabbatarwa a nan, wanda kuma shi ne aqidarsu, shi ne: Duk shugaban da Allah Ta’ala ya yi wa baiwar cikakken qarfi, da ikon tabbatarwa da aiwatar da manufofin shugabanci, to, shi ne karvavve kuma yardadde a wurin Allah da mutanen kirki. Kamar dai yadda duk wanda ke shiga gaba a bishi sallah shi ne liman ko an qi, ko an so. Wannan kuwa koda akwai wanda ya fi shi cancanta da shugabancin ko limancin. A haka kuma, yi masu xa’a, da taimaka masu cikin duk abin da ba savon Allah ba, wajibi ne a wannan mahanga ta Ahlus-Sunnah. Domin Buhari da Muslimu sun riwaito cewa, Ibnu Abbas Raliyallahu Anhu ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya ga abin da yake qi ga shugabansa, to, ya yi haquri. Haqiqa ba wanda zai fita daga xa’ar shugabansa ko da nisan taqa guda ne sannan ya mutu bisa wannan halin, face ya mutu irin mutuwar jahiliyyah.

 ZANGO NA BIYU

 2.0 Dalilan Wajabcin bin Imamiyyah!

A fasalin littafinsa na biyu, xan Shi’ar ya ce: Wajibi ne a bi Mazhabar Imamiyyah.

Wato, yana cewa, tunda Sahabbai sun yi savani bayan rasuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, to, wajibi ne a kan musulmi su yi biyayya ga mazhabar Shi’ah ‘yar sha biyu. Saboda wai a cewarsa, jagororin wannan mazhaba ba su kuskure. Duk abin da ya fito daga bakinsu, shi ne mafi inganci da zama gaskiya. Saboda haka mabiyan wannan mazhaba ne kawai za su sami tsira gobe qiyama.

Ya qara da cewa, babban abin da ke tabbatar da kasancewar wannan mazahaba mafi cancanta daga cikin mazhabobi shi ne, savanin can da wai, Sahabbai suka yi bayan Manzo. A qarshe wasu daga cikinsu suka mara wa wani baya saboda kwaxayin abin duniya, ya zama halifa. Kamar yadda Umar xan Sa’ad sarkin Tehran ya zavi kashe Husaini don ya tsira da mulki. Amma kuma duk da haka, wasu suka jajirce suka goyi bayan gaskiya; suka mara wa wanda ya fi cancanta baya, suka bar duniya da qyaleqyalinta.

Saboda haka, inji shi, wajibi ne a kan kowane musulmi, ya yi wa kansa qiyamullaili, ya bi mazhabar mutanen kirki, wato Imamiyyah, ya fita batun azzalumai. Musamman ma wai, ga shi Allah Ta’ala ya ce:

﴿ أَلَا لَعنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلظَّلِمِينَ١٨﴾ هود: ١٨

Ku saurara! La’anar Allah ta tabbata akan azzalumai. Suratu Hud 18.

Kafin mu ce wani abu a nan, muna son a fahimta cewa, a cikin wannan magana, xan Shi’ar ya kasa Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama gida huxu bayan wafatinsa. a) Wanda ya nemi halifanci, alhali bai cancanta ba, wato Abubakar. b) Wanda ya nemi halifanci bisa qa’ida, saboda haqqinsa ne, wato Ali c) Waxanda suka goyi bayan halifofi uku na kafin Ali, don kwaxayin abin duniya. d) Waxanda suka goyi bayan su don rashin basira.

Ka ga kenan, a kaikaice xan Shi’ar na cewa ne, gaba xayan Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sun halaka bayan rasuwarsa, in banda Ali. Saboda sun sani sun take sani.

Duk wanda ya dubi wannan iqirari nasa da idon basira, to, zai fahimci cewa, yana fifita Yahudawa ne da Nasara a kan sahabban Annabi. Tabbas abin da yake nufi kenan. Domin tarihi ya tabbatar da cewa, an samu shiryayyun mutane masu tsayawa a kan gaskiya daga cikin Yahudawa da Nasara kamar yadda Allah ya ce:

﴿وَمِمَّن خَلَقنَا أُمَّة يَهدُونَ بِٱلحَقِّ وَبِهِ يَعدِلُونَ١٨١﴾ الأعراف: ١٨١

Daga cikin mutanen da muka halitta akwai wata al’umma masu shiryarwa da gaskiya, sannan kuma da ita suke adalci. Al-A’araf 181.

To, idan kuwa har aka rasa shiryayyun mutane daga cikin Sahabbai, tattare da kasancewar zamaninsu mafi girman qarni, ka ga ba za a same su ba a kowane qarni. Wannan ita ce manufarsa.

Allah Sarki! Allah ya kiyashe mu da mugun masoyi. Ka ga wannan sukar lamiri da xan Shi’ah ya yi wa Sahabbai ta haxa har da Ali Raliyallahu Anhu. Domin kuwa duk abin da ya gudana bayan wucewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, har zuwa lokacin da shi ya zama halifa ai da hannunsa a ciki. Illa dai sun yi abubuwa ne shi da takwarorin nasa, Sahabbai, bisa ijtihadi da nufin kare alfarmar Shari’ah. Amma xan Shi’ar sai ya ce, wai sun yi hakan can ne, a sakamakon kasancewar su maqiya Allah da Manzo, kuma makwaxaita abin duniya. Wal iyazu billahi.

Ka ga wannan iqirari ko shakka babu, qaryata Allah Subhanahu WaTa’ala ne da ya ce:

﴿وَٱلسَّبِقُونَ ٱلأَوَّلُونَ مِنَ ٱلمُهَجِرِينَ وَٱلأَنصَارِ وَٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُم بِإِحسَن رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنهُم وَرَضُواْ عَنهُ وَأَعَدَّ لَهُم جَنَّت تَجرِي تَحتَهَا ٱلأَنهَرُ خَلِدِينَ فِيهَا أَبَدا ذَلِكَ ٱلفَوزُ ٱلعَظِيمُ١٠٠﴾ التوبة: ١٠٠

Kuma magabatan farko na Muhajirai da Ansarai da waxanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su kuma sun yarda da shi, kuma ya yi musu tattalin gidajen aljanna, qoramu suna gudana a qarqashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne rabo mai girma.

Suratut Taubah: 100

Da kuma inda Ya ce:

ﭽ مُّحَمَّدٞ رَّسُولُ ٱللَّهِۚ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ أَشِدَّآءُ عَلَىٰٰٰٰٰٰٰٰ ٱلۡكُفَّارِ رُحَمَآءُ بَيۡنَهُمۡۖ تَرَىٰهُمۡ رُكَّعٗا سُجَّدٗا يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِن ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗاۖ سِيمَاهُمۡ فِي وُجُوهِهِمۡ مِنۡ أَثَرِ ٱلسُّجُودِۚ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِۚ وَمَثَلُهُمۡ فِي ٱلۡإِنجِيلِ كَزَرۡعٍ أَخۡرَجَ شَطۡ‍َٔهُۥ فَ‍َٔازَرَهُۥ فَٱسۡتَغۡلَظَ فَٱسۡتَوَىٰ عَلَىٰٰٰٰٰٰٰٰٰ سُوقِهِۦ يُعۡجِبُ ٱلزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ ٱلۡكُفَّارَۗ وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ مِنۡهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمَۢا ٢٩ ﭼ الفتح:٢٩

Muhammadu manzon Allah ne. Kuma waxannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, ka na ganinsu suna masu ruku'i masu sujada, suna neman falala daga Ubangijinsu, da yardarsa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu, daga Kufan sujuda. Wannan ita ce siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu a cikin Linjila ita ce, kamar tsiron shuka wanda ya fitar da reshensa, sa’an nan ya qarfafa shi, ya yi kauri, sa’an nan ya daidaita a kan qafafunsa, yana bayar da sha’awa ga masu shukar, domin (Allah) ya fusatar da kafirai game da su. Kuma Allah ya yi alqawali ga waxanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan qwarai daga cikinsu da gafara da lada mai girma.

 Suratul Fathi, Aya ta 29.

Allah Ta’ala ya ce:

﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَهَدُواْ بِأَموَلِهِم وَأَنفُسِهِم فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَواْ وَّنَصَرُواْ أُوْلَئِكَ بَعضُهُم أَولِيَاءُ بَعض ﴾ الأنفال: ٧٢

Haqiqa, waxanda suka yi imani suka kuma yi hijira da jihadi da dukiyarsu da rayukansu a tafarkin Allah da waxanda suka karvi baquncin (su) suka kuma taimaka, waxannan sashensu majivinta lamurran sashe ne. Suratul-Anfal: 72

Har zuwa inda Allah ya ce:

﴿وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَهَدُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَواْ وَّنَصَرُواْ أُوْلَئِكَ هُمُ ٱلمُؤمِنُونَ حَقّا لَّهُم مَّغفِرَة وَرِزق كَرِيم٧٤ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِن بَعدُ وَهَاجَرُواْ وَجَهَدُواْ مَعَكُم فَأُوْلَئِكَ مِنكُم وَأُوْلُواْ ٱلأَرحَامِ بَعضُهُم أَولَى بِبَعض فِي كِتَبِ ٱللَّهِ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيءٍ عَلِيمُ٧٥﴾ الأنفال: ٧٤ – ٧٥

Kuma waxanda suka yi imani kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihadi a cikin hanyar Allah, kuma da waxanda suka bayar da masauki, kuma suka yi taimako, waxannan su ne muminai na gaskiya, suna da gafara da wani abinci na karimci. Kuma waxanda suka yi imani daga baya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihadi tare da ku, to, waxannan suna tare da ku, kuma ma’abuta zumunta, sashensu majivintan sashe ne a cikin littafin Allah. Lalle Allah ne Masani ga dukkan komi.

 Anfal: 74-75

Da kuma in da Maxaukakin Sarki ya ce:

﴿وَمَا لَكُم أَلَّا تُنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلِلَّهِ مِيرَثُ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ لَا يَستَوِي مِنكُم مَّن أَنفَقَ مِن قَبلِ ٱلفَتحِ وَقَتَلَ أُوْلَئِكَ أَعظَمُ دَرَجَة مِّنَ ٱلَّذِينَ أَنفَقُواْ مِن بَعدُ وَقَتَلُواْ وَكُلّا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلحُسنَى وَٱللَّهُ بِمَا تَعمَلُونَ خَبِير١٠﴾ الحديد: ١٠

Wanda ya ciyar daga cikin ku ya yi jihadi kafin addini ya yi qarfi ba su zama xaya da waxanda suka ciyar suka kuma yi jihadi bayan haka. Waxancan sun fi xaukaka. Kuma dukansu Allah ya yi masu alqawarin aljanna. Kuma Allah masani ne ga abin da kuke aikatawa. Al-hadid 10

Da kuma inda Allah Ta’ala ya ce:

﴿لِلفُقَرَاءِ ٱلمُهَجِرِينَ ٱلَّذِينَ أُخرِجُواْ مِن دِيَرِهِم وَأَموَلِهِم يَبتَغُونَ فَضلا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضوَنا وَيَنصُرُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُ أُوْلَئِكَ هُمُ ٱلصَّدِقُونَ٨ وَٱلَّذِينَ تَبَوَّءُو ٱلدَّارَ وَٱلإِيمَنَ مِن قَبلِهِم يُحِبُّونَ مَن هَاجَرَ إِلَيهِم وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِم حَاجَة مِّمَّا أُوتُواْ وَيُؤثِرُونَ عَلَى أَنفُسِهِم وَلَو كَانَ بِهِم خَصَاصَة وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفسِهِ فَأُوْلَئِكَ هُمُ ٱلمُفلِحُونَ٩ وَٱلَّذِينَ جَاءُو مِن بَعدِهِم يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱغفِر لَنَا وَلِإِخوَنِنَا ٱلَّذِينَ سَبَقُونَا بِٱلإِيمَنِ وَلَا تَجعَل فِي قُلُوبِنَا غِلّا لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوف رَّحِيمٌ١٠﴾ الحشر: ٨ - ١٠

(Arzikin qasa) na matalautan muhajirai ne, waxanda aka fitar da su daga gidajensu, aka raba su da dukiyarsu, suna neman falalar Allah da yarda, kuma suna taimakon Allah da Manzonsa. To, waxannan su ne masu gaskiya.

Waxanda da suka yi tanadin gidaje da imani gabaninsu suna son waxanda suka yi hijira zuwa wurin su, ba su jin wata buqata a cikin zukatansu game da abin da aka ba su. Kuma suna fifita wasu (‘yan’uwan su) akan kawunansu. Kuma wanda duk ya kange ransa daga tsananin rowarta to, waxannan su ne masu ribanta.

Kuma waxanda suka zo daga bayansu, suna cewa, “Ya Ubangijinmu! ka yi gafara a gare mu da kuma ga ‘yan’uwanmu waxanda suka riga mu yin imani. Kada ka sanya wani qulli a cikin zukatanmu ga waxanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Lalle kai ne mai tausayi, mai jinqai. Suratul Hashri: 10

Ka ga bisa ga abin da waxannan ayoyi suka qunsa, wajibi ne a kan kowane musulmi ya qaunaci Muhajiruna da Ansaru. Duk abin da ya faru tsakanin su kuma, na rayuwa da hidima ga addinin Allah, ya fahimce shi a matsayin ijtihadi to wata qaddara da ta riga fata. Savanin abin da ‘yan Shi’ah ke yi na zagi da cin mutuncin su, tare da xaukar su ba bakin komi ba.

Ibnu Baxxata da waxansu malamai sun riwaito hadisi daga Sa’adu xan abu Waqqas ya ce: Darajojin mutane uku ne. Biyu sun wuce saura xaya. Mafi kyan abin da za ku iya kasancewa shi ne, ku shiga cikin matakin qarshe. Sannan sai ya karanta:

(Arzikin qasa) na matalautan muhajirai ne, waxanda aka fitar da su daga gidajensu, aka raba su da dukiyarsu, suna neman falalar Allah da yarda, kuma suna taimakon Allah da Manzonsa. To, waxannan sune masu gaskiya.

Ya ce: Waxannan Muhajirai kenan, kuma sun wuce. Sannan ya karanta:

Da waxanda suka yi tanadin gidaje da imani gabaninsu suna son waxanda suka yi hijira zuwa wurin su, ba su jin wata buqata a cikin zukatansu game da abin da aka ba su. Kuma suna fifita wasu (‘yan’uwansu) akan kawunansu. Kuma wanda duk ya kange ransa daga tsananin rowarta to, waxannan sune masu ribanta.

Sannan ya ce: Waxannan sune Ansaru. Kuma su ma sun wuce. Sannan ya karanta:

Kuma waxanda suka zo daga bayansu, suna cewa: “Ya Ubangijinmu! ka yi gafara a gare mu da kuma ga ‘yan’uwanmu waxanda suka riga mu yin imani. Kada ka sanya wani qulli a cikin zukatanmu ga waxanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Lalle kai ne mai tausayi, mai jinqai. Suratul Hashri: 8-10

Ya ce: Waxancan biyu sun wuce, wannan daraja ita ta rage, to ku kyautata ga abin da ku ka kasacewa, ko da kuna samun wannan darajar da ta saura; ku kasance kuna nema masu gafarar Allah.

Ibnu baxxa xin kuma ya riwaito daga Maliku xan Anas cewa: “Wanda duk ya zagi magabata ba za a ba shi ganimar mayaqa ba, domin ba shi da alhaki a cikinta. Saboda waccan ayar da ta gabata”.

Malamai da dama sun ta fi a kan haka game da fassarar ayar kamar Baban Ubaidu xan Sallamu da sauran su.

Kamar yadda Ibnu Abbas Raliyallahu Anhu ya ce: “Allah Ta’ala ya yi umurnin a nema ma Sahabbai gafara, alhali ya san yaqi zai auku a tsakaninsu”.

Ita kuma Nana Aisha cewa ta yi: “An umrce su, su nema ma Sahabbai gafara amma sai suna zagin su”. Tana nuni zuwa ga ‘yan Shi’ah.

A cikin Buhari da Muslim, Abi Sa’id Al-khudri ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Kada ku zagi Sahabbaina. Domin kuwa da xayanku zai ciyar da zinarin da ya kai girman dutsen Uhudu, ba zai kai mudun da xayansu ya ciyar ba ko ma rabinsa”. Kuma Muslim ya riwaito irinsa daga Abu Hurairata Raliyallahu Anhu.

Harwayau a cikin Sahihu Muslim daga Jabir xan Abdullahi ya ce: An ce ma Nana Aisha: Akwai mutanen da ke zagin Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har ma da Abubakar da Umar, sai ta ce: “Me kuke mamaki a cikin wannan? Ayyukansu ne suka yanke, Allah yana son kada ladarsu ta yanke, sai ya samar masu ita ta hanyar masu zagin su”.

Ibnu Baxxata ya riwaito da ingantaccen isnadi daga Abdullahi xan Abbas Raliyallahu Anhu ya ce: “Kada ku zagi Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Don Allah Ta’ala ya umurce mu da roqa masu gafara alhalin kuwa ya san yaqi zai auku tsakanin su”.

An kuma riwaito daga Abdullahi xan Umar na cewa: Kada ku zaki Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin zaman da xayansu ya yi awa xaya a tare da shi Sallallahu Alaihi Wasallama, yana taimakon sa ya fi aikin xayanku na shekara arbain. A riwayar waki’u sai ya ce: “Ya fi ibadar xayan ku har qarshen ransa.

Allah Ta’ala ya ce:

﴿لَّقَد رَضِيَ ٱللَّهُ عَنِ ٱلمُؤمِنِينَ إِذ يُبَايِعُونَكَ تَحتَ ٱلشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِم فَأَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ عَلَيهِم وَأَثَبَهُم فَتحا قَرِيبا١٨ وَمَغَانِمَ كَثِيرَة يَأخُذُونَهَا وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيما١٩﴾ الفتح: ١٨ - ١٩

Haqiqa Allah ya yarda da muminai a lokacin da suke yi maka mubaya’a a qarqashin itaciya. Kuma saboda ya san abin da ke cikin zukatansu sai ya saukar da natsuwa a kan su, kuma ya ba su nasara makusanciya. Da ganimomi masu yawa waxanda za su samu. Kuma Allah ya kasance Mabuwayi ne, mai Hikima.

﴿وَعَدَكُمُ ٱللَّهُ مَغَانِمَ كَثِيرَة تَأخُذُونَهَا فَعَجَّلَ لَكُم هَذِهِ وَكَفَّ أَيدِيَ ٱلنَّاسِ عَنكُم وَلِتَكُونَ ءَايَة لِّلمُؤمِنِينَ وَيَهدِيَكُم صِرَطا مُّستَقِيما٢٠ وَأُخرَى لَم تَقدِرُواْ عَلَيهَا قَد أَحَاطَ ٱللَّهُ بِهَا وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيء قَدِيرا٢١﴾ الفتح: ٢٠ - ٢١

Allah ya yi maka alqawarin ganimomi masu yawa waxanda za ku samu, sai ya gaggauta maku wannan, ya kuma hana mutane kai wa gare ku, don wannan ya zama abin lura ga muminai, ya kuma shiryar da ku ga hanya miqaqqiya. Da wasu (ganimomin) da ba ku da iko a kansu (yanzu), Allah ya kewaye da sanin su. Kuma Allah ya kasance mai iko ne akan kome. Suratul-fathi: 20-21

To, ga shi dai qarara Allah ya ba da labarin cewa, ya yarda da Sahabban Manzonsa, kuma ya ce, ya san abin da ke cikin zukatansu, wanda a sakamakonsa ne ya ba su nasara makusanciya.

Waxannan da Allah ya yarda da su sun qunshi duk waxanda suka yi mubaya’a a qarqashin bishiya ranar Hudaibiyyah. Kuma daga kansu aka ja layin magabata. Su ne waxanda Alqur’ani ya kira su magaba ta wurare da dama. Sauran Sahabbai kuwa suna girmama su akan gabacinsu. Su ne kuma suka naxa sayyidina Abubakar, sauran jama’a suka amince musu.

Yawan waxanda suka samu wannan sheda dai ya kai dubu xaya da dari huxu. Kuma su ne Sabiquna a cikin Alqur’ani.

Amma wasu malamai na ganin cewa, magabatan farko su ne waxanda suka yi sallah zuwa Alqibla biyu, ma’ana waxanda suka musulunta kafin sauya Alqibla daga Baitul-Maqdis zuwa Ka’aba. Amma wannan ra’ayin yana da rauni akan na farko domin waccan Alqibla ba ta da fifiko a kan wannan. Ba kuma su ne suka canja Alqibla don raxin kansu ba balle ya zama dalilin wani girma gare su. Ga shi kuma babu wani dalili na Shari’ah da ke nuna fifikon yin sallah ga Alqibla biyu, kamar yadda dalilai ke nuna fifikon waxanda suka ciyar, kuma suka yi jihadi kafin qarfin musulunci da yarjejeniyar Hudaibiyyah, da kuma fifikon yin mubaya’ar da suka yi a qarqashin itaciya.

Masana kuwa sun sani cewa, daga cikin magabatan na farko tilas akwai Abubakar da umar da Usmanu da Ali da Xalhatu da Zubairu. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi mubaya’a da hannunsa a maimakon Usman. Saboda shi ya aike shi wurin mushrikai a garin Makka, sai aka yi mubaya’ar ba ya nan. Kuma a dalilin Usmanun ne aka yi mubaya’ar, jin cewa an kashe shi.

Ya tabbata a cikin Sahihu Muslim daga Jabir xan Abdullahi Raliyallahu Anhu cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Babu wanda zai shiga wuta cikin waxanda suka yi mubaya’a a qarqashin itaciyar”. Allah Ta’ala ya ce;

﴿لَّقَد تَّابَ ٱللَّهُ عَلَى ٱلنَّبِيِّ وَٱلمُهَجِرِينَ وَٱلأَنصَارِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ فِي سَاعَةِ ٱلعُسرَةِ مِن بَعدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيق مِّنهُم ثُمَّ تَابَ عَلَيهِم إِنَّهُ بِهِم رَءُوف رَّحِيم١١٧﴾ التوبة: ١١٧

Haqiqa Allah ya gafarta wa Annabi da Muhajirai da Ansarai waxanda suka bi shi cikin lokacin tsanani, bayan zukatan wasu daga cikinsu sun kusa karkata. Sannan Allah ya yi gafara a kansu. Haqiqa Shi, mai yawan tausayi ne da rahama a kan su. Suratut Tauba: 117

 Allah ya haxa tsakanin Manzo da su wurin yafewa. Allah Ta’ala ya ce:

﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَهَدُواْ بِأَموَلِهِم وَأَنفُسِهِم فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَواْ وَّنَصَرُواْ أُوْلَئِكَ بَعضُهُم أَولِيَاءُ بَعض وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَم يُهَاجِرُواْ مَا لَكُم مِّن وَلَيَتِهِم مِّن شَيءٍ حَتَّى يُهَاجِرُواْ وَإِنِ ٱستَنصَرُوكُم فِي ٱلدِّينِ فَعَلَيكُمُ ٱلنَّصرُ إِلَّا عَلَى قَومِ بَينَكُم وَبَينَهُم مِّيثَق وَٱللَّهُ بِمَا تَعمَلُونَ بَصِير٧٢﴾ الأنفال: ٧٢

Haqiqa waxanda suka yi imani, kuma suka yi hijira ga jihadi da dukiyarsu da rayukansa a cikin tafarkin Allah da waxanda suka karvi baqunci (Muhajirai) kuma suka taimaka, to, waxannan sashensu majivinta sashe ne.. Suratull Anfal: 72

Zuwa inda Allah ya ce:

﴿وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِن بَعدُ وَهَاجَرُواْ وَجَهَدُواْ مَعَكُم فَأُوْلَئِكَ مِنكُم ﴾ الأنفال: ٧٥

Waxanda da suka yi imani suka kuma yi hijira da jihadi, to, waxannan suna cikinku. Suratul Anfal: 75

Sai Allah ya tabbatar da jivintar lamarin juna tsakaninsu. Kuma ya ce ma muminai:

﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ ٱليَهُودَ وَٱلنَّصَرَى أَولِيَاءَ بَعضُهُم أَولِيَاءُ بَعض وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُم فَإِنَّهُ مِنهُم إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهدِي ٱلقَومَ ٱلظَّلِمِينَ٥١﴾ المائدة: ٥١

Ya ku waxanda suka ba da gaskiya! kada ku riqi Yahudawa da Nasara masoya. Sashensu masu jivintan sashe ne. Kuma duk wanda ya jivinci lamarinsu daga cikin ku, to, haqiqa shi, yana daga cikinsu. Tabbas Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai. Suratul-Ma’ida: 51

Zuwa inda Allah ya ce:

﴿إِنَّمَا وَلِيُّكُمُ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوةَ وَيُؤتُونَ ٱلزَّكَوةَ وَهُم رَكِعُونَ٥٥ وَمَن يَتَوَلَّ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ فَإِنَّ حِزبَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلغَلِبُونَ٥٦﴾ المائدة: ٥٥ - ٥٦

Abin sani kawai, majivincinku Allah ne da Manzonsa, da waxanda suka yi imani, waxanda suke tsayar da sallah, kuma suna bayar da zakka, alhalin su masu ruku’i ne. Kuma duk wanda ya jivinci Allah da Manzonsa da waxanda suka yi imani, to, haqiqa rundunar Allah su ne masu galaba. Suratul Ma’ida: 55-56

Kuma Allah Ta’ala ya ce:

﴿وَٱلمُؤمِنُونَ وَٱلمُؤمِنَتُ بَعضُهُم أَولِيَاءُ بَعض ﴾ التوبة: ٧١

Muminai maza da muminai mata sashensu masu jivintar sashe ne. Suratut Tauba: 71

To, ka ga Allah ya tabbatar da soyayya a tsakaninsu, kuma ya umurci muminai da son su da jivintar su. ‘yan-sha-biyu kuwa sun barranta daga gare su; zagin su su ke. Jivinta kuwa ita ce soyayya, adawa ita ce kishiyar soyayya. Su kuwa adawa suke yi da su, suna qin su.

Wasu maqaryata sun qago wani hadisi cewa, wannan ayar ta sauka ne saboda Ali, a lokacin da ya yi sadaka da zobensa yana a cikin sallah. Masana hadisi sun haxu a kan cewa wannan hadisi qarya ne.

Don ka gane qaryar wannan hadisi yi nazarin waxannan abubuwa da za mu faxa:

1)  Ayar ta zo ne da sigar jam’i ba mutum guda ba.

2)  Kuma “alhali” da aka faxa a cikin ayar ba yana nufin yin sadaka lokacin sallar ba, ballantana ya zamo dalili. Da ya zama dalili kuwa, to, da sauran sha biyun ba su cancanci shugabancin ba, tunda ba su yi hakan ba.

3)  Ba a yaba ma mutum sai in ya aikata wajibi ko mustahabbi. Yin zakka a cikin sallah kuwa ba wajibi ba ne, ba mustahabbi ba. Ba ya ma cikin abubuwan da ke nuna natsuwa a cikin sallah.

4)  In da bayar da zakka a cikin sallah abu ne mai kyau, to, da ba za a samu banbancin wanda ya bayar yana ruku’i da wanda ya bayar yana tsaye ko zaune ba. Wataqila ma hakan ya fi yiwuwa.

5)  Zakka ba ta wajaba a kan Ali a lokacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba.[56]

6)  Bayar da zobe ba shi ne ya fi ba a wajen zakka. Mafi yawan malamai ma sun tafi a kan cewa, fitar da zobe ga zakka ba ya inganta.

7)  Wannan hadisin ya nuna an bayar da zakka ga mai bara. Abin yabo shi ne a fitar da zakka tun da farin, kuma da gaggawa idan lokacinta ya yi. Ba sai ya jira almajiri ya roqa ba.

8)  Hawan ayar da gangararta na magana ne akan jivintar musulmi da barin jivintar kafirai.

Nan gaba za mu yi cikakken bayani a kan wannan ayar in Allah ya so.

Su dai ‘yan Shi’ah yana da wuya su kafa hujja da wata aya face ta zama hujja a kan su. Kamar yadda suka kafa hujja da wannan aya cewa wilayana nufin shugabanci, sai ga shi an gano abin da take nufi soyayya da jivinta, kuma su, ba su so kuma ba su jivintar waxanda ayar ta ce a so kuma a jivinta.

‘Yan Shi’ah, cikinsu har da Isma’iliyyah da na Nusairiyyah suna bayyana jivintar kafirai kamar Yahudawa da Nasara da Munafikai. Suna Qin Muhajiruna da Ansaru da waxanda suka biyo bayansu da kyautatawa har ranar qiyama. Wannan sanannen abu ne ga wanda ya nazarce su.

Kuma Allah Ta’ala yana cewa:

ﭽ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ حَسۡبُكَ ٱللَّهُ وَمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِن ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٦٤ ﭼ الأنفال: ٦٤

Ya kai Annabi Allah ya ishe ka da waxanda suka bi ka daga cikin muminai. Suratul Anfal: 64.

Abin nufi shi ne Allah ya isheka kuma ya ishi waxanda suka bi ka daga cikin muminai, Sahabbai su ne mafifitan waxanda suka bi Manzo daga cikin muminai kuma sune na farko.

Kuma Allah Ta’ala yana cewa:

﴿إِذَا جَاءَ نَصرُ ٱللَّهِ وَٱلفَتحُ١ وَرَأَيتَ ٱلنَّاسَ يَدخُلُونَ فِي دِينِ ٱللَّهِ أَفوَاجا٢ فَسَبِّح بِحَمدِ رَبِّكَ وَٱستَغفِرهُ إِنَّهُ كَانَ تَوَّابَا٣﴾ النصر: ١ - ٣

Idan nasarar Allah ta zo da buxi. Har ka ga mutane na ta shiga addinin Allah jama’a-jama’a. To, ka yi tasbihi da godiyar Allah. Haqiqa shi mai yawan karvar tuba ne. Suratun-nas: 1-3.

Waxanda Manzo ya ga sun shiga addinin Allah jama’a jama’a su ne waxanda suka kasanse a zamaninsa, Sahabbai kenan.

Allah Ta’ala kuma ya ce;

﴿وَإِن يُرِيدُواْ أَن يَخدَعُوكَ فَإِنَّ حَسبَكَ ٱللَّهُ هُوَ ٱلَّذِي أَيَّدَكَ بِنَصرِهِ وَبِٱلمُؤمِنِينَ٦٢ وَأَلَّفَ بَينَ قُلُوبِهِم لَو أَنفَقتَ مَا فِي ٱلأَرضِ جَمِيعا مَّا أَلَّفتَ بَينَ قُلُوبِهِم وَلَكِنَّ ٱللَّهَ أَلَّفَ بَينَهُم إِنَّهُ عَزِيزٌ حَكِيم٦٣﴾ الأنفال: ٦٢ - ٦٣

Idan har (Kafirai) sun yi nufin su yaudare ka , to, Allah Ya ishe ka. Shi ne ya qarfafa ka da nasararSa da kuma muminai. Kuma ya daidaita tsakanin zukatansu. Suratul-Anfal: 62-63.

Abin da kowa ya sani ne cewa, Allah ya qarfafa Manzonsa ne da Sahabbai a lokacin rayuwarsa.

Allah Ta’ala kuma ya ce:

﴿وَٱلَّذِي جَاءَ بِٱلصِّدقِ وَصَدَّقَ بِهِ أُوْلَئِكَ هُمُ ٱلمُتَّقُونَ٣٣ لَهُم مَّا يَشَاءُونَ عِندَ رَبِّهِم ذَلِكَ جَزَاءُ ٱلمُحسِنِينَ٣٤ لِيُكَفِّرَ ٱللَّهُ عَنهُم أَسوَأَ ٱلَّذِي عَمِلُواْ وَيَجزِيَهُم أَجرَهُم بِأَحسَنِ ٱلَّذِي كَانُواْ يَعمَلُونَ٣٥﴾ الزمر: ٣٣ - ٣٥

Wanda ya zo da gaskiya, kuma (da wanda) ya gasganta shi, waxannan ne masu tsoron Allah. Suna da abin da suke so wurin Ubangijinsu. Wannan shi ne sakamakon masu kyautatawa. Domin (Allah) Ya yafe masu mafi munin ayyukansu, kuma ya saka masu da mafi kyawon abin da suka kasance suna aikatawa. Suratuz-Zumar: 33-35.

Wannan nau’i da Allah ya faxi na mutane masu faxin gaskiya da waxanda ke gasgatawa, su savanin masu qirqiro qarya ne ko su qaryata gaskiya a lokacin da ta zo masu kamar yadda za mu fayyace wannan a nan gaba in Allah ya so.

Sahabbai da suka kasance suna shedar cewa, babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, kuma suka shedi annabtar Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama, duka gasgata Alqur’ani, su ne suka fi kowa shiga cikin ayar da ke maganar masu gaskiya da gasgatawa. Babu kuwa wasu jama’a da ke da’awar musulunci da suka fi ‘yan Shi’ah yi wa Allah qarya da kuma qaryata gaskiya. Babu kuma wanda ya fi su wuce makaxi da rawa a wajen so da qi kamar su.

Cikinsu ne aka samu waxanda ke xaukaka mutum har su kai shi matsayin Allah. Da waxanda ke jingina annabta ga wanda ba Annabi ba. Ga su da qaryar ma’asumanci ga waxanda ba Annabawa ba. Da ire-iren waxannan abubuwa na miyagun aqidodin da ba a samun su ga sauran qungiyoyi. Malamai sun haxu a kan cewa, ba wata qungiyar da qarya ta zame ma ruwan–dare kamar Shi’ah.

Kuma Allah Ta’ala ya ce:

﴿قُلِ ٱلحَمدُ لِلَّهِ وَسَلَمٌ عَلَى عِبَادِهِ ٱلَّذِينَ ٱصطَفَى ءَاللَّهُ خَيرٌ أَمَّا يُشرِكُونَ٥٩﴾ النمل: ٥٩

Ka ce: Godiya ta tabbata ga Allah, kuma aminci ya tabbata ga zavavvun bayinsa. Shin Allah Shi ya fi, ko abin da kuke shirka da shi. Suratun-namli: 59.

Wasu magabata sun ce: Ayar na nufin Sahabban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Ba shakka kuwa su ne mafifita daga cikin waxanda aka zava a cikin wannan Al’umma, waxanda Allah ya ce game da su:

﴿ثُمَّ أَورَثنَا ٱلكِتَبَ ٱلَّذِينَ ٱصطَفَينَا مِن عِبَادِنَا فَمِنهُم ظَالِم لِّنَفسِهِ وَمِنهُم مُّقتَصِد وَمِنهُم سَابِقُ بِٱلخَيرَتِ بِإِذنِ ٱللَّهِ ذَلِكَ هُوَ ٱلفَضلُ ٱلكَبِيرُ٣٢ جَنَّتُ عَدن يَدخُلُونَهَا يُحَلَّونَ فِيهَا مِن أَسَاوِرَ مِن ذَهَب وَلُؤلُؤا وَلِبَاسُهُم فِيهَا حَرِير٣٣ وَقَالُواْ ٱلحَمدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي أَذهَبَ عَنَّا ٱلحَزَنَ إِنَّ رَبَّنَا لَغَفُور شَكُورٌ٣٤ ٱلَّذِي أَحَلَّنَا دَارَ ٱلمُقَامَةِ مِن فَضلِهِ لَا يَمَسُّنَا فِيهَا نَصَب وَلَا يَمَسُّنَا فِيهَا لُغُوب٣٥﴾ فاطر: ٣٢ - ٣٥

Sannan muka gadar da littafe ga waxanda muka zava daga cikin bayinMu. Daga cikinsu akwai mai zaluntar kansa, kuma daga cikinsu akwai mai tsa kaitawa, kuma daga cikinsu akwai mai gaggautawa zuwa ayyukan alheri da izinin Allah. To, wannan ita ce babbar falala. (Akwai) Aljanna ta tabbata wadda suna shigar ta, ana qawata su a ciki da mundaye na zinari da lu’u’lu’i, kuma alhariri ne abin sawarsu. Suka ce godiya ta tabbata ga Allah wanda ya kuranye muna baqin ciki. Haqiqa Ubangijinmu mai yawan gafara ne da godiya.Wanda ya saukarda mu a gidan zama (mai daxi) daga cikin falalarSa. Ba wata wahala da za ta shafe mu a ciki, ba kuma gajiya. Suratu-Faxir: 32-35

Al’ummar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ita ce aka zava a bayan shuxewar Yahudawa da Nasara waxanda su ne al’ummomi biyu da aka yi gabanin ita wannan al’umma.

Hadisi mutawatiri ya zo da cewa: Mafifitan shi ne qarnuka shi ne qarnin da nake cikin sa. Sannan masu biyar su, sannan waxanda suka zo bayan su. Ka ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Sahabbansa sune zavavvu kenan daga cikin bayin Allah.

Allah Ta’ala kuma ya ce :

ﭽ مُّحَمَّدٞ رَّسُولُ ٱللَّهِۚ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ أَشِدَّآءُ عَلَىٰٰٰٰٰٰٰٰ ٱلۡكُفَّارِ رُحَمَآءُ ﭛﭼ الفتح: ٢٩

Muhammadu Manzon Allah ne. Waxanda ke tare da shi kuma masu tsanani ne akan kafirai, masu rahama a tsakaninsu. Suratul-Fathi: 29.

Allah Ta’ala ya kuma ce :

﴿وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُم وَعَمِلُواْ ٱلصَّلِحَتِ لَيَستَخلِفَنَّهُم فِي ٱلأَرضِ كَمَا ٱستَخلَفَ ٱلَّذِينَ مِن قَبلِهِم وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُم دِينَهُمُ ٱلَّذِي ٱرتَضَى لَهُم وَلَيُبَدِّلَنَّهُم مِّن بَعدِ خَوفِهِم أَمنا يَعبُدُونَنِي لَا يُشرِكُونَ بِي شَيا وَمَن كَفَرَ بَعدَ ذَلِكَ فَأُوْلَئِكَ هُمُ ٱلفَسِقُونَ٥٥﴾ النور: ٥٥

Allah ya yi ma waxanda suka yi imani da ayyuka na gari daga cikin ku alqawarin ba su shugabanci a bayan qasa, kamar yadda ya ba waxanda suka gabace ku. Kuma zai tabbatar masu da addininsu wanda (Allah) Ya yardar masu. Kuma zai musanya halin tsoron da suke a kai zuwa halin aminci. Suna bauta maNi, ba su yi maNi tarayya da kowa. To, wanda duk ya kafirta bayan haka, to, waxancan su ne fasiqai. Suratun-Nur: 55.

To, ga shi dai Allah ya yi alqawari ga waxanda suka yi imani da ayyuka na gari zai basu shugabanci a bayan qasa kamar yadda ya yi masu alqawarin gafara da lada mai yawa cikin waxancan ayoyin. Allah kuwa ba ya sava alqawari.

To, kuma Allah ya riga ya shugabantar da su kamar yadda ya shugabantar da waxanda suka gabace su xin, ya samar masu da aminci bisa alqawarinsa daidai-wa-daida. Abin da ya rage shi ne cikon alqawarin nasa na yi masu gafara da basu lada mai girma. Kuma tabbas, Allah zai qarasa cika alqawarinsa.

Waxannan ayoyi ana kafa hujja da su ta fuska biyu: 1) Cewa, waxanda aka ba shugabancin muminai ne kuma sun yi ayyuka na gari. 2) Kuma an gafarta masu, za a basu sakamako da lada mai girma don sun yi imani kuma sun yi ayyuka na gari. Waxannan su ne alqawurran da Allah ya yi a Suratun-Nur da kuma Suratul-Fathi.

Sanannen abu ne cewa waxannan sifofin da Allah ya ambata sun dace da na Sahabbai a zamanin halifancin Abubakar da umar da Usmanu saboda dai a wannan lokacin ne aka samu cikakken shugabancin da ya tabbatar da addini, da kuma aminci bayan tsoro. Aka sami galaba a kan mafi girman qasashen kafirci: Farisa da Roma. Aka buxe qasar Sham da Iraqi da Masar da Khurasana da yammacin Afirka.

A lokacin da aka kashe Usmanu sai aka samu fitina. Ba a sake buxe wani gari ko xaya ba na kafirai. Kai a lokacin ma kafirai suka yi kwaxayin kama qasashen musulmi, cikinsu har da Sham da Khurasana. Musulmi suka koma barazana ga junansu.

Wannan ya nuna imanin Abubakar da umar da Usmanu da waxanda ke tare da su a lokacin da aka tabbatar da su a bayan qasa, a ka ba su shugabanci. Suka kuma sami aminci. Waxanda ke tare da halifofin uku kuma suka riski lokacin fitina, ayar harwayau tana nuni ga imaninsu. Kamar su: Ali da Xalhatu da Abu Musal-Ash’ari da Mua’wiyah da Amru xan Asi. Domin suna cikin musulmin da Allah ya ba shugabanci, ya tabbatar masu da addini, kuma ya ba su aminci tun da farko.

Amma waxanda farkon lamarinsu ya fara ne a lokacin fitina da rarrabuwar kan musulmi kamar ‘yan Shi’ah da Harijawa masu saurin ficewa daga cikin musulunci, to, waxannan ba su shiga cikin ayar ba, ba su kuma cikin waxanda aka siffanta da imani da ayyuka na gari.

Kuma su waxannan ba a shugabantar da su ba, ba a kuma tabbatar da su ba, ba su kuma sami aminci bayan tsoro ba kamar yadda Sahabbai suka kasance. Haqiqanin lamarinsu shi ne, ba su gushe ba suna cikin tsoro da fargaba da rashin tabbas a rayuwa.

Wani zai iya tambaya: Me ya sa a ayar Suratul Fathi Allah ya ce: Ya yi alqawari ga waxanda suka yi imani da ayyuka na gari daga cikin ku.. Bai ce ya yi musu alqawari dukansu ba?

Haka ma kuma a ayar Suratul Ma’ida cewa Allah ya yi: Ya yi ma waxanda suka yi imani daga cikinku kuma suka yi ayyuka na gari alqawari..

Wannan a Larabce shi ake kira bayanin jinsi. An zo da shi don a nuna duk siffofin can nasu ba su ne dalilin gafarar su kaxai ba. Imaninsu dai ne da ayyukan qwarai su ne dalilin samun gafarar da suka yi. A haka kenan ana iya samun waxanda za su yi koyi da su, su ma su samu gafara da lada mai girma.

Kamar yadda Allah Ta’ala ya ce:

﴿ فَٱجتَنِبُواْ ٱلرِّجسَ مِنَ ٱلأَوثَنِ ﴾ الحج: ٣٠

Ku nisanci qazanta daga cikin gumaka. Suratul-Hajji: 30.

Wannan bai nufin cewa, akwai gumaka da ba su da qazanta. A’a yana nufin jinsin gumaka jinsi ne mai qazanta. Wannan yana da misalai da yawa a Alqur’ani da tsantsar harshen Larabawa

Haka ma wani zai iya cewa: Ai munafukai a zahiri suna cikin musulmi.

Sai a ce: Eh. Amma ba su siffantu da waxannan siffofin ba. Yaushe ne munafukai suka zamo masu rahama ga musulmi da tsanani akan kafirai, ko suka nace akan yawan ruku’i da sujada don neman yardar Allah? Kai, asali ma ayar tana maganar waxanda ke tare da Manzon Allah ne, su ko munafukai ba su tare da shi, ba su kuma cikin muminai. Kamar yadda Allah Ta’ala ya ce:

﴿فَتَرَى ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَض يُسَرِعُونَ فِيهِم يَقُولُونَ نَخشَى أَن تُصِيبَنَا دَائِرَة فَعَسَى ٱللَّهُ أَن يَأتِيَ بِٱلفَتحِ أَو أَمر مِّن عِندِهِ فَيُصبِحُواْ عَلَى مَا أَسَرُّواْ فِي أَنفُسِهِم نَدِمِينَ٥٢ وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ أَهَؤُلَاءِ ٱلَّذِينَ أَقسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهدَ أَيمَنِهِم إِنَّهُم لَمَعَكُم حَبِطَت أَعمَلُهُم فَأَصبَحُواْ خَسِرِينَ٥٣﴾ المائدة: ٥٢ - ٥٣

Zai yiwu Allah ya zo da wani buxi ko wani al’amari daga wurinSa, sai (munafikai) su wayi gari suna masu nadama a kan abin da suka voye cikin zukatansu. Kuma waxanda suka yi imani na cewa, shin waxancan ne suka yi mafi girman rantsuwa cewa, lalle suna tare da ku? Ayyukansu sun lalace, sai suka wayi gari suna masu hasara. Suratul-Ma’ida: 52

Kamar kuma cewar da Allah Ta’ala ya yi:

﴿وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ فَإِذَا أُوذِيَ فِي ٱللَّهِ جَعَلَ فِتنَةَ ٱلنَّاسِ كَعَذَابِ ٱللَّهِ وَلَئِن جَاءَ نَصر مِّن رَّبِّكَ لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُم أَوَ لَيسَ ٱللَّهُ بِأَعلَمَ بِمَا فِي صُدُورِ ٱلعَلَمِينَ١٠ وَلَيَعلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَيَعلَمَنَّ ٱلمُنَفِقِينَ١١﴾ العنكبوت: ١٠ - ١١

Daga cikin mutane akwai masu cewa, mun yi imani da Allah. Amma idan aka cutar da su a tafarkin Allah sai su mayar da fitinar mutane kamar azabar Allah. To, kuma wallahi inda wata nasara ta zo daga Allah haqiqa za su ce, lalle mun kasance tare da ku. To, shin Allah bai san abin da ke cikin zukatan dukan talikai ba? Wallahi Allah ya san waxanda su ka yi imani. Kuma wallahi ya san munafukai. Suratul Ankabut: 10-11

Ka ga waxannan ayoyin sun bayyana maka cewa, su munafukai ba su cikin muminai, ba su kuma cikin ma’abuta littafi.

Babu dai inda zaka sami munafunci ya yi katutu kamar cikin Shi’ah ‘yan-sha-biyu. Sun fi koya raya musulunci a zahiri, amma suna amfani da wannan suna cutar musulunci da musulmi.

Kuma munafukai a wancan lokaci da yawansu sun tuba, sun gyara zamansu, sun shiga sahun muminai, bayan da Allah ya fallasa su, ya bayyana siffofinsu, ya kuma yi razani a kansu in ba su daina ba. Duba abin da Allah Ta’ala ya ce masu:

﴿لَّئِن لَّم يَنتَهِ ٱلمُنَفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَض وَٱلمُرجِفُونَ فِي ٱلمَدِينَةِ لَنُغرِيَنَّكَ بِهِم ثُمَّ لَا يُجَاوِرُونَكَ فِيهَا إِلَّا قَلِيلا٦٠ مَّلعُونِينَ أَينَمَا ثُقِفُواْ أُخِذُواْ وَقُتِّلُواْ تَقتِيلا٦١﴾ الأحزاب: ٦٠ - ٦١

Wallahi in munafukai da waxanda ke da cuta a cikin zukatansu da masu yin varna a Madina ba su daina ba, za mu baka iko a kansu. Sannan ba za su sake yin maqwabtaka da kai a cikin ta ba, sai kaxan. (Su) la’anannu ne, a duk wurin da aka same su za a kama su a karkashe su kashewa. Suratul-Ahzab: 60-61

Idan muka duba wannan razani da Maxaukakin Sarki ya yi a kansu, muka kuma ga bai ba Manzonsa dama akan kama su da karkashe su ba, bai kore su daga Madina ba, mun san cewa, sun tuba, sun daina munafucci kenan. Ko banza dalilin munafucci ya riga ya kau, don addini ya xaukaka, babu sauran wanda za a goya ma baya sai gaskiya.

A lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya je Hudaibiyyah duk waxanda ke tare da shi sun yi masa mubaya’a qarqashin itaciya sai Jaddu xan Qaisu. Shi ne ya je ya vuya a bayan wani jan raqumi. Haka ya zo cikin hadisi cewa, dukkansu za su shiga aljanna sai na wancan na wajen jan raqumi.

A taqaice dai, munafikai sun kasance qasqantattu, waxanda ake da rinjaye a kansu, musamman ma a qarshen rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma lokacin yaqin Tabuka. Don Allah Ta’ala ya ce:

﴿يَقُولُونَ لَئِن رَّجَعنَا إِلَى ٱلمَدِينَةِ لَيُخرِجَنَّ ٱلأَعَزُّ مِنهَا ٱلأَذَلَّ وَلِلَّهِ ٱلعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِ وَلِلمُؤمِنِينَ وَلَكِنَّ ٱلمُنَفِقِينَ لَا يَعلَمُونَ٨﴾ المنافقون: ٨

Suna cewa: “Wallahi idan mun koma Madina masu xaukaka za su fitar da qasqantattu daga cikinta”. Xaukaka kuwa ta tabbata ga Allah da Manzonsa da muminai, amma munafukai ba su sani ba. Suratul-Munafiqun: 8.

Sai Allah Ta’ala ya ba da labarin cewa, xaukaka ta muminai ce ba ta munafikai ba. Daga nan muka san cewa, xaukaka da qarfi na tare da muminai ne, kuma muka gano qasqanci da wulakancin da munafukai su ke cikin sa. Saboda haka ba zai yiwu Sahabbai su zamo munafukai ba.

Sanannen abu ne cewa, shiryayyun halifofi da manyan Sahabbai na cikin mafi xaukakar mutane a wancan lokaci. Ka ga kenan ba zai yiwu su zamo munafukai ba. Qasqanci da wulaqancin da munafukai ke ciki shi ya yi daidai da halin ‘yan-sha-biyu waxanda, babu wata qungiya mai jingina kanta ga musulunci wadda zindiqanci da munafunci suka kai yawan na Shi’ah a cikin ta.

Kai ma tilas ne ka tarar da xayan alamomin munafunci cikinsu. Domin tushen munafunci shi ne qarya. Su kuma sun gina addininsu ne a kanta, da sunan Taqiyyah. Taqiyyah ko tana nufin mutum ya furta savanin abin da ke cikin zuciyarsa. Shi’ah ‘yan-sha-biyu sun mayar da wannan xaya daga cikin asullan addininsu, har ma suna rawaito wannan daga shugabanin Ahlul-Baiti waxanda Allah ya barrantar da su daga wannan. Kamar yadda suka hikaito wannan daga Ja’afar As-Sadiq cewa wai, ya ce: “Taqiyya addinina ce, kuma addinin iyayena”. Allah Ta’ala kuwa ya tsarkake Ahlul-Baiti da sauran muminai daga wannan. Ahlul-Baiti kam sun fi kowa gaskiya da imani. Taqawa ita ce addininsu ba Taqiyya ba.

Abu ne mai yiwuwa ‘yan Shi’ah su kafa hujja a kan wannan aqida tasu da cewa, ai Allah Ta’ala ya ce:

﴿لَّا يَتَّخِذِ ٱلمُؤمِنُونَ ٱلكَفِرِينَ أَولِيَاءَ مِن دُونِ ٱلمُؤمِنِينَ وَمَن يَفعَل ذَلِكَ فَلَيسَ مِنَ ٱللَّهِ فِي شَيءٍ إِلَّا أَن تَتَّقُواْ مِنهُم تُقَىة وَيُحَذِّرُكُمُ ٱللَّهُ نَفسَهُ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلمَصِيرُ٢٨﴾ آل عمران: ٢٨

Kada muminai su xauki kafirai majivinta lamurransu koma bayan muminai. Kuma wanda ya aikata haka shi ba kome ne ba a wurin Allah, sai fa in kun ji tsoron su don ku kiyayi cutarsu. Suratu Ali-Imran: 28

 Amsar da za mu ba su a nan ita ce, ai idan aka dubi wannan aya da kyau, tare da la’akari da dalilin saukarta, da sauran hukunce-hukuncen shari’ah, to, za a fahimci cewa, ba tana halasta wa muminai yin qarya da munafucci ba. Ko alama. Ta dai ba su damar kariyar kansu ne daga kafirai a lokacin da wani al’amari ya kai mashafar turare. Ya halasta ga musulmi bisa wannan qa’ida ya furta kalmar kafirci alhalin zuciyarsa na tsattsage da imani. Amma da sharaxin an tilasta shi a kan haka. Savanin abin da ya faru tsakanin Sahabbai da Ahlul-Baiti. Tarihi ya tabbatar da cewa, babu wanda ya yi wa Abubakar mubaya’a a kan tilas. To, ballantana a tilasta wani akan yabonsa. Ka ga kuwa sayyidina Ali da ‘yan gidan annabta da dama sun bayyanar da yabon halifa Abubakar da sauran Sahabbai, sun kuma yawaita du’ai gare su. Wa zai tilasta masu yin haka?

Ko a zamanin Banu Umayyah da Banul Abbas akwai ‘yan adawa da dama waxanda basu kama qafar Aliyu ba ta fuskar imani da tsoron Allah. Suna tsanar shugabannin lokacinsu saboda nasu dalilai, kuma ba su fitowa su yabe su don jin tsoronsu, amma sun rayu a cikin cikakken ‘yanci da walwala, ba a xauki kowane mataki a kansu ba. To, balle zamanin halifofi shiryayyu.

Daga nan za mu san cewa abin da Shi’ah ‘yan-sha-biyu ke faxa cewa su faxi abin da ba ya cikan zukatansu ba tare da wata tilastawa da aka yi masu ba, yana xaya daga cikin hanyoyin qarya da munafunci. Ga dai ko fursunonin yaqi, kafirai, ba wanda ya tava hana su bayyana addininsu a qasashen musulmin da suka kamo su. Haka su ma Harijawa, duk da aqidarsu ta kafirta sayyidina Usman da sayyidina Ali da sauran musulmi, ba su tava voye aqidarsu ko wani sarki ya tilasta su yin haka ba.

To, ya za a zaci Ali da sauran Ahlul-Baiti sun fi fursunonin yaqi raunin zuciya da imani, kuma Harijawa da xaixaikun Ahlus-Sunnah duk sun fi su qarfin hali da dauriyar bayyana abin da ke cikin zukatansu? Mu mun sani ta hanyar ilimi mutawatiri cewa, babu wanda ya tilasta wa Ali da ‘ya’yansa ambaton darajojin halifofi da nema masu rahamar Allah. A’a, sun dai kasance suna faxain wannan ba tare da an tilasta su ba, kuma xayansu na yin wannan yabon a gaban makusantansa, kamar yadda wannan ya tabbata ta hanyar ilimi mutawatiri.

A taqaice dai, duk maganar da ke cikin Alqur’ani wadda ta shafi muminai da masu taqawa da masu kyautatawa da yabonsu, su- Sahabbai- ne farkon waxanda ke shiga ciki daga cikin wannan al’umma. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Mafifitan qarnuka shi ne qarnin da aka aiko ni cikinsa, sannan waxanda ke bi masu, sannan waxanda ke bi masu.

Wani abu kuma da ke bayyana maka qaryar wannan xan Shi’ar shi ne, abin da ya riwaito game da halayyar Sahabbai bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa wai, wasu sun nema ma kansu shugabanci ba tare da suna da alhaki cikinsa ba, kuma mafi yawan mutane suka yi masu mubaya’a don son abin duniya.

Wannan maganar tasa da Abubakar Raliyallahu Anhu ya ke babu shakka. Domin shi ne mafi yawan mutane suka yi ma mubaya’a. kuma sanannen abu ne cewa, Abubakar bai nema ma kansa shugabanci ba, ko ta wace hanya. Abin da ma ya ce shi ne, na yardar maku da xayan mutanen nan biyu: Umar ko Abu Ubaida, duk wanda kuke so. A nan ne Umar ya ce: Wallahi da in shugabanci mutanen da Abubakar ke cikinsu na fi son in miqa wuyana a sare shi in dai wannan ba zai kusantar da ni ga savon Allah ba”. Wannan lafazinsa ne a cikin Sahihul Buhari da Sahihu Muslim. An kuma riwaito yana cewa: “Ku xauke mani wannan nauyi! Ku xauke mani wannan nauyi! Amma musulmi sun zave shi kuma sun yi masa mubaya’a don sun san cewa shi ne mafifici a cikinsu. Kamar yadda Umar ya ce musu ranar Saqifa a gaban Muhajiruna da Ansaru: “Kai ne shugabanmu, kuma wanda ya fi soyuwa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga cikin mu. Wannan ma yana cikin Sahihul Buhari da Muslim.

To, mu qaddara ma halifa Abubakar ya nemi wannan shugabanci, aka kuma ba shi, to, ko a haka, qarya ce tabbatatta a ce ya ba su abin duniya, kuma a kansa ne suka yi masa bai’a.

Dalilinmu a kan haka kuwa shi ne, koda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwanta dama Abubakar Raliyallahu Anhu duk ya qarar da dukiyarsa wurin taimakon addini. Kuma babu baitulmali a qarqashinsa balle a ce. Qari a kan haka, kuma sahabban da suka yi masa bai’a har da Ali Raliyallahu Anhu mutane ne da ba a yi masu gudun duniya kamar su ba.

A siyasar sayyidina Abubakar gwamnati tana raba kuxi ne daidai ga mutane. Ba a fifita kowa a kan wani. Wannan kuma ita ce siyasar Ali Raliyallahu Anhu a lokacinsa. Don haka, da ma sun yi wa Aliyu mubaya’a da abin da zai yi shi ne daidai abin da Abubakar ya yi. Kuma arzikin da za su samu shi xin ne. to, ya za a ce sun zave shi don abin duniya?

A siyasar Umar akan raba dukiyar gwamnati ne ga mutane daidai kusancinsu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma qoqarin da suka gabatar wajen kafa addini. Lokacin da Umar ya ba da shawarar yin haka ga Abubakar sai ya ce masa: Zan sayi imaninsu ne daga gare su?

To, wace dukiya ce mafi yawan musulmi suka samu don sun yi wa Abubakar mubaya’a? Tunda yake yana daidaitawa wurin ba da kyauta a tsakanin musulmin farko da waxanda suka shiga musulunci daga baya? Abubakar ya kasance yana cewa, sun shiga musulunci ne saboda Allah, kuma shi zai saka masu. Amma kuxin masarufi to, abin amfani ne kowa na da buqata da shi.

Ga shi kuwa Mahajiruna da Ansaru da waxanda suka kyautata bin sawunsu irin su Umar da Abu Ubaidata da Usaidu xan Hudairu da sauransu, duk Abubakar bai banbanta su ba da waxanda aka xiyauta da waxanda suka musulunta cikin mutanen Makka bayan an bude ta, kai har ma waxanda suka musulunta bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Shin ko waxannan sun sami wani abin duniya saboda shugabancin Abubakar?

Anan yana da kyau mu bayyana wata qa’ida wadda zata taimaka a fagen jayayya da Shi’ah ‘yan-sha-biyu waxanda suke zargin magabatan Sahabbai, musamman halifofi guda uku. Wannan qa’idar ita ce:

Savanin da ke tsakanin Ahlus-Sunnah da Shi’ah ‘yan-sha-biyu yana da matuqar kama da savanin da ke tsakanin musulmi da Kirista. Mu musulmi, mun yi imani da cewa Isa Alaihis Salamu bawan Allah ne, kuma Manzonsa. Ba mu wuce wuri game da shi kamar yadda Kirista ke yi. Ba mu kuma yi masa jafa’i kamar yadda Yahudawa ke yi.

Kirista na raya cewa, Isa Alaihis Salamu abin bauta ne. Sun fifita shi a kan Annabawa: Muhammadu da Ibrahimu da Musa da sauran su. Kai ma har ma suna fifita Sahabban Isa Alaihis Salamu a kan waxannan Manzanni. Haka Shi’ah ‘yan-sha-biyu ke son fifita waxanda suka yi yaqi a zamanin fitina tare da sayyidina Ali kamar su Muhammadu xan Abubakar da Ashtar An-Nakha’i a kan manyan Sahabban Annabi irin Abubakar da Umar da Usmanu da dukkan Muhajiruna da Ansaru.

To, a wajen jayayya, idan musulmi ya tattauna da Kirista ba zai iya faxin wani abu game da Isa Alaihis Salamu ba face gaskiya. Amma in kana son ka fito da jahilcin Kirista da rashin hujjarsa, to, sai ka qaddara jayayyar a tsakanin sa da Bayahude, ka koma gefe ka saurare shi. Idan har Kirista ba zai iya kare Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba, to, duk zargin da ya yi masa zai tarar Bayahude yana yi wa Annabi Isah Alaihis Salamu irin sa. Kuma duk hujjar da zai kawo don ya kare Annabi Isah Alaihis Salamu wannan hujjar ta fi kare Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama daga shi nasa zargin. Saboda haka, in zargin da Bayahude yake yi wa Annabi Isah Alaihis Salamu qarya ne, to, zargin Kirista ga Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi zama qarya.

Wannan ya tava faruwa a tsakanin malaman Kiristoci da wani malami musulmi shi ne, Alqali Abubakar At-Tabarani. A lokacin da musulmi suka aika masa da gayyata don ya zo fadar wani sarki na Kirista a Qusxanxiniya (Istanbul). Malaman na Kirista sun san girmansa, kuma suna jin tsoron cewa, ba zai yi sujada ga sarkinsu ba idan ya shiga wurinsa. Don haka sai suka shigar da shi ta wata gajeruwar qofa don ya shiga a sunkuye. Nan take sai malamin ya fahimci manufarsu. Sai ya juya ya shiga qofar da baya, ya sanya kuturinsa kamar shi ne mai gaida sarkin. Abin da ya faru anan sai ya zama akasin abin da suke nufi.

Zaunawar malamin ke da wuya sai wani daga cikin fada-fadansu ya tambaye shi: “Mene ne ya faru game da matar mai gidanku”? Yana nuni da habaici ga qazafin da munafukai suka yi wa Nana Aishah, kuma harwayau da yawan ‘yan Shi’ah suna ci gaba da yi mata wannan qazafin.

Amsar da malam Abubakar ya ba fadan Kirista a nan ita ce, ya ce masa: “Ai su biyu ne maqiyan Allah suka yi wa zargi da Zina; Maryam da Aishah. Amma Maryam ta haifi xa ba tare da tana da miji ba. Ita kuma Aishah ba ta haifi xa ba kodayake tana da miji”.

Ka ga a nan ya xaure su. Don haka, sai suka yi tsit kamar ruwa ya ci su. Abin nufinsa shi ne, barrantar Nana Aisha game da wannan qazafin ya fi qarfi qwarai, a kan barrantar Maryam, duk da yake ita ma wankakkiya ce. Don shubuha ta fi qarfi a game da lamarinta, to, in duk da haka ya tabbata cewa masu sukar Maryam qarya ce suke yi, to, tabbatar qaryarsu a game da sukar da aka yi wa Aisha Raliyallahu Anha ta fi qarfi.

Makamancin wannan ne, Allah Ta’ala ya yi wa mushrikai in da yake cewa:

﴿يَسَلُونَكَ عَنِ ٱلشَّهرِ ٱلحَرَامِ قِتَال فِيهِ قُل قِتَال فِيهِ كَبِير ﴾ البقرة: ٢١٧

Suna tambayar ka game da yaqi a cikin watan da aka haramta, ka ce yaqi a cikin babban laifi ne. Suratul Baqarati: 217

Sannan ya ce:

﴿ وَصَدٌّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَكُفرُ بِهِ وَٱلمَسجِدِ ٱلحَرَامِ وَإِخرَاجُ أَهلِهِ مِنهُ أَكبَرُ عِندَ ٱللَّهِ وَٱلفِتنَةُ أَكبَرُ مِنَ ٱلقَتلِ ﴾ البقرة: ٢١٧

Amma kange mutane daga hanyar Allah da kafirce ma Allah da (hana mutane isa) masallaci mai Alfarma da fitar da mazaunansa daga ciki, (wannan) ya fi girman laifi a wurin Allah. Kuma fitinar da mutane (don su bar addini) ya fi kisa girman laifi. Suratul Baqarati: 217

Wannan ayar ta sauka ne a lokacin da mushrikai suka aibanta musulmin da suka kashe Ibnul Hadrami, cikin xaya daga cikin watanni masu alfarma, sai Allah ya ce, wannan laifin da waxannan musulmi suka yi yana da girma, amma abin da mushrikai suke a kai na kafirci da kange mutane daga addini da fitar da musulmi daga garinsu, waxannan laifuffukan sun fi girma a wurin Allah. Kuma keta alfarmar Makka ya fi zama laifi a kan keta alfarmar wata.

A nan duk qungiyoyin biyu sun aikata laifi. Amma kuma mai babban laifi ya take nasa, ya rinqa hargowa a kan mai laifi qarami. Don haka, sai aka ce, su kare laifinsu tukuna kafin su yi maganar na wasu. Idan har sun kasa kare kansu daga wancan laifi, to, don me za su damu da masu laifin da bai kai nasu ba.

Wannan shi ne halin da ke tsakanin musulmi da Yahudawa da Nasara, kuma shi ne halin da ke tsakanin Ahlus-Sunnah da sauran ‘yan bidi’a, musamman ma ‘yan Shi’ar sha biyu.

To, wannan shi ne abin da ke tsakanin Ahlus-Sunnah da ‘yan-sha-biyu ga lamarin Abubakar da Ali. Xan Shi’ar ba zai iya tabbatar da imanin Ali ba, da cewa shi xan aljanna ne, ballantana ya tabbatar da shugabancinsa sai fa in ya tabbatar da haka ga Abubakar da Umaru da Usmanu.

Don in ba haka ba duk lokacin da ya so ya tabbatar da wata daraja ga Ali, to, dalilai ba sa taimaka masa, kamar yadda in Kirista ya so ya tabbatar da annabcin Isa Alaihis Salamu ba zai iya ba sai in ya yarda da annabcin Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama, domin dalilai ba za su taimake shi ba.

Bisa ga haka, idan ka tattauna da wani daga cikin ‘yan-sha-biyu, to, qaddara masa tattaunawar tsakanin sa da Harijawa masu kafirta Ali da Nasibawa masu fasiqantar da shi. Harijawa sun tafi a kan cewa, Ali azzalumi ne, mai neman duniya, wanda ya nemi halifanci da qarfi, ya yaqi mutane a kansa. A garin haka kuwa ya kashe dubun dubatar musulmi, abin da ya hana cin nasarar mulkinsa. Ya kuma kasa samun abin da yake so na kevanta da mulki, sai magoya bayansa suka dare masa, suka yaqe shi har daga qarshe suka kashe shi.

To, ka ga wannan magana in ta kasance qarya ce, to, ba shakka maganar xan Shi’ar a game da Abubakar da umar ta fi ta zama qarya. In kuma har maganar xan Shi’ar a game da Abubakar da Umar daidai ne, kuma magana ce ta gaskiya, to, lalle ko maganar Harijawa a kan Ali ta fi cancantar zama gaskiya.

Kowa ya sani cewa, shugaban da mutane suka zava a cikin yardarsu da amincewarsu ba tare da tilastawa da qarfin takobi ko sanda ba, kuma bai ba kowa kuxi ba cikin waxanda suka zave shi. Sannan duk suka haxu a kan shugabancinsa. Kuma bai shugabantar da ‘yan’uwansa ko ‘ya’yansa ba, bai kuma bar wa magadansa dukiya ba daga cikin dukiyar musulmi. Ya kasance shi yana da kuxi kuma ya qarar da su a hanyar Allah. Sannan bai nemi a maida masa kuxin ba. Ya kuma yi wasicci da cewa, abin da ya bari na dukiya a mayar da shi baitulmali tare da cewa, bai mallaki komai ba sai wani tsohon tufa da doki da baqar kuyanga.

Har ya kai ga lokacin da aka xauko wannan dukiyar tasa za a saka a baitulmali Abdurrahman xan Aufu ya ce wa Umar, qwace zaka yi wa iyalan Abubakar? Sai Umar ya ce: Abubakar ne ya sauke wa kansa wannan kaya, ni kuma ba zan xora wa kaina shi ba. A nan ne Abdurrahman ya ce: “Ya Allah! Ka jiqan Abubakar. Haqiqa Abubakar ka wahalar da shugabanni bayan ka”.

Ga shi kuma har ya qare mulkinsa bai kashe musulmi ko xaya ba, bai sa musulmi ya yaqi musulmi ba. A maimakon haka, ya xaura yaqi da murtaddai da kafirai har Allah ya bashi nasarar cin manyan garuruwa da isar da saqon musulunci cikinsu. Da ya ga manzon mutuwarsa kuma sai ya tsayar wa da musulmi halifa qaqqarfa, amintacce, mai xinbin hikima da tarin ayyuka, wanda ya tsara aikin gwamnati, ya ci garuruwa da birane, ya shimfixe qasa da adalcinsa.

To, wannan bawan Allah idan har mai sukar sa na da gaskiya, to, gaskiyar wanda yake sukar Ali ta tabbata. In ko har Ali wankakke ne daga tuhuma, to, wankuwar Abubakar ta zama dahir.

Idan kuma har murtaddai na da uzuri akan rashin yi wa Abubakar mubaya’a, to, uzurin su Mu’awiyah na rashin yi wa Ali mubaya’a ya fi qarfi. Domin su cewa suka yi, ba za mu yi mubaya’a ba sai ga wanda zai yi muna adalci, ya kare mu daga wanda ke son zaluntar mu, ya karva mana haqqinmu daga wanda ya zalunce mu. In ko har bai yi haka ba, to, shi azzalumi ne ko ajizi. Kuma bai wajaba mu yi mubaya’a ga azzalumi ko ajizi ba.

To, in har maganar su Mu’awiyah vatatta ce, to, vacin maganar mai cewa Abubakar da Umar azzalumai ne, masu neman duniya da shugabanci ya fi girma.

Duk mai hankali yana iyar fahimtar wannan magana cikin sauqi. Ya ya ma za a iya kwantanta shubuhar da Abu Musal-Ash’ari ya yi na cewa, a saukar da Ali daga shugabanci, Mu’awiyah kuma daga gwamna, a mayar da lamari ga musulmi su sake zave. Ina wannan shubha ta kai wadda Abdullahi xan Saba’i da ‘yan’uwansa ‘yan Shi’ah suka kawo cewa, Ali Imami ne ma’asumi, ko waxanda suka ce shi abin bauta ne ko an yi kuskuren annabta don shi ne ya cancance ta?

Ya za ka kwatanta shubhar masu ganin Mu’awiyah ya zama shugaba da shubuhar masu cewa Ali abin bauta ne ko kuma Annabi ne? Na farkon basu zama kafirai don irin wannan magana. To, amma na biyun fa?

A taqaice dai, ‘yan Shi’ar sha biyu ba su iya tabbatar da imanin Ali da adalcinsa matuqar sun tsaya a kan aqidarsu ta ‘yan-sha-biyu. Domin za mu lulluve su da zarge-zargen Harijawa da Nasibawa su rikirkita su.

Su dai Harijawa sun ce, ba su yarda cewa Ali mumini ne ba. Sai suka ce shi kafiri ne, azzalumi. Kamar dai yadda su ‘yan-sha-biyu ke faxa game da Abubakar da Umar. Kuma duk dalilin da ‘yan Shi’ah za su kawo a kan zargin Abubakar da Umar to, Harijawa za su kawo wanda ya fi shi qarfi. Idan kuma su, ‘yan Shi’ah sun kafa hujja da hadissan da aka riwaito mutawatirai cewa, Ali ya musulunta, ya kuma yi hijira da jihadi, to, ai an riwaito irin su da ma waxanda suka fi su qarfi a game da musuluncin Abubakar da Umar da Usman. Kai, da ma Mu’awiyah da Yazid da sarakunan Banu Umayya da na Banul Abbas.

In suka ce, ai an san Ali na sallah da azumi da jihadi, to, su ma halifofi ukun ai haka ne. In suka raya cewa su waxancan munafikai ne, to, su ma Harijawa sun ce, Ali Raliyallahu Anhu munafiki ne. Suka ce, ya kasance yana hasadar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama don yana xan qanin babansa, kuma wai, daman yana da qudurin vata addininsa, bai samu damar haka ba a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da zamanin halifofi ukun. Amma da ya samu dama wai, sai ya haxa kai aka kashe halifa na uku, don ya samu kujerarsa. Sannan ya hura wutar fitina, yana mai karkashe Sahabban Manzo da al’ummarsa don qin Manzo da yake yi da adawa da shi. Suka ce, shi munafiki ne a voye, wanda yake bayyana savanin abin da ke zuciyarsa, saboda addininsa shi ne taqiya. Kuma a baxini tare yake da ku ‘yan Shi’ah masu cin zarafin magabatan al’umma da masu ce masa shi Allah ne ko Manzo. Suka ce, don haka ne qungiyar Shi’ah Baxiniyyah suka zamo mabiyansa. Kuma su ne suka san sirrinsa, suke cirato shi daga wurinsa.

Ka ga duk yadda xan Shi’ah zai kare Ali da wata hujja, to, hujjar ta isa ta kare halifofi uku har da qari. Kuma idan maganar Harijawa qarya ce, to, qaryar maganar ‘yan Shi’ah a kan halifofi ta fi fitowa fili, kuma ta fi karvuwa a wurin jahillai. Amma ba wanda zai warware wannan rikicin sai Ahlus-Sunnah.

Idan kuma suka ce, za su tabbatar da imanin Ali Raliyallahu Anhu da adalcinsa ta hanyar wani nassi na Alqur’ani da za su ce ya kevance shi, sai a ce masu: Ayoyin Alqur’ani a game suke. Babu kuma wata ayar da za su iya raya cewa, ta kevance shi face ana iya raya cewa ita wannan ayar ta kevanci Abubakar da Umar. Kuma idan aka yi hujja sai hujjar wanda ya jingina ayar ga Abubakar da Umar ta fi karvuwa.

Idan kuma sun ce, darajojin Ali sun tabbata ne ta hanyar ciratowa da riwaya, sai a ce musu riwayoyin da suka bayyana darajojin waxancan halifofin sun fi yawa da qarfin inganci. In suka ce, mutawatiri ne, a ce masu wa ya yi tawaturin, tun da kun ce, Sahabbai duk sun kafirta sai kaxan daga cikinsu? Ga shi ko babu ‘yan Shi’ah a cikin Sahabbai waxanda yawansu ya kai na waxanda ke riwayar mutawatiri. Ba ta yadda za ku iya tabbatar da wannan ta hanya yankakkiya sai in kun bi hanyar Ahlus-Sunnah, kamar yadda kiristoci ba su iya tabbatar da annabcin Isa Alaihis Salamu in ba su bi hanyar musulmi ba.

Wannan ba shi da banbanci da wanda ke son tabbatar da cewa Ibnu Abbas faqihi ne ba tare da ya yarda cewa Ali shi ma faqihi ne ba. Ko ya faxi haka game da Ibnu Umar ba tare da ya yarda da haka ga babansa Umar ba. Ko ya ce, malam Alqamatu da malam Aswadu (almajiran Ibnu Mas’ud) masana ne, amma ba tare da ya tabbatar da sanin Ibnu Mas’ud ba. Da ire-iren wannan.

Rashin gano wannan ne ya sa ‘yan-sha-biyu suka fi kowa jahilci da vata, kamar yadda Kirista suke mafi jahilcin mutane. Haka Shi’ah ‘yan-sha-biyu suka fi kowa sharri da cuta kamar yadda Yahudawa suka fi kowa sharri da cuta. ‘Yan Shi’ah sun haxa tsakanin vatan Kirista da sharrin Yahudawa.

 2.1 Wannan da wannan Suna Da Banbanci

Xan Shi’ar ya ba da misali da qissar Umaru xan Sa’ad wanda ya nemi kuxi da mulki ya aikata abin da bai dace ba. To, wannan na nufin duk magabatan farko su ma sun kasance haka? To, ga babansa nan Sa’adu xan Abu Waqqas, yana cikin waxanda suka fi kowa gudun duniya game da mulki da shugabanci. A lokacin da fitina ta auku sai ya qaurace wa mutane ya yi zaman sa a gidansa da yake Al-Aqiq, sai da xan nan nasa ya same shi, yana nuna ganin laifinsa a kan ya bar mutane suna jayayya a kan mulki ya qauracewarsa. Sai Sa’adu ya ba shi amsa da hadisin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Allah Ta’ala na son bawa mai taqawa, mai voye kansa, kuma mai wadatar zuci”

Kar mu manta, Sa’adu xin nan fa a lokacin shi kaxai ya rage cikin ‘yan kwamitin naxin sarauta sai Ali. kuma jarumi ne da ya buxa qasar Iraqi, ya karya Kisran Farisa da rundunarsa. Kuma shi ne wanda ya yi saura daga cikin Asharatul Mubassharuna Bil Jannah.

To, idan ya kasance bai dacewa a kwatanta Umaru xan Sa’ad da babansa, ya za a kwatanta shi da Abubakar da Umar?

‘Yan Shi’ah suna darajanta xan Abubakar suna fifita shi a kan babansa Abubakar Siddiq, ba don kome ba sai don ya musguna wa sayyidina Usman, kuma yana cikin muqarraban Ali, kuma Alin na aure da uwarsa. A kan haka, ‘yan Shi’ah suke son sa, suna zagin ubansa, suna la’antar sa. To, ya za su yi da Nasibawa idan suka yi haka game Umaru xan Sa’ad, suka yabe shi a kan sa hannunsa wajen kisan Husaini, suka zagi babansa don bai goyi bayan Mu’awiyah ba a lokacin fitina? Akwai banbanci a tsakanin wannan jahilcin da wancan?

A gaskiya, gara ma Nasibawa, idan suka yi haka, da ‘yan Shi’ah. Domin Abubakar ya fi Sa’adu daraja, Usman kuma ya fi nisa ga cancantar kisa a kan Husaini. Tattare da cewa, kowannensu an zalunce shi, kuma duk sun yi shahada. Amma banbancinsu shi ne, Usman yana halifa aka kashe shi, kuma ya qi yaqar waxanda suka zo kisansa, bayan sun neme shi da ya yi murabus bai yi ba. Ga shi kuma cikin magabatan musulmin farko. Shi kuma Husaini ba sarki ba ne, ba gwamna ba. Amma ya nemi sarauta abin ya faskara, kuma da ya lura abin ba zai yiwu ba ya nemi a bar shi ya koma aka qiya. Da aka nemi ya miqa kansa a je da shi wurin sarki ya qi, a kan haka aka yaqe shi har aka kashe shi.

Haqurin da Usman ya yi babu shakka ya fi girma. Don haka shahadarsa tana gaba da ta Husaini. Wannan shi ya sa fitinar da ta cimma al’umma a kan kisan Usman ta fi girma.

A taqaice dai, duk wanda ‘yan Shi’ah suke yabo, to, za ka tarar a cikin waxanda Harijawa ke yabo akwai waxanda suka yi masu fintinkau wajen girman daraja. Haka kuma duk wanda ‘yan Shi’ah suke zagi, to, a cikinsu akwai wanda sharrinsa ya zarce na wanda suke zagin.

Su kuwa Ahlus-Sunnah sun tsaya tsaka ne, ta hanyar jivintar dukkan musulmi, waxanda suka haxa da Sahabbai da Tabi’ai da na bayan su. A lokaci xaya kuma sun yarda da matsayi da darajar da Ahlul-Baiti suke da su. Savanin abin da su Mukhtar suka aikata.

Magabatan wannan al’umma gaba xaya sun yarda da cewa, Abubakar da Umar da Usman na da fifikon daraja a kan Ali Raliyallahu Anhu. Magoya bayansa ma daga cikinsu basu musun haka.

Ya tabbata daga Ali Raliyallahu Anhu xin kansa ta hanya mutawatira cewa, ya ce: Mafifitan wannan al’umma bayan Manzonta su ne: Abubakar da Umar. Amma wasu daga cikin mabiyansa suna ganin cewa, Ali ya fi Usmanu. Amma dai akasarin malamai suna ganin rashin dacewar wannan ra’ayi, saboda ya ci karo da ijma’in Sahabbai. Har ma Ayyub – daga cikin malaman Tabi’ai – yana cewa: “Duk wanda ya fifita Ali a kan Usman bai raga ma Sahabbai ba”.

 2.2 Wai Imamansu Ba Su Kuskure!

 Xan-sha-biyu ya ce: “Dukkan musulmi in banda Imamiyyah da Isma’iliyyah sun ce Annabawa da imaman ‘yan Shi’ah suna iya yin kuskure. Sai suka ce yana yiwuwa a aiko wanda ke iya yin qarya da mantuwa da kuskure da sata. To, wace amincewa ta yi saura da mutane za su yi ga maganganunsu, ko yaya akai su yi masu xa’a? kuma yaya bin su ke zama wajibi ga jama’a alhali kuwa mai yiwuwa ne abin da suke umurni da shi kuskure ne? Kuma ba su taqaita imamai ga wani adadi ba, su dai duk wanda ya yi wa Baquraishe mubaya’a to wannan mubaya’ar ta yi daidai a wurinsu. Kuma wajibi ne duk musulmi su yi masa xa’a in dai wani abin qi bai bayyana gare shi ba, ko da ya kai matuqa ga kafirci da fasicci da munafunci a voye.”

Martani:

 Cewa mafi yawan musulmi na ganin Annabawa ba a kiyaye su daga kuskure ba, kuma wai, yana yiwuwa su yi qarya da sata, duk wannan ba haka yake ba. Duk musulmi sun haxu a kan cewa Allah ya kiyaye Annabawa daga yin kuskure ga abin da ya shafi isar da saqonsa. Ba shi yiwuwa wani kuskure ya dawwama a cikin shariah. Duk abin da suka isar da shi na umurnin Allah ko haninsa, to, wajibi ne a yi musu xa’a cikinsa. Abin da suka ba da labari kuma wajibi ne a gasgata su. Bin umurninsu da nisantar haninsu wajibi ne. Waxannan abubuwa duk qungiyoyin musulmi sun haxu a kansu, sai fa Harijawa waxanda ke halatta samun kuskure a cikin umurni ko hanin da Annabawa suka yi. To, waxannan vatattu ne. Ahlus-Sunnah sun haxu a kan haka.

 Ya gabata cewa in wasu mutane daga cikin musulmi suka faxi maganar da take kuskure ce, wannan ba a xaukar sa a matsayin suka ga dukan musulmi. In da kuwa ana haka, to, da kuskuren Shi’ah ‘yan-sha-biyu ya zama aibi a kan musulmi, ga shi kuwa ba a san wata qungiya da ta fi Shi’ah ‘yan-sha-biyu kuskure da qarya ba, wannan ba ya cutar da musulmi da komai, haka ma idan sauran qungiyoyi idan sun yi nasu kuskure.

 Mafi yawan mutane ko kuma da-yawansu ba su yarda cewa Annabawa na iya aikata kaba’ira ba. Amma mafi yawan malaman na ganin suna iya faxawa cikin wani cikin aikata wani qaramin laifi, daga baya sai a faxakar da su, su tuba, kuma sai Allah ya qara xaukaka darajarsu fiye da wadda suka kasance a kai.

 A taqaice dai babu musulmin da ya ce wajibi ne ayi wa Manzo xa’a in ana tsammanin cewa abin da ya yi umurni da shi kuskure ne. Abin da dai suka haxu a kansa shi ne, yin xa’a na rataya ne ga abin da yake sawaba ne.

 Malamai suna da ra’ayi biyu sanannu game da yiwuwar cewa in manzanni suka yi ijtihadi za su iya yin kuskure ko a’a. Dukan malamai sun haxu akan cewa in sun yi kuskure ga ijtihadi Allah zai gyara masu kuskuren, kuma ana yi masu xa’a ne ga abin da Allah Ta’ala ya bar su a kai, ba wanda Allah Ta’ala ya canza kuma yayi hani gare shi ba.

 Amma cewa imaman Shi’ah ba su yin kuskure to, lalle babu musulmin da ya ce haka in ba ‘Yan-sha-biyu da Ismailiyyawa ba. Wane vata ne ya kai ga maganar da babu musulmin da ya aminta da ita sai masu ilhadi da munafukai?

 Shin yana yiwuwa a sami waxanda suka fi vata akan masu qin Muhajiruna da Ansaru na farko sannan kuma su yi soyayya da kafirai da munafukai ga shi kuwa Allah Ta’ala ya ce:

﴿أَلَم تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ تَوَلَّواْ قَومًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيهِم مَّا هُم مِّنكُم وَلَا مِنهُم وَيَحلِفُونَ عَلَى ٱلكَذِبِ وَهُم يَعلَمُونَ١٤ أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُم عَذَابا شَدِيدًا إِنَّهُم سَاءَ مَا كَانُواْ يَعمَلُونَ١٥ ٱتَّخَذُواْ أَيمَنَهُم جُنَّة فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَهُم عَذَاب مُّهِين١٦ لَّن تُغنِيَ عَنهُم أَموَلُهُم وَلَا أَولَدُهُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيًا أُوْلَئِكَ أَصحَبُ ٱلنَّارِ هُم فِيهَا خَلِدُونَ١٧ يَومَ يَبعَثُهُمُ ٱللَّهُ جَمِيعا فَيَحلِفُونَ لَهُ كَمَا يَحلِفُونَ لَكُم وَيَحسَبُونَ أَنَّهُم عَلَى شَيءٍ أَلَا إِنَّهُم هُمُ ٱلكَذِبُونَ١٨ ٱستَحوَذَ عَلَيهِمُ ٱلشَّيطَنُ فَأَنسَىهُم ذِكرَ ٱللَّهِ أُوْلَئِكَ حِزبُ ٱلشَّيطَنِ أَلَا إِنَّ حِزبَ ٱلشَّيطَنِ هُمُ ٱلخَسِرُونَ١٩ إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحَادُّونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُ أُوْلَئِكَ فِي ٱلأَذَلِّينَ٢٠ كَتَبَ ٱللَّهُ لَأَغلِبَنَّ أَنَا وَرُسُلِي إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيز٢١ لَّا تَجِدُ قَوما يُؤمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱليَومِ ٱلأخِرِ يُوَادُّونَ مَن حَادَّ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَو كَانُواْ ءَابَاءَهُم أَو أَبنَاءَهُم أَو إِخوَنَهُم أَو عَشِيرَتَهُم أُوْلَئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلإِيمَنَ وَأَيَّدَهُم بِرُوح مِّنهُ وَيُدخِلُهُم جَنَّت تَجرِي مِن تَحتِهَا ٱلأَنهَرُ خَلِدِينَ فِيهَا رَضِيَ ٱللَّهُ عَنهُم وَرَضُواْ عَنهُ أُوْلَئِكَ حِزبُ ٱللَّهِ أَلَا إِنَّ حِزبَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلمُفلِحُونَ٢٢﴾ المجادلة: ١٤ - ٢٢

Shin ba ka ga mutanen da ke jivintar waxanda da Allah ya yi fushi da su ba. Su dai ba cikinku suke ba, ba kuma cikinsu suke ba, kuma suna rantsuwar qarya cikin sani. Allah ya tanadar masu azaba mai tsanani, haqiqa abin da suke yi ya munana. Sun riqi rantsuwarsu a matsayin garkuwa, sai suka kange (mutane) daga hanyar Allah. To, suna da azaba mai qasqantarwa. Dukiyarsu ba zata wadatar da su ba, haka ma ‘ya’yansu ba za su wadatar da su da wani abu ba, waxannan sune ma’abuta wuta, kuma masu dawwama ne a cikinta. Ranar da Allah zai tada su, dukan su, sai su yi masa rantsuwa kamar yadda suke yi maku suna tsammanin cewa suna bisa wata hujja, a’a lalle su ne maqaryata. Shaixan ya samu galaba a kansu, sai ya hana su tuna Allah. Waxannan su ne qungiyar shaixan. To, a sani cewa qungiyar shaixan ita ce ke yin hasara. Waxanda ke fito-na-fito da Allah da Manzonsa waxannan na cikin qasqantattu. Allah ya rubuta cewa: “Wallahi Ni da manzannina ne za mu yi galaba”, haqiqa Allah mai qarfi ne, mabuwayi. Ba za ka tarar da mutanen da suka yi imani da Allah da ranar lahira suna son wanda ya sava wa Allah da Manzonsa ba, koda sun kasance iyayensu ne ko ‘ya’yansu, ko ‘yan’uwansu. To, waxannan an rubuta imani cikin zukatansu, kuma zai sa su aljannar da qoramu ke gudana a cikinta, suna madawwama cikinta. Allah ya yarda da su, su ma sun yarda da shi. Waxannan su ne rundunar Allah, to kuma rundunar Allah sune masu ribanta. Al-Mujadalah: 14-22.

 Waxannan ayoyin an saukar da su ne akan munafukai, qungiyar ‘yan-sha-biyu kuwa ta fi duk sauran qungiyoyi yawan munafukai, har za ka tarar cewa ba wani xan Shi’ar face yana da xaya daga cikin alamomin munafunci. Kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Abu huxu duk wanda ya sifaitu da su to, munafuki ne tsintsa, wanda yake da sifa xaya daga cikinsu kuwa, to, ya na da sifar munafunci har sai ya bar ta: 1) Idan ya yi magana sai ya yi qarya, 2) In aka amince ma sa sai ya yi yaudara, 3) In ya yi alqawari sai ya sava, 4) In kuma ya yi husuma sai ya yi fajirci. Buhari da Muslim sun riwaito shi cikin sahihansu.

 Allah Ta’ala ya ce

 ﴿تَرَى كَثِيرا مِّنهُم يَتَوَلَّونَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَبِئسَ مَا قَدَّمَت لَهُم أَنفُسُهُم أَن سَخِطَ ٱللَّهُ عَلَيهِم وَفِي ٱلعَذَابِ هُم خَلِدُونَ٨٠ وَلَو كَانُواْ يُؤمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلنَّبِيِّ وَمَا أُنزِلَ إِلَيهِ مَا ٱتَّخَذُوهُم أَولِيَاءَ وَلَكِنَّ كَثِيرا مِّنهُم فَسِقُونَ٨١﴾ المائدة: ٨٠ - ٨١

 Za ka ga dayawa daga cikinsu na jivintar kafirai. Abin da zuciyarsu ta umurce su da shi ya munana, don ya kai su ga fushin Allah kuma su masu dawwama ne a cikin wuta. Da sun kasance sun yi imani da Allah da Annabi da abin da aka saukar ma sa da ba su riqe su majivinta ba. Amma dai dayawansu fasiqai ne. Al-Ma’ida: 80-81.

Allah Ta’ala kuma ya ce:

 ﴿لُعِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن بَنِي إِسرَءِيلَ عَلَى لِسَانِ دَاوُدَ وَعِيسَى ٱبنِ مَريَمَ ذَلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعتَدُونَ٧٨ كَانُواْ لَا يَتَنَاهَونَ عَن مُّنكَر فَعَلُوهُ لَبِئسَ مَا كَانُواْ يَفعَلُونَ٧٩﴾ المائدة: ٧٨ - ٧٩

An la’anci waxannan da suka kafirta daga cikin Bani Isra’ila a bisa harshen Dawuda da Isah xan Maryam. Wannan ya kasance ne don savon da suka aikata, kuma sun kasance suna wuce wuri. Sun kasance ba su hanin junansu daga munkarin da suke aikatawa. Wallahi abin da suke aikatawa ya munana. [Al-Ma’ida 78-79].

 Su ’yan Shi’ar sha biyu galibinsu ba su hani da munkarin da suke aikatawa, kai za ka tarar cewa an fi aikata munkari kamar zalunci da aikata alfasha da makamantansu a garuruwansu kuma su suna jivintar kafiran da Allah ya yi fushi da su, ba su kasance tare da musulmi ba, ba kuma tare suke da kafirai ba, kamar yadda Allah Ta’ala ya ce:

﴿أَلَم تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ تَوَلَّواْ قَومًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيهِم مَّا هُم مِّنكُم وَلَا مِنهُم وَيَحلِفُونَ عَلَى ٱلكَذِبِ وَهُم يَعلَمُونَ١٤﴾ المجادلة: ١٤

Shin ba ka ga waxanda suka jivinci mutanen da Allah ya yi fushi da su ba, ba su cikinku kuma ba su cikinsu? Al-Mujadala 14.

Saboda haka ne ‘yan-sha-biyu suke jinsi na daban a wurin musulmi. Wannan ne ya sa da musulmi suka yaqe su a wani tsaunin da suka fake cikinsa a wani sashe na Sham, inda suke zubar da jinin musulmi suna qwatar dukiyarsu, suka yi masu fashi da makami, suna masu halatta haka. Suna kuma cewa aikin addini ne suke yi, sai wasu turkawa suka yaqe su, sai ‘yan Shi’ah suka rinqa cewa su musulmi ne, turkawan na cewa ku dai wani jinsi ne daban da musulmi. Don banbantarsu daga musulmi.

 Ga shi kuma Allah ya ce (Suna rantsuwa akan qarya suna kuma sane da hakan)[Al-mujadala 14] wannan ita ce halayyar ‘yan-sha-biyu. Haka ma inda Allah Ta’ala ya ce:

 ﴿ٱتَّخَذُواْ أَيمَنَهُم جُنَّة فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَهُم عَذَاب مُّهِين١٦﴾ المجادلة: ١٦

 Sun riqi rantsuwarsu abin kariya, sai suka kange mutane daga tafarkin Allah. Har zuwa inda yake cewa: (Ba za ka tarar da mutane masu imani da Allah da ranar alqiyama suna son wanda ya sava wa Allah da Manzonsa ba). Al-mujadala: 22.

 Da yawansu na son kafirai har cikin zukatansu fiye da son musulmi, don haka lokacin da wasu kafirran turkawa suka fita daga gabas suna yaqar musulmai da zubar da jininsu a qasar Khurasana da Iraqi a Sham da Jazira da sauran garuruwan musulmi, Shi’ah ‘yan-sha-biyu sune masu taimaka masu wurin yaqar musulmi. Wazirin Bagadaza da aka fi sani da Ibnul Alqami shi da makamantansa sun fi kowa taimaka wa kafirran turkawan a kan musulmi. Haka ma Shi’ah ‘yan-sha-biyu na Halab a qasar Sham da sauran ‘yan Shi’ah, sun fi kowa taimaka wa kafirran wurin yaqar musulmi. Haka ma kafirran da musulmi suka yaka a qasar Sham ‘yan-sha-biyu sun fi kowa taimaka masu, haka ma in Yahudawa sun sami daula a Iraqi da waninsa to, ‘yan Shi’ah ne za su taimaka ma su, su kowane lokaci suna jivintar kafirrai suna kuma taimakon su wurin yaqar musulmi.

 Sannan wannan xin da ya raya cewa Imamai ba su kuskure bai kafa hujja ba a kan haka sai abin da ya gabata na cewa Allah ba zai bar duniya ba, ba tare da Imamai ma’asumai ba don abin da ke cikin haka na maslaha da luxufi sanannen abu ne. Cewa wannan Imamin na qarshe wanda ke fake kuma ana jiran sa babu maslahar da ya haifar ko luxufi. In ya kasance matacce kamar yadda mafi yawan musulmi ke gani ko in yana raye kamar yadda Shi’ah ‘yan-sha-biyu ke cewa, haka ma kakanninsa ba wata maslahar da aka samar daga gare su ko luxufi, kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance a Madina bayan hijira. Ya kasance shugaban muminai wanda ya wajaba a yi masa xa’a, kuma wannan ya zama sanadin tsirarsu, kuma bayansa ba a samu wani cikin imaman naku da ya riqa ragamar mulki ba sai Ali Raliyallahu Anhu a lokacin halifancinsa.

 Abin da duk musulmi suka sani ne cewa maslaha da luxufin da muminai suka samu lokacin halifofi uku na farko sun fi waxanda aka samu lokacin Ali, kasancewar lokacinsa lokaci ne na tashin hankali da fitina da rarrabuwar kan musulmi. To, idan babu wanda aka samu daga cikin waxanda Shi’ah ‘yan-sha-biyu ke cewa imamai ne ma’asumai sai Ali Raliyallahu Anhu kuma shi kaxai ne ya yi shugabanci bayan masu qarfi a cikin musulmi sun yi masa mubaya’a ga shi kuma maslahar addini da ta duniya da mumina suka samu bata kai wadda suka samu lokacin halifofi ukun na farko ba, mun sani a yanke cewa maslaha da luxufin da suka raya cewa ana samu don imaman da basu kuskure ya zama qarya, ba makawa.

 Wannan irin shiriyar da ake rayawa ce ga wasu mutanen da ke fake a tsaunukan lebanon da sauran tsaunukan kamar na Qasiyun ta Damaskas, da Magaratud Dami da tsaunin Al-Fatah a Masar, da tsaunuka da koguna makamantan su. Waxannan wurare ne na zaman aljannu, kuma akwai shaixanai a cikinsu, suna bayyana wasu lokuta ga wasu mutane, suna voyuwa daga mutane mafi yawan lokuta, sai jahilai su yi tsammanin cewa mutane ne, alhalin aljannu ne. kamar yadda Allah Ta’ala ya ce

﴿وَأَنَّهُ كَانَ رِجَال مِّنَ ٱلإِنسِ يَعُوذُونَ بِرِجَال مِّنَ ٱلجِنِّ فَزَادُوهُم رَهَقا٦﴾ الجن: ٦

Kuma haqiqa wasu mazajen mutane sun kasance suna neman tsari daga wasu mazajen aljannu. Sai wannan ya qara ma su (aljanun) girman kai. Al-Jin: 6.

 Waxannan ‘yan Shi’ah sun yi imani da su kuma sun yi imani da vatattun shehunan qungiyoyi bin waxannan aljannun, amma sharrin Shi’ah ‘yan-sha-biyu ya xara sharrin shehunan da ke raya cewa akwai mazan da ke voye, lalle sharrin da ke faruwa daga yan Shi’ah ‘yan-sha-biyu ya fi tsanani, don suna kira ne zuwa ga wani shugaban da ba ya yin kuskure a cewarsu, ba su da shugabanni masu qarfi waxanda ke iya taimakon su sai dai kafiri ko fasiqi ko munafuki ko jahili, shugabanninsu ba sa fita daga cikin waxannan da aka ambata.

 Qungiyar Shi’ah Isma’iliyyah ta fi Imamiyyah sharri. Su xin ma kira suke zuwa ga wani imamin da ba ya kuskure, kai dai su kira suke zuwa ga sarki mai yawan kafirci da zalunci, wannan abu ne sananne ga duk wanda ya san halin da suke a kai.

 Ga shi kuwa lalle Allah Ta’ala ya ce

 ﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلأَمرِ مِنكُم فَإِن تَنَزَعتُم فِي شَيء فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُم تُؤمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱليَومِ ٱلأخِرِ ذَلِكَ خَير وَأَحسَنُ تَأوِيلًا٥٩﴾ النساء: ٥٩

 Ya ku waxanda suka ba da yaskiya ku yi xa’a ga Allah da manzonsa da shugabanninku. To, in kun yi savani cikin wani abu, to ku maida shi zuwa ga Allah da Manzonsa wannan ne ya fi zama alheri, kuma shi ya fi kyakkyawan qarshe. An-Nisa’i 59.

 Sai Allah Ta’ala ya yi umurnin cewa a mayar da abin da aka yi savani cikin sa zuwa ga Allah da Manzonsa. Ka ga da akwai wani wanda ba ya kuskure wanda Allah Ta’ala ya yarda da shi bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ya yi umurnin cewa a mai da lamari zuwa wurinsa. Ta haka ne Alqur’ani ya yi nuni da cewa babu wani wanda ba ya yin kuskure face Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

 2.3 Adadin Imamai

Amma cewar da xan Shi’ar ya yi ba a qayyade yawan imamai ba. Wannan gaskiya ne, don abin da Allah ya ce shi ne:

 ﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلأَمرِ مِنكُم فَإِن تَنَزَعتُم فِي شَيء فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُم تُؤمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱليَومِ ٱلأخِرِ ذَلِكَ خَير وَأَحسَنُ تَأوِيلًا٥٩﴾ النساء: ٥٩

Ya ku waxanda suka ba da gaskiya! ku yi ma Allah xa’a ku kuma yi ma Manzo da shugabaninku. An-Nisa: 59.

Allah Bai qayyade adadinsu da wani yawa na musamman ba.

 Haka Annabi ya faxa a cikin hadissai masu yawa waxanda aka riwaito, bai qayyade yawansu ba. Ya zo cikin Buhari da Muslim ta hanyar Abu Zarri Raliyallahu Anhu cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:

Haqiqa babban masoyina ya yi mani wasicci da in ji magana in kuma yi xa’a ko da (shugaban) ya kasance bawa ne daga Habasha mai yankakkun gavvai.

 2.4 Wace Mubaya’a ce Ingantatta?

 Amma cewar da ya yi game da waxanda ba Imamiyyah da Isma’iliyyah ba wai, duk wanda ya yi wa Baquraishe mubaya’a to, shugabancinsa ya qullu, kuma yi masa xa’a ya zama wajibi akan dukan mutane idan halinsa voyayye ne koda kuwa ya fi kowa fasicci da kafirci da munafunci. To wannan koda ya ke wasu malaman tauhidi sun faxe shi, to ba shi ne mazhabar Ahlus-Sunnah ba. Umar xan Haxxabi dai ya ce: Duk wanda ya yi wa wani mutum mubaya’a ba tare da shawartar musulmi ba to, kada a yi masa mubaya’a shi da wanda ya yi masa mubaya’a….} Buhari ya riwaito shi.

Ahlus-Sunnah kuma ba su wajabtar da xa’ar shugaba ga duk abin da ya yi umurni da shi, sai dai ga abin da shariah ta yarda da shi. Ba su yarda a yi masa xa’a ga savon Allah Ta’ala koda ya kasance shugaba adili, in ya umurce su da xa’ar Allah sai su yi masa xa’a, kamar ya umurce su da tsai da sallah da ba da zakka da faxan gaskiya da adalci, da aikin hajji da jihadi soboda Allah, su dai ga haqiqanin lamarin Allah ne suka yi wa xa’a. Ba haramun ba ne in sun yi wa Allah Ta’ala xa’a wajabcin xa’a ga Allah ba ya faxuwa don kawai fasiqi ya yi umurni da xa’ar, kumar in fasiqi ya faxi gaskiya ba ya wajaba a qaryata shi, kuma wajabcin bin gaskiya ba ya faxuwa don kawai fasiqi ne ya faxe ta. Ahlus-Sunnah kuma ba su yi wa shugabanni xa’ar da ba ta da qaidi, suna dai yi masu xa’a ne qarqashin xa’ar Allah Ta’ala.

Kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce Xa’a dai tana kasancewa ne ga abin da shariah ta yarda da shi. Kuma ya ce: Ba a yi wa kowa xa’a in ya yi umurni da savon Allah Ta’ala. Ya kuma ce: Ba ayi wa mutum xa’a cikin abin da ya kasance savon mahalicci ne. Ya kuma ce: Wanda duk ya umurce ku da savon Allah to, kada ku yi masa xa’a.

 Maganar Shi’ah ‘yan-sha-biyu masu raya biyar Ali Raliyallahu Anhu cewa wajibi ne ayi wa wani ba Manzon Allah ba Sallallahu Alaihi Wasallama xa’a ga duk abin da ya yi umurni da shi, ya fi muni da Shi’ar aka dangantawa ga Usmanu Raliyallahu Anhu mutanen Sham masu cewa wajibi ne ayi wa shugaba xa’a ga komai don dai su suna xa’a ne ga mai mulkin da ke raye amman ‘yan-sha-biyu wanda suke yi wa xa’a ya vace, kuma babu shi.

 Sannan kuma waxancan bu su ce shugabanninsu ba su yin kuskure ba kamar yadda ‘yan Shi’ah suka ce. Su kam cewa suke yi, Allah zai karvi ayyukansu na gari kuma ya gafarta masu kurakuransu. Wannan ko ya fi sauqi a kan wanda ke cewa shugabanninsa ba su yin kuskure faufau.

 Daga nan ya bayyana cewa waxannan da ake dangantawa ga qin Ali Raliyallahu Anhu Shi’ar Usmanu koda yake sun fita daga wani sashen adalci da kuma gaskiya sai dai fitar da Shi’ah ‘yan-sha-biyu suka yi daga gaskiya da da adaki ta fi tsanani da muni. To yaya ma za’a kamanta ‘yan Shi’ah da Ahlus-Sunnah waxanda ke bin Alqur’ani da Sunnah, suna yi ma shugaba xa’a ga abin da yake umurni da shi na xa’ar Allah, su bar abin da duk suka yi umurni da shi in ya kasance savon Allah?.

 2.5 Mazhaba da Qiyasi

 Xan Shi’ar bayan haka kuma sai ya tuhumci Ahlus-Sunnah da cewa wai, sun rungumi qiyasi, sun sanya fahimtar malamansu a cikin addini. Da haka, inji shi wai, sai suka shigar da bidi’oi a cikin addini, kuma wai, a sandiyyar haka aka samu mazhabobi guda huxu waxanda babu su a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ko zamanin Sahabbai. Ya ce kuma wai, Sahabbai sun ja kunnen al’umma a kan yin hattara da qiyasi don hanyar shexan ce, amma sai malaman Sunnah suka yi biris, inji shi.

Martani:

 Ba gaskiya ba ne cewa gaba xayan Ahlus-Sunnah sun yarda da qiyasi. Domin kuwa wasu malaman bagadaza da ‘yan Zahiriyyah irin su Dawuda da Ibnu Hazam da wasu sufaye daga cikin Ahlus-Sunnah duk ba su yarda da qiyasi ba. Kamar dai yadda su ma ‘yan shi’ah bakinsu bai haxu a kan sa ba. Kuma hasali ma, riqo da qiyasi ai ya fi fatawowin Askari. Domin malaman da suka yarda da qiyasi irin su Malik da Laisu da Auza’i sun fi su ilimi da sanin makamar addini, balle daxa Malam-na-Voye da ko ganinsa ba a yi ba.

 Kuma Ahlus-Sunnah, mabiyan waxannan mazhabobi guda huxu suna kan tudu ne, a yayin da masu dakon MAlam-na-Voye suke kware. A qashin gaskiya babu wata ingantattar magana da za ta fiton bakin ‘yan-sha-biyu face akwai wadda ta yi daidai da ita ko wadda ta fi ta a wurin Ahlus-Sunnah. Banbancin kuwa da ke tsakanin Sunnah da bidi’ah kamar wanda ke tsakanin imani da kafirci ne. Ga shi kuma Allah Ta’ala na cewa: Ba za su zo ma ka da wani misali ba face mun zo ma ka da gaskiya da bayani mafi kyau. Al-Furqan:33.

 Babu kuma waxanda suka cika addinin Allah da qarya da varnace-varnace kamar ‘yan Shi’ah. Ta hanyar yi wa ayoyin Allah fassarar son zuciya. Nan gaba za mu kawo samfurin wannan fassara tasu tare da mayar da martani akai in Allah ya so.

 Dangane kuma da cewar da ya yi, wai, Ahlus-Sunnah sun yi biris da kiraye-kirayen Sahabbai. Abin da ban mamaki. Yaushe ne ‘yan Shi’ah suka fara ganin Sahabbai da gashi a ka balle har su nuna damuwa wai an yi biris da maganarsu? Ashe ba su ne suke qaryata Sahabbai ba, suna ce ma su azzalumai?! To, Sahabbai dai ba su yi wannan kiran ba. Da kuwa sun yi shi to, da babu shakka Ahlus-Sunnah ne farkon waxanda za su saurare su daga cikin qungiyoyin musulmi, don su ne suka yarda da musuluncinsu da adalcinsu da shugabancinsu.

 Abin da kuma ya faru a tarihin musulunci na samuwar mazhabobi, Allah ne ya hukunta shi. Ba haxin bakin malamai ne ba. Ba ma zama xaya ko wuri xaya aka yi su ba. Kuma tattare da hakan babu wani xaya daga cikin shugabannin mazhabobin da ya tava umurnin wani ya yi ma sa xa’a ya bar abin da littafin Allah da Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama suka qunsa. Kuma duk da samuwar waxannan mazhabobi, malaman Sunnah ba su yi kwance da sirdi ba. Kullum tsaye su ke kamar haure ga qara wa juna sani da yi wa kai hisabi dangane da hukunce-hukuncen da mazhabobin suka qunsa.

 Idan kuma xan Shi’ar na son ya ce ne, Sahabbai sun bar ma al’umma gadon fatawoyi da tarin ilimi, waxanda da malamai sun yi riqo da su babu buqatar su samar da mazhabobi, amma suka yi biris da su, to, wannan ba gaskiya ba ne. Littafan malaman waxannan mazhabobi shaqe su ke da fatawoyi da fahimtar Sahabbai. Kuma ba lalle ne a kira mazhabobin da sunan Sahabbai ba. Banbance-banbancen da ake samu tsakanin mazhabobin na fatawoyi ma duk ya samo asali ne daga Sahabban.

 Sannan yana da kyau a sani cewa, babu wani malami daga cikin Ahlus-Sunnah da ke jin cewa duk abin da shugabannin mazhabobin suka haxu a kansa hujja ne koda ya ci karo da wani ingantaccen nassi. A’a, aqidarsu ita ce, da zarar maganarsu ko ta xayansu ta sava wa nassi to, nassi shi ne abin biya. Haka kuma duk lokacin da aka samu wani savani to, komawa ga littafin Allah da Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne mafita.

 Haka kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai, Sahabbai sun yi kashedi ga musulmi daga bin qiyasi magana ce maras asali. Domin kuwa ta tabbata cewa, su kansu Sahabbai sun yi amfani da iliminsu da gogewarsu ta rayuwar musulunci suka yi qiyasin wasu hukunce-hukunce. Qiyasin da dai suka yi allawaddai da shi, shi ne irin na waxanda suka qiyasta halal a kan haram kamar waxanda suka kamanta Riba da halaltaccen ciniki da qiyasta mushe a kan yankakkiyar dabba. Ko irin qiyasin Shexan. To, in har ka ga wani nassi na Sahabbai mai nuna hattara da qiyasi, ka ji irin wanda suke nufi.

 2.6 Wai ‘Yan Shi’ah ne Kawai za su Shiga Aljanna!

 Xan Shi’ar ya ce: Dalili na biyu mai nuna wajabcin bin mazhabar Imamiyyah, shi ne: Abin da shehunmu jagora mafi girma, Khawwajah, mai taimakon addini da gaskiya, muhammadu xan Al-Hassan ax-Xusi Allah ya tsarkake ruhinsa ya ce, bayan na tambaye shi game da mazhabobi sai ya ce: Mun yi bincike game da su kuma da cewar Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama: “Al’ummata za ta rarrabu zuwa qungiyoyi saba’in da uku, daga cikinsu akwai qungiya guda mai tsira sauran kuma suna wata”. ga shi kuma ya bayyana a cikin wani hadisi ingantacce qungiyar da ke tsira da kuma qungiyoyin da za su halaka shi ne cewarsa: Iyalaina kamar jirgin Annabi Nuhu Alaihis Salamu ne, wanda ya shige shi zai tsira, wanda bai shiga ba kuma ya halaka. Sai muka tarar da cewa qungiyar da za ta tsira ita ce ta Imamiyyah, don sun sava wa dukan mazhabobi, dukan mazhabobi kuma sun haxu a cikin asullan aqidojinsu.

Martani:

 Da farko shi wannan xan Shi’ar ai ya kafirta wannan malamin nasa da yake fankamawa bai sani ba. Don malamin nasa na cikin masu cewa, duniya ba ta da farko. Shi kuma ya kafirta duk wanda ya ce haka a cikin littafinnan nasa da muke tattaunawa da shi.

 Wannan malamin nasa kuma yana da kyau a sani shi ne wannan da ya yi qaurin suna wajen taimakon arna ‘yan Shi’ah Baxiniyah Al-Isma’iliyyah a Alamauta. Sannan lokacin da Turkawa mushrikai su ka zo qasar musulmi, har suka iso bagadaza cibiyar halifanci, wannan mutum ne ya kasance malamin duban da ya ba mushrikai su Hulaku sa’a don su kashe halifan musulmi, da malamai da masu riqo da addini. Kuma ya ce kada a kashe masu sana’o’in hannu da ‘yan kasuwan da xan Shi’ar ke samun amfani na duniya daga wurinsu. Kuma ya yi rubda ciki da dukiyoyin waqafi na musulmi, yana bayarwa daga cikinta ga mushrikai, malamai da shehunnansa na qungiyar Bakhshiyyah masu siddabaru da makamantansu. Sannan kuma lokacin da ya yi wani gini a wurin da ake kira Maragah ya gina shi kamar ginin mabiyan addinin Sabi’awa mushrikai, ya fi quntata wa mutanen da addininsu ya fi kusa da addinin Allah, waxanda suka fi rabo wurinsa kuwa sune waxanda suka fi nisa daga addinin Allah kamar su Sabi’awa da masu kore sifofin Allah Ta’ala da sauran mushrikai, kodayake sana’arsu ta kasance duban taurari da tsibbu da makamantan wannan.

 Abu ne da yake sananne game da wannan da ya kira shehinsa – shi da mabiyansa, shi ne suna wulaqanta abubuwan da musulunci ya farlanta, suna qin barin abin da musulunci ya yi hani da shi, kuma ba su kiyaye salloli, ba su barin aikata savo kamar Zina da shan giya da miyagun abubuwa kamar waxannan, har ya kai ga cewa an san abin da suka aikatawa na munkari cikin watan azumi na dangin ashsha da shan giya, wannan malamin nasa bai kasance yana da wani tasiri ba sai tare da ‘yan’uwansa mushrikai waxanda addininsu ya fi na Yahudawa da Narasa zama qumsa cuta.

 Don hakan ne duk lokacin da musulunci ya qarfafa cikin turkawan Mugul, sai lamarin waxannan ‘yan Shi’ar ya yi rauni don tsananin qiyayyar da suke yi wa musulunci da musulmi. Don haka Sarki Nuruz mujahidi kuma Shahid ya nisantar da su. Shi ne kuma wanda ya kira Sarkin Mugul Gazan zuwa ga musulunci, ya yi masa alqawarin zai taimake shi in ya musulunta. Shi ne kuma ya kashe mushrikan da ba su musulunta ba cikin Bakhshiyyah mushrikai masu sihiri, ya rusa wuraren bautar gumakansu, ya karya gumakan, ya kuma halaka masu kula da su, sannan ya lizimta ma Yahudawa da Nasara biyan jiziya soboda bayyanar musulunci a cikin turkawa Magul da mabiyansu.

 A taqaice dai lamarin Tusi da mabiyansa mashahuri ne wurin musulmi, kuma ya fi qarfin a sifanta shi. Duk da haka an ce a qarshen rayuwarsa ya kasance yana tsare salloli biyar, kuma yana yawan karanta tafsirin Al-bagawi da fiqihu da makamantan haka. In dai har ya tuba ne daga ilhadi, to, Allah na karvar tuban bayinsa kuma yana gafarta zunubai. Allah Ta’ala na cewa:

 ﴿قُل يَعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ أَسرَفُواْ عَلَى أَنفُسِهِم لَا تَقنَطُواْ مِن رَّحمَةِ ٱللَّهِ إِنَّ ٱللَّهَ يَغفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِيعًا إِنَّهُ هُوَ ٱلغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ٥٣﴾ الزمر: ٥٣

 Ka gaya wa bayina waxanda suka wuce wuri cikin zaluntar kawunansu cewa, kada su yanke qauna daga rahamar Allah. Haqiqa Allah na gafarta dukan zunubbai. Haqiqa shi, mai gafar ne, mai jinqai. Az-Zumar: 53.

 Amma dai abin da xan Shia’ar ya riwaito daga shi Tusi in ya kasance kafin tuba ne, to, ba a karvar maganarsa. In kuma bayan tuba ne, to, bai tuba daga bin mazhabar Shi’ah ‘yan-sha-biyu ba kenan. Ya dai tuba ne daga ilhadi kawai. To, bisa qaddarawa ta biyun ma ba za a karvi maganarsa ba. Abin da ya fi bayyana shi ne cewa xan Shi’ar nan ya kasance yana huxuwa da shi da makamatan sa lokacin da yake yi ma mushrikan Al-magul duba, a wannan lokacin an san ilhadi ne halinsa.

 To, wanda ya kasance yana sukar mutane kamar Abubakar da Umar da Usmanu da Muhajirai da Ansarai na farko, kuma yake sukar irin su Maliki da Shafi’i da Abu Hanifa da Ahmad xan Hambali da mabiyansu, yana aibata su saboda kurakuran da ba nasu ba kamar cewa wasu na ganin halaccin wani nau’i na dara, ko waqe. Wanda yake haka, ya zai kafa hujja maganar irin waxansu da ba su ko yi imani da Allah da ranar qarshe ba, balle su haramta abin da Allah ya haramta da wanda Manzo ya haramta, kuma ba su bin addinin gaskiya. Waxanda kuma suke halatta haramtattun abubuwan da duk musulmi sun haxu a kan haramcinsu, kamar zina da shan giya da rana a cikin watan azumi. Waxanda suka tozarta sallah, suke bin son rayukansu, suka keta hurumin shariah, suka wofinta abubuwan da addini ya haramta, suka bi hanyar kafirai.

Wannan dai shi ne halin da Shi’ah ‘yan-sha-biyu suke a kai. Kodayaushe suna qiyayya da waliyyan Allah salihai magabata na farko daga cikin Muhajiruna da Ansaru, da waxanda suka yi masu kyakyawan bi, suna jivintar kafirai da munafukai.

 Abin mamaki shi ne wannan makirarren xan Shi’ar maqaryaci da yake ambaton Abubakar da Umar da Usmanu da sauran magabatan farko da Tabi’una da kuma sauran shugabannin musulmi da malamai da masu riqo da addini, yake ambaton su da munanan siffofi na qarya ba su ji ba, ba su gani ba, sannan ya zo wurin wanda ya shahara wurin musulmi da kasancewa mai sava wa Allah da Manzonsa, yana cewa wai: “Malaminmu mafi xaukaka” har da cewa: “Allah ya tsarkake ruhinsa”. Tare da cewa shi kansa ya sheda da kafircinsa da masu kama da shi, tare da la’anar da ya ke yi ma mafifitan muminai na farko da na qarshe.

 Waxannan ‘yan Shi’ar na shiga cikin ma’anar cewar da Allah Ta’ala ya yi:

﴿أَلَم تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ نَصِيبا مِّنَ ٱلكِتَبِ يُؤمِنُونَ بِٱلجِبتِ وَٱلطَّغُوتِ وَيَقُولُونَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ هَؤُلَاءِ أَهدَى مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ سَبِيلًا٥١ أُوْلَئِكَ ٱلَّذِينَ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُ وَمَن يَلعَنِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُ نَصِيرًا٥٢﴾ النساء: ٥١ - ٥٢

 Shin ba ka ga waxannan da aka ba su wani rabo na (ilmin) littafi ba, amma suna gasgata gunki da Xagutu, kuma suna ce ma waxanda suka kafirta: “Waxancan (mushrikai) sun fi muminai kasancewa bisa hanyar shiriya. Waxannan su ne Allah ya la’anta. Wanda duk Allah ya la’anta kuwa ba za ka sami mai taimakon sa ba. An-Nisa: 51-52.

 Su ma ‘yan-sha-biyu an ba su wani sashe na littafe, don sun yarda da wani sashe na littafin da Allah ya saukar, kuma suna da wani yanki na imani da sihiri da Xagutu wanda shi ne duk abin da ake bauta ba Allah ba. Saboda suna imani da falsafa da ta qunshi wannan, suna ganin cewa addu’a da ibada ana yi wa matattu, suna yin masallatai akan qaburbura, suna xaukar cewa, tafiya zuwa wurinsu kamar hajji ne.

 Wannan hadisi da xan-sha-biyun ke godogo da shi, fassararsa ta zo ta fuskoki biyu: Fuska ta farko, an tambayi Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama game da qungiyar da zata tsira, sai ya ce “wanda suke akan irin abin da nake yau a kansa; ni da Sahabbaina”. A wata riwayar ya ce: “Su ne jama’a”. Dukan waxannan maganganu biyu sun ci karo da ra’ayin ‘yan-sha-biyu, kuma suna nuna cewa, ba su ne qungiyar da za ta tsira ba, don sun fita daga cikin jama’ar musulmi, suna kafirta shugabannin musulunci suna kiransu Fasiqai, irin su Abubakar da Umar da Usmanu. Ba zancen su Mu’aawiyah da sauran Bani Umayyah ake yi ba. Suna kuma kafirtar da malaman Sunnah da masu ibada daga cikinsu kamar su Maliki da Sauri da Auza’i da Laisu xan Sa’adu da Abu Hanifa da Shafi’i da Ahmad xan Hanbali da Ishaqa, da Abu Ubaidi da Ibrahimu xan Adhama da Fudailu xan Iyal da Abu Sulaimanad-Darani da Ma’aruf Al-Karkhi da makamantansu.

‘Yan-sha-biyu kuma sun fi kowa jahiltar tarihin Sahabbai balle koyi da su, sawa’un lokacin rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ko bayansa. Ga su kuma da qin hadisi da malamansa. To, in har siffar qungiyar da za ta tsira ita ce bin abin da Sahabbai suke a kai lokacin Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama to, wannan taken Ahlus-Sunnati wal jama’a ne. Su ne qungiyar da za ta tsira. Don Sunnah ita ce abin da Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance a kansa shi da Sahabbansa, da abin da ya umurce su da shi, ko ya tabbatar da su a kanshi, ko ya aikata shi da kansa. Jama’a kuma su ne waxanda suka haxu, ba su rarrabe addininsu ba zuwa qungiyoyi. To, waxanda suka rarraba addininsu suka koma qungiyoyi ba su cikin Jama’a, Allah ya barrantad da Annabinsa dagare su. Wannan ya sa aka san cewa, Ahlus-Sunnati wal Jama’ah ne ke da wannan siffar ta masu tsira, ba siffar ‘yan-sha-biyu ba ce.

 Suna iya cewa, tunda hadisin ya ce: “Abin da nake a kansa ni da Sahabbaina a yau” to, duk wanda ya fita daga wannan hanyar ba ya a kan hanyar qungiyar da za ta tsira. Kuma Sahabbai sun yi ridda bayansa, don haka ba su cikin qungiyar da ke tsira.

 Sai a ce masu, haka yake. Mutanen da suka fi kowa shahara a ridda su ne masu jayayya da Abubakar da mabiyansa kamar Musailamu sarkin qarya da mabiyansa da ire-irensu. To, ‘yan-sha-biyu na son su, suna kariyarsu, suna ganin laifi Abubakar ya yaqe su wai, ba a kan gaskiya ba. Sannan waxanda suka fi kowa ridda bayansu su ne waxanda Ali Raliyallahu Anhu ya qona su a lokacin da suke cewa shi Allah ne abin bauta. Su ne sabi’awa mabiyan Abdullahi xan Saba’i waxanda suka fara bayyana zagin Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma.

 Haka kuma farkon wanda ya fara da’awar annabta a cikin musulunci shi ne Mukhtar xan Baban Ubaidu, xan Shi’ah ne. Daga nan ake sanin cewa waxanda suka fi kowa ridda suna cikin ‘yan Shi’ah. Don haka ba a san wata ridda da ta wuce wuri kamar ta qungiyar ‘yar Shi’ah Nusairiyyah, da ta ‘yan Shi’ah Isma’iliyya Baxiniyyah da makamantansu ba. Wanda ya fi kowa shahara wurin yaqar waxanda suka yi ridda dai shi ne Abubakar Raliyallahu Anhu. Kuma masu ridda daxai sun fi yawa cikin qungiyoyin da ke husuma da Abubakar. Ka ga dai ridda na nan biye da ‘yan-sha-biyu kenan.

 Wannan bayyane yake ga duk wanda ya bar musulunci da musulmi. Ba mai shakkar cewa jinsin masu ridda sun fi yawa cikin waxanda ke da dangantaka da ‘yan Shi’ah kuma riddarsu tafi kowace muni da tsanani a kafirci.

 Sai cewarsa wai: ‘Yan Shi’ah sun banbanta da kowace mazhaba, sannan duk sauran mazhabobi sun haxu a kan wasu asulla na aqida. Idan yana nufin cewa ‘yan Shi’ah sun savawa duk mazhabobi ga abin da suka kevanta da shi, wannan haka yake, ba ga ‘yan Shi’ah kaxai ba, ga duk sauran qungiyoyi. Ba ka ganin Harijawa sun banbanta da kowa ga abin da suka kevanta da shi kamar kafirta mai savo, da kafirta Ali Raliyallahu Anhu, da cewa ba a yi wa Manzo xa’a ga abin da Manzo bai ce Allah Ta’ala ne ya yi umurni da shi ba, da cewa yana yiwuwa Manzon Allah ya yi zalunci wurin rabon abubuwa da kuma cikin hukuncinsa, da kuma qin bin hadisi mutawatiri in ya sava wa zahirin Alqur’ani, kamar cewa hannu varawo ana yanke shi ne daga kafaxa.. da dai ire-iren waxannan.

 Amma in sun ce su ‘yan Shi’ah sun kevantu da dukan maganganansu, to, ba haka ba ne, don aqidunsu xaya ce da ta Mu’utazilawa. Kuma manyan ‘yan Shi’ah na farko masu sifaita Allah da jiki ne. Sannan sun yi muwafaqa da Mu’utazilawa a sha’anin yarda da qaddara. Manyansu na farko sun kasance suna tabbatar da qudura ga bawa, kuma na farkonsu masu tsananin inkari ne ga qudurar Allah fiye da inkarin da suke yi ma siffofin Allah, da cewar da suke yi masu zumubi ba su fita daga wuta.

 A taqaice dai ‘yan Shi’ah na da maganganun da suka kevanta da su, kuma akwai waxanda suke tare da wasu a cikinsu, kamar yadda Mu’utazilawa da Harijawa da makamantansu su ke.

 Amma Ahlul-hadith kuma Ahlus-Sunnah wal Jama’a sun kevantu da bin Alqur’ani da Sunnar da ta tabbata daga Manzonsu Sallallahu Alaihi Wasallama ga asuli da reshe, da kuma abin da Sahabban Manzo suka kasance a kansa. Wannan Savanin Mu’utazilawa da Harijawa da Shi’ah ‘yan-sha-biyu da waxanda suka yi muwafaqa da su a cikin wasu maganganunsu. Basu bin hadissan da amintattun malamai suka riwaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama waxanda malaman hadisi sun san ingancin su.

Kuma ai sava wa mazhabobin da suka yi ya fi nuna vacin maganganunsu fiye da nuna cewa maganganun qwarai ne. Kasancewar kuwa maganganun qungiya sun banbanta da na sauran qungiyoyi ba shi ke nuna cewa maganganun daidai suke ba, kamar yadda haxuwarsu ga wata magana ba shi ke nuna cewa kuskure ce ba.

 To in an ce: Annabi ya ce al’ummarsa za ta rarrabu zuwa kashi saba’in da uku, kuma xaya ce kawai ke tsira. Saboda haka dole ne xayar ta banbanta da saba’in da biyun da suka rage. Sai mu ce haka ne. Haka ma hadisin ke nuna cewa saba’in da biyun na banbanta da junansu kamar yadda suka banbanta da xayar mai tsira. Hadisin bai nuna cewa sauran qungiyoyin za su haxu a kan asullan aqidodi ba. Kai zahirin hadissin na nuna cewa saba’in da ukun dukansu sun banbanta da juna. A nan za a san cewa, gefen banbanci shi ne abin zargi ba gefen da suka haxu a kansa ba, don Allah Ta’ala ya yi umurni da jama’a da kuma jituwa tsakanin musulmi, ya kuma zargi rarrabuwa da savani. Allah Ta’ala ya ce:

﴿وَٱعتَصِمُواْ بِحَبلِ ٱللَّهِ جَمِيعا وَلَا تَفَرَّقُواْ ﴾ آل عمران: ١٠٣

 Ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya, kuma kada ku rarraba. Ali-Imran: 103.

Ya kuma ce:

 ﴿وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ تَفَرَّقُواْ وَٱختَلَفُواْ مِن بَعدِ مَا جَاءَهُمُ ٱلبَيِّنَتُ وَأُوْلَئِكَ لَهُم عَذَابٌ عَظِيم١٠٥ يَومَ تَبيَضُّ وُجُوه وَتَسوَدُّ وُجُوه فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱسوَدَّت وُجُوهُهُم أَكَفَرتُم بَعدَ إِيمَنِكُم فَذُوقُواْ ٱلعَذَابَ بِمَا كُنتُم تَكفُرُونَ١٠٦ وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱبيَضَّت وُجُوهُهُم فَفِي رَحمَةِ ٱللَّهِ هُم فِيهَا خَلِدُونَ١٠٧ تِلكَ ءَايَتُ ٱللَّهِ نَتلُوهَا عَلَيكَ بِٱلحَقِّ وَمَا ٱللَّهُ يُرِيدُ ظُلما لِّلعَلَمِينَ١٠٨﴾ آل عمران: ١٠٥ - ١٠٨

 Kada ku kasance kamar waxanda suka rarrabu suka yi savani bayan bayani ya zo masu, to, waxannan suna da babbar azaba. Ranar da wasu fuskoki za su yi fari, wasu kuma su yi baqi. Amma waxanda fuskokinsu suka yi fari sai a ce masu: “Shin kun kafirta ne bayan imanininku? To, ku xanxana azaba saboda abin da ku ka kasance kuna aikatawa. Ali-Imran: 105-106.

 Xan Abbas da waninsa sun ce, fuskokin Ahlus-Sunnah za su yi fari, fuskokin ‘yan bidi’a da masu savani su yi baqi. Allah Ta’ala ya ce

 ﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُم وَكَانُواْ شِيَعا لَّستَ مِنهُم فِي شَيءٍ إِنَّمَا أَمرُهُم إِلَى ٱللَّهِ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَفعَلُونَ١٥٩﴾ الأنعام: ١٥٩

Lalle waxanda suka rarraba addininsu; suka zama qungiyoyi ba ka cikinsu ga komai. Al-Anam: 109.

Ya kuma ce:

 ﴿ وَمَا ٱختَلَفَ فِيهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ أُوتُوهُ مِن بَعدِ مَا جَاءَتهُمُ ٱلبَيِّنَتُ بَغيَا بَينَهُم ﴾ البقرة: ٢١٣

 Ba waxanda suka yi savani a cikinsa face waxanda aka ba su shi bayan bayani ya zo masu, (suka yi haka) don zalunci tsakaninsu. [Al-baqara 213]

Ya kuma ce:

 ﴿وَمَا تَفَرَّقَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلكِتَبَ إِلَّا مِن بَعدِ مَا جَاءَتهُمُ ٱلبَيِّنَةُ٤﴾ البينة: ٤

 Waxanda aka ba su littafi ba su rarraba ba sai bayan bayani ya zo masu. Al-Bayyinah: 4.

 Idan lamarin ya kasance haka, to, qungiyar da tafi kowaci savawa jama’a da kuma savani tsakanin ita kanta, tafi sauran qungiyoyi cancantar zargi, wadda ta fi qarancin rarrabuwa da kusantar jama’a ta fi cancantar kasancewa a kan gaskiya. In dai Imamiyyah sun fi cancantar sava wa sauran qungiyoyin al’umma to, sun fi kowa nisa daga gaskiya, musamman ma kasancewar sun fi duk qungiyoyin al’umma savani tsakanin kansu, har aka ce qungiyarsu ta kasu zuwa saba’in da biyu. Wannan abin da muka faxa shi ne wanda aka riwaito daga Tusi da mabiyansa. Al-Hasan xan Musa An-Nubakhti ya rubuta littafi game da qididdigar qungiyoyin Shi’ah, ga shi kuma shi ma xan Shi’ar ne.

 Amma Ahlus-Sunnah sun fi kowa qarancin savani a cikin asullan addininsu, sun fi kowace qungiya kusantar juna kasancewa tsakiya a wuraren savani, don ba su faifayewa ba su kuma kasawa. Ka ga ko ai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mafi alherin lamurra shi ne matsakaicinsu”. Don haka Ahlus-Sunnah su ne mafifitan dukan qungiyoyi. Don su ne matsakaita a kowane fanni.Ko a mas’alar Sahabbai, Ahlus-Sunnah ba su wuce wurin da masu guluwi ke yi, ba su kuma cin zarafi. Xauki misali Ali Raliyallahu Anhu ‘yan-sha-biyu sun faifaye game da shi, a yayin da Harijawa suka ci zalunsa; suna kafirta shi, suna ce masa azzalumi, mai yunwar jinin musulmi, can ga bakinsu. Ahlus-Sunnah suka shiga tsakani, suka faxi gaskiya.

 Ni a iya sanina, ‘yan-sha-biyu ba su tava haxuwa a kan wata mas’ala ba koda qwaya xaya. Ita kanta wannan maganar da xan Shi’ar ya ambata xaya ce daga cikin maganganun ‘yan Shi’ar sha biyu ba duka ba. Daga cikinsu akwai masu sava ma wannan a tauhidi. Kuma mafi yawan ‘yan Shi’ah sun sava ma Imamiyyah (‘yan-sha-biyu) game da lamarin Imamai goma sha biyu. Zaidiyyah da Isma’iliyyah suna tsananin gaba da wannan aqidar ta imamai goma sha biyu.

 2.7 Maganar Wofi: Wai su Kaxai ke da

Tabbacin Suna Kan Gaskiya!

 Xan Shi’ar ya ce: Fuska ta uku, ita ce: Imamiyyah sun tabbatar cewa su da imamansu za su tsira, kuma cewa wanda ba su ba zai halaka. Ahlus-Sunnah ko ba su da tabbacin tsira ga kansu balle ga waninsu. Don haka bin ‘yan Shi’ah shi yafi cancanta ga mai hankali. Ka ga in da mutane biyu sun fita daga cikin Bagadaza suna son tafiya Kufa sai suka ga hanyoyi biyu kowanensu ya zavi xaya, sai wani mutum na uku ya zo shi ma zai je Kufa. Da ya tambayi na farkon, ka san hanyar da ka zava na kai ka Kufa? Kuma ita amintacciya ce ko a’a? Sai ya ce: Ni ban san komai ba game da wannan. Da ya tambayi na biyun sai ya ce masa, ni na tabbata tana kai ni Kufa, kuma amintacciya ce, kuma na san cewa hanyar da wannan ya bi ba zata kai shi Kufa ba, kuma ba amintacciya ba ce. To, in wannan mutum na uku ya bi hanyar mutumin farko lalle ya tabbata wawa a wurin masu hankali. Amma in ya bi na biyu to, ya nuna sanin-ya-kamata.

Martani:

 In dai har wajibi ne a yi wa shagabannin da Shi’ah ke rayawa xa’a don a tsira, to, bin shugabannin Bani Umayyah da yi masu xa’a shi ma wajibi ne. Kuma in haka ne, masu bin su ido-rufe suna bisa gaskiya duk da zagin da suke yi wa Ali Raliyallahu Anhu da yaqan ‘yan Shi’ar da suke tare da shi da suka yi. Kar ka manta su ma suna ganin cewa, yi wa shugabanni xa’a wajibi ne a komai, kuma wai, Allah Ta’ala ba zai kama shugaba da kowane irin zunubi ba, kuma wai mabiya ba su da laifi ga duk abin da suka yi wa shugaba xa’a a cikinsa. Kai, waxannan sun fi cancantar ace suna da hujja fiye da ‘yan Shi’ah, don su suna xa’a ne ga shugabannin da Allah ya tsayar, ya kuma qarfafa mulkinsu.

 Sanannen abu ne cewa maslaha da luxufin da aka samar wa bayin Allah ta hanyar sarakunan Bani Umayyah sun fi waxanda aka samu saboda shugaban ‘yan Shi’ar da babu shi, babu alamarsa, kasasshe; wanda bai iya bayyana don tsoro. Don haka ne maslahar duniya da ta lahirar da mabiya Bani Umayyah suka samu ta fi wadda mabiyan Na-Voye suka samu. Don duk tsawon jiran da suke ma sa ba ya umurnin su da kyakkyawa balle ya hane su daga aikata mumuna, bai taimakon su don samun wata maslaha ta addininsu ko ta duniyarsu. Savanin mabiyan Bani Umayyah da suka amfana qwarai ga lamurran addininsu da na duniyarsu ta hanyar shugabannin nasu da suke yi ma xa’a.

 Daga wannan ya bayyana cewa, idan hujjar da masu biyar Ali Raliyallahu Anhu ke kafawa daidai ta ke, to, mabiyan Usmanu su xin ma hujjarsu tana a kan hanya. Tasu ma ta fi cancantar kasancewa gaskiya. In ko hijjarsu vatatta ce, to ta ‘yan Shi’ah ta fi vaci. Don da su da saura Ahlus-Sunnah duk sun haxu a kan cewa, xa’ar imaman Shi’ah kuskure ne kawai da vata.

Maganar ‘yan-sha-biyu dai an gina ta a kan turaku biyu waxanda gara da gumxa suka zaizaye. Na farko, cewa suna da imami ma’asumi. Na biyu, cewa yana umurni da wani abu. To, ka ga ai imaman da suke raya cewa ma’asumai ne; ba sa kuskure sun mutu tun tuni, shi ko wanda suke jira ya vace tun fiye da shakaru xari huxu da hamsin. Wasu malaman tarihi ma sun ce ba a tava samun sa ba. To, wa suke yi wa xa’a? Sai fa malaman Shi’ah ko litaffan da suka rubuta waxanda suke cewa sun karvo daga imamai da ba su kuskure. To, kuma ai suna kuskure, sannan ba su da tabbacin cewa za su tsira.

 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama dai shi ne ke isar da saqo daga Allah Ta’ala game da abin ya yi umurni da shi kuma da wanda ya yi hani daga gare shi, ba wata halittar da ake yi wa xa’a kai tsaye sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. To, in an mayar da imami ko shaihi bayan fakuwarsa ko mutuwarsa abin kira, kuma ana neman ya biya wasu buqatu, kenan mamacin ya yi kama da Allah Ta’ala, wanda kuwa yin haka fita ne daga tushen musulunci shi ne Tauhidi.

 Duba mafi yawan ‘yan xariqu, suna dogaro ne a kan wasu hikayoyin da aka riwaito daga shehinsu, waxanda da yawa daga cikinsu qarya ce aka yi masa, wasu kuma kuskure ne shehin ya yi, sai su bar riwaya ta gaskiya daga Annabi ma’asumi zuwa ga riwayar da ba a gasgatawa kuma daga wanda ba ma’asumi ba. To, idan waxannan ‘yan xariqun sun yi kuskure ne anan, to, ‘yan-sha-biyu sun fi su kuskure don sun fi zura qarya a cikin abubuwan da suke riwaitowa daga imamansu, kuma sun fi tsananin wuce iyaka ga raya cewa imamansu ma’asumai ne.

 Misalin da ya bayar na masu tafiya Kufa shirme ne kawai. Wa ya sani ko wanda ya ce ya sani qarya yake yi? Wataqila ma dibara ce yake yi don ya samu abokin tafiya in sun yi nisa ya yi masa fashi! Shi dai na farkon ya bar ka da nazarinka, bai yi ma ka qarya ba don ka so shi. Ashe aikin hankali ba shi ne ka bi wannan kawai don ya cika baki ba, sai dai ka yi naka nazari har ka gano lafiyayyar hanya.

 Kuma wai, yana nufin duk wanda ke bisa aqidarsu ya sakankance zai shiga aljanna koda kuwa ya bar farillai, ya aikata haramun? To, wannan kam ko ‘yan-sha-biyun ba su ce haka ba. Kuma duk wani mai hankali ma ba zai faxi haka ba.

 Wai, a ganinsu sun samu tabbacin tsira ne saboda son Ali Raliyallahu Anhu a matsayinsa na aikin lada da suka ce, savo ba ya cutar da mai shi. Saboda haka kenan barin salloli da aikata alfasha koda zuriyar Ali ne Raliyallahu Anhu ba zasu cutar ba, kai, koda mutum ya zubar da jinin Bani Hashim, dangin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama matuqar dai yana son Ali Raliyallahu Anhu. Wa zai gasgata wannan wofintattar magana? In kuma sun dawo sun ce, so na gaskiya na sa mutum ya bi masoyinsa, sai lamari ya koma ga cewa dole ne kenan a aikata wajibbai kuma a bar abubuwan da Allah Ta’ala ya haramta.

In kuma suna nufin cewa, duk wanda ke da aqida ingantacciya ya kuma aikata wajibai ya nisanci abubuwan da aka haramta zai shiga aljanna, to, wannan ita ce aqidar Ahlus-Sunnah, don su suna yanke cewa wanda ya ji tsoron Allah Ta’ala zai shiga aljanna kamar yadda Al-Alqur’ani ya ba da tabbaci. Amma Ahlus-Sunnah ba su yanke hukuncin shiga aljanna akan wani mutum na musamman don ba su da tabbacin cewa yana cikin masu tsoron Allah Ta’ala. Amma in an san cewa, ya mutu akan taqawa to, ana sanin cewa ya na cikin ‘yan aljanna. Don haka ne suke cewa, waxanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ‘yan aljanna ne to, batu ya qare. Amma wanda mutane da yawa suka yaba da cewa mai rikon addini ne to, ba dukan Ahlus-Sunnah ke yarda da yin yanke a kan zamansa xan aljanna ba, sai dai kyautata zato.

 Daga nan ne ya bayyana cewa, ‘yan-sha-biyu ba su da wani yaqinin da ake yabawa wanda suka kevanta da shi koma bayan Ahlus-Sunnah.

 In sun ce suna da yaqini a kan wanda suka ga yana lizimtar aikata wajibai sannan yana nisantar muharramai cewa shi xan aljanna ne, ba tare da imami ma’asumi ya faxa masu abin da ke cikin zuciyarsa ba. Sai a ce masu wannan matsalar ba ta rataya da shugabanci ba. In ma an qaddara cewa akwai ingantacciyar hanya mai kai ga wannan to, ta Ahlus-Sunnah ce, kuma sun qwarewa shiga hanyar. In ko babu wata ingantacciyar hanya zuwa ga wannan, to, wannan magana da ba a gina a kan ilimi ba, babu wata falala a cikinta, haka ma cikin rashinta. A taqaice dai babu wani ingantaccen ilimin da za su raya face Ahlus-Sunnah sun fi su cancantarsa, amma abin da suka raya na jahilci to, wannan naqasu ne, kuma Ahlus-Sunnah sun fi kowa nisa daga gare shi.

 Kuma ma a qashin gaskiya yaqinin da Ahlus-Sunnah ke da shi na samun tsirar shugabanninsu ya fi na Shi’ah ‘yan-sha-biyu. Don shugabanninsu bayan Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama sune magabata na farko daga cikin Muhajiruna da Ansaru, sun kuwa sani yanke cewa, za su sami tsira. Suna sheda cewa Sahabban nan goma za su shiga aljanna, kuma Allah ya ce wa Sahabban Badar: “Ku yi abin da kuke so, lalle na gafarta maku”. Kai har ma suna cewa: “Babu wanda zai shiga wuta cikin waxanda suka yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama mubaya’a a qarqashin itaciyar nan”. Kamar yadda ya tabbata a cikin ingantaccen hadisi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Waxannan sun fi mutum dubu da xari huxu, kuma shugabanni ne na Ahlus-Sunnah. Suna sheda cewa babu wanda zai shiga wuta cikinsu, kuma shahada ce da aka gina ta a kan ilimi, kamar yadda Alqur’ani da Sunna suka nuna.

 Ahlus-Sunnah na yin sheda ko dai gamammiya ko kuma ga wasu sanannu, amma duk suna gina wannan akan ilimi. Amma ‘yan-sha-biyu su suna sheda a kan abin da ba su sani ba, ko su yi Shedar-Zur wadda sun san qarya ce, kamar yadda imamus-Shafi’i ya ce: “Ban ga mutanen da ke shedar qarya kamar Shi’ah ‘yan-sha-biyu ba”.

 Kuma duk imamin da aka shaida cewa zai tsira ko dai ya kasance wanda ake yi wa gamammiyar xa’a ne, ko kuma wanda ake yi wa xa’a in ya yi umurni da abin da yake xa’a ne ga Allah Ta’ala da Manzonsa, da kuma abin da yake faxa daga ijtihadinsa in ya san babu abin da ya fi wannan. In imami shi ne na farkon to, Ahlus-Sunnah ba su da wani shugaban da ke haka bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Su suna faxa ne kamar yadda Mujahid da Hakim da Malik da sauransu suka faxa cewa: “Duk mutum ana karva kuma ana barin maganarsa face Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama”. Su suna sheda cewa shugabansu shi ne mafificin halitta. Kuma suna sheda cewa duk wanda ya yi koyi da shi, ya bi umurninsa, ya hanu daga haninsa zai shiga aljanna. Kuma shaidar su Ahlus-Sunnah ta fi ta Shi’ah ‘yan-sha-biyu kamala har bisa wadda su ke yi wa shugabanninsu Askari i da ii da makamantansu cewa wanda ya yi masu xa’a zai shiga aljanna.

 Allah Ta’ala dai ya yi alqawarin ni’ima ga wanda ya yi masa xa’a kuma ya yi wa Manzonsa xa’a, kuma ya yi alqawarin tavarwa ga wanda bai aikata haka ba. To, an rataya ni’ima a kan xa’a ga Allah Ta’ala da Manzonsa. Kamar yadda Allah ya ce:

﴿وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنعَمَ ٱللَّهُ عَلَيهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَاءِ وَٱلصَّلِحِينَ وَحَسُنَ أُوْلَئِكَ رَفِيقا٦٩﴾ النساء: ٦٩

Kuma wanda duk ya yi wa Allah da Manzonsa biyayya to, waxannan suna tare da waxanda Allah ya yi wa ni’ima daga cikin Annabawa da siddiqai da shahidai da salihai kuma maqwabtaka da waxannan ta kyautata An-Nisa: 69.

Da makamantansa.

 Idan ya kasance haka, to, Allah Ta’ala na cewa:

﴿فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ مَا ٱستَطَعتُم ﴾ التغابن: ١٦

ku ji tsoron Allah gwargwadon ikonku At-Tagabun: 16.

Duk wanda ya yi iyakar qoqarinsa wurin yin xa’a ga Allah da Manzonsa to, zai kasance cikin ‘yan aljanna.

 Saboda haka cewar ‘yan-sha-biyu wai, ba mai shiga aljanna sai in shi xan-sha-biyu ne ba ya da banbanci da maganar Yahudawa da Nasara:

 ﴿وَقَالُواْ لَن يَدخُلَ ٱلجَنَّةَ إِلَّا مَن كَانَ هُودًا أَو نَصَرَى تِلكَ أَمَانِيُّهُم قُل هَاتُواْ بُرهَنَكُم إِن كُنتُم صَدِقِينَ١١١ بَلَى مَن أَسلَمَ وَجهَهُ لِلَّهِ وَهُوَ مُحسِن فَلَهُ أَجرُهُ عِندَ رَبِّهِ وَلَا خَوفٌ عَلَيهِم وَلَا هُم يَحزَنُونَ١١٢﴾ البقرة: ١١١ - ١١٢

Kuma sun ce ba wanda zai shiga aljanna face in ya kasance Bayahude ne ko Banasare. Wannan gurinsu ne. Ka ce, su kawo hujjarsu in sun kasance masu gaskiya. Ba haka ba ne, duk dai wanda ya miqa wuyansa ga Allah (ya musulunta) kuma ya kasance mai kyautatawa, to, yana da ladarsa wurin ubangijinsa. Kuma ba tsoro gare shi, ba baqin ciki. Al-Baqarah: 111-112.

Sanannen abu ne cewa, wanda ‘yan-sha-biyu ke jira ba shi wajaba a kan kuwa ya yi masa xa’a, don ba a san wata maganar da aka naqalta daga wurinsa ba. Don haka, wanda ya yi wa Manzo xa’a zai shiga aljanna ko da bai yi imani da wannan imamin ba. Wanda ya yi imani da wannan imamin kuma ba zai shiga aljanna ba in bai yi wa Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama xa’a ba. Don haka xa’ar Manzo ita ce abin dogara akai wurin samun tsira ba zama xan-sha-biyu ba. Ko a nan ta bayyana cewa, Ahlus-Sunnah sun tabbatar da cewa za su samu tsira da kuma tsira ga duk wanda yake bisa tafarkin na Sunnah.

 2.7 Wai Sun Karvo Mazhabarsu Daga Ma’asumai

 Xan Shi’ar ya ce: Fuska ta huxu, ita ce, ‘yan Shi’ah Imamiyyah sun karvo mazhabarsu ne daga imamai ma’asumai waxanda aka sani da falala da ilimi da gudun duniya da tsentseni, masu shagalta kowane lokaci da ibada da addu’a da karatun Alqur’ani, da dawwama a kan wannan tun yarantansu har mutuwarsu. Daga cikinsu akwai masu koya wa mutane ilimi, kuma a kansu ne suratul-Insan ta sauka. Da ayar tsarkin Ahlul-Baiti da wajabcin son su, da ayar la’ani da sauransu. Ali Raliyallahu Anhu ya kasance yana yin raka’a dubu kowane yini da dare kuma yana karanta Alqur’ani duk da jarabar yaqi da ya yi fama da ita.

 2.7.1 Imami na Farko:

Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu

Xan Shi’ar ya ce: Imami na farko shi ne Ali Raliyallahu Anhu wanda shi ne mafificin bayi bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Allah Ta’ala ya kira ran Manzo wurin da ya ce:

﴿ وَأَنفُسَنَا وَأَنفُسَكُم ﴾ آل عمران: ٦١

Da kawunammu da kawunanku. Al-Imran: 61

Manzo ya qulla ‘yan’uwantaka da shi, kuma ya aurar masa da xiyarsa. Falalarsa ba a voye take ba, mu’ujizozi da yawa sun bayyana a hannunsa har wasu mutane suka ce shi ma abin bautawa ne, ya kashe su. Wasu kuma suka bi maganarsu kamar Gulatu da Nusairiyyah.

Martani:

 Ba mu yarda cewa, ‘yan-sha-biyu sun karvo mazhabarsu daga Ahlul-Baiti ba, ba su ba ba sauran ‘yan Shi’a ba. Su da suka sava wa Ali Raliyallahu Anhu da Ahlul-Baiti a cikin duk asullansu da saka sava wa Ahlus-Sunnah a cikinsu! Abin da ya tabbata daga Ali Raliyallahu Anhu da Ahlul-Baiti shi ne tabbatar wa Allah Ta’ala da siffofin da ya tabbatar wa kansa da imani da qaddara da tabbatar da halifancin halifofi uku na farko, da tabbatar da falalarsu, kuma duk a nan ‘yan-sha-biyu sun sava ma su. An samu riwayoyi da yawa game da wannan cikin littaffan malamai ta yadda waxannan riwayoyin na sa mutum ya kai ga samun ilimi na yaqini cewa Ali da Ahlul-Baiti ba su tare da ‘yan-sha-biyu.

 ‘Yan-sha-biyu kuma harwayau sun sava a tsakanin junansu game da abubuwan da suka shafi sifofin Allah Ta’ala da imani da qaddara, da sauran abubuwan da suka shafi asullan addininsu. To wace magana ce suka karvo daga imamansun da ba su kuskure? Har ma abin da ya shafi imamancin suna da Savani da yawa cikin sa.

 Kai har ma game da Mahadin su ke jira suna da savani. Daga cikinsu akwai masu cewa Ja’afar xan Muhammad ne. Wasu kuma sun ce a’a xansa ne Musa xan Ja’afar. Akwai kuma waxanda suka ce Muhammad xan Abdullahi xan Hasan shi ne Mahadin. A yayin da wasu suka ce Muhammad xan Hanafiyya ne. Wasu kuma sun ce Ali xan Hassan xan Husain ya yi wasici ne ga xansa Abu Ja’afar, wasu kuma na cewa ga xansa Abdullahi. Haka dai a kowane imami sai da suka yi savani.

 Wasu abubuwan da ya faxa sharholiya ce kawai, irin cewar da ya yi, a kansu ne aka saukar da Suratul Insan. Domin wannan surar a Makka ta sauka tun kafin auren Ali da Nana Fatima. Ita ma ayar tsarkake Ahlu-Baiti da tafi da qazanta daga gunsu, tattare kasancewarta tana magana ne a kan matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ba labari take bayarwa ba, umurni ne kamar irin umurni da aka yi wa musulmi baki xaya da yin alwala kuma Allah ya yi irin wannan maganar a Suratul Ma’ida ya ce: Allah ba ya nufin ya quntata ma ku, amma yana son ne ya tsarkake ku. Al-Ma’ida:6.

 Sai cewar da ya yi wai, Ali na sallah raka’a dubu kowace rana. Wannan ya nuna bai ma san mene ne falala ba. Domin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava wuce raka’a goma sha uku a dare xaya ba kamar yadda ya zo a cikin Buhari da Muslim. A cikin Buhari da Muslim kuma, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mafificin tsayuwar dare shi ne na Annabi Dawuda Alaihis Salamu; ya kan yi baccin rabin dare, sannan ya yi tsayin sulusi, sannan ya sake baccin sudusi”.

 Haka shi ma cewar da ya yi, wai, Ali shi ne mafificin talikai bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, cika baki ne kawai, ba hujja.

 Hadisin da ya kawo cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qulla ‘yan’uwantaka tsakaninsa da Ali shi ma irin wancan ne. Don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya qulla tsakaninsa da kowa ba, bai kuma yi tsakanin Muhajirai wasu-wasu ba, ko tsakanin Ansarai wasu-wasu. Abin da ya tabbata a sahihan hadissai shi ne, ya yi wannan haxin zumunci ne tsakanin Muhajirai da Ansarai, kamar yadda ya yi a tsakanin Sa’adu xan Rabi’u da Abdurrahman xan Aufu, da kuma tsakanin Salmanul-Farisi da Abud-Darda’i.

 Sai cewa, Allah ya sanya Ali shi ne ainin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama in da ya ce: Da kawunanmu da kawunanku. Ali Imran: 61. Wannan in da Allah ya ce ne: In da ma lokacin da kuka ji shi (qazafin) muminai maza da mata sun zaci alheri ga kawunansu (yana nufin ga ‘yar uwarsu kuma uwarsu A’ishah). An-Nur:12. Ka ga duk muminai ‘yan’uwan juna ne sashensu majinvinta sashe.

 Aurar ma sa da Fatima kuma daraja ce kamar aurar ma Usman da Ummu Kulsumi da Ruqayyatu. Don haka ma ake ce ma Usman Dhun-Nuraini mai haske biyu. Haka auren ‘yar Abubakar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi daraja ne ga Abubakar. Haka auren xiyar Umar shi ma daraja ne ga Umar xin. Saboda haka duk halifofinsa huxu Allah ya ba su wannan falalar ta surukuta da shi Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Sai cewar da ya yi Ali na da mu’ujizoji masu yawa. Wataqila yana nufin karamomi. Wannan ko ba wani kayan gabas ne ba ga Ali, don ya fi daraja a kan mafi yawan waxanda suka samu karamomin, cikinsu har da jahilai. Kuma don wasu sun xaukaka shi har sun ce ma sa Allah, wannan bai zama daraja. Ai duk mu’ujizar da ta bayyana gare shi in har akwai to, ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta fi ta, amma babu mai hankalin da ya tava ce ma sa Allah. Shikenan don wasu sun ce Annabi Isah Allah ne sai a fifita shi a kan Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama? Ina banbancin shirmen masu ce ma sa Allah da na Harijawa masu kafirta shi? In ka ce saboda xaukakarsa ne da zamansa na Allah waxancan suka ce shi ne Allah, wani zai ce, saboda yawan zunubansa da miyagun ayyukansa Harijawa suka kafirta shi. In ka ce saboda rashin hankalin Harijawa ne suka kafirta shi, to, su ma waxancan ‘yan Shi’ar saboda rashin hankalinsu ne suka Allantar da shi. Kuma tare da haka Harijawa sun fi ‘yan Shi’ah hankali da riqon addini sau ba iyaka, sun fi su kafa hujja mai xan sauraruwa.

 A wurin Ali kansa gara Harijawa da Gulatun ‘yan Shi’ah masu Allantar da shi.

 2.7.2 Hasan da Husaini

 Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: ‘Yayansa biyu su ne jikokin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, kuma su ne shugabannin matasan aljanna. Imamai biyu ne bisa ga nassin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Su ne suka fi kowa ilimi da zuhudu a zamaninsu. Sun yi jihadi a tafarkin Allah yadda ya kamata har aka kashe su. Hasan ya sa rigar gashin dabbobi a qarqashin tufafinsa masu tsada ba tare da mutane sun san da haka ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama watarana ya xora Husaini akan cinyarsa ta dama ya xora xansa Ibrahimu akan cinyarsa ta hagu, sai Jibrilu Alaihis Salamu ya sauko ya ce ma sa: “Allah ya ce ba zai haxa ma ka su ba, don haka ka zavi xayansu”. Sai Manzo ya ce, in Husain ya mutu zan yi kuka, Ali ma ya yi, sannan Fatima ta yi, amma in Ibrahim ya mutu to, ni kaxai zan yi kuka, sai ya zavi mutuwar Ibrahim ya kuwa mutu bayan kwanan uku. Wannan ne ya sa, inji xan Shi’ar duk lokacin da Husaini ya zo wurinsa sai ya ce maraba da wanda na fansa da xana Ibrahim.

Martani:

 Tabbataccen abu shi ne Hasan shugaba ne da Allah zai kimtsa shirin musulmi da shi a lokacin tashin hankali da rikici a tsakaninsu. Haka Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa. Kuma ta tabbata cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan xora Hasan a xaya cinyarsa, Usamatu xan Zaidu a xaya, ya ce: “Ya Allah! Haqiqa ina son su, kai ma ka so su, ka so wanda yake son su”.

 Wannan kuwa na nuna abin da Hasan ya yi na sauka daga muqami da rashin ci gaba da tilasta waxanda ba sa son shugabancinsa shi ne abin da Allah da Manzo ya fi so. Yin hakan ba aibi ne ba, ba kuma keta alfarmar gaskiya ne ba kamar yadda ‘yan-sha-biyu ke gani. Wannan shi ya sa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya so su shi da Usamatu. Ka ga ai ko Usamatu yana cikin masu qyamar fitina da yaqi a lokacin tashin hankali, shi ya sa bai shiga cikin rundunar Ali ko ta Mu’awiyah ba. Shi kuma Hasan a kullum yana ba mahaifinsa shawarar barin yaqi. Savanin abin da ‘yan-sha-biyu ke cewa, Hasan ya tozarta musulmi da ya nemi a zauna lafiya. In da a ce, akwai wani shugaba da ya wajaba kowa ya bi shi don yana ma’asumi kuma duk wanda ya hau ba shi ba mulkinsa vatacce ne, ai da wannan sulhin da Hasan ya yi ya zama varna kamar yadda suke cewa. To, da haka ne ko za a yabi Hasan a kan wannan gyara? Sai dai ko a ce an yi masa uzuri don rauni ko kasawa. Hasan kuma ya fi Husaini damar yin yaqi, amma ya bar shi. Allah na xaukaka darajar muminai ko a aljannan wani ya fi wani. Tattare da kasancewar yardar Allah ta tabbata a gare su baki xaya.

 Sannan idan har Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya nassanta zamansu imamai, to, ba wani amfani ga nassanta su da Alin ya yi. Mu dai mun san Hasan da Husaini abar qaunar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne a duniya, kuma ya saka su a cikin bargo ya yi masu addu’a. Suna da darajoji masu yawa, da matsayi babba a wurin musulmi. Amma cewa, sun fi kowa ilimi ko gudun duniya wannan cika baki ne kawai, ba dalili.

 Sai cewar da ya yi wai, sun yi jihadi har suka bar duniya. Abin da duniya ta sani shi ne, Hasan ya kira Mu’awiyah da kansa ya damqa masa ragamar shugabancin musulmi duk da kasancewar rundunar Iraqi duka tana tare da shi. A tarihinsa bai tava zavin yaqar musulmi ba. A lokacin mutuwarsa kuma wasu sun ce an saka masa guba ne a abinci. Ta haka ya samu xaukakar yin shahada kenan. Amma dai bai mutu yana riqe da makami ba, sam. Shi kuma Husaini ya fita da nufin yaqi, amma a zatonsa zai samu goyon bayan ‘yan Shi’ar Iraqi. Da ya lura da cin amanarsu dai ya canza niyya, ya buqaci a bar shi ya koma gida, ko ya je jihadin kafirai ko ya tafi da kansa wurin sarki Yazidu. Rashin samun damar yin ko xaya daga cikin abin a ya nema shi ya sa ya yi yaqi kuma har aka kashe shi akan zalunci, ya yi shahada.

 Shi kuma Hasan da xan Shi’ar ya ce wai, yana sanya tufan gashin dabbobi a qarqashin tufan auduga, wannan ba wata daraja a cikinsa, don kamar shigen cewa, Ali na raka’a dubu a kullum ne. Kawai abin da za mu ce shi ne, da yin haka addini ne da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sunnanta haka, ko dai ta hanyar ya aikata, ko ya nuna ma wani ya aikata, ko wani ya yi haka Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbatar da abin da ya yi xin. Tunda kuwa aka ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba haka yake yi ba, ba kuma haka Sahabbai suke yi ba, mun san ba wata falala a cikin haka. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da kansa ya kan sanya rigar auduga musamman a cikin tafiye-tafiyensa.

 Daga qarshen hadisin da ya kawo cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya xora Husaini da Ibrahim a kan cinansa, kuma Jibrilu Alaihis Salamu ya zo ya ba shi zavi a tsakaninsu, tatsuniya ce kawai da ba ta da asali sai a cikin qwaqwalen jahilai. Kuma ai a ga Hasan nan an bari tare da Husaini. To, sai me?

 2.7.3 Zainul Abidina da Baqir da Sadiq

Shi kuma Ali xan Husaini Zainul abidina ya kasance yana azumi da rana, ya yi sallah da dare, ya kuma karanta Alqur’ani. Yana yin sallar raka’oi dubu ga yini da darensa kowace rana. Yana kuma addu’a bayan rakao’i biyu da addu’oi nasa da waxanda aka riwaito daga iyayensa, sannan ya jerfar da takarda yana mai cewa, yaya ma zan iya yin ibada irin ta kakana Ali. Kamar yana damuwa. Ya kasance yana yawaita kuka har hawaye suka yi masa tsaga a fuska, yayi sajada har aka kira shi mai tambon sallah. Kuma Manzo ya kira shi Sayyidul Abidina, shugaban masu ibada.

 Akwai lokacin da Hishamu xan Abdulmalik ya je aikin hajji ya yi qoqarin sunbuntar Hajarul-Aswad bai samu damar yin haka ba saboda gwamatso, amma lokacin da Ali xan Husaini ya zo yin haka sai dukan mutane suka ba shi wuri ya sumbaci dutsen shi kaxai. Sai Hishamu xan Abdulmalik ya ce, wane ne wannan? Sai Farazdaq ya yi waqoqin nan nasa da aka sani game da shi. Sai Zainul Abidina ya aika ma Farazdaq dinari dubu zuwa, shi ko ya qi karva, ya ce, abin da ya sa na yi wannan waqar don fusata saboda Allah da Manzonsa. Ba zan karvi kuxi a kansa ba. Sai ya ce mu Ahlul-Baiti abin da ya fita daga wurinmu ba ya komawa. Sai Farazdaq ya karvi kuxin.

 Akwai wasu mutane a Madina, abincinsu na zo masu da dare ba su san daga inda yake zuwa ba, sai da Zainul Abidina ya mutu sai suka gane cewa abincin daga wurinsa yake zuwa.

 Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Xansa Muhammad Al-Baqir ya fi kowa zuhudi da ibada. Sujada duk ta kware fuskarsa. Ya fi kowa ilimi a zamaninsa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kira shi Baqir, mai ramin sujada. Jabiru xan Abdullahi ya zo wurinsa a lokacin Baqir xin yana qarami a makarantar Allo, sai ya ce masa: “Kakanka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na gaishe ka”. Sai aka ce wa Jabir yaya aka yi haka? Sai ya ce: Na kasance wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Husaini na bisa qafarsa yana wasa, sai Manzo ya ce, za a haifa ma sa xan da ake kira Ali, ranar tashin qiyama wani mai kira zai kira yana cewa, shugaban masu ibada ya tashi, sai Alin ya tashi, sannan a haifa ma sa xan da ake kira Muhammad Al-Baqir, zai fexe ilimi fexewa. In ka haxu da shi ka isar ma sa da gaisuwata. Abu Hanifa ya riwaito shi da waninsa.

 Xan Shi’ar ya ce: Sai kuma xansa As-Sadiq wanda ya fi duk mutanen zamaninsa ilimi da ibada. Malamman tarihi sun riwaito cewa, shagaltarsa da ilimi ta hana masa neman shugabanci. Umar xan Abul Miqdami ya ce: Na kasance in na dubi Ja’afar xan Muhammad As-Sadiq sai in san cewa yana daga cikin zuriyar Annabawa. Shi ne ya yaxa fiqihun ‘yan-sha-biyu da ilimi na haqiqa da aqidodi na yaqini. Bai kasance yana ba da labarin abu ba face ya auku. Don haka na ake kiran sa As-Sadiq Al-Amin.

 Abdullahi xan Husaini ya tara mabiyan Ali don yin mubaya’a ga ‘ya’yansa biyu, sai Sadiq ya ce ma sa, wannan lamarin ba zai auku ba, sai ya yi fushi a kan haka. Sai ya ce, mai shuxin hular can ne zai zama sarki, yana nuna Mansur. Da Mansur ya ji haka, ya san cewa lamarin zai auku, kuma sarauta za ta kai wurinsa. Amma lokacin da ya samu matsala har ya gudu sai ya rinqa cewa, ina zancen mai gaskiyar nan nasu? A qarshe dai shi ya sami mulkin.

Martani:

 Shi dai Zainul Abidina yana daga cikin manyan Tabi’ai a fagen ilimi da riqon addini. Malaman Sunna sun yi ma sa sheda a zamaninsa.

 Malam Yahaya xan Sa’idu ya ce: “Zainul Abidina ne mafi darajar bahashimen da na tarar a Madina”. Shi kuma Muhammadu xan Sa’adu cewa ya yi: “Zainul Abidina ya kasance amintacce, yardajje, mai yawan hadisai, na qwarai; masu gajeruwar hanya”. Yahaya xan Sa’idu kuma ya ce, na ji Zainul Abidina na cewa: “Ya ku mutane! Ku so mu irin son musulunci. Wannan son da kuke yi mana ya kusa zama abin kunya a kanmu”.

 Sai cewa yana raka’a dubu kullum. Mun riga mun faxi cewa, wannan ba zai yiwu ba sai in an yi sallolin ba yadda shari’ah ta nema ba. Kuma tun can asali shari’a ba ta yi umurni da yin haka ba. Haka kuma ba wani hadisi mai asalai a kan cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya sa ma sa wannan laqabi na Sayyidul Abidina.

 Shi ma xansa Abu Ja’afar Al-Baqir yana daga cikin masu ilimi da riqon addini. An ce ana kiransa Baqir ne don ya tona ilimi, ba don sujada ta ci goshinsa ba kamar yadda xan Shi’ar ya ce. Amma shi ma ba gaskiya ba ne a ce ya fi kowa ilimi a zamaninsa. Ga irin su Zuhuri a zamaninsa wanda malamai sun san ya fi shi ilimi. Hadisin cewa, Annabi ya kira Baqir shi ma ba ya da asali, qarya ne. Haka cewa, wai, Jabir Raliyallahu Anhu ya isar ma sa da gaisuwar Annabi.

 Ja’afarus-Sadiq ma haka. Yana cikin malamai masu daraja. Amru xan Abul Miqdami ya ce: Duk na kalli Ja’afar xan Muhammadu nikan gano cewa, yana cikin zuri’ar annabta. Amma cewa, ya kama ibada ya bar sha’anin mulki ya ci karo da aqidarku ta ‘yan-sha-biyu. Domin a wurinku dole ne ya jagoranci jama’a tun da Allah ne ya xora ma sa, inji ku. In da ya tsaya ya yi wannan wajibin ai da ya fi ma sa yawan nafilfili ko?

 Sai cewa, shi ya yaxa ilimin Imamiyyah da aqidunsu. Yana son ya ce ya qago wani ilimi ne da babu shi kafin lokacinsa? Ko kuma waxanda suka gabace shi ne ba su yi bayanan da ya kamata ba? Ai duk mai hankali ya san cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya gama bayyana ma al’ummarsa duk wata aqida da ya wajaba su qudurta, ya karantar da su cikakken addininsu. Sahabbai kuma sun yi iya qoqarinsu wajen ganin sun xauko wannan sun isar da shi ga sauran musulmi. Maganar xan Shi’ar dai in ba ta zama suka ga Ja’afarus-Sadiq ba, to, suka yake nufi ga magabatansa. Kuma Ja’afarus-Sadiq ya zama shi ne alqiblar maqaryatan wannan al’umma, kowa ya kwaso sharar maganganunsa sai ya jingina a gare shi. Allah zai yi hukunci da adalci a tsakaninsa da maqaryata.

 2.7.4 Musa xan Ja’afar

Xan Shi’ar ya ce: Sai kuma xansa Musa Al-Kazim. Ana kiransa bawan Allah Nagari, ya fi kowa bautar Allah a zamaninsa. Yana azumi da rana kuma ya tsayar da sallah da dare. An kira shi Kazim don in wani abu ya zo masa daga wani sai ya aika masa kuxi. Ibnul jauzi xaya daga cikin Hambalawa ya ce: An riwaito daga Shaqiq Al-Balakhi ya ce, na fita zuwa hajji a shekarar 149H, sai na sauka a Qadisiyyah, sai ga wani saurayi kyakkyawa, wankan tarwaxa, yana sanye da tufa mai gashi, ya rataya gwado, yana kuma sanye da takalma, ya zaune shi kaxai. Sai na ce a raina, wannan saurayin Sufi ne, yana son ya zama nauyi akan mutane, wallahi zan tafi wurinsa in tsawace shi. Sai na kusanta gare shi. Lokacin da ya ga na nufo shi sai ya ce, ya Shaqiq: Ka nisanci mafi yawan zato don sashen zato zunubi ne. Al-Hujurat 12.

 Sai na ce cikin raina wannan bawa ne salihi ya furta abin da ke cikin raina, zan tafi wurinsa in ce ya yafe ma ni, sai ya vace daga idanuna. A lokacin da muka sauka Waqisa sai ga shi yana sallah, gavovinsa na kakkarwa, idonsa na zubar da hawaye, sai na ce: Zan je in ce ya yi mani uzuri, sai ya taqaita sallah ya ce, ya Shaqiq: Lalle ni mai yawan gafartawa ne ga wanda ya tuba, ya yi imani, ya kuma aiki na gari, sannan ya shiriya. Xaha:82. Sai na ce wannan yana cikin Abdalu zavavvun matanen da Allah kiyaye duniya da su, ya yi magana game da sirrina sau biyu kenan. Lokacin da muka sauka wurin da ake kira Zibalah, sai ga shi tsaye bakin wata rijiya, da wani abu a hannunsa don xibar ruwa, sai abin ya faxa cikin rijiya. Sai ya xaga kansa sama ya ce:

Kai ne Ubangijina idan na yi qishi

Kai ne kuma abincina idan na ji yunwa

Ya shugbana! Ba ni da wata guga in ba wannan ba.

Sai Shaqiq ya ce: Wallahi na ga rijiya ta taso, ya xauki gugarsa, cike da ruwa, ya yi alwala, ya yi sallah raka’a huxu, sannan ya tafi wurin wani tulin rairayi, sai ya rinqa xibar rairayin yana sa wa cikin guga yana sha, sai na ce ka ciyar da ni cikin sauran abin da Allah Ta’ala ya ciyar da kai, ko abin da Allah Ta’ala ya ni’imta ka da shi, sai ya ce: Ya kai Shaqiq! Ni’imomin Allah Ta’ala bayyanannu da voyayyu ba su gushe ba a kanmu, ka kyautata zato ga Allah Ta’ala. Sai ya bani gugar, sai na tarar cewa wani abin sha ne da aka haxa da sukari, ban tava shan abu mai daxi da qanshi ba irinsa. Na sha na yi dis. Na yi kwana da kwananaki bayan haka ba na sha’awar wani abin ci ko abin sha. Ban sake ganin sa ba sai a Makka, sai na gan shi a wani wuri cikin masallaci da tsakiyar dare yana sallah da natsuwa, yana nishi da kuka, bai gushe a cikin wannan halin ba har safiya ta waye, da asuba ta yi sai ya zauna wurin sallarsa yana tasbihi, sannan ya tashi don ya yi sallar farilla, sai ya yi xawafi shuxi bakwai sannan ya fita. Sai na bi shi, na kuma tarar cewa yana da mabiya da kuxi da bayi, savanin yadda na gan shi a hanya, sai mutane suka kewaye shi suna yi masa sallama suna neman albarkarsa. Sai na ce masu: Wane ne wannan? Suka ce: Musa ne xan Ja’afar. Sai na ce, na yi mamakin irin waxannan abubuwa ga wani ba irin wannan sharifin ba. Wannan bahambale ne ya riwaito shi.

 Kuma a hannunsa ne Bishir Al-Hafi ya tuba, don akwai ranar da ya wuce ta gidansa a Bagadaza sai ya ji ana ta yin ma-sha’a, da waqoqi da raye-raye a gidan nasa. Sai ga wata kuyanga ta fito da shara, sai ta jefar da ita a juji. Sai ya ce mata, ke yarinya, maigidan nan bawa ne ko xa? Sai ta ce da shi, xa ne. Sai ya ce, kin yi gaskiya, don da bawa ne da ya ji tsoron Ubangijinsa. Da kuyangar ta shiga gida sai ta tarar mai gidan yana shan giya, ya ce: me ya tsayar da ke? Sai ta ba shi labari. Sai ya fita ba takalma har ya isa wurin shugabanmu Ja’afar ya tuba a hannunsa.

Martani:

 Iyakar abin da aka sani a kan Musa shi ne, an haife shi a garin Madina, a bayan shekara ta 120. daga nan kuma Sarkin Musulmi Mahadi ya kira shi zuwa Bagadaza. Ya kuma sake dawo da shi Madina bayan haka. A nan ne ya ci gaba da rayuwa har zamanin Sarki Rashid. A zamanin Sarki Haruna Rashid da ya je Umrah, ya bi ta Madina, ya kuma ya xauki Musal Kazim karo na biyu zuwa hedikwatar mulki; Bagadaza, ya kuma tsare shi a can har ajalinsa ya riske shi yana a tsare.

Musal-Kazim mutum ne da ya shahara a fagen qoqarin ibada. Waxanda ke bayansa babu wani ilimi na addini da duniya ta qaru da shi daga wurin su, domin kuwa kafin ka yarda mutum na iya ba ka riga sai ka duba ta wuyansa. Labarin da aka yaxa kuwa cewa Bishir Al-Hafi ya tuba ne a hannunsa na daga cikin qarairayi na masu qarin gishiri. Domin kuwa bai samu sukunin da zai iya haxuwa ma da Bishir ba zuwansa Bagadaza, kuma a girke yake wuri xaya.

 2.7.5 Ali Ar-Ridha

Xan Shi’ar ya ce: Shi kuwa Ali Ar Ridha shahararren malami ne. kuma ya fi kowa Zuhudu a zamaninsa. Malaman Sunnah da dama ne suka yi karatu a wurinsa. Sarki Ma’amun ya naxa shi saboda iliminsa. Ya tava yi wa xan’uwansa Zaidu gargaxi yana tunatar da shi cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbatar wa zuri’ar Fatima cewa, Allah ya yi mata alqawarin wuta ba zata ci zuri’arta ba don kamun kan da ita Fatimar ta yi. Ya ce masa: To, me zaka ce ma Manzon Allah idan ka zubar da jinin musulmi, ka qwaci dukiyarsu babu dalili, ka razanar da hanyoyinsu saboda jahilan Kufa sun ruxe ka? A wata riwaya kuma an ce: Ali Raliyallahu Anhu ya ce da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama me ya sa ka sa wa Fatima wannan suna? Sai ya ce: Don Allah ya cire ta ita da zuri’arta daga masu shiga wuta. Ali ar-Ridha ya ci gaba da ce masa: Kasancewar ta kare mutuncinta ba zai hana ka shiga wuta ba in har ka yi zalunci. Wallahi zuri’arta ba su samu wancan matsayin ba sai don xa’ar Allah. Idan kuwa ka kuskura ka nemi abin da suka samu ta hanyar sava ma Allah, to, kamar kana so ne ka fifita kanka a kansu.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Kuma Sarki Ma’amun ya rubuta sunan Ali ar-Radha akan kuxi, ya aika zuwa garuruwa cewa, a yi masa mubaya’a. ya kuma daina sa baqaqen kaya, ya sanya kore a madadin haka.

Kuma wai, inji xan Shi’ar, a cikin wata qasida da Abu Nawwas ya yi yana yabon sa, ya faxi cewa: Ba za a iya qare yabon ka ba tun da Jibrilu ne da kansa ke hidimar kakanka.

Martani:

 Ba shakka zuri’ar sayyidina Husaini basu tava gamuwa da musibar da ta fi jinginar da ‘yan Shi’ah ke yi gare su ba. yabon da suke masu gara ma zargi da shi. In ba don Ahlus-Sunnah sun san waxannan bayin Allah ba, da an qware su a dalilin maganganun ‘yan Shi’ah da za su iya sa a munana zato ga waxannan talikai.

 Duk abin da xan Shi’ar nan ya faxi a kan Ali Ar-Ridha ba na kamawa a ciki. Ka ga dai cewar da ya yi, ya fi kowa ilimi da gudun duniya a zamaninsa. Maganar fanko ce wayam; babu hujja ko misqala zarratin akan ta. Duk wanda yake son wani in bai sa tsoron Allah da adalci ba zai iya faxin irin wannan a kansa. Cika baki kuwa ai kowa ma zai iya shi. In ba haka ba, wa zai haxa Ridha ta fuskar ilimi da Shafi’i, da Ishaqa xan Rahawaihi, da Ahmadu xan Hambali da Ashabu xan Abdul Azizi ire-irensu? Ko ina ya yi gudun duniyar irin su Abu Sulaiman Ad-Darani da Ma’aruf Al-Karkhi da ire-irensu?

 Kuma cewa, malaman Sunnah da yawa sun yi karatu wurinsa. To, kamar su wa? Ba wani malamin da aka san ya yi karatu wurinsa. Amma in an ce yana da xalibai waxanda ba sanannu ba, wannan abu ne mai yiwuwa, tunda masu neman ilimi duk inda suka samu abin tsinta ba su yin sakaci da shi. Amma a ce ga wani malami da aka sani ya yi xalibta wurinsa ba gaskiya ba ne.

 Sai maganar da suke yaxawa cewa, ma’aruf Al-Karkhi ya yi hidima a wurinsa. Kuma ma wai, a hannunsa ya musulunta. Duk irin waxannan kalamai ne da ba su da tushe. Kamar hadisin Fatima da ya kawo da cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi mata alqawarin kare ta da zuri’arta daga wuta don ta tsare mutuncinta. Wannan ba abu ne da aka sani a addini ba, cewa, zuri’ar wani zata haramta ga wuta don shi ya kama kansa. Ballantana kuma irin lafazinsu na ce ma Jibrilu (AS) mai hidimar Manzon Allah. Wannan duk da yake yana nuna kamar sun darajanta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, amma akwai cin haqqin Mala’iku da rashin sanin girmansu a cikin wannan magana. Amma su ‘yan Shi’ah koyaushe irin waxannan waqoqin daxinsu suke ji, har da kafa hujja da su a addini. Wannan ko ba xabi’ar masu basira ga addini ba ce.

 2.7.6 Muhammadu Al-Jawad

 Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Imami na gaba shi ne: Muhammadu Al-Jawad, wanda ya bi tafarkin mahaifinsa ta fuskar ilimi da taqawa da baiwa. Kuma a lokacin da mahaifinsa ya rasu, sai Sarki Ma’amun ya nutsa ga qaunarsa saboda iliminsa da addininsa, da kammalar hankalinsa cikin qarancin shekarunsa. A kan haka ne kuma ya so ya aura masa da ‘yarsa Ummul Fadhli kamar yadda ya aura wa mahaifinsa da ‘yarsa Ummu Habib. Anan ne kuma, inji xan Shi’ar, Abbasiyyawa suka tsananta masa, suka ji tsoron sarautar ta fice daga hannunsu, ta hanyar shi ya yi wa Jawad mubaya’a kamar yadda ya yi wa babansa. Don haka dattawansu suka haxu suka kira shi zuwa ga oda. Suka ce masa, wai, wannan xan qaramin yaro ne da ba shi da karatu. Sai Sarkin ya ce: Na fi ku saninsa. Amma in kuna so ku gwada shi. Sai suka aminta da haka. Anan ne kuma wai, suka ba Alqali Yahaya xan Aksamu kuxi mai yawan gaske don ya qure shi.

 Xan Shi’ar ya ci gaba da ba da labari: Wai, sai aka sanya rana da wuri da lokaci. Mutane suka haxu. Sarki ya sa aka kira shi, aka kuma kira Abbasiyyawa. Daga nan sai Alqali ya fara tambayar sa game da hukuncin mai harama in ya yi farauta. Nan take sai Jawad ya ce masa: A ina ya kashe shi; a harami ko a wajensa? Ya san hukuncin yin haka ko bai sani ba? Ya kashe dabbar ne don buqatarsa gare ta ko don ya kare kansa? Qaramar dabba ce ko babba? Cikin dangin tsuntsaye take ko cikin wani dangi na daban?

 Sai kawai aka ga Alqali ya rikice, in ji mai xan Shi’ar mai ba da labari. Ya shige gashi har kowa ma ya gane haka a wurin. Sai Sarki Ma’amun ya ce da jama’arsa: Kun fahimci abin da nike gaya muku, wanda kuma kuke musunsa? Sannan sai ya juya kan Imamu Jawad, ya ce masa: Ka shirya neman auren? Imamu ya ce: Na’am. Nan take kuwa ya nemi xiyar Sarki aka ba shi ita a kansadaki Dirhami xari biyar, daidai sadakin kakarsa Fatim. Ya kuma biya naqadan, ta zama matarsa.

Martani:

 Muhammad Al-Jawad, babu shakka, yana cikin fitattun Hashimawa, masu kwarjini ga idon jama’a. Ga shi kuma karimin mutum. Wannan laqabin nasa ma yana nuni ne ga karimci da sakin hannunsa. Bai yi tsawon rai ba, don a lokacin wafatinsa bai wuce shekaru ashirin da biyar ba (95H-120H). Kuma Sarki Ma’amun ya aurar masa da ‘yarsa. Yana kuma aika masa Dirhami miliyan xaya kowace shekara. Sannan Sarki Mu’utasim ya gayyace shi zuwa Bagadaza inda ya zauna can har ya cika.

 To, ka ji gaskiyar labari. Amma irin wannan saqaqqen labari na xan Shi’ar ko alama babu qanshin gaskiya a cikinsa. Wannan labarin warin qarya ma yake yi. Don masana sun san Alqali Yahaya ya fi qarfin ya yi tambaya don neman qurewa wai, a kan hukuncin farauta! Kai tafi ma labarin haka yake. To, sai me? Sai ya zan imami don ya jera ma Alqali waxannan tambayoyi? Magana da mai hankali da basira take da daxi. Amma su ‘yan Shi’ah kullum irin waxannan labarai su ne hajarsu da suke baje koli. Allah ya sawwaqa.

 2.7.7 Ali Al-Hadi

 Xan Shi’ar ya ce: Imamu na gaba shi ne, Ali xan Muhammad wanda ake ma laqabi da Askari. Mutawakkil ya tura shi daga Madina zuwa Bagadaza, daga nan kuma zuwa garin Surra Man Ra’a. A can ne ya sauka wani wuri da ake kira Askar, sai aka yi masa wannan suna. Ya ce: Mutawakkil dai ya gargaxo shi ne daga Madina don shi sarkin mai qin Ali ne. Sai ya lura da mutane sun karkata zuwa gare shi ainun, sai ya ji tsoron sa. Ya yi umurni a zo da shi. Mutanen Madina kuwa duk suka fashe da kuka, saboda alherinsa a wurinsu da yawan ibadarsa. Aka dai bincika gidansa ba a samu komai ba sai Alqur’ani da littafan karatu da na addu’oi. Wannan ya sa sai wannan imami ya yi daraja a wurinsa, har ya rinqa yi masa hidima da kansa.

 Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: A lokacin da Yahaya xan Hubairata ya zo da Al-Hadi a Bagadaza sai ya soma da gidan gwamna Ishaqu xan Ibrahim Ax-Xa’i yana mai ce masa: Ka ga wannan jikan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne, kuma ka san halin Sarki. In har ka ba shi shawarar kashe shi, to, da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zaka kyas ranar Alqiyama. Da suka shiga wurin Sarki kuma, aka ba shi labarin Zuhudunsa da tsentseninsa sai ya mutunta shi. Ana haka kuwa sai watarana sarki Mutawakkil ya yi rashin lafiya. Ya kuwa yi alwashin idan Allah ya ba shi lafiya zai yi sadaka da kuxi mai yawa, amma bai ayyana yawan ba. don haka da ya warke sai ya nemi malamai a Bagadaza babu wanda ya san amsar da zai ba shi. Sai da aka nemi Al-Hadi sannan ya ba shi da cewa, zai yi sadaka da Dirhami 83 domin su ne yawan yaqoqan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuma ga shi Allah ya kira da yawa inda ya ce: Haqiqa Allah ya taimake ku a cikin wurare masu yawa 9:25. Ya ce: Domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita yaqi 27 da kansa, ya tura an yi yaqi ba da shi ba har sau 56.

 Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Mas’udi ya ce, An ba sarki Mutawakkil labarin Al-Hadi na voye makamai, waxanda ‘yan Shi’arsa daga garin Qum ke kawo masa. Don haka nan gaba zai yi yunqurin juyin mulki. Wai, sai ya sa wasu turkawa suka shiga gidansa da dare amma ba su samu kome ba. suka tarar da shi ya kulle kansa a wani wuri yana ta karatun Alqur’ani, akan rairayi da tsakuwa, sai aka tungumo shi a haka zuwa wurin sarki, shi kuma a lokacin yana shan giya daa kofinta a hannunsa. Wai, sai sarki ya girmama shi, ya zaunar da shi kusa da shi har ya taya masa shan giyar. Sai Al-Hadi ya ce masa: Yi haquri. Ni ban tava shan ta ba, bale in saba da ita. A nan ne fa, inji xan Shi’ar, Al-Hadi ya yi masa gargaxi mai ratsa zukata, ya karanta masa ayoyin Alqur’ani. Mutawakkil kuwa ya yi ta rusa kuka har sai da ya jiqe gemunsa.

Martani:

 Wannan magana, ita da ta xazu duk ‘yan gida guda ne. Sunan gwamnan ma a yadda ya faxe shi ba haka yake ba, tunda shi bai san tarihi ba.

 Sunan gwamnan Bagadaza na wancan lokacin shi ne Ishaq xan Ibrahim Al-Khuza’i. Ba ya da alaqa da qabilar Xayyi’ balle a ce masa Xa’i. Kuma fa sanannen mutum ne, xan babban gida; duk masana tarihi sun san shi. Ga ma xan cikinsa ya yi gwamnan Bagadaza a zamanin Mutawakkil xin da bayansa! Kuma xan baffansa ne; Abdullahi xan Xahiru ya yi gwamna a Khurasan. Sannan shi ne wanda ya yi wa Imamu Ahmad sallah lokacin da ya cika. Ya yi gwamna ne tun zamanin Mu’utasim da Wasiq, da wani xan lokaci a zamanin Mutawakkil. Saboda haka wannan gida na Khuza’ata sanannu ne, ba abin da ya haxa su da Xayyi’, balle a kira xayansu Xa’i kamar yadda shi xan Shi’ar ya yi.

 Sai kuma zancen fatawar da ya ce an yi, wacce ke kware al’aurar jahilcinsa. Wane masani ne zai yarda da wannan fassara da fatawa da ya jingina ma Al-Hadi? Duk ma yaqoqan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba su kai adadin da ya faxi ba. Ba kuma dukan yaqoqan aya ke magana ba; waxanda aka yi kafin Hunainu take magana. A su xin ma, wuraren da aka ci nasara; ba irin Uhudu ba misali. Kuma don ayar ta ce waxannan yaqoqa na da yawa ba ya nuna duk wanda ya yi rantsuwa a kan wani abu mai yawa wannan adadin ne fatawarsa ba. Kana tsammanin a nan kaxai ne Maxaukakin Sarki ya faxi “Mai yawa”? Duba sauran ayoyin Alqur’ani mana gasu nan tari, a cikinsu har da masu nuni ga xari bakwai, da masu nuni ga dubu xari biyu, a kowacce an ce suna da yawa.

 Saboda haka, yawan abu, ba ya nufin wani kevantaccen adadi bale an yi hikima da ba da irin wannan fatawa. Wannan fa da a ce maganar tana da wani tushe da za a iya gaskata ta kenan. To, ina kuma ga shi an tabbatar da cewa, sun fesa ta?!

 2.7.8 Hasan xan Muhammad Al-Askari[57]

 Xan Shi’ar ya ce: Imami na sha xaya shi ne: Al-Hasan xan Muhammad Al-Askari, xan wannan da ya gabata. Kuma ya kasance malami, mai gudun duniya, mai yawan kirki da ibada. Shi ne mafifici duk a zamaninsa. Da yawa malaman Sunnah ke ruwaya daga wurinsa.

Martani:

 Maganarsa a nan ba ta banbanta da sauran maganganun da ya saba yi na cika baki ba, da faxin abin da ba shi aka sani ba. Duk dai malamai sanannu a zamanin wannan taliki an san su, an san riwayoyinsu. Kuma ba mu san xaya daga cikinsu da ya karvo kalima xaya ba daga wurin wannan Askari. Duba fitattun littafan Sunnah guda shida: Buhari da Muslim da Abu Dawuda da Tirmidhi da Nasa’i da Ibnu Majah duk sun rayu a kusan lokacinsa, amma ba wanda ya ce ya ji ko qala daga wannan mutum. Kai qarewa ma, ka duba littafin da Ibnu Asakir ya wallafa wanda ya jera sunayen malaman da aka yi ruwaya wurinsu. Ko samatar wannan mutum babu. To, ya za a saurari wannan cika baki wai, Da yawa malaman Sunnah ke ruwaya daga wurinsa?

 Haka ita ma cewar da ya yi wai, shi ne mafifici duk a zamaninsa. Mun saba da jin irin wannan tun ba yau ba.[58]

 2.7.9 Muhammad Xan Hassan

(Mahadi-na-Voye)

 Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Bayan Askari kuma sai xansa; shugabanmu Muhammadu Al-Mahadi amincin Allah ya tabbata a gare shi. Ibnul Jauzi ya riwaito daga Ibnu Umar cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wani mutum zai bayyana a qarshen zamani wanda sunansa ya yi daidai da nawa, haka ma alkunyarsa. Zai cika qasa da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci. Wancan shi ne Mahadi”.

Martani:

 Abin da malamai suka kawo irin su Xabari da Abdulbaqi da ire-irensu masana tarihi da ilmin dangantaka shi ne cewa, Askari bai tava haifuwa ba. Su kuma ‘yan Shi’ah sun ce ya bar cikinsa, amma xan nasa ya vuya tun yana qarami. Wasu daga cikinsu su ce, shekarunsa biyu, wasu uku, wasu ma har biyar. To, irin wannan yaro in har akwai shi, a shari’ar Allah da Manzo ai wajibi ne a sa shi qarqashin kulawar wata macce; uwa ko kaka ko inna, don ta kula da shi ta yi renonsa. Dukiyarsa da ya gada kuma a matsayinsa na maraya dole ne a ba da ita ga maza daga cikin dangin ubansa don su kula da ita. In har babu sai a bar ta a hannun sarki ya kula masa har sai ya girma ya isa aure. Kamar yadda Maxaukakin Sarki ya ce:

﴿وَٱبتَلُواْ ٱليَتَمَى حَتَّى إِذَا بَلَغُواْ ٱلنِّكَاحَ فَإِن ءَانَستُم مِّنهُم رُشدا فَٱدفَعُواْ إِلَيهِم أَموَلَهُم وَلَا تَأكُلُوهَا إِسرَافا وَبِدَارًا أَن يَكبَرُواْ وَمَن كَانَ غَنِيّا فَليَستَعفِف وَمَن كَانَ فَقِيرا فَليَأكُل بِٱلمَعرُوفِ فَإِذَا دَفَعتُم إِلَيهِم أَموَلَهُم فَأَشهِدُواْ عَلَيهِم وَكَفَى بِٱللَّهِ حَسِيبا٦﴾ النساء: ٦

Kuma ku jarraba marayu, har lokacin da suka isa aure. To, idan kun lura da shiriya daga gare su, to, ku miqa masu dukiyoyinsu. Kada ku ci ta da varna da yin gaggawa gudun su girma (su karvi abarsu) 4:6.

To, wanda ko kula da kansa ba a xora masa ba da nassin Alqur’ani, ba a kuma yarda a hannunta masa dukiyarsa ba, ina maganar a ce shugaba ne ga musulmi, kuma har wai mutum ba ya zama musulmi sai ya ba da gaskiya da shi?!

 Kuma wannan xan taliki, in har ma Allah ya halicce xin, to, bai amfanin su da komai a duniya ko a addini. Bai tava karantar da kowa bihin ba, ba a kuma tava qarar da hairinsa ba. Ba xaya daga cikin manufofin shugabanci da aka samu ta wurinsa. In da ma akwai shin, to, sharrin da samuwarsa ta haifar ya isa. Don kuwa masu ba da gaskiya da shi ba su more masa ba, masu qaryata shi kuma za su xanxani kuxarsu. To, ina amfanin wannan shugaba?! Wace maslaha zata sa Allah ya halicci wanda yake haka, sai ka ce ba gwanin Sarki ba?!! Tsarki ya tabbatar ma Allah daga yin irin wannan.

 Suna iya cewa, ya vuya ne saboda zaluncin mutane. To, amma ai ko a zamanin iyayensa ana zalunci. Me su, basu vuya ba? Kuma ga mabiyansa nan cike da sassan qasa. Me ya hana shi bayyana koda sau xaya a wurinsu, ko kuma ya aiko masu wani xan aike da zai karantar da su wani abu na addini? Kuma ai za iya fakewa wurin wasu magoya bayansa masu qarfi irin na Sham..

 In ko har bai iya faxa ma kowa kome saboda tsoronsa, to, ina amfanin kasantuwarsa? Ka ga ai ko Annabawan da aka aiko da mutane basu gaskata su ba, sun dai bayyana ga mutane sun isar da saqo, sun tsayar da hujja akan mutane. Su ko ‘yan-sha-biyu ba abin da abin jiran nasu ya tsinana masu sai wahala da damuwa, da qiyayya da mutane, da addu’ar da Allah bai karva. Fiye da shekaru 450 suna abu guda, basu je ko ina ba!

 Kai, ya ma sava ma hankali da al’adar da aka sani ga wannan al’umma. Don tun farkonta ba a tava sanin wani ya wuce shekaru 120 ba, balle 450. Imamul Buhari ya riwaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yana cewa: “Kun ga daren nan na yau? Duk wanda ke bayan qasa daga yau, ba zai rayu fiye da shekara xari ba”.

 Idan ya kasance a wancan zamanin ba a wuce shekaru xari, to, ga al’ada daga baya abin ma ragewa zai yi. Domin wannan ita ce sunnar Allah a cikin halitta; shekarunsu suna yi suna ragewa. Nuhu Alaihis Salamu shekaru 950 ya yi yana kiran jama’arsa. Adamu Alaihis Salamu shi ma sai da ya shekara dubu kamar yadda ya inganta a cikinsunan na tirmidhi. Amma tsawon rayuwa yana ta ragewa kodayaushe. Ya kuma inganta a cikin hadisi cewa: “Tsawon rayuwar al’ummata yana reto a tsakanin shukaru sittin zuwa saba’in. Kaxan ne za su wuce haka”.

 Sukan kafa hujja da cewa, wai ai Haliru ma yana nan raye. To, wannan hujja gara ma yin shiru da kafa ta. Domin ko wane ne ya yarda cewa har yanzu Haliru na a duniya?! Malamai na gaskiya tun tabbatar da mutuwarsa. Kai, in ma mun sallama; yana raye, to, ai shi ba cikin wannan al’umma yake ba. Shi ya sa ake samun maqaryata daga cikin aljannu da mutane koyaushe suna cewa, su ne Haliru. Waxanda ke ganin su kuma sai su gaskata hakan.

 Shi ma Muhammadu xan Hassan; Mahadin ‘yan biyu, mutane da dama sun yi da’awar su ne shi. Kuma wannan qarya ba ta banbanta da waccan ga masu basira da hankali.

 2.7.10 Hadisin Mahadi

 Cewar da xan Shi’ar ya yi wai, Ibnul Jauzi ya riwaito daga Ibnu Umar cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wani mutum zai bayyana a qarshen zamani wanda sunansa ya yi daidai da nawa, haka ma alkunyarsa. Zai cika qasa da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci. Wancan shi ne Mahadi”.

Martani:

 Tun farko dai baku yarda da hadissan Ahlus-Sunnah ba. To, don me za ku kafa hujja da shi? In kun ce, ai don mu kafa maku hujja da hadisan malamanku ne. Sai mu ce, to, ku bari mu kawo maganganunsu.

 Sannan kuma wannan hadisi ba ya da wani qarfin da za a kafa hujja da shi. Duk da haka kuma xan Shi’ar ya canza lafazin hadisin, domin in aka karanta shi a yadda ya ke, mu ne za mu kafa maku hujja da shi. Hadisin cewa ya yi: “Sunansa ya yi daidai da nawa. Na mahaifinsa kuma ya yi daidai da na mahaifina”. To, shi wannan Mahadin naku ai ba xan Abdullahi ne ba. Ya kuma zo a wani hadisin cewa, daga zuri’ar Hassan yake. Naku kuma jikan Husaini ne.

 A wannan wuri dai xan Shi’ar ya yi halinsu da aka san su da shi na maguxi da algussu don voye gaskiya. Ka ga cewar da ya yi Ibnul Jauzi ya riwaito. Ba fa Ibnul Jauzin da duniya ta sani ne; malamin Sunnah ba. Wani Ibnul Jauzi ne xan La’ilaha’ula’i. Sunansa na ainihi Yusufu xan Quzzu. Shi ne wanda ya wallafa wani littafin tarihi mai suna Mir’atuz Zamani, da kuma wani littafi akan Imamai goma sha biyu mai suna I’ilamul Khawasi. Shi wannan mutum kamar hawainiya ya ke; yana rikixewa ne duk inda ya je. Ya yi rubutu akan darajojin Khulafa’ur Rashiduna, ya kuma yi akan zaginsu. Shi xan maula ne kawai da sunan malamai. Wannan shi ne xan Shi’ar ya ke kafa hujja da shi.

 2.8 Wai Imamai Sha Biyu Sun fi Kowa!

 Xan Shi’ar ya qara sharhi bayan kawo waxancan Imamai yana cewa: Waxannan su ne Imamai masu girman daraja, ma’asumai, waxanda matsayinsu a wurin Allah ba ya misaltuwa, don sun kai qolin ga kamala. Sun tsaya inda Allah ya tsayar da su a lokacin da wasu suka shagalta da sha’anin mulki da sharholiya da shaye-shaye. Wanda hakan ta sa suka yi varna da danginsu kamar yadda kowa ya sani. Mu; ‘yan Shi’ah ba abin da muke sai Allah ya isa. Inji shi.

 Sannan sai ya yi kwaikwayon wani mawaqi xan’uwansa; xan Shi’ah da ke kira ga a jefar da mazhabobin Sunnah gaba xaya don taqaitar madogararsu, a koma ga masu karvo hukunce-hukunce kai tsaye daga Allah ta hannun kakansu!

Martani:

 Da kuka ce su ma’asumai ne ai baku ba da kowace irin hujja ba sai cika baki da cewa, ai dole ne Allah ya samar da shugaba ma’asumi; wanda ba ya kuskure ko tuntuven harshe, don hakan ta samar da maslaha da luxufi ga jama’a. Wannan hujjar kuwa yanar gizo ta fi ta qarfi. Shi ya sa kun kasa nuna ma kowa ma’asumin sai Malam-na-Voye wanda bai tava amfaninku ba; ku da kuka yarda da shi, ballantana sauran musulmi da suka xauke shi a matsayin Malam Babu.

 Cewa kuma matsayinsu a wurin Allah ba ya misaltuwa don sun kai qolin ga kamala. Wannan shi ma cika baki ne kawai. In wani ma yana so sai ya yi irin wannan cika bakin ga wasu da suka fi su ilimi da daraja daga cikin magabata. Kuma baku da abin da za ku ce masa. Duk wani masanin tarihi yana sane da cewa, Imamanku na goma da na sha xaya (Askari babba da qarami) ba su kai darajar wasu magabatan ba ma na lokacinsu.

 Ko kiran su shugabanni da kuka yi. Muna buqatar ku bayyana mana irin shugabancinsu. Suna da qarfi ne na mulki da iko akan jama’a ta yadda ake jin tsoron su? Ko kuwa shugabanni dai ne ta fuskar ilimi da karantar da jama’a? Idan kun ce suna da qarfi to, mun san kuna yaudarar kanku ne. Kuma kun sani in banda Ali daga cikinsu babu wanda ya samu wannan qarfi. Shi xin ma kuma bai same shi yadda ake so ba, tun da kusan rabin al’umma basu tare da shi, ko abin da ya fi haka ko ya kasa. Kai da yawa ma sun yaqe shi. Daga cikin waxanda ke tare da shi kuma wasu suka kauce masa lokacin da zai yaqi waxancan don rashin amincewarsu da yin yaqin. A cikin waxanda suka kauce ma yaqin kuwa akwai da dama da sun fi waxanda suka yi yaqin na kowane vangare.

 Idan kuma kun ce, su shugabanni ne ta fuskar ilimi da karantar da jama’a, don haka ya wajaba al’umma ta goyi bayansu. Sai mu ce, ba haka ba ne. Kasancewar mutum ya isa ya yi shugabanci ko limanci ko alqalanci ko jagorancin yaqi ba ta wajabta zamansa haka xin. Sallah kuwa a bayan liman ake yin ta, ba bayan wanda kawai ya cancanci limanci ba. Haka ma alqali mai iko ne ke yanke hukunci. Kuma kwamandan mayaqa shi ke jagoranci ba duk zarumin da yake iyawa ba.

 Harwayau muna neman qarin bayani. Kuna nufin waxannan bayin Allah kowanensu ya kamata ya zama shugaba a lokacinsa, shi kaxai? Ko ko a’a, yana cikin waxanda suka cancanta a cikin Quraishawa irin sa?

 Zancen da xan Shi’ar ya yi cewa, sun tsaya inda Allah ya tsayar da su a lokacin da wasu suka shagalta da sha’anin mulki da sharholiya da shaye-shaye, ba zancen adalci ba ne. Domin ba wani Ahlus-Sunnah da ya ce ayi koyi da masu sharholiya da varna; sara kai ne ko ba sara kai ba. Amma kasancewar Ahlus-Sunnah suna neman taimako da sara kai a kan abin da suke da amfani a cikinsa, suna kuma taimaka masu a cikin abin da shari’a ta yarda da shi. In har wannan laifi ne, to, ‘yan Shi’ah sun fi su yin wannan laifi. Domin su kowa ya san a wurin kafirai suke neman taimako da agaji. Shi kansa wannan malamin da muke taqaddama da shi shaida ne a kan haka, don kafiran Mugul da ire-irensu da dama sara kansa ne ta wannan fuskar. Kuma wannan shi ne tarihin ‘yan Shi’ah tun daxai.

 Muna qara nanata cewa, su waxannan imaman da ‘yan Shi’ah ke bi, waxanda suka ce ma’asumai ne, ba su da iko ko xaya na zartar da hukunci. Ba a yin sallar jum’ah, kai ko ma salawatul hamsi bayan xayansu don ba liman ne ba. Ba a neman warware jayayyar fili ko gado ko wata husuma tsakanin ‘yan’uwa a wurinsu. Ba su shugabantar jihadi ko hajji, balle su tsayar da haddi ga masu laifi. Mutum kuma ba ya neman haqqinsa kowane iri na zama xan qasa daga wurinsu. Ba su hana ‘yan fashi ko varayi wanzuwa. Basu raba ma jama’a dukiyar baitul-mali. Iyakacinsu yin fatawa kamar yadda sauran malamai ire-irensu suka kasance suna yi. To, duk wanda yake neman wani abu irin wannan kuma ya tasar ma wanda ba shi da iko ai sunansa wawa. Wanda ya nemi abu daga mai shi, mai iko a kanshi, shi ne mai hankali.

 Sannan malamin ya yi tsaga da faxi a cikin tuhumar da ya yi ma sarakuna. Domin kuwa kowa ya san a cikinsu akwai na kirki irin su Umaru xan Abdulazizi da sarki Mahadi. Da yawan waxanda ake tuhuma da savo a cikinsu kuma ba a bayyane suke yi ba. Wasunsu suna da zunubbai, amma akwai yiwuwar sun tuba, ko sun samu ladar da zata kankare zunubin nasu, ko Allah ya jarabce su da wani abin da ke kankare laifinsu. Abin da ya kamata a sani shi ne, su sarakuna ayyukansu na lada manya ne, haka ma zunubansu. Ba daidai suke da xaixaikun musulmi ba. Ina ko zaka haxa talaka mai qoqarin ibada gwargwadon qarfinsa da wanda ke tsayar da dokokin Allah akan al’umma, ya hana savo, ya qarfafi ayyukan alheri da yawa, ya yaqi kafirai, ya sadar da haqqoqan mutane da dama zuwa gare su, ya kwatanta adalci, ya hana da yawa daga cikin zalunci?!

 Mu, bamu tava cewa sarakuna basu savo ko aikata zunubi ba. Kamar yadda sauran gama-garin musulmi duk suke, haka su ma sarakuna. Amma wa ya ce in mutum na zunubi an gama zaman lafiya da shi, kuma ba a taimakon sa a inda yake akwai maslaha da alheri a ciki?

 ‘Yan Shi’a na iya cewa, imamansu na da wani voyayyen ilimi da babu shi a wurin kowa! To, ina amfani voyayyen ilimi da ba a bayyana shi? Me ya raba shi da taskar kuxi da aka tsuke ta ba a ba kowa? Ya za a kira mutane ga bin wanda bai iya karantar da su kome irin Malam Babu na ‘yan Shi’ah?

In ko har suka ce, a’a, suna bayyana ma kevantattun mutane ne da suke da kusanci da su, to, mun san qarya suke yi. Dubi Ja’afar As-Sadiq, wanda malamai irin su Malik da Sufyanu xan Uyainata da Shu’ubatu da Sufyanus-Sauri da Ibnu Juraiju da Yahaya xan Sa’idu da ire-irensu daga cikin mashahuran malamai suka yi karatu wurinsa. Wa zai yarda cewa, As-Sadiq ya voye ma waxannan taurari wani karatun da ya bayyana ma jahillai, da al’umma ba ta ko san da zamansu ba?! Babu shakka waxannan malamai da muka ambata da ire-irensu sun fi qaunar Allah da Manzo da kishin tsare addini da isar da shi ga al’umma da son masu son Allah da qiyayya da masu qin sa fiye da shaihunan Shi’ah. Wannan ko shi ne halin ‘yan Shi’ah a kowane zamani. Mutum ya duba lokacinsa. Ga wannan xan Shi’ah da muke magana a kansa. Suna ganin shi ne mafificinsu a wannan zamani. Amma in ya furta wata magana ko kare ba ya ci ba. Sai ya nace a kan maganar da duk mai hankali ya san qarya ce. To, in ya sani ya ya yima Allah da Manzonsa qarya? In kuma bai sani ba ai iya qurewar jahilci kenan.

 2.9 Malaman Sunnah Sun fi Qarfin Zargi

 A qoqarinsa na xaukaka alqadarin mazhabarsa, xan Shi’ar ya zargi Ahlus-Sunnah yana mai cewa: Babu wani mutum xaya daga cikin Ahlus-Sunnah in dai ya san inda kansa ke ciwo, kuma ya kalli mazhabobi da idon basira, sai ya zavin mazhabar ‘yan-sha-biyu ya bar saura. Amma ta kan yiwu ya voye, ya bayyana akasin haka don neman abin duniya. Tun da an gina masu makarantu da cibiyoyi don su ci gaba da yin farfaganda ga sarakunan Banul Abbas, su sanya qaunarsu cikin zukatan mutane.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Sau da yawa ni kan ga cikinsu wanda yake ibada ta hanyar Shi’anci irin na Imamiyyah (‘yan-sha-biyu), amma ba ya bayyana shi don kwaxayin abin duniya. Na ma tava ganin wani shugaba a mazhabar Hambali yana iqirarin shi xan sha biyu ne. Sai na ce masa: “To, don me kake karantar da Hambaliyyah?” Sai ya ce, “Don wurinku ba masqi!” Kuma babban malamin Shafi’awa a wannan zamani da zai mutu wasicci ya yi da wasu muminai (yana nufin ‘yan Shi’ah) su yi masa wanka. Ya kuma nemi a rufe shi a maqabartar Kazim ta ‘yan Shi’ah. Har ma kuma ya kafa shedu a kan zai mutu bisa mazhabar Shi’ah!

Martani:

 Ko shakka babu wanda yake furta wannan magana bai fita daga xayan biyu; ko dai bai san su waye Ahlus-Sunnah ba, ko kuma maqaryaci ne na gidi. Yaushe ne aka kafa makarantu da cibiyoyi? Sunnah ta riga su kafuwa da nisa. A Bagadaza ne aka fara gina makarantu a cikin qarni na biyar. Kamar makarantar Nizzamiyyah an kafa ta a kusan shekarar 460H. Kuma akan mazhaba xaya kacal manhajarta ta ke. A lokacin ma duk mazhabobin Sunnah sun gama yaxuwa a gabascin duniya da yammacinta. Kuma babu wanda yake da makaranta a cikinsu. Malikawa kuma da ke yamma ai basu ko ambaton sarakunan Banul Abbas, balle su yi kira ga a so su.

 Kai, a haqiqanin gaskiya ma Sunnah ta fi qarfi kafin kafa daular Abbasiyyah. Domin a zamanin Abbasiyyar ne ‘yan Shi’ah da wasu ‘yan bidi’a irin su suka fara miqe qafafu. Kuma ba wani Ahlus-Sunnah da ya ce halifanci kayan gidan Abbas ne kamar yadda ‘yan Shi’ah kuka ce gadon gidan Ali ne. A wurin malaman Sunnah duk Baquraishe in yana da cancanta ana iya ba shi, Alawi ne ko Abbasi ko Umawi ko ma ba su ba. Zargin magabata shugabannin mazhabobin Sunnah da fadanci ko zargi ne maras tushe. Su malamai ne ‘yan “Sunnah sak”! Amma suna ganin halifofi huxu na farko da gashi, ga shi ko babu xan gidan Abbas a cikinsu.

 Duk mai hankali ya san ba a samun xan sha biyu cikin malaman Sunnah. Domin sun fi kowa ganin wautarsu da jahilcinsu da vatan kansu. Kai sun fi kowa nisa daga shiriya. Dole ne a qyamace su, don sun haxa duk sharrin da ke cikin sauran qungiyoyin bidi’ah, kamar Jahamiyyah da Qadariyyah. Waxannan kuwa kowace ta samu rabonta na zargi da suka daga bakunan magabatan al’umma.

 Wallahi, duk da yawan nazarce-nazarcena ga maganganun malamai na Sunnah da na Shi’ah ban tava ganin wanda ake zargi da zama xan Shi’ah Imamiyyah daga cikin mutanen kirki ba, balle ko a ce yana qudurta ta a voye. Amma ka ga Zaidiyyah, an tuhumci Hasan xan Salihu xan Hayyu da yin ta. Ga shi ko malami ne na kirki, mai gudun duniya. Amma babu wanda ya ce ya soki Abubakar ko Umar balle ko a ce bai yarda da halifancinsu ba. Daman su Zaidiyyah ba su wannan. Kuma ko ‘yan Shi’ah na farko babu wanda aka zarga cikinsu da ganin fifikon Ali a kan Abubakar da Umar. Suna dai son sa. Kuma cikinsu akwai masu fifita shi a kan Usman. Kuma ko cikin jama’ar Ali xin, waxanda suka taya shi yaqi ba kowa ne ke ganin ya fi Usman ba.

 Game da maganarsa kuwa, wai ya ga malaman Sunnah fitattu waxanda a voye ‘yan Shi’ah ne. Sai mu ce masa: Ku ne duniya ta san kuna wannan xabi’a; ku shiga cikin musulmi ku voye aqidarku, kuna ganin wannan wani abin neman kusanci zuwa ga Allah. Kuma a cikin musulmi a kansamu munafuki. To, ina abin mamaki don an samu munafikin xan Shi’ah ya saqe jiki cikin almajiran wata mazhaba ta Sunnah? Wanda ya kafa hujja da irin waxannan munafukai akan vacin aqidar Sunnah shi ne jahili.

 2.9.1 Malaman Sunnah ba su Ta’assubanci

 Xan Shi’ar ya ce: Su dai ‘yan-sha-biyu ba su da ra’ayin riqau ga abin da ba gaskiya ba. Savanin Ahlus-Sunnah. Misali a nan shi ne Imamul Ghazali da Mawardi daga cikin malaman Shafi’iyyah sun tafi a kan cewa, daidaita qaburbura shi ya yi daidai da shari’ah. Amma saboda ‘yan-sha-biyu sun mayar da shi al’ada mun bar shi. Za mu rinqa xaga qaburburanmu zuwa sama. Kuma wai, Zamakhshari daga cikin malaman Hanafiyyah ya fassara faxar Allah Ta’ala da ya ce: (Allah) Shi ne wanda yake yin salati akan ku da Mala’ikunsa Ahzab :43. Zamakhsharin ya ce: Ya halalta bisa ga wannan aya ayi salati ga xaixaikun musulmi. Amma saboda ‘yan-sha-biyu suna yi wa imamansu salati sai muka hana.

 Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Mai littafin Al-Hidaya daga cikin Hanafiyyawa ya ce, sanya zobe a hannun dama shi ne Sunnah. Amma tunda ‘yan-sha-biyu na yin sa to, mun mayar da shi hagu. Ire-iren wannan na da yawa, inji shi. Ya kuma ci gaba da cewa: “Duba wanda ke canza shari’ah, ya musaya hukuncin da Annabi ya sanya don kawai yana adawa da wasu mutane. To, ina dalilin bin wannan da xaukar maganarsa?”

Martani:

 Duk waxannan maganganu da xan Shi’ar ya yi sun fi dacewa da a mayar masa da su. Domin Allah ya tsarkake malaman Sunnah daga irin wannan.

 A haqiqanin gaskiya, bamu tava sanin wata qungiya mai ra’ayin riqau ga qarya kamar ‘yan-sha-biyu ba. Su ne waxanda aka san suna shedar zur idan shari’ah za ta hau kan xan Shi’ah irin su. Wane ta’assubanci ma ya wuce qarya? Su ne fa suka ce, wai, ‘ya macce na gadon duk dukiyar ubanta, don su kori Abbas daga magadan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, su bar Fatima ita kaxai! Kuma a cikinsu akwai masu haramta cin naman raqumi, wai, don Nana A’ishah ta hau kansa a ranar yaqin basasa. Suka sava ma Alqur’ani da Sunnah da ijma’in Ahlul-Baiti da malaman Sunnah don bin son ransu. Abin da kowa ya sani ne cewa, koda wancan raqumin da Nana A’ishah ta hau yake a raye ba za a haramta hawansa a Shari’ah ba. Domin kuwa ko kafirai da suka hau dabbobi ba a haramta hawansu ba, balle cin namansu.

 Kai, ta’assubancin ‘yan Shi’ah ya kai ga suna qyamar lamba 10 don kauce ma mutane goma da Allah ya yi wa bushara da aljanna. Sai ka ji sun ce, tara da xaya. Suna qoqarin kada su yi komai ya dace da goma saboda haka.

 Don tsananin ta’assubancinsu ma, in suka ga mai suna Ali ko Ja’afar ko Hasan da Husaini sai suna zanzari wajen girmama shi koda fasiqi ne. Dubi kuma yadda suka kafa ma Banu Umayyata qahon zuqa don wasu daga cikinsu sun kasance suna qyamar Ali. Alhali kuwa akwai mutanen kirki da dama daga cikin Banu Umayyata waxanda sun mutu tun kafin faruwar fitinar da ta gudana. Hasali ma babu wata qabila da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yawaita sanyawa cikin aikin gwamnati kamar su. Kamar yadda ya shugabantar da Attabu xan Usaidu akan Makkah. Ya kuma shugabantar da Khalidu xan Sa’idu da ‘yan’uwansa Abanu da Sa’idu a wasu wurare daban. Haka kuma ya shugabantar da Abu Sufyan xan Harbu xan Umayyata ko xansa Yazidu akan Najran. Har Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya cika kuwa yana gwamna a wurin. Sannan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya aurar da ‘ya’yansa mata uku ga dangin na Umayyata. Domin babbar ‘yarsa Zainab ya aurar da ita ne ga Abul Asi xan Rabi’u, wanda Annabi ya yabe shi a lokacin da Ali ya so ya auri xiyar Abu Jahali. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya nuna jin daxinsa da surukutar Abul Asi, kuma ya qara da cewa: “Ya faxa mani magana ya yi gaskiya, ya kuma yi mani alqawari ya cika”. Sannan ya aurar da Ruqayyatu da Ummu Kulsumi ga sayyidina Usman. Duk waxannan ‘yan gidan Umayyata ne.

 Yana daga cikin jahilcin ‘yan Shi’ah, qyamar da suke ma mutanen Sham gaba xaya, domin can farko an samu waxanda ba su son Ali Raliyallahu Anhu. To, ai ko Makkah an yi lokacin da kafirai ke a cikinta; waxanda ba su son Manzo. A Madina ma kuma an yi munafukai. Amma a halin da ake ciki yau, babu mai qyamar Ali ko xaya a Sham. To, don me suka tsane su?

 Haka ma suna jin haushin duk wanda ya yi amfani da wani abu da ya rage na Banu Umayyata kamar shan ruwan rijiyar Yazid. Alhalin Yazidu bai ma gina rijiyar ba, ya dai yalwata ta ne kawai, sai aka kira ta da sunansa. Basu kuma son a yi sallah a masallacin Banu Umayyata. In don Banu Umayyata sun gina shi ne kuwa, ai Ka’aba mushrikai suka gina ta, amma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi sallah a cikin ta. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava qin shiga gidajen da suka gina, ko ya qi shan ruwan rijiyar da suka haqa, ko sa tufan da suka saqa ko kashe kuxin da suka buga ba. To, wannan kafirai kenan fa; ina ga musulmi?!.

 Wani amintacce ya bani labarin wanda yake da kare a cikinsu, sai aka kira karen nasa Bukairu, sai nan take ya fusata, wai an sa ma karensa sunan ‘yan wuta. Wal iyazu billahi. A dalilin haka suka yi ta faxa har abin ya kai aka zubar da jini. Wa ya fi mai yin wannan ta’assubanci da wauta?.

 Su dai malaman Sunnah daxai ba su ce abar wani abu da shari’ah ta yarda da shi don wani xan bidi’ah ya aikata shi ba. Ka ga maganar daidaita qabari da ya yi. Mazhabar Abu Hanifa da Ahmad ita ce xaga shi ya fi. Hujjarsu kuwa ita ce, haka aka yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma suka ce, hakan ya fi nisantar da shi daga kama da gine-ginen duniya, kuma yana taimakawa wajen hana a zauna a kansa. Amma Imamus-Shafi’i sai ya so a shafe shi; ya ce mustahabbi ne. Domin akwai dalilai da suka nuna haka. Wasu daga cikin almajiransa suka ce, ai yin haka xabi’ar ‘yan Shi’ah ce, don haka suka karhanta. Amma akasarin almajiransa suka ce ba haka ba ne; mustahabbi dai ne ko ‘yan Shi’ah na yinsa.

 Haka shi ma bayyana karatun bismillah shi ne mazhabar ‘yan-sha-biyu. Kuma a kan wannan ne da maganar qunutin asuba wasu suka yi magana akan Imamus-Shafi’i, saboda abin ya shahara a Iraqi garin ‘yan Shi’ah. Amma duk da haka, shi Imamus-Shafi’i bai daina ba tunda yana ganin shi ne Sunnah. To, ka ga ba wani malamin da ya tava barin Sunnah saboda wai wasu ‘yan bidi’ah irinku na yin ta.

 2.9.2 Addu’a ga Halifofi Cikin Huxuba

 Sannan xan Shi’ar ya ce: Su dai Ahlus-Sunnah sun qago bidi’oi da yawa a cikin addini alhlai suna sane. Kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Kowace bidi’ah vata ce. Kuma kowace vata makomarta wuta”. Ya kuma ce: “Duk wanda ya shigar da wani baqon abu a cikin addininmu to, ya yi ta banza”. Kuma ko an so a hana su waxannan bidi’oi ba su bari. Kamar addu’ar da suke ma halifofi a cikin huxuba, wadda ba ta da asali a cikin addini. Kuma ba a yi ta ba a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da zamanin Sahabbai ko na Tabi’ai. Kai, ko ma zamanin Banu Umayyata da Banul Abbas ba a yinta. Sarki Mansur ne ya qago ta don ya musguna ma Alawiyyah sa’adda ya yi wata hatsaniya da su. Ga shi ko Ahlus-Sunnah na yinta har ila yaumina haza.

Martani:

 Yana da kyau a rinqa ba ilimi da tarihi haqqinsu. Shi dai yin addu’a ga halifofi huxu a kan mimbari abu ne da tarihi ya tabbatar da an yi shi tun zamanin Sarkin Musulmi Umaru xan Abdulazizi. Dalilin yin sa kuwa shi ne, don kariyar martabar sayyidina Ali da wasu ‘yan kazagin Banu Umayyata suka fara zagi a cikin huxubobinsau. Saboda adalcinsa sarki Umaru xan Abdulazizi ya ce a musanya wannan da yin addu’a da fatar alheri ga halifofi huxu shiryayyu, cikinsu har da Ali. Ya yi haka ne kuwa a matsayin wani salo na kawar da waccan mugunyar al’adar da ya ji tsoron yaxuwarta.

 Kuma tuhumar da ya yi wa sarki Mansur ba ta da makama. Domin ba wata musgunawa ga Alawiyyawa don an yi ma Abubakar da Umar da Usman addu’a an haxa da Ali. Tunda daman sun riga shi yin halifanci kuma ban yi jayayya da su ba. Ba kuma wani Ahlus-Sunnah da ya ce yin wannan addu’a farilla ne a cikin huxuba. Bidi’ah kam sananna ita ce, yi wa Ali shi kaxai addu’a ko ambaton imamai goma sha biyu da ‘yan shi’ah suka naxa. Kamar yadda zagin Ali ko duk wani magabaci a cikin huxuba yake bidi’ah mummuna.

 Sanannen abu ne dai cewa, halifofi uku na farko al’umma ta haxu a kan naxinsu. Kuma a zamaninsu kafirai sun xanxana kuxarsu, musulmi sun zauna lafiya. Shi kuma na huxu ya zo bisa qaddarar Allah a lokacin fitina, musulmi basu haxu a kansa ba, ba su kuma zauna lafiya da juna ba. Don haka kafirai sun ci karensu babu babbaka a lokacinsa. To, ka ga faxinsa shi kaxai cikin huxuba a bar waxancan uku babu bidi’ar da ta wuce shi.

 2.9.3 Shafar Qafa Wajen Arwalla

 Xan Shi’ar ya ce: Ahlus-Sunnah sun canza nassin da Allah ya tabbatar na shafar qafafu a wajen arwalla madadin wanke su, inda Allah ya ce: Sai ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa ga magincirori, kuma ku yi shafa ga kanunku da idanun sau. 5:6. Kuma Ibnu Abbas ya ce: Gava biyu ake wankewa, biyu kuma ake shafawa. Amma suka canza suka wajabta wanke qafafu.

Martani:

 Adadin waxanda suka ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana arwalla, da waxanda suka koya daga wurinsa da waxanda suka yi a zamaninsa har ya gani da idonsa sun fi yawa akan adadin waxanda suka karantar da wannan aya. Domin duk musulmi suna arwalla. Kuma sun gan shi yana yin ta sau shurin masaqi. Kuma gaba xayansu sun gan shi yana wanke qafafu. Har ma sun ce, ya tsoratar da waxanda wankinsu bai yi ba da cewa, wuta zata wanke dugadugansu.

 Kuma su matsalar ‘yan Shi’ah ita ce, ba su da cikakkiyar fahimtar Larabci. Don ita wannan aya sam bata sava ma aikin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba; ta yi daidai da shi. Sannan abin al’ajabi shi ne, duk bayan wannan ‘yan Shi’ah su ce ba a shafa a kansafa wadda ta tabbata daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a cikinsunnah mutawatira. Wai suna ganin yin haka ya sava ma Alqur’ani, su da Harijawa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuwa shi ne wanda yake fassara Alqur’ani.

 2.9.4 Mutu’ar Hajji da ta Aure

 Xan Shi’ar ya ce: Haka kuma Ahlus-Sunnah sun haramta mutu’a biyu da Alqur’ani ya zo da su; Mutu’a hajji da Allah ya ce: To, wanda ya ji daxi da Umra zuwa Hajji, sai ya biya abin da ya sauqaq na hadaya 2:196. Kuma da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasa samun yin wannan mutu’a ba saboda ya yi qirani sai da ya yi nadama a kan haka. Sai kuma mutu’ar aure da Allah ya ce: Kuma abin da kuka ji daxi da shi daga gare su, to, ku ba sadakinsu bisa farilla 4:24.

Xan Shi’ar ya ce: Kuma waxannan mutu’oi biyu, musulmi sun ci gaba da gudanar da su tsawon zamani rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da halifancin Abubakar da Umar. Haka kawai watarana sai Umar xin ya hau mimbari ya haramta su. Kuma ya ce, duk wanda ya yi su zai to, jikinsa zai gaya masa.

Martani:

 Ita dai mutu’ar Hajji da Umrah duk musulmi sun haxu a kan halalcinta. Kuma qarya ne a ce Ahlus-Sunnah sun haramta ta. Da yawan malaman Sunnah na ganin mustahabbi ce. Akwai ma masu rinjayar da ita da masu ganin ta wajibi.

 Ita ko mutu’ar aure ba ta a cikin ayar da ya karanta. Ayar dai tana magana ne akan matar da aka xaura ma aure aka kuma ji daxi da ita ta cancanci sadakinta duka. Savanin wadda aka xaura ma aure ba a ji daxi da ita ba wadda ta cancanci kawai rabin sadakinta. Saboda haka ayar ba tana magana kan kowane irin jin daxi da macce ne ba, sai fa jin daxi na halas. Kuma malamai sun haxu a kan bata sadakinta duka idan aure ya tabbata koda vatacce ne. Amma wanda ya ji daxi da ita ta hanyar haram ba wani sadaki da Allah ya ce a ba ta.

 Maganar cewa Umar ya haramta mutu’ar aure ba gaskiya ba ce. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya haramta ta bayan a da mutane na yin ta. Sayyidina Ali ne ma ya bayyana wannan Sunnah ga Ibnu Abbas da bai sani ba. Ya ce masa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya haramta auren mutu’ah da cin jakin gida a ranar Haibara. Kuma ya tabbata a cikin Sahihu Muslim cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya haramta ta a ranar da aka ci Makka haramci na har abada.

 Ita kuma cewar da sayyidina Ali ya yi: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya haramta auren mutu’ah da cin naman jakin gida a ranar Haibara. Wasu malamai kamar su Ibnu Uyainata na ganin yana nufin ranar Haibara ranar haramta jakin gidan ce. Amma shi auren mutu’ah a ranar buxa garin Makkah aka haramta ta. Wasu kuma na ganin ranar buxa Makkah haramtawa ta biyu ce. Don haka suke cewa, an haramta ta, sannan aka halalta, sai aka sake haramtawa daga qarshe. Akwai ma har masu cewa, an sake halalta ta kafin ranar Fatahu Makkah, sannan a ranar aka yi mata haramci na qarshe. Amma maganar can ta farko ta su Ibnu Uyainata tafi qarfi cewa, mutune suna yin mutu’ah ba a kuma hana su ba sai ranar buxa Makkah. Daga nan kuma ba wani halalci da ya zo akan ta. Shi kuma Ibnu Abbas da ya yi fatawa akan halaccinta da na cin naman jakin gida bisa ga rashin sani, sai sayyidina Ali ya ankarar da shi ga haramcin da ya tabbata daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Don haka, Ahlus-Sunnah su ne suka bi Ali da sauran halifofi a cikin abin da suka cirato daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Su kuma ‘yan Shi’ah sun sava ma Ali, sun bi wani ra’ayi na qashin kansu.

 Ka ga ai a cikin Alqur’ani mata biyu Allah ya halalta; matar aure, da baiwa. Ita kuma matar mutu’a ba matar aure ba ce, don ba ta gado, ba a sakin ta, balle a ba ta rabin sadaki idan an yi shi kafin baiko. Sannan ba ta idda. Waxannan hukunce-hukuncen kuwa su ne Allah ya tabbatar ma matan aure cikin Alqur’ani. Sannan ita ba baiwa ba ce. Ka ga ta tabbata haramtacciya. Tunda Allah Ta’ala ya ce: Kuma waxanda su masu kariya ne ga al’aurarsu. Sai fa akan matan aurensu ko abin da damansu ta mallaka (na bayi). To, su haqiqa ba waxanda ake zargi ba ne. To, duk wanda ya nemi (jin daxi) bayan wannan, to, su ne masu tsallake iyaka. Mu’minun:5-7.

 2.9.5 Ba a Cin Gadon Annabawa

 Sai kuma xan Shi’ar ya zargi sayyidina Abubakar Raliyallahu Anhu yana mai cewa: Abubakar ya hana Fatima gadonta. Sai ta ce masa: Kai xan Abu Quhafata! Kai zaka gaji ubanka, ni ban gaji nawa ba? Wai sai Abubakar ya lava ga wata riwaya da kowa bai san ta ba in ba shi ba. Alhalin kuma shi ne abokin jayayyarta, don shi yana cin sadaka. Ya kawo mata hadisin da Alqur’ani ya qaryata shi. Ya ce wai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mu Annabawa ba a gadonmu. Duk abin da muka bari sadaka ne”. Alhalin kuwa Allah Ta’ala na cewa:

﴿يُوصِيكُمُ ٱللَّهُ فِي أَولَدِكُم لِلذَّكَرِ مِثلُ حَظِّ ٱلأُنثَيَينِ ﴾ النساء: ١١

Allah yana yi maku wasicci a game da ‘ya’yanku. (Idan kun mutu) namiji zai gadi rabon mace biyu 4:11

Kuma Allah bai sanya wannan ga sauran al’umma banda Manzo ba. Sai ya qaryata riwayarsu. Kuma Allah ya ce:

﴿وَوَرِثَ سُلَيمَنُ دَاوُدَ ﴾ النمل: ١٦

Kuma Sulaimanu ya gadi Dawuda

Ya kuma ce:

﴿وَإِنِّي خِفتُ ٱلمَوَلِيَ مِن وَرَاءِي وَكَانَتِ ٱمرَأَتِي عَاقِرا فَهَب لِي مِن لَّدُنكَ وَلِيّا٥ يَرِثُنِي وَيَرِثُ مِن ءَالِ يَعقُوبَ وَٱجعَلهُ رَبِّ رَضِيّا٦﴾ مريم: ٥ – ٦

Kuma haqiqa ni, na ji tsoron dangi a bayana, kuma matata ta kasance bakarariya (maras haifuwa)! To, ka ba ni wani mataimaki daga wajenka. Ya gaje ni, kuma ya yi gado daga gidan Yaquba 19:5-6

Martani:

 Cewar da ya yi wai, Nana Fatima ta ce wa Abubakar: “Kai za ka gaji ubanka, ni ba zan gaji ubana ba?”. Ba maganar da aka san ingancinta ba ce. Da ta inganta kuwa, ba za ta zama hujja ba. Domin babu shakka babanta Sallallahu Alaihi Wasallama yana da nisan banbanci da nasa. Ya ko za a yi wannan gwaji? Ai su Annabawa Allah ya kare su daga a gaji duniya daga wurinsu. Don kada wannan ya zama marataya ga masu son zarginsu. Amma irin Abubakar sai ya gaji mahaifinsa lamui lafiya ba wata damuwa. Kamar yadda Allah ya kare Manzonsa daga iya rubutu ko tsara waqa, ba don hakan tana aibi ga sauran jama’a ba; sai don toshe qofar zargi.

 Cewa kuma wai, Abubakar ya lava ga wata riwaya da shi kaxan ya zo da ita, zargi ne da ba shi da qamshin gaskiya. Domin hadisin da ya bayyana ba a gadon Annabawa ba Siddiqu ne kawai ya karantar da shi ba. An same shi daga Umar da Usman da Ali da Xalhatu da Zubairu da Sa’adu da Ibnu Aufi da Abbas da matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Abu Hurairata. Kuma riwayoyinsu na nan cikin sanannun littafai ta hanyoyi ingantattu. Masana sun san da haka. Ya rage ma mai wannan zargi xayan biyu; jahilci ko katovara.

 Ya kuma ce wai, Abubakar ne abokin jayayyarta. Ba kuwa haka ba ne. Don Abubakar bai ce shi zai ci gadon ko iyalansa ba. Cewa ya yi sadaka ce ga musulmin da suka cancanta. Ba shi kuma cikin masu karvar sadakar don ba shi da buqata da ita. Haka ma iyalansa ba su tava amfanuwa daga gare ta ba daxai saboda wadatarsu. Wannan yana daidai da wani attajiri ya yi shaida cewa, wani ya yi wasicci da wata sadaka ga talakawa. Ba abin da zai hana a karvi shaidarsa a nan, don shi ba abin tuhuma ba ne. Kai, koda yana da wani amfani a cikinta, in ya riwaito ana karva, don ba shaida ba ce; riwaya ce. Riwaya kuma hukunce ne da yake game kowa, a wannan mas’ala ko wata irinta har abada. To, ina kuma ga shi Sahabin Manzo! Ai wannan kamar ganin wata ne. Wanda zai gan shi yana cikin waxanda hukuncinsa zai hau kansu amma ba shi kaxai ba.

 Kuma ka ga riwayar nan hukunci ne na Shari’a wanda ya haramta gado har ga matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cikinsu har da ‘yar Abubakar. Ya kuma haramta a sayar ballantana ko shi Abubakar ko wani ya saya.

Sai maganar wai, wannan hadisi ya sava ma Alqur’ani. Ka ga dai ita ayar ba inda ta ce Manzo zai bar gado. To, tunda Sunnah ta tabbatar da ba a gadon nasa, ga kuma Sahabbai sun yi ijma’i a kan haka, ina rikici a nan? Ko ka ji wani cikin sauran magadan ya nace akan neman gadon? Gonar kuma ai ta kai zamanin Ali amma bai raba ta ba alhalin akwai sauran magada, da magadan magada. Ayoyin da ya kawo na gadon su Annabi Sulaiman da Annabi Yaqubu gadon ilimi da Annabta da mulki ake nufi. Ai daman ba wata fa’ida a ce xa ya gaji uba in dukiya ce ya gada. Daman kowa na gadon dukiyar ubansa.

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Lalle Annabawa ba su gadar da dirhami, ko dinari. Suna gadar da ilimi ne. Saboda haka, duk wanda ya riqe shi to, ya yi riqo da babban rabo”. Abu Dawuda ya riwaito shi da wasu ba shi ba.

To, wannan shi ne. Ka ga ai gadon kuxi ba wani abin yabo a cikinsa. Ita kuma wannan aya ta zo ne da yabon Sulaimana Alaihis Salamu. Amma cewa, Sulaimana ya gadi dukiya daga mahaifinsa Dawuda kamar wani ya ce ne, wane ya ci abinci, ya yi bacci. Ba irin labaran Alqur’ani ba ne wannan.

 2.9.6 Fatima ta Nemi Gonar Fadak

Xan Shi’ar ya ce: A lokacin da Fatima ta gaya masa cewa mahaifinta Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba ta kyautar Fadak, sai ya ce, ki zo da wani mutum baqi ko ja don ya shede ki a kan haka. Sai ta zo da Ummu Aimana ta sheda cewa haka ne. Sai ya ce mata: Mace ce wadda ba a karvar maganarta. Ga shi kuma duk sun riwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ummu Aimana mace ce ‘yar aljanna”. Sai Ali ya yi sheda cewa maganar gaskiya ce. Sai Abubakar ya ce: Wannan mijinki ne. Yana son abin ya koma masa, ba za mu yi maki hukunci da shaidarsa ba. Ga shi ko duk sun riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ali na tare da gaskiya, gaskiya kuma na tare da Ali, tana juyawa duk inda ya juya. Ba za su rabu ba har su zo wurina a qoramar Alkausara.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa, sai, Fatima ta yi fushi a kan haka, kuma ta tafiyar ta. Ta rantse ba za ta sake magana da Abubakar ko abokinsa ba har sai ta haxu da babanta ta yi qarar su, gare shi. To, a lokacin da zata rasu, inji shi, sai ta yi wa mijinta Ali Raliyallahu Anhu wasicci cewa, ya rufe ta da dare, don kada xayansu ya yi mata sallah.

Xan Shi’ar ya ci gaba: Dukansu sun riwaito cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ya Fatima! Allah Ta’alah yana fushi don fushinki, kuma yana yarda don yardarki”. Kuma duk sun riwaito cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Fatima sashena ce. Wanda ya cuta mata ya cuta mani, wanda ya cuta mani kuwa ya cuta wa Allah Ta’alah”.

Ya ci gaba da cewa: Da wannan labarin gaskiya ne, to, da bai hallata Abubakar ya bar alfadari da takobi da rawanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wurin Ali Raliyallahu Anhu ba, a lokacin da Abbas ya nemi a ba shi su. Kuma da Ahlul-Baitin da Allah Ta’alah ya tsarkake su cikin littafinsa sun aikata abin da ba ya halatta, don an haramta masu sadaka amma sun neme ta. Bayan haka ne kuma Jabiru xan Abdullahi ya zo ya ce wa Abubakar: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce mani: Idan dukiya ta zo daga Bahraini to, zan xibar maka cikon tafina har sau uku. Sai Abubakar ya ce masa: Ka tafi Baitul-Mali ka xibi daidai abin da ya ce. Jabir ya je ya xiba daga cikin dukiyar musulmi ba tare da wani shedu ba; don kawai maganarsa shi kaxai.

Martani:

Wannan maganar dai ta qunshi qarairayi da qage mai yawa. Bari mu soma bayanin su:

Tun farko, a cikin maganarsa akwai tuqa da warwara, don da farko cewa ya yi Fadak gado ce. Yanzu kuma ya ce kyauta ce. Amma, bari mu bi shi a haka. Sai mu ce: Ita wannan kyautar yaushe ne aka yi ta? Mu mun san Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tsarkaku daga yin wasicci ga mai gado. Don hakan ya sava ma Shari’a. Idan kuma tun lokacin da yake cikin qoshin lafiyarsa ne ya yi mata kyautar, to, me ya sa ba ta karva ba sai yanzu? Idan mutum ya yi kyauta, ba a karve ta ba har ya mutu, kyauta ta tashi kenan. Ya ko za a yi Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba da kyautar Fadak ga Fatima kuma matansa da sauran musulmi ba su sani ba, har ya zame cewa Ummu Aimana ko Ali Raliyallahu Anhuma ne suka kevanta da sanin hakan?

Danganta wannan neman Fadak shi kansa ga Fatima, qarya ne. Abul Abbas xan Suraiju ya soke maganar yana mai cewa: Hadissan Buhturi xan hassanu da ya karvo daga Zaidu xan Ali cewa Fatima ta gaya ma Abubakar Raliyallahu Anhu cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba ta kyautar Fadak, kuma wai, ta zo da shedar mace da namiji sai ya qi karva, wannan maganar na da ban mamaki!! Lalle Fatima ta tambayi Abubakar gadonta, sai ya faxa mata cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ba a gadon mu”. Amma ba a ce Fadak ce ta nema ba, balle a ce ta shedar da wani a kan haka.

Amma Jarir ya riwaito daga Mugirata daga Umaru xan Abdulaziz cewa: “Fatima ta nemi Annabi ya ba ta Fadak, bai ba ta ba. Kuma Annabin ya kasance yana ciyar da wasu Banu Hashim, danginsa daga cikinta, yana taimakon masu rauninsu, ya aurar da marasa aure duk daga cikinta. Haka aka ci gaba har qarshen rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Fatima kuma ta karvi gaskiya”. Sarki Umaru xan Abdulazizi ya qare da cewa: “Don haka, ina sheda maku cewa, ni ma na bar ta yadda take lokacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama”.

Ba wani ingantaccen hadisi da ya tabbatar da cewa Fatima ta ce an ba ta Fadak, ko wani ya yi sheda a kan haka. Da kuwa an yi haka da an riwaito shi, don abin jayyayya ne wanda ya shafi al’umma, kuma aka yawaita maganganu game da shi. Tun a lokacin ba xaya daga cikin musulmi da ya ce ya ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba Fatima ita, ko ita Fatima ta ce an ba ta. Sai daga baya wannan Buhuturi xan hassan ya yo wannan riwaya.

To, ko da an qaddara cewa wannan hadisin ya tabbata, babu hujja a cikinsa. Don Fatima ba ta ce zata rantse tare da shedu aka hana ta ba. Kuma Abubakar bai ce ba shi yarda da shedu da rantsuwa ba.

Abin da tarihi ya bayyana shi ne, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama gonaki uku ne ya zava, waxanda suka haxa da gonar Banun Nadhir, da ta Haibara da Fadak. Sai ya keve ta Banun Nadhir don biyan buqatunsa da ke iya tasowa. Fadak kuma ya keve ta don matafiya masu buqata. Haibara kuma sai ya raba ta kashi uku; kashi biyu daga ciki ya raba su a tsakanin musulmi, xayan kuma don ci da shan iyalinsa. To, duk abin da ya saura bayan an fitar wa iyalinsa sai a sake raba shi ga matalautan Muhajiruna.

A riwayar Laisu lokacin da Fatima Raliyallahu Anha ta aika ma Abubakar tana tambayar sa game da gadonta cikin dukiyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wadda ta haxa da abin da Allah ya ba shi a Madina ba tare da yaqi ba, da kuma Fadak, da abin da ya saura daga cikin humusin Haibara sai ya gaya mata cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ba a gadonmu (Annabawa). Abin da duk muka bari sadaka ne. Kawai dai ‘yan gidan Manzo suna iya amfani da ita dukiyar, amma ba mallaka ba”. Abubakar ya qara da cewa: “Wallahi ba zan canza komai ba cikin dukiyar daga yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya saba yi da ita. Don haka sai bai ba Fatima komai na gado ba.

Duk wanda ya san farihin sayyidina Abubakar tare da duba riwayoyin da suka zo kan wannan al’amari ya san lalle Abubakar yana ganin girman Fatima kuma yana karvar maganarta. To, ina kuma ga a ce ta zo da shaidu irin waxanda suka ambata.

Bisa qaddara cewa, ana iya gadon Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, to, waxanda ke da haqqi su ne matansa da wan mahaifinsa Abbas. A irin wannan kuwa da an buqaci shedu mace xaya ko namiji xaya ba zasu wadatar ba bisa ga Alqur’ani da sunnah da haxuwar malamai. Don haka, in har jayayya ce ba Abubakar ne mai yinta ba.

Kafa hujja a irin wannan lamari da kasancewar Ummu Aimana ‘yar aljanna jahilci ne da ya wuce wuri. Domin hujja ce a kansa. Ba wai sayyidina Abubakar ba, koda Hajjaju xan yusufa da Mukhtaru xan Abi Ubaid suka ce basu amsar shedarta ita kaxai ga haqqi, su faxi gaskiya, don qa’ida ce ta Shari’a cewa, ba a karvar shedar macce ga abin da ya shafi kuxi. Zamanta ‘yar aljanna ko bai canza hukuncin Shari’a a wurin masu ilimi da hankali.

Ummu Aimana dai, ita ce uwar Usamatu xan Zaidu. Kuma ita ce wadda ta yi renon Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Tana kuma cikin muhajirai mata, masu daraja. Don girman darajarta ne ‘yan Shi’ar suke so su lava gare ta suyi mata qarya. Kuma babu wani littafi na msulunci da aka yarda da shi wand aya kawo wannan magana.

Haka ma cewar da ya yi wai, Ali Raliyallahu Anhu ya yi shaida cewa, an ba ta aka qi karvar shaidarsa don yana mijinta. Duk ba gaskiya ne ba. Amma bisa qaddara an yi hakan, to, ba aibi ba ne. Don shaidar miji ga matarsa ba a aiki da ita a wurin mafi yawan malamai. Wanda kuma suka yarda a karve daga cikin malaman cewa suka yi sai idan an samu qari akan mijin, kamar a samu wani namiji xaya ko kuma mata biyu.

Hadisin da ya kawo cewa, Ali na tare da gaskiya, ita ma gaskiya tana tare da Ali duk inda ya juya ba za su rabu ba har ya zo mani a wurin Alkausar. Wannan magana ce ta qarya da jahilci. Don ba ta da madogara ko daidai yanar gizo. Ka ga kuwa akwai muni matuqa, mutum ya qaga qarya ya jingina ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuma ya ce wai, duk malaman Sunnah sun san da ita a matsayin gaskiya.

Sai maganar da ya jingina ga Fatima cewa ta fusata da Abubakar kuma ta rantse ba zata sake yi masa magana ba, shi da abokinsa. A zatonsa yana yabonta ne, alhalin kuwa suka ce mai girma a gare ta. Ina abin fushi a nan? Abubakar bai yi wani hukunci ba da ya sava ma gaskiya. Kuma gama-garin musulmi na iya haqurin karvar irin wannan gaskiya, to, ina ga Fatima ‘yar gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Ba yabo gare ta a nan, ba aibantawa ga Abubakar.

A bisa imaninmu da iya saninmu, yawancin abubuwan da ake riwaitowa game da Fatima da wasu Sahabbai irin waxannan qarairayi ne. Wasu hikayoyin kuma suna da fassara mai ma’ana wadda ke fitar da su daga zargi. Idan kuma har xayansu ta tabbata cewa, ya aikata kuskure ko laifi, to, ai su ba ma’asumai ba ne, waliyyan Allah dai ne, ‘yan aljanna da Allah Ta’ala ke gafarta ma zunubbansu.

Haka ma abin da ya ambata na cewa ta yi wasicci da Ali ya rufe ta da dare don kada xayansu ya yi mata sallah. Jingina wannan irin wasicci ga Fatima shi ma jahilci ne da wauta. Me zai sa Fatima ta yi wannan wasicci? Ai kowa ya san sallar musulmi qarin alheri ce da lada ga mamaci. Kuma mafificin halitta ba zai cutu ba koda mafi sharrin halitta ya yi masa sallah. Ga dai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, kowa ya yi masa sallah; muminai da fajirai. Kai har ma da munafikai. Irin wannan in bai amfane shi ba, ba zai cutar da shi ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuwa ya san cewa a cikin al’ummarsa akwai munafukai amma bai yi wasicci kada wani ya yi masa sallah ba.

Hadisin cewa, Allah na fushi da fushin Fatima, kuma yana yarda da yardarta. Shi ma qarya ne irin wancan. Babu shi a cikin ko xaya daga cikin littafan hadisi. Ba shi kuma da wani sanannen isnadi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Mu dai mun sheda cewa Fatima yar’aljanna ce, kuma tabbas Allah ya yarda da ita. Muna kuma irin wannan shedar ga Abubakar da Umar da Usmanu da Ali da Xalhatu da Zubairu da Sa’adu da Sa’idu da Abdulrahaman xan aufu da Abu Ubaidata. Mun kuma aminta da abin da Allah Ta’alah ya ba da labari a wurare da yawa game da su; cewa ya yarda da su. Kamar in da maxaukakin Sarkin ya ce:

﴿وَٱلسَّبِقُونَ ٱلأَوَّلُونَ مِنَ ٱلمُهَجِرِينَ وَٱلأَنصَارِ وَٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُم بِإِحسَن رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنهُم وَرَضُواْ عَنهُ وَأَعَدَّ لَهُم جَنَّت تَجرِي تَحتَهَا ٱلأَنهَرُ خَلِدِينَ فِيهَا أَبَدا ذَلِكَ ٱلفَوزُ ٱلعَظِيمُ١٠٠﴾ التوبة: ١٠٠

Magabata na farko daga cikin Muhajiruna da Ansaru da waxanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su, su ma sun yarda da shi. Attauba 100.

Da cewar da Allah Ta’ala ya yi:

﴿لَّقَد رَضِيَ ٱللَّهُ عَنِ ٱلمُؤمِنِينَ إِذ يُبَايِعُونَكَ تَحتَ ٱلشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِم فَأَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ عَلَيهِم وَأَثَبَهُم فَتحا قَرِيبا١٨﴾ الفتح: ١٨

Haqiqa, Allah ya yarda da muminai a lokacin da suke yi ma ka mubaya’a a qarqashin itaciya. Suratul Fathi: 18.

Mun kuma yarda da abin da ya tabbabata cewa, Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu yana mai yarda da Sahabbansa. Kuma mun san duk wanda Allah ya yarda da shi da Manzo, to fushin wani ko wane ne ba zai cutar da shi ba.

Hadisin da ya kawo cewa, Fatima sashen Manzo ce. Wanda duk ya cuta mata ya cuta masa. Duk da yake ya yi qari a cikinsa. Amma dai Annabi ya faxe shi ne a lokacin da Ali Raliyallahu Anhu ya nemi auren xiyar Abu Jahali. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hau mimbari a kan haka, ya yi huxuba yana cewa: “Haqiqa mutanen gidan Hashimu xan Mugirata sun nemi in ba da izinisu aurar da ‘yarsu ga Ali xan Abu Xalib. To, ba zan yi izini ba, kuma ba zan yi izini ba, kuma ba zan yi izini ba. Domin Fatima shashena ce; duk abin da ke damun ta yana damu na. Sai dai in Ali yana son ya saki xiyata ya Auri tasu.

Sai cewar da ya yi, in da gaskiya ne da bai halatta Abubakar ya bar alfadarin Manzon Allah da takobinsa da rawaninsa wurin Ali ya hana ma Abbas shi lokacin da ya nema. Sai a ce masa: Wa ya ce Abubakar da Umar sun ba Ali don ya mallaka? Ai sun bar su ne a hannunsa kamar yadda suka bar sadakarsa wurin Ali da Abbas don su ba da ita ga waxanda Shariah ta ce a ba.

Maganar tsarkake Ahlul-Baiti daga cin sadaka. Da farko, Allah Ta’ala bai ce ya tsarkake dukkan Ahlul-Baiti ba. Ku ma kun san cewa akwai daga cikin Banu-Hashim waxanda ba a tsarkake daga savo ba, musamman ma a gun ku ‘yan-sha-biyu, da ke xaukar duk wani dangin Banu-Hashim da ke son Abubakar da Umar a matsayin wanda ba tsarkakakke ba.

Abin da dai Allah Ta’ala ya ce yana son haka gare su, kamar yadda ya ce yana son haka ga muminai cikin ayar taimama. Allah na son haka, kuma ya yarda da haka, ya yi umurni a kan haka. Wanda ya aikata, to, ya cimma muradin da aka so masa, wanda kuma bai aikata ba, to, ba zai sami muradin ba.

Sai maganar sadaka xin da aka haramta masu. Abin da aka haramta masu shi ne sadakar wajibi, ita ce Zakka. Amma sadaqoqi na ganin dama ba laifi ba ne a kansu in sun amfana da su. Ai suna shan ruwan rijiyoyin sadaka misali, waxanda ake ajiyewa tsakanin Makka da Madina. Da kansu kuma suna faxin cewa, sadakar farilla ce aka haramta mana, ba a haramta mana sadakar nafila ba. To, in ko haka ne, me zai hana su amfana da sadakar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ga jama’ar musulmi? Wannan dukiyar ba zakkar da aka farlanta wa Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ba ce. Kuma na haramta masu zakka ne don tana dauxar mutane. Amma abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bari na ganimar da Allah ya ba shi halal ce ga re shi, kuma ya sanya sashenta ya zama sadaka ga musulmi. Don haka Ahlul-Baiti na iya cin moriyarta kamar sauran musulmi.

Game da tsokacin da ya yi kan karvar da Jabir Raliyallahu Anhu ya yi ga alqawarin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ma sa daga wurin Abubakar. Jabir dai bai raya cewa yana son haqqin wani ba, ya dai nemi wani abu ne daga baitul-mali, shugaba kuma na da damar xaukar sa ya ba shi, ko da kuwa Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi masa alqawari ba. Ka ga ba a buqatar shedu a nan.

 A gaskiya, duk maganganun da suke yi game da Fatima Raliyallahu Anha cewa ta nemi Fadak kuma ta kafa sheda akan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba ta ita. Duk wannan suka ce suke yi gare ta a fakaice ba yabo. Kuma Allah ya raba ta da waxannan qazuffa nasu, ya nisantar da ita daga gare su.

2.9.7 Wai Don me Aka ce da Abubakar “Siddiqu”?

 Xan Shi’ar ya ce: Malaman Sunnah duk sun riwaito hadisi game da cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa game da Abu Zarri cewa: “Qasa ba ta taxa xaukar mafi gaskiyar magana fiye da Abu Zarri ba. Ita ma sama ba ta rufe wanda ya fi shi gaskiyar magana ba”. Amma duk da haka ba su kira shi Siddiqu ba sai Abubakar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi masa irin wannan shedar ba.

Martani:

 Hadisin da ya ambata cewa duk malaman Sunnah sun riwaito shi ba shi a cikin Buhari da Muslim ko littafan Sunan na Ahlus-Sunnah. Amma tun da yake an riwaito shi a wasu littafan Sunnah, to, zamu qaddara ingancinsa mu ba shi amsa.

Ba wani malamin da ya fahimci wannan hadisi a matsayin cewa, Abu Zarri ya fi duk mutanen da ke bisa doron qasa faxin gaskiya. Don wannan na fifita shi a kan Annabawa da Manzanni, cikinsu har da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da sayyidina Ali. Ka ga kenan ya sava ma ijma’in musulmi; Sunnah da Shi’ah baki xaya. Don haka ne aka san cewa ma’anar wannan kalimar ita ce, Abu Zarri mai gaskiya ne. Kuma waninsa bai fi shi neman yin daidai da gaskiya ba. Amma wannan ba ya lizimtar da cewa, babu wanda ya fi shi yawan gaskiyar da girmanta. Haka ma abin wani ya gasgata na iya zarce wanda shi Abu Zarri xin ya gasgata.

 Abubakar dai ba a kira shi Siddiqu don kawai yana faxin gaskiya ba, a’a, don girman gasgatawar da ya yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. In aka lura da lafazin da kyau za a gane cewa, kowane Siddiqu mai gaskiya ne, amma ba kowane mai gaskiya ke zama Siddiqu ba.

 2.9.8 Abubakar Halifan Manzo

 Xan Shi’ar ya ce: Sun kira shi halifan Manzo ga shi kuma Manzo bai tava sa shi ya waqilce shi ba; a rayuwarsa ko bayan rayuwarsa, koda a wurinsu. Ba su kira Ali halifan Manzo ba, ga shi kuma Manzon ya sha sa shi ya waqilce shi a lokacin rayuwarsa kamar yadda ya wakilce shi a kan garin Madina lokacin yakin Tabuka, har ya ce masa: “Madina ba ta gyaruwa sai da ni ko kai. Ba ka son ka zama a wurina kamar matsayin Haruna a wurin Musa? Sai dai fa babu wani Annabi bayana”.

 Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ya shugabantar da Usamatu xan Zaidu akan rundunar yaqin da Abubakar da Umar ke ciki. Kuma bai sauke shi ba har ya rasu, ga shi kuma ba su kira shi halifa ba. A lokacin da Abubakar ya zama halifa sai Usamatu ya fusata, ya ce masa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya shugabantar da ni akan ka, to wa ya shugabantar da kai a kaina? Sai ya tafi shi da Umar suka ba shi haquri. Kuma suka rinqa kiran sa Amir (sarki) har tsawon rayuwarsa.

Martani:

Halifan mutum shi ne wanda ya sa don ya maye gurbinsa ko kuma wanda ya maye gurbinsa koda ba da izininsa ba. A harshen Larabci wannan ma’anar ta biyu ita aka sani. Kuma shi ne ra’ayin mafi yawan malamai. Amma wasu daga cikin Zahiriyyah da kuma ‘yan Shi’ah cewa suka yi sai in shi ya sanya wanda zai maye bayansa sannan za a kira shi halifansa.

To, a kowane ra’ayin dai Abubakar Raliyallahu Anhu halifan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne, don shi ne ya maye gurbinsa bayan rasuwarsa. Ko ‘yan Shi’ah ma ba su jayayyar cewa shi ya zama shugaban musulmi bayan Manzo. Shi ke ba musulmi sallah, ya tsayar da haddi, ya yi jihadi, ya raba ganima, ya naxa sarakuna da alqalai. To, idan an ce halifa shi ne wanda wani ya sa ya maye gurbinsa, harwayau dai Abubakar ne. Domin daga cikin Ahlus-Sunnah akwai masu ganin cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya ce Abubakar ya maye gurbinsa bayan rasuwarsa, ko dai ta hanyar nassi bayyananne ko wanda sai an yi tunani. Kamar yadda su ma ‘yan Shi’ah ke ganin cewa akwai nassi a kan Ali. Wasunsu su ce bayyanannen nassi, wasu su ce mai buqatar nazari. Ra’ayin farko shi ne na ‘yan-sha-biyu, na biyun kuma na Jarudiyyah, wani vangare na Zaidiyyah. Kuma ra’ayin Ahlus-Sunnah masu ganin akwai bayyanannen nassi game halifancin Abubakar ya fi qarfi nesa ba kusa ba a kan ra’ayin masu cewa akwai nasssi a kan Ali saboda yawan hadissai masu nuni ga Abubakar da ingancinsu.

 Amma cewa ya saka Ali Raliyallahu Anhu ya kula da Madina ba ya cikin abin da Ali ya kevanta da shi. Domin duk lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yake fita daga Madina yakan sa wani daga cikin Sahabbansa ya kula masa da ita. Kamar yadda ya sa Abdullahi xan Ummu-Maktumi ya kula da ita a wani lokaci, da yadda ya sa Usmanu xan Affana ya riqa garin a wani lokaci na daban.

 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa wani ba Ali ba a wasu lokutta ya kula da tsaron Madina da waxanda ke cikinta, sa’adda aka fi son a riqa ta don muhimmancin waxanda aka bari a cikinta. Amma dai duk wannan halifance ne qayyaddade ga wasu mutane da wasu lokuta, ba halifanci ne a kan duk al’umar Annabi ba. Ba kuma halifanci ne na bayan rasuwarsa ba. Idan har aka Ali da sunan halifa da wannan ma’ana to, da yawa waxanda za su karva irin wannan sunan, don sun yi irin wannan halifancin a wasu lokutan su ma.

 Halifanci na bai xaya shi ne wanda ake yi bayan cikawar Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama. Shi ne kuma wanda ya kamata mai yin sa ya zan ya fi sauran jama’a daraja. Amma halifanci a kan Madina kawai ba a cika kula da fifikon mutum a wajen yinsa ba. Domin masu fifikon a wannan lokaci duk suna can tare da Manzo. Don can ne suka fi amfani. Wanda za a bari kuwa ana barin sa ne don kula da iyali. Ka ga ta wannan fuska wanda aka tafi da shi ma ya fi fifiko.

 Kamantawar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa Ali da Haruna kuwa kan asali maye gurbin ne. Don ba ta ko ina suka yi kama ba. Ali Raliyallahu Anhu kuwa yana da waxanda suka yi tarayya da shi a wurin maye gurbin Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama idan ya fita daga garin Madina. Amma Haruna ba ya da shi. Kuma a lokacin da Annabi Musa Alaihis Salamu ya tafi ganawa da Allah shi kaxai ya tafi, ya bar duk jama’arsa. Amma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama lokacin da ya tafi yaqin Tabuka ya tafi ne da dukkan musulmi in banda masu uzuri. Bai bar Ali ga kowa ba sai qananan yara da mata. Sai ko maza masu uzuri. Don haka halifancin nasa bai kai kamar na Haruna ba. Amma ya yi daidai da shi ta fuskar kasancewarsa an ba shi amana a lokacin da maigidansa ba ya nan kamar yadda haruna ya yi wa Annabi Musa. Wannan shi ya sa Ali Raliyallahu Anhu ya nuna damuwa, sai Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ya nuna masa cewa, barin sa tsaron bai nuna cewa don wani naqasu ba ne. A’a, an dai danqa ma sa amana ne kamar yadda Musa Alaihis Salamu ya yi wa xan uwansa Haruna.

Maganar cewa Madina ba ta gyaruwa sai da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ko Ali, qarya ce zunzurutunta. Kuma ba a san ta ba a cikin xaya daga cikin litaffan ilimi da ake dogaro a kansu. Kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ta fita Madina tare da Ali Raliyallahu Anhu, ba abin da ya same ta sai alherin Allah. Wannan na cikin abin da ke bayyana tsananin jahilcin ‘yan-sha-biyu. Sai su rafka qaryar da duk mai xan hasken karatu yana gane ta.

Sai maganar cewa, Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa Usamatu Raliyallahu Anhu ya shugabanci rundunar da Abubakar da Umar ke ciki. Wannan ma qarya ce da ba ta wuyar ganewa ga wanda ya san hadisi. Don kowa ya san cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya waqilta Abubakar ya maye gurbinsa wajen ba da sallah tun lokacin da ya fara rashin lafiya har zuwa rasuwarsa. Rundunar Usamatu kuwa an riwaito cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya shirya ta ne kafin rashin lafiyarsa. To, in har ma Abubakar na ciki, ka ga daga radda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ya ba mutane sallah, shi an fitar da shi daga rundunar kenan. Ballantana ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava sa Abubakar qarqashin Usamatu ba.

Kuma cewar da ya yi har Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya cika bai cire Usamatu ba. Ai Abubakar xin ma bai cire shi ba, tare da yana da haqqin yin haka da ya fuskanci shi ne maslaha a wancan lokaci. Amma Abubakar ya zartar ta tafiyar rundunar Usamatu da barinsa a matsayin shugaba duk da kiraye-kirayen da aka yi ta yi ma sa daga musulmi na ya saurara kada rundunar ta je a wancan hali da ake ciki na tashin hankali da ruxuwa. Abubakar ya rantse ba zai fasa ci gaban abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya soma ba.

Cewa kuma Usamatu ya yi fushi a lokacin da aka naxa Abubakar. Wannan qarya ce mai tsananin muni, domin son da Usamatu ke wa Abubakar da xa’arsa gare shi mashahurin abu ne da ba a iya musu. Usamatu ya fi kowa nisantar savani da rarraba. Ko lokacin fitina bai yaqi cikin kowace ruduna ba. Kuma shi ba Baquraishe ba ne, balle ya yi tunanin zama halifa. Bai ma zo masa a zuciya cewa zai iya zama halifa. To, in haka ne wace fai’da zai samu in dai ya yi irin wannan maganar ga wanda ya zama halifa, tare da ya san cewa duk wanda ya zama halifa, na da iko a kansa. Qaddara cewa Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa Abubakar qarqashin shugabancinsa. To, bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ci gaban wannan shugabancin zai rataya ne ga yardar sabon shugaba bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma lamarin zartar da runduna ko hana ta ya koma a hannunsa. Kuma ci gaba da shugabancin Usamatu da rashinsa ya koma hannun sabon halifa. To, idan an qaddara cewa Usamatu zai ce wa ya shugabantar da kai a kaina? Sai Abubakar Raliyallahu Anhu ya ce: Wanda ya shugabatar da ni akan dukkan musulmi, cikinsu har da waxanda suka fi ka. In ya ce amma ni an shugabantar da ni a kanka, sai Abubakar Raliyallahu Anhu ya ce wannan ya kasance kamin in zama halifa, amma bayan na zama halifa to, ka koma qarqashin shugabancina.

 Shi dai Usamatu Raliyallahu Anhu mai hankali ne da ilimi da tsoron Allan da ba za su bari ya yi irin wannan magana maras ma’ana da xan Shi’ar ya jingina ma sa ba, ga mutum mai matsayi irin na Abubakar Raliyallahu Anhu.

 Abin da yafi wannan ban mamaki shi ne cewa wai sayyidina Abubakar da Umar sun tafi wurin Usamatu suna neman ya yarda da su, tare da cewa su ‘yan Shi’ah ne suka ce Abubakar da Umar da qarfi suka rinjayi Ali Raliyallahu Anhu da Banu-Hashim da Bani-Abdimanafi, ba su nemi yardarsu ba. Ga shi kuwa waxannan sun fi yawa da qarfi da xaukaka a kan Usamatu Raliyallahu Anhu. Wanda ya rinjayi qabilu kamar Bani-Hashim da Bani-Umayyata da sauran Bani-Abdimanafi da rassa daban-daban na Quraishawa, wacce yarda yake nema daga Usamatu xan Zaidu wanda ya kasance cikin mafi raunin talakkawansu, ba shi da wata qabila ko ‘yan’uwa, ko kuxi ko wasu mutane tare da shi. Ba don son da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi masa ba, da gabatar da shi da ya yi zai zama kamar sauran talakkawan musulmi masu rauni.

 ‘Yan Shi’a na iya cewa, sun nemi yardarsa ne don Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama na sonsa. Wannan ko zai rosa ma ku aqida gaba xaya. Don ga shi kun ce sun musanya alqawarin Manzo, sun zalunci wanda ya yi wa wasicci, sun yi masa qwace. To, sai a tambaye ku: Wanda bai bi ingantaccen umurni ba, ya musanya bayyanannen al’amari, ya yi zalunci da wuce iyaka, ya sa qarfi, bai kula da xa’ar Allah Ta’ala da ta Manzonsa Sallallahu Alaihi Wasallama ba, kuma bai kula da alqawalin ‘yan gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da alfarmarsu ba, zai nemi yardar Manzo dangane da Usamatu? Kuma bayan haka kun ce bai nemi yardar Fatima ba, ya yi wa qwace, ya cutar da ita. Duk wanda ya aikata wannan to, lalle ba ya buqatar neman yardar Usamatu. Abin da ke sa mutum ya nemi yardarka shi ne don kana riqo da addini ko kuma don kana da duniya a hannunska. Ka ga a cewarsu, nan babu ko guda. ‘Yan Shi’ah sun fi kowa yawan takin saqa a cikin maganganunsu saboda wautarsu da jahilcinsu.

 2.9.9 Wai Don Me Aka Ce Da Umar “Faruqu”?

Xan Shi’ar ya ce: Kuma sun kira Umar Faruqu, mai rabe gaskiya ga shi kuma ba su kira Ali da wannan suna ba, kodayake Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Ali ne mai rarrabewa tsakanin mutanen gaskiya da mutanen banza”. Umar da kansa ya ce: Ba mu kasance muna sanin munafukai a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba sai wanda muka ga Ali na fushi da shi daga cikinsu.

Martani:

Da farko waxannan hadisan biyu malaman hadisi ba su shakkar cewa qarya ne. Kuma ba wani malami da ya riwaito su a cikin littaffan ilimin da ake dogaro a kansu. Ba kuma xaya daga cikinsu da ke da sanannen isnadi.

Ko ga mas’alar fiqihu, duk wanda ya kafa hujja da hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wajibi ne ya bayyana madogarar hadisinsa. To, ballantana mas’ala irin wannan? In ba haka ba don kawai mutum ya ce: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce”, duk malamai sun haxu a kan cewa wannan ba hujja ba ne. In kuwa har yin haka hujja ne, kenan duk hadisan da Ahlus-Sunnah suka kawo su zama hujja kenan a kan ‘yan Shi’ah. Mu dai a wannan babin muna gamsuwa da hadisin da duk wata qungiya ta musulmi ta riwaito idan dai isnadinsa na sanannun mutane ne masu gaskiya.

Amma idan hadisi ba shi da isnadi, kuma wanda ya cirato shi ya jingina shi ne ga littaffen wani, wanda bai riwaito shi ba, to, ba ya halatta ga mutum ya yi shaida a kan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ga abin da bai san madogararsa ba.

Sanannen abu ne ga duk mai masaniya cikakka cewa, malaman hadisi ne suka fi kowa qoqarin sanin maganganun Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama da ya faxa, kuma sun fi kowa kwaxayin bin maganarsa, da nisantar son zuciya. Inda ya tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxi wannan game da Ali Raliyallahu Anhu da sun fi kowa cancanta ga bin wannan maganar, don suna bin maganarsa ne bisa ga imaninsu da shi, da son binsa, ba don neman wata buqata ga wanda aka yaba ba.

 Da ya tabbata a wurin malaman hadisi cewa Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa Ali: “Wannan shi ne mai rarrabe ma al’ummata gaskiya” da sun karvi wannan sunan, sun riwaito shi kamar yadda suka riwaito maganarsa game da Abu Ubaidata Raliyallahu Anhu cewa: “Wannan shi ne amintaccen wannan alumma” da kuma cewar da ya yi game da Zubairu: “Kowane Annabi na da mataimaka. Ni ko Zubairu ne mataimakina”. Kamar kuma yadda suka karvi abin da suka riwaito na cewar da ya yi ga Ali Raliyallahu Anhu “Lalle, gobe zan miqa wannan tutar ga wani mutum da Allah da Manzonsa ke so, kuma yake sonsu” da hadisin Kisa’u wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa Ali da Fatima da Hasan da Husaini addu’a yana cewa: “Ya Allah, waxannan iyalaina ne. Ka gusar da qazanta daga gare su, kuma ka tsarkake su tsarkakewa” da makamantan waxannan hadissan.

 Duk hadisan nan biyu da marubucin ya kawo mun san cewa qarya ne bisa ga dalili. Ba ya halatta a danganta su ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma ma mene ne ma’anar kasancewar Ali Raliyallahu Anhu ko waninsa mai rarrabewar alumma tsakanin gaskiya da qarya? In suna nufin cewa zai iya banbancewa tsakanin mumini da munafuki, to wannan babu mutumin da ke iya yin sa. Don Allah Ta’ala ya ce: Daga cikin waxanda ke kewayenku akwai munafikai da kuma cikin mutanen Madina. Sun saba da munafucci, kai ba ka san su ba, mu ne muka san su. Attauba: 101. To, idan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai san ainihin munafikai da fuskokinsu ba cikin mutanen da ke tare da shi a Madina da kewayenta, to yaya wani zai iya sanin su?

 Son da ‘yan Shi’ah ke cewa suna yi wa Ali Raliyallahu Anhu shi kansa babu shi. Domin wanda suke son babu shi. Shi ne imamin da ba ya kuskure, wanda kuma nassi ya zo da shugabancinsa, babu wani shugaba bayan Manzon face shi, wanda kuma ke da imanin cewa Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma azzalumai ne, ‘yan qwace, kuma kafirai. To, ka ga in Ali ya zo ya bayyana gare su ranar alqiyama zasu san cewa ba shi ne wanda suke so ba. Wannan shi zai bayyana maka cewa, ‘yan-sha-biyu maqiyan Ali ne, babu tanbaba.

 Daga nan ne za ka fahimci hadisin da Muslim ya riwaito daga Ali Raliyallahu Anhu cewa: “Haqiqa Annabi ya tabbacin cewa, ba mai sona sai mumini, kuma ba mai qina sai munafiki.

Son da ‘yan Shi’ah ke yi wa Ali ba shi da banbanci da son da Yahudawa ke cewa suna yi ga Annabi Musa da wanda Kirista ke cewa suna yi ga Annabi Isah. Kai ‘yan-sha-biyu ma suna qin abin da ya sifofin gaskiya na Ali kamar yadda Yahudawa ke qin sifofin gaskiya na Annabi Musa, Kiristoci kuma suke qin sifofin gaskiya na Annabi Isah. Domin dukkansu suna qin wanda ya yarda da Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama.

 2.9.10 A’isha Uwar Muminai

Xan Shi’ar ya ce: “Sun xaukaka lamarin Aisha ga shi kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance yana ambaton Khadija ‘yar Khuwailidu, har Aisha ta ce masa: “Ka cika ambaton ta ga shi kuwa Allah ya musanya maka waxanda suka fi ta”. Sai ya ce: “Wallahi ba a musanya mani waxanda suka fita ba. Ta gasgata ni lokacin da mutane suka qaryata ni, ta karve ni lokacin da mutane suka kore ni, ta amfanar da ni da kuxinta. Allah kuma ya azurta ni da ‘ya’ya daga wurinta, bai a ba ni daga wata ba ita ta.

Martani:

 Ahlus-Sunnah dai ba su haxu a kan cewa Aisha Raliyallahu Anha ce ta fi duk matansa ba. Amma da yawa daga cikinsu na ganin haka, saboda hadisin da ya zo cikin Buhari da Muslim ta hanyar Abu Musa Al-Ash’ari da Anas Allah ya yarda da su cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce “Falalar Aisha a kan sauran mata kamar falalar Saridu ne a kan sauran abinci. Saridu shi ne tuwon alkama da miyar nama, kuma mafificin abinci. Domin alkama ta fi sauran dangin abinci, nama kuma ya wuce sauran abubuwan haxi a miya kamar yadda ya zo a hadisin da Ibnu qutaibata ya riwaito daga Manzon Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: “Fiyayyar miyar da mutane ke sha duniya da lahira ita ce nama”. To, ka ga da haka mai gaskiya abin gasgatawa ya fifita Aisha a kan sauran mata kamar yadda Saridu yake da fifiko a kan sauran abinci.

 Ya zo a cikin hadisi ingantacce da Amru xan Asi Raliyallahu Anhu ya riwaito inda ya ce: “Na ce, ya Manzon Allah, duk cikin mutane wa ka fi so?” Sai ya ce: “Aishah”. Sai na ce: “To, daga cikin maza fa?” Sai ya ce: “Babanta”. Na ce: “Sai wa?” Ya ce: “Sai Umar”. Sannan ya ambaci sunayen wasu mutane.

 Cewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Wallahi ba a musanya mani waxanda suka fita ba”. Idan ya inganta ba ya da shan kai. Domin Khadija ta amfane shi a farkon musulunci irin amfanin da waninta bai yi ma sa ba. Ta wannan fuska Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba shi da kamarta, don ta amfane shi lokacin buqata. Ita kuma Aisha ta kasance tare da shi ne a qarshen sha’anin annabta; lokacin da addini yake kammala. Wannan ne ya sa ta samu qarin imani da ilimin da mutanen da suka rasu tun farko ba su samu ba. Don haka sai ta zama mafi xaukaka ta wannan fuskar. Babu shakka kuma al’ummar musulmi ta amfana da ita fiye da yadda ta amfana da duk wata ba ita ba. Ta samu ilimi na Sunnah da wani ba ita ba bai samu ba, ta kuma karantar da mutane shi. Khadija ta amfani Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ga kansa, A’ishah kuma ta amfane shi ga al’ummarsa. Addini kuma ya kammala A’ishah tana raye, ita kuma Khadijah, Allah ya karvi ranta gabanin haka. Shi kansa yin imani da musulunci da yin aiki da shi a lokacin cikarsa yana da wani fifiko babu shakka.

 2.9.11 Ina Laifin Nana A’isha?

Xan Shi’ar ya ce: Ta tona asirin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce mata: “Za ki yaqi Ali kina mai zaluntar sa”. Sannan kuma ta sava wa umurnin Allah in da ya ce: Kuma ku zauna a gidajenku. Al-Ahzab:33. Ta fito fili tana yaqar Ali ba don laifin kome ba. Don duk musulmi sun haxu a kan kashe Usman, kuma ita kanta kowane lokaci tana umurni da a kashe shi, tana cewa: “Ku kashe tsohon banza. Allah ya kashe shi”. Lokacin da kuma ta ji cewa an kashe shi sai ta yi murna, sannan ta tambaya: “Wane ne ya zama halifa?” Aka ce mata: “Ali”. Sai ta fito don yaqar sa wai tana neman fansar jinin Usmanu. To, mene ne laifin Ali a cikin wannan? Ya aka yi Xalhatu da Zubairu suka halatta wa kansu yi mata xa’a a kan wannan? Da wace irin fuska za su sadu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Ga shi kuwa da xayanmu ya yi magana da matar wani, ya fitar da ita daga gidanta, ya yi tafiya tare da ita, da ya zama mafi girman maqiyinmu. Ya aka yi dubun dubatar musulmi suka yi mata xa’a ga wannan, suka taimake ta ga yaqan Sarkin Muslumi? Su ne kuwa aka rasa wanda zai taimaki ‘yar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikinsu koda da maganar fatar baki a lokacin da ta nemi haqqinta daga wurin Abubakar?

Martani:

Ahlus-Sunnah mutane ne masu tsayuwa da gaskiya, da yin sheda don Allah, kuma bisa ga adalci. Shi ya sa maganarsu a kodayaushe gaskiya ce da ba taqin saqa a cikinta. Amma ‘yan-sha-biyu da sauran ‘yan bidi’a maganarsu ba ta rabuwa da qarya da taqin saqa. A wurin Ahlus-Sunnah duk waxanda suka yi yakin Badar ‘yan Aljanna ne. Haka ma matan Manzon Allah iyayen muminai; A’ishah da sauran matan duka. Haka Abubakar da Umar da Usmanu da Ali da Xalhatu da Zubairu su ne shugabannin ‘yan aljanna bayan Annabawa. Sannan Ahlus-Sunnah ba su ganin sharaxi ne ga ‘yan aljanna su kasance ba su kuskure ko ba su laifi. A’a, suna iya yin tuntuve ko su yi zunubi qarami ko babba sannan su tuba. Wannan maganar ita ce aqidar duk musulmi. Kuma in har mutum bai tuba daga qananan zunubbai ba, nisantar manya na kankare su. Kai, a wurin mafi yawansu manyan zunubbai ma na kankaruwa da aikata kyawawan ayyukan da suka fi su, sai ladarsu ta shafe zunubin waxancan. Haka ma musibun da ke sauka a kan musulmi, akan shafe zunubbai da su. Da sauran abubuwa dai.

A kan wannan tushe na aqida ne malamai ke cewa, mafi yawan abubuwan da aka ambata game da Sahabbai ba su wuce qarairayi. Wasu kuma ijtihadi ne suka yi, sai ya kasance mafi yawan mutane ba su gane ta inda suka vullo ma abin ba. In da aka qaddara sun yi zunubi kuma, Allah zai gafarta ma su shi, ko dai don sun tuba, ko don sun aikata manyan ayyukan lada, ko an jarabce su da wata musiba mai shafe zunubbai. Ko dai wani abu daban ba wannan ba. Amma tun da hujja ta tsayu a kan zamansu ‘yan aljanna, to, ba zai tava yiwuwa su aikata abin da zai wajabta ma su shiga wuta ba, faufau. Kai ko da ba irin waxannan bayin Allah da muke da tabbacin aljanna gare su ba, ba ya halatta a yi sheda a kan wani daga cikin xaixaikun musulmi da shiga wuta don abin da tabbas ba. Magana kuwa ba tare da ilimi ba haramun ce a Shari’a.

 Sai cewar da ya yi wai, Nana A’ishah ta tona asirin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Sai mu ce, ku halinku kenan; ku kan farauto zunubban wani, ku take naku, sai ku rinqa fallasa shi kome darajarsa. Mu kam, a wurinmu, masu waxannan zunubai sun tuba, kuma Allah ya xaukaka darajarsu da yin tuban. Ba ka ganin Allah Ta’ala ya ce ma matan da suka yi wancan laifi: Idan kun tuba to, zukatanku sun karkata. Attahrim:4. Sai Allah Ta’ala ya kira su zuwa ga tuba. Kuma ba shi yiwuwa a yi zaton cewa ba su tuba ba duk da xaukakar da Allah Ta’ala ya yi masu, da kasancewarsu matan Annabinmu a aljanna. Ga shi har Allah ya ba su zavi tsakanin Allah da Manzonsa da gidan aljanna ko kuma duniya da qawace-qawacenta, suka zavi Allah da Manzonsa da gidan aljanna. Bisa ga haka har Allah ya haramta wa Manzonsa ya musanya wata daga cikinsu ya auro wata. Ya kuma haramta masu qara wani aure a kansu. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu ya barsu a matsayin iyayen muminai. Ba mu zaton ya zan ba su tuba ba bayan wannan aya kamar yadda ba mu zaton ya zan Ali Raliyallahu Anhu bai daina neman auren xiyar Abu Jahli da ya yi niyya ba koda a zuciyarsa bayan waccan ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wadda a cikinta ya nuna damuwarsa akan haka, har ma ya ce: “.. Sai fa in xan Abu Xalib na son ya saki xayata ya auri xiyarsu”.

Shi ko hadisin da xan Shi’ar ya kawo cewa; “Za ki yaqi Ali kina mai zaluntar sa”. Ba a san shi ba a cikin littafan ilimi da ake dogara a kansu, ba ya kuma da sanannen isnadi. Kai ya ma fi kama da qarya don A’ishah ba ta fita ne don ta yi yaqi ba. Ta fita ne don sasantawa tsakanin musulmi, tana tsammanin cewa fitar ta fi alheri, sai ta gano daga baya cewa rashin fitar shi ne ya fi. Shi ya sa ta kasance idan ta tuna ta kan yi kuka har hawaye ya jiqa mayafinta.

 Cewar kuma ta sava wa umurnin Allah, ta yi fita irin ta jahiliyyar farko. Wannan qazafi ne da Allah zai kama mai yinsa in bai tuba ba. Don Allah ya cewa su zauna cikin gidanjensu ba ya hana su fita idan akwai wata maslaha da ake yin umurni da ita kamar suka fita tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama wurin aikin hajji bayan saukar wannan aya, kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya aika ta tare da qanenta Abdurrahaman ta hau bayansa akan taguwa ta yi Umara daga wurin xaukar harama da ake kira Tan’imu

Abin da dai ya kamata a sani wanda kuma shi ne tarihi ya tabbatas, cewa Uwar Muminai ba ta fita a lokacin yaqin basasar Raqumi da nufin yaqi ba. Su ma Xalhatu da Zubairu Raliyallahu Anhuma ba su fita da niyyar su yaqi Ali ba. Kuma wannan shi ne yaqin da aka ambata cikin Alqu’ani inda Allah Ta’ala ya ce:

﴿وَإِن طَائِفَتَانِ مِنَ ٱلمُؤمِنِينَ ٱقتَتَلُواْ فَأَصلِحُواْ بَينَهُمَا فَإِن بَغَت إِحدَىهُمَا عَلَى ٱلأُخرَى فَقَتِلُواْ ٱلَّتِي تَبغِي حَتَّى تَفِيءَ إِلَى أَمرِ ٱللَّهِ فَإِن فَاءَت فَأَصلِحُواْ بَينَهُمَا بِٱلعَدلِ وَأَقسِطُواْ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلمُقسِطِينَ٩ إِنَّمَا ٱلمُؤمِنُونَ إِخوَة فَأَصلِحُواْ بَينَ أَخَوَيكُم وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُم تُرحَمُونَ١٠﴾ الحجرات: ٩ - ١٠

 Kuma idan qungiyoyi biyu na musulmi suka yi faxa, to, ku yi sulhu a tsakaninsu. Sai idan xayarsu ta yi zalunci akan xaya, sai ku yaqi wadda ta yi zalunci har ta koma zuwa ga hukuncin Allah. Idan ta dawo, to, ku yi sulhu a tsakaninsu da adalci. Kuma ku daidaita. Haqiqa Allah na son masu daidaitawa. Haqiqa su dai musulmi ‘yan’uwan juna ne. To, ku yi sulhu tsakanin ’yan’uwanku. Al-Hujura’at: 9-10.

Ka ga duk da cewa sun yi yaqi da juna, amma sunan ‘yan’uwantaka na nan a tsakaninsu. To, idan wannan hukunci ya tabbata ga waxanda ba su kai waxannan zama muminai ba, to, babu shakka ya fi cancantar ya kasance ga manyan Sahabbai.

Sai cewar da xan Shi’ar ya yi, wai duk musulmi sun haxu a kan kashe Usman Raliyallahu Anhu. Wannan na cikin bayyanar qarya. Don mafi yawan musulmi ba su yi umurni da kisansa ba, ba su kuma yarda da kisan ba. Kai da yawan musulmi ba su ma zaune a Madina lokacin da abin ya faru. Musulmi kowa na garinsa. Mutanen Madinar ma wasu duk sun tafi aikin hajji.

 Sannan duk mafifitan musulmi ba su shiga cikin waxanda suka wannan xanyen aiki na kashe Usmanu ba, ba su kuma yi umurni da shi ba. Waxanda suka kashe shi wasu ‘yan tsiraru ne mavarnata kuma qasqantattun daga wasu qabilu masu son fitina. Ali Raliyallahu Anhu ya kan ce a kowane lokaci yana mai rantsuwa cewa, shi bai kashe Usmanu ba, kuma ba shi da hannu cikin kisansa. Kuma yana cewa: “Allah ya la’ani duk wanda ke da hannu a cikin kisan Usman, a tudu da rafi duk inda su ke.

Wanda ba shi kusa a lokacin da abin ya faru na iya cewa, me ya sa su Alin ba su taimaka masa ba kamar yadda ya kamata? Amsa ita ce, su dai Sahabbai da su ke a Madina a lokacin irin shi kansa Ali ba su yi zaton cewa zai yiyuwa ‘yan ta’addar su aikata haka ba. Da sun sani kuwa da sun toshe duk wata hanyar da za ta kai ga yin haka, kuma su gama da su.

Kuma ku ‘yan-sha-biyu kun san cewa, haxuwar da mutane suka yi a kan yi wa Usmanu mubaya’a ta fi wadda aka yi a kan kashe shi. To, in har kun yarda da kafa hujja a kan haxuwar mutane ga yin wani abu, to, me yasa ba ku kafa hujja da haxuwarsu akan naxa shi, ku amince tun farko da naxinsa? Ku ne fa kuke cewa, waxanda suka yi ma sa mubaya’a tsorata su aka yi, suka yi ta a kan tilast. Ka ga da an so a yi irin wannan magana ta ku a wajen maganar kashe shi ta fi karvuwa. Don kuwa kowa zai iya yarda in aka ce, Sahabbai sun ji tsoron ‘yan fitina ne shi ya sa suka qyale su, fiye da yardar da zai yi akan cewa, tsoro ya sa aka naxa Usman tun da farko. Ina mai ba da tsoron? Wa kuma ake tsoratarwar? Akan me za a tsorata shi?

 Wannan duk bisa ga qaddara cewar da suka yi wai duk musulmi sun yarda a kashe shi. Ballantana mafi yawan musulmi ba su yarda da yin hakan ba. Kuma ba su ma so faruwar hakan ba. Daga cikinsu ma har akwai waxanda suka kare shi a gidansa kamar Hasan da Husaini ‘ya’yan Ali da Abdullahi xan Zubair da sauransu .

 In da wani zai yi irin wannan qarya ya ce, duk musulmi sun haxu a kan kashe Husaini, me ‘yan Shi’ah za su ce ma sa? Alhalin mafi yawan musulmi sun tashi tsaye don ramuwa a kan waxanda suka kashe shi Usman yadda ba su tashi tsaye wajen ramuwa a kan waxanda suka kashe Husaini ba. Wannan qaryar ta fi sauqin karvuwa ga hankali a kan ta ‘ya Shi’ah cewa wai, duk musulmi sun haxu a kan cewa a kashe Usman.

Kowa ya san cewa, ramuwar da mataimakan Husaini suka yi a kan maqiyansa ba ta kai wadda mataimakan Usmanu suka yi ba akan maqiyansa. Kuma fitina da sharri da varna da suka auku bayan kisan da aka yi wa Usmanu Raliyallahu Anhu sun fi girma nesa ba kusa ba a kan waxanda suka faru a dalilin kisan Husaini. Kuma kisan Usmanu ya fi girman zunubi a wurin Allah da Manzonsa da muminai a kan kisan Husaini. Don Usmanu yana cikin magabatan farko na muhajirai, irin su Ali da Xalhatu da Zubairu. Kuma ga shi, shi ne halifan musulmi wanda suka haxu a kan naxinsa. Kuma tsawon zamanin halifancinsa na shekaru 12 bai tava kashe kowa ba. Bai tava zare takobinsa don tsorata da wani musulmi ko kashe shi ba. Takobinsa a wancan lokaci ya yi amfani ne kawai wajen yaqar arna da isar da saqon musulunci, kamar yadda aka yi a zamanin halifancin Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma .

Sai cewar da ya yi wai, Nana A’ishah ta yi ta kira ga a kashe Usmanu, tana cewa ku kashe mugun tsoho, Allah ya kashe mugun tsoho. Kuma wai tayi murnar kashe shi. Da za a bar shi ya yi shekarun Abarshi yana neman madogarar wannan magana ba zai samu ba. Gaskiyar magana ita ce, Nana A’isah kamar sauran ‘ya’yanta muminai ba ta yarda da kisansa ba, kuma ta zargi waxanda suka kashe shi, har ma ta yi mummunar addu’a a kan qanenta Muhammad xan Abubakar da duk waxanda ke da hannu a cikin kisan.

 Idan ma za mu qaddara cewa, xaya daga cikin Sahabbai Aisha ko wani ya ce haka a kan fushi don inkarin wani abin da ya kamata ayi inkarin sa, to maganarsa a nan ba ta zama hujja, ba ta kuma zama suka ga imanin wanda ya yi ta ko wanda aka wa ita. Domin dukkansu waliyyan Allah ne, ‘yan aljanna. Koda kuwa xayansu ya zaci halaccin kashe xaya, ko ma ya zaci cewa ya kafirta. Ba abin da zai hana ya zamo mai kuskure ga wannan zato, kuma kowannensu na nan a matsayin xan aljanna.

 Ita dai magana duk wanda zai yi ta, wajibi ne ya yi ta akan ilimi da adalci, musamman in ta shafi mutuncin wani mutum musulmi kowane iri ne. Ba daidai ba ne a yi ta a kan jahilci da zalunci, kamar yadda ‘yan bidi’a ke yi a ko’ina. Dubi yadda ‘yan-sha-biyu ke bijirowa da mutane masu kusanci da juna ta fuskar girma da xaukaka, da zamansu waliyyan Allah, amma sai su raba su; wasu su ce ma’asumai ne da ko rafkanwa xayansu ba ya yi. Sauran kuma su ce masu fajirai ko fasiqai ko kafirai. Kai tsaye kana iya gane jahilcinsu da taqin saqar maganarsu. Kamar Bayahude ne ko Kirista, duk sadda xayansu ya buqaci tabbatar da annabcin Musa ko Isah Alahimas Salam, tare da yin suka ga annabcin Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama, ba zai iya ba, don nan take jahilcinsa da taqin saqar maganarsa zasu fito fili.

Sai maganar da ya yi cewa, Nana A’ishah ta tambayi wanda aka naxa, aka ce mata Ali, sai ta fito tana yaqarsa a kan neman fansar jinin Usmanu. Kuma ya qara da tambaya wai, wane laifi ne ga Ali Raliyallahu Anhu game da wannan?

 Sai mu ce masa, duk wanda ya ce Aishah da Xalhatu da Zubairu sun yaqi sayyidina Ali a kan suna tuhumar sa da kashe Usmanu Raliyallahu Anhu ya yi ma su qarya. Sun dai nemi Ali ya hannunta ma su waxanda suka kashe Usmanu, kuma wasunsu na nan saqe cikin rundunarsa. Amma sun fi kowa masaniya game da barrantar Ali daga jinin Usmanu kamar yadda suka san su ba su da hannu a ciki. Amma kowannensu; da su, da Alin ba wanda yake da haqiqanin iko a kan yin haka a wancan lokaci. Ita kuma fitina idan ta auku to, masu hankali na kasa shawo kanta. Sai ya kasance manya Sahabbai suka kasa kashe wutar wannan fitina da kange wawaye daga yin varna. Wannan ko shi ne sha’anin fitina duk inda ta kunna kai. Shi ya sa Allah mabuwayi ya ce:

﴿وَٱتَّقُواْ فِتنَة لَّا تُصِيبَنَّ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنكُم خَاصَّة وَٱعلَمُواْ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلعِقَابِ٢٥﴾ الأنفال: ٢٥

Ku ji tsoron fitina da ba za ta kevanta da waxanda suka yi zalunci cikinku kawai ba. Al-Anfal: l25.

Don haka, idan fitina ta auku ba mai tsira daga dauxarta sai fa wanda Allah ya tsare.

Amma cewar da ya yi, menene laifin Ali Raliyallahu Anhu ga kisan Usman? Duk ya warware abin da ya yi can baya. Ba da farko ya ce Ali Raliyallahu Anhu na cikin waxanda ke halatta yaqar Usmanu ba har da kashe shi? Da yawa cikin mabiyan Ali da na Usman na da ra’ayin cewa, Ali na da hannu cikin wannan juyin mulki da ya kai ga kashe Usman. Waxannan sun ce Ali na da hannu don ba su son Usman. Suna son su ce ko Ali ma ba ya sonsa. Waxancan su kuma sun ce Ali na da hannu don ba su son Alin. Suna son su shafa masa kashin kaji. Amma mafi yawan musulmi sun san qarya vangaroran biyu ke yi.

Wannan fa shi ne rikicin. ‘yan Shi’ah na ganin cewa, Ali Raliyallahu Anhu ya halasta kisan Usman, kai har ma da Abubakar da Umar. Kuma wai, wannan na cikin abubuwan da ake neman kunsanci ga Allah da yin su. To, sai ga wannan shi ko yana cewa, mene ne laifin Ali Raliyallahu Anhu a cikin wannan kisan? Ka ga babu wanda ya ke tsarkake Ali bisa adalci sai Ahlus-Sunnah.

Ka tuna kuma ya ce: “Ya aka yi Xalhatu da Zubairu suka halatta wa kansu yi mata xa’a a kan wannan? Da wace irin fuska za su sadu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Ga shi kuwa da xayanmu ya yi magana da matar wani, ya fitar da ita daga gidanta, ya yi tafiya tare da ita, da ya zama mafi girman maqiyinmu”.

Wannan shi yake daxa bayyana jahilicin ‘yan Shi’ah da takin saqarsu. Su ne fa suke jifar Nana A’ishah da mafi munin abu a duniya ga ‘ya mace, bayan Allah ya tsarkake ta. Amma su faxi wannan magana, wai magana da matar wani ma laifi ce! To, ce ma ta karuwa fa? Qazafinsu kuma bai tsaya ga matar iyalin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ba, a’a, har da matan wasu daga cikin Annabawa. Kamar yadda suka ce matar Annabi Nuhu Alaihis Salamu mazinaciya ce, kuma wai, xanta da Annabi Nuhu ya kirazuwa shiga jirgin tsira bai karva ba, wai ba xansa ne ba, ta hanyar zina ta same shi. Sai suna karkatar da ayoyin Alqur’ani don su qarfafa son ransu, su samu mashiga ta yin suka ga iyayen muminai. Hakanan ita ma matar Annabi Ludu Alaihis Salamu ba ta tsira daga mugun bakinsu ba. Sun yi mata qazafi suna kafa hujja da ayar da ta ce, matar Nuhu da ta Luxu sun yaudare shi (Suratut-Tahrim:10). To, waxannan ne za su ce wani ya fita da matar Annabi kuma ya yi laifi?

 ‘Yan-sha-biyu dai sun yi kama da Munafukai da Fasiqai waxanda su ka jefi uwar muminai da alfasha, kuma ba su tuba ba. A kan irin su ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi huxuba yana cewa: “Wane ne zai yi mani uzuri ga mutumin da ya kai matuqa wajen cutarwa ga iyalina? Wallahi ban san wani abu game da iyalina ba sai alheri. Wanda kuma suka tuhumce da shi mutun ne da, wallahi ban san wani abu game da shi ba sai alheri”.

 Ga al’ada duk mutumin da aka ce ma mijin mazinaciya an gama kai maqura ga cutata ma sa. Wannan kuwa shi ne abin da ‘yan-sha-biyu ke yi wa Annabawa. Wal’iyazu billahi.

 Babu wani zargin da aka sa wa haddi sai qazafin zina. Don babu wani zargi da ya kai shi haxari. Kai ko kafirci aka zargi mutum da yi, yana iya qaryatawa ta hanyar bayyanar da ayyukan musulunci. Amma ita zina ya za a iya qaryata ta?

 Sannan daga cikin jahilcin ‘yan-sha-biyu suna girmama nasabar Annabawa amma suna sukar matansu. Suna wannan ne don kawai tsananin ta‘assubanci da son rai, wai suna son girmama Fatima da Hasan da Husaini. Amma sai su soki A’isha Uwar Muminai. Don haka suke cewa Azara mahaifin Annabi Ibrahim mumini ne. Haka su ma mahaifan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wai suna gudun in aka ce wani Annabi mahaifansa na iya zama kafirai, wani ya kafa masu hujja da cewa, ko ‘ya’yansa na iya zama kafirai. To, ka ji kai.

 Shi dai Xalhatu ko Zubairu ko ma duk wani bare (ajanabi) ba su xauki uwar muminai ba. Don a cikin sansaninsu akwai muharramanta kamar Abdullahi xan Zubairu; xan yarta, wanda shari’a ta yarda ya kaxaita da ita bisa ga nassin Alqur’ani da Sunnah da ijimain malamai. Haka ma tafiyar mace tare da muharramanta halal ne kamar yadda ya ke sanannen abu a shari’ah. Ko a sansanin Ali xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu ba don qaninta Muhammad Xan Abubakar ya miqa hannunsa ya fito da ita ba, ai da an sami wani da ba muharrami ba ya yi hakan. Wannan ne ya sa Nana A’ishah ta yi masa mummunar addu’a da ya miqa hannunsa gare ta kafin ta gane shi. Ta ce: “Wannan hannun wa ne? Allah ya qona shi”. Nan take sai qanenta ya ce: “A nan duniya ba a lahira ba”. Da ta ji muryarsa sai ta ce: “A nan duniya ba a lahira ba”. Haka kuwa aka yi, don an qona shi a Masar.

Game da maganarsa a kan goyon bayan da mutane suka ba A’ishah kuma wai, ba su taimaki Fatima a rikicinta da Abubakar ba, a cewarsa. Sai mu ce masa, ganwo ya jirkice ma dame kenan. Domin duk mai hankali ba ya shakkar cewa, Sahabbai na tsananin son Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma girmama shi. Suna kuma ganin girman dangin Manzon Allah da ‘ya’yansa fiye da yadda suke ganin girman Abubakar da Umar. Kuma babu shakka sun fi son Manzon Sallallahu Alaihi Wasallama a kan kawunansu da iyalansu. Ba mai hankalin da ka shekkar cewa, dukkan Larabawa na biyayya ga ‘yan gidan Abdumanafi, dangin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama suna girmama su fiye da yadda suke girmama Tamimawa da Adiyawa waxanda Abubakar da Umar suka fito daga cikinsu. Don haka ne lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu aka ce wa Abu Quhafata, mahaifin sayyidina Abubakar: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu. Sai ya ce: “Babban abu ya auku. To, wa ya maye gurbinsa?” Aka ce masa: “Abubakar”. Ya ce: “‘Yan gidan Abdumanafi da Makhzumawa duk sun yarda?” Aka ce masa: “Qwarai kuwa”. Sai ya ce: “Wannan falalar Allah ce, da yake bada ita ga wanda ya so”.

 Wannan ne ya sa lokacin da Abu sufyana ya zo wurin Ali ya ce masa: Kun kuwa yarda cewa shugabanci ya zamo cikin Tamimawa (qabilar su Abubakar)? Sai ya ce masa: Ya Abu sufyan! Lamarin musulunci ba irin na jahiliyyah ne ba.

 To tunda yake ba’a samu wanda ya ce an zalunci Fatima ba daga cikin Sahabbai, ko ya ce tana da wani haqqi wurin Abubakar ko Umar da suka hana ma ta, ko ya ce su biyun azzalumai ne. Wannan ya nuna cewa musulmi basu xauki al’amarin a haka ba. Da ba abin da zai hana su su taimake ta.

To, yaya mutanen da suka tashi tsaye wajen fansar jinin Usmanu Raliyallahu Anhu har suka zubar da jinainansu sakamajon wannan za ace ba za su taimakawa wanda ya fi soyuwa gare su akan Usmanu ba, ina nufin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da iyalan gidansa?

 2.9.12 Suna Jin Haushin a Kira ta “Uwar Muminai”

Xan Shi’ar ya ce: Sun kira ta “Uwar Muminai”, amma ba su kira sauran matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da wannan sunan ba. Ba su kira qanenta Muhammad xan Abubakar “Kawun muminai” ba duk da xaukakarsa da ta babansa da kusancinsa ga ita A’ishar. Sai suka kira Mu’awiyah da wannan suna don kasancewarsa xan’uwan Ummu Habiba xiyar Abu Sufyana, ga shi ko Muhammad xan Abubakar da babansa sun fi xaukaka akan Mu’awiyah da ‘yar’uwarsa.

Martani:

 Babu qanshin gaskiya sam a cikin maganar cewa, A’ishah kaxai Ahlus-Sunnah ke kira “Uwar Muminai” ba da sauran matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Ni ban sani ba, wannan mutum da ire-irensa da gangan suke qira qarya ko dai Allah ne ya taushe basirarsu don tsananin bin son zuciya ta yaddaba su iya gane qarya idan sun faxe ta? Wannan ya zan kamar yadda suke zargin wasu maqiyan Ali da cewa, sun musanta Husaini jikan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne a lokacin da za su kashe shi. Ya ko za ayi wani ya musanta nasabar Husaini in ba wanda Allah ya taushe wa basira don bin son zuciyarsa ba?

 To, su ‘yan-sha-biyu sun fi kowa inkarin gaskiya da gangan kuma sun fi kowa makanta. Ka ga a cikinsu akwai Nusairiyyah masu cewa Hasan da Husaini ba xiyan Ali ba ne, xiyan Salmanul-Farisi ne. Akwai daga cikinsu masu cewa Ali bai mutu ba. Akwai kuma masu cewa Abubakar da Umar ba su kwance tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin xakin A’ishah. Cikinsu kuma akwai masu cewa Ruqayyah da Ummu Kulthum ba xiyan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne ba, don kawai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya aurar da su ga sayyidina Usmanu Raliyallahu Anhu. Suka ce ‘ya’yan wani mushriki ne da Nana Khadija ta haifa ma sa kafin ta auri Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Banbance min jahilcin waxannan mutane da jahilcin wasu daga cikin waxanda suka kashe Husaini Raliyallahu Anhu waxanda suka ce sam, ba su yarda Husaini jikan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne ba.

 Musulmi dai a duk in suke sun san cewa, kowacce daga cikin matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ana kiran ta “Uwar Muminai”. Kuma wannan magana nassin Alqur’ani ce. Kamar yadda Allah Ta’ala ya ce: Annabi ya fi cancantar gabaci ga muminai a kan kawunansu. Kuma matansa iyayen muminai ne. Suratul Ahzab:6. Wannan sanannen abu ne. Saninsa bai kevanta da malamai ba. Kuma musulmi sun haxu a kan cewa, haram ne wani musulmi ya auri xaya daga cikin matan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya aura. Haka kuma girmama su wajibi ne. Suna da alfarmar girmamawa da haramci, amma ba ya halatta wani musulmi ya kaxaita da su kamar yadda yake kaxaita da uwar cikinsa. Duk da yake hukuncisu hukuncin uwaye mata ne, amma kuma suna da banbanci ta wannan fuska. Don haka ne malamai ke savani game da kiran iyayensu kakannin muminai ko ‘yan’uwansu kawunnan muminai. Wasu malamai suka ce ana iya kiran su haka. Kuma wannan hukunci bai kevanta da Mu’awiyah ba, a’a, ya haxa da Abdurrahaman da Muhammad ‘yan’uwan A’ishah da Ubaidullahi da Asimu da Abdullahi ‘yan’uwan Hafsatu da Amru xan Haris ‘xan’uwan Juwairiyah da Utbatu xan Abu sufyana xan’uwan ita Ummu Habiba da Muawiyah.

 Ra’ayi na biyu na malamai shi ne na masu ganin ba a iya kiran ‘yan’uwan matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama maza ko mata da sunan kawunne ko innonan muminai, don rashin tabbatuwar haramcin aure a tsakaninsu da miminai. Nassi da haxuwar kan malamai sun nuna cewa, ana iya auren ‘yan’uwansu kamar yadda Abbas ya auri Ummul-Fadhli ‘yar’uwar Maimunatu ‘yar Harisu har ta haifa masa Abdullahi da Falalu. Abdullahi xan Umar da Ubaidullahi da Mu’awiyah da Abdurrahaman xan Abubakar da qaninsa Muhammad duk sun auri mata muminai. Da kuwa kawunnensu ne na nasaba da ba su aure su ba.

Waxanda ma suka ce masu kawunnen muminai daga cikin malamai ba jayayya suke akan wannan hukunci ba. suna dai nufin sun samu darajar surukuta da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Amma wannan ya fi shahara game da sayyidina Mu’awiyah, kamar yadda ya fi shahara da zama Katibul Wahyi, marubucin wahayi, duk da yake ba shi kaxai ya rubuta wahayi ba. Kuma Mu’awiyahn dai ne ya yi suna da Radifu Rasulillah, abokin hawan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, alhalin ba shi kaxai ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hau dabba tare da shi ba. Duk waxannan abubuwa ba a faxe su ga Mu’awiyah don ya kevanta da su ba kamar yadda muka gani.

Sai cewa, Ahlus-Sunnah sun xaukaka darajarsa. Idan yana nufin darajarsa ta gida sai mu ce, ai wannan darajar ba ta da wani matsayi a gurinku. Don ga shi kuna sukar babansa da ‘yar’uwarsa matar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Su kam Ahlus-Sunnah ba su fifita kowa don kawai matsayin gidansu, sai dai don tsoron Allansa. Kamar yadda maxaukakin sarki ya ce:

﴿ إِنَّ أَكرَمَكُم عِندَ ٱللَّهِ أَتقَىكُم ﴾ الحجرات: ١٣

Haqiqa mafi xaukakarku shi ne mafi tsoron Allanku. Suratul Hujurat:13.

In kuma yana nufin Ahlus-Sunnah na girmama Mu’awiyah ta fuskar gabaci da hijira da taimakon Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da jihadi saboda Allah, to, ba su ce yana cikin magabatan farko ba. In kuma ma ta fuskar ilimi ne da riqon addini, Ahlus-Sunnah ba su ce ya fi kowa ba. To, ina laifin an faxi gaskiya ga mutum don kuna qin sa?

 Kuma wai, inji shi, ‘yar’uwar Muhammad da babansa sun fi na Mu’awiyah. To, a wurin wa suka fi na Mu’awiyah? Su Ahlus-Sunnah, a wurinsu dangantaka ita kaxai ba ta fifita mutum, balle a ce ‘ya’uwantakar Muhammad ga A’ishah ta fifita shi. Kuma Mu’awiyah ba zai cuta wa Muhammad don ya fi shi asaba, kamar yadda magabatan farko irin su Bilalu da Ammar da Suhaibu da Khabbabu da ire-irensu ba su cutu da ‘yan girma irin su Abu Sufyana da suka fi su asaba ba, tun da su sun makara ga shiga musulunci a kansu. Haka sauran waxanda suka shiga musulunci daga baya irin su Abu Sufyana xan Harisu da Aqilu xan Abu Xalib da Mu’awiyah da Yazidu, ‘yan manyan gidaje ne, amma nasabarsu ba ta fifita su a kan su Bilal xin ba.

 2.9.13 Sukar ‘Yan Shi’ah ga Mu’awiyah

 Xan Shi’ar ya ce: Tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya la’anci Muawiyah, ‘yantacce xan ‘yantacce, la’antacce xan la’antacce. Ya kuma ce: Idan kuka ga Mu’awiyah a kan minbarina, to, ku kashe shi. Ya kuma kasance cikin waxanda ake tausasa zukatansu. Ga shi kuma ya yaqi Ali wanda ko a wurin Ahlus-Sunnah shi ne halifa na huxu. Kuma shugaba ne na gaskiya. Wanda duk ya yaqi shugaba na gaskiya kuwa ya zama mai tsallake iyaka, azzalumi.

Xan Shi’ar kuma sai ya alaqanta wannan ga wai, son da Muhammad xan Abubakar ke yi wa Ali Raliyallahu Anhu da kuma cewa shi ya rabu da ubansa Abubakar Raliyallahu Anhu kuma wai, da kasancewar Mu’awiyah Raliyallahu Anhu na qin Ali Raliyallahu Anhu. Ya ce kuma, sun kira shi mai rubuta wahayi, ga shi bai rubuta ko kalma xaya ba ta wahayi. Wasiqu ne kawai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa shi ya rubuta. Kuma wai mutane goma sha huxu sun rubuta wahayi a gaban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Na farkonsu, inji shi, kuma mafi kusancinsu da Manzon Allah da kevantuwa da shi, shi ne Ali xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu. Ya ce: Ga shi kuwa Mu’awiyah bai gushe mushriki ba tsawon lokacin da aka aiko Manzon Allah xin; yana qaryata wahayi yana izgili da shariah.

Martani:

 Cewa wai, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya la’ani Mu’awiyah kuma ya ce a kashe shi idan a gan shi a kan mimbari. Wannan magana ba a iya samun ta a cikin littafan musulunci da ake dogara a kansu, kuma ma dai qarya ce zunzurutunta. Xan Shi’ar da ya riwaito ta kuma bai ambata mata isnadi ba balle a bincike shi. Abul Faraj Ibnul Jauzi ya ambace shi cikin hadissan qarya da aka jingina ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Daga cikin abin da ke tabbatar da qaryar wannan labari shi ne cewa, akwai mutane da dama da suka hau minbarinsa waxanda kuma Mu’awiyah ya fi su daraja bisa ga ijima’in musulmi. To, idan kisansa ya wajaba don kawai ya hau minbari, kenan wajibi ne a kashe duk waxancan. In kuma ya wajaba ne don ya yi shugabancin da bai cancanta ba, to wajibi ne a kashe duk waxanda shi Mu’awiyahn ya fiya, cikin waxanda suka zo bayansa. Wannan kuwa ya sava wa abin da hadissan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama suka tabbatar na hani ga kisan shugabanni. In da za ayi haka da zai zama sanadiyyar varna da yawaita kisann musulmi, sai an gwammace shugabancin azzaluman a kan wannan varna. To, ya ko za a yi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi umurni da abin da sharrinsa ya fi alherinsa?.

Xan Shi’ar dai zato ya ke ya aibata Mu’awiyah ne da ya ce masa “’Yantacce xan ‘yantacce”. Alhali wannan ba aibi ba ne, don waxanda aka ‘yanta su ne waxanda suka shiga musulunci ranar da aka buxa garin Makka, waxanda adadinsu ya kai dubu biyar. Daga cikinsu kuwa akwai waxanda Allah ya xaukaka su har suka zama cikin mafifitan musulmi kamar Harisu xan Hishamu da Suhailu xan Amru da Safwanu xan Umayyata da Ikrimatu xan Abu Jahali da Yazidu xan Abu Sufyana xan Harisu, xan baffan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wanda a da yake izgili da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana yi masa zambo, sai daga baya ya musulunta, kuma ya kyautata musuluncin nasa. Haka ma Attabu xan Usaidu wanda Manzon Allah ya naxa shi gwamnan Makka na farko a musulunci. Duk waxannan da ire-irensu ‘yantattu ne. To, ina aibi kenan ga zama ‘yantacce?

Mu’awiyah xan Abu Sufyana yana cikin waxanda suka kyautata musuluncinsu. Wannan ne ya sa Umar Raliyallahu Anhu ya naxa shi kwamandan Jihadi a qasar Sham bayan rasuwar xan’uwansa Yazidu. Yazidun nan kuwa na daga cikin mafifitan musulmi waxanda Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma suka naxa a muqamai masu alaqa da yaqar kafirai, musamman a qasar Sham. Waxannan shugabanni su ne: Yazidu xan Abu Sufyana da Shuraihu xan Hassan da Amru xan Asi da Abu Ubaidata da Khalidu xan Walidu. A lokacin da Yazidu xan Abu Sufyana ya rasu sai Umar ya ba Mu’awiyah shugabancin Sham. Umar Raliyallahu Anhu kuma bai ji tsoron wani zargi ba. Kamar yadda ba a zargin sa da son rai wajen zaven shugabani. Ba ya kuma cikin masoyan Abu Sufyana. Abin da ma za a iya cewa shi ne, Umar na cikin waxanda suka fi kowa qin baban Mu’awiyah, wato Abu Sufyana kafin ya musulunta. Har ma lokacin da Abbas, baffan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kawo Abu Sufyana ranar buxa garin Makka, Umar ya yi kwaxayin kashe shi, sai da magana ta tsananta tsakaninsa da Abbas xin don qin da yake yi wa Abu Sufyana. Ka ga kuwa da Umar bai san ya cancanci shugabanci ba da bai shugabantar da shi ba. Don ba wani abin duniya da yake nema a wurinsa.

 Sai cewar da ya yi Mu’awiyah na cikin waxanda ake kyautatawa don kwaxaita masu shiga musulunci. Haka ne. Kuma mafi yawan waxanda aka ‘yantar kamarsa, su ma haka suka kasance. Daga cikinsu kuwa akwai mafifitan musulmi kamar Harisu xan Hisahamu da Ikrimatu xan Abu Jahali da Suhailu xan Amru da Safwan xan Umayyata da Hakimu xan Hizamu. Waxannan babu shakka suna cikin zavavvun musulmi. Kuma mafi yawan waxanda aka kyautata ma don kwaxaitar da su, sun yi kwaxayin musuluncin, sun kyautata shi ta yadda xayansu ya kasance yana shiga musulunci da safe don xan wani abu na duniya, amma kafin marece musulunci ya zame ma sa mafi soyuwar a duniya.

 Yaqar Ali kuwa da ma duk wani shugaba na gaskiya tana iya kasancewa bisa ga tawili, ko bisa ga son zuciya, ko haxuwar abu biyun baki xaya, wanda shi ne ya fi yawan faruwa. To, kowanne ne ya kasance ba zai zama suka ga fahimtar Ahlus-Sunnah ba, don ba su tsarkake Mu’awiyah ba balle wani wanda ya fi shi daga aikata savo ko kuskuren ijtihadi. Abin da suka ce shi ne, savo akwai abin da ke shafe shi, kamar tuba da istigfari da ayyukan alheri da musibun da ke zama kaffara ga mutum da sauransu. Wannan kuma ya haxa da Sahabbai da waxanda ba su ba.

Abu na biyu kuma shi ne: Ahlus-Sunnah suna kan turba guda xaya ne a nan. Amma ku a cikin takin saqa kuke. Domin kuwa maqiyan Ali Raliyallahu Anhu masu kafirta shi da masu fasiqantar da shi, Harijawa da Mu’utazilawa da Marwaniyyawa da ire-irensu masu shakka ga addininsa, in da za su ce maku: Minene hujjar da ke tabatar da imanin Ali Raliyallahu Anhu da shugabancinsa da adalcinsa? Ba ku da abin da za ku ce sai an samu labari mutawatiri mai nuna cewa ya musulunta. Nan take sai su ce maku, ai wannan ko sauran Sahabbai da Tabi’i da Umawiyyawa da Yazidu da Abdulmalik xan Marwan da sauransu duk an samu labari mutawatiri a kan musuluntarsu, amma kun kafirta su. To, me ya banbanta su da Ali? Ku kun kafirta su, mu mun kafirta shi. Sukar da ku ke yi game da imanin waxancan ta fi sukar da muke yi ga imanin Ali, don waxanda kuke suka sun fi waxanda muke suka yawa.

 Idan kuma kuka kafa hujja da yabon da aka yi a cikin Alqur’ani, sai su ce ma ku, ayoyin Alqur’ani ba kan Ali xai suka sauka ba. Sun game muminai a lokacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kenan sun haxa da Abubakar da Umar da Usmanu da sauransu. Kamar yadda ayoyin suka haxa da Ali. To, ga shi kun kafirta sauran Sahabbai kun bar shi daga cikin waxanda Allah Ta’ala ya yaba duk da yawansu. To, mu ma mun fitar da Ali Raliyallahu Anhu daga cikinsu shi kaxai mun bar saura. Haka Hawarijawa za su ce muku.

 In kuwa kuka ce za ku kafa hujja da abin da aka riwaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama game da falalolinsa, sai su ce maku, waxannan falalolin ai Sahabbai ne suka riwaito su kamar yadda suka riwaito sauran falalolin Abubakar da Umar da Usman. In kun yarda da adalcinsu da gaskiyarsu, to, ku karvi duk abin da suka riwaito mana. In kuma ba ku yarda da su ba to, duk hadissan falalar Ali sun zama wofi kenan.

 Sai cewar da ya yi wai, don Muhammad xan Abubakar na son Ali ne da kuma rabuwar da ya yi da babansa, shi ya sa Ahlus-Sunnah suke qinsa da fifita Mu’awiyah a kansa. Wannan qarya a fili ta ke. Don Muhammad xan Abubakar bai ko san rayuwar babansa ba, don bai ma shekara uku ba a lokacin mutuwarsa. Da ya girma kuma yana cikin masu darajanta mahaifin nasa don da bazarsa yake rawa.

Sai cewar da xan Shi’ar ya yi, wai, an ce wa Mu’awiyah kawun muminai ba a ce wa Muhammad ba don yana son Ali Raliyallahu Anhu alhalin shi Mu’awiyah Raliyallahu Anhu yana qin sa. Wannan ma qarya ce. Don Abdullahi xan Umar duk ya fi su cancantar a ce masa hakan, ga shi kuwa bai taimaki Mu’awiyah ko Ali a wurin yaqi ba. Ya kasance yana girmama Ali Raliyallahu Anhu yana faxin darajojinsa, yana kuma son sa. Ya kuma yi wa Mu’awiyah mubaya’a a lokacin da mutane suka haxu a kansa. ‘Yar’uwarsa Hafsa kuma ta fi ‘yar’uwar Mu’awiyah, haka ma mahaifinsa Umar ya fi na Mu’awiyah. Kuma mutane sun fi son sa da xaukaka shi a kan Mu’awiyah da Muhammad xan Abubakar, Allah ya yarda da su baki xaya. To, duk da haka shi shi xan Umar bai shahara da sunan kawun muminai ba. Saboda haka cewa an qi sa ma Muhammad xan Abubakar wannan suna don yana qin Ali zuqi ta mallau ce kawai.

Sai kuma cewar da ya yi, wai, an kira shi mai rubuta wahayi ga shi bai rubuta ko kalma xaya ta wahayi ba. Wannan magana ce maras-kai. Don ko ina dalilin cewa bai rubuta ko kalima xaya ta wahayi ba sai dai wasiqu?

 Maganar da ya yi game da yawan marubutan wahayi, da cewa sun fi goma, kuma na farkonsu, mafi kusancinsu da kevantuwa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne Ali. Babu shakka cewa, Ali Raliyallahu Anhu na cikin marubutan wahayi, kamar yadda ya rubuta yarjejeniyar da aka yi tsakanin musulmi da mushrikai a ranar Hudaibiyyah. Amma Abubakar da Umar ma na ciki. Don sun kasance suna rubuta masa wahayi su ma. Kuma babu shakka Zaidu xan Thabitu na cikinsu. Don shi ya rubuta ayar da ta ce: Waxanda suka zauna gida daga cikin muminai ba su daidaita da waxanda suka fita jihadi. An-Nisa’i:95. Haka shi ma Usmanu da Amiru xan Fuhairata da Abdullahi xan Arqamu da Ubayyu xan Ka’abu da Thabitu xan Qaisu da Khalidu xan Sa’idu xan Asi da Hanzalatu xan Rabi’u Al-Asadi da Mu’awiyah da Shurahabilu xan Hasanata, dukkansu Allah ya qara masu yarda.

 Amma cewar da ya yi wai, Mu’awiyah musiriki a duk tsawon rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Amsar maganar ita ce, kowa ya san cewa, Mu’awiyah da xan’uwansa Yazidu da babansu duk sun musulunta ne a shekarar da aka ci Makka da yaqi kafin cikawar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kusan shekaru uku. To, yaya zai masa mushriki duk tsawon rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Mu’awiyah ai qaramin yaro koda aka aiko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, don lokacin uwarsa Hindu ke tawansa. Mu’awiyah ya musulunta a shekarar da aka ci Makka tare da xan’uwansa Yazidu da Suhailu xan Amru da Safwanu xan Umayyata da Ikrimatu xan Abu Jahali da Abu Sufyana xan Harbu. Duk waxanda sun fi nuna gaba da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kafin musuluntarsu fiye da Mu’awiyah.

 2.9.14 ‘Yan Shi’ah Sun Tsani Mu’awiyah

Xan Shi’ar ya ce: Mu’awiyah ya kasance a qasar Yaman koda aka ci Makka. Yana can yana sukar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, har ma ya rubuta wa babansa Sakhru xan Harbu waqe yana aibanta shi don ya shiga musulunci yana ce masa: Ka karkace, tunda ka shiga addinin Muhammadu. Sai ya rubuta masa.

An dai buxa garin Makka ne a cikin watan azumi na shekara ta takwas bayan hijira. Mu’awiyah yana a kan kafircinsa, yan gudun Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama don ya ba da umurnin a kashe shi, inji xan Shi’ar. Sai ya gudu zuwa Makka. Amma da ya ga ba wata mafaka sai ya tafi ala tilas wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ya musulunta. Musuluntar tasa ta kasance ne watanni biyar kacal kafin rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Da zuwansa sai ya jefa kansa ga Abbas, wanda ya nema masa afuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuma ya samu. Sannan Abbas xin ya nema masa aka ba shi damar yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama rubutu don ya samu girma. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yarda ya haxa shi da sauran mutane goma sha huxu. To wane rabo ya samu a cikin wannan aiki koda mun ba shi wannan suna na marubucin wahayi a cikin wannan xan qanqanin lokaci? Tattare da cewa Zamakhshari, xaya daga cikin malaman Hanafiyyah ya ce a cikin littafansa mai suna Rabi’ul Abrar : Daga cikin masu rubuta wahayi akwai Abdullahi xan Sa’adu xan Abu Sarhi, kuma ya yi ridda ya koma mushriki. A kansa ne ma aya ta sauka cewa:

﴿ وَلَكِن مَّن شَرَحَ بِٱلكُفرِ صَدرا فَعَلَيهِم غَضَب مِّنَ ٱللَّهِ وَلَهُم عَذَابٌ عَظِيم١٠٦﴾ النحل: ١٠٦

Amma wanda ya buxe wa kafirci qirjinsa, to, fushin Allah na kansu. Kuma suna da azaba mai girma. An-Nahli:106.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Abullahi xan Umar ya ruwaito yana cewa: Na zo wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, sai na ji yana cewa: Yanzu wani mutum zai zo muku wanda ba zai mutu a kan sunnata ba. Wai, sai Mu’awiyah ya shigo masallaci. Sai kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fara huxuba, shi kuma Mu’awiyah ya riqa hannun xansa Zaidu ko Yazidu ya fita bai saurari huxubar ba. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Allah ya la’anci wanda ya ja, da wanda aka ja xin. Kaicon al’ummata a ranar da Mu’awiyah zai munana ma su.

Ya ci gaba da cewa: Mu’awiyah ya kai matuqa ga yaqar Ali, kuma ya kashe da yawa daga cikin zavavvun Sahabbai. Sannan ya la’anci Ali akan minbari. Aka kuma ci gaba da wannan zagi nasa har tsawon shekaru tamanin sai da Umaru xan Abdul’aziz ya yi sarauta sannan ya hana haka. Shi ne kuma ya kashe Hassan ta hanyar sa masa guba. Xansa Yazidu kuma ya zo ya kashe Husaini, ya qwace matarsa. Ubansa kuma shi ya karya wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama xaya daga cikin haqoransa, uwarsa kuma ta ci antar Hamza baffan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Martani:

Cewar da ya yi Mu’awiyah ya kasance a qasar Yaman yana sukar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, wai har ya zargi babansa Sakhru a kan ya musulunta. Duk wannan ba gaskiya ba ne. Don yana a Makka ne aka ci ta da yaqi. Babansa kuwa ya musulunta kafin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya shiga garin, a daidai wurin da Manzon ya sauka, in da ake kira Marruz-Zahran, a wannan daren da Annabi ya sauka. Nan ne Abbas ya ce ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama: Ka ga Abu Sufyana yana son girma. Ka yi masa wani abu kan haka. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya shiga gidan Abu Sufyana ya tsira”.

 Amma cewar da ya yi an buxe Makka a ranar takwas ga watan azumi. Wannan gaskiya ne.

 Sai cewa Mu’awiyah yana a kan kafircinsa har ma ya gudu daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba da umurnin a kashe shi, sai da ya ga ba mafaka sannan ya tafi tilas wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ya musulunta a zahiri. Kuma wai an yi haka ne watanni biyar kacal kafin rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Duk wannan zulala ce da bayyanannar qarya. Mu’awiyah kam ya musulunta ne a shekarar da aka buxe Makka. Duk masana sun haxu a kan haka. To, ina cewar da ya yi can baya: “Mu’awiyah na cikin waxanda ake rarrashi, ana basu dukiya don a kwaxaitar da su ga musulunci”? Ai duk wanda aka rarrasa an yi masa haka ne daga cikin ganimar yaqin Hunainu wadda aka samu daga Hawazinawa. In ko har Mu’awiyah ya gudu, to, ta yaya aka yi rarrashinsa? In kuma ya musulunta ne watanni biyar kafin rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama to, kenan ba a ba shi komai ba daga cikin ganimar Hunainu. Kuma duk wanda manufarsa ita ce yin imani ko don ya kare kansa, to, ba ya buqatar kyautatawa.

Daga cikin abin da ke bayyana qaryar wannan xan Shi’ar shi ne abin da ya tabbata a tarihi cewa, ba wanda ya jinkirta musulunta daga cikin Quraishawa har zuwa lokacin da ya ambata. Kuma duk malaman tarihi sun haxu akan cewa Mu’awiyah ba ya cikin waxanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya halatta jininsu a shekarar da aka buxe Makka.

Kuma tuhumar da ya yi wa Ahlus-Sunna cewa, suna siffanta Mu’awiyah da marubucin wahayi shi kaxai ba da kowa ba, ba ta da qamshin gaskiya. A cikin Ahlus-Sunnah babu wanda ya ce Mu’awiyah ya kevanta da wannan siffar shi kaxai.

Game da riddar Abdullahi xan Sa’adu xan Abu Sarhi kuwa, wannan ta faru, amma ai ya sake tuba ya dawo musulunci. Ayar da ya faxa kuma ba kansa ta sauka ba. Ta ma sauka ne a Makka lokacin da aka tilasta wa Ammaru da Bilal yin ridda; su kafita. Shi ko wannan mutum ya yi ridda ne a Madina bayan hijira, sannan ya sake tuba. Kai ko an qaddara cewa a kansa ayar ta sauka, to, amma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya karvi tubansa, da mubaya’arsa.

 Ruwayar da ya kawo daga Abdullahi xan Umar Raliyallahu Anhu kuma game da fitar Mu’awiyah daga masallaci don kar ya ji huxuba.. har zuwa qarshen maganarsa. Ba zai iya kare waxannan maganganu ba ballantana ya tabbatar da ingancinsu. Malaman hadisi kuma sun daxe da tada masu wannan qarya. Shi ya sa ba zaka same ta ba a cikin xaya daga cikin littafan hadisi da ake dubawa, balle a samu wani sannanen isnadi da ake jingina ta gare shi. Ka ga don cikar jahilcinsa sai ya jingina wannan magana ga Abdullahi xan Umar. Shi ko ya fi kowa nisantar zagin Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Ga shi kuma ya tabbata cewa, Abdullahi xan Umar Raliyallahu Anhu ya yabi Mu’awiyah, in da ya ce: “Ban ga wanda ya fi Mu’awiyah iya tafi da shugabanci ba bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama”. Sai aka ce masa: “Har da Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma?” Ya ce: “Abubakar da Umar sun fi shi, amma ban ga wanda ya fi shi iya shugabanci ba, bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama”.

 Imamu Ahmad xan Hambali ya kira Mu’awiyah “Shugaba mai haquri”. Ya ce kuma, ya kasance mai karimci da yawan kau da kai daga wautar jahilai.

 Sannan huxubobin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba guda ba ne. Ya kan yi huxuba a ranaikun Jumu’a da idi da lokacin Hajji da dai sauransu. Kuma Mu’awiyah da babansa na halarta kamar yadda sauran musulmi ke yi. Ko kana nufin a kowane lokaci Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai yi huxubar su fita suke yi su tafiyarsu ba su saurarawa? Kuma duk aka qyale su? Wannan ai ba qaramar suka ba ce ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da sauran Sahabbansa.

Cewa ya kama hannun xansa Zaidu ko Yazidu, to Mu’awiyah dai ba ya da xa mai suna Zaidu. Shi kuma Yazidu malaman tahiri sun haxu a kan cewa, an haife shi ne lokacin halifancin Usmanu xan Affana Raliyallahu Anhu. Mu’awiyah bai haifu ba sam, a lokacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Hafizi Abul fadhli Ibnu Nasir ya ce: Mu’awiyah Raliyallahu Anhu ya nemi aure a lokacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama amma bai samu ba saboda talauci. Sai zamanin Umar ya samu yi. Aka kuma haifar masa Yazidu a lokacin halifancin Usmanu xan Affana a shekara ta ashirin da bakwai bayan hijira.

 Game kuma da yaqar Ali. Babu shakka cewa, rundunonin biyu sun yi yaqi a Siffin. Mu’awiyah Raliyallahu Anhu kuwa bai so yaqin ba tun da farko. Kai ya ma fi kowa gudun yaqin. Kuma an fi shi son yinsa.

 2.9.15 Tuqa da Warwarar ‘Yan Shi’ah

Daga abin da ya gabata, za mu fahimci cewa, maganar ‘yan Shi’ah ta fi kowace magana zama maganar shirme da tuqa da warwara. Ga su suna ganin tsananin muni ga yaqar Ali Raliyallahu Anhu, amma kuma suna yabon waxanda suka kashe Usmanu Raliyallahu Anhu. A shariah kuwa zargi da zunubin waxanda suka kashe Usmanu Raliyallahu Anhu ya fi tsanani a kan wanda ya kashe Ali Raliyallahu Anhu don Usmanu Raliyallahu Anhu ya kasance halifan da duk musulmi suka haxu a kan yarda da shugabancinsa, kuma bai kashe musulmi ko daya ba. Suka kashe shi don su tilasta masa barin shugabanci. Don haka uzurinsa na son ci gaba da shugabanci ya fi uzurin Ali Raliyallahu Anhu qarfi shi da ya nemi sai an yi masa mubaya’a tun da farko. Usmanu Raliyallahu Anhu kuwa ya yi haquri har aka kashe shi bisa ga zalunci, ya yi shahada bai yi faxa don kare kansa ba. Ali Raliyallahu Anhu kuwa shi ya fara yaqar jama’ar Mu’awiyah, ba su fara yaqarsa ba, sun dai yi masa mubaya’a ne.

 Wani zai iya cewa, an kashe Usmanu Raliyallahu Anhu ne don ya aikata wasu abubuwa da ba a so. To, amma ai waxannan abubuwa ba su halatta tsige shi, ballantana kashe shi. Qorafin da mutanen Sham suka yi a kan Ali Raliyallahu Anhu wanda ya hana su yi masa mubaya’a, in aka auna su da qorafe-qorafen waxanda suka kashe Usman za a ga cewa, na mutanen Sham sun xara qarfi.

 Hadissan da ke nuna cewa, halifanci zai yi shekaru talatin kuwa, ba mashahurai ne irin shaharar da za ta sa irin mutanen Sham duk su san su ba. Hadissai ne da mutane kevantattu suka riwaito. Ka ga ai ba su ko a cikin Buhari da Muslim da ire-irensa. To, idan hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya shiga duhu ga mutum irin Abdulmalik xan Marwan, hadisin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa A’ishah: “Ba don kasancewar mutanenki (Quraishawa) suna sababbin shiga musulunci ba, da na sake gina Ka’aba, in saukar da qofarta qasa, sannan in yi mata qofofi biyu”. Abdulmalik sai da ya rosa abin da Abdullahi xan Zubairu ya gina, sannan ya ji wannan hadisi na A’ishah. Sai ya yi fatar da ya san hadisin kafin haka don ya tabbatar da abin da Abdullahi xan Zubairun ya yi. Wannan hadisin na A’ishah kuwa tabbatacce ne a cikin Buhari da Muslim; malamai sun yarda da ingancinsa. To, ka ga cewa shi wannan hadisi na tsawon lokacin halifanci ya shige wa Mu’awiyah Raliyallahu Anhu da mabiyasa duhu ya fi sauqin yiwuwa. Ga shi kuma hadisin a farkon shugabancin Ali Raliyallahu Anhu ba ya nuna Ali xin shi kansa. An dai gano wannan ne bayan rasuwarsa. Kodayake wannan hadisi ba nassi ne yankakke ba mai kevance wani halifa na musamman. Su ko mutanen Sham cewa suke yi: Idan har Ali ba zai yi mana adalci wajen hannunta mana waxanda suka kashe Usman ba, saboda wani tawili ko don kasawa, to, ba wajibi ba ne mu yi mubaya’a ga wanda zai zalunce mu, ko ya kasa taimakonmu.

 Sai cewar da xan Shi’ar ya yi: Wai Mu’awiyah ya kashe da yawa cikin fiyayyun Sahabbai. Sai mu ce masa: Waxanda aka kashe, an kashe su daga cikin vangarorin biyu. Kowane vangare kuma akwai Sahabbai a ciki. Kuma mafi yawan waxanda ke rura wutar yaqin daga cikin vangarorin ba su biyayya ga Ali ko Mu’awiyah. Ali da Mu’awiyah sun fi da yawan mayaqan neman kada a zubar da jini, amma an fi qarfin su. Daman ita don fitina idan da auku masu hikima daga cikin mutane na kasa kashe wutarta. Daga cikin masu hura wutar a vangaroran akwai irin Al-Ashtar An-Nakha’i da Hashimu xan Utbata da Abdurrahaman xan Khalid xan Walid da Abul A’awar As-Sulami da makamantansu. Waxannan na tsanantawa a kan neman fansar jinin Usmanu, waxansu na tsananin qin sa. Wasu kuma na tsananin taimaka wa Ali Raliyallahu Anhu, a lokacin da wasu ke qin sa.

 Amma abin da ya faxa game da la’antar Ali Raliyallahu Anhu, to, kowane sashe daga cikin biyun sun rinqa la’antar junansu kamar yadda suka yaqi juna. Sun kuma rinqa yin addu’oi akan juna. Kai yaqin da suka yi ma ai ya fi la’anta da harshe tsanani.

 Sannan abin mamaki game da ‘yan-sha-biyu shi ne ganin laifin an zagi Ali alhalin su, suna zagin sauran halifofi magabatansa, suna kafirta su da duk wanda ya so su. Mu’awiyah Raliyallahu Anhu kuwa da da masoyinsa ba su kafita Ali Raliyallahu Anhu ba. Harijawa ne dai su ka kafirta shi. Gara su kuwa da ‘yan-sha-biyu.

 A qashin gaskiya, zagin kowane Sahabi ba ya halatta. Ali ne ko Usmanu ko wani ba su ba. Wanda kuwa duk ya zagi Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum to, ya fi girman zunubi a kan wanda ya zagi Ali Raliyallahu Anhu koda kuwa ya aikata haka ne bisa tawili, to, tawilinsa ya fi na waxanda suka zagi Ali Raliyallahu Anhu muni.

 Maganar sanya ma Hassan guba a cikin abinci na cikin abin da wasu mutane suka ambata, amma kuma bai tabbata ba ta hanyar shedu ko iqirarin da ake la’akari da shi. Ba kuma wata riwaya yankakkiya cewa hakan ta auku. Ga shi kuma wannan na cikin abubuwan da ba a iya sani. Sanin gaibu ko sai Allah.

 Game da kisan Husaini da cewa Yazidu ya qwace masa mata. Gaskiyar magana ita ce, Yazidu bai yi umurni da kashe shi ba. Duk malaman tarihi sun haxu a kan haka. Amma shi ne ya rubuta wa Ibnu Ziyad cewa, kada ya bari Husaini ya kafa wata sabuwar gwamnati a Iraqi. Shi kuma Husaini Raliyallahu Anhu ya zaci cewa, mutanen Iraqi za su cika alqawarinsu da suka rubuta masa; su naxa shi. Sai ya aika masu da xan baffansa, muslim xan Aqilu sun ya samu tabbaci. Amma da ya san cewa, mutanen Iraqi sun yaudare shi, sun kashe Muslim, kuma sun yi mubaya’a ga Ibnu Ziyad, gwamnan Yazidu, sai Husaini Raliyallahu Anhu ya yi niyyar komawa. Amma rundunar nan azzaluma ta riske shi, ya kuma nemi su bar shi ya je wurin Yazidu ko wani wurin jihadi, ko ya koma gida, sai suka hana shi. Buqatarsu su kama shi a hannu, wulaqancin da shi kuma Husaini bai xauka ba. Da haka yaqi da su ya zame masa dole, kuma cikin haka ne suka kashe shi bisa zalunci, ya samu shahada. A lokacin da wannan labarin ya kai ga Yazidu ya nuna damuwa da jin ciwo ainun. Kuma an yi kuka a gidansa sosai. Ba a kuma tava matarsa ba, sam. A maimakon haka ya girmama iyalin Husaini, ya yi masu kyauta, ya sa aka mayar da su gida.

 Sai kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai, Abu Sufyana ne ya karye wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama xayan haqoransa, ita kuma Hindu ta cinye antar Hamza baffan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Babu shakka cewa Abu Sufyana shi ne shugaban rundunar da kawo wa musulmi hari a yaqin Uhud. Kuma a nan ne aka karya wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama xayan haqoransa. Amma babu wani masanin tarihi da ya ce Abu Sufyana ne ya yi wannan xanyen aiki. Wanda aka tabbatar ya yi shi, shi ne Utbatu xan Abu Waqqas. Ita kuma Hindu ta tauna antar Hamza Raliyallahu Anhu sai ta kasa haxiye ta, ta tofar da ita. Duk wannan ya faru kafin musuluntarsu. Kuma bayan haka sun musulunta, suka kuma kyautata musuluncinsu da su da Hindu. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance ya na karrama ita Hindun. Musulunci kuma yana shafe abin da ya gabace shi. Allah maxaukakin Sarki kuma ya ce:

﴿قُل لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ إِن يَنتَهُواْ يُغفَر لَهُم مَّا قَد سَلَفَ ﴾ الأنفال: ٣٨

Ka ce ma waxanda suka kafirta in suka bari, to, Allah zai gafarta masu abin da ya gabata. Al’Anfal:38.

 2.9.16 Khalidu Xan Walidu “Takobin Allah”

Xan Shi’ar ya ce: Sun kira Khalidu xan Walidu takobin Allah, kawai don tsaurin kai ga Amirul Muminina Ali, wanda shi ne ya cancanci wannan suna. Don shi ya kashe kafirai da takobinsa.

Martani:

 Kiran Khalid xan Walid takobin Allah ba ya nufin shi ya kevanta da wannan suna. A’a, shi dai “xaya ne daga cikin takubban Allah akan mushrikai”. Haka ya zo a cikin hadisi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne wanda ya fara kiran sa da wannan sunan kamar yadda ya tabbata a cikin Sahihul Buhari ta hanyar Anas xan Malik Raliyallahu Anhu a wajen maganar yaqin Mu’utah da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba da labarin shahadar Zaidu da Ja’afaru da Abdullahi xan Rawahata yana zubar da hawaye. Ya ce: “Har sai da wani takobi daga cikin takubban Allah ya xauki tutar, shi ne Khalid, har Allah Ta’ala ya ba su nasara”.

Cewa Ali ne ya fi shi cancantar wannan suna. Sai mu ce masa wa ya musanta wannan? Wa ya ce Ali Raliyallahu Anhu ba takobi ne daga cikin takubban Allah ba? Shi kansa wannan hadisi na nuna cewa, Allah Ta’ala yana da takubba masu yawa. Kuma ba shakka cewa, Ali Raliyallahu Anhu na cikin mafi girma waxannan takubban. Ba wani musulmi mai fifita Khalid a kan Ali, balle har a ce ya keve Khalid da wannan suna. Wanda ya yi masa wannan kirarin kuwa shi ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kansa.

 Ai shi Ali Raliyallahu Anhu ya fi Khalid Raliyallahu Anhu xaukaka nesa ba kusa ba. Ya ma fi gaban a ce xaukakarsa ita ce kawai kasancewarsa xaya daga cikin takubban Allah, don matsayin imaninsa da martabar iliminsa da fasaharsa da riqon addininsa da kasancewarsa cikin musulmi magabata shi ya fi girma a kan kasancewa xaya daga cikin takubban Allah. Takobi ya kevanta ne da wurin yaqi kawai. Ali Raliyallahu Anhu kuwa yaqi xaya ne daga cikin falalolinsa. Savanin Khalid da yake yaqin shi ne falalar da ya ya fice da ita a kan sauran mutane. Ba za a sa shi cikin musulmin farko ba, ko cikin masu yawan ilimi ko zuhudu. Don haka ake yi ma sa kirari da takobin Allah.

 Cewar da ya yi Ali ne ya kashe kafirai da takobinsa. Ai kowa ya san cewa, wasu kafirai ne ya kashe, haka ma sauran waxanda suka shahara ga yaqi daga cikin Sahabbai kamar Umar da Zubairu da Hamza da Mikdadu da Abu Xalha da Bara’u xan Malik da sauransu. Ba xaya daga cikinsu face ya kashe wasu kafirai. Bara’u xan Malik shi kaxai ya kashe kafirai xari ta hanyar fito-na-fito, banda waxanda ya yi tarayya da wasu a wurin kashe su.

 Sai kuma xan Shi’ar ya ce wai, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ma Ali: “Kai ne takobin Allah kuma mashinsa”. To, wannan hadisi ba a san shi ba a cikin littaffan hadisi sanannu. Kuma ba shi da isnadi. In ma har ya inganta a bisa qaddarawa, to, ma’anarsa mai kyau ce. Ba ya kuma nufin Ali ne kaxai takobin Allah da mashinsa.

 Sai ya ce kuma wai, Khalid bai gushe ba maqiyin Manzon Allah mai qaryata shi. Wannan kuwa gaskiya kafin ya musulunta, kamar yadda dukan Sahabbai suka kasance masu qaryata shi kafin musuluntarsu.

 Sai kuma xan Shi’ar ya ce: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya aike shi wurin qabilar Bani Huzaifa don ya karvo zakkarsu, sai ya yaudare shi, ya sava wa umurninsa, ya kashe musulmi. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tashi yana mai yin huxuba, ya yi inkarin abin da Khalid ya aikata yana mai xaga hannunsa zuwa sama har aka ga farin hamatansa, yana cewa: “Ya Allah! ina barranta zuwa gare ka daga abin da Khalid ya aikata”. Sannan ya aika Amirul Muminina Ali don ya gyara abin da vata, ya umurce shi da ya nemi yardar matanen da aka yi wa hakan.

 To, wannan labari nasa akwai jahilci da canza magana ga duk wanda ya san wani abu game da tarihin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, domin kuwa Manzo ya aike shi zuwa wurinsu ne bayan an buxe Makka don su shiga musulunci, sai suka yi amfani da kalimar da ake izgili da ita ga musulmin da suka shiga musulunci. Khalid kuwa ya qi karva masu wannan furuci. Ya ce wannan ba shi ne musulunci ba, ya kuma kashe su. Sahabban da ke tare da shi sun musanta masa, kamar su Salim na gidan su Abu Huzaifa da Abdullahi xan Umar da wasu ba su ba. To, lokacin da wannan labarin ya isa ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya xaukaka hannayensa zuwa sama ya yi wannan addu’a don kada Allah Ta’ala ya tambaye shi game da abin da khalid ya aikata na wuce iyaka. Haka Allah ya umurce shi da yi in da ya ce: Idan sun sava maka, to, ka ce: Haqiqa ni barrantacce ne daga abin da kuke aikatawa. As-Shura:216. Sannan ya aika Ali da dukiya, ya ba su rabin diyyar waxanda aka kashe, ya kum ranka masu abin da ya salwanta na dukiya har ma abin da kare ke shan ruwa cikinsa. Sannan abin da ya saura a hannunsa na dukiya ya bar masu don ya tabbata cewa kowa ya sami haqqinsa.

 Duk da wannan, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai fitar da Khalid daga shugabancin rundunar ba. Kai bai gushe ba yana shugabantar da shi da gabatar da shi saboda wannan kuskuren. Don shugaba idan ya auka cikin kuskure ko zunubi akan umurce shi ne da tuba, a kuma bar shi a kan shigabancinsa. Khalid kuma bai kasance mai yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tsaurin kai ba, mai xa’a ne. Sai dai bai kai ilimin wasu da riqon addininsu ba. Don haka hukuncin wannan lamari ya shige masa duhu.

 Wasu cewa suke yi wai, akwai qiyayya tsakaninsa da su tun a lokacin Jahiliyyah. Kuma wai, wannan shi ya sa ya kashe su.

 Amma cewar da ya yi wai an umurce shi ya nemi yardar mutanen. Ba maganar masani ba ce. Abin da ya sa aka aika shi shi ne don ya yi masu adalci, ya kuma ranka ma su abin da suka rasa, ba don kawai neman yardarsu ba.

 Haka ma cewar da ya yi Khalid ya yaudari Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sava umurninsa, kuma ya kashe musulmi. Wannan ba gaskiya ba ce. Domin Khalid bai yi gangancin sava ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba, balle ya yaudare shi. Bai kuma kashe wanda ya san cewa musulmi ne mai haramtaccen jini ba. Ya dai yi kuskure kamar yadda Usamatu xan Zaidu ya yi sadda ya kashe wanda ya yi kalmar shahada don ya yi tsammanin yaudara ce kawai yake yi. Hakanan wata runduna ta musulmi a zamaninsa Sallallahu Alaihi Wasallama ta tava irin wannan kuskuren, suka kashe wani mai kiwon tumaki da ya ce ni musulmi ne, suka tafi da tumakinsa.

 2.9.17 ‘Yan Shi’ah Suna Kariyar Murtaddai

 Xan Shi’ar ya ce: Lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya cika sai Abubakar ya aika Khalid don ya yaqi mutanen Yamamah, sai ya kashe mutum dubu da xari biyu duk da kasancewarsu suna amsa sunan musulmi. Ya yi wa Maliku xan Nuwairata kisan gila ga shi kuwa musulmi, sannan ya kwana da matarsa. Suka kira Banu Hanifata murtaddai don ba su kai wa Abubakar zakka ba, saboda rashin yardarsu da shugabancinsa. Aka halatta jinainansu da dukiyarsu da matansu har sai da Umar ya yi masa inkari.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Sun kira wanda bai ba da zakka ba murtaddi, amma ba su kira waxanda suka halatta jinin musulmi da waxanda suka yaki Amirul Muminina murtaddai ba, tare da sun ji cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa Ali Raliyallahu Anhu: “Yaqinka yaqina ne, kuma zaman lafiyarka zaman lafiyata ne”. Wanda ya yaqi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ko kafiri ne. Duk an haxu a kan haka.

Martani:

 Allahu Akbar! Sannunku magoya bayan murtaddai masu bayyana qin Allah da Manzo da addini da Qur’ani. Waxanda suka fice daga addinin musulunci suka yi watsi da shi, suka sava wa Allah da Manzonsa da muminai, suka jivinci mutanen ridda da ‘yan-a-ware. Ire-iren waxannan bayanai na tabbatar mana da cikakken qawancenku da kafirai don tsananin adawarku ga sayyidina Siddiqu; adawar da ba ta da wani dalili.

 Mutanen Yamama dai su ne qabilar Bani Hanifa, mabiyan Musailamatu sarkin qarya wanda ya raya cewa shi Annabi ne tun a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ya kuma zo Madina ya nuna musulunci a zahiri. Amma a voye sai ya ce, idan Muhammadu ya naxa ni magajinsa zan ci gaba da yin imani. Da ya koma Yamama sai ya raya cewa ya yi tarayya da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ga annabci. Ya ce kuma wai, Annabi Muhammadu ya gasgata shi a kan haka. Ya samu wani fajiri irinsa mai suna Rajjalu xan Unfuwata ya yi masa sheda a kan wannan qarya.

Haka kuma musailamu ya rubuta nasa Alqur’ani wanda yake cike da tsabar rashin kunya da shirme. A lokacin da aka karanta ma sayyidina Abubakar wannan shirmen sai ya ce: “Kaiconku! Ba ku da hankali ne? Ina wannan maganar ta ta yi kama da maganar annabta?”

 Wannan maqaryacin na Yamama har wasiq ya rubuta wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wadda ya buxe ta da cewa: “Wasiqa daga musailamatu Manzon Allah zuwa ga Muhammadu Manzon Allah. A cikinta kuma yake raya cewa ya yi tarayya da Annabi a cikin annabta. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rubuta amsa yana cewa: Daga Muhammadu Manzon Allah zuwa ga musailamu sarkin qarya. To, ka ji asalin wannan sunan da ya bi shi, Manzon Allah ne ya sa masa shi, saboda girman qaryar da ya yi wa Allah. Bayan rusuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuma sai Abubakar Raliyallahu Anhu ya aika Khalidu xan Walidu don yaqar sa, bayan da Khalid ya gama da wani annabin qarya irinsa mai suna Xulaihatul-Asadi da ya bayyana a qasar Najadu. Allah Ta’ala kuwa ya ba Khalid nasarar gamawa da duk waxannan mutanen. A can ne aka kashe fitaccen Sahabin nan Ukashetu xan Muhsinu, xaya daga cikin waxanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, za su tsallaka siraxi ba tare da sun gamu da ko wace irin wahala ba. Bayan haka ne shi wancan annabin qaryar, Xulaihatul-Asadi ya musulunta. Sai aka wuce zuwa Yamama wurin musailamu wanda kuma sojojin musulunci sun sha fama mai yawa a kansa. Kuma a can ne a ka kashe wasu baraden Sahabbai irin su Zaidu xan Khattabi, qanen Umar da Thabitu xan Qaisu da Usaidu xan Hudhairu da wasu da dama.

 A taqaice dai lamarin musailamatu da ‘yan qabilarsa Bani Hanifa da suka bi shi ba a voye yake ba. Abubakar Siddiqu Raliyallahu Anhu kuwa ya yaqe su. Wannan a tarihi ya fi zama gama-gari a kan yaqin da Ali ya yi na Raqumi da na Siffin. Don ba a tava jin wanda ya musanta faruwar hakan ba. Amma daga zaqaquran magana Ahlul-Kalami akwai waxanda suka musanta faruwar yaqin Raqumi da na Siffin. Ka ga kodayake shirme ne suke yi, amma mai cewa bai san mutanen Yamama sun bi annabin qarya; musailamatu ba, kuma cewa a kan haka aka yaqe su ai ya fi wancan zama sarkin shirme.

 Amma su ‘yan-sha-biyu don tsananin qin gaskiya da jahilcinsu sukan yi fiye da haka. Tunda yake an samu a cikinsu masu qaryata cewa Abubakar da Umar ne ke kwance kusa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, kuma wai, tun can ba su tare da shi a lokacin rayuwarsa. Da masu cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya naxa Ali a matsayin halifansa. Kai har ma daga cikinsu akwai masu cewa, Ruqayya da Zainab da Ummu-Kulthumi ba ‘ya‘yan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne ba, wai ‘ya’yan khadija ne na wani mijinta kafiri. Da masu cewa sayyidina Umar ya yi qwacen ‘yar sayyidina Ali har ta haifa masa ‘ya’yan da suka samu. Da masu cewa Sahabbai sun fasa cikin Fatima har ta zubar da abin da ke ciki, kuma wai, an rusa gidanta ya faxa a kan waxanda ke ciki. Da qarairayi ga su nan marasa makama da ko mai qaramin sani na iya warware su.

Mun dai riga mun saba da jin irin waxannan daga wurinsu. Domin su kodayaushe qoqarin suke su ga abubuwan da suka tabbata, waxanda babu shakka a cikinsu, sai su ce sam, ba su auku ba, su zo ga abubuwan da ba a tava yi ba, su yi qoqarin tabbatar da su. Shi ya sa ‘yan-sha-biyu na da babban kaso cikin ayar da Allah Ta’ala ke cewa a cikinta:

﴿وَمَن أَظلَمُ مِمَّنِ ٱفتَرَى عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَو كَذَّبَ بِٱلحَقِّ لَمَّا جَاءَهُ أَلَيسَ فِي جَهَنَّمَ مَثوى لِّلكَفِرِينَ٦٨﴾ العنكبوت: ٦٨

Shin wane ne ya fi zalunci a kan wanda ya qira wa Allah qarya, ko ya qaryata gaskiya a lokacin da ta zo masa.

 Al-Ankabut: 68.

 Suna raya cewa Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma sun yi ridda alhali babba da yaro kowa ya san cewa su ne suka yaqi waxanda suka yi ridda. Kasancewarsu suna bai wa masu ridda hanzari, suna zargin Abubakar da zaluntar su, dalili ne babba na xayantakar tafarkinsu, da cewa Abubakar da Ahlus-Sunnah mabiyansa har abada suna cikin yaqi da masu ridda.

 Maganar hana zakka kuwa, wasu mutane ne daban ta shafa ba na Yamama ba. Kuma wasu Sahabbai sun yi ciris kan lamarinsu, wasu sun yi shakkar halalcin yaqar tasu. Cikinsu har da sayyidina Umar, amma nacewar da Abubakar ya yi, da qarfin hujjar da ya kafa ta sanya kowa ya gamsu. Su xin ma yana da kyau a sani cewa, ba an yaqe su ne don kawai ba su ba da zakka ga Abubakar Raliyallahu Anhu ba. A’a, don dai ba su yarda da fitar da ita ba suka ba da ita ga masu haqqi. In da sun aminta da bayar da ita da kansu ga waxanda suka cancanta da ba za a yaqe su ba. Don haka, sanannen abu ne cewa, Siddiqu bai yaqi kowa ba akan sai ya yi masa xa’a, ko ya yi masa mubaya’a. Don haka ne lokacin da Sa’adu ya yi jinkirin yi masa mubaya’a bai tilasta shi ba.

 Sai hadisin da xan Shi’ar ya jingina ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama don ya kafirta waxanda suka yaqi Ali. Hadisin dai kamar sauran ire-iren hadissan da ya saba kawowa ne, waxanda ba su a cikin sannannun littafan hadisi, balle ko a ce suna da isnadi da za a duba a yi hukunci a kansu. Kuma ko bisa ga qaddarawa in har gaskiya ne Manzon Allah ya faxe shi, ba lalle ne waxanda suka yaqi Ali su kasance sun ji shi ba.

Lokacin da Ali Raliyallahu Anhu ya yi yaqin Raqumi da na Siffin bai ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya umurce shi da yin hakan ba. Ijtihadi dai ne ya yi. Abu Dawuda ya ruwaito daga Qaisu xan Abbad cewa: Na tambayi Ali game da fitarsa daga Madina zuwa yaqi, na ce ma sa: Shin umurni ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba ka, ko kuwa ra’ayinka ne? Sai ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai umurce ni da komai ba cikin wannan lamari. Ra’ayina ne kawai.

 Ka ga da gaskiya ne cewa wanda ya yaqi Ali Raliyallahu Anhu ya yaqi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, kuma ya zama murtaddi, to, da Alin ya yi masu abin da ake yi wa murtaddai. Ga shi kuwa abokan faxansa a yaqin Raqumi da na Siffin duk hanawa ya yi a bi wanda ya juya a cikinsu. Masu rauni kuma ya hana a gama da su. Ya kuma ce, kada a xauki ganimar dukiya ko iyali ko ‘ya‘ya. Waxannan ko ba hukunce-hukuncen yaqar murtaddai ne ba. Hasali ma cikin waxanda ke xaya vangaren yaqin akwai uwar muminai A’ishah. Wa zai ce ba uwarsa ce ba ya kafirta? Kuma wa zai bautar da uwarsa?

 Kuma in da abokan faxan Ali kafirai ne, da Hassan Raliyallahu Anhu bai miqa lamarin musulmi ga hannun kafiri, murtaddi ba. Ga shi kuma ma’asumi ne; ba ya kuskure a wurinku. Miqa akalar musulmi zuwa ga kafirai ba aikin mumini ba ne balle ma’asumi.

 Shi dai Allah Ta’ala bai kafirta kowane vangare ba. Cewa ya yi: Idan qungiyoyi biyu na muminai suka yi yaqi to, ku yi sulhu a tsakaninsu. Al-Hujurat:9. Sai Allah ya tabbatar da cewa suna nan a matsayinsu na muminai ‘yan’uwan juna ne koda yake sun yaqi juna.

 Kuma ya tabbata cikin ingantaccen hadisi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: “Wasu ‘yan-a-ware za su fice a lokacin rarrabuwar musulmi, sai wata qungiyar da ta fi kusa da gaskiya ta kashe su”. Ya kuma ce: “Haqiqa jikan nan nawa shugaba ne. A nan gaba Allah zai sasanta wasu manyan qungiyoyi biyu na musulmi ta hayarsa”. Ya kuma ce ma Ammar: “Wata qungiya mai ta’addanci za ta kashe ka”. Sai ya sifaita ta da savo ba kafirci ba.

 Duk waxannan hadisan ingantattu ne a wurin malamai. Sai ta tabbata cewa, gaskiya ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba da labarin cewa qungiyoyi biyu masa savani da juna musulmai ne. Kuma ya yabi wanda Allah zai sa ya sulhunta su. Ya kuma bayyana cewa wata qungiyar ta fi wata kasancewa kusa da gaskiya, wacce kuma ita ce za ta kashe Ammar.

 Bari yanzu mu haxa ‘yan Shi’ah da wasu maqiyan Ali Raliyallahu Anhu su tattauna don mu ji amsar da za su ba su. Maqiyan Ali sun ce, ya halatta jinin musulmi, ya yaqe su ba bisa umurnin Allah da Manzo ba, don kawai kariyar muqaminsa. Ga shi kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Zagin musulmi fasiqanci ne, yaqarsa kuma kafirci ce”. Ya kuma ce: “Kada ku juya bayana ku koma kafirai; sashenku na kisan sashe”. Suka ce, bisa ga qaxannan hujjoji Ali Raliyallahu Anhu ya kafirta.

To, faxa min wace amsa ce ‘yan-sha-biyu za su bayar? Duk hujjar da za su bayar ba za ta fi hujjar waxancan ba, don hadissan da suka kafa hujja da su ingantattu ne.

 Sannan kuma Nasibawan, maqiya Ali na cewa: Kashin rayuka varna ne. Don haka duk wanda ya kashe rayuka don a yi masa xa’a to, yana neman xaukaka ne a bayan qasa, da yaxa varna. Suka ce, wannan shi ne halin Fir’auna da ire-irensa. Kamar yadda Allah Ta’ala ya ce: Waccan gidan lahira ce (Aljanna) muna ba da ita ga waxanda ba su neman xaukaka a bayan qasa, ba su kuma son varna. Kuma qarshen qwarai na masu tsoron Allah ne. Al-Qasas: 83. Suka ce duk wanda ya nemi xaukaka a bayan qasa ta hanyar yin varna kamar kisan mutane, to, ba ya cikin masu rabo a ranar lahira saboda wannan aya. Kuma suka ce Ali na cikinsu. Suka ce, amma Abubakar ya yaqi waxanda suka hana zakka ne da waxanda suka yi ridda don mayar da su zuwa ga xa’ar Allah da Manzonsa, ba don a yi shi a yi masa xa’a ba.

 2.9.18 Wai Iblisu Ma Ya Fi Mu’awiyah.. Inji shi!

 Xan Shi’ar ya ce: Wani malami na kirki ya kyauta inda yake cewa: “Wanda ya fi iblis sharri shi ne wanda bai wuce shi ga xa’ar da ya tava yi ba, sannan ya tafi tare da shi a cikin fagen savonsa”. Babu wata shakka a tsakanin malamai cewa, Iblisu ya kasance ya fi mala’iku ibada, kuma yana xauke da Al’arshi shi kaxai har tsawon shekaru dubu shidda. Amma lokacin da Allah ya halicci Adam, ya sanya shi halifa a bayan qasa, an umurce shi da ya yi sujuda sai ya yi girman kai, sai ya cancanci la’ana da kora. Haka Mu’awiyah bai gushe ba yana shirka da bautar gumaka tsawon lokaci bayan bayyanar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Sannan kuma ya yi girman kai da aka sa Ali ya zama shugaba, kowa ya yi masa mubaya’a bayan an kashe Usmanu sai shi Mu’awiyahn ya yi zamansa a inda yake. Don haka gara ma iblis da shi.

Martani:

Wannan maganar inda mafaxinta ya yi tunani zai gano ta qunshi jahilci da vata da fita daga cikin musulunci, kai har ma da dukan addinai da kuma fita daga aikin hankali irin wanda ko kafirai na da shi.

 Da farko dai ba a haxa kafircin Iblis da na kowa. Kuma duk wanda ya shiga wuta to, yana cikin mabiyansa ne. Don haka Allah Ta’ala ya ce masa: Wallahi zan cika wutar jahannama da kai da duk wanda ya bi ka gaba xaya. Sad: 85. Duk laifin da aka yi a duniya shi ne ya yi umurni da shi, ya qawatar da shi, ya sa ayi shi. To, yaya wani zai fi shi sharri, musamman daga cikin musulmi, kuma daga cikin sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama?

 Cewa wanda ya fi iblis sharri shi ne wanda bai yi irin xa’ar da Iblis ya yo can baya ba, sannan ya bi shi a wajen savo. In aka bi wannan magana tana nuna cewa duk wanda ya sava wa Allah ya fi Iblis sharri kenan. Don bai kai shi ga waccan xa’ar da kuka ce ba, sannan suka yi tarayya a fagen savo. A haka, kenan Annabi Adamu da zurriyarsa sun fi Iblis sharri, don Allah Ta’ala ya ce: Kuma Adamu ya sava wa Ubangijinsa, sai ya vata. Suratu Xaha 121. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kuma ya ce: “Duk ‘yan Adam masu yawan kuskure ne. Mafi alherin masu kuskure su ne masu tuba”.

 Akwai kuwa wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira da ke iya qarfin halin cewa gara Iblis da musulmin da ya yi savo? Ashe wannan ba ya cikin abubuwan da aka san cewa vata ne da kaucewa daga tafarkin addinin musulunci? To, bisa ga wannan maganar, ‘yan Shi’ah ma gara Iblis da su, don koyaushe suna cikin zunubi.

 Idan Kharijawa suka ce maku: Ali Raliyallahu Anhu ya aikata savo, don haka gara Iblis da shi. Me za ku ce mu su? Ba abin da za ku ce sai shi ma’asumi ne da ba ya kuskure. Ku da ba za ku iya tsayar masu da hujjar da ke tabbatar da imaninsa da shugabancinsa da, ina maganar ma’asumancinsa? Duk abin da ‘yan-sha-biyu ke kafa hujja da shi sokakke ne kuma yana karo da dalillai irinsa daga gefen Kharijawa, don haka bai inganta a kafa hujja da shi. Amma Ahlus-Sunnah na iya tabbatar da imanin Ali da shugabancinsa da hujjojin da ‘yan-sha-biyu ba su da hannu gare su, don suna warware aqidarsu.

 Abu na biyu kuma shi ne: Wannan magana bayan dai ba ta da hujja, kuma ba ta da ma’ana. Don ina dalilin cewa, wanda bai yi irin aikin da shaixan ya yi ba kafin kafircinsa ya fi shi sharri in sun tafi tare a savo? Akwai daga cikin ‘yan Adam wanda zai iya tafiya tare da shaixan cikin dukan savonsa? Don ba shi yiwuwa a sami mutumin da zai kai Iblis wajen savo, ta yadda zai iya vatar da dukan mutane, ya ruxe su.

 Idan Iblis ya gabatar da wata xa’a kome yawanta, ta riga ta rushe da kafircin da ya yi bayanta. Saboda ridda tana vata aiki. Sannan savon da yake yi har abada kowa bai iya yin sa. To, ta yaya za a sami wanda ya fi shi sharri?

 Idan mun tafi a kan wannan qa’idar da xan Shi’ar ya kafa, kenan magoya bayan Ali Raliyallahu Anhu waxanda suka yi yaqi tare da shi kuma suka kasance a wasu lokutta suna sava masa, sun fi sharri a kan waxanda ba su yi masa mubaya’a ba cikin Sahabbai. Don su, suna da xa’a da ta gabata sannan waxancan sun tafi tare da su a fagen savo.

To, sannan ina hujjar cewa, Iblis ya fi Mala’iku ibada? Da kuma cewa ya kasance yana xauke da al’arshi tsawon shekaru dubu shidda? Ko ma cewa yana cikin masu xaukar al’arshi? Ko shi ne xawusun Mala’iku? Ko ba wani bigire a sama ko a qasa face ya yi wa Allah sujada ko ruku’i a cikin? Da makamantan waxannan maganganu da wasu mutane ke faxa. Irin wannan lamarin hanyar saninsa kawai ita ce ingantacciyar riwaya. To, ba a faxi wani abu mai kamar haka ba a cikin Alqur’ani, kuma ba a riwaito wani ingantaccen hadisi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba game da shi. To, in ba jahili ba wa zai kafa hujja da irin wannan ga manyan mas’aloli haka?

 Abin da duk ya fi ban mamaki shi ne cewarsa wai, babu savanin tsakanin malamai cewa Iblis ne ya fi dukan mala’iku ibada. Wane ne ya ce haka cikin malaman Sahabbai ko Tabi’ai da wasunsu daga cikin malaman musulmi, ballantana ya kasance malamai sun haxu a kan sa? Wannan maganar ba wanda ya tava yin ta cikin malaman musulunci da ake karvar maganarsu. Kuma abu ne wanda ba shi yiwuwa a san shi sai ta hanyar riwaya, kuma ba a riwaito wannan daga kowa ba, koda da isnadi mai rauni. To, idan wasu masu wa’zi ne suka faxe shi, ko masu rubutu game da tarbiyyar zuciya, ko masu xauko labaran da aka riwaito daga Yahudawa cikin wasu littaffan tafsiri ba tare da isnadi ba. Wannan ba a kafa hujja da shi ga abin da ya shafi kwandon albasa. To, yaya zai kafa mana hujja da shi a kan cewa, Iblis ya fi duk wani wanda ya savawa Allah cikin ‘yan Adam, kuma ya sa Sahabbai cikin waxannan da Iblis ya fi su?

Allah Ta’ala bai tava siffanta Iblis da alheri ba, haka ma Manzonsa Sallallahu Alaihi Wasallama, to, balle cewa ya tava yin wata xa’a ko wace iri ce. Tattare da in ya yi to, ta vaci saboda riddar da ya yi da kafircinsa.

 Wani abin al’ajabi daga cikin maganar xan Shi’ar, wai babu wani savani tsakanin malamai cewa, Iblis ya kasance yana xauke da al’arshi shekaru dubu shidda shi kaxai! Tsarki ya tabbatar ma Allah. Shin akwai kuwa wanda ya tava furta wannan magana daga cikin malaman musulmi da ke ganin girman Allah? Idan ma har wannan labarin gaskiya ne, to, ai ba a iya saninsa sai ta hanyar Annabawa. Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama kuwa bai faxi komai ba game da wannan batu. To, ta ina suka san shi?

 Shi dai Mu’awiyah Raliyallahu Anhu musuluncinsa ya tabbata. Kuma musulunci na shafe duk abin da ya gabace shi. Sannan bai tava yin ridda ba bayan ya musulunta. Amma wanda ke raya cewa Abubakar Raliyallahu Anhu da Umar Raliyallahu Anhu da Usmanu duk sun yi ridda, ina mamaki don ya haxa da Mu’awiyah Raliyallahu Anhu? Kuma ina banbancin hujjarsa da ta waxanda suka ce Ali Raliyallahu Anhu ya yi ridda shi ma, Harijawa kenan? In dai ta vangaren hujja ne to, Harijawa sun fi hasken hujja a kan ‘yan-sha-biyu.

 In da kuma har wayau za mu xauki maganar xan Shi’ar a yadda ya yi ta, ba wanda take suka gare shi kamar Ali da xan Al-Hassan. Don kenan murtaddai sun samu galaba a kansa shi Ali., Hassan kuwa ya miqa shugabancin musulunci ga murtaddai. Kuma kenan taimakon da Allah ya yi wa Khalid akan kafirai ya fi wanda ya wa Ali Raliyallahu Anhu. Da yake Allah Ta’ala mai adalci ne da ba ya zaluntar kowa, ya ba Khalid xan Walid abin da ya cancanta na taimako. Shi kuma Ali bai cimma Khalid ba, tun da Allah bai taimake shi a kan waxanda ya yaqa ba. Khalid dai kenan ya fi xaukaka a wurin Allah sama da Ali.

 Maganar mubaya’ar da ya ce kowa ya yi ma sa bayan kisan Usmanu. Idan wannan hujja ce, to, mubaya’ar da aka yi wa Usmanu Raliyallahu Anhu ta fi girma. Ga shi ko ku ba ku ganin wanda ya qi wa Usmanu mubaya’a a matsayin kafiri. Kuna ma ganin cewa, shi ne musulmin qwarai mai tsoron Allah.

 Kuma bisa wannan maganar taku, sai mu ce, haxuwar kan mutane a lokacin yi wa Abubakar mubaya’a ta fi kammaluwa. Ga shi ko ku da wasu ba ku ba na cewa Ali Raliyallahu Anhu bai yi mubaya’a ba sai bayan wani lokaci. To, wannan yana kai mu ga cewa ya yi girman kai ga yi wa Allah Ta’ala xa’a bisa ga wannan qa’idar taku. Wannan yana kai wa ga kafirta Ali Raliyallahu Anhu bisa wannan hujjar taku in da ta kasance gaskiya. Amma mu mun san hujjarku vatacciyar hujja ce, ba mu kafirta Ali Raliyallahu Anhu ko waninsa da ita. Ku dai da ke amfani da ita in kun gane sai ku tuba.

 Fita batun qaryar da ya shara wajen cewa, kowa ya yi ma Ali mubaya’a bayan Usmanu. Don da yawa daga cikin musulmi; rabi ko abin da bai kai haka ba, ko wanda ya fi haka basu yi ma sa mubaya’a ba. Manya irin su Sa’adu xan Abu Waqqas da Abdullahi xan Umar na cikin waxanda ba su yi ba.

 Daga qarshe, cewar da ya yi, wai, Mu’awiyah ya zauna wurinsa, babu adalci a ciki. Don can farkon lamari Mu’awiyah bai nemi shugabanci ga kansa ba, bai kuma tafi wurin Ali Raliyallahu Anhu don ya karve masa mulki ba, amma yaqi yi masa mubaya’a ne shi da mabiyansa. Ya kuma ci gaba da shugabancinsa na gwamna wanda tun lokacin Umar da Usman yake yi. Ko lokacin da aka nemi sasantawa, aka sanya mutum biyu su yi hukunci, Mu’awiyah ya kasance yana shugabantar waxanda ke qarqashinsa ne kawai. In kuma xan Shi’ar na nufin ne Mu’awiyah ya haye mulkin Sham xin ne, bai bar Ali Raliyallahu Anhu ya naxa wani ba, to, wannan gaskiya ne. Amma abin da Mu’awiyah Raliyallahu Anhu ke cewa shi ne, ba zan yi jayayya da shi a cikin abin da ke hannunsa ba, kuma ban ga abin da ke wajabtar da shigata qarqashin xa’arsa ba. Wannan maganar kuwa sawa’un in gaskiya ce ko qarya, ba ta isa ace wanda ya yi ta ya fi Iblis sharri ba.

Wanda ya mayar da Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama matsayin waxanda suka fi Iblis sharri, to, bai raga ma Allah da Manzo ba. Ya kuma yi shisshigi, ya wuce iyaka ga mafi alherin qarni da aka tava yi na ‘yan Adam. Allah Ta’ala zai taimaki Manzanninsa da waxanda suka yi imani a rayuwarsu ta duniya da ranar qiyama, sa’adda shaidu za su tsayu, su ba da shaida a gabansa. Shi kuma son zuciya idan ya kai mai shi zuwa ga irin wannan madatsa yakan fitar da shi daga cikin hankalinsa, fita batun ilimi da doka. Allah muke roqo ya kiyashe mu daga miyagun fitinu.

Tabbas, Allah Ta’ala zai qasqantar da wanda ke furta irin wannan magana, kuma zai taimaki bayinsa muminai, waxanda suka haxa da Sahabban Annabinsa da masoyansu a kan waxannan azzalumai masu qiren qarya.

 2.9.19 Yazidu Ya Zama Sarki, Husaini Ya Samu Shahada

 Xan Shi’ar ya ce: “Duk da miyagun ayyukan da Yazidu xan Mu’awiyah ya aikata, waxanda suka haxa da yi wa Husaini kisan gilla, tare da wasashe dukiyarsa, da ribace matansa, da sukwane lungu–lungu na garuruwa da su a kan raqumma; haka nan babu ko siridda a kansu. Suna kuma jaye da shugabanmu Zainul Abidina sun zuba masa sarqa a hannu kamar bawa.

Wannan wulaqanci da suka yi wa Zainul Abidina bai ishe su ba. A qarshe dai suka aika shi lahira. Kuma duk da haka hankalin su bai kwanta ba, sai da suka tattaka haqarqarinsa da dawaki suka sare kansa tare da soka shi a kan tsinin mashi, tare da na waxanda ke tare da shi, suka ratsa gari tsaye suna murna da annashawa.

Duk waxannan abubuwa ba su hana wani sashe na Ahlus–Sunna imani da cewa Yazidu ya karva sunan shugaba a musulunci ba, saboda tsananin qabilanci.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: “Kuma wani abin ban mamaki shi ne, waxannan mutane sane suke da cewa malamansu sun riwaito cewa; ranar da Yazidu ya yi wannan aika–aika ta aika Husaini lahira sai da aka yi mamakon ruwan jini daga sama. Wannan magana da nake gaya ma, Rafi’i ne ya kawo ta a cikin littafin: Sharhul Wajizi, haka nan kuma Ibnu Sa’ad ya faxa a cikin littafin: Ax-Dabaqat cewa; a wannan rana sama’u tayi ja jawur. Abin da ba a tava gani ba. Ya kuma ci gaba da cewa; babu wani dutse da za a tava a duniya, saboda wani dalili a wannan rana, face an taras da ruwan jini a qarqashinsa. Haka kuma an yi wani irin ruwan sama da ya zama takalmin kaza a jikin tufafin mutane.

Kuma Imamuz-Zuhri ya ce; babu wanda ya tsira daga azaba tun nan duniya daga cikin waxanda ke da hannu kai tsaye a cikin kisan Husaini. Gaba xayansu mummunan qarshe suka yi. Wasu daga cikinsu karkashe su aka yi. Wasu kuma aka jarabce su da makanta ko baqin jini ko kubcewar mulkinsu, duk a cikin xan qanqanin lokaci.

Kuma sau da yawa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi wa musulmi wasiyya da su raga wa jikokin can nasa guda biyu, wato Hasan da Husaini. Yana mai cewa: “Waxannan sune amanar da na bari hannunku”.

Kuma wai ma a kan haka ne Allah ya saukar da ayar da ke cewa: “Bani tambayar ku wata ijara a kansa face dai soyayya ta cikin zumunta” (42:23).

Tirqashi! Gwanin abu mai yin sa, kai ka ji.

Martani:

Bismilahi. Mun fara.

Ina fatar dai baka mance da farkon maganar xan Shi’ar ba. Don ta ita ne zamu fara mayar masa da martani.

Muna son mu gane abin da yake nufi da cewar da ya yi; wai, tsananin qabilanci yasa wasu Ahlus – Sunnah imani da cewa Yazidu xan Mu’awiyah ya karva sunan shugaba (Imamu) a musulunci.

 Ixan xan Shi’ar na nufin waxannan Ahlus-Sunnah sun yi imani da kasancewar Yazidu xaya daga cikin shiryayyun halifofi da nagartattun shugabanni a musulunci. Kamar su Abubakar da Umar da Ali Raliyallahu Anhum. to, muna tabbata masa cewa babu wani malami daga cikin malaman musulunmi da ya yi imani da haka. Amma dai muna jin labarin cewa akwai wasu jahilai daga cikin qurdawa da makamantansu da sukayi imani da cewa Sahabbai ba su fi Yazidun da komai ba; shi ma Sahabi ne. Kai! Wasu ma daga cikinsu na jin cewa shi Annabi ne. A ya yin da wasu suka tsaya kusa-kusa; suka ce a a, yana dai kafaxa-da-kafaxa da shiryayyun Halifofi.

To, amma irin waxannan mutane ba su daga cikin ma’abuta ilimi, balle a yi guzurin maganarsu.

Amma kuma duk da haka, sun fi jahilai da zindiqai daga cikin ‘yan-Shi’ah sauki. Waxanda ke jin cewa sayyidina Ali Raliyallahu Anhu Allah ne, ko Annabi. Kuma wai shari’ar musulunci ba komai ba ce illa yaudara, saboda zahirinta na takin saqa da baxininta. Kai! qarewa da qarau ma Isma’iliyyah da Nasiriyya da wasunsu daga cikin qungiyoyin Shi’ah na .jin cewa salla da azumi da zakka da hajji, sun faxi daga kan malamansu. Kuma wai tashin qiyama qarya ne. Wal’iyazu billahi. Can ga bakinku.

 Amma ka sani, babu wani daga cikin malaman ahnlus –sunna, irin waxanda ake shiga xaka da maganarsu, da ya yi imani da cewa Yazidu da makamantansa na kafaxa-da-kafaxa da halifofin Manzon Allah, irin su Abubakar da Umar da Usmanu da Ali. Raliyallahu Anhum a daraja da xaukaka. Ko alama. Hasali ma ahlus- sunna riqe suke da hadisin nan da ke cikin: As –sunanu, wanda ke cewa: “Halifancin annabta zai qare bayan shekaru talatin, mulkin gargajiya ya maye gurbinta.”

Wannan kenan. Idan kuma xan Shi’ar na so ne ya ce waxannan mutane da ya kira sashen Ahlus-Sunnah sun yarda da Yazidu, har quryar zukatansu, a matsayin Sarkin Musulmi kuma halifa a zamaninsa, mai wuqa da nama. Kamar yadda suka aminta da sauran halifofi; Umawiyyawa da Abbasiyyawa, to, babu wata jayayya a cikin haka. Duk wanda ma ya ce ba zai yarda da haka ba, to ya tabbata kangararre. Domin kuwa gaba xayan duniyar musulunci ta ji kuma ta yarda da bai’ar da aka yi wa Yazidu bayan rasuwar mahaifinsa Mu’awiyah. qasashen musulmi da suka hada da Sham da Masar da Iraqi da khurasan da sauransu duk, suka kasan ce qar qashin ikonsa.

Ka ga da haka ne ya zama shugaba kuma halifa kuma Sarkin Musulmi. Babu kuma wani dalili da za a iya riqo dashi, a hana shi zama haka. Yadda kasan dole ne a kira mai ba mutane salla da sunan liman; ko anqi ko anso. Domin dazarar kowa ya yalla ido ya ga mutum ya rungume hannuwa gaban sahu, to wautace wani ya qi yarda da kasancewarsa liman gare su. Shi kuwa zancen kasancewarsa mutumin kirki ko asharari, wata maganace daban.

To, a kan wanan ma’auni ne Ahlus-Sunnah suka yi imani da kasan cewar Yazidu da Abdulmalik da Mansur da wasunsu sarakunan musulunci. Shi kuwa duk wanda ke musun haka, dai-dai yake da wanda ke musun halifancin Abubakar da Umar da Usmanu. Da mulkin kisra da qaisar da Najjash, da wasu sarakuna.

Amma cewa xaya daga cikin waxannan halifofi da sarakunan musulunci ma’asumi ne. Ko kuma adali ne a cikin gaba xayan al’amurransa; baya sava wa Allah fai da voye, wannan ba aqidar malamai da shugabanin musulunci ba ce.

Sanya wannan mala tukuna.

Shi kuwa Husaini Raliyallahu Anhu a wurin Ahlus-Sunnah, ko shakka babu kisan da aka yi masa zalunci ne. Kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya karvi shahadarsa. Wannan kisa nashi a wurinmu daidai yake da na duk wanda aka kashe bai ji bai gani ba, sai don kawai ya ce Allah! Kuma duk wanda ya aikata wannan mugun aiki ko ya taimaka cikin tabbatuwarsa ko ya yi farin ciki da haka, to ya sava wa Allah ya kuma cutar da Manzo. Don ya yi tarayya da maqiya Allah a cikin jefa musulunci cikin fitina.

Amma kuma a wuri xaya, kamar yadda muka faxa, hakan ta zama sanadiyyar samun shahada da daraja da xaukaka ga Husaini Raliyallahu Anhu. Allah Ta’ala ya nufi cewa shi da xan’uwansa za su sami irin wannan babban rabo, da ba a samu sai da zufan goshi. Eh! Tsuntsu ne daga sama gasashshe suka samu. Don ba su ga abubuwan da wasu daga cikin mutanen gixansu suka gani ba na hawa da gangara. Domin kuwa ko da aka haife su yabanyar musulunci ta qetare siraxin fari. Suka rayu cikin girma da aminci, sai ga shi cikin ikon Allah xayansu yara su ta hanyar shayar da shi guba. Xayan kuma ta hanyar kisan ga-ni-ga-ka. Da haka ne kuma suka sami shiga sahun manyan shahidai.

Amma kuma daxa, duk da haka, zunubin wannan kisan gilla da aka yi wa Husaini da ‘xan’uwansa, bai kai girman zunubin kisan gillar da waxansu al’ummomi suka yi wa Annabawa ba. Ka tuna irin yadda Allah Ta’ala yake ba mu labarin irin yadda bani’isra ila ke karkashe Annabawa ba li ba la. To, musiba da zunubin da ke cikin kashe ba annabe sun yi wa wanan fintinqau. Kai! Ko kisan gilar da aka yi wa halifa Ali da Halifa Usmanu Raliyallahu Anhuma duk sun fi wannan girman zunubi da musiba.

To, tunda kuwa har haka ne. Ashe ka ga kenan babu abin da ya wajaba a kan musulmin qwarai a cikin waxannan lokuta na sabkar musibu, sai haquri da mayar da al’amari a wurin Allah. Kamar yadda Allah da Manzonsa ke so,

Amma a maimakon haka, sai gashi wannan kisa na Husaini Raliyallahu Anhu ya sa wasu mutane sun biye wa qixan shexan. Inda hakan ta zama sanadiyar tsiruwar waxansu bidi’oi guda biyu: bidi’ar zama cikin baqin ciki da jimami tsawon yinin ranar Ashura, tare da mare maren kai da kai, da hargowa da koke- koke da bege da rera wakokin ta’aziyya. Tare da wannan kuma, sai ka taras sun buge ga: Bidi’a ta biyu wato zagin magabata da la’antar su, tare da shafawa waxanda ba su ji ba su gani ba daga cikinsu kashin kaji. Wanda hakan kan kai su ga zagin uwayen tafiya (Assabiqunal auwaluna) A qarshe kuma su zauna xandali suna qaranta yadda al’amarin abin ya faru wai. Wanda mafi yawan labarun da suke faxa wa mutane a kan hakan qarya ce tuburan.

Kuma kar ka daxa kar ka qara.’Yan Shi’a sun tsiri waxannan abubuwa ne tare da mayar da su wata sunna tasu, don kawai su haifar da fitina a cikin musulmi tare da raba kanunsu. Gaba xayan musulmi sun yi itifaqi a kan cewa, ko ga matsayin mustahabbi waxannan abubuwa da suke yi a wanan rana ba su kai ba balle wajibi. Kai! Hasali ma fita hayyaci da jimami saboda wasu musibu da suka daxe da faruwa a rayuwa, na daga cikin manyan abubuwan da Allah da Manzonsa suka haramta. Kamar yadda suka haramta matsanacin xoki da annashawa tare da fita hayyaci saboda wani abu na farin ciki.

Ita kuwa cewar da xan Shi’ar ya yi wai an ribace mata da ‘ya’ya matan Husaini Raliyallahu Anhu An kuma xauke su a kan raqumma babu ko siridda, aka zagaya qasa da su, qarya ce lafiyayyarta.

Alhamdu lillahi. A iya saninmu da tarihin musulunci, musulmi ba su tava ribace wata Bahashima ba. Hasali ma babu wani lokaci da aka tava jin al’ummar Muhammadu Sallalahu Alaihi Wasallama ta halatta ribantar wani Bahashime. Amma dai muna jin qarya ce – qarya cen da wasu jahilai ma’abuta son zuciya ke yaxawa. Kamar yadda muka ji wata qungiya daga cikinsu na cewa wai Hajjaju, ya tava kashe sharifai (Banu Hashim).

Haka kuma cewar da ya yi wai babu wani dutse da za’a xaga, a kan wata lalura a duniya, a ranar da aka kashe Husaini face an taras da jini qundum a qarqashinsa, ita ma qarya ce bayyananna.

Amma ka ga cewar da ya yi imamu Az-zuhri ya ce: Babu wan da yara ge daga cikin waxanda ke da hannu a cikin kisan Hussai Raliyallahu Anhu face Allah ya azabtar da su tun duniya.

Wannan abune mai yiyuwa. Domin ta tabbata cewa zalunci shi ne zunubin da Allah ke gaggauta azabtarda wanda ya yi shi tun duniya.babu kuwa zaluncin da ya kai kisan Husaini Raliyallahu Anhu girma.

Amma kuma ko shakka babu, cewar da ya yi wai, a kan Hassan da Husaini ne ayarda ke cewa: Ka ce, Bani tambayar ku wata ijara a kansa face dai soyayya ta cikin zumunta. (42:23) ta sauka qarya ce lafiyayya.

Dalili kuwa shi ne; ita dai wannan aya tana cikinsurar shura ne. Ita kuwa wannan surar ko shakka babu a Makka ne ta sauka; wato tun kafin a aurar wa Ali da Fatima Raliyallahu Anhama har su haifi Hasan da Husainin. Tarihi ya tabbatar da cewa an yi wannan aure ne bayan anyi Hijra zuwa Madina da she karu biyu. Kuma ba suyi baiko ba sai bayan yaqin Badar, wanda akayi a cikin watan azumi na sheqarar.

Abin da wannan aya ke nufi, kamar yadda xan Abbas yabayyana, Imamul Buhari kuma da waninsa suka riwaito, shi ne; Allah (S W A) na magana ne da harshen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa ; ka ce musu ba ka neman wani sakamako daga wurin su a kan alherin da ka zo masu dashi na musulunci,face su dubi abin da ke tsakaniku na zumunta;kada su cutar da kai.

Xan Abbas ya qara da cewa, hakan kuwa ta faru ne: saboda babu wata qabila daga cikin qabilun Quraishawa, wadda Manzon Allah ba yada zumunci da su. Ka ji xan xangi.

Amma kuma duk da haka munji wasu marubuta daga cikin Ahlus-Sunnah wal jama’a da ‘yan Shi’a, daga cikin muqarraban imamu Ahmad da wasunsu na yayata wani qagaggen hadisi, wanda kecewa wai: A lokacin da wannan aya ta sauka, Sahabbai sun tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: su waye ma kusantan naka? Wai sai ya ce: Ali da Fatima da ‘Ya’yansu guda biyu.

To, malamai ma’abuta ilimin hadisi sun yi ittifaqi a kan cewa, wannan hadisi qagagge ne.

 2.9.20 Yazidu Bai Cancanci La’anta ba

Xan Shi’ar ya zargi wasu daga cikin Ahlus-Sunnah, waxanda hankalinsu bai natsu da cancantar Yazidu da shiga sahun sarakunan musulunci ba. Amma kuma tattare da haka ba su yarda da a la’ance shi ba. Amma kuma wai, A cewar xan Shi’ar, sun yarda da kasancewarsa azzalumi. Tunda ya kashe Husaini ya kuma yi awon gaba da duk abin da ya mallaka.

To, wai ko sun manta da faxar Allah Ta’ala: To, La’anar Allah ta tabbata a kan azzalumai. (11:18)?

Kuma ga shi Abul-Faraji Ibnul-Jauzi, xaya daga cikin malaman mazhabar hanbaliyyah ya ce: An samo daga xan Abbas Raliyallahu Anhu wanda ya ce wai: Allah Ta’ala ya yi wahayi zuwa ga Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: Na karvi rayukan mutum dubu saba’in akan kashe Annabi Yahya xan Zakariyya. Zan kuma karvi rayukan mutum dubu xari da arba’in akan kashe jikanka.

Haka kuma As-suyudi, xaya daga cikin mutane masu girma a wurin Ahlus-Sunnah ya bayar da labarin cewa: “Watarana na sauka karbala ina xauke da kayan abinci na na kasuwanci a inda wani mutun ya karvi baqunci na. Bayan mun qare cin abincin dare, sai muka xauko hirar kisan gillar da aka yi wa Husaini a wannan wuri. Sai ni da fatake yan uwana muka ce: “ Ka ko ga babu wanda bai yi mutuwar qasqanci ba, daga cikin waxanda ke da hannu a cikin kisan Husaini.” Sai mai masaukinnan namu ya kada baki ya ce: “Lallai kune sarakunan qaryar duniya! To, ni xin nan dake gabanku tare da ni aka kashe shi, Amma kuma gani daram”. Ah! Ai dare na tsalawa; alfijiri na gab da ketowa, sai kawai muka ji ana cewa kai baqi ku tashi ba lafiya. “Muka ce me ya faru?”

Sai aka karva mana da cewa: Ai jiya da dare mai masaukin nan namu yana gyaran a-ci-bal-bal xinsa, sai kawai yatsansa ya lashi wuta. Nan take wutar ta bi ta jinin sa ta kone shi qurmus. Wallahi haka muka taras da gawarsa baqi qirin kamar gawayi.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: kuma Muhammad xan Yahya ya tambayi Ahmad xan Hambali watarana, a kan Yazidu. Sai ya karva masa da cewa: Shi ne wanda ya aikata aika-aikan nan.ya ce: “sai na ce masa; meya aikata?” sai ya karva mani da cewa: Keta alfarmar Madina ya yi.

Kuma wai watarana Salihu, xaya daga cikin ‘ya’yan Ahmad xan Hambali ya ce wa mahaifin nasa: Baba naji wasu mutane na cewa muna daga cikin waxanda suka yarda da jivintar Yazidu. Sai wai shi kuma ya karva masa da cewa: Haba Salihu, ai ba wanda ke yarda da jivintar Yazidu, sai wanda bai yi imani da Allah da ranar lahira ba. Ko me kace? Sai Salihun ya ce masa: To baba me ya sa ban ji kana la’antar sa ba? Sai wai shi kuma ya karva masa da cewa: Me ko zai hana in la’anci wanda Allah ya la’anta a cikin littafinsa? Ba ka dai dace da hakan ba ne. Sai kuma ya sake ce wa uban: To, baba a ina Allah ya la’ance shi? Sai ya karva masa da cewa a cikin faxar sa: To, shin kuna fatar idan kun juya (daga umurnin) za ku yi varna a cikin qasa, kuma ku yanke zumuntarku? Waxannan su ne waxanda Allah ya la’ane su, sannan ya kurumtar da su, kuma ya makantar da ganinsu (47:22-23).

 Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: To, akwai zalunci da varnar da ta kai kamar kisan kai da keta alfarmar birnin Madina tsawon kwana uku tare da ribance mutanen da ke cikinta? Tare kuma da kashe wasunsu da dama, da suka haxa da Quraishawa da Ansaru da Muhajiruna, waxanda adadinsu bai kasa xari bakwai. Da wani adadin na bayi da ‘ya’ya da mata da ba a san iyaka ba. Aika-aikar da tasa sai da gawawwaki suka yi iyo a cikin gulbin jini. Wanda kuma ya kai har ga qabarin Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wasallama; raudarsa ta cika maqil da jini. A qarshe kuma suka koma suka harbi Ka’aba da manjaniqu, ya roshe, suka kuma liqa mata wuta; ta ci ta canye. Akwai varnar da ta kai ga haka?

Me zai sa waxannan mutane su yi shayin la’antar mai irin wannan aiki? Ko sun manta da cewar da Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wasallama ya yi: Allah zai sanya duk wanda ya kashe Husaini a cikin wani akwati na wuta, ya kuma yi masa rivin azabar da zai yi wa ‘yan wuta. Ta hanyar xaure hannuwansa da qafafunsa da wata sarqa ta wuta, a tungumi akwatin a jefa wuta ya yi qasa.Ya dinga wani wari da ko ‘yan wuta sai sun roqi Ubangiji tsari daga gare shi. Haka zai tabbata cikinta har abada, yana shan azaba mai raxaxi. Duk lokacin da fatar jikinsa ta nina ta kware, sai Allah ya mayar da ita sabuwa fil, don azabar ta shigeshi sosai; da minti xaya ba za’a sassafta masa ba.Ana yi ana shayar da shi ruwan zafin jahannama.Kaico qaryar maqaryata ta qare sun shiga hannun Allah.

 Xan Shi’ar ya rufe da cewa: Kuma wai Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wasallama ya ce: “Hushin Allah da nawa sun tsananta a kan wanda ya zubar da jinin zuri’ata ya kuma lave da su ya cutar da ni”.

Martani:

 Babu wani dalili da zai sa a la’anci Yazidu shi kaxai domin kuwa bai cancanci hakan ba; duk kuwa wanda ya dage akan tabbatar da la’ana a kansa to kamar yana cewa ne takwarorinsa daga cikin wasu sarakuna da halifofin musulunci duk la’anannu ne, kai sun ma fishi zama haka. Domin kuwa duk wanda ya san tarihin musulunci, ya san cewa akwai dayawa daga cikin shugabanni waxanda Yazidu yafisu dama-dama, kamar: Mukhtar xan Abu Ubaidu as-saqafi, sarkin Iraqi.Wanda ya tsaya kai da fata akan xauko wa Husaini fansa ta hanyar azzabtar da waxanda suka kashe shi.Wanda qarshe yai da’awar cewa Jibirilu ya zo masa da wahayi .haka kuma Yazidu yafi Hajjaju xan yusuf dama.

 Domin kuwa gaba xayan mutane sun yi ittifaqi a kan cewa zaluncin Yazidu bai ko kama qafar nasa ba.

 To, kuma dai duk da tabbatar haka,qololuwar hukuncin da ake iya yanke wa Yazidu da waxannan sarakuna takwarorinsa da makamantansu, shi ne na kasancewa “fasiqai” amma ba a la’ance su ba.Domin kuwa babu inda shari’a tayi umurni da la’antar wani fasiqi.

 Nau’in mutanen da Sunnah ta zo da lafuzzan la’antar su sanannu ne. Kamar cewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi: Allah ya la’anci varawon da zai saci qwarar qAai har a yanke masa hunnu. Da cewar da ya yi:Allah ya la’anci wanda ya qirqiro bidi’a ko ya daurewa mai qirqiro ta gindi. Da kuma cewar da ya yi: Allah ya la’anci mai cin riba da kuma mai bayar da ita da mai rubuta ta da mai shaida akan ta. Da kuma cewar da ya yi: Allah ya la’anci mai auren xibar wuta da wan da akeyinsa don shi. Haka kuma da cewar da ya yi: Allah ya la’anci giya da mai shirya ta da kayan haxinta da xan dakon ta da abin da ake xaukar ta a ciki, da mai rarraba ta ga mashaya, da wanda yaci kuxinta.

 To, ka ga ba zancen la’anta kenan,ga wanda ba xaya da ga cikin waxannan mutane ba.

 To, kuma kowancan abu da mutane ke ta yakutar Yazidu a kansa. Wato abin da ya aikata wa mutanen Al-harrah, ai akan hujja ya yi shi. Domin kuwa bai xauki wani mataki a kansu ba bayan sun yaya ta yimasa tawaye da qorar xan ginsa da ke wakiltarsa a can, sai da ya aika masu Manzo bayan Manzo, yana neman su dawo suyi masa da’a. Amma hakan ta ci tura. A qarshe dai ya yanke shawarar aika Muslimu xan uqbata al-mariyyu, ya kuma umurce shi da keta alfarmar Madina tsawon kwana uku waxanda ya halatta yaqi a cikin ta idan ya yi nasara a kansu. Haka kuwa akayi. To kaji abin da mutane ke qyama matuqa a cikin al’amarin Yazidu. Wanda har watarana aka cewa Ahmad: ko zaka iya karvar hadisin da aka samo da ga Yazidu? Ya ce Allah ya sawwaqe. Ashe ba shi ne ya yi wa mutanen Madina abin da ya ga dama ba?!

 Wannan kam gaskiya ne ya tabbata.Amma bai sa aka qarar da irin sharifan ba. kuma adadin waxanda aka kashe bai .kai dubban xaruruwa ba. Kuma jini bai malala har hubbaren Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba, balle ya maqare raularsa. Artabin da aka yi ma a lokacin ba a cikin masallaci aka yi shi ba.

 Wannan kenan. Ita kuwa Ka’aba da ya ce wa an rusa an qona, wannan ba gaskiya ba ne. Domin kuwa Allah ya riga ya xaukaka ta ya girmamata, ya bata cikakar kariya, ta hanyar sakata qarqashin kulawar sa.

 Babu wani lokaci; kafin musulunci ko bayansa, da Allah ya taba yar darwa wani tozarta wannan xaki nasa mai alfarma. Ai ka dai ji irin yadda ya yi biji-biji da ashabul fili, A lokacin da suka yi nufi tava dakinsa. Duk duniya babu wanda bai ji har gowar su ba.

 Kuma tarihi ya tabbatar da cewa, ba a tava samun wani daga cikin sarakunan musulunci ba. Tun daga Umawiyyawa har Abbasiyawa da hakimansu, wanda ya tava nufar Ka’aba da wani mugun nufi; Babu wani daga cikin wakillan Yazidu ko Abdulmalik; Hajjaju xan Yusuf ko waninsu da ya tava nufatar haka.

 Abin da ya tabbata shi ne, gaba xayan musulmi, na matuqar girmama wannan daki na Allah. Abida ma yakawo Ka’aba a cikin wannan mas’ala shi ne shigar da Ibn Zubairu ya yi a cikinta, wanda shi ne dakarun Yazidu suka so datsewa, har suka har ba masa manjariqu. Amma ba a Ka’abar sukayi niyyar harbi ba.

 Wani abu da kuma zai qara tabbatar maka da cewa ba Ka’abar ce sukayi niyyar harbi ba shi ne, shigar da sukayi cikin masallacin bayan sun kashe xan Zubairu, suka yi xawafi. A matsayin hajjin wannan shekaara, a qarqashin jagorancin Hajjaju wanda ya gudanar da ibadar akan tafarkin xan Umar, ba tare da ya sava masa ko da a mas’ala xaya ba, kamar yadda Abdulmalik xan Marwanu ya hore shi da yi.

 Ka ga a hankalce, da a ce sun zo ne da nufin tozarta Ka’aba da keta alfarmarta, da sun mayar da ita labari,tunda sun sami galaba da iko a kan haka. Kamar dai yadda suka aika da Zubairu lahira da ya shiga hannun su.

 Haka kuma hadisin da xan Shi’ar ya kawo, wanda ya bayyana halin da wai, wanda ya kashe Husaini zai sami kansa a ranar qiyama, qar ya ce lafiyayya, tun daga far kon sa har qarshe ( ina fatar baka manta da hadisin ba).

 Ko shakka babu wannan hadisi maganace irin ta shaqiyyan mutane maqaryata, waxanda basu jin kunyar yi wa Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam yaye-yayen qarya. Ah! To, idan ba haka ba,ya za’ace a hukunta wa wani mutum xaya xaukar rabin azabar gaba xayan ‘yan wuta kan wani laifi? Wa ma ke iya kimanta rabin azabar ta su? balle Kadubi irin azabar da Allah ya tanadar wa Alu Fir’auna da Alu ma’idata da munafukai da sauran kafiran duniya. Haxa da wadda ya tanadarwa waxanda suka kashe Annabawa ba li ba la, da waxanda suka kashe nagartattun bayi magabata. Al’amarinfa na da matuqar girma.

 Na kuma tabbata cewa baka musun kasancewar zunubin waxanda suka kashe halifa Usmanu, ya fi na waxannan da suka kashe Husaini Raliyallahu Anhu girma nesa ba kusaba. To, irin wannan wuce gona da iri a cikin sha’anin Husaini ta wannan fuska, daidai yake da azarvavin Nasibawa da suke raya cewa matsayin Husaini daidai yake dana Harijawa (‘yan tawaye) sa boda haka in an kashe shi an kashe banza. Dalilinsu kuwa a kan haka wai shi ne cewar da Annabi sallallahu Alaihi Wasallam ya yi: duk wanda ya taras da ku qar qashin jagorancin mutun xaya,ya so ya xaixaitaku, to ku sare kansa da takobi, ko xan waye. Muslimu ne ya riwaito hadisn, kai ka ji.

 To, amma mu Ahlus-Sunnah wal jama’a, mun yi Allah wadai da waxannan ra’a yoya guda biyu na ‘yan Shi’a (‘yan Shi’ah) da Nasibawa; ba mu tare da kowannensu.

 Mu a wurin mu, Kisan gillar da aka yi wa Husaini zalunci ne, kuma ya yi shahada. Waxanda kuwa sukayi karen aikin mutanen banza ne tantirai. Sannan kuma hadissan da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi umurni cikinsu da kashe duk wanda ya yi nufin xaixaita al’ummarsa, ba su shafi Husaini ba.

Ah! Ta yaya ko za su shafe shi Raliyallahu Anhu tun da bai yi nufin fasa taron jama’ar Amada ba. Kuma ko da aka kashe shi yana bisa niyyar xayan abubuwa guda uku ne: ko dai ayar de masa ya koma inda yafi to, wato garin su. Ko ya yi sansani a wani wuri, a matsayin mai ribaxi. Ko kuma abashi dama ya yi tozali da Sarkin Musulmi Yazidu.

Ka ga babu xaya daga cikin waxannan abubuwa uku, da za’a iya fahimta a matsayin wariya da yuqurin basa garke, ko da akan tawili. Tafi munji waxanda ya nemi xaya daga cikin waxannan da mamaki daga gare su, adadin su bai tava kara ya karya ba, idan akayi la’akari da gaba xayan jama’ar Yazidu, na gida da dawa. Amma duk da haka, tunda har ya roka, to ya zama wajibi a karva masa.

Babu wani dalilin da zai sa ayi kunnen uwar shegu da shi, a matsayinsa na jikan Manzon Allah. Domin kuwa a hankali da shari’a, ko wanda bai kai darajarsa ba, ya nemi alfarmar xaya daga cikin waxancan abubuwa, ba ya halatta aqi saurarensa, Balle abashi baya ko a tage shi, Daxa balle a aikashi lahira.

Wannan ita ce aqidar Ahlus-Sunnah wal jama’a a kan wannan mas’ala.

Wannan kenan, haka kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Hushin Allah da nawa ya tsananta a kan duk wanda ya zubar da jinin wani daga cikin dangina ko ya lava ga zuri’a ta ya cutar da ni. qar ya ce.

Magana ce da babu wan da zai yarda da ta fito daga bakin ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallama sai jahili. Domin kuwa imani da tsoron Allah Subhanahu WaTa’ala ne ya kamata agindaya a matsayin garkuwa da gambun tsari ga ran Hasan da Husaini, da ma kowane musulmi, ba dangantaka ba, ina fatar ka gane. Ah! Yau da wani daga cikin mutanen gidan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai aikata wani laifi, da hukuncinsa kisa ne ko datse hannu sai a ce: a’a tunda Ahlul baiti ne shi ya sha! Halas ne bisa haxuwar musulmi, Kai! Wajibi ne a zartar masa da hukuncin yadda za’a zartar wa kowa. Ko banza ingantattar magana ta zo daga shi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yana cewa: Haqiqa abin da ya halakar da waxanda suke a gabanin ku shi ne kasancewar suna qyale wanda ya yi sata daga cikinsu idan xan wane ne. Amma idan ya-ku-bayi ne, nan take za su zartar masa da haddi. To, ku sani wallahi da yau Fatima ‘yar Muhammadu za ta yi sata (Allah ya tsare) wallahi sai na yan ke hannunta.

Subhanallahi! Allah ya daxa tsira gare ka da aminci.

Ka ga shugaban talikai ya tabbatar maka da cewa da Fatima za ta faxa cikin wannan tarko, ba zai tsamo ta ba don tana ‘yar cikin sa. Ka kuwa san, babu wanda Annabi ke so a cikin iyalansa kamarta.

Kuma idan baka sani ba. A kan haka ne malaman musulunci suka haxu a kan wajabcin jefe Bahashime har lahira, da zai yi zina, yana kuma da aure ko ya tava yi, da kashe shi, da zai kashe wani akan ganganci, babu sixixi ba saxaxa. Ko da kuwa wanda ya kashe bahabashe ne, ko barume ko baturke ko badaulame.

Kuma ai ta tabbata cewa: Annabi Sallalahu Alaihi Wasallama ya ce: Farashin jinanen musulmi xaya ne.

Wato ma’aiki na cewa ne: jinin bahashime baifi na waninsa tsada ba. Matuqar dai sun yi tarayya a qarqashin lemar xiyauci da musulunci. Kuma a kan haka ne gaba xayan al’ummar musulunci ta sandare. Ka ga kenan hukuncin da za’a zartar wa wanda ya zubar da jinin bahashime shi za’a zartar wa wanda ya zubar da na wanda ba shi ba, matuqar dai ba da alhakinsu ba.

To, idan kuwa haka ne, ka ga ba wanda ya isa, ko xan uban waye. Ya ce mana wai Annabi Sallalahu Alaihi Wasallama ya ware mutanen gidansa da wata daraja, ta tsanantar hushin Allah a kan wanda ya zubar da jininsu. Ai adinin musulunci ba shegantaka ne ba.

Abin da Allah Ta’ala ya haramta shi ne kashe wata rai ba akan haqqi ba. Amma duk wanda za’a kashe a kan wani haqqi na shari’a, ko shi xan waye ko jikan wa, Bahashime ne ko waninsa, ba ruwan Allah balle har hushinsa ya tsananta a kan wanda ya zartar da hukuncin kisan a kansa.

Wanda Allah ke hushi, ya kuma ya la’anci wanda ya kashe shi, tare da tanadin azaba mai girma ga makashi, da yanke masa hukuncin dawwama cikin wutar jahannama, shi ne muminin da aka aika lahira bai ji bai gani ba.

Abin da ke sa jinin mutum ya tsira ko ya halatta a shari’ar musulunci, abu ne da ya kundume bani hashim da wanda ba su ba.

Irin waccan magana ta banza, babu wanda ke jingina ta ga Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wasallama sai munafuki. Wanda ke son gurvata tsarkaken ruwan annabcinsa. Idan kuwa har ba munafuki ba ne, to lalle kuwa jahili ne, wanda bai san irin adalcin da Allah Ta’ala ya aiko Muhammadu don tabbatarwa ba.

Cewar da xan Shi’ar ya yi, hushin na Allah da manzon sun haxa da: wanda ya lave ga zuri’ar manzo ya cutar da shi.

To, duk da yake gaba xayan hadisin bai ingantaba. Amma ai ana iya lavewa ga al’ummar Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wasallama ko sunnar sa a cutar da shi domin kuwa ko shakka duk wanda ya keta alfarmar waxannan abubuwa biyu, dai dai yake da wanda ya keta ta zuri’arsa, kuma duk cutarwa ce gareshi Sallalahu Alaihi Wasallama yin haka kuwa haramun ne tabbas.

 2.10 Garin Neman Qiba an Samo Rama

A qoqarin ‘Yan Shi’ah na ganin jikinsu yafi na musulmin duniya yin vul-vul, sai gashi sunfi kowa rama, wanda hakan ta sa mazahabarsu zama cibiyar vata da varnace-varnace. Bari kaji..

Xan Shi’ar ya ce: Muna son masu hankali da su sa idon basira su gane mana waxanda sukafi cancanta da amincin Allah, tsakanin waxanda su ka tsarkake Allah da mala’ikunsa da Annabawansa da imamansa. Suka kuma tsarkake shari’ar sa daga duk wata qazanta. Da waxanda suka vata sallar su sanadiyar qin yin salati ga imaman da Allah ya zavar masu. Suka koma suna ambaton imaman wasunsu, shin waxannan ne suka fi ko waxanda suka tsaya kan zavin Allah suka watsar da wanin sa?

Kaji tambayar mutumin naka!

Martaninmu a nan shi ne: qoqarin da kuka yi na kore wa Allah Ta’ala waxancan siffofi na kamala, waxanda suka hada da: Rayuwa, ilimi, qudura, magana, cikakken iko, so, qi, yarda da fushi. Sai ka ce Allah yafi qarfin waxannan siffofi balle ya siffanta da su. Kuma wai za’ayi su dace dashi tunda sandararrun abubuwa da siffofi ma na da su?.

To ku sani wannan ba wani abin mazan gwari ne ba. Nakkasa alqaxarin Ubangiji ne da Annabawansa kuka yi. Kuma zance ne kuka yi irin na jahamiyawa. Waxanda ke cewa: Tsarkake Allah daga kama da wanin sa, na wajabta kore waxancan siffofi daga gare shi. A kan haka sukace Allah Ta’ala ba ya da rai, jahili ne, kasasshe, kurma, kadar kasuwa. Bai so bai qi, bai yarda bai fushi. Ba a ganin sa, kuma ba ya da hannu a cikin komai. Kuma a karansa, ba ya iya sukkuna komai.

To ka ga haka, sun kamanta Allah da sandararrun abubuwa nakkasassu;

adai dai lokacin da suka kore masa siffofin cika da kamala. Ka ga kenan

wannan ba tsarkakewa ce ba. Qazantawa ce da gurguntawa.

Abin da ake cewa tsarkakewa a wannan babi, shi ne: kore wa Allah duk wata naqasa da ke takin saqara da wata siffa ta kammala ta yarda ba ta yiwuwa su sha innuwa xaya. Wato a kore masa: mutuwa, da angaje, balle barci. A kore masa: kasawa, jahilci, da bukata, kamar yadda ya kore wa kansa su a cikin littafinsa. Wato a lokaci xaya, tabbatar masa da duk wata siffa ta kamala, tare da kore masa kishiyoyinsu; na naqasa. A kuma tsarkake shi da ga yin kama da wani abu daga cikin halittarsa, ta kowace fuska, tare da kore masa duk wata naqasa, ba tare da iyakancewa ba. Haka kuma a tsarkake shi daga yin kama da wani abu a cikin waxancan siffofi da aka tabbatar masa na kamala.

Wannan kenan. Ta vangaren Annabawa kuma, sai aka wayi gari kun kore masu abin da Allah Ta’ala ya tabbatar masu na kamala da xaukakar daraja. Waxanda ke samuwa garesu ta hanyar tuba da neman gafara. Wanda hakan ke xaukaka darajar su ninkin-ba-ninkin. Da wannan mugun aiki naku, sai aka wayi gari kun qaryata abin da Allah Ta’ala ya fadawa duniya ta wannan fuska; kuka canza wa tuwo suna. Kuka ce wai ciratar xan Adamu daga duniyar jahilai da vata da zalunci zuwa ta ilimi da shiriya da adalci, naqasa ne gare shi.

Kun jahilci kasancewar haka wata ni’ima da qudura mafiya girma daga wurin Allah. A inda yake xaukaka darajar wasu bayi nasa daga matakin naqasa zuwa na kamala. Ta yadda xayan su zai iya kasancewa mai iko akan xanxana alheri da sharri, da tantance banbancin su. Har a wayi gari son da yake na ganin alheri ya tabbata, sharri ya gushe, ya shafe na wanda alheri kawai ya sani. Kamar yadda Umar xan Haxxabi Radiyallahu Anhu ya ce: Ba za a iya yi wa musulunci sukuwar salla, a yi wa xan mansa dai dai ba. Sai an wayi gari al’umma ta haifi wanda bai son komai na jahiliyya ba.

Wannan kenan.Shi kuwa zancen tsarkake imamai, wani abu ne na kunya da bai kamata mai hankali ya fada ba,musaman ixan akayi la’akari da wancan imamin mai taken “Malam Babu”,wanda baya da wani amfani duniya da lahira.

Haka kuma zancen tsarkake shari’ah daga qazanta da qasqanci, wani abu ne tuni an riga an rufe littafinsa. Domin kuwa bayani ya riga ya gabata akan cewa a cikin mas’alolin da Ahlus-Sunnah suka yi ittifaqi a kansu a matsayin shari’ah, babu xaya da keda ko da amon qazanta balle qasqanci. Savanin ’yan Shi’ah waxanda mazahabarsu ke maqil da qazantattu kuma qasqantattun mas’aloli irin waxanda ba mai su a duniyar musulunci.

Bari kuma mu koma ga cewar da ya yi:.........ko waxanda su ka bata sallarsu sakamakon qin yin salati ga imaman da Allah ya zabar masu. Suka koma suna ambaton imaman wasunsu.

To, a nan xayan biyu. Ko dai ya kasance xan Shi’ar na nufin yi wa imamai goma sha biyunan nasu salati wajibi ne. Koko a’a, wajibi dai ne a yi wa wani kevantacce daga cikinsu, ko kuma wani can baqon haure; wanda dai ba Annabi Sallalahu Alaihi Wasallama ba. Ko kuma ya kasance yana nufin yin salati ga mutanen gidan Annabi Sallalahu Alaihi Wasallama kacokwan wajibi ne.

Idan xan Shi’ar na nufin fassara ta farko, to, ko shakka babu hakan ta tabbatar da kasancewarsu kwatarnen vata da varna, da yi wa shari’ar Muhammadu Sallalahu Alaihi Wasallama tawaye. Domin kuwa da mu da su babu wanda tilas ba ta sa ya san cewa Annabi Sallalahu Alaihi Wasallama bai umurci musulmi ya yi wa wani daga cikin imaman nasu goma sha biyu salati ba, daxa ko a cikin sallah ne ko wajen ta. Kuma babu wani musulmi ma da aka samu yana aikata haka a zamaninsa. Babu kuma wanda ya riwaito haka daga Annabi Sallalahu Alaihi Wasallama, ta hanya ingantatta ko mai rauni. Kai! Hasali ma ba wajibi bane a kan wani musulmi ya riki xaya daga cikin imaman goma sha biyu shugaba, alhali ga Annabi raye, balle har yi masa salati acikin sallah ya zama wajibi.

Duk kuwa wanda ya ce yi wa waxannan imamai salati cikin sallah wajibi ne, har kuma ya vata sallar wanda bai yi haka ba, to ya canza alqiblar addinin MuhammaduSallalahu Alaihi Wasallama ya mayar da shi wani abu, kamar yadda Yahudawa da nasara suka sauyawa addinin Annabawansu fasali.Wannan abun da ‘yan Shi’ah ke qoqarin tabbatarwa, baya tabbatuwa. Domin kuwa sallar da musulmi suka yi zamanin rayuwar Annabi, ingantattace bisa haxuwar kan al’umma tabbas. Tattare kuma da rashin yin salati ga imaman a cikinta.

Idan kuwa xan Shi’ar ya ce a’a muna nufin fassara ta biyu ne, wato wajabcin yin salati wa mutanen gidan su Annabi Sallalahu Alaihi Wasallama saboda matsayin da suke da shi.

To, sai mu ce masu: Mutanen gidan su Annabi yawa ne da su. Matansa kaf, da gaba xayan banu Hashim, har ma da banu Abdul-muddalibi, a bisa wani zance, duk Ahlun-nabiyi ne. Kuma Shi’ah imamayya ba su ganin mafi yawan waxannan bayin Allah da gashi a kai. Domin a wurin su abbasiyyawa ba kowa ba ne. Musamman halifofi daga cikinsu. Ga shi kuwa suna daga cikin Ahlu Muhammadin. Haka kuma suna sukar lamarin duk wanda ya yarda da shugabancin Abubakar da Umar Radiyallahu Anhum. Ga shi kuma mafi rinjayen banu Hashim sun yarda da shugabancinsu, Duk wanda yake xan halas daga gidan Hashim yana tare da Abubakar da Umar Raliyallahu Anhumam sai fa ‘yan qwarori. Amma in ban da su, duk wani ma’abuci ilimi da kishin addini a wannan gida baya qyamar Abubakar da Umar Raliyallahu Anhumam.

Babban abin ban mamaki ko ince ban ta kaici da waxannan ‘‘yan Shi’ah, duk bai fi tattare da irin tinqahon da suke yi na so, da girmama mutanen gidansu Annabi Sallahu Alaihi Wasallama. Sai gashi kuma sune a gaba, a lokacin da Tatar suka far wa bagadaza, Hedikwatar Hilafar musulunci a lokacin. Su dai ‘yan Shi’ah nan sune suka yi masu jagora suka salwantar da rayukan musulmi Hashimawa. Waxannan Allah ne ka xai yasan adadinsu, balle daxa waxanda ba su ba. Suka kuma kashe kusan mutum dubu xari da goma sha takwas da xari tara da saba’in a cikin sasannin Bagadazar. Suka kuma kashe Halifan lokacin, Ba abbase. Suka ribace mata da kananan yaran Hashimawa; Aka hada kan ‘yan matan Hashimawa da wasunsu duk aka kai wa Yazidu da takwarorinsa sarakuna. Duk haka ta farune da taimakon ‘rafelawa.

Ka ko ga babu wata qiyayya da za’a nuna wa Alu Muhammadin Sallalahu Alaihi Wasallama wadda ta kai haka. Ko shakka babu.

Kai! In ta kaice maka labari, babu wani abu da ‘yan Shi’ah za su soki lamirin wani da shi, a wannan babi, face hakan tafi cancanta da su ,nesa ba kusa ba.

 2.11 Na Gaba ya yi Gaba

Xan Shi’ar ya yi qoqarin karkata akalar wasu darajoji na Sayyidina Ali, tare da kafa hujja dasu, don tabbatar da fifiko da imamancinsa. Ga abin da yake cewa:

Abu na shida: Ai ba da banza jama’ar Shi’ah ‘yan-sha-biyu suka zavi Sayyidina Ali a matsayin shugaba abin yi wa da’a ba gare su, sun yi haka ne saboda ganin irin darajoji da martabobin da basu qidayuwa. Waxanda masoya da magabatansa su ka riwaito, waxanda kuma ke tabbatar da kasancewarsa xan goma.

Bayan wannan kuma sun ga iri aibubban da wai junansu su ka riwaito a kan wasu Sahabbai waxanda yawansu ya zarta hankali amma ba su samo aibi ko xaya ta a kan sayyidina Ali. To wai a kan haka ne su ka sakakance da babu wanda ya cancanci saurarawa da shiga gaban sahu sai shi, wai saboda ya sami shedar tsarki daga bakin masoya da maqiya.

Sun kuma yi watsi da duk wanda ba shi ba, saboda ganin waxanda ma suka yarda da shugabancin nasa, sunyi masa raxan-raxan ta hanyar riwaito abun kunya a kansa. Wanda hakan ke hana shugabancinsa karvar sunansa a shari’a.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa, kuma yanzu za mu ambaci kaxan daga cikin darajojin Alin, waxanda suka inganta a wurin Ahlus-Sunnah. Domin kuwa littafai da zantukan da suka aminta tare da dogara a kansu duk sun naqalto su. Za mu kuma yi haka ne, don ta zama hujja a kansu ranar alkiyama. Inji shi.

Daga cikin waxannan darajoji akwai abin da Abul-Hasan Al-Andalusi ya riwaito a cikin littafin: Al-jam’u Bainas-sihahis-sitta, da: Muwaxxa Maliku, da ingantattun littafan Buhari da Muslimu, da sunanu Abu Dawuda, da sahihu Tirmizi, sahihu Nisa’i, daga Ummu–Salmata matar Annabi Sallalahu Alaihi Wasallama wadda tace: Ayar da Allah Ta’ala ke cewa: Allah na nufin ya tafiyar da kazanta kawai daga gareku, ya ku mutanen babban Gida! kuma ya tsarkake ku, tsarkakewa.(33:33) ta sauka ne ga Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wasallama a lokacin da yake xakinta. Ta ce: a lokacin ina zaune daura da kofa. Sai na ce ya Manzon Allah! ina fatar dai ni ma ina daga cikin mutanen gidanka xin nan, sai ya karva mata da cewar: Anya? Ina dai yi maki fatar alheri ki na dai daga cikin matar Annabin Allah. Taci gaba da cewa: A lokacin da wannan abu ke faruwa, Ali da Fatima da Hassan da Husaini Radiyallahu Anhum duk suna cikin xakin nawa. Sai kuwa ma’aiki ya yafa masu mayafinsa, ya ce: Ya Ubangiji waxannan su ne mutanen gidana. Allah ka tafiyar da kazanta daga garesu, ka kuma tsarkake su tsarkakewa.

To abin da za mu gayawa wannan xan Shi’ar a matsayin martani, a kan wannan magana shi ne: Na farko dai ya sani, Nagaba ya yi gaba. Domin kuwa darajojin halifa Abubakar da Umar Radiyallahu Anhum waxanda suka tabbata a cikin ingantattun hadisai, sun fi waxanda suka tabbata na darajojin halifa Ali Radiyallahu Anhu yawa da kabri.

Kuma waxannan hadisai da ya ambata. Ya ce kuma suna kunshe a cikin ingantattun littafan hadisan Jumhurun musulmi, kuma wai amintattun littafai da zantukan su duk sun nakalto su, qarya ce yake yi wa Jumhurun. Domin kuwa masana ilimin hadisi sun yi ititfaqi a kan kasancewar mafi yawan waxancan hadisai da ya ambata qarya, ko masu rauni. Su ku wa waxanda suka inganta daga cikinsu ba su xauke da wani abu da ke nuna imamancin Ali, ko fifikon darajar sa a kan Abubakar da Umar. Hasalima bai kevanta da darajojin da hadisan suka qunsa ba; ya dai yi tarayya da wasu ne daga cikinsu. Savanin darajojin da suka tabbata na Abubakar da Umar Raliyallahu Anhu waxanda babu wanda ya yi tarayya da su, a cikin mafi yawan su. Musamman ma dai Abubakar Raliyallahu Anhu wanda bai yi tarayya da kowa ba a cikin gaba xayan darajojin da ya kevanta da su.

Su kuwa abubuwan kunyar da ya ce an riwaito na waxannan halifofi uku, wai ya sani sun fi qarfin haka. Idan ma har wani abu ne, sai dai a ambace shi “qorafi”. Amma ba abin kunya ba. Sannan kuma, babu wani qorafi da za’ayi kan su, face akwai kwatankwacin sa ko wanda ya fi shi, da za’a iya yi kan Ali Raliyallahu Anhu.

Ka ga da haka, ta tabbata duk abin da ya faxa a wannan fasali kar ya ce cas. Nan gaba kaxan kuma za mu tona asirinsa a kan haka, dalla-dalla, in Allah ya so.

Wannan kenan, idan kuma ba ka manta ba, xan Shi’ar ya ce wai: Shi’ah ‘yan-sha-biyu sun riki imamu Ali shugaba a gare su. Saboda ganin irin yadda masoya da magabata suka yi masa wankan tsarki, tare kuma dayin biris da duk wanda ba shi ba. Saboda kasancewar har waxanda ma suka yarda da shugabancinsu nada qaiqayi a zukatan su a kansu.

To, kafin muje ko ina, muna tabbatar wa ‘yan Shi’ah cewa wannan magana qarya ce. Domin kuwa waxanda ba su yarda da Ali Raliyallahu Anhu ba, su ne kan gaba wajen sukar sa. Hasali ma yawan QungIyoyin da ke sukar lamirin sa su ne mafiya rinjaye, idan akayi la’akari da masu qorafe-qorafe a kan Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhu da kuma waxanda suka wuce wurin cikin girmama Alin kansa; wato “Gulatu”.

Ka ga dai tumun fari, Harijawa sun yi ittifaqi a kan kasancewar Ali kafiri. Wai Kuma duk da haka sun fi Gulatu daraja a idon musulmin qwarai; saboda su Gulatun, a wurinsu Sayyidina Ali Allah ne. Sukan kuma sassafta wani lokaci su ajiye shi matsayin Annabi.

Ba wannan kawai ba. Jamhurun musulmi sun fi ganin Harijawa da sauran Sahabban da suka shaya daga da Ali tare da su, da gashi aka, a kan ‘‘yan Shi’ah masu aqidar biyar imamai goma sha biyu. Waxanda ke kan aqidar kasancewar Alin imami ma’asumi.

Wani abun kuma da zai qara tabbatar wa ka da irin yadda halifofin can uku na kafin Ali, suka yi masa fintinqau a wannan fage, shi ne irin gaba xayan al’ummar Amada ke saka masu bakin albarka, idan ka cire ‘yan Shi’ah la’anannu. Duk da kuwa Harijawan can da ke kafirta Ali Raliyallahu Anhu da Marwaniyawa da suka xauke shi matsayin wani qasurgumin azzalumi. Suka kuma sa qafa sukayi fatali da halifancinsa. Duk waxannan mutane sun yarda da shugabancin Abubakar da Umar, har ma da na Usman Raliyallahu Anhu tare da zama qarqashin tutocinsu, tattare kuwa da kasancewar babu zumunci a tsakaninsu da su ko na anini. To, ta yaya za a ce wai masoya da magabata su yi wa Ali Raliyallahu Anhu wankan tsarki, tare da yin kunnen uwar shegu da waxancan halifofin uku. Alhali kuwa wannan ingantattar magana da muka fada ta cika kunnen duniya?

Haka kuwa tabbataccen abu ne cewa mutanen da ke sa wa waxancan halifofi uku bakin albarka daga cikin wannan al’umma, su ne mafi yawa da girman daraja a cikinta. Su kuwa masu yi wa Ali Raliyallahu Anhu kwarar vawan kalgo, ta hanyar naxa masa rawanin kafirci da fasiqanci da varna, qungiyoyi ne sanannu kuma tantantattu. Amma kuma tattare da ha akan sun yi wa ‘‘yan Shi’ah ko-ta-kwana a fagen ilimi da kishin addini, da qarfin tuwo. Ko alama ‘‘yan Shi’ah ba su kai su ba a wannan fage. Balle su yanke su da takobin hujja ta hankali da basira, ko su goga a kaifunsu a kan fandun dutse ranar fama.

Kuma kasan wani abu? Babu qungiya xaya daga cikin qungiyoyin can da ke kafirta Ali ko ganinsa azzalumi, da aka sheda da wani aiki na ridda. Savanin waxanda ke kuxa da kwarzanta shi tare da sukar lamirin waxancan duwatsu guda uku na daular musulunci. Wato kamar Nusairiyya (Al-Galiyah) waxanda ke jin shi Allah ne. Da Isma’iliyah (Al-Mulhidah) waxanda har gwamma Nasiriyya da su. Da kuma Galiya, waxanda ke jin shi Annabi ne. Duk waxannan qungiyoyi kafirai ne murtaddai. Bisa shaidar Allah da Manzonsa da duk wani malamin musulunci na gari.

Ko shakka babu duk wanda ke da masaniya da addinin musulunci komai qanqantarta, ba ya musun kafirci duk wanda ya naxawa wani mutum rawanin ubangizantaka. Ko ya yi imani da wani Annabi bayan muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama koko a’a anabcin ba nasa ba ne, na Aliyu ne mala’ika Jibrilu ya kai masa a kan kuskure.

Haka kuma ba ya musun musulncin Harijawa. Waxanda ke kafirta

Ali Raliyallahu Anhuda la’antarsa. Da kuma na waxanda suka yaqe shi suka kuma la’ance shi daga cikin Sahabban Mu’awiyah da Bani Marwanu da wasunsu. Waxannan mutanen gaba xayan su musulmi ne. Domin sun yarda da musuluncin da shari’o’insa; suna salla, suna azumi, suna zakka, suna hajji. Suna kuma haramta duk abin da Allah da Manzonsa suka haramta. Babu mutum xaya daga cikinsu wanda kafircin sa ya bayyana. Duk wanda ya san tarihin musulunci ya san waxannan mutane na matuqar girmama musulunci da shari’o’insa.

Ka ga hakan ta tabbatar mana da cewa,cewar da xan Shi’ar ya yi wai gaba xayan magabata sunyi wa Sayyidina Ali wankan tsarki, savanin waxancan halifofi uku, qarya ce kawai.

 2.13 Hadisin Mayafi ba Hujja ba ne

Shi kuwa hadisin mayafi ko shakka babu ingantacce ne. Domin kuwa Ahmada da Tirmizi sun riwaito shi da ga cikin hadisan Ummu Salma. Haka kuma Muslimu ya riwaito shi a cikin ingantaccen littafinsa, daga cikin hadissan Aisha, wadda tace: Watarana da hantsi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya fita yafe da wani mayafi mai faxi na baqin gashi. Sai ga Hasan xan Ali ya iso, sai ya gayyace shi ciki. Sai kuma ga Husaini ya iso,shi ma ya gayyaceshi, sai kuma ga Fatima ta iso, ita ma ya gayyace ta, qarshe kuma sai ga Ali ya iso, shi ma ya gayyace shi ciki. Sannan ya ce: Allah na nufin kawai ya tafiyar da qazanta kawai daga gare ku ya ku mutanen Babban Gida! Kuma ya tsarkakeku tsarkakewa (33:33).

Abin da muka son tabbatarwa anan shi ne,wannan hadisi tattare da ingancinsa, ba ya zama hujja akan imamancin Ali,kamar yadda xan Shi’ar ke qoqarin tabbatarwa.

Dalininmu shi ne: Kasancewar ba Ali kawai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya gayyata a cikin mayafin ba,balle ace ya gayyaci Fatima, Hassan da Husaini, ka kuwa san mace bata shugabanci, ka ga kenan wannan falalar bata nufin tabbatar da lasisin shugabanci ga waxannan mutane.A’a abu ne da wasu keda hakki a kansa.

Iyakar fassarar da wannan hadisi ke iya xauka itace: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya roi Allah ya tafiyar da kasanta daga waxannan mutane, ya kuma tsarkake su tsarkakewa. Wato su zama mutane masu tsoron Allah a dalilin tsarkin can da tsarkakewa.

Shi kuwa nisantar qazanta da Allah ya yi alkawali abu a kan kowane mumini, kamar yadda aka ambaci gaba xayan mumine da tsarki. Dubi abin da Allah ke cewa: Allah baya nufin domin ya sanya wani kunci a kanku kuma amma yana nufin domin ya tsarkake ku, ya kuma cika ni’aimar sa a kanku (5:6).

A wata ayar kuma ya ce: Ku karvi sadaka da dukiyoyinsu kana mai tsarkake su, sanan kana mai tabbatar da kirkinsu. (9:103).

A wata ayar kuma ya ce: Haqiqa, Allah yana son masu tuba, kuma yana son tsarkakewa (2:222).

To, ka ga iyakar abin da wanan hadisin ke nufi, shi ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya roi Allah Subhanahu Wa Ta’ala akan aikata alheri da nisantar sharri, Amma ba imamanci ba.

Ka kuwa ba afi Abubakar siddiqu Raliyallahu Anhu ba a fagen aikata alhairi. Tun da har Allah Ta’ala ya bayar da labarinsa da cewa, shi mafi taqawa ne wanda yake bayar da dukiyarsa, alhali yana tsarkaka. Alhali babu wani mai wata ni’ima wurinsa wanda ake neman sakamakonta. Face dai neman yardar Ubangijinsa mafi xaukaka. To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da za a ba shi) (92:17-21).

Haka kuma cewar da Allah ya yi: Kuma masu tserewa na farko daga Muhajirun da Ansar da waxanda suka bisu da kyautatawa, Allah ya yarda daga gare su, kuma ya yi masu tattalin gidajen aljanna: qoramu suna guxana a qarqashinsu. Suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma (9:100) na tabbatar da cewa waxannan bayin Allah sun tsaya tsayin daka akan aikata abin da Allah ya yi horo dashi, da nisan tar abin da Allah ya yi hani da shi. Domin sai da haka ne suke iya samun wannan sakamako na yar dar Allah.

Ka ga kena a haka, kanfa, kazantar da samun cikakken tsarki daga zunubi sun zama daga cikin siffofin su. Kuma sun yi tarayya da mutanen can huxu (ahlul baiti) a cikin wancan bakandamin du’a’i da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi masu.

Ba wannan ma ka wai ba, tarihi ya tabbatar da cewa akwai mutane da dama; ba waxancan huxun ba. Waxanda Manzon Allah ya roi Allah ya yi salati a kansu. Ya kuma rokar wa wasu masu yawa aljanna da gafarar allah da wasu muhimman abubuwa daba waxannan ba. Waxanda suka fi waccan du’a’i girma. Amma kuma hakan ba ta wajabta zaman waxanda ya yi wa du’a’in na biyu mafiya girma a kan sabikunal auwaluna.

Kuma dalilin da ya sa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi wa Ahlul- kisa’i wannan du’a’i, shi ne kasancewar nisantar qazanta da zankake wajibi a kansu. Saboda haka ya roi Allah ya taimakesu a kan tabbatar da haka. Don kada kashinsu ya bushe; su wayi gari ana Allah waddai da su, kuma cikin azaba.

Wannan du’a’i da Annabi ya yi masu, da kasancewarsa karvabbe a wurin Allah, zai sa waxannan mutane su zama abin madalla da lulluvewa da rahama.

 2.13 Tilas Mai Hawan Ruwa ya yi Babban Masaki

Xan Shi’ar ya yi qoqarin kafa hujja a kan fifikon darajar Ali Raliyallahu Anhu da imamancinsa, da ayar da Allah Ta’ala ke cewa a cikin ta:

﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ إِذَا نَجَيتُمُ ٱلرَّسُولَ فَقَدِّمُواْ بَينَ يَدَي نَجوَىكُم صَدَقَة ذَلِكَ خَير لَّكُم وَأَطهَرُ فَإِن لَّم تَجِدُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُور رَّحِيمٌ١٢﴾ المجادلة: ١٢

Ya ku waxanda suka yi imani! Idan za ku ganawa da Manzon Allah, to ku gabatar da ‘yar sadaka(58:12)

Xan Shi’ar ya kafa hujja da cewa, Sarkin Musulmi Ali xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu ya ce: Babu wanda ya yi aiki da wannan aya daga cikin Sahabbai sai ni. Kuma albarkaci na ne Allah ya sassautawa wannan al’umma al’amarin wannan aya.

Martani:

Ya kamata xan Shi’ar ya fahimta cewa wannan ummarni da Allah Subhanahu Wata’ala ya yi, na gabatar da wata ‘yar sadaka don gana wa da manzon. Bai zama wajibi a kan kowane musulmi ba. Balle wanda bai yi ba yayi laifi. Wajabcin ya ta kaita ne a kan wanda lalurar ganawa da manzo ta kama. To, kuma sai akayi sa’a, a lokacin da wannan ayar ta sauka Ali Raliyallahu Anhu ne kawai wannan bukatar ta ganawa da manzo ta kama. Bai kuma yi wata-wata ba sai ya gabatar da sadakar. Kamar yadda dai malamai suka yi ittifaqi.

Ka ga kenan, wannan ummarni dai- dai yake da ummarnin da Allah ya yi da yanka hadaya, ga wanda ya hada hancin aikin hajji da na umara lokaci xaya. Ko kuma wanda aka datse.

2.14 Ayar:

﴿أَجَعَلتُم سِقَايَةَ ٱلحَاجِّ وَعِمَارَةَ ٱلمَسجِدِ ٱلحَرَامِ ﴾ التوبة: ١٩

Xan Shi’ar ya ce an samo daga Muhammad xan ka’abu al-kwrari, wanda ya ce: Watarana Xalhatu xan Shaibata; xan Bani Abdud-xari, da Abbas xan Abdulmuddalibi, da Aliyu xan Abu xalib sun yi musanyyar alfahri wa junansu wai. Na farkon ya ce: In na ga dama sai in buxe Ka’aba in kwana ciki tun da a hannuna mabuxanta suke. Na biyun kuma ya ce: Ni kuma tunda ni ke shayar da Alhazzai ruwa, in na so sai in kwana a cikin masallacin. Shi kuwa na ukun, wato Sayyidina Ali, wai sai ya ce: To duk kusaurara. Ni nayi malinku. Don na share tsawon wata shida ina fuskantar Ka’abar ina sallah, kafin kowa ya yi. Kuma nine Antaru sarkin yaqin Manzon.

Wai rufe bakunan su keda wuya sai Allah ya saukar da ayar da ke cewa:

Shin kun sanya shayar da mahajjata da ruwar da masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, kuma ya yi jihadi a cikin hanyar Allah? Ba su dai-dai ta a wurin Allah. Kuma Allah ba ya shayar da mutane azzalumai( 9:19).

Martani:

Martanimu a kan wannan magana shi ne: Wannan hadisi dai qarya ne. Domin babu wani littafi daga cikin littafan hadisi da ya zo da shi. Kuma kayan cikin hadisin na daxa tabbatar da haka. Bari ka ji:

Mutumen can na farko da xan Shi’ar ya ambata; wato Xalhatu xan Shaibatu, babu shi a cikin kundin tarihin musulunci. Shaibatu xan Usmanu xan Xalhatu shi ne wanda aka sani mai hidimar xakin Ka’aba. Ka ga wannan kawai ya isa tabbatar da rashin ingancin hadisin.

Sannan cewar da ya yi wai xan Abbas ya ce: in na ga dama sai in kwana a cikin masallacin (Ka’aba) To, xan saurari wannan magana da kyau. Ka kuma tambayi kanka, wace daraja ce kega wanda ya kwana a cikin masallacin Ka’aba, balle har ya kafa wa wani hujja da shi?

Haka kuma cewar da ya yi Ali Raliyallahu Anhu wai ya ce: Na share wata shidda ina fuskantar Ka’abar ina sallah kafin kowa.

Wannan magana ce da babu mai musun kasancewarta karya. Domin kuwa tarihi ya tabbatar da cewa tsakanin musuluntarsa da ta Zaidu da Abubakar da Khadijah Raliyallahu Anhu bai fi kwana xaya ba ko qasa ga hakan ba. To ya ya za’a ce ya riga kowa sallah da wata shiddah? Ko a ce ya ce shi ne gishirin yakokan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Tunda tare da dubban mutane akayi su, ba shi kadai ba?

 2. 15 Hadisin Wasiyya Qagagge Ne

Xan Shi’ar ya kafa hujja a kan cewa wai, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wasicci ga Ali Raliyallahu Anhu da ya zama magadin halifarsa kai tsaye ba yan ya wuce, da hadisin da ya ce wai, Ahmad xan Hambali ya riwaito daga Anas xan Maliku. Wanda ya ce: watarana mun nemi salmanu ya tambayar mana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shin waye yarima mai jiran gadon sa? Sai kuwa ya tambaye shi.

Wai sai Manzon Allah ya mayar wa Salmanu da tambayar da cewa: waye ka ji ance shi ne yariman da ya gaji gadon Musa? Sai Salmanu ya karva masa cewa: Yusha’u xan Nunu ne. Daga nan manzon ya ce masa: To ni, Yariman da ke jiran gadona, ya biya bashin da ke kaina, ya kuma cika arqawurra na shi ne Aliyu xan Abu Xalib.

Martani:

Ka ga wannan maganar qarya ce lafiyayyarta bisa haxuwar malamai masana hadisi. Kuma ko alama babu shi a cikin musnadin Imamu Ahmad xan Hambali. Eh! Gaskiya ne Ahmad xin ya wallafa littafi akan darajojin Sahabbai. A inda ya ambaci darajojin Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhu da na wasu Sahabbai. Amma kuma ka sani ba duk abubuwan da fada a kansu suke ingantattu ba; ya ambaci har yaye-yaye a cikin don a san su, a yi hattara da su.

Kuma ka sani shi wannan littafi nasa cike ya ke makil da abubuwan da al-kaxai’i ya riwaito da ga malamansa. Waxanda mafi yawansu qaryayyaki ne. Kamar yadda za mu fexe Biri har wutsiya a kan haka nan gaba in Allah ya so, ta hanyar ambato wasu daga cikinsu.

Wani abin da ya kwabe wannan lamari shi ne, kasancewar malaman can qadai’i kan riwaito hadissai daga tsararrakin Ahmad. Su kuwa ‘‘yan Shi’ah saboda tsabar jahilci, da sun yalla ido sun ga irin wannan hadisin qadai’in ya riwaito daga waxancan malamai nasa, ya kuma cusa shi cikin wancan littafi na Ahmad, sai suce Ahmad ya ce. Ahmad din ma xan Hanbali. Alhali kuwa zancen kudai’i ne ba na shi ba. Shi kuma wanda aka riwaito zancen daga gare shi xaya ne daga cikin malaman kudai’in. Waxanda ke yowar riwaya daga tsararrakin Ahmad din.

Bayan wannan ma, a cikin wannan littafin akwai qare-qaren da da Ahmad xin; wato Abdullahi ya yi. Musamman a kan masaniya na Aliyu xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu Abubuwan da wannan yaro ya qara a wannan wuri na da yawa sosai.

 2.16 Bai Isa Kayan Gabas Ba

Xan Shi’ar ya kawo wata magana mai kama da hadisi. Wadda ya so ya yaudari mutane da ita a qoqarin fitowa da darajar Ali Raliyallahu Anhu. Ga abin da ya ce:

An samo wai da ga Yazidu xan Abu maryam daga Ali Raliyallahu Anhu wanda ya ce: Watarana ni da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama mun kama hanya tinki-tinki har muka isa xakin Ka’aba. Ya ce in duka. Sai ya taka kafa xuna. Na yunqura inyi sama da shi. Abun ya fasqara. Ganin haka sai ya sauko ya duka a gabana. Ya ce: Taka kafaxuna. Taka wata keda wuya sai ya yi sama dani. Sai na ji da zan so a lokacin zan iya tavo sama’u. Sai dai na kama saman Ka’aba na xale, a in da wani gumki na azurfa yake. na kama shi ina ta girgizawa hagu da dama, gaba da baya har na tizge shi.

Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce mani: Jefo shi qasa. Ni kuma na wurgo shi. Nan take ya far fashe shi kamar yadda qarau ke fashewa. Sannan na sauko. Daga nan sai muka sheqa ni da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam muna rigyangyanto, muka vuya cikin gidaje, don tsoron kada wani mutum ya ganmu.

To, martaninmu a nan shi ne: muna tabbatar wa wannan barafilin da cewa, wannan hadisi, ko da ya inganta bai isa wani kayan gabas ba. Don babu wani abu na falala a cikinsa da ta ke banci Imamai ko Ali Raliyallahu Anhu. Idan kuwa har baka yarda da haka ba. Ya za ka ce a kan Umamatu ‘yar Abul-Asi xan Rabi’u wadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan dora a kan kafadunsa yana kuma salla? Idan ya mike tsaye ya xauketa a hannu, idan kuma ya yi sujada ya ajiye ta?

Ya kuma za ka yi da sayyidina Hassan da kan zo ya xale wuyan Manzon Allah idan ya yi sujada. Har yakan ma ce: Ai xanane ya hau wuyana. Har kuma ya qara da sunbutar sa?

To, ka ga ixan dai har Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zai xauki wani yaro ko wata yariya a kan kafadunsa, xaukar da ya yi wa Ali ba zata wajabta kasancewarsa wani gagarabadau ba. Domin kuwa ba shi ne kawai wanda Annabi ya taba yi wa hakan ba. Kuma shi xin ma da ya xauka a kafaxar ta sa, ya xaukeshi ne domin kasawar da ya fahimci Alin nada ita ta xaukar sa shi.

Ka ga kenan a haka, abin alfahari a nan na Manzon Allah ne, shida ya yi xaukar. Ka kuma san darajar wanda ya xauki Manzon Allah, ta fi ta wanda Manzon Allah ya xauka Sallallahu Alaihi Wasallama. Kamar yadda irin wannan darajar ta tabbata ga wani daga cikin Sahabbai, da ya xauki Manzon ranar yaqin Uhudu; wato Xalhatu xan Ubaidullahi da waninsa. Ina fatar ka gane banbancin. Ka ga wannan shi ya amfanar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama wancan kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya amfanar da shi. kuma tabbataccen abu ne cewa wanda ya amfanar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da jinkinsa da dukiyarsa, ya fi wanda ya amfana da jiki da dukiyar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama

 2.17 Siddiqai Basu Qidayuwa

Haka kuma xan Shi’ar ya yi amfani da wani hadisi na qarya, a qoqarinsa na tabbatar da imamancin Ali Raliyallahu Anhu. A inda yake cewa wai: An samo daga Abu Laila, wanda ya ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Siddiqai a duniya guda uku ne kawai. Na farko Habibu an-Najjar; muminin nan na Ali Yasin. Na biyu kuma Huzkilu; muminin nan na Ali firaun. Sai kuma na qarshensu kuma mafi xaukakarsu; wato Ali xan Abu Xalib.

To, martaninmu a nan shi ne: Wannan magana dai qarya ce aka qagawa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Domin kuwa ta tabbata a cikin wani ingantaccen hadisi, Manzon Allah ya tabbatar da siddiqancin Abubakar Raliyallahu Anhu.

Haka kuma akwai wani ingantaccen hadisi, wanda aka samo daga xan Mas’ud Raliyallahu Anhu daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Wanda ya ce: ina horonku ku tsare gaskiya. Domin gaskiya ma shiriya ce zuwa ga da’a da nagarta. Ita kuwa nagarta ta farki ce na shiga Aljannah. Mutum ba zai gushe ba yana aiki da gaskiya tare da kirdadon ta, face ya karva sunan mai gaskiya, a wurin Allah. Ina kuma yi muku kashedi da karya. Domin karya na batarwa zuwa ga fajirci da kangara. Ita kuwa kan gara tafarki ce ta shiga wuta. Mutum ba zai gusheba yana karya tare da kirdadonta, face ya karva sunan makaryaci a wurin Allah.

Ka ga wannan hadisin kawai ya ishi mai hankali ya gano cewa siddiqai ba su kidayuwa.

Wannan kenan. Wani dalili kuma da ke tabbatar da kasan cewar wannan hadisi qarya shi tabbtarwar da Allah Ta’ala ya yi cewa, maryamu ‘yar Umrana “Siddiqa ce” tattare da kasancewarta mace.

Kuma a wani wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: Girma da xaukakar mazaje da yawa sun kai. Mata kuwa sai kwara huxu kacal.

Ka ga kenan wannan hadisin ma na tabbatar da cewa yawan adadin siddiqai. Domin kuwa duk yadda aka yim girma aka sami xaukaka ba a kamar “siddiqi” balle a fi shi.

 2.18 Ba Aliyu ne Farau ba

Daga cikin hadissan da wannan xan Shi’ar ke wasa da hankalin fararen fulla da shi, a qoqarinsa na samar wa tatsuniyar imamancin Ali Raliyallahu Anhu gindin zama a soron aqidar musulunci, akwai hadisin da aka samo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama inda ya ce wa Ali Raliyallahu Anhu : kaza da kwai sune misali na da kai.

Martani:

Eh! Ko shakka babu wannan hadisi ingantacce ne. Domin .kuwa Buhari da Muslim duk sun kawo shi a cikin ingantattun littafansu, a cikin jerin gwanon hadisan Bara’u xan Azibu, wanda ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yan ke hukuncin zaman wata ‘ya ta sayyidi Hamza a hannun gwaggon ta, a sakamakon jayayyar da Sayyidina Ali da Ja’afaru da Zaidu Raliyallahu Anhu suka yi a kan wanda zai rike ta. A qarshe ya lallashi Ali Raliyallahu Anhu da cewa : kar ka damu, kaza da kwai sune misali na da kai. ya juya ya ce wa Ja’afaru: kai ma kar ka damu, ganin ka gani na a hali da siffa. Ya kuma juya ya ce wa Zaidu: kai ma kada kada mu kai xan’uwa ne kuma abin so a wurimu.

Amma duk da haka muna son xan Shi’ar ya san cewa, wannan al’amari ba Aliyu Raliyallahu Anhu ne farau ba. Domin kuwa waxancan kalmomi: “Anta minni wa ana minka” Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fade su ga wasu daga cikin Sahabbansa a cikin siga daban-daban. Bari ka jita daga bakin da baya karya ko ana ruwan harshashi.

Ya zo a cikin littafin Buhari da Muslim daga Abu Musa Al-Ash’ari, wanda ya ce Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Idan ash’ariyawa suka rasa mazaje a wurin yaki, ko shekara tayi musu barkwanci, abicinsu ya qaranta, yunwa ta dafafi iyalansu a Madina; sai kowanen su ya kawo abin da ya mallaka a yamutse a raba dai-dai wa daida, kowa ya samu. Kaza da kwai su ne misali na da su. Kaji wannan ko?

Haka kuma manzon ya fadi irin wannan babbar magana ga Julaibibu, a wani hadisi da Muslim ya riwaito a cikin sahihinsa, daga Abu hurairata, wanda ya ce: mun kasance tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wajen wani yaki wanda Allah ya bashi gagarumar nasara. A inda ya ce wa Sahabbansa wa-dawa muka rasa? Muka ce masa: wane da wane. Ya sake cewa: Wa-dawa muka rasa kuma bayan waxannan? Muka karva masa da cewa: sai kuma wane da wane, da kuma wane. Ya kuma sake cewa: sai wa kuma? Muka ce masa sukenan.

Sai ya ce: Amma ni ban ga Julaibibu ba. Ku gano mani shi. Sai muka fantsama cikin gawawwaki muna nema. Kwanfa, sai ga gawar sa tsakiyar wasu dakarun kafirai guda bakwai, waxanda ya kashe kafin su kashe shi. Nan take muka kyafato Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya iso wurin. Tsayawar sa ke da wuya sai ya kalli yana yin da Julaibibu yake ciki, sai ya ce: Ko shakka babu shi ya kashe bakwan nan kafin su kashe shi. Kaza da kwai sune misalin wannan (Julaibibu) da ni.

Sai Manzon Allah ya ciccive shi, shi kaxai qarshe aka haqa qabari aka saka shi.

Mai riwayar ya ce: Mai bayar da labarin bai ce mana an yi masa wanka ba.

Ka ga kenan a haka, ta tabbata ba Ali Raliyallahu Anhu ne farau a wannan kirari na manzo ba, balle ya qare kansa, domin kuwa gashi ya yi wa ash-ariyyawa da Julaibibu irin sa, waxanda ma ba halifofi ba.

To, idan kuwa har waxanda ba su kai darajar halifofin can uku ba, sukayi tarayya da Ali Raliyallahu Anhu a cikin wannan kuxa, babu dalilin da zai sa hakan ya zama dalilin kasancewarsa mafi xaukaka a kansu. Balle wajabcin imamancin sa.

 2.19 Fixar Hadisin Amru Xan Maimun

Daga cikin waxancan hadissai da xan Shi’ar ke sojan gona dasu, akwai wani hadisi misali, na Amru xan Maimun, wanda wai ya ce, inji xan Shi’ar: Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu nada wasu darajoji guda goma waxanda babu mai su a Duniya: Shi ne wanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce a kansa: Zan aika wani mutum, wanda har aBadar Allah ba zai kunyatar ba. Wanda kuma ke son Allah da manzon sa, su ma suke so sa. Wai jin hake ke da wuya sai sai Sahabbai suka yo ca, sukayi dako- dako. Kowa na jiran ace shi.

Sai Annabi wai ya kayar da baki ya ce: ina Aliyu xan Abu Xalib? Aka ce masa yana fama da ciyon ido, wanda ya tsayar da shi gidin dutse yana niqa. Sai wai ya ce: Bai kamata irin sa ace yana niqa ba.

Amru ya ce: Aka kira shi ya taho yana dundumi. Nan take Annabi ya yi masa addu’a idon ya warke. Ya kuma girgiza tutar yaqi har sau uku, sannan ya danqa masa. Kuma wai a wannan yaki ne ,ya taho da Safiyyatu ‘yar Huyaiyu.

Bayan haka ne kuma wai, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya aiki Abubakar Raliyallahu Anhu da suratul- Tauba. Bai samu isar da ita ba, kuma Manzon ya tura Ali Raliyallahu Anhu ya karve ta daga hannunsa. Ya kuma kafa hujja da cewa: bai kamata dama wani ya isar da irin wannan sako daga gare ni ba. Sai wanda ni da shi kamar kaza da kwai ne. Daraja ta farko kenan.

Ta biyun kuma. Watarana tarayyar ‘ya-yan Ammin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na zaune, a cikin ma har da Aliyun. Sai Annabi ya dube su ya ce: waye daga cikin ku zai jibince ni duniya da lahira? Wai sai kawai suka dube shi biris. Sai Aliyu ya karva masa da cewa: Ni zan jibince ka duniya da lahira. Sai Annabi yaqi kula shi. Daga nan kuma sai ya bisu xaya bayan xaya, yana yi musu waccan tambaya. Su kuma kamar farko, suna yi masa kallon haxarin kaji. Shi kuma Ali bai daddara ba . ya sake karva masa da irin waccan amsa ta farko. Ganin haka sai wai Annabi ya kula shi da cewa: kai ne majibincin al’amarina duniya da lahira.

Daraja ta uku kuwa: Aliyu ne wanda ya rufa wa sayyida khadija baya wajen mika wuya ga addinin Allah.

Ta huxu kuma : Aliyu ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya lulluvawa mayafin sa, tare da Fatima da Hassan da Husaini. Ya kuma ce: Allah na nufi ne ya tafiyar da qazanta kawai daga gare ku, ya ku mutanen babban gida, ya kuma tsarkake ku tsarkakewa (33:33).

Daraja ta biyar kuma: Aliyun ne wanda ya saxaukantar da rayuwarsa. Ta hanyar saka tufafin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tare da kwantawa a kan shimfixarsa. Ga kuma mushrikai na ruwan wutar duwatsu a kansa.

 Ta shida kuma: Aliyu ya nemi iznin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a kan ya bishi zuwa yaqin Tabuka tare da rundunarsa da zai fita da ita. Manzon Allah ya ce masa: A’a. Jin haka sai Aliyu ya fashe da kuka. Sai wai Annabi ya ce masa: Ba zaka so matsayinka a wurina ya zamo kamar matsayin Haruna a wurin Musa ba? Duk da yake kai ba Annabi ba ne. Ba ta yiwuwa in tafi face na bar ka a matsayin wakilina.

Daraja ta bakwai kuma: wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce ma Ali: ”Kai ne madadina ga kowane mumini bayan na bar duniya”..

Ta takwas kuma: Manzon ya ce babu wata qofa ta masallaci da ke buxe sai ta Ali.

Daraja ta tara kuma: Babu lokacin da masallaci baya shiguwa ga Ali Raliyallahu Anhu ko yana da janaba.

Daraja ta goma kuma: Itace cewar da manzon Alla Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a kan Ali: “Duk wanda ya yarda da ni a matsayin majivinci, to, ya riqi Aliyu a matsayin haka”.

An kuma samo daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama marfu’an. Cewa ya aika Abubakar Raliyallahu Anhu da surar Bara’atu zuwa Makka. Bayan kwana uku da haka kuma sai ya tashi Ali Raliyallahu Anhu ya ce masa ya yi gaggawa ya riski Abubakar xin, ya karvi sakon ya kai, shi kuma ya dawo. Dawowar Abubakar ke da wuya, sai ya iske Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya na kuka. Ya ce: Ya Manzon Allah, Allah yasa ba wani laifi na yi ba? Manzon ya ce: ko alama. An dai umarce ni ne da kada in aika wani da wannan sakon sai jini na. Bisa ga na riga na baka shi.

Wannan duk inji Xan Shi’ar.

To, ga martaninmu: Na farko dai wannan hadisi ba masnadi ba ne, mursali ne. Wannan kuwa ko da ya tabbata daga Amru xan Maimun xin.

Bayan wanna kuma, akwai magangannu da dama a cikin sa, waxanda tabbas qarya ce aka yi wa ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallama kamar cewar da a kayi ya cewa Ali Raliyallahu Anhu Ba ka fatar matsayinka a wurina ya zama kamar matsayin Haruna a wurin Musa? Duk da yake kai ba Annabi ba ne. Ba ya kamata in tafi face na barka a matsayin wakilina.

Ka ga wanna magana, qarya ce shararra. Domin kuwa akwai tafiye-tafiye da dama da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, ya kuma bar wani,wanda ba Ali ba, matsayin wakilinsa a Madina. Kamar tafiyar da ya yi don Umratul Hudaibiyya, da yaqin Haibara, da yaqin Fathu, da na Hunainu da Da’ifa, da Hajjin ban kwana, da yaqin Badar.

Duk waxannan tafiye-tafiyen da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, duk ya yi sune tare da shi Alin Raliyallahu Anhu. Wani Sahabi na wakiltarsa a Madina. To, in ji?!

Kuma wannan magana da nake gaya maka, tabbata ce kuma sananna. Don bana kwai ni da xai sai da zaqara. Ingantattun riwayoyi waxanda malamai masana hadisi suka haxu a kansu, sun tabbatar da cewa, mafi yawan gumurzun da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi da kafirai, ya yi shi ne tare da Alin, ko da Allah bai kaddari aka gwabza a wurin ba.

To, ka ga a kan haka, idan muka tafi akan fassarar xan Shi’ar. Wadda ke qoqarin nuna cewa, duk wanda manzo ya bari ya wakilce shi a Madina, don wata tafiya, to, ya zama mafi xaukakar Sahabbai a lokacin. Kenan fara shin alkaxarin Ali ya faxi warwas, a waxancan lokuta da manzon ya wakiltar da wani a Madinar bashi ba. Musamman idan aka yi la’akari da waqilcin da aka bar wa Sahabban a lokutan na kula da mazaje ne kuma Muminai. Shi kuwa waqilcin da manzo ya bar Ali ya yi a lokacin yaqin Tabuka, na kula ne da mata da kananan yara da ashararan munafikan musulmin nan guda uku. Waxanda suka yi raggon kaya da gangan a lokacin yaqin, suka darewa ma’aiki.

Kuma ma wannan lokaci ne na aminci ga birnin na Madina, ba a fargabar faruwar wani abu na illa gareshi. Ta yarda har wanda aka wakilta xin zai yi amfani da qarfin tuwo balle. Savanin sauran lokutan, da a mafi yawansu magajin garin na Madina keda bukatar yin jan ido da murza gashin baki.

Ita kuwa ce war da xan Shi’ar ya yi wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Babu wata kofa ta masallaci da ke buxe sai ta Ali. Magana ce da ‘yan Shi’ah suka qaga don su daidai ta tsawon darajar Ali da ta Abubakar Raliyallahu Anhu. Domin kuwa abin da ya tabbata ya kuma inganta a wannan babi, Shi ne abin da ya zo daga Abu Sa’id, daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, ya ce a lokacin da yake jinyar ajali: Babu wani mutum da dukiyar sa da abokantakarsa suka amfane ni kamar Abubakar. Da na kasance mai riqon wani a matsayin badaxayi koma bayan Ubangijina, da na riqi Abubakar. Amma dai ku sani bani da masoyi kuma xan’uwa na musulunci kamar sa. Babu wata qofa da haske ke shigowa tata a wannan masallaci da ta rage face ta Abubakar.

Xan Abbas kuma ya riwaito hadisin a cikin Buhari da Muslim.

Haka abin yake a cikin cewar da xan Shi’ar ya yi Annabi ya ce wa Ali: kai ne majivincin kowa ne mumini bayan na qaura. Magana ce qagagga bisa haxuwar malaman hadisi. Domin kuwa lafazin da ya inganta na wannan magana bai kevanci imamai ko Ali ba Raliyallahu Anhu; wani wanda ba shi ba ya yi tarayya da shi a cikin haka. Kamar kasancewar sa masoyin Allah da manzon sa kuma mai sonsu. Ko wakila shi da manzo ya tava yi ya tsare birnin Madina. Ko lalla shin sa da ya yi da yi masa bushara da zama kamar Haruna a wurin Musa, shi kuma a wurinsa. Ko kasancewar sa majibincin kowane mumini matuqar ya yarda da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, a matsayin majibinci.

Duk waxannan wasu mukamai ne da babu muminin da bai cancanci riqawa ba.

Ko kuma surar bara’a, da manzon ya ce: ba ta kamata wani ya isar da ita saqo ba, wanda ba jinin sa ba, wato Bani Hashim. Ka ga ai wannan magana ta qundume gaba xayan Hashimawa. Tun da ba Aliyu ne kawai Bahashime ba.

Kuma abu ne tabbatacce a tarihin Larabawa cewa, a al’adance ba wanda ke da isar walwale wani arqawari sai xaya daga cikin ‘ya’yan qabilar wanda aka qulla arkawarin da shi a matsayin shugaba.

 2.20 Mafi Yawan Hadisansu na Qarya ne

Babu wani hadisi da wannan xan Shi’ar zai kafa hujja da shi a kan fifikon Ali Raliyallahu Anhu, a kan sauran Sahabbai. Musamman guda ukun nan; halifofi kafisa, face ka taras da hadisin ya xauki matsayin xaya daga cikin matsayai biyu:

Wato ko dai ya kasance qarya ce tun daga maxigarsa har babban yatsar kafansa. Ko kuwa:

Ya kasance ingantacce, amma ya kar kata akalarsa. Ta hanyar yi masa qare - qare ko wani abu mai kama da haka.

Ga guda goma daga cikin waxanda gaba xayan su qarya ne:

Xan Shi’ar ya ce: Daga cikin hadissai kuma akwai wanda Akhxabu ya riwaito, wanda ya ce wai Annabi Sallalahu Alaihi Wasallama ya ce: ya kai Ali! da wani mutum zai bautawa Allah Subhanahu WaTa’ala tsawon shekarun da Annabi Nuhu ya yi a cikin mutanensa yana kira , ya kuma kasance ya mallaki zinarin da ya yi tulin dutsen Uhudu, ya kuma ciyar da da shi kaf, a kan tafarkin Allah , a kuma tsawaita rayuwar sa yaje aikin hajji sau dubu a qasa, a kuma kashe shi a ta qarshe tsakanin safa da marwa, bai ji bai gani ba. To ba zai ji ko qanshin aljanna ba, balle ya shige ta. Matukar bai rike ka abin jivinta ba.

Na xaya kenan.

Na biyu kuwa: Wai wani mutum ya tambayi Salmanu cewa: Me ya sa naga ka na tsananin son Ali? sai wai ya karva masa da cewa: Na ji manzon Allah ne Sallalahu Alaihi Wasallama na cewa: Duk wanda yaso Ali, haqiqa ya so ni. Duk wanda kuma yaqi shi haqiqa ya qini.

Hadisi na ukku kuma, wai shi ne: abin da aka riwaito daga Anas wanda ya ce: Manzon Allah sallahu alaihi wa sallam ya ce wai: Allah ya halicci mala’iki dubu saba’in daga hasken fuskar Ali Raliyallahu Anhu waxanda aikinsu kawai yi wa Ali istigfari da masoyansa, har Allah ya naxe qasa.

Na huxu kuma wai an samo daga xan Umaru, wanda ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wai ya ce: Allah na karvar sallar da azumi da tsayuwar daren duk wanda ke son Ali, ya kuma jabi du’a’insa. Ku saurara! Allah zai bayar da birane a cikin aljanna ga duk wanda ke son Ali, gwar gwadon yawan digaggen zufan da jikinsa ya zuba a duniya. Ku saurara! Allah zai amintar da duk wanda ke son iyalan gidan Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama daga tashin hankalin Hisabi da mizani da siradi. Ku saurara! Ni da sauran Annabawa za mu zama maga’isa ga duk wanda ya mutu a kan son iyalan Muhammadu, a gixan aljanna. Ku saurara! Duk wanda ke kin iyalan Muhammadu, a gidan aljanna. Ku saurara! Duk wanda ke qin iyalan Muhammadu zai tashi ranar qiyama, a goshinsa an rubuta: “Ya yanke qauna daga rahamar Allah”.

Hadisi na biyar: Wai an karvo daga Abdullahi xan mas’udu, wanda ya ce: na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: wai duk wanda ke jin ya yi imani da ni, da abin da nazo da shi. alhali baya son Ali to yana yaudarar kansa ne kawai, shi ba mai imani ne ba. Maqaryaci ne.

Na shida kuma wai shi ne, wanda aka samo daga Abu Barzata, wanda ya ce: watarana muna zaune sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama

 ya ce: Na rantse da wanda raina yake hannun sa. Babu wani bawa da zai xaga kafarsa ranar qiyama face Allah Tabaraka wa Ta’ala ya tambaye shi a kan wasu abubuwa guda wato

: Shekarun sa da yadda ya qarar dasu. Jikinsa da yadda ya miqe shi. Dukiyarsa, yadda ya same ta yadda ya kashe ta. Da kuma son da ke tsakaninsa damu (mutanen babban gida) wai sai Umar ya ce: Ya za’a gane mutum na son ku bayan kun qaura? Sai wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya xora hannunsa a kan Ali xan Abu Xalib, wanda alokacin yake gefen sa. Ya kuma ce: Soyayyar mutum gareni bayan na qaura ita ce ya so wannan.

Hadisi na Bakwai kuma wai: shi ne wanda aka samo daga Abdullahi xan Umar, wanda ya ce wai: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce; a lokacin da aka tambaye shi cewa: da wane yare ne Ubangijinka ya yi magana da kai daren mi’iraji? Sai ya karva da cewa : ya yi magana dani ne da yaren Ali. Sai kuma ya yi mini ilhami na samu ikon ce wa: Ya Ubangiji shin kaine ke magana da ni ko Ali? Sai kuma yayi mini irhami da sanin ikon cewa: ya Ubangiji shin kai ne ke magana da ni ko Ali? Sai kuma ya karva mani da cewa: Ya kai Muhammadu! Ka sani babu wani abu da ke zama da ni. Ba ni miisaltuwa da mutane ko siffan tuwa da wasu abubuwa. Na halicce ka daga haske na, na kuma halicci Aliyu daga haskeka. Amma da na leqa kariyar xakin birnin zuciyar ka, naga babu wanda kake mutuwar so kamar Ali, sai na zavi inyi maka magana da yaren sa don ka sami natsuwa.

Na takwas kuma shi ne wai aka samo daga xan Abbas, wanda ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Da duk gandunan duniya za su zama alqaluma, gulabenta su zama ruwan tawada, aljannu su zama masu kididdiga, mutane su zama marubuta, ba za su iya lissafe darajojin Aliyu xan Abu Xalib ba.

Ga yadda warwarar bakin hadisan zata kasance idan muka koma ta kan isnadinsa:

 wai cewa xan Abbas ya yi: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Allah Ta’ala, haqiqa ya tanadi lada wadda ba ta iyakantuwa saboda yawanta, a kan abin da ya shafi darajojin Ali.

Daga nan wai sai Manzo ya shiga lissafi da rattafawa: Duk wanda ya ambaci wata daraja daga cikin darajojin Ali, yana mai kudurce imani da ita. Allah zai gafarta masa gaba xayan zunubansa; na farko dana qarshe. Duk kuma wanda ya rubuta darajarsa xaya a kan takarda. Mala’iku ba za su gushe suna yi masa istigfari ba, matuqar rubutun nan na wanje. Duk kuma wanda ya saurari ambaton darajarsa xaya, Allah zai gafarta masa gaba xayan zunuban daya xauka ta kunne. Duk kuma wanda ya kalli wata daraja tasa dake rubuce, Allah zai gafarta masa gaba xayan zunuban da ya xauka ta ido.

Sannan kuma wai ma’aiki ya ce: kallon fuskar Sarkin Musulmi Ali Raliyallahu Anhu da ambaton sa duk ibada ne. Kuma wai Allah ba ya karvar imanin bawan da bai riki Aliyu majibinci ya kuma yi wa magabansa bara’a ba.

Na tara kuma wai shi ne wanda aka samo daga Hakimu xan Huzama, daga mahaifinsa shi kuma daga nasa mahaifin wanda ya ce wai: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Wallahi fito na fiton da Ali ya yi da Amru xan Abdu wuddin ranar yaqin kadarko(khandak) ta fi duk aikin da al’uma ta zata yi girma a wurin Allah, har ranar qiyama.

Hadisi na goma kuma wai shi ne: wanda aka samo daga Sa’ad xan Abi Wakkas, wanda ya ce: Mu’awiyah xan Abu Sufyanu ya umarce ni watarana da in zagi Ali Raliyallahu Anhu sai na qi. Sai ya tambayeni dalili, sai na ce masa: Saboda naji wasu Abubuwa guda uku na falala da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa a kansa. Waxanda da zan sami xaya daga cikinsu. Da na fi wanda kakarsa ta yanke saka damawa.

Na farko naji watarana Aliyu na yi wa Annabi qorafin barinsa da ya yi gida tare da qasan shi; wato mata da qananan yara. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa: Ba ka fatar matsayinka a wurina ya zama kamar matsayin Haruna a wurin Musa? Duk da yake dai babu wani Annabi baya na.

Na biyu kuma. Na ji manzon, a ranar yaqin Haibara, yana cewa: yau zan xanka tutarmu ta yaqi hannun wani jarumi. Wanda ke son Allah da manzon sa, suke kuma son sa. Sai kowanen mu ya fara zura wuya. Sai manzon ya ce: kai! Ku kiran man Aliyu. Sai gashi ya taho da ciyon ido. Nan take manzon ya yi masa tohi a idon ya kuma xanka masa tutar. Allah kuwa ya yarda akayi nasara a yaqin albarkacinsa. Kuma ya saukar da ayar da ke cewa: To ka ce: “ ku zo mu kira yi ‘yayanmu da ‘ya’yanku....(3:61) A inda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gayyato Ali da Fatima da Hassan da Husaini Raliyallahu Anhu ya kuma ce: Waxannan sune iyali na.

Martani: Eh! Gaskiya ne Akhdabu Khawarazumi ya yi wallafa a cikin abin da ya shafi darajojin Ali Raliyallahu Anhu sai dai masana hadisi sun dade da fahimtar cewa mafi yawan hadisan da ya riwaito a wannan babi ka gaggu ne. Wanda hakan ke tabbatar da cewa shi ba malamin hadisi ba ne da dai, balle har a iya riqon shi Hujja ko wata madogara.

Wani kuma abin da ke tabbatar da rashin cancantarsa da taka wanna rawa da yake ta qoqarin takawa a fagen hadisi, shi ne cewar da ya yi babu wani hadisi da zai riwaito face wanda ya inganta a idon waxannan mazaje. Wanda kuma suka riwaito a cikin nagartattun zantuka da littafansu. Sai kuma ga shi hakan ta faskara. Domin kuwa babu wani daga cikin malaman da ya riwaito wani hadisi daga cikin waxannan hadisai, a cikin litafai a cikin dogaro, balle ya inganta shi . hasali ma kansu haxuwa ya yi a kan kasancewar hadisan qarya.

Da haka ne kuma gaba xayan waxancan hadisai tara da muka ambata suka tabbata qarya; har zuwa kar shensu.

Amma hadisi na goma, wanda Mu’awiyah ya umarci da Sa’ad da la’antar Ali Raliyallahu Anhu shi kuwa yaqi. Da muhawarar da ta gudana tsakanin su har ya kafa masa dalilai a kan haka. Hadisi ne .ingantacce. domin imamu Muslimu ya riwaito shi a cikin ingantaccen littafinsa. Sai dai darajojin da aka ambata na Ali Raliyallahu Anhu a cikinsa, ba su kevanta da shi ba.

Xauki misalin daraja ta farko: wato barinsa a birnin Madina da manzo ya yi a matsayin waqili, da abin da ya gudana tsakaninsu qari da busharar da manzon ya yi masa. Ka ga ai ba Ali Raliyallahu Anhu ne kawai wanda ya tava waqiltar birnin na Madina ba.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sha barin wasu su waqilce shi a Madina, waqilci kuma irin wanda yafi wanda aka bar Ali Raliyallahu Anhu yi xaukaka; domin shi mata da qananan yara aka barshi tsaro. A kan haka ma ne ya koka wa Annabi, har waccan busharar ta biyo baya.

Ga al’ada babu wani yaki da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai fita, face ya bar wasu dakarru muminai daga cikin Muhajiruna da Ansaru a Madina, ya kuma na xawa garin magaji kafin ya dawo. A lokacin da zai tafi yaqin Tabuka ne kawai ya tabbata wa Sahabbai cewa yau kan ba a xauke wa kowa fita ba. Sai masu kunnuwan qashi da mata da qananan yara da masu wasu lalurori. To kaji dalilin da ya sa Ali Raliyallahu Anhu ya kyamaci wannan waqilci, har ya koka wa ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallama A kan haka ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa bayani da cewa: Bai wakilta shi a wannan karo don ya tozarta shi, ko qasqan tashi ba. A’a ya yi haka ne, saboda gamsuwa da irin amanar da yake da ita. Kamar yadda Musa ya kiltar da Haruna saboda yarda da amanar sa. Duk da yake wanda Musa ya wakilta xin Annabi ne. Amma ni babu wani Annabi da zai zo baya na.

Amma idan ka dubi wannan salon na kamantawa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi amfani da shi tsakanin shi kansa da Musa zuwa ga Haruna da Ali, abu ne da ya ta kaita akan “waqilci” kawai. Amma ba gaba xayan mas’aloli ba.

Eh! Ba gaba xaya ba mana. Tunda ai ka ga gaba xayan Bani Isra’ila ne Haruna ya tsare a matsayin waqilin Musa Alaihis Salamu. A ya yin da shi kuwa Ali Raliyallahu Anhu wasu ‘yan tsiraru ne daga cikin musulmi ya waqilci Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama tsarewa. Adai - dain lokacin da ya fita tare da mafi yawansu. Ka gani ko.

Wannan kenan. Wani kuma abin da ke qara tabbatar da rashin kasancewar wannan. kamanta wani abin godoro ko alfahri ga Ali Raliyallahu Anhu da ‘yan Shi’ah, shi ne irin yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kamanta Abubakar Raliyallahu Anhu da Annabi Ibrahim da Annabi Isa Alaihis Salamu Umar Raliyallahu Anhu kuma da Annabi Nuhu da Annabi Musa Alaihis Salamu ka kuma san darajar waxannan Annabawa huxu tafi ta Haruna nesa ba kusa ba. Kuma kasancewa ma’aiki ya kamanta Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma da biyu daga cikin Annabawa kowannen su, ta sa salon kamanta war nasu zama mafi xaukakar daraja a kan na Ali Raliyallahu Anhu a matsayinsa na wanda aka kaman ta da mutum (Annabi) xaya kacal. Wannan kuma tattare da kasancewar Alin ba farau ba daga cikin Sahabbai, a cikin wannan aiki da muqami na “magaji Gari” mai taqaitaccen wa’adi, balle ya zama qarau.

 2.21 Yamutsa Hazon Hadisin Ranar Shura

Idan baka manta ba. A baya kaxan na gaya maka cewa xan Shi’ar nan yana da hanyoyi biyu, da ya kan bi don tabbatar da fifikon Ali Raliyallahu Anhu a kan Sahabbai, wato hanyar kawo hadissan qarya ko yamutsa hazon wasu ingantattu tare da karkata akalar su.

To anan zan kawo maka wani hadisi da ya inganta a cikin Buhari da Muslimu, a kan yadda Usmanu ya zama halifa, ka ga irin yadda xan Shi’ar ya yamutsa hazon sa. Amma kafin haka sai ka fara da gurbataccen, don a qarshe ka she she baki da nagartacce.

Xan Shi’ar ya ce: An samo daga Amiru xan wasilata, wanda wai ya ce: Na kasance tare da Ali Raliyallahu Anhu ranar shura. Sai na ji yana cewa Sahabbai: zan kafa muku hujja a kan fifikona, da wasu abubuwa da babu wani daga cikin ku; Xan Shi’a ko Bobawa da ke iya karkare shi. Sannan wai ya ci gaba da cewa:

Ya jama’a tsakanin ku da Allah, ko akwai wani daga cikinku, da ya kaxaita Allah Ta’ala kafin na?

Suka wai karva masa da cewa: wallahi babu.

Ya ce: tsakanin ku da Allah ko akwai wani daga cikinku, da ke da xan’uwa irin Ja’afaru, wanda ke shawagi a cikin Aljanna kamar tsuntsu, tare da Mala’iku in ba ni ba?

Suka ce: wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah ko akwai wani daga cikinku da ke da Ammi kamar Ammi na Hamza; zakin Allah da manzonsa kuma limamin shahidai.

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakaninku da Allah ko akwai wani daga cikin ku da ke da mata kamar matata Fatimatu; ‘yar Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama shugaban matan aljanna?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah ko akwai wani daga cikinku, da ke da ‘ya’ya biyu kamar nawa; Hassan da Husaini, shugabannin samarin aljanna?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah ko akwai wani daga cikinku daya tava ganawa da Manzon Allah sallahu alaihi wa sallam sau goma, kowace da manzon sadaka kafinta kamar yadda nayi?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, ko akwai wani daga cikinku, da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa irin yadda ya ce mani: Duk wanda ya yarda dani abin jibinta to ya riqi Ali abin jivinta. Ya Allah ka jivinci al’amarin duk wanda ya jivinci Ali. Ka kuma qi duk wanda ya qishi. Wanda ya ji ya sanar da wanda bai ji ba?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah ko akwai wanda addu’ar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wadda ya ce: Ya Ubangiji ka koxo mani mafi soyuwar halitta a wurin ka, mu yi kalaci da wannan tsuntsu tare da shi. Ta faxa kansa; ya faxo suka ci tare in ba ni ba?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah ko akwai wani daga cikinku, wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya shelartawa duniyar Sahabbai cewa: yau zan danqa tutarmu ta yaqi a hannun wani mutum da ke son Allah da manzonsa suke kuma sonsa. Wanda ba zai dawo ba sai da guxar nasara. Ashe ni yake nufi. Hakan kuma ta tabbata. Bayan wasu sun kutsa fagen famar suka dawo suna tavavvi. Ko akwai shi?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakaninku da Allah ko akwai wani daga cikinku, da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa bani waki’ata: ku bari. Ko wallahi in aiko muku da aradu; wani dakare daga cikin dakarruna. Wanda ni da shi ba banbanci; yi masa biyayya kamar yi mani ne. Kuma sava masa kamar sava mani ne; wanda zai shiga tsakanin ku da kaifin takobi. qarshe ya aika ni?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, ko akwai wani daga cikinku, da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce a kansa: Duk wanda ya ce yana so na ba ya son wannan (Ali) makaryaci ne. In ba ni ba?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, ko akwai wani daga cikinku, da mala’iku dubu uku suka yi wa sallama a lokaci xaya, wato; Jibrilu da Mika’ilu da Israfilu. A lokacin da suka kawowa Manzon Allah ruwa daga wata rijiya. In ba ni ba?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, ko akwai wani daga cikinku, da aka gwarzanta daga sama’u da cewa: Yau duk wani takobi in ba “zul-kifaru” ba labari ne. [hadari mai kashe qarfi rana, goga mai kashe qarfi molo] In ba niba?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, waye daga cikinku, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce zai yaqi Baqaqe da jajaye da kore-koren musulmi a kan umarnin sa, in ba ni ba?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakani ku da Allah ko waye daga cikinku, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce zai yi yaqi don tabbatar da ingantattar fassarar Alqur’ani. Bayan shi ya yi yaqi don samar masa gindin zama, in ba ni ba?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, waye daga cikin ku Allah Subhanahu WaTa’ala ya dawo wa da rana bayan ta faxi don ya sallaci sallar la’asar cikin lokacinta, kamar yada aka yi mani?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah ko akwai wani daga cikinku, da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umarta da karvar sakon surara bara’atu daga hannun Abubakar. Har da Abubakar xin ya tambaye shi cewa: ko an saukar da wani abu ne a kaina? Manzon ya tabbatar masa da cewa: ko alama. Na dai ga babu wanda ya kamata ya isar da irin wannan saqon sai Ali kawai, kamar yadda ya umarce ni?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, waye daga cikin ku, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa: Babu mai son ka sai mumini, babu kuma mai qinka sai munafuki. In ba ni ba?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, ashe ba kune Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi umarni da’a rufe qofofinku, a buxe tawa ba. Har kuka yi qorafi a kan haka. Ya tabbata maku cewa; ba shi ne yake da sha’awa a kan haka ba. umurnin Allah ne? Ko kun manta?

Suka ce: Wallahi bamu manta ba.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, Ashe ba kune kuka kalubalanci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba, a kan ya xauki lokaci yana ganawa da ni, ranar yaqin Xa’ifa; savanin irin yadda yake ganawa da mutaane. A qarshe ya tabbatar maku da cewa, Allah ne ke ganawa da ni a lokacin ba ni ba. Ko kun manta?

Suka ce: Wallahi bamu manta ba.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, kun manta da cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi: Ali na tare da gaskiya; gaskiya kuma na tare da shi, duk in da ya yi tana biye da shi?

Suka ce: Wallahi bamu manta ba.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah kun manta da cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi: Haqiqa na bar muku waxansu abubuwa guda biyu masu nauyi; Littafen Allah da mutanen gidana. Ba za ku vata ba matukar kuna rike dasu. Kuma su, ba za su saki hannun juna ba. Ko sun isa gabar kogina?

Suka ce: Wallahi bamu manta ba.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah waye daga cikinku, ya saxaukar da rayuwarsa, saboda kariya ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga mushrikai. Ta hanyar kwanciya a kan shimfixarsa Sallallahu Alaihi Wasallama kamar yadda na yi?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, waye daga cikinku, ya yi gum da Umar xan Abdul-Widdi a lokacin da yakewa musulmi kuce. Ashe bani ne nace masa cas ba?

Suka ce: Wallahi kai ne.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah, ko akwai wani da cikinku wanda Allah Subhanahu WaTa’ala ya saukarwa ayar tsarkakewa a kansa, wadda ke cewa: kuma Allah na nufin ya tafiyar da qazanta kawai daga gare ku, ya kuma tsarkake ku tsarkakewa (33:33) kamar yadda ya saukar a kai na?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: Tsakanin ku da Allah ko akwai wani daga cikinku, wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa: Kai ne shugaban sahun muminai, kamar yadda ya ce mani?

Suka ce: Wallahi babu.

Ya ce: tsakanin ku da Allah ko akwai wani daga cikinku, da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tava cewa: Ban tava roqon Allah wani abu ba face na roqa maka kwatankwacin sa; kamar yadda ya ce mani?

Suka ce: Wallahi babu.

Akwai kuma daga cikin irin waxannan hadisai na qarya da xan Shi’ar ke dogaro dasu, hadisin da wai aka samo daga Abu Amru Azzahidu, daga kuma xan Abbas, wanda wai ya ce: Ali Raliyallahu Anhu nada wasu darajoji guda huxu da babu wanda ke dasu daga cikin mutane; Shi ne mutum na farko daga cikin Larabawa da Bobayi, wanda ya yi sallah tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne kuwa wanda tutarsa bata tava faxuwa a kowane yaqi. Shi ne kuma gagarraren damon yaqin hunainu. Shi ne kuma wanda ya yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wanka, ya kuma saka shi cikin kabarinsa.

Ka ji kai! Allah da iko shi ke.

Haka kuma xan Shi’ar ya ce wai, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Ni da Jibrilu mun taras da wasu mutane, a daren da akayi mi’iraji dani, ana shatar naman jikinsu. Sai na tambayi Jibrilu ko suwaye? Ya ce sune waxanda ke cin naman mutane ta hanyar giba. Can kuma muka taras da wasu an shashshavesu kamar daudawa. Na tambayi Jibrilu kosu waye? Ya ce kafirai ne. Daga nan sai muka sake hanya.

Isarmu sama ta huxu keda wuya sai ga Ali na sallah. Sai na cewa Jibrilu: Ah! Kai ji Ali har ya riga mu isowa. Sai ya ce mani: wannan ba Ali ne ba. Na ce: To waye? Sai ya ce: wani mala’ika ne Allah Subhanahu WaTa’ala ya halitta a cikinsurar Alin. Wai dalili kuwa mala’ikun da ke hidma faxar Allah ne, da shugabannin su, suka sami kansu cikin matsanancin shauqi da begen Ali, a sakamakon yawan jin darajojinsa da suke ji. Musamman cewar da wai Annabi AllahSallallahu Alaihi Wasallama yayi: Matsayin Ali a wurina kamar matsayin Haruna ne a wurin Musa. Duk da yake babu wani Annabi bayana.

Saboda haka a duk lokacin da shauqin Ali ya motsowa mala’kun sai suzo su kewayi wannan mala’ika mai siffar Ali; an huta dasu kenan.

Kai ka ji magana kamar irinta mata da qananan yara.

Kuma wai xan Abbas ya ce: watarana Almusxafa Sallallahu Alaihi Wasallama na jin nishaxi. Sai kawai muka ji ya ce: Ni bajini ne, xan bajina kuma xan’uwar bajini.

Xan Abbas xin wai sai ya ce: Annabi na nufin: Shi bajinin Larabawa xan bajinin Annabawa Ibrahim. Saboda cewar da Allah Ta’ala yayi: Munji wani saurayi (bajini) yana ambatar su. Anace masa Ibrahim (21:60) kuma shi ne xan’uwan bajinin sahabbi Ali.

Kuma wai wannan magana da kirari da koxa da manzo yayi, ita ce fassarar guxar da Jibrilu ya tashi sama’u yana yi a ranar yaqin Badar yana cewa: Duk takobi yau idan ba “zul-qifari” neba labari ne, kuma duk dakare (bajini) in ba Aliyu ne ba labari ne.

Wai kuma an samo daga xan Abbas xin dai, wanda ya ce: Na ga Abu Zarrin, watarana riqe da labulayyen Ka’aba yana cewa: Wanda ya sanni cikinku ya sanni. Wanda kuma bai sanni ba, to ni ne Abu Zarri. Kuma ku ji ta daga bakina: Da za kuyi azumi ku rame kamar tsarkiya, kuyi ta sallah har ku yi doro kamar baka. Hakan ba zata amfane ku da komai ba. Matuqar baku son Ali.

Tammat! Magana ta qare. Kai ka ji. Wasu dai Allah ya hore masu iya qarya. Kai kasan wannan ko Musailamatul-kazzabu albarka ko?!

To, martanin mu kan zaqaqarun malamai a fagen ilimin hadisi ya haxu a kan cewa gaba xayan abin da xan Shi’ar ya ce an riwaito daga Amru xan wasilatu dan gane da wannan rana ta shura da abin da ya faru a cikinta qarya ne; babu wani abu da Ali Raliyallahu Anhu ya fada mai ko kama da wannan a wannan rana.

Iyakar abin da ya tabbata a wannan rana shi ne, Abdurrahman xan Aufi ya ce wa Ali Raliyallahu Anhu : ina fatar da Allah zaisa in zaveka a matsayin halifa da zaka yi adalci? Ali ya ce: ko shakka babu, da yardar Allah zan yi iyakar qoqarina. Abdurrahman ya kuma sake ce masa: To da Allah zai nufi inyi mubaya’a ga Usmanu a matsayin shugaba fa, za ka yi masa xa’a? Ali Raliyallahu Anhu ya sake karvawa da cewa: Tabbas zan yi.

Kuma irin wannan muhawara ce ta gudana tsakanin Abdur-Rahman xin da Usmanu a kan Ali Raliyallahu Anhu.

A qarshe sai Abdur-Rahman ya fahimci cewa matsayin su duka xaya ne; wato babu wanda keda nufin qin yin adalci da zai zama halifa. Ko yaqi yarda da hukuncin Allah, da xan‘uwansa zai zama. Saboda haka, ba abin da ya rage wa shi illa shawara. Sai ya kwashe kwana uku ya na gudanarda tattaunawa da dai-dakin musulmi a kan wannan mas’ala.

Bari ka ji yadda Buhari da Muslim suka kawo wannan waqi’a a cikin ingantattun littafansu.

Buhari ya ce: An samo daga Amiru da Maimun, a kan abin da ya faru na kashe Umar xan Khaxxabi. Ya ce: qare hidimar kawar da Umar keda wuya sai waxannan manyan Sahabbai suka haxu. Sai Abdur-Rahman ya ce: To, ku zavi mutum uku daga cikinku ku fice masu nauyin jagorancin nan. Nan take zubairu ya ce: Ni na jaye na zavi Ali. Xalhatu kuma ya ce: Ni kuma na jaye na zavi Usmanu. Shi kuwa Sa’ad ya ce: Ni kuma na jaye na zaveka kai Abdur-Rahman.

Sai kuma Abdur-Rahman ya sake cewa: To, waye daga cikinmu zai ba wannan al’amari baya. Mu kuma mu yarda da shi, ya zavi wanda ya ga ya fi dacewa daga cikin biyun, bisa sharaxin kiyaye alfarmar Allah da addinin musulunci. Sai Usmanu da Ali suka yi tsit. Sai Abdur-Rahaman ya ce: ko za ku yarda dani a kan haka? Ni kuma ina tabbatar maku ba zan kasa zabar mafi cancanta daga cikinku ba, da yar dar Allah. Nan take suka karva masa da cewa: mun amince.

Daddale wannan magana a kan haka keda wuya, sai Abdur-Rahman ya kama hannun xaya daga cikinsu (Ali) ya ce: kai dai xan’uwan Manzon Allah ne na kusa. Kuma kana daga cikin na farko-farko na shiga musulunci. Ka kuma san haka. Kuma ka riga ka tabbatar mini, tsakanin ka da Allah cewa, da Allah zai baka halifancin nan, za ka yi adalci. Kuma da zai ba wanin ka zaka yi xa’a. Ko ba haka ba?( Ali ya ce tabbas haka ne) Sai kuma ya kevace da xayan (Usmanu) shima ya tuna masa irin wannan yarjejeniya da suka yi. Shi kuma ya qara tabbatar masa da haka.

Qare wannan shiga da fita keda wuya sai Abdur-Rahaman ya xaga hannun Usman, a matsayin wanda Allah ya zava.

Wannan kenan. Shi kuma wancan hadisi da wannan xan Shi’ar ya yamutsa hazon wannan da shi, cike yake fal da qarya ce qarya ce, irin waxanda Allah ya tsarkake Ali daga furtawa. Kamar hujjar da ya ce Alin ya kafa da matsayin xan’uwansa dana Amminsa da na matarsa. alhali kuwa duk ya fisu girman daraja. Ka ga gaba ta koma baya kenan, inji xan tanoma.

Ko alama Aliyu ba zai yi haka ba, don ya daxe da sanin cewa mafificin mutane a wurin Allah shi ne wanda ya fi kowa jin tsoronsa.

Yan da Abbas zai kafa hujja da cewa: babu wanda ya kai darajata daga cikinku, don ni keda ‘ya’yan ‘yan‘uwa da suka haxa da: Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama da Ali da Ja’afar Raliyallahu Anhu , ka ga babu abin da ya banbanta wannan hujja ta sa da wacan ta Ali.

kuma da abi zai tsaya nan ma da sauqi. Don alfahari da ‘ya’yan ‘yan’uwa yafi zama xaukaka, bisa yinsa da ‘ya’yan ammi.

Abin kamar dai Usmanu Raliyallahu Anhu ne ya tashi ya bugi qirji ya ce: Akwai wanda ya auri ‘ya’yan Annabi mata biyu kamar yadda na yi? Ka ga babu wani abin alfahari da dogaro a nan. Kuma da shi da wanda ya ce: ko akwai mai mata irin tawa a cikinku, duk jirgi guda ya xauko su. Domin kuwa da Fatima da waxancan ‘ya’ya na manzo mata biyu da Usmanu ya aura duk ba wanda ke raye a daidai wannan lokaci na “shura”. Musanman ma Fatimatu da Allah ya karva bayan kamar wata shidda da rasuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

Haka kuma cewar da xan Shi’ar yayi, wai alin Raliyallahu Anhu ya ce: ko akwai daga cikinku mai ‘ya ‘ya irin nawa? Da cewar da ya yi wai, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Ban tava roqon Allah wani abu ba face na rokar wa Ali irin sa. Da kuma wai cewar da ya yi: Ba wanda ya isa ya isar da wannan saqo daga gare ni sai Ali.

Duk waxannan magangannu qaryayyaki ne da ba su da tushe balle makama.

Ita wannan magana kuma ta qarshe, ta cewa babu wanda ya kamata ya isar da wannan saqo daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sai xan cikin gidansa, Alkhixabi ya ce a cikin littafinsa: ‘Shi’arud-dini’: magana ce mutanen Kufa suka yayata daga bakin Zaidu xan Yazidu. Wanda yake kuma ana tuhumar sa da shi’anci, da rashin gaskiyar zance. Kuma ta tabbata duk waxanda sukayo riwaya daga gare shi, ba su san komai ba a kansa.

Sannan kuma wannan malami, wato Al-khixabi ya kalli waccan ‘sako’ da ake qoqarin kore cancantar isar da shi ga kowa in ba ahlu Baitin na biyu ba, a matsayin sakon musulunci. Ta wannan mahanga ne ma, ya kafawa ‘yan Shi’ah hujja da cewa: Suna ina Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya aika As’ad xan Zurarata zuwa Madina don ya isar wa jama’ar can da saqon musulunci, tare da koyawa Ansaru karatun Alqur’ani da sanin makamar addini. Ya kuma aika al-Ala’u xan Al- Hadharami zuwa baharaini da irin wancan saqo. Abu Musa da Mu’azu kuma zuwa Yaman. Utba xan Asidu kuma zuwa Makkah?

Ka ga da haka malamin ya tabbatar masu da cewa, zancen rashin cancantar wani wanda ba Ahlul baiti ba, ga isar da saqon musulunci ya tashi.

Wani abu kuma wanda ke tabbatar da kasancewar wannan xan Shi’a limamin maqaryata shi ne: hadisin daya ce an samo daga xan Abbas. Wannan hadisi ko shakka babu qarya ce lafiyayya. Xauki misalin cewar da ya yi wai mai riwayar ya ce: Babu lokacin da tutar musulunci ta faxi daga hannun Ali Raliyallahu Anhu a dukkan yaqoqan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi. Alhali kuwa babu wanda baisan cewa Mu’ab xan Umari ne, ke riqe da wannan tuta ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin yaqin Uhudu ba. A ranar yaqin Falhu Zubairu ne xan Auwamu ne ke riqe da ita. Wanda har Manzon Allah ya umarce shi da ya kafata a wani wuri da ake kira Al-ityan. Har Abbas yake tambayar sa da cewa: Anya kuwa nan ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umarceka da kafa wannan tutar?

Buhari da muslimu duk sun riwaito wannan hadisin.

Haka nan kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai xan Abbas ya ce: Aliyu Raliyallahu Anhu ne ya ari tutar haquri da juriya a ranar yaqin Hunainu, a inda ya tsaya tare da Manzon Allah .

Itama wannan magana qarya ce kamar sauran. Domin kuwa tarihi ya tabbatar da cewa Abbas xan Abdul-mudallib ne da Abu Sufyanu xan Harisu xan Abdul-mudallibi ne suka kasance gidin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan rana. Abbas na riqe da ragwamar jakar ma’aiki, a yayin da Abu sufyanu ke riqe da shimfixar da yake kanta, a matsayinsu na hurrasu. Wanda a wannan lokaci ne ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umarci Abbas xin da ya xaga murya ya kira masa “masu faren kaya da bakar karraba”.

Xan Abbas ya ce: Nan take nayi kururuwa na kiransu. Kuma wallahi irin yadda suka danno zuwa wurina, kai kace saniya ce taji kukan lavovon xanta; suna isowa suna faxar: Ga mu ya Manzon Allah, ga mu. Shi kuwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin ya xau kyarma, ya na kirari yana cewa: Ni Annabi ne haqiqa kuma xan Abdul-mudallibi ne ubana.

Yana qare faxar haka sai ya sauko daga kan jakarsa, ya xibi tsakwankwani da hannun sa, ya watsawa abokan gaba, yana cewa: Allah ka karya su don girman Ka’aba. Abbas ya ci gaba da cewa: Wallahi wannan aiki na Manzon Allah keda wuya sai naga bangonsu yana darewa suna juyawa da baya, har Allah ya kunyata su.

Buhari da Muslim duk sun riwaito wannan hadisin. Amma Buhari cewa yayi Abu Sufyanu xan Harisu ne ke riqe da ragwamar jakar ta Ma’aiki ba Abbas ba. Kuma a wannan martani nasa, cewa Buhari yayi: Abbas ya ce: Ni da Abu Sufyanu mun kafe gindin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ranar yaqin Hunainu, har akaci aka suxe.

Ka ji wannan. Shi kuwa zancen cewa, Ali Raliyallahu Anhu ne ya yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wanka ya kuma saka shi cikin kabarinsa, magana ce dake da bukatar ‘yar kwarye - kwaryar garan fuska. Domin kuwa babu wani daga cikin: Abbas da ‘ya’yansa da barorin sa shakran. Da wasu Ansaru, wanda bai sa hannunsa a cikin wannan al’amari ba. Illa dai Ali Raliyallahu Anhu shi ne wanda ke wanka jikin ma’aiki kai tsaye, Abbas na bashi umarni a matsayin sa na kan gida, da kuma kasancewar Aliyu mafi cancanta daga cikinsu da xaukar wannan nauyi kai tsaye.

 2.22 Wata Sabuwar Tatsuniya Tasu

Shi kuwa hadisin da xan Shi’ar ya kawo. Inda ya ce: Allah Ta’ala ya halicci wani mala’ika a cikin siffar Ali Raliyallahu Anhu don ya kashe wa wasu manyan mala’iku (Jibrilu, Israfilu da Mika’ilu) kwandar shauqin da suke yi wa Ali Raliyallahu Anhu wanda ya zamar masu kamar ciwo, sanadiyar jin irin falalolin da yake dasu. Da cewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ma shi: Baka fatar matsayin ka a wurina ya zama kamar matsayin Haruna a wurin Musa?

Ka ga wannan magana, tatsuniya ce da jahilai irin waxanda ko qarya ta gagare su iyawa kan yi. Domin kuwa babu wani musulmin kirki wanda bai san cewa mi’irajin da a kayi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, anyi shi ne ba, tun ana Makka; kafin ayi hijra zuwa Madina kamar yadda Allah Ta’ala ya ce: Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da bawan sa, da dare daga masallaci mai alfarma zuwa ga masallaci mai nisa,wanda muka sanya albarka a gefensa domin mu nuna masa daga ayoyinmu. Lalle shi, shi ne maiji, mai gani (17:1)

Ka ga kenan daga masallacin Makka ne aka yi wannan tafiya.

Haka kuma Allah Ta’ala ya ce: Ina rantsuwa da tauraron, a lokacin da ya faru. Ma’bucin ku bai vata ba kuma bai qetare haddi ba. Kuma baya yin magana daga son zuciyar sa.(maganarsa) ba ta zamo ba, face wahayi ne da ake aikowa (53:1-4). Har zuwa inda ya ce: Shin za kuyi masa musu a kan abin da ya gani? Kuma lalle ya ganshi, haqiqatan, a wani lokacin saukarsa. A wurin da magaryar tukewa take(53:12-14). Har kuma zuwa inda ya ce: Shi kunga lata da uzza? (53:19)

Ka ga duk waxannan ayoyi a Makka suka sabka bisa haxuwar kan malamai da almajiran sanin makamar Alqur’ani da tafsirinsa.

Kuma ka ga cewar da ya yi manzon ya ce wa Ali: Ba ka fatar matsayinka a wurina ya zama kamar matsayin Haruna a wurin Musa? Magana ce da manzon yayi alokacin yaqin Tabuka; yaqi na qarshe a shekara ta tara bayan hijira. Shi kuwa mi’iraji in baka mantaba kafin hijira aka yishi. To ta yaya za’a ce mala’iku sunji wannan magana shekaru da yawa kafinta. Ko sun san gaibi ne?

 2.23 Bajini Xan Bajini Xan’uwan Bajini

Haka kuma daga cikin irin waxannan hadisai na wofi, da xan Shi’ar ke tuma goda dasu, akwai wanda ya ce wai: An samo daga xan Abbas, wanda wai ya ce: Watarana Al-Musdafa Sallallahu Alaihi Wasallama na cikin nishaxi, sai muka ji yaqata ya ce; Ni bajini ne xan bajini kuma xan ‘uwan bajini.

Kuma wai sai xan Abbas xin ya ce: Annabi na nufin shi ne bajinin Larabawa, xan bajinin Annabawa; wato Annabi Ibrahim Alaihis Salamu wai saboda Allah ya ce:

ﭧ ﭨ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﴿قَالُواْ سَمِعنَا فَتى يَذكُرُهُم يُقَالُ لَهُ إِبرَهِيمُ٦٠﴾ الأنبياء: ٦٠

Munji wani saurayi yana ambatar sa. Ana ce masa Ibrahim (21:60). Xan’uwan nasa kuwa shi ne Ali. Wanda shima wani bajinin ne. Wai kuma wannan magana ta ma’iki itace fassarar abin da Jibrilu ya ce a lokacin yaqin Badar, daidai lokacin da yake kutsa hatson samaniya. Inda ya ce: Duk wani takobi yau idan ba “zul-qifani” ne ba, labari ne. Duk kuma dakaren da ba Ali ba, shi ma labari ne.

To bari ka ji.

Na farko dai, kan malaman hadisi ya haxu a kan cewa wannan hadisi qagagge ne. Kuma kasancewar sa qarya na tabbatar da bayyana ta fuskoki kamar haka:

Fuska ta farko: duk da yake kalmar “al-fata” Balarabiyar kalmar ce wadda aka ce manzon yayi amfani da ita a cikin wannan kirari na nufin “bajini” a babin. Wadda kuma ke nuna “yabo”. Sai dai a harshen al-qur’ani da Hadisi; (sunnah) da abin da harshen Larabci ya al-adanta(?) kalmar bata nufin “yabo” ko “ suka”. A kan yi amfani da ita ne kawai a waxannan wurare da nufin alamta: matashi ko saurayi ko dattijo, ko wani abu mai kama da haka. Domin ai waxanda suka cewa Ibrahim Alaihis Salamu “ al-fata” a cikin wanccan aya, kafirai ne. Ka kuma san ba yabonsa suke nufin yi ba.

Ka ga a nan kalma ta “al-fata” na nufin “saurayi” ko “ matashi”.

Wata fuskar kuma itace: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yafi qarfin yin alfahari ( kirari) da ka kansa da xan ammin sa.

Kuma ko alama Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai qulla zumunci da Ali Raliyallahu Anhu ko wani ba. Hadissan dake nuna haka, da waxanda ke nuna qulla zumunci tsakanin Abubakar da Umar duk ka gaggu ne. Abin da dai ya tabbata shi ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qulla zumunci ne tsakanin Muhajiruna da Ansar. Amma bai qulla shi tsakanin Muhajiruna da xan’uwansa Muhajiri ba.

Kuma cewa wannan abu ( kirarin) ya faru ne a ranar yaqin Badar, yama fi komai zama qarya.

Kuma. Aliyu bai tava mallakar wani takobi mai suna “zul-qafari” ba. Abin da ya tabbata a tarihi shi ne, shi wannan takobi yana daga cikin takubban Abu Jahil. Wanda ya faxa a cikin ganimar da musulmi suka samu a wurin yaqin na Badar. Ka ga kenan takobin a wannan rana ba mallakar musulmi ba ne. Na kafirai ne. Kamar yadda Ahlu-sunan: Imamu Ahmad, Tirmizi, xan Maja suka riwaito daga xan Abbas cewa: takobin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na ganawa na abu Jahil (zul-qafari) azaba, ta hanyar yi masa giyavu, idan sukayi karon battar karfe (majaz).

Kuma. Xan Shi’ar ya manta cewa shekarun Annabi na bayan Annabta, shekaru ne na manyanci; ya wuce a ce masa “saurayi” a lokacin, balle ya cewa kansa, tunda ba magori bane shi.

 2.24 Son Ali Da Sauran Sahabbai Duk Wajibi Ne

Shi kuwa hadisin da xan Shi’ar ya riwaito daga Abu Zarri, hadisi ne mai gajeren asali (maukit) ; nan zariyarsa ta tuqe ga Abu Zarri xin. Darajar sa ba ta kai ta marfu’i ba (hadisi mai cikakken asali) saboda haka ba a shiga xaka da shi, balle kafa hujja watarana.

Kuma cewa ma an riwaito shi daga Abu Zarri, magana ce da keda xan mirtsi-mirtsi.

To kuma ma duk aje wannan. Ko da hadisin ya inganta, to abin da ya qunsa xin can bai kebanci Ali ba. Domin kuwa son sauran Sahabbai, da suka haxa da: Abubakar da Umar da Usman Raliyallahu Anhu da Ansaru wajibi ne, yadda son Ali Raliyallahu Anhu yake wajibi a kanmu.

Wani abu dake tabbatar da wannan magana tamu shi ne ingantaccen hadisin da ya ce Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Son Ansaru shi ne alamar imani. Kamar yadda qin su yake alamar manafucci.

Haka kuma wani ingantaccen hadisi a cikin sahihu Muslim ya ce; Ali Raliyallahu Anhu ya ce: Annabin nan da bashi da malami sai Allah ya yi mini busharar cewa: duk wanda yaso ni mumini ne. Wanda kuma duk ya qini munafuki ne.

 2.25 Son Aliyu Bai Isa Shinge

Xan Shi’ar ya ce daga cikin darajojin Ali Raliyallahu Anhu wai akwai hadisin da marubucin littafin: al-fiddausi ya riwaito daga Mu’zu xan Jabalu, wanda ya ce wai: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Son Ali wani kyakkyawan aiki ne mai silke. Wanda mugun aiki ba ya hudawa, balle ya cutar da mai shi. Haka kuma qinsa, wani mugun aiki ne mai sida, wanda ran mai shi bai daxa shi da komai ba.

Martani: Muna tabbatar wa da wannan xan Shi’ar cewa wannan hadisi qarya ne. Kuma wannan littafi na: al-fiddausi cike yake makil da ka gaggun hadisai. Tattare kuwa da kasancewar mawallafinsa; Shirawahi xan Shahradaru ad-Dailami xaya daga cikin mafarauta hadisi da riwayarsa. Hakan bata hana wannan littafi nasa zama maqoshin kolo ba, ta hanyar tarkata duk hadisin da yaci karo dashi a ciki, tare da share isnadinsa, ba kuma tare da kula da kasancewar sa ingantacce ko mai rauni ko qagagge ba. Saboda haka ne ma su gizo da qoqi suka sami ranar shanya jikakken garin su a cikin littafi, barkatai.

Babu wani musulmi na qwarai da zai yarda cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya furta wannan magana. Domin kuwa sanin kowane son Allah da manzonsa sun fi son Ali falala nesa ba kusa ba. Amma duk da haka ba su hana a kama mai su da laifin mugun aikin daya aikata. Ka ga ashe kenan son Ali baya isa shinge.

‘Yan Shi’ah suna ina, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kansa a yi wa Abdullahi xan Hammaru xan karan duka, saboda yasha giya, tattare kuwa da shaharar da ya yi da son Allah da manzonsa? Son Allah da Manzonsa kuwa wajibi ne a kan kowane mumini. Amma kuma hakan ba zata hana a kama shi da laifin wani mugun aiki ba; za’a kama shi da shi harma a hukunta shi .

Kuma abu ne sananne ga xaukacin jama’ar musulmi; sani na lalura, a sakamakon kasancewarsu musulmi, cewa duk wanda ya rayu ya kuma mutu yana shirka, kashin sa ya bushe; Allah ba zai gafarta masa ba, ko da kuwa yana lasan dugadugan Ali Raliyallahu Anhu saboda tsananin so da qauna.

Ai ka ga son da mahaifin Ali; wato Abu Xalib, da Shi’ah al-Galiyya ke yi wa Alin bai hana su shiga wuta ba a matsayin kafirai.

A ta kaice wannan aqida kafirci ce bayyananne , irin wanda Allah ke sauraron mai ita idan ya tuba. Kuma haramun ne ga duk wanda ya yi imani da Allah da ranar qarshe ya kudurta haka, balle furta shi.

Wannan kenan. Haka nan kuma cewar da ya yi wai Annabi ya ce: qin Ali wani mugun aiki ne mai sida, wanda wani aiki na mai shi, ba zai amfane shi da komai ba. Magana ce da ke son a kalleta sau biyu.

Ah! Sau biyu mana. Ai ko shakka babu, sai dai kafircin kafirin da yaqi Ali, ya zame masa qarqiya daga shiga Aljannah, ba kin Alin ba. Kamar yadda imanin mai imani zai zame masa sanadin shiga aljannar, ko yana qin Alin kuwa. Don ba shi ne ma’auni ba.

Haka kuma malaman hadisi sun yi itifaqi a kan cewa hadisai biyu da xan Shi’ar ya riwaito daga xan Masa’udu inda ya ce wai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: ladar son Alu Muhammadin ta yini xaya ta fi alheri bisa ga ibadar shekara xaya. Kuma wai duk wanda ya mutu a kan sonsu xan aljanna ne.

Da kuma xayan da ya ce a cikin sa: Ni da wannan (Ali) hujjar Allah ne a kan halittar sa. Duk hadisai ne ka gaggu. Domin ai ibadar shekara xaya ba wasa bace; dubi girman imani da sallah biyar kowace rana da azumin watan Ramadana, har na tsawon shekara xaya. Ko a kansu xai aka tsaya. Waxanda saboda girmansu ne kan masulmi ya haxu a kan cewa sun fi qarfin son Alu Muhammadin na tsawon zamani, balle kwana xaya, a lada.

Sannan kuma ai hujjar Allah akan bayinsa , ta riga ta tabbata sakamakon aiko manzanni kawai. Dubi abin da Allah Ta’ala ke cewa:

ﭧ ﭨ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﴿رُّسُلا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى ٱللَّهِ حُجَّةُ بَعدَ ٱلرُّسُلِ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيما١٦٥﴾ النساء: ١٦٥

Domin kada wata hujja ta kasance ga mutane a kan Allah bayan manzanni (4:165)

Ka ga bayan manzanni Allah bai lava imamai ko waliyyai ko wasunsu ba ko?

Haka kuma nagartattun malamai; ma’abuta ilimi da kishin addini sun haxu a kan cewa, cewar da xan Shi’ar ya yi wai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Da gaba xayan mutane za su haxu suso Ali Raliyallahu Anhu da Allah Subhanahu WaTa’ala ya shafe wuta. qarya ce gangariya. Suka kuma qara tabbatar da cewa da mutane za su haxu suso Alin baki xaya. Hakan ba zata amfane su da komai ba ranar qiyama. Matukar ba su yi imani da Allah da mala’ikunsa da littafansa da manzaninsa da Ranar lahira, suka kuma aikata aikin qwarai ba.

Da zarar haka ta samu daga gare su, to aljanna gare su har quryar xaki, ko dako basu tava sanin ko waye Ali ba, balle su soshi ko su qishi.

 2.26 Hadisan Gizo Da Qoqi

Kusan mafi yawan hadisan da wannan xan Shi’ar yake shawagi dasu, a sararin samaniyar qoqarin tabbatar da fifikon Ali Raliyallahu Anhu hadisai ne na gizo da qoqi.

Daga cikin waxannan hadisai, akwai wanda xan Shi’ar ya ambaci wani arqawari da Allah ya yi a kan Ali Raliyallahu Anhu. Da cewa shi tutar shiriya ne kuma shugaban sahun masoya Allah (waliyai) kuma wai Ali shi ne abu xaya da Allah ya wajabtawa masu tsoronsa so a matsayin wata xaya-xayan kalma... har dai qarshen hadisin.

To, malamai masana sirrin hadisi da makamar sa sun yi itfaki a kan cewa wannan hadisi qagagge ne. Kuma baya zama ingantacce don kawai mawallafin littafin al:Hilyah ya riwaito shi, ko wani mai kama dashi. Domin tabbataccen abune shi wannan malami ya riwaito hadisai masu yawa a cikin wannan aiki nasa. Waxanda kusan duk masu rauni ne, a kan darajojin, Abubakar da Umar da Usmanu da Ali da wasu waliyai da wasunsu. Kai! Wasunsu ma ka gaggi ne bisa haxuwar malamai. Duk da yake shi da takwarorinsa daga cikin “huffaru” amintattu, ma’abuta hadisi, amintattu ne a karan kansu, a kan duk abin da za su riwaito daga shehunninsu. Illar tare da su shehunan.

Haka ma hadisin Ammaru da na xan Abbas, waxanda xan Shi’ar ya kawo duk na gizo da qoqi ne.

 2.27 Sun Mayar Da Sahabbai Dalga

Sahabbai a wurin ‘yan Shi’ah ba kowa bane. Saboda haka suka mayar da su dalga. Ta hanyar kai masu ko wacce irin suka, da zuba masu kowacce irin qazanta kamar salga.

A qoqarin tabbatar da wannan manufane , xan Shi’ar ya ce wai: Jumhurun malamai sun riwaito abubuwan kunya da basu kida yuwa a kan Sahabbai. Wanda har wani marubuci mai suna al-qalibi ya wallafa littafi mai suna. Ababen kunyar Sahabbai wai. Amma bai ambaci wani abun kunya ko xaya ba, ko wata naqasa dangane da Ahlul-Baiti a cikin littafin.

To ka ga irin wannan xanyen aiki na ‘yan Shi’ah abin yayi hattara ne da.

Martani: To, kafin mu shiga walwale wannan qullin maqodo filla - filla, muna tabbatar wa xan Shi’ar da cewa, duk wani abu da wani zai ga la’arin Sahabban Manzon Allah a kansa, bai kamata a kira shi abin kunya ba. Sai dai wata qila ko qorafi.

Amma daxa ga dalilai na:

Qorafe-qorafen da a kanyi kan Sahabbai nau’i biyu ne:

Ko dai su kasance: 1) qarya zalla. Wato an qaga masu ne; ba su ji basu gani ba. Ko kuma 2) lauje cikin naxi. Wato abubuwan sun faru a cikin nagartattar sura. Amma sai magabata suka sake masu fuska. Ta hanyar rage wasu abubuwa daga cikinsu ,da qara wasu. Ta yadda za su bayyana a matsayin miyagun ayukka ga idon duniya. Waxanda a qarshe za su tsirar da itatuwan suka da zargin waxannan bayin Allah.

To mafi yawan korafe - korafen da ake riwaitowa a kansu, na qarqashin wannan kashi na biyu ne. Kuma za ka taras da cewa, waxanda ke riwaito sun, mutane ne da suka shahara da qarya; kamar su Abu Mukhnif; Lud xan Yahya, da Hisham xan Muhammad as-Sa’ibi al-kalibi, da wasu maqaryata takwarorin su. Kuma ka ga dashi wanna al-kahbin ne xan Shi’ar ya kafa mana hujja. Alhali kuwa limami ne daga cikin limaman qarya a duniyar Shi’ah. Kuma duk abin daya riwaito kan biyo takan mahaifisa ne daga hannun abu Muhnif xin can. Waxanda dukansu biyun ba a shiga xaka da maganarsu.

Nau’i na 3), kuma daga cikin waxannan qorafe - qorafe, shi ne, : Tantagaryar gaskiya. Wato abubuwa waxanda tabbas Sahabbai sun aikatasu a matsayinsu na ‘yan adamu. Amma kuma suna da uzuri a kan haka. Wanda la’akari dashi, ke xauke ayyukan daga zama tantagaryar zunubi, zuwa matsayin ijtihadi. Irin wanda mai shi ke samon lada biyu idan ya yi muwafaka. Yake kuma samun xaya idan yayi kuskure.

To gaba xayan abin da ya inganta, daga cikin qorafe - qorafen, na qarqashin wannan inuwa ne.

Kuma duk ma qorafin da aka qaddara wa wani tantagaryar zunubi, za ka taras ba wata alka da yake iya yi wa Sahabban, idan akayi la’akari da darajojinsu da kyawawan ayukkansu, da kasancewarsu ‘yan aljanna tun duniya. Domin ba garesu kawai ba. Ga kowa ma, tantagaryar zunubai kan zama labari a lahira, a yayin da mai su ya sami xaya daga cikin waxannan lanbobi ko masu kama dasu, tun duniya:

(a)             Tubar wankan tsarki. Kamar yadda ta tabbata daga bakin malaman Shi’ah ‘yan-sha-biyu cewa, waxannan Sahabbai sun yi irin wannan tuba ga Allah Subhanahu WaTa’ala a kan duk kurakuran da suka aikata.

(b)             Kyawawan ayyuka. Kamar yadda ta tabbata cewa kyawawan ayyuka na wanke zunubai. Kuma Allah Ta’ala ya ce: Idan kuka nisanci manyan abubuwan da ake hanaku aikatawa, to, za mu kankare muna nan ayukanku daga gare ku (4:31)

(c)             Manyan musibu. Waxanda ta tabbata suna kankare zunubai

(d)             Addu’ar muminai waka junansu. Da kuma ceton da Allah zai ba su damar yi wa junan nasu gobe qiyama.

Kai! Babu wani abu dake zaman dalilin kwaranyewa, wani daga cikin al’ummar nan wani zunubi ko wata azaba, face waxannan Sahabbai sun fi cancanci da shi a kan kowa. Sune kuma ya kamata su zama sha yabon masu yabo, varin varin masu vari kafin kowa.

Bayan xan Shi’ar ya qare waccan dunqulallar maganar, sai kuma ya ce: Al-Kalbi ya ambaci waxancan abubuwa na kunya masu yawa. Bari in xan gutsuro maku kaxan daga ciki. Sai ya ce: An riwaito cewa watarana Abubakar Raliyallahu Anhu na kan munbari sai ya ce: haqiqa Annabi ya kasance yana samun gudunmuwar wahayi a kan duk abin da yake aikatawa. Ni kuwa shexan na iya dagula mani lisafi. Ina fatar za ku mara mani baya a duk lokacin da kuka ga na kama hanya shararra. Za ku kuma kevo ni, idan na kama daji.

Ka ji qarshen maganar Siddiqu.`

To sai xan Shi’ar ya ce: To ta yaya za’a yarda da shugabancin wanda ke da buqata da taimakon talakawa, alhali kuma su suna da bukata da nasa taimakon? An yi haihuwar guzuma kenan.

Martani:

Ai wannan hadisi aya ne, dake tabbatarwa da nuna xaya daga cikin manyan darajojin Abubakar Sidiku Raliyallahu Anhu. Kuma ba wani abin da ke nuna kasancewarsa wanda ba ya nufin homa da varna a bayan qasa kamar wannan magana da ya yi. Dama kuma bai nemi shugabancin ba, bai kuma tava sha’awar zalunci ba. Bai kuma da nufin yin mulkin mallaka a halifancinsa. Saboda haka ya kama hannun mutane ya haxa dana Allah da manzonsa; ya ce subi su.

Tabbas abida yake nufi kenan. Don fassarar waxancan kalmomi da ya yi amfani dasu itace: idan kun ga na tsayu a kan xa’a ga Allah, to ku agaza mani a kan haka. Idan ko kun ga na bar tafarkin gaskiya to (don Allah) ku ceto ni. Kamar yadda wata magana daya tava yi ke tabbatarwa, in da ya ce: kubi ni matuqar na bi Allah, idan kuma nayi kuskure daga yi masa xa’a ku yi ta kanku.

Allahu Akbar!!! Ka ji baraden musulunci.

Kuma cewar da halifan yayi, shexan na iya dagula masa lissafi, magana ce da bai kamata mai hankali da ilimi ya yi wa kallo biyu ba. Saboda abu ne dake iya faruwa ga kowane xan Adam. Don babu wanda Allah bai sawa abokin zama daga cikin mala’iku da shexanun (aljannu) kowane xaya-xaya ba.

Ka ga a nan Siddiqu na sone ya faxawa duniya tun da asuba, cewa fa shi ba ma’asumi ne kamar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Wannan kuma gaskiya ne.

Wannan kenan. Ita kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai: ya za’a amince da shugabancin wanda keda bukata da agajin talakawansa don ya dawo ga hanya. Maganace irinta waxanda suka jahilci tantagar yar manufa da ma’anar shugabanci (Imama)

Ai a tsarin musulunci shugaba ba Ubangijin talakawansa ne ba, balle ya kasance baya da bukata dasu. Kuma ba Manzon Allah bane, zuwa gare su, balle ya zama hamzatul-wasali tsakanin suda Allah. A’a, ko alama. Shi, shugaba ne, kuma abokin tarayyar talakawa cikin duk abin da zai tabbatar da nagartar rayuwar su ta addini da duniya; dolene su yi masanyar hannuwan gudunmuwar alheri a tsakaninsu. Wato ya zama kamar dai madugun tafiya, wanda ayari zaibi baki alaikum, idan ya kama lafiyayyar hanya. Su kuma faxakar da shi idan yaci tuwon gigi; su dawo dashi a kan hanya madaidaiciya. A qarshe kuma idan wani abu; mutum ko dabba ya kawo masu hari, to sai ayi ba babba ba yaro; dashi dasu duk sun tuve ayi ta katakka. Idan an qare lafiya, ya koma ya nax a rawaninsa ya fike amawali ya buxe mahuta.

Amma kuma tattare da haka akwai bukatar duk wanda zai shugabanci jama’a ya kasance mafificinsu kamala a ilimi da kudura da jinqai, don ya zama masu rariya matatar komai.

 2.28 Tawali’u Ne Ba Rashin Cancanta Ba

Daga cikin abubuwan da xan Shi’ar ke sukar lamarin Sahabi Abubakar Raliyallahu Anhu dashi akwai cewar da ya yi wai, Abubakar Raliyallahu Anhu ya yiqoqarin butsewa a lokacin da aka zave shi matsayin halifa, saboda sanin da ya yi cewa bai cancanci muqamin ba; Don ba haqqin sane ba. Wai sai ya ce: (Don Allah) ku fita ba tuna, tunda ga Aliyu na raye, ai ba ni da wani matsayi. Balle a dage a kan sai Ni.

Daga nan ne xan Shi’ar ya ce: Idan dai har Abubakar na jin cewa ya cancanci wannan shugabanci, kuma haqqinsa ne, to qoqarin bultsewar nan da ya yi savo ne. Idan kuwa har kamuyamiya ce zai faxa wa; kamar yadda shi da kansa ya hango haka, har yayi qoqarin bultsewa. Kuma tattare da haka ya ci gaba da riqe mukamin, to abin kunya ya tabbata a kansa.

Lalle, kai kasan kafiri dai bai san kunya ba!!!

Martani: Babu inda wannan magana ta fito a cikin littafan hadisi ingantattu. Babu kuma mai cewa ga isnadinta. Saboda haka qarya ce kawai.

Abubakar Raliyallahu Anhu baice: “Tun da Aliyu na raye---ba”) Ingantattar maganar da dai ta tabbata itace, cewar da ya yi a ranar da sukayi taro a “saqifa”: ya ku jama’a ina kiranku ga ku naxa xaya daga cikin: Umar xan khaxxabi da Abu Ubaidatu xan Al-Jarrar . yana qare faxar haka sai Umar ya yi kazazam ya ce: A’ah! Kai dai za’a naxa. Ko banza mun daxe da gamsuwa da zaman ka shugaba a gare mu, kuma mutum mafi alheri da soyuwa a wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuma wallahi da za’a rataye ni a sare kai na, in tafi wurin Allah ina tsarkakakke, ya fi soyuwa gareni. Bisa ga a naxani shugaban mutanen da kake cikinsu.

Kaji iyakar abin da ya gudana a wannan taro ta wannan haujin.

To kuma tafi naji. Muqaddara cewa Abubakar xin Raliyallahu Anhu ya ce: “kuma Aliyu na raye” kamar yadda xan Shi’ar ke son ya ce. To ai wannan shedar da Umar ya bayar a kansa ta isa ta cancantar da shi ga halifancin fiye da kowa. Haka kuwa akayi, ka gani ko?!

To kuma mu dawo ga cewar da xan Shi’ar ya yi wai: Da Abubakar na jin halifancin haqqinsa ne, ya kuma nemi ya butse, to ya aikata savo.

To abin da za mu cewa a nan shi ne: Mu qaddara cewa Abubakar xin Raliyallahu Anhu ya nemi ya butse. Hakan bata nuna rashin kasancewar ta haqqi gare shi. Domin kuwa zaman abu haqqi ga mutum na nufin ko dai 1) halas ne gare shi. Ko kuma 2) Wajibi. Babu kuwa inda barin halas don kunya (fillanci) ya zama laifi, balle a ce. Na farko kenan. Kuma ka ga zancen aikata sabo bai taso ba.

Na biyu kuma, halifanci na zama wajibi a kansa, idan sauran Sahabban suka qi janye naxin da suka yi masa balle su naxa wani. Rashin yin haka kuwa da suka yi ya tabbatar da shi a haka.

Kuma ai ka ga da yawa mutum ka qulla ciniki ko jinga, ta yadda wanzar da su zai wajaba, amma kuma ya iya fasawa. Kamar haka ne. Abu ne mai yiwuwa ya kasance Abubakar ya nemi ya butsewa shugabancin ne saboda tawali’u da irin nauye - nauyen dake kansa. Tattare da kasancewar babu wanda yafi shi cancanta da ita a wurin dama wani wuri. Kuma ai tawali’u bai tava kayar da haqqi ba.

 2.29 Abu Ne Daga Allah

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa wai: Umar ya ce: Mubaya’ar da suka yi wa Abubakar Raliyallahu Anhu a matsayin halifa baqar qaddara ce. Wadda ba don da Allah ya tsare ba. Da hakan ta saukar da wata alloba. Saboda haka, duk wanda ya sake irin wannan gigi ku kashe shi.

Xan Shi’ar yaci ka da cewa: Ka ga inda shugabancin Abubakar ba baqar qaddara ce ba, Umar bai cancantarwa wanda ya sake irinta da kisa. Idan kuwa ya yi haka to abin kunya ya tabbata gare shi. A yayin da tabbatar zamanta baqar qaddarar, da rashin cancantar Abubakar da ita, zai tabbatar da abin kunya a kansu su biyu.

Kai ka ji magana kamar ta mai ilimi da imani.

Martani: Za mu kawo wa mai karatu cikakken martanin wannan hadisin, mu kuma fexe shi har wutsiya. Saboda gaskiya ne abu ya faru, amma mutumin naku (Xan Shi’ar) ya yi halin nasa.....

Kafin haka ga dai ingantaccen abin da Umar xin Raliyallahu Anhu ya ce a cikin hadisin: kada in qara jin wani daga cikinku yayi varin bakin cewa ba Abubakar ne aka shirya yi wa bai’a ba, illa dai abune daga Allah. Eh! Ko shakka babu haka ne. Kuma sai ga shi Allah ya sa ta zama alheri ga mutane. Don babu wanda mutane ke goyon bayansa daga cikinsu kamar Abubakar.

Wato yana bayyana irin yadda mutane suka yi ta yin tururuwa suna kai caffa ga Abubakar Raliyallahu Anhu ba tare da wata inda - inda ba.

Babu wani abin mamaki ko kaxan a cikin haka. Domin kuwa Sahabbai sun riga sun sallama wa Abubakar fai da voye, tun Annabi na raye. Musamman ganin irin yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke gabatar da shi ga al’amurran zahiri da baxini. Saboda haka Sahabbai a wannan lokaci ba su bukatar wata shawara ko jinkiri kafin suyi wasa bai’ar. Savanin wani, wanda ba shi ba, da ba ta yiwuwa (halatta) a yi masa mubaya’a haka nan ba tare da an xanyi wani batun zucci ba, da ‘yan shawarwari.

Saboda haka duk wanda ya yi wa Abubakar mubaya’a, a wannan lokaci, ba tare da wata ida-inda ba, daidai yake. Saboda ai nuni ya ishi mai hankali.

 2.30 Halifa Abubakar Bai Damu Ba

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa wai: A lokacin da ajalin Abubakar Raliyallahu Anhu ya qaraso, halifan yayi nadamar karvar halifancin da ya yi, inda ya ce: kaicona! Na so ace na samu damar tambayar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama; shin ko Ansaru nada wani haqqi a cikin wannan al’amari( halifanci)?

Xan Shi’ar ya kammala da cewa wai: Wannan shi ke nuna cewa ko da Abubakar ya karvi halifacin yana cike da kokwanton cancantarsa da shi; yana kuma jin naxa shi da aka yi kuskure ne.

Martani: Wannan magana qarya ce xan Shi’ar ya yi wa Abubakar; ko ban za bai ambaci isnadin ta ba. Kuma sannen abune cewa wajibi ne ga duk wanda ya kafa hujja da wata riwaya, ya kawo isnadinta matukar yana son hujjarsa ta zama karvavva. Balle wanda ke son tabbatarwa duniyar musulmi da cancantar keta alfarmar Sahabbai. Sai kuma ya buge ga kafa hujja da wata shegiyar hikiya; maras uba balle kaka da kakanni.

Sannan kuma muna tabbatarwa da xan Shi’ar cewa, da yana da hankali da wayo da bai kawo wannan magana ba. Domin .kuwa tana qaryata iqirarin da suke yi ne, na cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya bar sallahun Ali ya gaje shi, a nassance. Ka ga kenan da akwai wancan nassi da suke tutiya, da Abubakar Raliyallahu Anhu bai nemi sanin ko Ansaru nada wani haqqi cikin al’amarin ba. Wannan idan mun qaddara tabbata da ingancin wannan shegiyar riwaya keNan.

Wannan magana tabbas ce.

 2.31 Tsananin Tsoron Allah Ne

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa wai: wani abu kuma dake nuna cewa Abubakar Raliyallahu Anhu ba kowa bane shi ne cewar da ya yi lokacin daya kai gargara : kaicona! Ina ma ace mahaifiyata bata haifeni ba, ina ma ace buntu aka yoni a yi dawun kungu da ni.

Xan Shi’ar ya ce: kaji abin da Abubakar ya ce: Tattare da kuma kasancewar Ahlus-Sunnah sun riwaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama wanda ya ce: babu wanda zai kai gargara daga cikin mutane face Allah ya nuna masa mazauninsa na aljanna da wuta.

Martani: Cewa halifan ya faxi wannan magana a wannan lokaci abu ne ba a tava ji ba. Saboda haka ko shakka babu wannan ba gaskiya ba ne.

Amma dai ya inganta cewa, nana Aisha Raliyallahu Anhu tazo wurinsa. Yana gargara, tana mai maita wani baitin waqa dake cewa:

Wadata ba tada wani amfani ga mutum,

Idan qirjinsa ya buwayi numfashinsa zuwa,

Ya dawo yana gargara a maqogwaro.

Tana faxar haka sai halifan Raliyallahu Anhu ya kware fuskarsa ya ce: bari wannan magana kamata yayi ki ce: Kuma mayen mutuwa yaje da gaskiya. Wannan shi ne abin da ya kasance daga gareshi kana bijirewa (50:19)

Wannan alokacin da ya kai gargara kenan. Amma alokacin daya ke lafi yayye, an tava jin yana cewa: kaicona! Ina ma a ce mahaifiyata bata haife ni ba. Wannan kuwa tsananin tsoron Allah ne, in har ta tabbata ya ce hakan.

Kuma irin wannan kalami dake nuna tsoron Allah mai shi, ba Abubakar Raliyallahu Anhu ne farau ba. An riwaito mutanen kirki da dama, sun furta irin haka, saboda tuna irin tashin hankali da firgita da ranar tashin qiyama ta qunsa. Har wani daga cikinsu ya ce: Da za’a bani zavi, tsakanin in mutu ayi min hisabi, tare da lamanar shiga aljanna, ko a mayar dani turxa? Dana zama turxa.

Imamu Ahmad ma ya riwaito cewa Abu Zarri ya tava cewa: Wallahi na so ace ni wata itaciya ce da ake taunawa a furzar.

 2.32 Ja Da Baya Ba Tsoro Ba

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Abubakar Raliyallahu Anhu ya kuma ce: Kaicona dana sani dana marawa xayan mutanen nan biyu baya ( Umaru xan Haxxabi da Abu Ubaidat xan al-Jarraru) a ranar taron sa’idata, ya zama shugaba. Ni kuma inzama wazirinsa.

Xan Shi’ar ya ce: To ka ga wannan magana, tana tabbatar da cewa Abubakar bai cancanci halifancin ba. Tunda gashi; da kansa yana da ya sani; da bai karva ba.

Martani: A hankalce, wannan magana, idan ma har ta tabbata cewa Abubakar xin yayi ta. To tana kawai nuna cewa ba Ali Raliyallahu Anhu ne ya cancanci halifanci ba. Kuma ya faxe tane, shi abubakar Raliyallahu Anhu xin, saboda tsoron kada alfarmar halifancin ta tozarta kuma ko da Allah zai kaddari haka, to shi dai ya fi son haka ta kasance hannun wani ba shi ba. Wannan kuma na nuna irin yadda ya san girman shugabancin. Kuma wannan abu da ya yi, jada baya ne ba tsoro ba.

Wato ya fi son ko da zai kasance da hannu a cikin shugabancin, to kada ya wuce na wazirci. Ta yadda nauyin ba zai tattara a kansa ba. Kuma haka baya nuna wani tsoro ko kasawa. Domin kuwa qarshen ta dai nauyi kansa ya qare.

Kuma ka ga inda nassin halifancin Aliyu Raliyallahu Anhu ya inganta, Abubakar Raliyallahu Anhu ba zai kudurta marawa waxancan mazajen baya ba. Don yin haka tare da sanin waccan masaniya tozarta alfarmar halifancin ne. Kuma kenan shi zai kasance wazirin halifa mai shigar kutse. Wato ya sayarda lahirarsa kenan, saboda duniyar waninsa ta gyaru.

Ka kuwa san ba irin Abubakar Raliyallahu Anhu ba. Duk wanda ke tsoron Allah, yake kuma fatar gamawa lafiya ba zai yi haka ba.

 2.33 Wani Jihadin ne ya Tsayar Da Siddiqu

Wani qoqarin kashe isa, da xan Shi’ar yayi ga Siddiqu, shi ne cewar da ya yi wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, watarana yana jinyar ajali. Yayi yana maimaitawa: ku tabbata da ganin rundunar Usamatu ta xaga. Kuma Allah ya la’anci duk wanda ya bari jirgin wannan rundunar ya bar shi tasha.

Kuma wai a wannan lokacin halifofin can uku na kafin Ali Raliyallahu Anhu na tare da Manzon Amma wai qarshenta Abubakar ya hana Umar Raliyallahu Anhu halartar yaqin.

Martani: Gaba xayan masana tarihin musulunci da mazajensa, sun yi ittifaqi a kan cewa wannan magana qarya ce. Kuma babu wani daga cikin ma’abuta ilimi da ya riwaito cewa Abubakar da Usmanu Raliyallahu Anhu na daga cikin waxanda Manzo ya umarta da fita tare da rundunar Usamatu. Abin da dai aka riwaito shi ne ya umarci Umar da yin haka.

To, yama kamata duk mai hankali ya tambayi kansa cewa: yaya za a yi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tura Abubakar xin Raliyallahu Anhu tare da waccan runduna ta Usama, Alhali ya riga ya xaura masa nauyin ba musulmi sallah. Matuqar shi ba zai iya ba saboda rashin lafiyar da yake fama da ita?! Kuma ingantattun riwayoyi mutawatirai sun tabbatar da cewa sai da manzon ya share kwana goma sha biyu kwance yana jinya. Bai kuma sa wani Sahabi bayar da sallar ba, baya ga AbubakarRaliyallahu Anhu.

Ka ga kenan ba wai sallah xaya ce ko biyu, ko ta yini xaya ko biyu ba, Abubakar Raliyallahu Anhu ya waqilci Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bayarwa balle a zaci yiwuwar faruwar wannan dama lissafin da ‘yan Shi’ah ke qoqarin haifarwa. Har ma suna qarawa da cewa; wai ‘yarsa ce Aisha, don dai hilqon tsiya ta tura mahaifin nata ga bayar da sallar; Annabi bai ji bai gani ba.

To ba haka al’amarin ya kasance ba. Manzo ne da kansa ya hore shi da hakan. Kuma tsawon kwanukan jinyar sa.

Ko ka gane. Gaba xayan mutane sun yi ittifaqi a kan cewa tsawon kwanakin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yayi yana jinya, Manzon bai samu fitowa limanci ba. Babu kuma wanda ke waqiltarsa a kan haka sai Abubakar Raliyallahu Anhu kuma ya share tsawon kwanaki yana wannan waqilci. Lokaci da malamai suka kimanta mafi qaramcin sallar da Siddiqu ya jagoranta a cikinsa da sallah goma ce; sallar isha’i ta daren Jumu’a. Aka wayi gari kuma ya jagoranci juma’a, tare da yin khuxubar ta.

Wannan shi ne abin da ingantattun hadisan mutawatirai suka tabbatar:

Haka kuma Siddiqu Ya ci gaba da ba musulmi sallah, bayan wannan salla ta jumu’a, har safiyar ranar litinin. Ranar da yana cikin limancin sallar subahi dinta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yaye labulensa, yayo dogon haske; ya dubi tsayuwar sahun almajiran da ya yaye, a jami’ar farko ta musulunci, suna koyi da jami’insu Siddiqu.

A lokacin da Sahabbai suka ji a jikinsu cewa ana kallon su. Suka kuma daga kai suka ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kaxan ya rage hankalin su ya rabu biyu. Shi kuma ma’aiki daya fahimci haka sai ya saki labulen.

Wannan shi ne gani na qarshe da suka yi wa Manzon, yana raye hantsi na gab da qarewa a wannan rana ya ce ga garinku nan.

 2.34 Ba Rashin Yarda Ba Ne

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa kuma wai: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava wakilta Abubakar ba a kan wani al’amari, tsawon ra yuwarsa. A maimakon haka ma sai dai ya shugabantar da Umar xan Asi a kansa, wani lokaci. Wani lokacin kuma yasa shi qarqashin jagorancin Usama. Qarewa da qarau ma, ko lokacin da Manzon ya tura shi isar da saqon surar Bara’a,ba afi kwana uku ba, Allah ya yi wa manzon wahayi da ya karvi saqon daga gare shi ya ba wani (Ali RA). Wai haka kuma aka yi.

Xan Shi’ar ya kammala da cewa wai: to ya za a yi mai hankali ya yarda da shugabancin wanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai yarda da shi ba. Kuma ma har Allah da kansa yayi horo da dakatar da shi daga isar da saqon ayoyi goma kacal daga cikinsurar Bara’a? Wai ya za a yi mai hankali ya yarda da irin wannan mutum a matsayin shugaba?!

Martani: Ko shakka babu wannan magana qarya ce feqaqqa. Domin masana tarihin musulunci, da malaman tafsiri, dana sira, da na hadisai da fikhu, da wasunsu duk sun tabbatar da cewa Abubakar Raliyallahu Anhu ne ya waqilci Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a hajjin sheqara ta tara; hajji na farko a tarihin musulunci, wanda musulmi sukayi daga birnin Madina. Idan a kwai wani, hajji da za’a ce musulmi sunyi kafin wannan, sai fa wanda suka yi bayan anci garin Makka da yaqi nan take, a qarqashin jagorancin Asyad xan Abilt-Asi xan Umayyata, mutumin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya shugabantar a kan mutanen Makka, bayan wannan nasara. Wannan hajji da aka yi a qarqashin jagorancin wannan Sahabi anyi shi ne a cikin shekara ta takwas. Shekara na dawowa kuma sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tura Abubakar Raliyallahu Anhu bayan sun dawo daga yaqin Tabuka, don ya jagorancin hajjin wannan shekara. Ya kuma Umarce shi da shedawa kafiran Makka cewa: daga wannan shekara an haramta wa da wani mushriki aikin hajji, balle xawafi uryan.

Ta kuma tabbata cewa babu wani daga cikin Sahabbai da Manzon Allah ya tava naxawa irin wannan waqilci sai Abubakar Raliyallahu Anhu ka ga wannan abin godiya ne ga Allah. Wani abin ma shi ne, Ali Raliyallahu Anhu na cikin waxanda Abubakar xin Raliyallahu Anhu ya jagoranta a lokacin. Wanda ma a lokacin da ya isa Makka, sai Abubakar Raliyallahu Anhu ya tambaye shi: kazo ne a matsayin shugaba ko talakka? Shi kuwa ya ce: A‘a na zone a matsayin talakka.

Haka wannan aikin hajjin ya guda na; Aliyu na sallah bayan Abubakar Raliyallahu Anhu tare da sauran musulmi, ya na kuma sauraron umurninsa kamar yadda kowa ke saurare; babu wani abu da musulmi suka yi wa Abubakar Raliyallahu Anhu a wannan lokaci face ka ji amon muryar Ali Raliyallahu Anhu a ciki.

Haka kuma Abubakar Raliyallahu Anhu ne mutum xaya kwal daga cikin Sahabbai , wanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya waqilta ya riqa bawa musulmi sallah tsawon kwanakin jinyarsa ta ajali.

Ka ga waxannan waqilce- waqilce biyu da Abubakar Raliyallahu Anhu ya yi wa manzo, darajoji ne guda biyu daya kevanta dasu. Savanin irin waqilcin da wasu Sahabbai suke yi masa; irin su Ali Raliyallahu Anhu da wasunsa; Babu wani nau’i na waqilci da Ali Raliyallahu Anhu ya yi wa manzon, face wasu Sahabbai sun yi masa irinsa ko wanda ya fishi.

Wannan kenan. Haka nan kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava shugabantar da Usamatu ko Amir xan Asi a kan abubakar ba Raliyallahu Anhu a matsayin waqillai. Nagartattun malamai sun yi itfaqi a kan haka.

Ita kuwa qissar jagorancin Amir xan Asi ga Abubakar da sauran Sahabbai Raliyallahu Anhu Xan Shi’ar yasa son zuciya a ciki.

Yadda al’amarin ya faru a haqiqa shi ne: Watarana ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tura Amru xin ya jagoranci yaqin zatis- salasilu, wanda za a yi da Bani uzurata; kawunnan shi Amru xin. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi haka ne don wataqila, hakan ta zama sanadiyar musuluntarsu, ganin xansu gaba-gaba.

Tafiyar su keda wuya kuma sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi shawarar qara kabrin jagorancin rundunar. A inda ya tura Abubakar da Ubaidatu harma da Umar Raliyallahu Anhu da wasu Sahabbai daga cikin Muhajiruna. Ya kuma yi masu gargaxin cewa: ku haxa kai dashi kada ku bari a ji ku.

Bayan sun isa, Ubaidatu madugun wannan ayari na biyu ya cewa Amru: Manzon Allah ya turomune mu kama muku wannan daga. Saboda haka idan lokacin sAllah ya yi, sai kowanenmu; ni da kai, ya jagaranci rundunarsa Salla. Don gashin kanmu muke ci. Sai Amru ya ce: A’a, ashe ba cewa kayi manzo ya turoku ne ku kama mana daga ba? Ya ce : Eh, haka ne.

Sai Amru ya ce: To ai, ba batun cin gashin kai kenan za ku yi Sallah ne a bayana. Sai Ubaidatu, ganin irin yadda Amru ya kafe, ya ce: To ba komai, da ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umarce ni da cewa, kada inyarda ajimu da kai. Nan take Abubakar ya qara daddale wannan magana ta haxa kai tare da qarawa Ubaidatu qwarin gwiwa a kanta. Wannan ra’ayi kuwa na Abubakar shi ne mafi dacewa.

Daga nan sai suka ci gaba da Sallolin su bayan Amru a matsayin liman. Amma kuma kowa yasan cewa darajarsa ba ta kai tasu ba.

Amma cewar da xan Shi’ar ya yi wai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya karve isar da saqon suratul bara’a daga hannun Abubakar Raliyallahu Anhu bayan kwana ukku, wai saboda rashin yarda da aminci. Kuma wai ma Allah Subhanahu WaTa’ala ya yi masa wahayi da hakan.

Wannan magana ko shakka babu qarya ce, da kowa ya san qarya ce. Amma kuma babu mai musun cewa xauke saqon waccan sura (ayoyi) daga hannun abubakar zuwa na Ali Raliyallahu Anhu umurni ne daga Allah, amma ba rashin yarda ba ne. Bari kaji yadda abin yake, ya kai jahili uban jahilai.!

Sayyidi Abubakar Raliyallahu Anhu ya waqilci Manzo a hajjin wannan shekara ta tara kamar yadda ya ummarce shi. Bai dawo garin Madina ba sai da anka qare aikin hajji. Ya kuma shelantawa kafiran Makka saqon manzo na shekara; cewa kada mushrikin daya sake aikin hajji daga wannan shekara ,balle yayi xawafi uryan; abin da suka al’adanta. Abubakar ya shelanta wannan saqo kowa naji, sauran Sahabbai na yi masa amshi, har ma da Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu a cikinsu.

To dama akwai daddalallin arkawwura tsakanin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da mushrikan Makka. Dawowarsu Abubakar Raliyallahu Anhu daga wannan aiki na hajji keda wuya, sai nan take Manzon ya sake tayar da Ali Raliyallahu Anhu don ya koma ya walwale waxancan arqawwulla, tunda mushrikan sun kasa tsare alfarmarsu.

Dalilin kuwa da ya sa Manzon, bai bari Abubakar radiyallahu anhu ya qarqare ayyukan wannan shekara na sakwanni a matsayin waqilinsa ba shi ne: da ma a al’adar Larabawa babu wanda ya isa a kulla wani arqawari da shi ko ya walwale shi, daga cikin wasu mutane, sai shugabansu ko wani daga cikin danginsa na jini. Saboda haka ne Manzon ya tura Ali Raliyallahu Anhu ba don komai ba; kuma iyakar abin da ya tura shi yayi kenan. Saboda haka ne ma Alin ya kasance yana Salla bayan Abubakar Raliyallahu Anhu yana kuma biyar sawunsa a cikin ayukan hajji kamar yadda sauran musulmi keyi saboda shi Abubakar xin ne waqilin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na wannan shekara.

 2.35 Siddiqu Ba Jahili Ba Ne

Sai kuma xan Shi’ar ya ci gaba da cewa wai: kuma saboda tsabar jahilci Abubakar ya tava sa aka yanke hannun hagun wani varawo; saboda bai san na dama ne ake yankewa ba.

Martani: ko shakka babu cewa Siddiqu jahili ne, bai san cikin da wajen wannan mas’ala qanqanuwa ba, qarya ce bayyananna. Inda ma har cewa aka yi yana ganin yanke hannun hagun varawo shi ne mafi dacewa, bisa ga na dama. Da maganar tafi xan shiga. Domin kuwa babu inda Alqur’ani ya bayyana cewa lalle ne idan za’a yanke hannun varawo a yanke na dama, balle.

Xan Mas’ud ne, a salon qira’arsa ya tafi a kan yanke hannun dama; ba na hagu ba. Kuma sai kawai daga nan abin ya zama “sunna”. Shi a wurinsa, maimakon a karanta ayar kamar haka: “Faqda’u Aidihima”( ku yanke hannayensu) sai ya karanta ta da: “Faqda’u Aimanahuma” ( ku yanke hannayensu na dama). Ka ga kenan mas’alar ta ijtihadi a salon qira’a ce.

Kuma ma duk aje wannan jerangiya. A wane littafi, ko daga bakin waye xan Shi’ar ya naqalto cewa, Abubakar Raliyallahu Anhu ya yanke hannun hagun varawo. Ya faxa masa asalin maganar da isnadinta. Mu dai mun bi diddigin littafan masana tarihin musulunci na haqiqi, amma ko misali mislin wannan magana babu a ciki. Kai! Ko malaman da suka shahara da tattara wandararrun magangannu (al-ikhwabat) basu naqalto wannan magana ba. Su ne kuma gaba-gaba a fagen jinjinawa Abubakar da ganin girmansa Raliyallahu Anhu .

 2.36 Aliyu Mai Wuta Aljihu

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Wani abin kunya kuma da Allah waddai da Abubakar ya yi, wai shi ne qone Fuja’atis-salami da ya yi a wuta. Alhali Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana horo da wuta.

Martani: Idan dai har qone wanda ya cancanci qonewar, kunya ne da Allah waddai to Ali Raliyallahu Anhu ya fi cancanta da qunyar. Don shi ne mai wuta aljihu a jerin Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Domin kuwa akwai ingantattar magana da ke tabbatar da cewa ya qone wasu mutane masu yawa daga cikin Shi’ah Gullatu. Harma da labarin haka ya kai kunnen xan Abbas, Sahabin yayi Allah waddai dashi har ya ce: Da nine shi, ba zan qone su a wuta ba. Saboda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana yin azaba da abin da Allah ke azaba dashi. A maimakon haka sai dai in sare kawunansu. Saboda cewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yayi: ku kashe duk wanda ya canza addinin sa.

Da wannan magana ta kai kunnen Alin, Sai ya ce: kash! Yanzu xan Ummul-fadhli zai yi wannan magana?!

Ka ga kenan Ali Raliyallahu Anhu shi ya fi dacewa da wannan suka da xan Shi’ar ya yi wa Abubakar Raliyallahu Anhu Don shi ne ya qone dubban jama’a da wutar dake aljihunsa. Idan kuwa har ‘yan shi’a za su iya shafe shi da mai su haxe tattare da haka, to kuwa Abubakar Raliyallahu Anhu yafi cancanta su fara shafawa suhaxiye. Domin kuwa kowanensu ya xauki matakin da ya xauka ne, a matsayinsa na shugaba mai wuka da nama.

 2.37 Barewa Ba Ta Gudu Xanta ya yi Rarrafe

A nan kuma xan Shi’ar ya soki lamarin Abubakar Siddiqu Raliyallahu Anhu da cewa, wai masaniyar da yake da ita da hukunce-hukuncen shari’a ba ta taka qara ta qarya ba.

Ga abin da yake cewa: mafi yawan hukunce-hukuncen shari’a sun gagare shi (Abubakar) sani; don bai san hukuncin kalalah ba. Don riwaito shi (Abubakar) da kansa yana cewa: A kan abin da ya shafi kalalah, sai dai in faxi ra’ayina kawai. Idan nayi muwafaqa, to nufin Allah. Idan kuma na kuskure to sharrin sahaixan ne.

Xan Shi’ar ya ce: saboda haka ne, sau saba’in yana bawa kaka haqqin kalalah. Ka ga wannan, na nuna tatatarsa(Abubakar) a faqon dimi.

Ka ji kai!

Martani: ko shakka babu, wannan magana qarya ce hamshaqiya.

Da gaskiya ne Abubakar ya jahilci mafi yawan hukunce- hukuncen shari’a, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba zai ba shi damar yin fatawa da Alqalanci a gabansa ba, ba tare da kuma ya ba wani Sahabi irin wannan dama ba. Har kuma ya kasance yana shawara da ganawa da shi fiye da kowa daga cikin Sahabbai, Umar na rufa masa baya.

Abubakar Raliyallahu Anhu nefa, da yawa daga cikin malamai, irin su: Mansur xan Abdul Jabbar as- Sam’ani da wasunsa, suka riwaito cewa kan malamai ya haxu a kan kasancewarsa mafi ilimi a cikin wannan al’umma. Wannan kuwa tabbas ne. Domin kuwa a lokacin halifancinsa, babu wata mas’ala da musulmi za su shiga tajin- tajin a kanta, face ya walwale masu zare da abawarta. Ta hanyar amfani da iliminsa da kafa masa hujjoji daga cikin Alqur’ani da sunna.

Misalin wannan shi ne irin yadda ya tabbatar masu da rasuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama; ya ceci imaninsu, ta hanyar kafa masu hujja da ayar Alqur’ani. Sannan ya bayyana masu inda ya kamata a yi wa Manzon makwanci. Ya kuma wayar masu da kansu a kan halacci da wajabcin yaqar waxanda suka hana zakka. Wanda kafin haka har ruxani ya kama Umar Raliyallahu Anhu shi ne kuma, a taron da aka yi a saqifafatu Bani Sa’idu, ya tabbatar wa Sahabbai da cewa: lallai idan ba Quraishawa aka danqawa halifanci ba; kowa an kaba shi da sakal. Wannan, a yayin da wasu kejin cewa ana iya bayar da shi ga waxanda ba Quraishawa ba. Ko ma sune suka fi su cancanta da haka.

Wannan kenan. Kuma ai da Abubakar Raliyallahu Anhu jahili ne, da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai waqiltar da shi ga aikin hajjin farko a tarihin musulunci, daga birnin Madina ba. Ka kuwa san mas’alolin aikin hajji sune mas’aloli mafi sassarqiya a cikin mas’alolin ibada. Da kuwa bai naqalcesu nakalta ba, ba abin da zai sa Manzon ya shugabantar da shi a ibadar. Haka kuma waqilcin daya sa shi na limanci. Ka ga shi ma ba a sa jahili. Ta kuma tabbata cewa shi ne kawai Sahabin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya waqilta ga jagorancin aikin hajji da limancin salla.

Bayan wannan kuma. Littafin da Abubakar Raliyallahu Anhu ya wallafa a kan sanin makamar zakka, shi ne littafi mafi inganta a wannan hauji. Shi ne kuma wanda Anas ya karva daga hannunsa. Shi na kuma madogarar malaman fikhun musulunci a kan sha’anin zakka. To in ji.

A taqaice babu wanda zaice ma, komai iliminsa, ga wata mas’ala ta shari’a da Abubakar Raliyallahu Anhu yaci tuwon gigi a cikinta, kamar yadda wasu Sahabbai suka ci.

Za mu yi wannan magana idan lokacin ta yayi.

Ita kuwa cewar da xan Shi’ar yayi, wai Abubakar bai san hukuncin kalala ba. Saboda haka ne yayi amfani da ra’ayinsa...

To sai muce: ai barewa bata gudu xanta yayi rairahe; A matsayin Abubakar Raliyallahu Anhu na xan hannun daman Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kuma babban almajirin makarantarsa, hukuncin kalala ya yi masa kaxan.

Amfani da ra’ayinsa da ya yi a cikin wannan hukunci, na daga cikin abubuwan dake nuna zurfin iliminsa. Kuma haka ne tasa junhurun malamai suka karvi ra’ayin nasa da hannun biyu- biyu, ba yan rasuwarsa, a matsayin tsayayyen hukunci a kan al’amarin kalalah; wato wanda ba yada mahaifa ko ‘ya’ya raye.

Kuma amfani da ra’ayi (hasashe) a cikin hukuncin shari’a ba gare shi farau ba. Umar da Usman da Ali kansa, da xan Mas’ud da Zaidu xan Sabitu da Mu’azu xan Jabalu Raliyallahu Anhu duk suna amfani da hasashensu a cikin hukunce- hukunce. Kuma a duk lokacin da hasashen mutum ya dace da gaskiya, Allah zai bashi lada biyu; kamar dai irin wannan hasashe na Abubakar Raliyallahu Anhu. Shi ne kuma mafi alheri bisa ra’ayin da mai shi zai kafe kansa, tattare kuma da sanin qundin ladarsa xaya ce. Wato kamar dai ra’ayin da Ali Raliyallahu Anhu ya kafe kansa na neman tilastawa Mu’awiyah ya yi masa bai’a a matsayin halifa. Ra’ayin da a qarshe ya yi sanadiyar zubar da jini da rasa rayuka .

Eh! Ra’ayinsa ne shi kadai tallin tal. A kan haka nema aka riwaito cewa Karsu xan Ubaidu ya ce masa, kafin wuta ta kama: ina son in gane ya Ali, shin wannan ra’ayi da ka yi tsaye kyam a kansa, Umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne koko dai ra’ayin qashin kanka ne? Sai ya karva masa da cewa: Ra’ayina ne dai.

Abu Dawuda da wasunsu duk sun riwaito wannan magana.

To ka ga idan har irin wannan ra’ayi daya zama sanadiyar salwantar rayuka, bai hana jama’a yarda da kasancewar mai shi halifa ba. To qaqa za’ayi da jumhurun malamai suka karva hannu biyu-biyu, kuma bai zama sanadiyar kashe ko kiyashe ba, ya zama dalilin qin yarda da mai shi, ko abin suka a kansa?!

Ita kuwa cewar da ya yi wai sau saba’in Abubakar na hukuntar da hukuncin kalalah ga kaka, maganace ta qarya Xan Shi’ar ya yi. Wadda kuma ke tabbatar da kasancewarsu (‘yan Shi’ah) imaman jahilai da maqaryata.

Wannan hukunci bana Abubakar Raliyallahu Anhu ne ba, babu wanda ya tava riwaito shi daga gare shi.

 2.38 Mafi Yawan Mutanen Kufa Jahilai Ne

A qoqarin wannan xan Shi’a ne, na fifita Ali Raliyallahu Anhu Ya ci gaba da cewa: Ina Abubakar ina imamu Ali! Ai lizami yafi qarfin bakin kaza. Imamu Ali ne fa ya cewa mutane: ku tambayeni duk abin da kuke so, kafin ku nemeni ku rasa. Ku tambaye ni a kan duk abin da keda alaqa da sama’u. Ni kuwa in baku amsa daga nan qasa.

Xan Shi’ar ya kafa hujja a kan wannan magana tasa da cewa: Abul-Buhtari ya ce: Na ga Ali watarana a Kufa; a kan mimbari yana sanye da sillken Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na yaqi. Yana kuma rataye da takobinsa, naxe da rawaninsa kuma sanye da zobensa Sallallahu Alaihi Wasallama a hannu. Nan take sai ya zauna ya kware cikinsa, ya kuma cewa jama’a: ku tambayeni duk abin da kuke so, kafin ku nemi ni ku rasa. Domin haqarqarina cike suke da tarin ilimi. Kuma cikin nan nawa salkar ilimi ce. Ni ne sirrin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne ya tsatsageni da ilimi; ba wahayi ne aka yi mani ba. Wallahi da za’a shimfixa mani darduma in zauna a kai. Zan iya yi wa mutanen Attaru fatawa da Attaurarsu. In kuma yi wa mutanen linjila da linjilar su. Har Allah ya hukunci Attaura da magana, tace: lallai Aliyu yayi gaskiya. Haqiqa fatawar da ya yi maku dai dai take da abin da Allah ya saukar a cikina. Amma kuka kasa ganewa sai kace ba ku karanta al-qur’ani?!

Martani: Ba musun cewa, Aliyu ya ce: ku tambaye ni. Amma ai yana magana ne da mutanen Kufa. Kamar yadda riwayar ta nuna. Ya kuma ce masu haka ne,don su cika shi da tambayoyi, har yayin amsa su, shi kuma ya cika su da ilimin Addini , saboda mafi yawansu jahilai ne; ba suyi tozali da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

Amma ka ga mutanen da ke kewaye da mimbarin Abubakar Raliyallahu Anhu sune manya - manyan Sahabban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama waxanda kuma suka sha suka ya tatil da ilimi mai kabri na addini a hannun manzo Sallallahu Alaihi Wasallama wanda hakan ta sasu kasance mutane mabiya ilimi da kishin addini a cikin wannan al’umma.

A yayin da waxancan mutane da Ali Raliyallahu Anhu ke waccan magana dasu ya ku bayi ne, tabi’ai kawai. Kuma mafi yawansu ashararu ne ko a cikin tabi’an. Wanda hakan ta sa Alin kodayaushe yake yawan kuka da su, tare da xebe masu albarka. Hakan tasa aka wayi gari tabi’ai daga cikin mutanen Makka da Madina da Sham da Basara suka fisu nagarta.

Sannan kuma idan xan Shi’ar ba yada labari: Ai matsayin kowane daga cikin waxannan halifofi huxu a fagen ilimi ba abu ne voyayye ba. Domin kuwa malamai a wancan lokaci da sauran almajiran ilimi, sun hada hancin fatawowi da hukunce- hukuncen da kowane xaya daga cikinsu yayi. Qarshe dai aka jinjina na kowane, sai aka taras da cewa na Abubakar Raliyallahu Anhu sun fi haxuwa. Wanda hakan ke nuna irin yadda ya yi wa sauran fintinqau a fagen ilimi.

Bayan na Abubakar sai na Umar suka biyo baya Raliyallahu Anhu kuma shi ne dalilin da ya sa xan takin saqar da ake samu tsakanin fatawowin Umar da na Abubakar, idan aka xorasu akan ma’aunin nassi, bai taka qara ya qarya ba. Idan aka yi la’akari da yadda kodayaushe na Ali ke yin yamma a lokacin da na Abubakar xin Raliyallahu Anhu suka yi gabas maxauka lada. Da wuya matuqa a samu wani nassi da yaqi amincewa da wata fatawa ko wani hukunci da Abubakar Raliyallahu Anhu yayi.

Kuma ai Xan Shi’ar sanine bai yiba. Abubakar Raliyallahu Anhu ne wanda kodayaushe ke warwarewa waxannan Sahabbai (halifofi) zare da abawa duk wata mas’ala mai rikitarwa. Ba a kuma tava samun wanda ya tava bijire masa a kan haka ba, tsawon rayuwarsa. Sai bayan rasuwarsa ne aka fara jinsu, ana kuma ganin su rana a kan hukunce-hukunce. Don mai kwance daragar, Abubakar Raliyallahu Anhu ya kwanta dama.

Wannan kenan. To amma cewar da ya yi wai Ali Raliyallahu Anhu zai yi wa mutanen Attaura da Linjila hukunci da littafansu, magana ce da ke son nazari. Domin kuwa abu ne sananne kuma tabbatacce cewa al-qur’ani da hadisi da ijma’i sun haramta yin hukunci tsakanin Yahudawa da nasara; wa-su-wa-su sai da abin da Allah ya saukar wa Muhammadu. Ko da kuwa hukuncin bai yi daidai da abin da ke cikin littafin nasu ba.

To ka ga ashe kenan duk wanda ya ce Ali Raliyallahu Anhu ya yi waccan magana, har ya kwarzanta shi da ita. Ko dai ya kasance qaton jahilin addini. Wanda kuma bai san abin da kamata a ajinginawa lamirin Ali Raliyallahu Anhu a matsayin yabo. Ko kuma ya kasance zindiqi ne., da ya yi nufin sukar lamarin Alin. Ta hanyar jingina masa wannan magana da ke jawa wanda ya yi ta zargi da azaba maimakon yabo da lada.

 2.39 Girma Ya Kai !

An dai gama ta xan Shi’ar nan ya cimma gavar abin da yake son tabbatar. Don ga shi yaba Ali Raliyallahu Anhu muqamin “shafe zane” ta hanyar amfani da wani qagaggen hadisi:

Bari ka ji abin da ya ce:

Wai baihaqi ya riwaito, da isnadinsa daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wanda ya ce wai: duk wanda yake son yaga Adamu a cikin rigarsa ta ilimi da Nuhu a cikin rigarsa ta tsoron Allah, da Ibrahim a cikin rigarsa ta haquri, da Musa a cikin rigarsa ta kwarjini, da Isa a cikin rigarsa ta ibada, to yakalli Aliyu xan Abi Dalib. Wai Allah ya tarkata masa duk waxannan siffofi da ya rarraba wa waxannan. Annabawa

Ka ji kai. Lalle girma ya kai!

Martani: kafin komai muna son muja hankalin xan Shi’ar a kan cewa fa, ya manta ya ambaci isnadin wannan hadisi. Kuma idan bai sani ba Imamul-Baihaqi kan riwaito raunana, kai harma da ka gaggun hadisai, a kan abin da ya shafi falaloli. Kamar dai yadda takwararorinsa ma’abuta ilimi suka al’axanta.

Sannan abu na biyu: ko shakka babu wannan hadisi qarya ce aka yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kamar yadda ma’abuta ilimi suka tabbatar. Saboda haka nema duk da irin kwaxayin da suke dashi ga tattara darajojin Ali Raliyallahu Anhu ba su riwaito wannan hadisi ba.

Ka ga nisa’i, a cikin littafinsa mai suna: “Al-khasais”, da Tirmizi a cikin tarin hadisan daya ambata a kan darajojin Ali, duk da kasancewar akwai masu rauni da qagaggu a cikinsu. Amma duk basu ambaci wannan hadisi da makamancinsa a cikin ayyukan nasu ba.

 2.40 Ba Dai A Madina Ba

Bayan wannan kuma sai xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: kuma Abu Umar Az-zahidi ya ce: Abu Abbas ya ce: Ba musan wani daga cikin Sahabbai ba, da ya bugi qirji saboda tarin iliminsa, ya ce wa musulmi, bayan Annabi ya kaura: ku tambaye ni duk abin da kuke so; na tun daga zamanin Annabi shisu har zuwa zamanin Annabi Muhammadu. Sai Ali Raliyallahu Anhu kuma a kan wannan dama ce da ya bayar, manyan Sahabbai irin su Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma da makamantansu, suka dinga yi masa ruwan bama - baman tambaya, yana ba su amsa, har ya shaqe su. Sannan ya ce: ya kai Kumailu xan Zayyad, ka sani tsatsage nake da tarin ilimin da, da zan sami mazaken qwarai da ke iya xaukar sa, da anga abu.

Martani: Wannan magana ba ingantatta bace. Domin kuwa ko shi Sa’alabu wanda ya riwaito ta asalatan bai ambaci isnadinta ba, balle ta cancanci zama abin kafa hujja. Kuma hasali ma, Sa’alabu baya cikin malaman da suka san kabli da ba adin hadisi, balle ya iya gane gangariyarsa da mai sanqara. Wanda hakan za ta iya ba wani damar iya bugun qirji ya ce: hadisi kaza ya inganta a wurin Sa’alabu. Kamar yadda ake iya yin garkuwa da riwayar Ahmad ko Yahya xan Mu’inu ko Axuwa uba Buhari, da matara kama da su.

To ko waxannan malaman, da makamantansu daga cikin waxanda suka yi malin sa’alabu a wannan fage. Kan ambaci hadisan da ba su da tushe. Balle makama, a cikin ayyukansu, balle shi. Muna iya yi wa Sa’alabu uzuri domin wannan magana, ya riwaito tane daga bakin irin mutanen nan da suka kware a fagen halin hankaka, na mayarda xan wani nata; don ba sukan ambaci sunayen waxanda suka samo magana daga gare su ba.

Wannan kenan. To kuma tafi, mu xauka cewa gaskiya ne Ali Raliyallahu Anhu ya yi wannan magana. To ba ko a Madina ba; daidai lokacin halifancin Abubakar ko Umar ko Usmanu Raliyallahu Anhu Ali Raliyallahu Anhu ya na da dama da sararin faxin haka amma a Kufa, lokacin da yake halifa. Don hakan ta zama wani qarani da salon jawo hankalin mutanenta zuwa ga qaratu da neman sanin duk abin daya kama ce su sani, daga wurinsa. Saboda asalatan su mutane ne masu tsananin ragganci da kasawa fagen neman ilimi.

Wani abu dake qara tabbatar da ingancin wannan fixa da muka yi wa wannan magana, shi ne, kasancewar kumailu nan tabi’i. Bai yi tare da Ali Raliyallahu Anhu ba sai a Kufa. Ka ga wannan na tabbatar mana da cewa leke su da Ali Raliyallahu Anhu yayi; ya gama fahimtar kasawarsu a fagen ilimi tasa ya yi waccan magana. Ko alama Ali Raliyallahu Anhu ba zai ‘iya buxa baki ya fadi irin wannan magana a cikin Muhajiruna da Ansaru ba. Allah ya daxa yarda da su, amin.

Sannan kuma cewa Abubakar Raliyallahu Anhu ya tava tambayar Ali Raliyallahu Anhu wani abu na ilimi wala. Amma da an tsaya ga Umar Raliyallahu Anhu to maganar na sauraruwa. Don shi ya kan yi shawara da Sahabbai irin su Usman da shi Aliyun da Abdurrahman da xan Mas’udu matsayinsu na ‘yan majalisar shawara.

Ka ga ko a haka akwai magana.

 2.41 Akwai Abin Da Siddiqu Ya Gani

Har yau dai mutumin naku; sarkin jahilai bai gaji da xaukar zunubi ba a cikin haqqin Sahabbai. A nan kuma cewa ya keyi wai, Siddiqu ya yi wa hukuncin Allah zinbire tunda bai kama Khalidu xan Wahdu ya aika shi lahira, saboda ya kashe malik xan Nuwairatu, tattare da kasancewarsa musulmi ba. Wanda hakan har tabawa shi Khalidun damar aure matar Malikun, ya kuma yi baiko da ita a daren da tsohon mijin ta ya baqunci lahira. Kuma ma wai har sai da Umar ya jawo hankalin Abubakar xin Raliyallahu Anhu a kan wajabcin kashe Khalidun. amma wai saboda tsabar qin Allah, Abubakar Raliyallahu Anhu yayi shayulatin vangare da maganar tasa. Duk inji xan Shi’ar.

Farkon abin da za mu fara faskarawa xan Shi’ar a ka, a matsayin martani kan wannan magana shi ne: idan har akyale wanda ya kashe wani ba bisa haqqin shari’a ba, wani abin kunya da ashane ga shugabanni, to, lalle kuwa dangin Halifa Usmanu nada babbar hujja akan qayar bayan da suka tayarwa Ali Raliyallahu Anhu akan lalle ya bimasu kaxin jinin xan’uwansu. ya kuma qi. Ka kuwa san a matsayin Usmanu Raliyallahu Anhu na halifa ga musulunci. Wanda kuma aka yi wa kisan gilla; bai ji bai gani ba. Darajarsa ta linka ta Maliku xan Nuwaira ta fiye da sauran yawan qasa. Amma kuma duk da haka Aliyu yaqi kashe makasansa. Wanda hakan ya zama qwaqqwaran dalilin da dangin na Usmanu Raliyallahu Anhu suka riqa a kan qin yi wa Aliyu mubaya’a.

To. Idan kuwa har kuna ganin akwai wani uzuri na shari’a daya hana Alin kashe maka shin Usmanu Raliyallahu Anhu kashe makashin maliku shi ne mafi qarfi. Idan kuwa kuna ganin cewa abubakar Raliyallahu Anhu baya da wani dalili a kan haka, to ko, Ali Raliyallahu Anhu shi ne mafi zama marashin dalilin a kan yarda wa makasan Usmanu Raliyallahu Anhu ci gaba da rayuwa.

Ka ga kenan a haka, ta tabbata cewa jahilci ne daya yi wa ‘yan Shi’ah riga da wando, da kuma tinka da walwala, suka sa suna zargin Abubakar Raliyallahu Anhu tare da qorafi a kansa, a wannan ‘yar kankanuwar matsala. Alhali ga wata qasaitacciyar matsala can ta kewaye Ali Raliyallahu Anhu amma sun sa qafa sun taushe; kamar ba a yiba. Tattare da cewa duk mai hankali da basira isassa ya san cewa, lalle akwai abin da Siddiqu ya gani.

Ba a kan Abubakar Raliyallahu Anhu kawai suka tsaya ba. Sun soki lamarin halifa Usmanu Raliyallahu Anhu shi ma. A kan wai yaqi kashe Ubaidullahi xan Umar saboda kisan gillar da ya yi wa Hurmuzanu.

To, duk wannan martani, ya isa kariya ga waxannan halifofi biyu masu girman daraja.

Wannan kenan. To idan kuwa har ‘yan Shi’ah za su yi qarfin halin ce mana: To ai Ali Raliyallahu Anhu nada Uzuri a kan rashin kashe makasan Usmanu, kamar yadda muka qaddara yiwuwar su ce. Qarshe kuma suce mana uzurin kuwa shi ne: Rashin cikar sharuxxan dake wajabta qisasi; koko a’a, Aliyun bai san waxanda suka yi mugun aikin ba. Ko kuma ya sansu, amma sun fi qarfinsa saboda kasancewarsu buwayayyi. Ko kuma dai wani dalili mai kama da wannan.

To sai mu ce masu mu kuma: Eh! To mun ji, mun kuma yarda. Sai dai, su ma makasan Maliku da Hurmuzanu, duk babu wanda dalilan da za su wajabta qisasi a kansa suka cika. Saboda akwai shubuha (ruxani) a cikin mas’alolin nasu. Shubaha kuwa dalilice mai kwari da ke tunkuxe haddi.

Na san kuma saboda tsananin qarfin hali da kangara, suna iya sake cewa: Bawata shubuha dake ciki. Tunda har sai da Umar da Ali suka tabbatar wa Abubakar da Usmanu Raliyallahu Anhu rashinta, tare da wajabcin kashe makasan; wato Khalidu da Ubaidullahi. Amma suka qi.

To amsarmu a nan itace: Idan wannan na zama dalili, me ya hana Ali Raliyallahu Anhu kashe makasan Usmanu, tunda har sai da Xalhatu da Zubairu da wasu Sahabbai suka tabbatar masa da wajabci da yiwuwar haka? Me ya hana shi?

Kuma aje ma duk wannan. idan tonon silihi kuke so a yi, bisimillah...!

Kun mace cewa, Abubakar Raliyallahu Anhu bai kyale waxanda suka ba shi shawarar kashe khalidu haka nan ba; sai da ya kafa masu hujjar da ta gamsar da su, da cewa: qisasi bai wajabta kan khaladu. Saboda abu ne mai yiwuwa qwarai ya kasance a kan haqqin Allah na ya kashe Malikun. Saboda a mafi rinjayen zato dakare kuma barden musulunci irin Khaladu, ba zai kashe musulmi haka kaxai ba; saboda haka lalle ne akwai wani ijtihadi daya dogara a kansa, kafin ya aika shi lahira.

Amma rashin gamsuwar da Ali Raliyallahu Anhu yayi da waxanda su ka ba shi shawarar kashe makasan Usmanu, mummunan yaqi ta haifar tsakaninsu. Wanda muninsa yafi na kisan da aka yi wa Usmanu. Kowa yasan irin nauyin abin da ya faru a yaqin sibbaini da Jamalu.

To idan kuwa har za’a iya yi wa Ali uzri a nan, to yi wa Abubakar Raliyallahu Anhu uzuri a can shi ne mafi cancanta da dacewa. A matsayinsa na waxanda suka dogara a kan wani karvavven ijtihadi.

Na daxe da sanin cewa ‘yan Shi’ah na iya izgilin cewa, maganar kisan gillar da aka yi wa Usmanu, ba wata matsala bace, domin jininsa halattace ne. Saboda yadda ya tozartar da alfarmar dukiya da halifancin musulunci.

To, harwayau dai. Mu qaddara cewa waxancan abubuwa sun halatta jinin Usman xin Raliyallahu Anhu Amma babu mai hankali da musun cewa jinin Maliku xan Nuwairatu yafi cancanta da halatta. Domin kuwa, hasali babu wanda ke iya tabbatar da rashin cancantar Malikun da wancan kisa da khalidu ya yi masa ta fuskar shari’a; mu dai a wurinmu babu wannan dalili.

Amma halifa Usmanu Raliyallahu Anhu dalilai da nassosa daga cikin al-qur’ani da sunna sun tabbatar da cewa kisan da aka yi masa zalunci ne. Kuma kowa ya san fifikon da Usmanu yake dashi a kan xan Nuwairata, Allah kadai ne ya san iyakarsa.

Kuma babu ta yadda za a yi wanda ya halatta jinin Usmanu, ya iya haramta na Ali ko Husaini Raliyallahu Anhu Domin kuwa dalilan dake tabbatar da haramcin jininsa sun fi qarfi da bayyana bisa waxanda ke haramta nasu. Abubuwan da ke kaiwa ga sa a zubar da jinin mutum, qalilan ne matuka a cikin al’amarin Usmanu, idan sha’anin Ali da Husaini Raliyallahu Anhu kuma ruvavvun dalilan da makasan Usman suka lave bayansu, sun fi waxanda makasan Ali da Husaini suka lave bayansu nuqa da ruva.

 Fara lissafi.

Ka ga dai halifa Usmanu bai kashe musulmi ko xaya ba. Bai yaqi kowa a kan rashin yi masa muba a ba; ko niyar haka bai kulla ba. Mu tsaya ma anan.

To ka ga renin hankali da ilimi ne, a ce wanda ya shaya daga da musulmi don neman shugabanci, jininsa haramtace ne. Don abin can da ya yi ijtihadi ne. Amma wanda bai yaqi ko sauro ba, a ce jininsa ya halatta, ko shakka babu Usmanu Raliyallahu Anhu shi ne mafi cancanta da kasancewa mai haramtaccen jini, kuma mujtahidi a cikin irin yadda ya riqa dukiya da halifancin al’umma.

Wannan kenan. Sannan kuma mun yarda da cewa jinin Malilku xan Nuwairata haramtacce ne asalatan. Amma khalidu ya halatta shi a kan wani tarihi, har ya aika shi lahira. To ai, wannan ba komai ba ne balle har ya halatta ko wajabta kashe khalidun.

Ah! Kun manta da Usamatu xan Zaidu ya kashe wani mutum a wurin yaqi, bayan ya furta kalamar shahada. Har Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ga laifinsa;. Ya ce: ya zaka kashe mutum bayan ya ce: La’ilaha illal-lahu?. Ya maimata haka ga Usama har sau uku.

Amma duk da haka Annabi bai nemi Usama da biyan wata diyya ko kaffara ba a kan haka, balle ramuwa, tunda ya yi kisan ne a kan wani tawili. Ya kuma yi nadama a qarshe.

Sannan zancen auren matar Maliku da yin bai ko da ita a daren da yabar duniya, da shi Xan Shi’ar ya ce khalid yayi, magana ce da bata inganta ba. Ko da kuma Allah yasa ta ingantan, to babu wani dalili da zai wajabtar da haddin jifa a kansa. Domin kuwa malaman fiqihu sun qara wa junansu ilimi ta hanyar kasuwa gida biyu a kan wajabcin iddar mutuwar miji kafiri tantagarya ko na tawili. Wasu suka ce wajibi ce, wasu suka ce ba wajibi ba ce. Kamar yadda ta faru tsakaninsu a kan wajabcin iddar a kan zawariyyar da mijin ta ya rasu. Sabanin iddar saki, wadda take wajabtarwa. Ita kan babu wani ka-ce-na-ce a kanta. Lalle ne sai an tsalkake mahaifa kafin ayi wani aure.

Amma ita iddar mutuwa, ta na wajabta ne, daga lokacin da aka tofa fatiha anka daura aure. Amma da mijin zai mutu a dai - dai lokacin da kuma yake kafirta asalan, iddar na ci gaba da zama wajibi kan matar ko qaqa? A nan ne malamai suka xan wasa kwakwalwa. Kamar yadda suka yi akan wajabcinta kan matar da irin wannan miji yayi baiko da ita bayan xaurin auren kuma ta yi wanki xaya bayan haka.

To amma idan qaddarar ridda ce ta fada masa, sai kuma ga mutuwa kwaram. A mazhabar Shafi’i da Ahmad da Abu Yusuf da M uhammad za ta yi idda, amma ba ta wadda mijinta ya rasuba, ta dai wadda aka rabu da ita, rabuwa ba’ina. Saboda aure na vaci da zarar miji yayi ridda. A wurin Shafi’i da Ahmad kuwa irin wannan rabuwa da ke faruwa saboda ridda, ba a ce mata saki. Saboda haka ne ma suka qi wajabtawa matar iddar rasuwa, sai dai ta rabuwa ba’ina.

Idan kuma dama bai yi baiko da ita ba, ya rasu to ba kowace irin idda a kan ta, a wurinsu. Kamar yadda ba zata yi iddar ba ko da sakin ta yayi, matukar dai bai .kusance ta ba.

Amma irin waccan rabuwa ta mutuwa, kamar rabuwa ce ta saki a wurin Maliki.

To, idan har ka fahimci wannan qullin makodo na malaman fikhu, zaka yarda da cewa lalle akwai abin da Siddiqu ya gani ya qi kashe khalid. Domin kuwa bai kashe maliku ba sai da ya gama yanke masa hukuncin ridda. Ka ga idan har anyi sa’a bai kusanci matar ba, shi Maliku. To ba za tayi wata idda ba, a matsayin gaba xayan malamai. Idan ma har koya kusance ta, to wanki xaya ya isa tabbatar da tsarkin mahaifarta, da ba dole sai ta yi cikakkar idda ba, bisa xayan zancen malaman; wanda xayan sun ke wajabta mata wanki uku.

Idan kuwa asalatan kafiri ne, matar ba za tayi idda saboda mutuwar sa ba, bisa xayan zancen waxannan malamai. Idan kuma har tsarkin mahaifar tata ba zai tabbata ba, sai idan tayi wanki bayan mutuwar mijin, to haka ba zata wajabta akan taba, sai idan ta tava wanki kafin baikon.

A haka ma, akwai malaman da ke jin wani sashe na kwanakin wanki ya isa tabbatar da tsarkin mahaifa.

A ta kaice dai mu a iyakar saninmu, duk yadda aka kixa kuma aka raya, ba yadda za a yi wannan mas’ala ta kasa karvar sallamar ijtihadi karvavve a idon shari’a. Kuma sukar wani da irin wannan al’amari xabi’a ce ta jahilai. Kuma abune da Allah da Manzonsa suka haramta.

 2.42 Gadon Fatima Da Laqabin “Halifa”

Daga nan kuma sai xan Shi’ar ya ci gaba da cewa wai: kuma Abubakar ya savawa umurnin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama tunda har ya hana Fatima gadon mahaifinta, da Fadak. Kuma ya qaqabawa kansa laqabin “halifatu Rasulullahi” alhali ba Annabin ne ya zave shi halifansa ba.

Martani: Bari mufara da matsalar gadon Fatima. Wannan batu mun riga munyi magana a kansa. Mun kuma tabbatar wa duniya da cewa matakin da Abubakar Raliyallahu Anhu ya xauka a kansa shi ne madaidaici. Wanda saboda haka ne ma gaba xayan musulmi suka marawa baya a kai, in ban da wasu ‘yan Shi’ah. Haka kuma mun tabbatar wa ku da cewa matsayin nasa hukunci ne da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yayi. Kuma abin da ‘yan Shi’ah nan ke yayatawa a kan wannan matsala, da ta Fadak, babu gaskiya a cikin ko kaxan.

Kuma halifancin da suka biyo bayan Abubakar Raliyallahu Anhu babu wanda ya tayarda wancan hukunci nashi. Kuma babu wani abu; ko da kwatankwacin Allura, da Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma suka xaukar wa kansu, ko suka ba iyalinsu daga Fadak xin, balle a ce. Kuma Fadak ba kome ba ce, idan aka yi la’akari da irin abin da waxannan halifofi suka mallaka wa Banu Hashim.

Kuma yau da wani daga cikin musulmi zai yi qorafi, da kafa hujja da cewa, ai Ali Raliyallahu Anhu ma ya hana wa xan Abbas da sauran Bani Hashim ko sisi daga cikin Baitil mali, har hakan ta sa xan Abbas xin ya dahe wasu kuxaxe a Busra yasa su mala. Na san ba abin da za kuce, a qoqarin bawa Alin kariya illa cewa, ya yi haka ne saboda tabbatar da gaskiya da riqon amana, a matsayinsa na shugaba adili; saboda haka bai kamata a zarge shi ba.

To ku sani Abubakar Raliyallahu Anhu shi ya fi dacewa da cancanta da irin wannan kariya. Domin kuwa son da yake yi wa Fatima da qoqarin tsare alfarmarta, sun fi waxanda Aliyu Raliyallahu Anhu ke yi wa xan Abbas. Kuma matakin da xan Abbas ya xaukarwa Aliyu Raliyallahu Anhu na nuna kasancewarsu qare ba a tsaga ba. Savanin Fatima ga Abubakar Raliyallahu Anhu. ko alama abin arzikin da ke tsakanin Ali da xan Abbas, bai kai wanda ke tsakanin Abubakar da Fatima ba Raliyallahu Anhu.

Shi kuwa laqabin “Halifa” da xan Shi’ar ya ce wai, Abubakar Raliyallahu Anhu ya qaqalawa kansa, qaryar banza ce. Duk wanda ya san tarihin musulunci yasan cewa musulmi ne suka yi wa shi wannan laqabi a qaran kansu.

Kuma idan kalmar “Halifa” na nufin wanda anka halifantar, kamar yadda maganar xan Shi’ar tazo, to ai cewa Abubakar Raliyallahu Anhu halifa ba laifi bane, don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne da kansa ya halifantar dashi. Kamar yadda Ahlus-Sunnah suka yi imani. Idan kuwa kalmar na nufin wanda ya maye gurbin wani, ko da shi wanin bai yi umurni da hakan ba. kamar yadda jumhuru suka yi imani, to ai kuma babu sunan da ya kamata a ambaci Abubakar xin da shi in ba “Halifa” ba Raliyallahu Anhu .

Wannan ma’ana ta biyu kuwa, itace abin da Alqur’ani da sunna ke tabbatarwa. Bari ka ji. Allah Ta’ala na cewa: Sannan muka sanya ku masu mayewa (halifa) a cikin qasa daga bayansu, domin muga yaya kuke aikatawa (10:16).

 2.43 Ya Kuma Dira A Kan Umar

Bayan kuma da wannan xan Shi’ar ya gaji da cin mutun cin Abubakar Raliyallahu Anhu sai ya dira a kan Umar Raliyallahu Anhu.

Ga alama haka zai bi manyan halifofi xaya bayan xaya.

Farkon abin da ya fara da shi, shi ne cewa wai; Daga cikin abubuwan dake tabbatar da cewa halifofin nan uku ba kowa bane, a wurin Allah, akwai abin da aka riwaito a cikin littafin: “Hilyatul-auliya’u”. Marubucin littafin; Abu Nu’aimi al-Hafiz ya ce wai anji Umar na cewa, a lokacin da ya kai gargara: kaicona ina ma dai rago Allah ya yi ni, daga cikin ragunan dangina. Su yi ta kiyona har kitse ya rufe mani qoda. Qarshe su yanka ni liyafa ga mafi soyuwa daga cikin baqinsu. Su soya rabin namana rabi kuma suyi romo. A taru ayi mani kaf, in zama turoso ba mutum.

Xan Shi’ar ya ce: To ka ga wannan magana ta Umar, wai tayi dai - dai da ta kafircin da zai buxa baki gobe lahira ya ce: kaitona dama dai na zama turxaya (79:40).

Daga nan kuma sai ya koma kan xan Abbas, ya ce wai shima ya ce,

a lokacin da ya kai gargara: wallahi dana mallaki zinarin da ya yi yawan qasa da na bayar dashi, don in tserewa tashin hankalin ranar lahira.

Mutumin naka ya ce ita kuma wannan magana wai dai - dai take da cewar da Allah Ta’ala ya yi: kuma da waxanda sukayi zalunci suna da abin da ke cikin qasa gaba xaya, da misalinsa a tare dashi, lalle da sun yi fansa dashi daga mummunar azaba (39:47).

Sannan ya ce: To don Allah muna son masu hankali su dubi waxannan maganganu, na waxannan mutane biyu, su kuma auna su dacewar da Ali Raliyallahu Anhu yayi:

-          “Wai yaushe ne mutuwa zata xauke ni, in sadu da masoyana;... Muhammadu da rundunarsa.

-          Wai yaushe ne zan yi tozali dasu ... in kuma ga yadda za a yi tawayya da marasa arziki daga cikinsu”

Da kuma kalimar da ya yi a lokacin da xan Muljamu ya xora shi kan godaben zuwa lahira wadda ya ce:

-          “Wallahi na taki sa’a”

Wato xan Shi’ar naso ne ya ce, Umar kafiri ne. Xan Abbas kuma azzalumi ne Raliyallahu Anhu. wal’iyazu Billahi.

Martanin mu a kan wannan magana shi ne; ko alama wannan zance bai kai lasaba kuma wata alama ce, da ke nuna kabrin jahilcin xan Shi’ar. Domin kuwa ba Aliyu Raliyallahu Anhu ne aka tava jin ya furta irin waxancan kalmomi dake nuna jaruntaka da rashin fargaban zuwa lahira ba. Wasu Sahabbai da ba su kai darajar sa, balle ta Abubakar ko Umar ko Usmanu Raliyallahu Anhu har ma da wasu daga cikin masu kafirta Alin, daga cikin Harijawa, sun furta irin waxancan kalmomi.

An riwaito cewa Bilalu, Sahabin da Abubakar Raliyallahu Anhu ya yi wa hidima da karimcin “’yanci”, an ji yana yin aras da matarsa, a lokacin da ya kai gargara. Hankalinta ya tashi tana cewa: yau mun shiga uku mun lalace!. Shi kuwa yana cewa: can gareki ni kam farin ciki nake yi. Gobe zan haxu da masoyana; Muhammadu da rundunarsa

Bilalu kenan. Sahabin da Umar Raliyallahu Anhu ya yi wa “Allah ya isa” shi da wasu Sahabbai, saboda sun fitine shi, a kan lalle sai ya raba ko rayen tuxxan Iraqi ga mayaqa. Shekara kuwa bata zagayo ba sai da Allah ya karvi rayuwarsu gaba xaya.

Amma ka ji kalmomincan da Ali Raliyallahu Anhu ya furta basu fi waxannan da shi ya furta zaqi da qarfi ba.

Wani kuma abu dake qara tabbatar da cewa, ba Ali Raliyallahu Anhu ne farau a irin wannan baiwa ba shi ne abin da Abu Nu’aimi xin ya riwaito a cikin wanna littafi nasa “al-Haya” inda ya ce: kudai’i da Hasan xan Abudullahi da Amir xan Sayyaru da Abudul-Hamid xan Hushub, daga Abdur-Rahman xan Ganami, daga kuma Harisu xan Umairin, wanda ya ce: watarana an soki Mu’azu da Abu Ubaidata da Shuraihabilu xan Husnata da Abu Malik al-Ash’ari, a wurin yaqi. Sai Mu’azu ya ce: Ai wannan ba abin mamaki ne ba. Wannan suka da aka yi mani a rana xaya, muna kuma dangin juna, wata rahama ce daga wurin Ubangijinmu, wadda Annabinmu ya roqar mana. Kuma nagartattun bayi waxanda suka gaba cemu suka ce”Amin” a lokacin da Annabi ya ce: ya Ubangiji ka yanka wa mutanen gidan su Mu’azu babban rabo daga cikin irin wannan rahama.

Mu’azu Ya ci gaba da cewa; marece na gaba dayi, bayan wannan adu’a sai kuwa aka kaiwa xana Abdur-Rahmanu Bikrah; xaya daga cikin ‘ya’yana da nafi so, suka. Ina dawowa masallaci na same shi murtut da fuska, yana cikin zilla. Na ce masa me ya faru ne Abdurrrahman? Sai ya ce: Bari baba. Gaskiya ta tabbata daga Ubangijika, kada kuma ka zama cikin mutane masu ruxani.

Sai ni kuma nace masa: Ni kuwa da yardar Allah zan kasance daga cikin mutane masu haquri.

Mai riwaya Ya ci gaba da cewa: Haka Mu’azu Ya ci gaba da rungume wannan xa nasa, har zuwa lokacin da ransa ya fita. Safiya nayi aka yi jana’izarsa.

Anan kuma shiga ta kawo ga Mu’azu, shi ma aka soke shi. Ya shiga cikin wani irin magagi; ransa na zuwa yana dawowa. Amma hakan ba tasa ya fita hayyacinsa har yamanta da Allah. Duk lokacin daya farko za a ji yana cewa: Ya Ubangiji! A shirye nake mutuwa ta xauke duk lokacin daka shata. Kuma ka sani, wallahi ina matuqar son ka, har cikin quryar xakin birnin zuciyata.

Mu’azu kenan.

Haka ita ma cewar da xan Shi’ar yayi Ali Raliyallahu Anhu ya ce: “wallahi na taki sa’a” ba gare shi farau ba. An riwaito cewa Amiru xan fuhairiyatu; barwan Sahabi Abubakar Raliyallahu Anhu A wannan matsayi nasa, da bai kai na Aliyun ba. Shi ma ya faxi irin wannan kalma a lokacin da yake gab da xauke shexa, a wani wuri gab da Najdu, a sanadiyar sukuwar sallar da magabata suka yi kansa da makamai, a wannan wuri da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tura shi tare da wata runduna.

Malaman tarihi suka ce, a wurin ne wani kafiri da ake cewa Jabbaru xan Salimi, ya kai masa suka ta qarshe, wadda ta kama jikinsa sosai, ya kuma tabbata lalle tashi ta qare. To a lokacin ne ya ce: “ wallahi na taki sa’a.” jin haka sai Jabbaru xin ya ce: me yake nufi da wannan magana? Sai Urwatu xan Zubairu ya ce: wannan sa’a ta tabbata domin kuwa mun ga mala’iku sun halarto jana’izarsa.

Haka kuma an riwaito cewa a lokacin da aka kaiwa Shubaibu al-Hariji suka, ta kama jikinsa sosai, shi ma ya ce: Allah ka karvi wannan shahada tawa.

To ba waxannan magabata ba. Ni xin nan na san wani mutum daga cikin amitattu, wanda a lokacin daya kai gargara sai aka ji yana cewa: ya masoyina ga ni nan isowa don mu sadu.

Wannan kalami ne Ya ci gaba da maimaitawa har ransa ya fita. Irin waxannan misalai akwai su da yawa.

Sannan kuma wancan tsoro da fargaba da suka kama Umar Raliyallahu Anhu a lokacin gargararsa, ba wani abu hakan ke tabbatarwa ba illa tsananin tsoron Allah, wanda ke tsatsage da birnin zuciyarsa. Wanda kuma ke nuna cika da kamalarsa a fagen ilimi. Saboda Allah Ta’ala ya ce: Malamai kawai ke tsoron Allah daga cikin bayinsa(35:28)

Kuma tsoron Allah da bayyanarsa sunna ce da ta samo asali daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama Domin da yawa idan yana salla, ake jin qirjinsa na zavarvaka kamar tukunya ta tafasa, saboda tsananin kukan da yake shara.

Ita kuwa waccan magana ta Umar Raliyallahu Anhu da xan Shi’ar ya ce wai, daidai take da abin da kafiri zai ce gobe qiyama: Kaicona da ma turxaya aka yoni (79:40)

Wannan zumuncin da xan Shi’ar ya qulla tsakanin waxannan kalamai biyu, aiki ne irin na jahilai. Domin kuwa babu abin da ya haxa wannan magana da waccan saboda ta farko an yi tane a duniya; gidan da ake neman lahira a cikinsa. Kuma maganar na nufin tabbatar da tsoron Allah ne a cikin zuciyar Umar Raliyallahu Anhu ka ga kenan zai sami ladar haka daga wurin Allah. A yayin da ita kuma magana ta biyu za a yi tane a ranar qiyama; ranar da ba a karvar tuba kuma wani aiki mai kyau ba ya da wani anfani.

Ka ga ashe hanyar jirgi daban ta mota daban.

Kuma a irin wannan tafarki Sayyida Maryam tace: kaitona, da dai na mutu a gabanin wannan kuma na kasance wani abu walaqantacce wanda aka manta (19:23)

Ka ga babu mai hankali da ilimin da zai daidaita matsayin wannan gurin mutuwa da Maryam ta yi, a duniya, da wanda wani kafiri zai yi a lahira; kamar cewar da ‘yan wuta za suyi goben: Ya maliku! Ubangijinka ya kashe mu mana (maliku) ya ce, “ lalle ku mazauna ne (43:77) Da kuma gurin da waxanda sukayi zalunci a duniya za suyi a goben kamar yadda Allah Ta’ala ke cewa: kuma da waxanda suka yi zalunci suna da abin da ke cikin qasa gaba xaya, da misalinsa a tare dashi, lalle da sunyi fansa dashi daga mummunan azaba, a Ranar qiyama. Kuma abin da basu kasance suna zato ba, daga Allah ya bayyana gare su (39:47)

Ka ga waxannan ayoyi suna ba mu labarin halin da waxannan mutane za su kasance ne a ciki gobe qiyama ne kawai; ranar da tuba da tsoron Allah ba su da wani amfani.

Amma a nan duniya, sanannen abune cewa, a duk lokacin da bawa yayi tsoron Ubangijinsa, to yayi ibada. Wadda kuma Allah zai bashi lada a kai, Ya kuma amintar dashi gobe qiyama. Duk kuwa wanda ya daidaita matsayin wannan tsoron Allah da wancan, to, daidai matsayinsa yake dana wanda ya daidaita matsayin haske da duhu, ko inuwa da rana, ko na rayayyu da matattu.

Sayyidina Umar:

 2. 44 Umar: Mai Gani Da Hasken Allah

A wani yunquri kuma da xan Shi’ar yayi na bice haske da martabar Umar Raliyallahu Anhu, sai ya xauko zancen rubuta wasiyya, a matsayin makami, inda ya ce: Mawallafan ingantattun littafan hadisan na shida, sun riwaito daga Musnadin xan Abbas, wanda ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya nemi Sahabbai, a lokacin da yake jinyar ajali, dasu kawo masa alqalami da farar takarda don ya rubuta masu abin da idan suka yi riqo da shi, ba za su vace ba a bayansa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na bayar da wannan umurni, sai Umar ya ce: ina sa ran magagin mutuwa ne ya kama shi. Kuma ai littafin Allah ya ishe mu.

Umar na qare faxin haka sai wuri ya kece da hayaniya. Jin haka sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: ku watse ku ba ni wuri, bai kamata kuna rikici gaba na ba. Daga nan kuma sai xan Abbas ya ce: Amma dai ba mu ji daxin hana Manzon Allah ya rubuta mana wannan wasiyya ba.

Abu na farko kenan.

Abu na biyu kuma inji xan Shi’ar shi ne, wai a lokacin da labarin rasuwa Manzon Allah ya bazu Umar Raliyallahu Anhu bai yarda ba, har ya ce: Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ba zai mutu ba sai ya yanke hannaye da kafafun wasu mutane. A nan ne Abubakar Raliyallahu Anhu ya ce ya kama bakinsa, ya kuma karanta masa ayar dake cewa: lalle kai mai mutuwa ne, kuma suma lalle masu mutuwa ne (39:30) da kuma wadda ke cewa: ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, za ku juya akan dugaduganku? (3:144)

Qare karanta waxannan ayoyi da Abubakar Raliyallahu Anhu yayi ke wuya, sai Umar ya ce: Na ji kamar ban tava jin su ba .

Kafin mu shiga walwale bakin zaren wannan magana a matsayin martani, bari mu fara shimfida darajojin Umar Raliyallahu Anhu waxanda suka tabbata a cikin ingantattun hadisai. Waxanda za su sa mai karatu ya gane matsayinsa na wanda ke gani da hasken Allah. Kuma cewar da ya yi “wata qila magagin mutuwa ne ya kama Manzon Allah” hasashe ne irin na masu ilimi da hangen nesa.

Sayyidina Umar nada darajojin da babu wanda keda irinsu daga cikin Sahabbai in ba Abubakar Raliyallahu Anhu ba.

Ya zo a cikin sahihu Muslimu daga Aisha Raliyallahu Anhu wadda ta ce: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance yana cewa: An yi mutane masu kyakykyawan hasashe a cikin al’umomin da suka gabace ku. Idan akwai irinsu xaya a cikin al’umma ta, to, Umar ne.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi amfani ne da kalmar “muhaddisuna” a cikin wannan hadisi da wanda zai biyo bayansa. Kalmar Larabci wadda muka fassara da “kyakykyawan hasashe”. Mun yi haka ne ta hanyar shiga rigar arzikin malam da Wahabi, wanda ya ce: kalmar na nufin “waxanda Allah ke yi wa ilhamu”.

Haka kuma Buhari ya riwaito daga Abu Hurairata, wanda ya ce Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: An yi mutane masu kyakykyawan hasashe a cikin al’ummomin da suka gaba ce ku. Idan akwai wani irinsu a cikin wannan al’umma tawa to Umar xan Haxxabi ne.

A wani matakin kuma Buhari cewa yayi Annabi ya ce: An yi wasu mutane a cikin Bani Isra’ila; waxanda suka gabace ku, waxanda ke magana ta zama kata’un, tattare kuma da cewa su ba Annabawa ba ne. Da akwai xaya daga cikinsu cikin al’ummata , to Umar ne.

Haka kuma yazo a cikin wani hadisi ingantacce hadisi daga xan Umar, wanda ya ce, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: watarana yayi mafarkin an zo mani da wata kwarya cike da nono. Na sha na qoshi, har a kaihuna suka nuna. Da na rage sai na miqawa Umar xan Haxxabi.

Sai Sahabbai suka ce: To da me ka fassara wannan nono ya Manzon Allah? Ya ce: Da ilimi.

A wani hadisi kuma sahihi, wanda aka samo daga Sa’id, wanda ya ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: watarana nayi mafarkin wasu mutane sanye da ‘yan guntayen tagguna da basu wuce qirazansu ba. Wasu kuma nasu sun xan gota nan. Can sai ga Umar xan Haxxabi tasa rigar har tana jan kasa.

Sai Sahabbai suka ce: To da me ka fassara wannan riga ta Umar ya Manzon Allah? Ya ce: Da faxaxxiyar addini a hannunsa.

Wannan kenan. To mu koma kan asalin wannan magana kuma. Wato abin can da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yaso ya rubuta wa Sahabbai a matsayin wasiyya. Wannan abu sananne ne baga Umar kawai ba. Domin kuwa Aisha Raliyallahu Anhu ta faxa a cikin wani ingantaccen hadisi, cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce mata a liqacin da yake jinyar ajali: kira mani mahaifinki (Abubakar RALIYALLAHU ANHU) da xan’uwanki. Zan rubuta masu wata takarda. Don ina tsoron wani mai guri yayi guri, kuma mai cewa ya ce: Ni ne mafi cancanta. Amma Allah da muminai su qi kowa sai Abubakar.

Ya kuma zo a cikin sahihul Bukari daga Kasim xan Muhammadu, wanda ya ce: Aisha Raliyallahu Anhu ta xaga murya watarana tace: Boni ko zai ci fatun lihidda! Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: idan ina raye zan yi maki istigfari in kuma yi maki addu’a. Sai tace: kaicona! Wallahi ina zaton dai kana sone in mutu. Ina tabbata maka idan haka ta faru zan ci gaba da zama rataye ga wasu daga cikin matanka. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: kenan ni bonin zai ci ba fatun lihidda ba. Haqiqa nayi nufin in aika wurin Abubakar da xansa don in danqa masa amana. Don kada gobe wani mai faxa ya faxa ko mai guri ya gurata. Qarshe kuma Allah da muminai Abubakar za su zava.

Ka ga kenan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya riga yayi ishara da abin can da yake son rubutawa, tare kuma da bayyana dalilansa a kan haka.

Wannan darga ta qare qarau ga mai hankali. Shi kuwa Umar kokwanto ne ya kama shi a kan haqiqanin matsayin waccan magana da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yayi; shi yayi ta ne a sakamakon zafin ciwo da kusantowar ajali, koko yana cikin hayyacinsa?!

Wannan hasashe da Umar Raliyallahu Anhu yayi ba laifi ba ne. Domin tabbas Annabawa na arashin lafiya. Kuma ko ba komai halin da Manzon ke ciki ya isa tabbatar da haka. Kuma kalmar “ina sa rai” wadda ya yi amfani da ita a lafazin nasa, na nuna cewa bai yanke wa matsalar hukunci ba; a’a yana dai kokwanto da hasashe ne. Ka kuma sani Umar bai fi qarfin kokwanto ya kama shi ba, tun da shi ba Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ba, wanda Allah ya ba lasisin ma’asumanataka. Kuma wannan kokwanto daya kama shi, an yi sa’a yana wurin zama a cikin al’amarin, tunda ga Annabi kwance kuma ribxe a cikin zafin masassara. Saboda haka yayi hasashen ko zafin ciwo ne yasa shi maganar, ta yadda ake iya yin wani xan batun zucci kafin a saurareta kai tsaye. Koko karvar ta nan take wajaba, ba tare da wani nazari ba?! Kamar dai yadda ya yi kokwanton tabbacin mutuwarsa daga baya, har sai da ya gama gane lalle dai ya rasun, sannan ya miqa wuya.

Kuma ka ga cikin ikon Allah, sai abin can da Umar Raliyallahu Anhu ke hasashe ya tabbata. Wato abin can da manzo yaso rubutawa, ya riga ya faxawa Nana Aisha Raliyallahu Anhu shi. Saboda haka ne ma daya ga ruxani ya shiga tsakanin Sahabbai a kan abun, ya kuma san ko da ya nace a kan sai ya rubuta maganar, hakan ba zai kawar da ruxanin ba, tunda ya riga ya faru, sai ga fita batun hakan. Ya kuma san cewa Allah zai haxa kansu a kan abin da ya yi niyyar rubuta masun. Kamar yadda ya riga ya faxa cewa: qarshe kuma Allah da muminai Abubakar za su azaba Raliyallahu Anhu.

Ita kuwa cewar da xan Abbas yayi: Bamu ji daxin hana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rubuta mana wannan wasiyya ba..... magana ce dake nuna rashin jin daxin zai tabbata cikin qirazan waxanda ba su yarda da halifancin Abubakar Raliyallahu Anhu ba samsam. Ko kuma suka yi shakkunta. don tabbas da rubutun ya yiwo, da abin da ya farun nan bai faru ba.

Amma duk wanda ke da masaniya da barwa Abubakar Raliyallahu Anhu amanar al’umma, da Annabi yayi, ba wani rashin jin daxi gare shi.

 Alhamdu lillahi

Rashin jin daxi na nan ga waxanda ke zaton cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yaso ne ya rubuta cewa Ali Raliyallahu Anhu ya gade halifarsa kai tsaye bayan ya qaura. Kuma vattatu ne bisa haxuwar kan gaba xayan malaman sunna da na Shi’ah.

Eh! Tabbas haka wannan magana take. Domin kuwa malaman sunna sun haxu a kan cewa Abubakar Raliyallahu Anhu shi ne mafifici a cikin Sahabbai, kuma shi ne mafi cancanta da halifanci a lokacin. A yayin da su kuwa malaman Shi’ah, waxanda ke ganin cewa Ali shi ne mafi cancanta da kujerar a lokacin, cewa suke yi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya riga ya daddale maganar kasancewar Alin yazama mai jiran gadon manzanci, da yankakken “nassi” tun kafin wannan lokaci na jinyar. Ka ga kenan ba bukatar wani rubutu.

To ina suka ga makama? Babu

Kuma da ‘yan Shi’ah za su ce: A’a akwai buqatar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya rubuta waccan naxi da ya yi wa Ali Raliyallahu Anhu duk da yake yayi shi ne a cikin dubu; Don gudun kada al’umma ta musa nan gaba.

To shi mu karva masu da cewa, duk al’ummar da ke iya musanta abin da aka yi (magana) cikin dubu, to musa wanda aka yi (rubutu) cikin ‘yan kwarorin mutane yafi sauqi da cancanta gare ta.

Kuma muna nan akan bakar mu, na cewa in dai har wancan nassi (magana) ya inganta, to babu buqatar wannan rubutu yanzu. Saboda baya halatta ga Annabawa su jinkirta wata magana (saqon Allah) har sai lokacin mutuwasu. kuma da wajibi ne a kan manzon ya rubuta waccan wasiya, shakku da kokwanto da hayaniyar da Sahabbai suka sami kansu a lokacin ba ta hana ya dage a kan sai an kawo kayan rubutun ya rubuta; maganar Umar Raliyallahu Anhu ko wani daga cikinsu duk ba za ta hana shiba, a matsayinsa na mafi xa’a ga Allah daga cikin bayinsa.

Ka ga fita batun rubutun da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ya tabbatar da cewa ba wajibi ba ne. Ba kuma wani abu ne mai muhimmanci a addini ba, wanda rubuta shi a lokacin ke wajaba. Don da haka ne, da ya yi.

Kuma shi Umar ya riga ya gama leqen cewa abin ba wani abu bane. Don inda wani abu ne, kuma Annabi ya zartar da hukuncin lalle sai ya rubuta shi, lalle Umar Raliyallahu Anhu a matsayinsa na mai hasashe (ijtihadi) kawai ba zai yi gangancin wandarewa ba. Kokwanton da ya aure shi a kan gaba xayan lamarin ko sashensa; daga baya, ba zai ba shi damar yin haka ba. Ko banza kokwanto a kan kasancewar abin da yake gaskiya gaskiya, ya fi sauqi bisa ga yanke masa hukuncin zama qarya.

Ina fatar dai ka gane.

To kuma tafi naji. A matsayin Umar Raliyallahu Anhu na mai ijtihadi iyakar abin da za’a iya cewa yayi na rashin sa’a shi ne, kuskure. Allah kuwa ba ya kama mai ijtihadi da wani laifi don ya kuskure daidai. Kamar yadda ba zai kama Ali Raliyallahu Anhu da kuskuren da ya yi a cikin ijtihadi, ya wajabta ma wata mata da mijinta ya rasu yin iddar mutuwa ta tsawon mafi tsawon iyakoki biyu ba. Tattare kuma da abin da ya tabbata ya kuma inganta daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne cewa a lokacin da aka ba shi labarin cewa Abus-Sanabilu ya yi wa Subai’atul-Aslamiyyah irin wannan fatawa. Sai Annabi ya ce: Qarya Abus-Sanabilu ke yi. Jeki ki auri duk wanda kike so kin halatta.

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qaryata Abus-Sanabilu ne, saboda bai isa yin ijtihadi ba. Musamman ma da yake Manzo na kusa.

Amma ka ga ba za’a qaryata Ali da xan Abbas Raliyallahu Anhuma ba, saboda sun bayar da irin wannan fatawa. Domin sun bayar da ita ne bayan rasuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kuma ba su da masaniya da wannan qissa ta Subai’atu.

 2.45 Halifa Umar ba Azzalumi ba ne

A wani qoqari kuma na cin mutuncin Umar Raliyallahu Anhu da tozarta shi, sai xan Shi’ar ya yi masa qazafin zalunci, da wasu siffofi da halaye na naqasa. Inda ya ce wai, bayan da nana Fatima Raliyallahu Anha ta yi wa Abubakar Raliyallahu Anhu gargaxi a kan abin da ya shafi Fadak, sai halifan ya rubuta takarda, wadda ke nuna ya mallaka ma ta qasar; ta fita hannun kowa daga wannan lokaci. Wai kuma fitowarta daga wurinsa ke da wuya, sai ta yi kicivis da Umar Raliyallahu Anhu wanda ya qwace takardar daga hannunta ya qona. Wannan abu ya dugunzuma ranta sosai. Nan take ta yi ma sa baqar addu’a da “Allah ya isa”. Wai kuma sakamakon wannan addu’a ne, Abu Lu’alu’ata ya yi wa Umar abin da ya yi masa.

Kuma xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Haka kuma saboda rashin sanin hukunce-hukuncen shari’a, Umar ya yi wa haddin Allah wanda ya hau kan Mugiratu xan Shu’ubata targazo, ta hanyar qin hukunta shi. Kuma ya kasance yana bai wa sauran matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama fiye da abin da suka cancanta daga Baitul-Mali. Amma sai ya ba wa Aisha da Hafsatu Raliyallahu Anhuma dirhami dubu goma kowace shekara. Ya kuma canza hukuncin Allah a kan waxanda aka kora.

Martani:

Ko shakka babu wannan magana baqar qarya ce, irin wadda ba masanin da zai kokwanton ta. Domin babu wani malamin hadisin da ya tava riwaito ta, balle a iya gane isnadinta. Kuma tabbataccen abu ne, Abubakar Raliyallahu Anhu bai tava tabbatar wa Fatima Raliyallahu Anha ko wani mallakar qasar Fadak ba. Kuma ba ta yi wa Umar wata baqar addu’a ba.

Kuma ko shakka babu abin da ya faru ga Umar Raliyallahu Anhu na kisan gillar da Abu Lu’alu’ata ya yi masa, wani karamci ne daga wurin Allah Ta’ala irin wanda Ali da Husaini Raliyallahu Anhuma ba su samu ba. Eh! Ba su samu wannan karimci ba mana. Tunda xan Muljamu da Yazidawa waxanda suka kashe su, musulmi ne ‘yan‘uwansu. Shi kuwa Abu Lu’alu’ata, makashin Umar Raliyallahu Anhu kafiri ne baqin. Ka kuwa san ba abin mamaki ba ne kafiri ya kashe musulmi, balle ma halifa sukutum. Ai ko banza babu abin da ke tsakanin mumini da kafiri sai yaqi.

Saboda haka ne shahadar wanda ya rasa ransa hannun kafiri ta fi ta wanda ya rasa nasa hannun musulmi xan’uwansa girma da karvuwa a wurin Allah. Kuma ta yaya ne ma za’a iya gane cewa addu’ar da Fatima wai ta yi wa Umar xin Raliyallahu Anhu ce sanadiyyar kisan nasa, tunda sayyidar ta rasu ne bayan halifancin Abubakar da wata shidda kafin qarewar na Umar Raliyallahu Anhu ka ga abin na da kamar wuya.

To, kuma ko qaddarawar muka yi Nana Fatima ta yi wa Umar xin waccan baqar addu’a, ta fatar ajalinsa ya kasance hannun kafiri. Ai wannan abin alheri ne da alfahari ta roqa ma sa. In kafiri bai kashe shi ba sai rayuwarsa ta xore? Ai irin wannan addu’a ce Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi ga Sahabin da matsayinsa ya kai gare shi, wato ya roqar masa shahada. Har ma Sahabbansa suka gano cewa, da zaran sun ji Manzo ya ce: “Allah ka yi gafara ga wane”. To sun san shahadarsa ta kusa. Saboda haka ne ma, wani lokaci sukan katsi nunfashinsa, idan ya yi wa wani Sahabi irin wannan addu’a, su ce: ya Manzon Allah! Ba mu gaji da ganinsa ba.

Haka kuma a da ‘yan Shi’ah za su dage a kan cewa lalle sakamakon zaluncin da Umar Raliyallahu Anhu ya yi wa Fatimar ne da baqar addu’ar da ta yi masa, wancan abu ya faru gare shi. To, sai mu ce masu: Idan dai har hankalin masu hankali zai karvi wannan magana taku, to, ba zai kasa karvar ta wanda ya ce: kisan gillar da xan Muljam ya yi wa Ali Raliyallahu Anhu ya faru ne sakamakon zaluncin da ya yi wa mutanen Siffin da Harijawa da “Allah ya isa”ﷺ‬ da suka yi masa. Kuma Abu Sufyana da Harisu ne suka yi wa Husaini baqar addu’a, ta zama sanadiyyar kashe shi a karbala.

Ita kuma cewar da xan Shi’ar ya yi, wai Umar ya yi wa hukuncin Allah targazo, ta hanyar qin yi wa Mugiratu xan Shu’ubata haddi, qarya ce. Domin kuwa jumhurun malamai sun karvi abin da halifan ya yi a cikin wannan sha’ani da hannu bi-biyu; wato yi wa sauran shedu haddin qazafi, idan suka kasa cika. Kuma sauran malaman da ke ganin ba haka ya kamata hukuncin ya kasance ba, sun gamsu da cewa mas’alar ta ijtihadi ce.

Sannan kuma, kamar yadda muka faxa a baya; abin da Ali Raliyallahu Anhu yayi na qyale makasan halifa Usmanu ba tare da ya hukunta su ba. Shi ne yi wa hukuncin Allah targazo, ba wannan ba. Idan kuwa kuna ganin mai wannan ra’ayi; na ganin laifin Ali, ya yi varna. To, wanda ke ganin laifin Umar Raliyallahu Anhu a cikin waccan mas’ala shi ne babban mavarnaci, bisa la’akari da matsayi da banbancin mas’alolin biyu.

Haka kuma, xan Shi’ar ya soki halifan da cewa, yana ba wa sauran matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama fiye da abin da suka cancanta daga Baitil-Mali. Amma Nana Aisha da Hafsatu sai ya ba su dirhami dubu goma-goma kowace shekara...

Martani: Da Allah ya sa xan Shi’ar nan na cikin masu hankali, to da ya fahimci cewa, ai wannan abu da halifan ya yi, wani abu ne da ke nuna cikar taskai da adalci. Tare da haxuwarsa da Allah, ta hanyar hana zuciyarsa abin da take so.

Kai ka san in ba haka ba, babu abin da zai sa ya fifita wata a kan ‘yar cikinsa a cikin wannan sha’ani na dukiya. Shi a hankali da tunaninsa Hafsatu ‘yarsa da Abdullahi xansa, ba su isa su yi kafaxa-da-kafaxa da sauran matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da mutanen gidansa ba, balle su karvi daidai abin da su suke karva. Daxa balle ma su wuce su, don Ubansu ne halifa.

Tirqashi ka ji masu tuqen dabaibiya malam.

A fahimtar halifa Umar Raliyallahu Anhu arzikin qasa ana raba shi ne ga jama’a gwargwadon girma da xaukakarsu. Saboda haka ne shi, a duk lokacin da ya tashi rabo, sai ya fifita matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a kan sauran mata. Kamar yadda yake fifita Banu Hashim; wato Aliyu xan Abu Xalib da Abbas da sauransu, a kan sauran qabilun da ba su ba.

Duk wanda Umar Raliyallahu Anhu ya fifita a cikin wannan al’amari na rabon arzikin qasa, to za ka taras makusancin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne. Ko kuma yana daga cikin na sahun farko a shiga musulunci. Ko kuma yana da wani abu na bajinta ko mai kama da haka, wanda zai sa ya cancanci wannan fifiko. Har ma an riwaito yana cewa: Babu wanda ya fi wani cancanta da wannan arziki a cikinmu; ina dai la’akari ne da buqatar mutum, ko hidimarsa ga addini, ko sammakosa a cikinsa, ko wadatarsa.

Waxancan mata na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da xan Shi’ar ke zargin Umar Raliyallahu Anhu da basu kuxi mai yawa. Halifan bai yi hakan don tsoron wani abu ko rojin wani ba. Don babu wata dangantaka tsakaninsa balle a ce. Kuma ka ji irin ma yadda ya yi da ‘ya’yan cikinsa, da makaman tansu. Ba ya fifita mutum sai don wani dalili na addini tsantsa. Kuma ko a hakan ma yana fifita mutanen gidan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama tare da farawa dasu, a kan mutanen sauran gidaje. Kuma babu wanda ya bi sawun Umar Raliyallahu Anhu a cikin wannan kyakyawan aiki, daga cikin Usman da Ali Raliyallahu Anhu halifofin da suka zo bayansa, ko wasunsu.

Idan kuwa har za’ayi wani qorafi a kan Umar, kan fifita waxancan mata na Manzo, to sai a kuma yi qorafi a kan fifita Ahlul-Baiti da ya yi a kan wanda ba su ba, tare da gabatar da su. Koko?

 2.46 Gargaxi ne ba Haddi ba

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa wai kuma: Umar Raliyallahu Anhu ya canza hukuncin Allah a kan waxanda ake kora saboda aikata wata kaba’ira.

Martani: Da xan Shi’ar nan ya san cewa, canza hukuncin Allah na tabbata ne a lokacin da aka xauke shi, aka kuma maye gurbinsa da abin da ke walwale shi. Kamar haramta abin da Allah ya wajabta ko halatta abin da ya haramta. Da bai faxi wannan magana ba.

Shi kuwa korar da shari’a ta yarda a yi wa wanda ya sha giya misali, gargaxi ne ba haddi ba. Kuma gargadi a shari’a wani fage ne na ijtihadi. Musamman a kan shan giya. Domin kuwa har Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwanta dama, bai daddale haddin mashayin giya ba ta fuskar yawan abin da za a yi ko siffarsa. Iyakar abin da aka san ya bar wa musulmi a matsayin sunna, shi ne; dukan mashayin da ganyen dabino da takalmi da wutsan tufafi, har ya yi tivis. A yayin da ake bulale mai qazafi da mazinaci.

Abin da Sahabbai suka gada kenan a wannan vangare. Wato “dukan” mashayin giya. Amma vangaren adadin dukan (buloli) Sahabban sun yi amfani da basira, ilimi da gogewarsu, a matsayin ijtihadi. Wasu daga cikinsu suka yi bulala arba’in, wasu kuma tamanin.

Kuma hadisi ingantacce ya tabbata cewa, Ali Raliyallahu Anhu ya ce: kowane adadi aka xauka an yi Sunnah.

 2.47 Allah Ne Kawai ba ya Mantuwa ba ya Kure

A nan kuma Xan Shi’ar cewa yake yi, wai Umar Raliyallahu Anhu kamar Abubakar ne. Shi ma masaniyar da yake da ita da hukunce-hukuncen shari’a ‘yar qanqanuwa ce; saboda wai ya yi umurni da a jefe wata mata da ke da juna biyu, saboda kama ta da laifin zina da aka yi. Sai wai Ali Raliyallahu Anhu ya ce ma shi, idan kana da hujjar sa a kashe ta, to ba ka da hujjar sa a kashe xan da ke cikinta. Wai saboda haka sai Umar Raliyallahu Anhu ya janye umurnin, har kuma ya ce: “Wallahi ba don Ali ba yau da Umar ya halaka”.

Martani: Babu wani abu qasa, da ke tabbatar da kasancewar wannan qissa gaskiya. To kuma ko da mun qaddara kasancewarta hakan, to lalle ne xayan biyu; ko dai ya kasance Umar bai san matar na da juna biyu ba, sai da Ali ya labarta masa Raliyallahu Anhu, ka ga kenan rashin sani ya shiga. Kuma faxakar da shi, da Ali ya yi a kan haka, kamar abin da aka saba ne na, muqarraban shugaba su faxakar da shi a kan abubuwan da suka shige masa duhu, na halayen talakawansa. Ko kuma irin abin da shedu zai bayyana a gabansa. Babu kuwa wani Annabi ko shugaba da ba ya da buqata da irin wannan gudunmawa ta alheri. Hakan kuma ba ya daga cikin hamshaqan hukunce-hukuncen shari’a.

Na farko kenan. Ko kuma a’a ya san da matar na da juna biyu. Amma ya sha’afa da cewa ba a jefe irinta sai ta sauka. Da kuma Ali Raliyallahu Anhu ya tunatar da shi, sai ya gamsu. Ka ga ba zancen rashin sani a nan, sai dai sha’afa. Don da ace ya riga ya gamsu da halaccin jefe irinta, to, babu wanda ya isa ya hana shi zartar da hakan, a matsayinsa na mujtahidi. Tattare da masaniyar da yake da ita da cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci Gamidiyyah da ta je sai bayan ta sauka, ta dawo a zartar ma ta da haddin zinar da ta yi iqirarin ta yi har ta xauki ciki.

To, kuma ai ba abin mamaki ba ne, don wannan mas’ala ta shige wa Umar Raliyallahu Anhu duhu. Kuma ba abu ne da ya kamata a soke lamarinsa a kai ba. Domin kuwa Allah ne kawai ba ya mantuwa ba ya kure, Subhanahu WaTa’ala. Kuma halifa irin Umar, barde, jarumi uban jarummai, kamata yayi a yi masa kyakkyawan zato. Musamman idan aka yi la’akari da yadda ya shugabanci musulmi da kafiran amana. Ta hanyar ba wa kowa haqqinsa, da zantar da haddoda. Da zama Alqalin gaba xayan jama’a, da irin yadda musulmi ya sami ranar baje garinsa a zamaninsa, irin yadda bai samu ba kafinsa.

Babu wani lokaci da za ka taras da halifa Umar Raliyallahu Anhu face, ko dai yana fatawa, ko yana Alqalanci. Ka kuwa san mai cikin cokalin ilimi ba zai iya haka ba ko alama ko?!

To tunda kuwa haka ne, ashe ba aibi ba ne don mai irin wannan fama, ya manta mas’ala xaya daga cikin mas’aloli dubu xari ko fiye, sai da aka tuna masa. Kai! xauki ma bai san ta ba sai da aka sanar da shi. Ai duk xan Adamu ajizi ne.

Kuma ai tabbataccen abu ne, cewa mas’alolin da suka shige wa Ali Raliyallahu Anhu duhu, daga cikin sunnar Manzon Allah, sun fi a qirga. Wasu ma har ya mutu bai san su ba.

Ina fatar baka jahilci haka ba?

 2.48 Halifa Umar ba Jahili ba ne

Wata sukar lamirin kuma, mai kama da waccan itace cewar da xan Shi’ar yayi kai tsaye, wai halifa Umar jahili ne. Saboda ya yi umurni da a jefe wata mahaukaciya saboda samunta da laifin zina da aka yi. Sai da Ali Raliyallahu Anhu ya faxakar da shi cewa, an xauke Alqalami daga kan mahaukaci, har sai ya warke. Jin haka sai Umar ya janye umurnin, kuma ya ce: “Wallahi ba don Ali ba da Umar ya halaka”.

Martani: kafin mu shiga fashin baqin wannan magana a matsayin martani, muna tabbatar wa xan Shi’ar da cewa; Eh! Wannan mas’ala, gaskiya ne ta faru. Amma wannan magana ta cewa Umar xin ya ce ba don Ali ba da ya halaka qari ne; babu ta a cikin lafiyayyar ruwaya.

Nan kenan. Kuma lalle ne Umar Raliyallahu Anhu bai san waccan mata mahaukaciya ce ba. Ko kuma ya sani amma ya sha’afa. Saboda haka ya yi umurni da zartas ma ta da haddin. Amma da aka faxakar da shi ya gamsu ka ga ba abin sukar lamiri a nan.

Koko a’a, halifan ya fahimci cewa haddodin da ake zartarwa a kan masu lafiya, ana zartar da su ne, don alqinta rayuwar duniya, ta hanyar hana wani cutar da wani. Saboda haka babu dalilin da zai hana a hukunta mahaukaci, matuqar ya zo da wani mugun aiki da ke iya cutar da jama’a; waxanda suka haxa da masu hankali da mahaukata. To, tunda kuwa zina mugun aiki ce, da ke cutar da al’umma, lalle, idan mahaukaci ya yi ta a hukunta shi. Amma daga baya sai aka faxakar da shi cewa, irin wannan haddi na zina, haddi ne da Allah Ta’ala bai yi umurni da zartarwa ba, sai a kan mukallafai.

Wannan kenan. Wani abu kuma da ke iya zama madogara, ga halifan a kan wannan ijtihadi nasa, shi ne horon da shari’a ta yi na ladabtar da qananan yara, ta hanyar duka idan suka qi yin sallah. Har Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ku hori yara da yin sallah suna ‘yan shekara bakwai. Ku kuma doke su, idan suka qi, in sun shekara goma. Ku kuma rabe masu shinfixun bacci”.

Bayan wannan kuma, ai ba mutumin da ba ya da hankali ba, ko dabba, a shari’a idan tana fitinar jama’a, daidai ne a kashe ta. Haka idan mahaukaci na fitinar jama’a shi ma aka rasa yadda za ayi da shi a yi maganinsa, sai ta hanyar kisa, ya halatta.

Kuma, waccan dabba da za’a kashe bisa wancan dalili, idan ta gida ce kuma mallakar wani, ba za’a biya shi diyyarta ba, bisa ra’ayin Jumhurun malamai, irin su: Maliku da Shafi’i da Ahmadu da wasunsu.

A taqaice, duk abubuwan da xan Shi’ar nan ya ambata na suka ga Umar Raliyallahu Anhu ko waninsa daga cikin Sahabbai, na kawai tabbatar wa mai hankali da ilimi, xayan abubuwa biyu ne: 1) ko dai ya kasance xan Shi’ar ya faxe su, sakamakon fama da ciwon qarancin ilimi. Ko 2) tsanar wannan bawan Allah da qarancin kishin addini.

Dalili kuwa shi ne, ya xauka cewa halifan ya hana Fatima haqqinta, ya kuma yi son zuciya a cikin rabon arzikin qasa, ya kuma yi wa hukuncin Allah tasgaro da makamantan wannan.

Ka ga a taqaice yana so ne ya ce halifan ba adili ba ne. Alhali kuwa babu inda labarin adalcin Umar Raliyallahu Anhu bai kai ba a faxin duniya. Ta yadda har ma ake buga misali da shi; ana cewa: A yi koyi da rayuwar Umarora biyu. Maganar da malamai irin su Ahmad xan Hmbali da wasu malaman hadisi suka fassara da cewa; ana nufin Umar xan Haxxabi ne da Umar xan Abdulaziz. A ya yin da Abu Ubaidata da wasu malaman Lugga da Nahawu, suka ce: Umarun na biyu na nufin Abubakar ne Raliyallahu Anhu.

A taqaice dai, Umar xan Haxxabi ya tabbata adali.

 2.49 Wannan Shi Ne Halin Bayin Allah Na Gari

Daga nan kuma sai xan Shi’ar ya lalubo zancen qayyade sadakin aure, da halifa Umar Raliyallahu Anhu ya yi, ya soki lamirinsa da shi. Bari ka ji abin da ya ce:

Wani abu kuma da ke nuna kasancewar Umar jahili shi ne, watarana yana huxuba sai ya ce: Daga yau duk wanda ya sake bulbula wa mata kuxin sadaki, to zan karve toliyar in saka ta Baitil-Mali. Yana faxar haka sai wata mace, can daga cikin sahun mata ta xaga murya ta ce: Ya halifan Manzon Allah! Ya za ka hana a ba mu abin da Allah ya yi umurni da a ba mu a cikin littafinsa? Inda ya ce: Alhali kuwa kun bai wa xayarsu qinxari (4:20). Dasa ayarta ke da wuya sai Umar ya ce: Kai madalla da aka samu waxanda suka fi Umar sanin makamar addini har a cikin mata. Na kuma janye wannan magana.

Martani:

Ko shakka babu wannan qissa, na tabbatar da kamalar Umar Raliyallahu Anhu ne kawai, da kishin addini da tsoron Allansa. Da kuma irin yadda yake shirye kodayaushe, ya bar ijtihadinsa ya koma yana saurare da karvar gaskiya, ko da kuwa daga bakin mace ta fito, har ma ya cire hula ya sara mata. Kuma a shirye yake yayi tawali’un tabbatar da fifikon wani a kansa, a cikin irin wannan qanqanuwar mas’ala. Wannan kuwa shi ne halin bayin Allah na gari.

Kuma Alhamdu Lillahi, da ya zan ba sharaxi ba ne, sai mafi girman mutane ya zama wanda babu mai iya faxakar da shi a kan wani abu daga cikinsu, kafin ya karva sunansa. Kuna ina tsuntsun Hudahuda ya ce wa Annabi Sulaiman: Na san abin da ba ka sani ba, kuma nazo maka daga Saba’i da wani labari tabbatacce (27:22)?. Kuma kuna ina Annabi Musa Alaihis Salamu ya ce wa Haliru: Ka yarda in bi ka a kan ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya (18:66)?. Ka kuma san abin da ke tsakanin Annabi Musa Alaihis Salamu da Haliru na fifikon daraja ya fi wanda ke tsakanin Umar Raliyallahu Anhu da na takwarorinsa Sahabbai, balle wata mace. Kuma hakan ba ta wajabtar da kasancewar Halirun ko kusa da darajar Musa ba Alaihis Salamu balle yayi kafaxa-da-kafaxa da shi. Kai! Ba Musa ba, ko Annabawan da suka zo bayansa. Irin su: Haruna da Yusha’u da Dawuda da Sulaimana da wasunsu, duk sun fi Halirun girman daraja; ko an xauke shi a matsayin Annabi.

Kuma tabbataccen abu ne cewa Sahabbai su ne mafificiyar al’umma. Imamus Shafi’i ya ce: Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sun yi mana ko-ta-kwana a fagen kowane irin ilimi da fiqihu da riqon addini da shiriya. Kuma ijtihadinsu shi ne mafi alhairi gare mu, bisa ijtihadinmu a kan kansu.

Imamu Ahmad xan Hambali ko cewa ya yi: Tuwasun Sunnah a wurinmu shi ne riqo da abin da Sahabban Manzon Allah suke a kai.

Abdullahi xan Mas’udu, ya ce: Ya ku mutane! Duk wanda zai yi koyi da wani daga cikinku, to ya yi da waxanda suka riga mu gidan gaskiya. Saboda babu fitinar da ba ta iya faruwa ga wanda yake raye. Ku yi koyi da Sahabban Muhammadu. Don su ne mafiya girma daga cikin wannan al’umma, mafiya kuma nagartattun zukata da zurfin ilimi da sauqin kai. Su ne kuma mutanen da Allah ya zavar wa Annabinsa a matsayin abokai. Kuma mataimaka don tabbatar da addininsa. To, saboda haka ku kiyaye alfarmarsu, ku kuma yi koyi da su. Ku yi kwaikwayon duk abin da kuke iyawa daga cikin halayensu da kishinsu ga addini. Don suna kan tafarkin madaidaici.

Haka kuma an riwaito Huzaifatu na cewa: Ya ku gardawa ku shiga taitayinku. Ku dawo kan tafarkin waxanda suka gabace ku. Idan Allah ya taimake ku a kan haka, to wallahi kun sami babban rabo. Idan kuwa kuka bar tafarkin nan nasu madaidaici kuka dinga mashalo, ba ku gidan Ango ba ku gixan Amarya, to, haqiqa sai magenku ta sha qasari.

 2.50 Halifa Umar Bai Jahilci Haddin Shan Giya ba

Daga nan kuma sai xan Shi’ar ya ce kuma wai halifa Umar Raliyallahu Anhu bai san haddin shan giya ba. Saboda ya sa wa Qudamatu na shafin kwalli a lokacin da ya sha yayi tatil, bisa dalilin ayar da ya karanta masa. Wadda Allah Ta’ala ke cewa a cikinta: Babu laifi a kan waxanda suka yi imani ga abin da suka ci, idan sun yi taqawa kuma suka yi imani (5:93). Sai da Ali Raliyallahu Anhu ya ce wa Umar: Ai Qudamatu ba ya daga cikin mutanen da wannan aya ke magana a kai. Wai sai Umar ya yi sakabo, saboda bai san hukuncin wanda ya sha giya ba. Balle ya zartar wa Qudamatu. Ganin haka sai Ali Raliyallahu Anhu ya ce: ka yi masa bulala tamanin. Saboda shan giya na sa maye da fita hankali da yin qazafi da qaga karya.

Ka ji abin da mutumin ya kafa hujja da shi.

Martani:

Ko shakka babu wannan magana ba haka take ba. Domin kuwa ilimin da Umar Raliyallahu Anhu ke da shi a kan wannan mas’ala, ya fi qarfin a tsaya ja-in-ja don tabbatar da shi. Kafin wannan mas’ala ta Qudamatu, ta tabbata a tarihin halifancin Abubakar da shi Umar xin Raliyallahu Anhu cewa sukan yi wa mashayin giya bulala arba’in ko tamanin wani lokaci. Wani lokacin ma, idan al’amarin bai hayaqa ba, Umar Raliyallahu Anhu kan sa a aske kan mashayin ko a kore shi daga Madina a matsayin gargaxi. Sukan kuma yi amfani ne da kabar dabino wani lokaci, idan za su bulale mashayin. Wani lokaci kuma su sa takalmi ko hannayensu ko wutsan mayafansu, su faffalke sa.

Ita kuwa waccan qissa ta Qudamatu, gaskiya ne ta faru. Amma xan Shi’ar yayi son zuciya a cikinta, irin yadda dai ka san ya saba yi. Ga kuma haqiqanin yadda al’amarin ya faru:

Abu Ishaka al-Jauzajani da wasu malamai sun riwaito daga xan Abbas, wanda ya ce: watarana Qudamatu xan Maz’unu ya sha giya ya yi tatil. Sai Umar ya ce ma sa: Ya aka yi haka? Sai shi kuma ya karva ma sa da cewa: Ai Allah Ta’ala ya ce: Babu laifi a kan waxanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan qwarai, a cikin abin da suka ci. Idan sun yi taqawa kuma sun yi imani, kuma sun aikata ayyuka na qwarai (5:43). Ka kuwa san ina daga cikin Muhajiruna na farko-farko, waxanda kuma suka halarci yaqin Badar da na Uhudu.

Daga nan sai Umar ya kalli sauran Sahabbai ya ce: “Ku ba shi amsa mana”. Sai suka yi tsit.

Ganin haka sai ya dubi xan Abbas ya ce: “Ba shi amsa”. Sai ni kuma na ce masa: “Qudamatu ka ci tuwon gigi. Ai wannan aya ta sauka ne a matsayin uzuri ga magabatanmu waxanda suka sha giya kafin Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya haramta ta ka suka kwanta dama. Ya kuma haramta ta da cewar da ya yi: Ya ku waxanda suka yi imani! Abin sani kawai, giya da caca da refu kiban quri’a qazanta ne daga aikin shaixan. Sai ku nisance su (5:90). Kuma ka sani wannan aya hujja ce a kanka”.

Sannan sai Umar Raliyallahu Anhu ya nemi shawarar Sahabban a kan bulolin da ya kamata a yi masa a matsayin haddi. Sai Ali xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu ya ce: Tunda idan mutum ya sha giya tana sa shi maye, idan kuma ya yi maye hankalinsa kan goce har ya yi wa wani qazafi, ai sai a yi masa bulala tamanin (haddin qazafi). Sai Umar ya sa aka sha shi tamanin.

Wannan shi ne haqiqanin abin da ya faru. Kuma ka ga shawara ce kawai Ali Raliyallahu Anhu ya bayar ta a yi bulala tamanin. Kuma duk da haka akwai yar magana a wurin.

Abin da ya sa na ce akwai ‘yar magana a wurin shi ne, saboda ta tabbata a ingantaccen hadisi cewa Abdurrahaman xan Aufu ne ya ba Umar Raliyallahu Anhu waccan shawara ta bulala ku dama tamrin ba Ali ba. Hasali ma shi Alin Raliyallahu Anhu ijtihadinsa a kan haddin shan giya bai tava wuce bulala arbain ba. Kuma su ne ya yi wa Walidu xan Uqubata a lokacin da ya sha giyar, a zamanin halifancin Usmanu Raliyallahu Anhu, tare da faxar cewa bulala tamanin Umar Raliyallahu Anhu kan yi. Amma kuma an sami wata riwaya da ke cewa, bayan Alin Raliyallahu Anhu ya zama halifa, ya kawo wancan ijtihadi nasa, na bulala arba’in ya koma ga na Umar, wato bulala tamanin. Kamar yadda Sahabi Abdurrahaman ya bayar da shawara. Ka ga kenan ya haxa haddodi biyu.

Amma duk da yake babu wani daga cikin Sahabban da malaman fiqihu da ya mara wa Ali Raliyallahu Anhu baya a cikin waccan magana ba musamman idan hakan ta faru a cikin bulala arba’in ko qasa ga haka, bai kamata a xauki maganar tasa a matsayin ficewa daga ijma’i ba.

 2.51 Ba Ta San Zina Haramun Ce Ba.

A nan kuma matsala biyu ce xan Shi’ar ya soki sawun Umar Raliyallahu Anhu da su; matsalar diyyar vari da ta haddin zina. Ga abin da yake cewa:

Watarana Umar ya aika a kira ma sa wata mata mai juna biyu. Isar saqon ke da wuya sai cikin nata ya zuba, saboda tsoron abin da zai biyo baya idan ta yi ido huxu da halifan. Da aka dawo aka ba shi labarin, sai ya samu damuwa. Sai Sahabban suka ce masa: “Kar ka damu. Ba ka da wani laifi a wurin Allah, tunda a kan haqqin shari’a ce haka ta faru”.

Amma dai duk da haka Umar bai gamsu ba. Sai ya tambayi Ali Raliyallahu Anhu shi kuma ya ce lalle sai dangin Umar sun taru sun biya diyyar cikin da ya zuba.

Wai a haka inji xan Shi’ar, fifikon Ali Raliyallahu Anhu a kan Umar da sauran Sahabban ya tabbata.

Matsala ta biyu kuma ya ce wai: Watarana an zo da wata mata da aka kama da laifin yin zina, a wurin Umar Raliyallahu Anhu gaba xayan Sahabbai suka yi ittiffaqi a kan a jefe ta.Amma Umar xin ya yi biris da su, ya qyale ta.

Martani:

Ita waccan matsala ta farko, kamata ya yi a jinjina wa Halifa Umar Raliyallahu Anhu a kanta.saboda nacewar da ya yi sai ya samu wani abu da zai ba ya ntsu a kan sha’anin. Tunda matsala ce ta ijtihadi.

Kuma neman shawarar Ali Raliyallahu Anhu da ya yi bayan ya gama jin ta bakin sauran Sahabbai, ba wani abin qumaji ba ne. Domin kuwa da ma al’ada ce ga Umar xin, ya shawarci Sahabbai a kan al’amurra. Ya saba da haka. Ya kan shawarci Usmanu da Ali da Abdurrahamanu xan Aufu da xan Masu’du da Zaidu xan Sabitu da waxansu daga cikin Sahabbai. Wani lokaci ma har xan Abbas ya kan shawarta. Wannan kuwa na nuna kammalar darajarsa da hankalinsa da kishin addininsa. Wanda hakan tasa ya fi kowa daidaitaccen ra’ayi da ijtihadi.

Ita kuma waccan mata da yake faxa, an zo masa da ita ne akan ta furta cewa ta yi zina. Sai Sahabbai suka yanke mata hukuncin jifa, sayyidina Usmanu bai ce qanzil ba. Ganin haka sai halifa Umar Raliyallahu Anhu ya ce ma sa: Na ji ba ka ce komai ba, don me? Sai ya karva ma sa da cewa: Na yi shiru ne saboda na ga yadda take taka qasa da kallon mutane kamar wadda ta aikata wani abin alheri. Saboda haka nake jin ko shakka babu, ba ta san zina haramun ce ba.

Jin wannan magana ta dattijo Usmanu Raliyallahu Anhu sai halifa Umar ya fasa zartar ma matar da haddi. Ko banza yayata labarum ta yi zinar da take ta yi da kanta, ya sa aka kame ta a matsayin wadda ta yi iqirari. Kuma har aka gurfanar da ita gaban halifa Umar Raliyallahu Anhu ji take yi da ita da wanda ya ci wani abinci ko ya sa wata kuyangarsa xaka duk xaya.

 2.52 Annabi Sulaimana ne ba Halifa Umar ba

A lalabe-lalaben da wannan xan Shi’ah ke yi, na kashin kajin da zai shafa wa halifa Umar, ya lalubo wata qissa da ta faru ga Annabi Sulaimana Alaihis Salamu, amma saboda cikar jahilci ya yava ta ga sayyidina Umar Raliyallahu Anhu.

Ga abin da xan Shi’ar ya ce: Watarana wasu mata biyu sun yi jayajjar wani jariri kowace daga cikinsu na cewa nata ne. qarshe suka xunguma sai gaban halifa Umar. Amma wai saboda zamansa kidahumi, sai ya rasa yadda zai raba gaukar. Saboda haka ya garzaya wurin Ali Raliyallahu Anhu sai Alin ya sa aka kira matan nan gaban Umar Raliyallahu Anhu ya yi masu nasiha. Amma abin ya faskara. Sai ya ce a kawo masa zarto zai raba ma su jinjirin. Jin haka sai xaya daga cikinsu ta ce: Don Allah, baban Hassan kar ka yi haka, idan ma har wajibi ne sai ka raba mana shi biyu, to na yafe ma ta. Sai Ali Raliyallahu Anhu ya ce; Allahu Akbar! Ko shakka babu wannan yaro naki ne, ba na waccan ba, don lalle da xanta ne da ta yi yadda kika yi. Nan take kuma sai xayar can ta tabbatar wa Alin da cewa, xan dai na waccan ne.

Wai ganin haka, inji xan Shi’an sai hankalin Umar ya tashi ya kuma qara sakar wa Ali Raliyallahu Anhu har ma ya yi masa addu’a.

Martani:

Kasancewar xan Shi’ar bai ambaci madogarar wannan qissa ba, balle a binciki didiggin ingancinta. Kuma ni ban san wani malami da ya ambace ta ba. Duk hakan na tabbatar da cewa ba ta faru ga waxannan Sahabbai ba. Domin ko shakka babu, da ta faru da sun faxe ta.

Amma dai ta tabbata a wurinmu cewa Annabi Sulaimana Alaihis Salamu ya yi irin wannan hukunci.

 2.53 Ra’ayin Shiryayyaun Halifofi Ne

Daga nan kuma sai xan Shi’ar ya ce: kuma jahilcin Umar bai tsaya nan ba. Watarana ya yi umurni da jefe wata mata wai don ta haihu da wata shida bayan aure. Sai Ali Raliyallahu Anhu ya ce ma sa: Ya za ka yi da ita idan ta kawo maka hujja da cewar da Allah Ta’ala ya yi a cikin littafinsa: Kuma cikinsa da yayensa wata talatin ne. Da kuma cewar da ya yi: Kuma masu haifuwa suna shayar da abin da suka haifa shekaru biyu cikakku, ga wanda ya yi nufin ya cika shayarwa (2:233).

Martani:

Kamar yadda muka ambata a baya, babu wani abu da zai fuskanci halifa Umar Raliyallahu Anhu ba tare da ya shawarci manyan Sahabbai ba, kuma a mafi yawan lokuta ba yakan tsallake shawarwarin Usman Raliyallahu Anhu ba. Ya kan kuma shawarci Ali Raliyallahu Anhu wani lokaci. Wani lokacin kuma Abdurrahaman xan Aufu ko waninsu. Kuma a kan wannan kyakkyawan hali na waxannan magabata ne, Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yabi muminai da cewa: Kuma al’amarinsu shawara ne a tsakaninsu (42:33).

Bayan kuma wannan daraja da ta daxe da tabbata ga Umar Raliyallahu Anhu malamai sun qara wa junansu sani, a kan cewa shin ko macen da ciki ya bayyana gare ta, ba miji, ba Ubangida, ba ta kuma kafa hujja da wani ya take ta a kan kuskure ba, ta cancanci jifa? Sai malaman Madina suka tafi a kan cewa lalle za a jefe. Kuma a kan wannan hukumci ne Ahmad yake, a xaya riwayarsa. A yayin da Hanafawa da Shafi’awa suka tafi a kan cewa ba za a jefe ta ba. Wannan hukunci kuma shi ne riwaya ta biyu daga Ahmad. Dalilin waxannan malamai na biyu kuwa, a kan ijtihadin nasu shi ne, a tasu fahimta, abu ne mai yiwuwa qwarai ya kasance ta sami cikin ne saboda wani taki da aka yi mata na dole, ko na kuskure. Ko kuma Allah ne kawai ya hukunce ta da samun cikin ba tare da an take ta ba, a’a ta wata hanya dai daban.

Shi kuwa wancan ijtihadin na farko, wanda ke cewa ana jefe wannan mata, ra’ayin shiryayyun halifofi ne, dukansu a kansa suke. Har an riwaito cewa a qarshen rayuwar Umar Raliyallahu Anhu halifan ya hau mimbari ya yi wa mutane huxuba da cewa: Jefe mazinaci hukunci ne da ya tabbata a cikin littafin Allah, a kan maza da mata. Da zarar an samu shedu ko ciki ya bayyana, magana ta qare.

Ka ga kenan Umar ya daidaita bayyanar ciki da shedu a cikin tabbatar da laifin zina.

 2.54 Ijtihadi ne Wannan

Sai kuma xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: kuma Umar ya kasance yana nuna banbanci idan yana rabon ganima, tattare da cewa Allah Ta’ala ya wajabta raba-daidai a cikinta.

Wato xan Shi’ar na so ne ya ce Umar ya qi bain umurnin Allah.

Martani:

Tarihin musulunci ya tabbatar da cewa ba halifa Umar Raliyallahu Anhu ne ke raba ganimar yaqi da kansa ba. Mayaqan ne dai da kansu ke rarraba ta tsakaninsu, bayan sun debe zumunci.karon da suke aika wa Umar din Raliyallahu Anhu kamar yadda ake aika wa kowane halifa. Wand shi ne zai warware wa mutanensa.iyakar abin da muka sani tabbatacce kenan.amma ba a taba jin Umar ko waninsa ba ya ce wajibi ne a fifita wasu da kansu a kan wasu, idan aka zo rabon ganinsa. Amma sane muke da cewa malamai sun dayi tsokace-tsokace a kan cewa, shin ko shugaba nada dammar kara wa wani daka ce wani abu idan ana rabon ganinsa. Saboda wani kwazo da aka ga ya nuna fiye da kowa?

Iyakar maganar kenan.kar ka dada kar ka kara.

Kuma a ta kaice, ya kamata kafin in kirein sheda wa mai karatu cewa wannan matsala ta ijtihadi ce.da Umar Raliyallahu Anhu zai ga dacewar nuna banbancin ta wannan hanya, akan waccan tsakaci da malamai suka yi. Ba wanda ya ba ya ce masa do me? Ko waye shi ko. Yana da dammar yin haka, a matsayinsa na shugaba wanda Allah ya sa zuciyarsa da harshensa, suka zama wani labaron hangen gaskiya komai nisanta,

Amma zancen rabon arzikin kasa, wanda baya da alaka da ganina, ko shakka babu Umar Raliyallahu Anhu na nuna banbanci a cikinsa, amma ban a son kai da son zuciya da ko da ba. Yakan fifita fifita wasu mutane nne a kan wasu, gwargadon girman darajarsu, kamar dai yadda muka yi bayani baya kadan. Kuma shi kansi ya so ya bar wannan salo, ya koma ga akasirinsa.don an riwaito yana cewa: idan Allah ya kai ranmu badi zan yi wa mutane bugu guda.

Wannan kenan. Ita kuwa cewar da xan Shi’ar ya yi wai: Allah ya wajabta da daitawa a cikin rabon ganina. Magana ce da ya bari haka nan, bai kafa wani dalili a kant ba, balle mu kacaccala tada shi. Kamar yadda mukan yi a cikin al’amuran da ke karvar ijtihadi.

 2.55 Ra’ayin Sahabbai Hujja ne

Daga nan kuma sai xan Shi’ar ya ce: Kuma Umar na aiki da ra’ayi da zato da hasashe.

Martani:

Bayyana hukuncin wani abut a hanyar aiki da ra’ayi, bag a Umar Raliyallahu Anhu bawan ba.hasali ma tarihi ya tabbatar da cewa Ali Raliyallahu Anhu shi ne Sahabi mafi amfani da hasashe da ra’ayi a surin yanke hukunci. Haka Abubakar da Usman da zaidu dad an mas’udin da wasunsu daga cikin Sahabbai, duk sukan yi amfani da hankali da basirarsu da gogewar da suke da ita a rayuwar musulunci su bayyana ra’ayinsu a kan wani hukunci.

Kuma ma ra’ayin da Ali Raliyallahu Anhu ya yi amfani da shi ya halatta jinin masallata, ya fi komai ban mamaki.

Kamar yadda kaisu dan ubbadu ya tabbatar a cikin wani ingantaccen hadisi, wanda aka riwaito daga Hasan, a cikinsunanu Abu Dawuda da waninsa. Inda kaisun ya ce: Na ce wa Ali: don Allah muna son mu gane shin Manzon Allah ne Sallallahu Alaihi Wasallama ya alkawanta maka wannan al’amari, ya kuma umurci ka da yi haka.koko dai ra’ayinka ne? sai ya karva masa da cewa: babu wani abu da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya alkawanta mani. Ra’ayina ne kawai.

Wannan magana tabbatatta ce. Don haka ma ne ka ji Ali Raliyallahu Anhu bai riwaito wani abu gane dayakin basasar raqumi da siffan ba, kamar yadda ya riwaito game da yakin da ya yi da Harijawa.

Wannan kenan. Sannan kuma idan dai mutum nada hankali da sanin ya kamata komai kakantarsu, to bai kamat ba ya yi ko kwantontsarkin tarihin Umar da umurninsa da adalansa da darajojinsa ba, balle har ya soki umurnsa, har ma yah ado da halifa Abubakar Raliyallahu Anhu don sun yi amfani da hasashen su a cikin wani hukunci. Ai ra’ayin Sahabbai hujja ne.

Duk kuwa wanda ka ji yana sukar lamarin waxannan bayin Allah, a kan wannan al’amari, to xayan biyu:

Ko dai ya kasance munafuki ne, zindiqi, mulhidi, maqiyin musulunci. Wanda ke son ya yi amfani da sukar lamirinsu, ya soki lamirin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da addinin musulunci kamar yadda malamin ‘yan Shi’ah na farko, wanda ya kafa qungiyar ya kasance. Wanda ya yi daidai da matsayin ‘yan Baxiniyyah.

Ko kuma ya kasance jahili mai biyar son zuciya. Kamar yadda mafi yawan ‘yan Shi’ah suke. Ko da a cikin zukatansu musulmi ne su.

Amma na san xan Shi’ar na iya cewa: To ai Ali Raliyallahu Anhu ma’asumi ne. wanda duk abin da zai faxa ba ra’ayinsa kawai ne ba, wahayi ne daga wurin Allah. Kamar yadda ake yi wa Manzon Allah, kuma shi ne wanda manzon ya tabbatar da imamancinsa a nassanace.

Da zai mana haka, sai mu kuma mu ce masa: Da kai da Harijawa duk jirgi xaya ya xauko ku, kowanenku motar bidi’arsa ce ya take har kwano. Ku kun kai Ali Raliyallahu Anhu inda Allah bai kai shi ba. Su kuma sun ce kafiri ne ma.

Banbancin da ke tsakaninku da su kawai shi ne, su mutane ne masu ilimi da son gaskaiya da kishin addini fiye da ku. Don haka sun fi iya kare bidi’arsu da hujjoji masu dama. Duk kuwa wanda ya san ku ya san su ba ya shakkar wannan magana.

 2.56 Shawara Ba Laifi Ba Ce.

Bayan wannan kuma sai xan Shi’ar ya soki lamirin halifa Umar Raliyallahu Anhu da cewa: Ya sava wa sunnar halifa Abubakar Raliyallahu Anhu tunda ya kafa kwamitin da zai zavi halifa daga cikinsa, tun yana raye. Alhali, shi ba kwamiti aka naxa kafin ya zama halifa ba.

Ya ci gaba da cewa: Halifa Abubakar bai ce ga wanda zai zama halifa bayansa ba. Iyakar abin da ya yi dai shi ne, ya faxi alherin Salimu bawan Abu Huzaifa. Inda halifan ya ce: Da Allah ya sa Salimu na raye, ba zan yi shakkun komai a kansa ba.

Kuma ya faxi wannan magana ne gaban Sarkin Musulmi Ali Raliyallahu Anhu. Kuma a taqaice, inji xan Shi’ar wai, Umar ya riga ya gama zaven magadinsa. Tun da a cikin wancan kwamiti na shawara da ya kafa, ya haxa hancin waxanda ya san ba yadda za a yi su yi kafaxa-da-kafaxa da sauran, balle su shiga gabansu. Sannan kuma wai sai ya biyo da dasisar sukar ‘yan kwamitin, da cewa ya yi haka ne don ba ya son wani bara gurbi ya hau karagar sai dai nagari. Qarshe kuma sai ya damqa ta ga bara gurbin. Saboda yanke hukuncin da ya xaya daga cikin ‘yan kwamitin ya yi.

Ya dawo kuma ya bar ta tsakanin huxu daga cikinsu. Ya kuma mayar da su. Har sai da ta kama hanyar zuwa ga xaya daga garesu. Kuma a haka sai ya damqa ragamar zave na qarshe a hannun Abdurrahaman xan Aufu. Bayan kuma can ya siffanta shi da rauni da kasawa. Sannan kuma ya ce: Idan Ali Raliyallahu Anhu da Usman Raliyallahu Anhu suka rage a faifai, to duk shawarar da suka yanke a kansu tayi. Idan kuwa suka kai uku, to duk hukuncin da waxanda Abdurrahman xan Aufu ke cikinsu suka yanke shi ne abin karva. Kuma wai Umar ya yi haka ne, inji xan Shi’ar saboda ya san har abada Ali da Usmanu Raliyallahu Anhu ba su haxuwa qarqashin inuwa xaya. Kuma babu yadda za a yi Abdurrahman ya bar Usman a matsayinsa na xan amminsa, ya zavi Ali.

Sannan kuma wai sai Umar, don tsananin iya makida, inji shi, ya yi umurni da shace kan duk wanda ya kwana uku bai yi bai’a ga wanda aka zava ba. Alhali kuwa sun yarda da kasancewar sauran manbobin kwamitin daga cikin waxanda Allah ya yi wa albishirin aljanna tun duniya. Ya kuma yi umurni da kashe wanda ya sava wa ra’ayin huxu daga cikinsu, da wanda ya sava wa na uku daga cikinsu, waxanda Abdurrahaman ke cikinsu. Kuma gaba xayan wannan shiri da Umar ya yi ya sava wa addini. Inji xan Shi’ar.

Ya ci gaba da cewa: Kuma a qarshe da aka bar Abdurrahaman da Ali da Usman, wai sai Abdurrahaman ya ce wa Ali: Da za a zave ka a matsayin halifa, kana ganin zaka iya jagorancin al’ummar nan bisa tafarki madaidaici? Ka ga, wai kai tsaye wannan magana, na nuna ba su da niyyar zavensa. Sannan kuma ya ce wa Usmanu: Ka yarda da, da za a naxa ka a matsayin halifa, kuma ka bautar da mutane ga ‘yan gidanku a kashe ka? Ka ga wai kai tsaye wannan magana na nuna, an riga an shirya kashe shin da haka za ta faru. Inji shi.

Martani:

Da farko, abin da za mu ce a matsayin martani a kan wannan magana shi ne: tabbatar xayan abubuwa biyu a kan wannan zance, wajibi ne: Ko dai mu yanke mata hukuncin kasancewa qarya ta fuskar naqali. Ko kuma qoqarin canza wa tuwo suna, ta hanyar bice hasken gaskiya da qarfi da yaji. Wannan wajibi ne, saboda haxuwar hakin tantagaryar qarya, da na bobawan birni a cikin maganar.

Eh! Gaskiya ne. Akwai abin da yake tabbas ne ya faru, xan Shi’ar bai yi qarya ba a ciki. Amma babu wani abu a ciki da ke wajabta sukar lamirin halifa Umar Raliyallahu Anhu a ciki. Hasali ma kamata ya yi a qididdiga wannan mataki da ya xauka daga cikin manyan karamomi da kyawawan ayyukansa.

Amma a maimakon haka, sai ‘yan Shi’ah suka karkata akalar wannan aiki da ya cancanci yabo, suka mayar da shi abin suka. Saboda su halinsu na jahilci da qoqarin tabbatar da kasancewar abin da bai kasance ba, da kore wanda ya tabbata. Tare da saka wa alheri rigar sharri da yi wa balbela baqin fenti. Hakan ta sa su rasa tsuntsu da tarko, ba su ga hankali balle karatu. Suka zama daidai da waxanda Allah Ta’ala ke bayar da labarinsu da cewa:

﴿وَقَالُواْ لَو كُنَّا نَسمَعُ أَو نَعقِلُ مَا كُنَّا فِي أَصحَبِ ٱلسَّعِيرِ١٠﴾ الملك

Kuma sukka ce: “Da mun zamo muna saurare ko muna da hankali, da bamu kasance a cikin ‘yan sa’ira ba (67:10).

Wannan kenan. To mu dawo kan nassin maganar tasa daki-daki.

Xan Shi’ar ya ce: kuma Umar Raliyallahu Anhu ya kafa kwamitin da zai yi shawara ya zavi wanda zai zama halifa bayansa. Wannan kuwa ya sava wa abin da Abubakar Raliyallahu Anhu ya yi kafinsa.

To, savawa na xaukar ma’ana biyu: Ko dai: 1) savani na taho-mu-gama; wanda zai haifar da gaba da rashin ga-maciji tsakanin juna. Ko kuma, 2) savani na yaxuwa, wanda zai haifar da kaurin arziki da yalwa, ta yadda zai ishi kowace matsala da darga.

Misalin nau’in savani na farko shi ne, kamar: wannan ya ce: abu kaza wajibi ne. Wancan kuma ya ce: A’a haramun ne. Shi kuwa nau’i na biyu shi ne, kamar banbance-banbancen da ke tsakanin makarantar Alqur’ani wanda, a sanadiyyarsu, suka sassava a wasu wurare. Amma kuma duk da haka, kowace qura’a daga cikinsu karvavva ce a idon shari’a. Kamar yadda ingantattun hadissai suka tabbatar daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kuma ta dubun dubutar hanyoyi.

Wani abin da ke tabbatar da cewa wannan banbancin fahimta (savani nau’i na biyu) halas ne, ko ma wajibi, kuma yana da asali a shari’ar musulunci, shi ne abin da Ibnu baxxata ya riwaito, ta hanyar wani gagarabadan isnadi, cewa: Watarana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma: “Ba don da kuna ra’ayi biyu a wasu lokuta ba, da ba zan sava ma ra’ayinku ba”.

Ka ji wannan magana. Kuma gaba xayan salaf har da magoya bayan Ali Raliyallahu Anhu sun yarda da fifikon waxannan Sahabbai biyu. Kar ka yi wani mamaki, don jin na ce, magoya bayan Ali Raliyallahu Anhu wato ‘yan Shi’ah san yarda da fifikon Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma a kan gaba xayan Sahabbai, har ma da Alin kansa.

Ko shakka babu, ‘yan Shi’ah na farko a kan wannan aqida su ke. Daga baya ne al’amarin ya xauki sabon salo, lokacin da vata gari suka kunno kai. Abin da zai tabbatar maka da wannan magana shi ne abin da Ibnu baxxata ya riwaito daga cewa: Watarana Abu Ishaqas-Sabi’i ya zo Kufa. Sai Shamir xan Axiyyah ya ce: Mu je mu gaishe shi. Qare gaisawarmu ke da wuya, sai suka shiga zance. A cikin haka ne muka ji Abu Ishaqan na cewa: Wai ya aka yi ne? Ko da na bar Kufa ban san akwai wani mutum xaya a cikinta ba, da ke shakkar kasancewar Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma mafifita daraja a cikin Sahabba. Amma ga shi yanzu da isowata na ji mutane na wasu ‘yan maganganu da ban gane kansu ba.

Kuma Ibnu baxxata xin ya ruwaito daga Laisu xan Abu Sulaimu cewa: Na tarar da ’yan Shi’a na farko ba su ganin girman kowa a kan Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma.

Kuma Imamu Ahmad xan Hambali ya ruwaito daga Masruq, xaya daga cikin mafi girman Tabi’ai, yana cewa: “Son Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma da kiyaye alfarmarsu na cikin sunna. Haka shi ma Xawisu ya faxa da Ibnu Mas’ud.

Ah! To, me ko zai hana ‘yan Shi’ah na farko su yarda da fifikon darajar Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma a kan sauran Sahabbai, tunda sane suke da cewa hanyoyi kusan tamanin na riwaya, sun tabbatar da cewa, Ali Raliyallahu Anhu ya ce: Mafi girma da alheri a cikin wannan al’umma bayan Annabinta, su ne Abubakar da Umar.

Imamul Buhari ma ya riwaito wannan magana cikin ingantaccen littafinsa, daga bakin Hamdaniyyawa, waxanda su suka fi kowa kusanci da Ali Raliyallahu Anhu. Su ne fa Alin yake ce wa: “Da an ba ni mabuxin qofar aljanna, da na fara sa Hamdanawa a ciki”.

Buhari ya riwaito Muhammadu xan Hanafiyya, ya ce, na ce wa mahaifina (Ali Raliyallahu Anhu): Don Allah wa ye mafifici a cikin mutane bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Sai ya karva mani da cewa: Af! Kai ba ka sani ba? Na ce: Wallahi ban sani ba. Sai ya ce: Abubakar. Na ce: Sai kuma wa? Ya ce: Umar.

Haka kuma an riwaito Alin Raliyallahu Anhu na cewa: Duk wanda ya kuskura ya shigo hannuna, yana fifita ni a kan Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma sai na yi masa bulalar qazafi.

Kuma a cikin Sunan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ku yi koyi da mutum biyu a bayana: Abubakar da Umar”.

Mu koma kan qorafin da xan Shi’ar ke.

Bismillahi!

A matsayin Umar Raliyallahu Anhu na shugaba, yana da cikkakiyar damar zavar wa musulmi halifa mafi dacewa daga cikinsu. Kuma abin da ya yi qoqarin yi kenan. Wanda ijtihadinsa ya tabbatar ma sa da cewa babu wanda ya cancanci wannan nauyi fiye da xayan waxannan Sahabbai shida. Ba a kuma samu wani mutum xaya a lokacin da ya musa masa ba.

Wani abin ban sha’awa ma da qayatarwa, da tabbatar da kaiwar halifa Umar Raliyallahu Anhu qololuwa a fagen ijtihadi da adalci da nagarta, da kauce wa son zuciya, shi ne barin wannan kwamiti ya zavi halifa daga cikinsa. Don gudun shi ya zavi xaya daga cikinsu kawai ya tabbatar, tunda duk ya yarda da su. Amma hakan ta sava wa ra’ayin sauran manbobi. Kuma ya kasance akwai wanda ya fi shi cancanta a cikinsu.

Tattare da cewa, ba a rasa wanda yafi kwanta masa a rai daga cikinsu. Amma kuma ya rinjayar da burin kwamitin yayi zaven, ko da zai zavi wanda ba shi ne, shi a zuciyarsa ba Raliyallahu Anhu.

Kuma ai shawara ba laifi ba ce. Musamman ga musulmi, balle manyan Sahabbai.Tunda cewa Allah Ta’ala yayi: Kuma al’amarinsu shawara ne a tsakaninsu (42:38). Ya kuma ce: Kuma ka yi shawara da su a cikin al’amarin (3:159). Kuma ko shakka babu, wannan kwamiti na shawara da halifan ya kafa, shi ne mafi dacewa da tabbatar maslaha ga al’umma a wannan lokaci. Kamar yadda abin da Abubakar Raliyallahu Anhu ya yi a lokacinsa na zaven Umar xin Raliyallahu Anhu a matsayin halifansa ba tare da ya kafa wani kwamitin shawara ba, shi ne abu mafi zama maslaha a wancan lokaci. Domin kuwa halifan bai yi haka ba, sai da ijtihadinsa ya gama tabbatar ma sa da cewa Umar xin shi ne mafi cancanta, kuma lalle gadon bayansa na iya xaukar nauyin. Kuma babu buqatar kafa irin wannan kwamiti. Kuma hakan ta tabbata. Don abin can da Abubakar Raliyallahu Anhu ya kyautata zato ga Umar ya tabbata, duniyar musulmai ta sheda.

Kuma babu mai hankalin da bai san cewa, ‘yan kwamitin can, da halifa Umar Raliyallahu Anhu ya kafa, da suka haxa da: Usmanu da Ali, Xalhatu da Zubairu, Sa’adu da Abdurrahaman xan Aufu kowannensu na iya cike gurbin Umar ba, kukkukkuf. Saboda haka zaven cancantar da Abubakar ya yi wa Umar Raliyallahu Anhu daidai yake da mubaya’ar da Sahabbai suka yi wa Abubakar xin Raliyallahu Anhu a matsayin mafi cancanta a wancan lokaci.

Saboda haka ne ma aka riwaito xan Mas’ud Raliyallahu Anhu na cewa: Mutanen da suka fi kowa dacewar hasashe a duniya uku ne: 1) ‘Yar Sarkin Madayana, da tace: Ya baba! Ka ba shi aikin ijara, haqiqa mafi alherin wanda ka bai wa aikin ijara shi ne mai qarfi amintacce (23:26). Da 2) Matar Fir’auna, da tace: Akwai yiwuwar ya amfane mu, ko mu riqe shi a matsayin xa (28:9). Sai kuma 3) Abubakar Raliyallahu Anhu da ya zavi Umar a matsayin halifa.

Gaba xayan hasashen da waxannan mutane uku suka yi a duniya, ya zama gaskiya.

Abin da ijtihadin Abubakar Raliyallahu Anhu ya nuna masa kenan. Shi kuwa Umar Raliyallahu Anhu sai nasa ijtihadi ya nuna masa, kusan babu wanda bai iya riqe muqamin halifa daga cikin waxannan mutane guda shida. Duk kuwa da yake akwai daga cikinsu waxanda suka fi wasu xaukaka da alfarma. Amma idan aka duba da kyau, za’a taras cewa suma waxanda aka fi xin suna da wasu martabobi da waxanda suka fisu ba suda. Ka ga an yi tangan kenan.

Bayan wannan kuma halifa Umar mai gani da hasken Allah, ya hangi cewa da zarar ya zavi wani daga cikinsu kai tsaye. To fa, duk abin da hakan ta haifar na tajin-tajin shi zai zama abin zargi. Saboda haka sai ya kauce, don gudun talalaviya ta kwashe shi amma kuma kafin haka, sai ya tattara waxanda suka fi kowa cancanta da matsayin ya danka masu al’amarin. Ka ga a hakan ya jefi tsuntsu biyu da dutse xaya kenan. Wato ya zavi halifan a kaikaice, amma a kai tsaye ba shi ne mai zaven ba, ya xauke haqqin Allah ya kuma xauke nauyin mutane kenan.

Kuma ko shakka babu mutanen nan shida da Umar ya xauka wa wannan al’amari, sun sami yardar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har qarshen rayuwarsa. Babu wanda ya kai darajarsu daga cikin Sahabbai. Duk kuwa da kasancewar Manzon ya qyamaci wani abu a cikin kowannensu. Amma kuma ai duk xan Adamu xan tara, banda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuma ko shakka babu da za’a xora su a kan sikeli tare da waxanda ba suba, to za su rinjaya.

Babban abin da zai tabbatar maka da haka kuwa, shi ne kasancewar rawar da halifa Usmanu ya taka, ta fi ta wanda yazo bayansa qayatarwa. Shi (Ali Raliyallahu Anhu) kuwa tasa ta fi ta na bayansa. Kuma babu wani Sarki a tarihin musulunci da ya taka nagartattar rawa irin wadda Mu’awiyah ya taka Raliyallahu Anhu abun da mutane da dama suka tabbbatar.

To, a haka, idan har za’a ce ga wani zunubi da xaya daga cikin waxannan Sahabbai keda, lalle wanda waninsu keda yafi girma da duhu. Kuma kyawawan ayyukansa ba za su kama qafar nasu ba. Wannan na daga cikin abubuwan daya kamata a sani a kuma kiyaye. A kuma fahimci cewa da wuri mai qazanta. Shi kuwa mai hankali, kodayaushe yakan auna al’amurra ne ta hanyar la’akari da qwansu da qwarqwatarsu.

To, waxannan ‘yan Shi’ah da kake ji, sune mutane mafiya jahilci a cikin wannan al’umma. Suna aibanta wanda ba su so, da wani abin da wanda suke so da yavo, ya daxe da yin dumudumu da abin da yafi shi. Kuma da za’a dawo a kafa ma’aunin adalci, za’a taras da cewa wadda suke sukar da kushewa, shi yafi cancanta da yabo da sarawa, in ba don da suke manyan jahilai ba.

Wannan kenan. Shi kuwa zancen Salimu bawan Abu Huzaifata, da xan Shi’ar yayi, kamar yadda ake riwaitowa, magana ce qarama. Domin kuwa sanannen abune cewa Umar da sauran Sahabbai Raliyallahu Anhu sun san da cewa, babu wanda ya dace da shugabancin al’ummar sai baqwaishe. Kamar yadda littafan sunnan suka cika suka katse da haka, daga bakin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Kamar yadda Buhari da Mushini suka riwaito daga Abdullahi xan Umar Raliyallahu Anhu wanda ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Wannan al’amari (halifaci) ba zai gushe daga hannun Quraishawa ba. Matuqar akwai ko da mutum biyu a bayan qasa. Wani martanin kuma ya ce: matuqar akwai mutum ko da biyu daga cikinsu a raye.

Sannan kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai, kwamitin can da Umar ya kafa ya haxa masu manya da qananan darajoji. Kuma a al’adance kamata yayi mai babbar daraja ya shige gaban mai qanqanuwa a komai.

To, da farkon abin da za mu cewa a nan shi ne: Xan banbancin da ke tsakanin waxannan Sahabbai na daraja, ko alama bai kai yadda xan Shi’ar ya xauke shi ba. Idan ma mutum bai kwantar da hankali da kyau ba, ba zai gane komai ba. Don fifikon darajar ba kamar wanda kega Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma ne a kan sauran Sahabbai ba. Wanda ko makaho ya sani. A kan wannan dalili ne ma, idan aka zauna tarihin shawari ake karvar ta Usmanu wani lokaci. Wani lokacin kuma a karvi ta Ali, ko Abdurrahman Raliyallahu Anhu domin kowane daga cikinsu nada wata daraja da waninsa baya da.

Abu na biyu: idan har abu ne mai yiwuwa daga cikin ‘yan kwamitin can a samu mai babbar daraja da mai qanqanuwa, kamar yadda xan Shi’ar ya faxa, tunda zavo su aka yi, ba tare da ance wane shi ne gulbi, wane shi ne qorama ba. Wane dalili kega xan Shi’ar na cewa Ali Raliyallahu Anhu shi ne teku, ba ma gulbi ba shi kuwa Usman Raliyallahu Anhu da sauran fadammu ne, ba ma qorammu ba? Alhali kuwa muhajuruna da Ansaru, sun haxu a kan cewa Usmanu na gaban Ali Raliyallahu Anhu a falala. Kamar yadda Abu Sakhtayani, xaya daga cikin jigajigan malamai ya ce: duk wanda ya fifita Ali a kan Usmanu Raliyallahu Anhu haqiqa ya tozarta Muhajiruna da Ansaru.

Ya kuma tabbata a cikin Buhari da Muslimu, daga Abdullahi xan Umar, wanda ya ce: Mun kasance a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama muna fifita Abubakar, sannan Umar, sannan Usmanu Raliyallahu Anhu a wani martanin kuma ya ce: Sai kuma mu qyale sauran Sahabban na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba tare da mun fifita wani a kan wani ba.

Ka ga wannan magana babba ce matuqa, saboda tana gaya mana, yadda Sahabbai a lokacin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke fifita darajar Abubakar Raliyallahu Anhu a kan sauran Sahabbai. Sannan ta Umar da Usman Raliyallahu Anhu. Kuma Annabin na sane bai ce kanzil ta hani ba.

Kenan wannan daraja tasu tabbatatta ce nassance ko kuma tunda Manzo bai hana ba tattare da sanin Muhajiruna da Ansaru na kan haka. Ko kuma saboda tattarar gaba xayansu su yi wa Usamanu Raliyallahu Anhu bai a bayan rasuwar Umar ba tare da an tilasta su, ko don rashin samun wani abu ba: ba a sami wanda ya wandare daga cikinsu ba.

Kamar yadda imamu Ahmad ya tabbatar da cewa: Babu bai’ar da mutane suka haxu a kanta kamar ta Usmanu Raliyallahu Anhu. Haka kuma da aka tambaye shi a kan halin da halifancin Annabta ya kasance. Sai ya ce: Duk wanda aka yi wa bai’ar a Madina. Kuma rayuwar Sahabbai da sauran musulmi ta bunqasa, a qarshen halifancin Umar fiye da yadda take kafinsa matuqa.

Wani babban abin da ke tabbatar maka da cewa bai’ar da Sahabbai suka yi wa halifa Usmanu Raliyallahu Anhu sun yi ta ne khalisan li wajhillahi. Ba kamar yadda xan Shi’ar ke son nuna cewa akwai wata gane-ta-kai a ciki ba, shi ne, kasancewar duk da Abdurrahman, farkon wanda ya yi masa bawar, halifan bai bashi wata dukiya ko sarauta ba daga baya. Hasali ma shi ne mafi nesa-nesa da abin duniya a tsawon halifancin Usmanu Raliyallahu Anhu tattare da kasancewarsa wanda ya shawo kan al’amurra, a matsayin shugaban shawara, a daidai lokacin da babu Umayyata xin ba su da wani tsimi ko wata dabara. Kuma baya ga shi Usmanu xin Raliyallahu Anhu ba su da kowa a cikin wancan kwamiti na shawara.

Kuma duk wanda ya san irin halin Sahabbai, ya san inda ba su gamsu da cancanta da fifikon Usmanu Raliyallahu Anhu ba wanda ya isa ya tilasta suyi masa bai’a. Ka tuna fa Allah Ta’ala ya sifanta su da cewa: Yana son su kuma suna son sa, masu tawalu’i ne a kan muminai, masu izza a kan kafirai. Suna yin jihadi a cikin hanyar Allah, kuma basu jin tsoron zargin mai zargi (5:54). Bayan wannan sheda kuma, sun yi wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai’a da alqawarin faxar gaskiya ko waye shi. Matuqar an ci iyakar haqqin Allah. Amma tattare da haka, tarihi ya tabbatar da cewa babu xaya daga cikinsu da ya qi yi wa Usmanu Raliyallahu Anhu bai’a, balle ya yi wani korafi.

Ka tuna dakaru, ’yan zafi masu jiran ko-ta-kwana, irin su: Ammaru xan Yasiru da Suhaibu da Abu Zar da Khabbabu da Miqdadu xan Aswadu da xan Mas’udu duk sun yi masa bai’a suna murna da xoki da Annashawa. Har xan Mas’udu ke cewa: Mun yi wa mafi girman daraja daga cikinmu bai’a. Ba mu kangare ba.

Kuma ka tuna manyan mutane irin su Abbas xan Abdul-Muxxalib, da Ubaidatu xan Samitu da makamantansu, irinsu Abu Ayyub al-Ansari da ire-irensu, duk fa sun yi wa Usmanu Raliyallahu Anhu bai’a.

Babu shakka a duk lokacin da masu hankali da basira suka yi wa wannan al’amari nazari qwaqwaf sai sun qara ilimi da hankali da basira, bisa waxanda suke dasu. Duk kuwa mai ilimin da ka ji yana ko karanton wani abu a cikin sha’anin, to lalle Allah bai ba shi ikon nazarinsa da kyau ba. Sai kuwa idan jahili ne wanda baisan makamar zaren ilimi da rayuwar duniya ba.

Ita kuwa cewar da xan Shi’ar ya yi wai: Umar ya soki lamirin kowane xaya daga cikin ‘yan wannan kwamiti daya kafa. Ya kuma bayyana cewa yana gudun ne alhakin abin da ka iya biyowa baya idan shi ya zavi mutum xaya, ya bi shi har lahira. Saboda haka ne ya bar aikin hannun wannan kwamiti. Amma kuma wai, sai ga a kaikaice kamar shi ne wanda ya zavi halifan. Tunda ya sharxanta wa kwamitin zaven xayansu a muqamin. Ka anyi ba a yiba kenan, inji xan Shi’ar.

Matani: Eh! Gaskiya ne Umar ya yi xan qorafin a kan waxannan manbobi. Amma abin bai kai ga ace ya soki lamirinsu ba, ta yadda hakan zata sa waninsu ya fi su cancanta da karagar. Hasali ma shi a wurinsa, babu kamarsu a wannan sha’ani, balle a fi su kamar dai yadda shi da kansa ya tabbatar. Abin da kawai yayi, wanda xan Shi’ar ke kira sukar lamiri wai,shi ne bayyana dalilin da ya sa yake tsoron zavar xayansu a matsayin halifan, balle har alhakin haka yahau kansa. Amma baya ganin wani abu na haufi, idan ya zavi mutum shida xin ya kuma yi masa muni irin wanda ya ishi mai hankali. Ya kuwa yi haka ne saboda yaqinin da yake da shi a kan cewa, kowanensu taqarqari ne daya isa xaukar kaya. Kuma ijtihadinsa ya tabbatar masa da cewa yin haka shi ne mafi zama salama, ko da wasu na ganin hakan can shi ne sawaba. Shi kuwa salama yake nema, ba don yana kyamar sawaba a karan kanta ba. Kuma haka shi ne mafi zama alheri gare shi, da al’umma baki xaya.

Wannan irin hikima na daxa tabbatar da cikar hankali da kishin addinin da halifa Umar ke dasu Raliyallahu Anhu.

Sannan kuma xan Shi’ar ya ce: sai kuma wai ga Umar ya yi qasa a gwiwa ta hanyar shatawa kwamitin yadda alhakin zaven zai koma hannun mutum huxu daga cikinsu, sannan uku. Har dai ya koma ga xaya tal. Wanda kuma zai kasance Abdurrahman xan Aufu. Bayan kuma shi Umar xin ya siffanta shi da rauni da kasawa.

Ka ji wannan qulli da kyau ko?

Martani:

Da farko dai, muna tabbatar wa xan Shi’ar cewa wannan magan irin ta ‘yan sandace. Musamman da yake bai faxi yadda ta inganta ba. Baya kuwa kamata ga mutum mai hankali, ya kafa hujja da abin da ba yada toshe balle makama. Don nan take ne za’a iya kwashe masa kafafu. Kamar yadda za mu yi masa yanzu…

Abin da ya tabbata a cikin sahihul Buhari da wasu littafai, ya tabbatar da cewa wannan magana qarya ce. Domin kuwa waxannan ‘yan kwamiti, su ne a qashin kansu, uku daga cikinsu suka zavi salama daga xaukar wannan nauyi suka bar uku. Sannan sauran ukkun kuma suka xorawa Abdurrahman xan Aufu fitar da gwani daga cikin biyunsu, tunda shima ya bi sawun ukkun can na farko kuma Umar Raliyallahu Anhu ba yada hannu a cikin wannan tsari.

Abin da zai tabbatar maka da wannan magana shi ne tabbataccen hadisin da aka riwaito daga Amru xan Maimun, wanda ya ce: kafin shexar Umar Raliyallahu Anhu ta qarshe ta kai ga bugawa, a lokacin da aka soke shi, ya ce: tun kafin yau wasu mutane ke neman in nada magaji, don kada a sami tajin-tajin bayan na wuce. To na danqa wannan al’amari hannun sababban nan shida. Waxanda ko da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu yayi matuqar yadda da al’amarinsu, wato: Ali da Usman da Xalhatu da Zubairu da Abdur-Rahmanu xan Aufu da Sa’adu xan Maliku Raliyallahu Anhu sannan Abdullah xan Umar ya zama Alqali. Amma kada su kuskura su zave shi a matsayin halifa.

Idan Allah ya sa Sa’adu ne suka zava, daidai. Idan kuwa wani ne, to ina horonsa da ya yi aiki da shi. Domin kuwa ba wata kasawa ko yaudara ce tasa na tuve shi ba.

Daga nan kuma sai ya ce: ina yi wa duk wanda Allah ya xorawa wannan nauyi, bayan na wuce, wasiyya da tsoron Allah Ta’ala. Kuma don Allah ya tsare alfarmar muhajiru na. mutanen nan na farko da aka zava da gidajensu da dukiyoyensu don kawai sunce Allah, ya kuma ba su haqqinsu. Haka kuma don Allah ya kula da Ansaru. Mutanen nan da suka saxaukantar da gidajensu, suka kuma yi imani tun gabaninsu, duk abin da suka yi na kyautatawa ya qarva, ya kuma yafe kura - kurarsu haka kuma ina yi masa wasiya daya kula da mutanen sauran garuruwa, yayi tayi man alheri. Domin kuwa ba don su ba, da musulunci bai kai labari ba, sun turawa magabata haushi. Suna kuma tsaye haiqan ga tara haqqin Allah na dukiya. Kada ya kula da wani abin da suka yi ko za su yi, sai na alheri kuma ya jira sai sunci sun raga, sannan a nemi yardarsu a kan saura. Haka kuma Larabawan qauye, suma don Allah ya kyautata masu. Don sune tushen Larabawa da makamashin musulunci. Idan aka tashi karvar zakka daga gare su, a kuma raba ta ga talakawa daga cikinsu. Haka kuma kafiran amana, don Allah ya tabbata ya cika duk arqawarin dake tsakaninmu dasu, bisa yardar Allah da Manzonsa. Ya kuma yaqi duk wanda ke dagagensu. Kada kuma ya xora masu duk abin da basu iyawa.

To ka ji iyakar abin da Umar Raliyallahu Anhu ya ce, gab akin wanda ba ya qarya.

Mun qare da wannan. Bari mu koma ga cewar da xan Shi’ar yayi, kuma wai Umar ya ce: idan bakin Ali da Usman Raliyallahu Anhu ya haxu to, duk wanda suka zava ya zavu. Idan kuma suka kai su uku, wato kwamitin ya rabu gida biyu, to duk wanda inda Abdur-Rahman, yake suka zava ya zavu. Kuma wai inji xan Shi’ar Umar Raliyallahu Anhu ya yi haka ne don ya san ba yadda za a yi bakin Ali da Usman Raliyallahu Anhu ya haxu a kan wani al’amari, haka suke kamar Annabi da kafirci. Kuma wai halifan ya san da cewa Abdur-Rahman ba zai kasa zaven xan Ammininsa Usmanu ba.

To a nan, muna son xan Shi’ar ya gaya mana wanda ya ce Umar Raliyallahu Anhu ya ce haka. To kuma tafi. Ko da ta tabbata ya ce haka xin, baya halatta da dacewa a yi masa irin wannan fassara, cewa ya kutsa haka ne don yana son a zavi Usman, yana kuma kyamar a zavi Ali Raliyallahu Anhu. Ai inda wannan itace manufarsa, to kai tsaye tun farko, zaice na zavi Usman ya gaje ni. Kuma babu wanda zai yi gigin musa - masa. don kuwa gashi bayan ma ya qaura xin Usman xin ne aka zava. Wanda hakan ke nuna suna son sa fiye da kowa. Kuma inda ma hakan yayi, to alqadarin Usman xin zai fi fitowa, don xa’arsu gare shi za tafi kauri a matsayinsu na mutane masu son addini da rajen aikata alheri da tabbatar da adalci. Kamar yadda muminai suka shede su. Kai I ko da akasin haka suka kasance. Kamar yadda munafukai ke zarginsu, ba za su kasa fesawa wannan zave na Umar turaren xa’a ba.

Ko shakka babu, da wannan itace manufarsa, kamar yadda na faxa a baya kaxan. To babu abin da zai hana shi tabbatar da ita, kai tsaye ba tare da wasu kewaye - kewaye ba. Tunda ba wanda yake tsoro. Wanda har hakan tasa ‘yan Shi’ah nace masa: Fir’aunan al’ummar Muhammadu.

Kai kasan idan dai har halifa Umar Raliyallahu Anhu ba zai ji shakkun miqewa ba shi kaxai, ya zavi Abubakar Raliyallahu Anhu a matsayin magaji Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Ba kuwa zai ji shakkar tabbatar wani, ko ba Usmanu Raliyallahu Anhu ba, da halifanci bayansa ba. A lokacin da mutane suka riga suka saba da biyayya, musamman gare shi.

Ka ga a hankalce Umar Raliyallahu Anhu ba yada buqatar shirya irin wannan qungiya - qungiya don tabbatar da irin wannan sassauqar manufa. Kuma tafi na ji. Wai ma me zai ba Umar yaqi Ali saboda Usman Raliyallahu Anhu? ai babu wata alaka dake tsakaninsa da Usman fiye da Alin Raliyallahu Anhu wadda zata wajabtar da faruwar haka. Babu wata kariya tsakaninsu ta qabilanci ko akasin haka balle a ce.

Ko harma a ce wai: Umar Raliyallahu Anhu ya san ba yadda za a yi bakin Ali da Usman Raliyallahu Anhu ya haxu a kan wani al’amari xaya. Wai Shi ya sa ya shirya waccan munqisa.

Haba! Wace irin qiyayya ce wannan?

Wannan magana qarya kawai aka yi wa halifa Umar Raliyallahu Anhu domin kuwa ba a tava ganin halifofin a rana biyu ba, tsawon rayuwar halifan. Hasali ma dangantakar dake tsakaninsu, babu ta tsakanin xayansu da wani daga cikin sauran manbobin kwamitin gida huxu. Domin duka su biyun bani Abdulmunafi ne. Mutanen da kodayaushe kansu haxe yake tsawon tarihi.

Haka kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai halifa Umar Raliyallahu Anhu ya san cewa Abdurrahman ba zai kasa zaven Usmanu Raliyallahu Anhu ba, a matsayinsa na xan ammininsa, qarya ce kawai.

Na farko dai Umar bai da alaqa da wannan magana. Na biyu kuma babu wani zumunci tsakanin Abdurrahman da Usman Raliyallahu Anhu balle ya zama xan ammininsa. Kai i hasali ma ba ’yan qabila xaya bane. Abdurrahman xan qabilar bani Zahrata ne. shi kuwa Usman xan qabilar bani Umayya ne. kuma ma hulxar jakadancin dake akwai tsakanin banu zahrata da banu hashim tafi wadda ke tsakaninsu da banu Umayyata nesa ba kusa ba. Domin su banu Zahrata xin kawanni ne ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kuma daga cikinsu ne shi Abdurrahman yake. Har ma da Sa’ad xan Abi Wakkasin, wanda har watarana Annabi yayi alfahari da shi, da cewa: Sa’ad xaya ne daga cikin kawannina, mutum ya gwada mani nasa kawon.

Kai ba wannan dangantaka ta jini ba. Ko da irin zumuncin nan na musulunci babu shi tsakanin Usman da Abdurrahman. Domin kuwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai qulla irin wannan zumunci tsakanin Muhajiruna ko Ansaru wasu - wasu ba. Ya dai qulla shi ne tsakanin jinsunan mutanen biyu. A inda shi Abdur-Rahman a matsayinsa na muhajiri ya zama xan’uwan Sa’adu xan Rabi’u Ansari. Sahabin da keda hadisi shahararre a cikin Sihahu da wasu littafai. Babu wani malami a cikin wannan fanni da bai san da shi ba. Amma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai qulla irin wannan zumunci tsakanin Usman da Abdur-Rahman ba. Balle ace ko don shi ya zave shi. Kai! Hasali ma, ko irin wanan hulxa ta rayuwar duniya Usman bai cika yi dashi, balle.

Sannan kuma idan tsawon wannan mujadala bai sa ka manta ba. Xan Shi’ar ya ce wai kuma: Umar ya yi umurni da a kashe ‘yan kwamitin idan suka kasa yi wa xayansu bayi’a har tsawon kwana uku.

Ina fatar ka tuna.

To da farko dai wannan magana qarya ce. Ko kuma idan xan Shi’ar na musu, to ya gaya mana wanda ya inganta ta. Ko tabbataccen asalinta.

Abin da kawai ya tabbata a tarihi shi ne, halifan ya hori Ansaru da cewa kada suyi nesa da kwamitin har sai an zavi wanda aka zava an kuma yi ma sa bai’a.

Sannan kuma abu na biyu: Wannan magana kamar yadda muka faxa, qarya ce. Babu wani ma’abuci ilimi daya riwaito ta. Kuma ma dai ai abin ya savawa hankali Umar Raliyallahu Anhu ya yihoro da kashe waxannan Sahabbai. Alhali ya san babu kamarsu a wannan al’umma. Kuma idan aka kashe su, lalle sai an yi da an sani irin matsanancin fasalin da zai faru, dalilin haka. Kuma inda gaskiya ne ya bayar da wannan umurni, to lalle ne a samu ko ya ce: bayan kun kashe sai ku naxa wane da kowane. dole ne a samu haka. Don bata yiwuwa mai hankali ya karva wa makaho sanda, ba tare da ya ba shi wata ba. Daxa ko ko ta raga ce.

Ka ga a haka wannan xan Shi’ar ya tabbata maqryaci, irin wanda bai san abin daya kamata ya rubuta ba, shar’ance da al’adance.

Kuma ma wani abin ban mamaki dake kasa tabbatar maka da cewa rashin kunyar fafilawa ya vaci shi ne, cewa suka yi wancan kisa da Umar Raliyallahu Anhu ya yihoro da shi ayi wa ‘yan kwamitin. Hukuncin ya dadare dasu amma banda gogan nasu Ali Raliyallahu Anhu.

To mu qaddara cewa gaskiya ne ya bayar da umurnin. To ya za a yi da cewar can kuma da suka yi wai yana matuqar son sune ban da Ali don haka ya taqaita halifancin a da’irarsu?

Ka ga a haka kamar suna sone su haxa ruwa da wuta ne wuri xaya.

Wannan kenan. Amma kuma na san saboda tsananin kangara. ‘yan Shi’ah na iya cewa, Umar Raliyallahu Anhu ya bayar da wancan umurni ne kawai. Amma Ali Raliyallahu Anhu kawai yake nufin a kai.

To sai mu ce masu: wannan ma ba ta savo, wai bindiga a ruwa. Yau da gaba xayan ‘yan kwamitin za su yi mubaya’a ga wanda suka zava. Amma Ali Raliyallahu Anhu ya qiyi, hakan ba zai hana naxin yiwuwa ba. Balle har a nemi kau da shi. Ga al’adar irin wannan sha’ani na shugabanci ana gafartar da wanda ake jin yana iya kawo tsagaro gare shi ne idan ya wandare. Ai ka ga Sa’adu xan Ubaidata bai yi wa Abubakar Raliyallahu Anhu bai’a ba amma ko jan ido ba a yi masa ba. Balle xauri ko duka. Daxa balle kashi.

Ka dai sake vulo mun daddale wannan.

Kuma ai ka ga akwai masu cewa Ali Raliyallahu Anhu da gaba xayan banu Hashim, duk ba su yi wa Abubakar Raliyallahu Anhu bai’a ba sai bayan wata shida. Amma kuma kafin haka babu wanda ya yi masu ko jan ido balle duka, ko tilasta su bai’ar. To bai’ar Abubakar Raliyallahu Anhu kenan wadda gaba xayan Sahabbai ke jin wajibi ce a kansu. Ka ga ya savawa hankali matuqa wannan bai’a ta Usmanu. Wadda ko shi kansa Umar xin bai wajabtawa kansa balle wani.

To, aje ma duk wannan. Tarihin musulunci ya tabbatar da cewa tsawon lokacin halifancin Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma sahabba na matuqar karrama Ali Raliyallahu Anhu da sauran bani Hashim, fiye da yadda suke karrama sauran mutane. Harma an riwaito Abubakar Raliyallahu Anhu kan ce: ya ku mutane! ku kiyaye alfarmar Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ta hanyar tsare mutuncin mutanen gidansa.

 Kuma yakan taka da kafafunsa har gidan Ali Raliyallahu Anhu a inda yakan taras da banu Hashim anjin. Ya zauna suyi taxi: ya ba su girman suna kasancewa dangin Manzon Allah. Su kuma su bashi nashi na kasancewa halifa kuma shugabansu, harma suyi masa jinjina. A irin wannan haxuwa ce suka bashi haquri a kan rashi yi masa bai’a cikin dubu. Nan take kuma suka yi ta xaga su sai shi.

Bayan haka kuma dubban dalilai, sun tabbatar da cewa akwai matuqar qauna da fahimtar juna tsakanin Ali Raliyallahu Anhu da waxannan sabahabbai biyu. Abin da kuma ire-iren wannan shaqiyin xan Shi’a ke faxa qarya ne. Ah! qarya ne mana. Kai ka san da Sahabban na da qudurin cutar da Alin Raliyallahu Anhu a lokacin da suke halifofi suna da wannan iko. Ba sai sunyi qoqarin yin haka ta kure shi daga halifancin ba. Abun bai kai can ba.

Qarya ce da rennin hankalin mutane ‘yan Shi’ah ke yi, suce wai Sahabban sun zalunci Ali Raliyallahu Anhu a daidai lokacin da yake iya yi wa kansa faxa. Amma kuma sun kasa zaluntarsa a lokacin ba su da wani qarfi ko iko a kan haka, ko da sun so. Ka ga a hankalce, lokacin da suka yi qarfi ne, mutane na sauraransu ya kamata ace sun zalunce shi xin, da suna da kudurin haka ko?

Haka kuma ita ma cewar da xan Shi’ar ya yi wai Umar xin ya yi wani umurnin da kashe duk wanda ya savawa mutum huxu ko uku da bakinsu yazo xaya, kuma cikinsu da Abdurrahman, qarya ce.

To muma qaddara ya ce hakan, to sai me kuma? Ai hakan ba ta savawa addini ba. Hakan ma yafi dacewa. don a kashe wanda ke son tayar da fitina ibada ne. kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: duk wanda ya taras daku tsintsiya maxaurinki xaya, kuna da’a ga mutum xaya, ya nemi raba kanku, to ku sare kansa da takobi ko xan waye.

Abin da kawai ya tabbata shi ne Umar Raliyallahu Anhu ya yi umurni ne da kashe duk wanda ya yi wa wani bai’a, ba tare da ya shawarci sauran musulmai ba. Kuma ya dogara ne akan wannan hadisi da ya gabata.

Amma kashe wani don xai ya qi yin bai’a, bai kuma nemi tayar da wata fitina ba, balle raba kan musulmai. Umar Raliyallahu Anhu bai yi wannan umurni ba. Hasali ma kashe irin wannan mutum ba ya halatta.

Haka kuma isharorin da xan Shi’ar ya ambata wai na kashe Usman da qin zaven Ali Raliyallahu Anhu duk qarya ne, Umar bai qulla haka ba.

Cewar da Abdur-Rahman yayi : idan ka aikata (kaza) wallahi suna kashe ka. Labari ne kawai yake bayarwa, ko ya riga ya bayar ba. Kamar yadda cewar da ya yi: ba za su zave shi ba. Ita ma labarin abin da yake ganin zai faru ne kawai yake bayar wa. Ba wai umurni ne yake bayarwa da aikata hakan ba.

Duk da yake gaba xayan waxannan lafuzza, a cikin irin wannan siyaki basu tabbata daga bakin halifa Umar Raliyallahu Anhu ba. qarya ce aka yi masa.

Allah Ta’ala shi ne mafi sani.

 2.57 Xan Shi’ar ya Dira A Kan Usman

Dama na gaya maka cewa ina zaton xan Shi’ar nan zai ta kan halifofin nan uku ne, xaya bayan xaya. Ga shi tako tabbata. Ya qare da Umar bayan Abubakar Raliyallahu Anhu yanzu kuma ya dira kan Usmanu Raliyallahu Anhu inda ya fara sukar lamarin halifan da cewa:

shi kuwa Usmanu, babban laifinsa shi ne xaukar muqami ya danqawa waxanda ba su dace dasu ba. wanda hakan tasa a qarshe, babu abin da suka sukkuna wa jama’a, in banda yaxa fasiqanci da varna a bayan qasa. Wani kuma daga cikinsu suka xaure wa zalunci gindi. Kuma abin ban ta kaici, inji xan Shi’ar duk waxanda yaba muqaman nan ‘yan‘uwansa ne na kusa. Saboda haka, da mutane suka yi qorafi a kansa, yayi kunnen uwar shege dasu.

Ka ga Walidu xan Ikibata, wanda halifan ya naxa gwamna, babu abin da ya aje sai shan giya. Har watarana ta kai shi gaba mutane salla yana lage. Shi kuwa Sa’idu xan Asi wanda halifan ya kai Kufa, aika - aikar da ya yi bata faxuwa. Wadda har tasa mutanen garin suka kore shi. Sai Abdullahi xan Sa’ad xan Abi Sarhu, wanda ya kai masar. Shi kuwa saboda tsanancin zaluncinsa saida talakawansa suka kawo qararsa wurin halifan. Amma saboda qin Allah, sai halifan ya aika masa a rubuce, cewa wannan ba komai bane, Ya ci gaba da mulkinsa yadda ya saba. Ya aika masa da wannan saqo ne asirce, savanin abin da ya rubuta masa a bayyane. Ya kuma yi masa umurni da kashe wani mutum da ake kira Muhammad bin Abubakar.

Haka kuma dai inji xan Shi’ar, Usman ya naxa Mu’awiyah gwamnan sham, inda yaje ya shimfixa maqaqiyar tabarmar fitina, haka kuma ya kai Abdullahi xan Amru a busra. Shima yayi ganin damarsa a can. Qarewa da qarau ma, sai ya danqa wa Marwanu ragamar gudanar da komai. Har da tasarrafi da hatiminsa na halifanci. Wanda a qarshe hakan ta zama sanadiyar kashe Usmanu Raliyallahu Anhu wutar fitina ta kama sosai a cikin al’umma. Kafin haka inji xan Shi’ar, halifan ya kasance yana xibar dukiya mai yawa daga baitil mali yana ba ‘yan’uwansa da iyalinsa. Wanda har watarana ya xibi dinari dubu xari huxu yaba wasu kuraishawa huxu dake auren ‘yayansa mata. Ya kuma ba Marwanun can dinari dubu biyu.

Ya ci gaba da cewa: Usmanu ne, bayan yahau gadon halifanci, yasa aka yi wa xan mas’ud dukan tsiya, har saboda yana suka tare da kafirtarsa har ransa ya fita. Haka yasa aka yi wa Amru har fatar jikinsa ta farfashe. Alhali kuwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Amru wata fata ce daga cikin fatun idona. Kuma ina jin wasu la’ananni ne za su kashe shi. Waxanda nake fatar Allah ba zai sasu cikin cetona ba, ranar qiyama. Shi ma Amru ya sami wancan xanyen hukunci ne saboda sukar halifan da yake yi.

Haka kuma wai kafin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwanta dama, sai da ya kori ammin halifan, Hakamu xan Abilas, tare da xansa Marwan daga birnin Madina. Birnin da ya yi masu qarshen xan goma tsawon rayuwar manzon da halifa Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma amma wai hawan Usmanu karagar keda wuya sai ya dawo dasu birnin. Ya kuma naxa Marwanun magatakardansa, kuma sarkin fada. Alhali Allah Ta’ala ya ce: Ba zaka sami mutane masu yin imani da Allah da Ranar lahira ba suna soyayya da wanda ya sava wa Allah da manzonsa, ko da sun kasance ubanninsu ne, ko xiyansu (58:22).

Kuma inji xan Shi’ar, Usman Raliyallahu Anhu xin dai ne wanda ya kori Abu Zarrin daga Madina ya koma Rabzata, bayan shima ya yi masa xan Karen duka. Alhali kuwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: kasa bata tava xaukar wani mutum mai faxin gaskiya inuwa ba kamar Abu Zarri. Ya kuma ce: haqiqa Allah ya yi mani wahayin cewa akwai wasu Sahabbai nawa da yake matukar so. Saboda haka ni ma ina so su. Sahabbai suka tambaye shi su waye waxannan ya Manzon Allah? Sai ya ce : limaminsu shi ne Ali, sai Salmanu da Miqdad da Abu Zarri.

Kuma wai halifan ya keta alfarmar hukuncin Allah. Saboda yaqi kashe Ubaidullahi xan Umar wanda ya kashe Hurmazanu bawan Ali Raliyallahu Anhu wai Alin ne ya tashi tsaye yana qarsheta dai wurin Mu’awiyah ya fake . kuma wai halifan yaso yaqi zartar da hukuncin shan giya ga Wahdu xan Ukbata, saida Ali Raliyallahu Anhu ya karvi aikin a hannunsa ya zartas, yana mai cewa: bata yiwuwa a tozarta hukuncin Allah ina nan kuma raye.

Haka kuma wai Usman Raliyallahu Anhu xin ne ya bidi’ar da kiran salla na biyu a ranar juma’a. har aka wayi gari hakan ta zama sunna a yau. Kuma wai saboda waxannan halaye ne nasa, gaba xayan musulunci suka juya masa baya har suka aika shi lahira, tare da yin Allah waddai da ayyukansa. Suka yi masa rakiya da cewa : kaqi fita yaqin Badar, ka fita na Uhudu ka gudo. Kuma bada kai aka yi bai’atur - Ridhwan.

Xan Shi’ar ya kamala da cewa: irin waxannan miyagun labarai a kan Usmanu ba su da iyaka.

Martan: kafin mu shiga fixar wannan magana dalla-dalla tare da warwarar zare da abawarta, muna tabbatarwa xan Shi’ar da cewa, ai ba lalle Sarkin mugun ba faxa ya zama mugu. Kuma daga tai dahakimai su cuci sarkinsu, a tarihin musulunci bag a halifa Usmanu aka fara ba. Cutar da wakilan Ali Raliyallahu Anhu a garuruwa suka guma masa, tare da yin yamma a duk lokacin da ya yi gabas, tafi wadda wakilan Usman Raliyallahu Anhu suka yi.

Akwai rubuce-rubuce da dama da aka yi a kan wasu waqilai da Alin Raliyallahu Anhu ya naxa suka kwashe dukiyar talakawansu. Wasu kuma suka bar shi, suka koma gindin Mu’awiyah. Kuma ta tabbata Alin Raliyallahu Anhu yayi aiki tare da Zayyadu xan Abu sufyanu, baban Abdullahi xan Zayyadu, makashin Husaini, a matsayin waqilinsa. Haka kuma yayi da Al-ashtar An-Nakh’i da Muhammad xan Abubakar da makamantarsu. Duk a wannan matsayi. Kuma kai kasan Mu’awiyah xan Abu Sufyanu Raliyallahu Anhu yafi duk waxannan zama mutumin kirki ga duk mai hankali.

 Sannan kuma naxa ‘yan’uwa da makusanta muqamai baga halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ne karau ba. Balle ‘yan Shi’ah su addabe shi damu. ai tarihi ya gaya mana cewa a lokacin da Ali Raliyallahu Anhu ya zama halifa shima ya naxa nasa ‘yan’uwa da makusanta, na wajen uwa da uba. Kamar irin su: Abdullahi da Ubaindullahi ‘’ya’yan Abbas. Ya kai Ubaidu a yaman, Qasimu xan Abbas xin kuma Makka da Daya. A Madina kuma ya naxa Sahlu xan Hunaifu a matsayin gwamna. Wasu malaman tarihi kuma suka ce: a’a Samamatu xan Abbas ne ya kai can. A yayin da ya kai Abdullahhin can xan Abbas, harwayau, Barra. A masar kuma ya kai xan ‘yaye da renonsa, wato Muhammad xan Abubakar.

Kuma qarewa da qarau ma, saboda tsananin mamaya, handama da babakere, Aliyun Raliyallahu Anhu bai bar duniya ba saida ya yi wasicci a kan kada a fitar da halifanci daga hannun zu’arsa, xaya bayan xaya. Kamar yadda Shi’ah ‘yan-sha-biyu ke faxawa duniya.

Ina fatar xan Shi’ar ya san wannan tarihi:

Kuma kai mai karatu, ka san idan wanda ya naxa danginsa sarautu da muqamai ya yi wani abin qi da kyama. To abin da waninsa yayi a qaqaice masu uwar muqamai, wato halifancin yafi zama laifi. Musamman kuma idan aka taras ‘ya’yansa da jikokinsa ne, ya yi wa wancan qaqacin ba danginsa ba a wajen Uba kamar yadda wancan yayi. Kuma ma a kan wannan ma’auni ne wasu malaman fiqihu suka yanke hukuncin cewa, duk wani waqili ko waliyin da baya isarwa kansa ga wata hulxa ta ciniki, to baya halatta ya waqilci xansa a irin wannan mu’amala. Kuma ko da dukiya ce aka ba shi don yayi kyauta da ita ga duk wanda yaga dama, to wanda yaba shi ba zai karvarwa kansa ko xansa ita ba, a xayan zantukan.

Haka kuma malaman sun karu da junansu sani, a kan halacci da yiwuwar halifa ya yi wasicci da xansa ya gade shi. Wasu suka yarda da ha kan wasu kuma suka ce, faufau. Kuma a wurin mafi yawan malamai, ba a karvar shedar mahaifi ga dansa. Amma shedar mutuma ga ammininsa karvavva ce. Haka hukuncin yake a cikin sauran hukunce-hukunce.

Wato abin da muke son fitarwa a nan shi ne, a shar’ance, xa da mahaifi abu xaya ne ya rabu biyu. Haka kuma abin da ke tsakaninsu na haqqoqi. Kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: da mutum da dukiyarsa duk mallakar mahaifinsa ce. Ya kuma ce: babu wanda keda xamar tayar da kyamutar da ya yi. Sai fa idan xan cikinsa ya yi wa.

Wannan kenan. Amma kuma da ‘yan Shi’ah za su ce: Ai Ali Raliyallahu Anhu yayi abin da ya yi ne da umurnin Allah da Manzonsa.

To sai mu ce masu: Eh! To, ba mu musun kasancewar Ali Raliyallahu Anhu halifa nagartacce, kamar yadda Usmanu Raliyallahu Anhu yake. Amma kuma koba musan dalilin kowanensu ba, a kan abin da ya yin. Duk mai hankali zai fi shakku da zargin Ali fiye da Usman Raliyallahu Anhu.

Amma kuma na san ‘yan shi’ah za su kawai qale ni biris ne, suce wata qila ko ban gane abin da suke nufi ba. Alhali kuwa na gane.

Suna sone suce: Ali na da hujja a kan wancan aiki da ya yi.

To naji na kuma yarda. Amma ina tabbata masu hujjar da Usmanu Raliyallahu Anhu keda ita tafi tasa nesa ba kusa ba. Don na san iyakar abin da za suce shi ne, ai Ali Raliyallahu Anhu Ma’suni ne, duk abin da ma ya aikata daidai ne a shari’a. saboda haka sai a kame baki daga sukar sa haka nan. To wannan ma naji kuma na yarda. Amma kuma ina tabbatar masu da cewa hujjar da kega Usman Raliyallahu Anhu ta kasancewarsa mujtahidi, tafi iya sa masu sukar sa su saurara, ta kuma fi zama kusa ga hankali da naqali.

Allah dai ya sawwaqa.

Idan ka kwantar da hankali , za ka fahimci cewa iyakar abin da xan Shi’ar ke guri da wannan aiki nasa tun farkonsa, shi ne ya shafawa mutanen da lafiyayyen hankali da ingantaccen naqali suka tabbatar da fifikonsu a kan takwarorimu qashin kaji. A lokaci xaya kuma ya yi wa waxanda ake bin wancan tsarki. Duk ta hanyar sukar wadancan da yabon waxannan, kamar yadda Nasara suka yi tsakanin Annabawan Allah. Suka qasqanta darajar waxanda Allah ya xaukaka daga cikinsu, tare da nuna darajarsu bata ko kai ta Sahabban Annabi Isa Alaihis Salamu ba. Shi kuwa Isan Allah ma sukutum.

Babban abin ban ta kaici da mamaki ma duk bai fi yadda suka naxawa Sahabban na Annabi Isah Alaihis Salamu rawanin ma’asumanci ba. Tattare da kasancewar darajarsu ko gata Annabawa ba ta kai ba. A lokaci guda kuma suna sukar lamirin Annabawan. Kamar Annabi Sulaimanu da waninsa.

Kai! Ba Sulaimanu kawai ba. A wajen nasara darajar Sahabban Annabi Isah Alaihis Salamu tafi ta Annabi Ibrahim da Muhammad Alaihis Salamu ka kuwa san dalilai da yawa na shari’a sun tabbatar da fifikon darajar waxannan Annabawa biyu a kan Isan kansa, balle Sahabbansa. Amma kaji aqidar nasara a kansu.

Irin wannan aiki na jahilci kuwa, da shishshigi na daga cikin abubuwan da Allah Ta’ala ya hana nasara yi. Inda ya ce: Ya mutanen littafi! Kada ku zurfafa a cikin addinku. Kuma kada ku faxa ga Allah face gaskiya. Abin da aka sani kawai, Al-Masihu Isah xan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarsa, ya jefa ta zuwa ga Maryama, kuma ruhi ne daga gare shi (4:171).

To yadda ka ji haka, haka ‘yan Shi’ah suke, su da Nasara ba wani banbanci.

Eh! Ba wani banbanci mana a tsakaninsu. Tunda su ma shishshiginsu yasa sunce Ali Raliyallahu Anhu Allah ne. to ka ga a nan ma har gwamma Nasarawa dasu. Don Isa Annabi ne, to Ali fa. A yayin da wasu ragilawan ke cewa Annabi dai ne shi Alin ba Allah ba. To ka gasu waxannan dai- dai suke da mabiyan Musailamatul-Kazzabi, waxanda suka yarda da wani Annabi bayan Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama illa dai shi Ali Raliyallahu Anhu ba yada wani laifi cikin wannan al’amari. Don ba shi ne ya kira kansa Allah ko Annabi ba. Savanin Musailamatu da takwarorinsa.

Su kuwa Shi’ah ‘yan-sha-biyu abin da suke iqirari shi ne, imamancin Ali Raliyallahu Anhu tabbataccen abune bisa nasu. Kuma shi da, da yawa daga cikin zuri’arsa duk ma’asumai ne. Kuma wai sauran Sahabbai sun zalunce su.

Ma’asumancin nan da kake ji, ma’anarsa a wurinsu daidai take da ta Annabci. Domin kuwa wajibi ne wai a yi wa ma’asumi xa’a a cikin duk abin da ya faxa, sava masa haramun ne. Ka kuwa san Annabawa kawai ne keda wannan matsayi. Saboda sune Allah Subhanahu WaTa’ala ya umurce mu da yin imani da abin da aka saukar masu, inda ya ce: ku ce: “mun yi imani da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrahim da Isma’ila da Ishaka da yaqubu da Jikoki, da abin da aka bai wa Musa da Isah, da abin da aka bai wa Annabawa daga Ubangijinsu, bamu rarrabewa a tsakanin kowa daga gare su, kuma mu a gare shi masu salamawa ne (2:136).

Ka ga a nan Allah ya umurce mu damu ce: mun yi imani da abin da aka ba Annabawa. Kuma gaba xayan musulmi sun yi ittifaqi a kan cewa imani dakowane Annabi wajibi ne. duk kuwa wanda ya kafirce wa waninsu to kafuri ne. idan da kuma izgilin zagin xaya daga cikinsu wani yayi to jininsa ya halatta inji malamai.

Wannan matsayi kuwa na Annabawa ne kawai, babu wani wAliyu ko shugaba ko fasihi ko malami ko waninsu da keda irinsa. Duk kuwa wanda ya ce ga wani mutum wai shi ma’asumi ne da imani da duk abin da ya faxa yake wajibi, bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama to yana aufin shi ma Annabi ne.

Eh! Haka yake nufi mana ko da kuwa bai ambace shi da sunan ba. Kuma babu wani banbanci tsakanin wannan da Annabawan bani Isra’ilu.Waxanda aka umurta biyar shari’arttawa.

Wannan kenan. Sannan kuma sanannen abune cewa irin waxannan kudurce - kudurce na wuce gona da iri, da qoqarin samarwa da wani gunki a haxa shi da Allah da manzonsa a bauta, ya savawa Addinin Musulunci, Alqur’ani da Sunna da ijma’in al’umma da malamanta duk ba su yarda da haka ba. Ga kuma abin da Allah Ta’ala ke cewa: Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi xa’a ga Allah, kuma kuyi xa’a ga manzonsa, da ma’abuta al’amari daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar dashi zuwa ga Allah da manzonsa (4:59).

Ka ga ashe kenan duk wanda ya samar da wani mutum ya kuma ce ma’asumi ne, bayan Manzon. Wanda kuma duk abin da ya faxa gaskiya ne. to yana nufin kenan wajibi ne a mayar da abin da ya faskara gare shi. Wannan kuwa ya savawa umurnin Alqur’ani.

Domin kuwa Manzo ne kawai Alqur’ani ya wajabta yi wa xa’a maras adadi, ba ma’asumi ba kamar yadda Shi’ah ‘yan-sha-biyu ke cewa, ya kuma tabbbatar da alwashin farko ga duk wanda ya sava masa. Tabbataccen wannan magana. Shi ne abin da Allah Ta’ala ke cewa: Kuma waxannan da suka yi xa’a ga Allah da Manzonsa, to, waxannan suna tare da waxanda Allah ya yi ni’ima kansu daga Annabawa da masu yawan gaskiya, da masu shahada, da salihai. Kuma waxannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya (4:69). Ya kuma ce: to, wanda ya savawa Allah da Manzonsa, to, lalle yana da wutar jahannama, suna masu dawwama a cikinta har abada (27:23).

Ka ga anan da wurare da dama Alqur’ani ya nuna cewa gidan aljanna shi ne sakamakon wanda ya yi xa’a ga Manzo. Amma bai sharxanta haka ga wani don yayi xa’a ga wani wai shi ma’asumi ba duk kuwa irin yadda zai yi xa’a ga ma’asumi to makomarsa ita ce wuta, matuqar bai yi xa’a ga Manzo ba.

Domin Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne Alfijirin da Allah ya ware ‘yan aljanna daga ‘yan wuta da shi. Ya kuma sa shamaki tsakanin fajirai da nagatattun bayi da albarkarsa. Ya kuma yi katangar qarfe tsakanin qarya da gaskiya, da bata da shirya, da sanadarinsa. Wanda kuma tahowarsa ce ta kafawa shaqiyai tasu bukka daban, ta kuma kafa wa Sa’idai tasu. Shi ne wanda ake yi wa xa’a a rabbanta, a saba masa a vakita. Babu kuma mai irin wannan daraja sai shi Sallallahu Alaihi Wasallama.

A kan haka ne, kan gaba xayan malaman da suka naqalci sirrin Alqur’ani da sunna, ya haxu a kan cewa babu wanda yafi qarfin a xauki maganarsa in anso, ko a saka ta kwandon shara in anso sai mijin Khadija baban Zainab Sallallahu Alaihi Wasallama shi kan wajibi ne duk abin da ya faxa a gasgata, duk abin da ya yi umurni kuma a aikata. Saboda shi ma’asumi ne da komai ya faxa umurni ne daga Allah Subhanahu WaTa’ala ba son zuri’arsa ba. Don baya dashi. Shi ne kuma wanda Allah zai tambayi mutane a kan yadda suka xauke shi, ranar qiyama. Kamar yadda Allah Ta’ala ya faxa mana: sa’annan lalle ne muna tambayar waxanda aka aika zuwa garesu, kuma lalle muna tambayar manzanni (7:6) .

Shi ne kuma wanda Allah zai jarraba mutane a kansa, a cikin qaburburansu yasa ace wakowannensu: waye Ubangijinka? Mene ne kuma Addininka? Kuma wanene Annabinka? Wace irin sheda kake iya bayarwa a kan manzon da aka aika maku? A nan ne Allah zai taimaki masu imani na gaskiya, ya ba su ikon cewa: Annabinmu dai shi ne xan Abdullahi (Muhammadu) bawan Allah ne kuma Manzonsa. Ya zo mana da walihahhen abubuwa da shirya kuma munyi imani dashi mun bishi.

Da mutum zai kuskure ya ambaci wani ba Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ba, kamar wani Sahabi ko tabi’i. Ko wani malami, to kashinsa ya bushe. Don lokacin ba a son jin sunan kowa in ba shi ba.

A taqaice dai, kada inji ka da nisa. Abin da kawai muke son tabbatar da wannan dogon karatu shi ne, duk uzurin da wani zai iya kawowa, don ya ceci wuyan Ali Raliyallahu Anhu a kan abubuwan da ake qorafi a kansa, to akwai dubunsu da qari, da ake iya kawowa don a daxa gyara wuyan rigar Usman Raliyallahu Anhu a kan shigen waxannan abubuwa.

A taqaicen taqaitawa ma ka ga, Ali Raliyallahu Anhu ya yaqi musulmi tantagarya saboda kujerar halifanci, har aka salwantar da rayukan jama’a da dama. Kuma tsawon halifancinsa bai yi yaqi da kafirai balle yaci garuruwansu, xaukar musulunci ta faxaxa ba. Babu wani ci gaba da musulmi suka samu a lokacinsa. Kuma ya ba waxanda ya ga dama daga cikin makusan tansa muqamai, kamar yadda Usman Raliyallahu Anhu yayi. Illah dai hikimar Usman sun fi nasa xa’a da misantar sharri.

Ita kuwa dukiyar da ake zargin Usmanu Raliyallahu Anhu wai da Almubazzarantarwa, halifan yana da hujja a kan haka (tawili) kamar yadda wai Ali Raliyallahu Anhu keda tashi hujja (Tawuli) a kan zubar da jinin musulmi. Ka kuwa san jinainai sufi dukiya haxari ko?!

Sannan abu na biyu kuma shi ne, wannan nassi kuke ta gogogo dashi, a matsayi hujjar Ali Raliyallahu Anhu a kan wannan abu da ya yi, ku kanku kun kasa haxa kanku a kansa, idan wasunku suka yi gabas sai wasu suyi yamma. Wannan kuwa shi ke tabbatar da cewa gaba xayanku baku da wata taqammar hujja. Tunda ‘yan kame - kame ne da kurin qarya kowannen ku keyi. Kuma jumhurun malamai sun tabbatar da haka.

Wannan kenan. sannan abu na ukku kuma, da za’a kalli abin da halifa Usmanu yayi a bawa banu Umayyatu muqamai, da idon taura, to za’a fahimci cewa wani abune kamar sunna. Kamar yadda shi halifan kan kafa hujja a duk lokacin da aka qalubalance shi, da cewa: ai bani na fara ba: ko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi aiki dasu a lokacin da yake raye. Kuma halifa, Abubakar Raliyallahu Anhu ma yayi aiki dasu. ba kuwa don suna danginsa ba, balle a tuhumce shi. Kai har Umar ma bai ki suba.

Hasali ma iya saninmu ba musan wata qabila da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yawaita aiki tare da ‘ya’yanta, daga cikin qabilun Larabawa, kamar banu Abdush-shams. Ko banza qabilace mai tsananin yawa da gabaci. Wanda hakan tasa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya naxa Uttabu xan Asyad dan Abi Aisu xan Umayyata gwamnan qasa mafi daraja, wato Makka. Da fatar hakan ta taimaka ga bunqasa musulunci. Ya kuma kai Abu sufyanu xan Harbu xan Umayyata a Najiranu. Khaddu xan sa’id xan Asi ya kai shi Wan’a’al-yaman bayan yasa shi karvar zakka daga banu mazhajin. Yana yamen din ne a matsayinsa na gwamna Allah ya karvi ran manzo Sallallahu Alaihi Wasallama. Haka kuma manzon ya kai sa’id xan Asin taima’a da Haibara da sauran Alkaryun Uraibah, don ya rike su. Ya kuma sa Abban dan sa’idun kula da balahyoyi.daga nan kuma ya yi masa canjin aiki zuwa Bahrain, bayannan xauke Ala’u dan Hadhrami daga can. A can ne Abbanun ya ci gabada aiki har qarshe rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama haka kuma manzon ya yi aiki da walidu dan ukubata. Wanda a kansa ne ma Allah Ta’ala ya saukar da: idan fasiqi ya zo muku da wani babban labari, to, ku nemi bayani, domin kada ku cuci wadansu mutane a cikin jahilci (49:6).

Ka ga a haka halifa Usman nada cikakar hujja ta cewa: ai na raya sunnar Annabi ne. Don na yi aiki da waxanda ya yi aiki dasu.

Kuma irin wannan aiki da Usman Raliyallahu Anhu ya yine Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma suka yi kafinsa. Don Abubakar Raliyallahu Anhu ya yiaiki da Yazid xan Abu Sufyanu xan Harbu a yaqin da aka ci sham, a matsayi shugaba. Kuma da Umar Raliyallahu Anhu yazo bai canza masa wurin aiki ba. Bayansa ne kuma Umar xin Raliyallahu Anhu ya maye gurbinsa da xan’uwansa Mu’aiwiyya.

Wannan magana da muke gaya maka ta aikin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yayi da waxannan mutane tabbatattace. Matsayinta ma a wurin marubutan ilimi ya kai na mutawatura. Wani sashe nata ma har malaman hadisi sun karvetada hannu biyu - biyu a wannan matsayi. A yayin da sashenta ma daga bakinsu ne malamai suka jita. Kuma a jumlance ma dai babu wani daga cikinsu dake musun kasancewarta gaskiya.

 2.58 Mu Zuba Zuwa

Wannan Martani da muke yiga wannan xan Shi’ar a kan cin mutuncin halifa Usmanu Raliyallahu Anhu da ya yi bai tsaya nan ba. Mun xan yaxa zango ne mu sha ruwa mu koma daga. Yanzu kuma tunda mun nunfasa, to mu zuba zuwa.

Xazu kaxan mun yi qoqarin bayyana dalilan halifan ne a kan wadancan abubuwa da xan Shi’ar ke qorafi, tare da suka. To yanzu kuma, tattare da waxancan dalilai da muka bayyana, mu qaddara halifan bai dace da sawaba. To ko a hakan bai cancanci cin mutunci da tozartawa ba ga duk mai hankali da ilimi.

Domin kuwa a shari’ance babu wanda yafi qarfin kuskure baya ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan ita ce qa’ida, halifofi da waxanda basu ba, duk na iya faxawa a cikin kuskure. Wannan abune ja’izi a haqqinsu. Amma kuma abune mai sauqi ga Allah (subhanahu wa ta;ala) ya gafarta masu zunuban kurakuransu, ta hanyar la’akari da xinbin kyawawan ayyukansu. Ko kuma ya jarabce su da waxansu musibu irin waxanda ke karkare kantar zunubai da iznin Allah. Ko kuma ta wata hanya da ba wannan ba.

To duk kuwa wani laifi da za’a iya cewa halifa Usmanu Raliyallahu Anhu yayi bai wuce masa yin kuskure ba. Kuma a waje xaya yana da wasu sanadaran gafara da malalonsu ke iya shafe zunuban har gaba. Xauki misalin zamansa da sahun farko a shiga musulunci, da qarfin imaninsa, da irin jihadin da ya yi, da sauran ayyukan xa’arsa zuwa ga Allah, ta kuma tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa kyakkyawar sheda tare da albishirin shiga Aljanna a kan waxansu Bala’o’i da za su faxa masa.

To kuma abune tabbatacce cewa halifan ya tuba ga Allah, tuba irin ta cikon sunna, a kan duk abubuwan da ake zarginsa da aikatawa. Kuma ga jarrabawar da Allah Ta’ala ya yi masa da gwagwarmayar musulunci. Wadda ta zama sanadiyar rasa ransa ba tare da ya yi wani fargaba ko zarewa ba. Wannan kisan gilla da aka yi masa da sauran bala’o’i da ya haxu dasu kafin haka na daga cikin nau’o’in sanadaran da Allah kan karkarwa bawansa zunubai saboda su. Gashi kuma ya mutu shahidi.

Ba halifa Usman Raliyallahu Anhu kawai ba. Ko imamu Ali Raliyallahu Anhu qololuwar abin da Harijawa da sauran magabatansa ke zarginsa dashi, bai wuce zama kuskure ba ko zunubi. Kuma shima a wuri xaya yana da tarin ayyuka na alheri, irin waxanda haskensu yafi qarfin duhun zunubi komai girmansa ya bice. Waxanda suka haxa da kasancewarsa xan gaban goshin musulunci, da qarfin imaninsa, da jihadin daya zuba, da wasu ayyuka na xa’a waxanda ba waxannan ba. Kuma shi ma gashi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa kyakkyawar sheda, tare da busharar shiga Aljanna. Kuma ta tabbata shi ma ya nemi gafarar Allah ta gaba xaya, ya kuma yi nadammar abubuwan da suka faru sanadinsa ga shi kuma shima ya mutu shahidi.

Ka ga wannan qa’ida bakandamiya, ta isa sa mai hankali kame bakinsa daga abubuwan da dai - daikun Sahabban nan suka aikata, balle har ya yanke masu hukuncin zama wajibi ko mustahabbi. Matuqar buqatar hakan bata taso ba.

Ka ga kenan, a kan haka, ko dai cewar da xan Shi’ar ya yi wai halifa Usman Raliyallahu Anhu ya naxa waxanda ba su cancanta. Ko kuma ya kasance basu cancanta xin ba. Wato ijtihadin nasa ya kuskure kenan. To ko a haka bai cancanta sukar lamiri ba. Don yana da lada a wurin Allah a matsayinsa na mai ijtahidi.

Kuma ba halifa Usman ba, ko Annabawa sukan zaci abu, ya kuma kasance ba hakanan ba.

Xauki mi’salin Wahdu xan Ukubatu, wanda ake ta ganin laifin halifan, saboda ya bashi muqami. Ai tafsirai da hadisai da dama, da littafan sura sun tabbatar da cewa, watarana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tura shi karvo zakka daga wajen wasu Larabawa. Isarsa kusa da tungarsu keda wuya, sai suka yo tururuwa don su haxu dashi. Shi kai gogan naka sai ya zaci sun fito ne don su gama dashi. Nan take sai ya aikawa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da signal cewa gasu nan za su yaqe shi. Nan take sai ya aika wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yayi shirin aikawa da runduna don ta kama masa. Sai Allah Ta’ala ya saukar masa da ayar da ke cewa: yaku waxanda suka yi imani! Idan fasiqi yazo muku da wani babban labari, to ku nemi bayani, domin kada ku cuci waxansu mutane a cikin jahilci, saboda haka ku waye gari kuna abin da kuka aikata kuna masu nadama (49:6).

To ka ga, idan har wani abu na iya shigewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama duhu, to waye Usman Raliyallahu Anhu da hakan ba za ta iya faruwa gare shi ba?

Amma duk da haka na san fitsararrun (‘yan Shi’ah) na iya cewa, ai bayan faruwar haka ne Usmanun ya naxa shi.

To, sai mu karva masu da cewa, ai qofar tuba buxe take kodayaushe. Ai ta tabbata a zamanin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa Abdullahi xan sa’ad xan Abu Sarhu yayi ridda. Amma kuma yazo gaban Manzo ya faxi yana ahi yana tuba. Kuma Manzon ya karvi tubansa bayan ya riga har ya yanke masa hukuncin kisa.

Idan ba a karvar tubar mai laifi, meyasa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya karvi ta wannan?

Wannan kenan. Kuma ko da bayan naxa shinne, ta bayyana cewa shi ba mutumin kirki ba ne. Hakan baza tasa a zargi halifan da komai ba. Don ai ko Ali Raliyallahu Anhu daga baya, wasu hakimansa sun bayar daba yada ake zato ba. Kuma haka bai zama abin suka da qorafi a kansa ba. Iyakar abin da ake iya cewa halifa Usmanu yayi shi ne, naxa wasu mutane, alhali kuma yasan akwai waxanda suka fisu cancant. To ko a hakan bai cancanci suka ba, don al’amari na ijtihadi ne.

Ko kuma a ce, son da yake wa danginsa yaba shi karkata gare su, har hakan tasa ya zaci sun fi kowa cancanta da mukaman. Kuma hakan lalle laifi ne. to ko a hakan ba a binda ya gano shi. Domin kuwa mun riga mun yi bayanin yadda Allah ya wanke laifukansu.

Sannan kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai daga baya, sai hakiman na halifa Usmanu suka cika qasa da fasiqanci da varna, maganar banza ce, daba ta isa hujja ba. Domin kuwa faruwar abin bayan naxasu da aka yi, baya nuna cewa ansanda haka kafin naxin. Koma halinsu ne fil’azal. Domin tabbataccen abune cewa, lokacin da halifa Usmanu Raliyallahu Anhu yaji labarin Walidu xan Ukabatu ya sha giya. Bai yi wata - wata ba yasa aka kamo shi ya bulale shi haddi. Haka kuma halifan kan tuve duk wanda ya cancanci tuvewa daga cikin hakiman. Ya kuma tsayar da haddi a kan wanda ya cancanci hakan.

Sannan kuma xan Shi’ar ya zargi halifa Usman Raliyallahu Anhu da arzulta danginsa da dukiyar musulmi. To tafi munji wannan laifi ne, ai halifan gafartacce ne a wurin Allah. Balle ma mas’ala ce ta ijtihadi.

A ta kaice ma dai kai, babu wanda yahau wannan karaga ta halifanci, bayan halifa Umar Raliyallahu Anhu face ya fifita ko kevance danginsa makusanta da wani abu na muqami ko dukiya. Kamar yadda ta tabbata Ali Raliyallahu Anhu ya kama da makusantarsa.

Shi kuwa zancen shan giyar da Walidi yayi bayan naxa shi, kamata yayi ta zama abun yabo ga Usman Raliyallahu Anhu ba suka ba. Domin ya zartar masa da hukuncin Allah. Kamar yadda muka faxa a baya. Kuma Ali Raliyallahu Anhu ne sheda. Don halifan ya umurta da bulala hamsin. Shi kuma ya umurci Hassan a cikin. Da Hassan ya kasa, sai ya umurci Abdulllahi xan Ja’afar. Wanda ya tashi yayi ta zabga wa Walidu bulala baji ba gani. Yana daga kannunsa daga ta azba’in sai Ali Raliyallahu Anhu ya ce masa: ya isa haka nan. Su Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Sahabi Abubakar Raliyallahu Anhu suka yi wa mashayin giya. Amma Umar Raliyallahu Anhu har tamanin yayi. Kuma kowanensu sunna ne. Amma dai ni nafi gamsuwa da arba’in.

Muslim da waninsa duk sun riwaito wannan hadisi.

Ka ga a hankalce da shar’arce halifan ne ya zartar da hukuncin, ba Ali Raliyallahu Anhu ba tunda shiya bashi umurni.

Sannan kuma xan Shi’ar ya ce wai mutanen Kufa har sai da suka kori Sa’id xan Asi gwamnan da Usman Raliyallahu Anhu ya tura masu, saboda mugun halinsa.

To ka ga wannan magana, tana tabbatar maka da cewa xan Shi’ar nan xan soke ne a kasuwar karatu.

Eh mana! Xan soke ne. domin kuwa fitinar mutane Kufa sananna ce. Korar da suka yi wa wannan gwamna, bata tabbatar da cewa ya yi wani abu da zai cancantar masa da haka. Halinsu ne duk gwamnan aka tura masu haka suke yi masa, sun yi wa Sa’ad xan Abu Wakkas tawaye. Wanda shi ne yaci garin da yaqi, ya karya lagon rundunonin qasar. Yana kuma daga cikin majalisar shawara. Kuma basu tava samun gwamna irinsa ba. Haka kuma sun yi ta qorafi a kan Amru xan Yasir da shi Sa’ad xin da Mugirata xan Shu’ubata da sauran gwamnonin da aka aika masu. Harma da abin yayi yawa, saida Umar xan Khaxxabi ya yi masu mugunyar addu’a da cewa: ya Ubangiji ka dagula lissafin mutanen Kufa yadda suka dagula mani lissafi.

To kuma, mu qaddara cewa wannan gwamna ya aikata zunubin da zai sa mutanen Kufa su kore shi. To meye laifin halifa Usmanu Raliyallahu Anhu a nan. Ai ko daga cikin waqilan Ali Raliyallahu Anhu har ma dana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama an samu da yawa, waxanda suka aikata ayyuka na zunubi. Abin da zai sa a kalli shugaba a matsayin mai laifi a wannan hauji, shi ne, idan ya kasa gurfanar da irin waxannan mutane a gabansa, balle ya hukun tasu. Ko ya kasa kwatowa wani haqqinsa, ko wani abu mai kama da wannan, daga ma’aikatansa.

In ma har dai akwai wani laifi a nan, daya hau kan halifa Usmanu Raliyallahu Anhu mun riga mun baje shi. Balle ma babu shi.

Haka kuma idan baka manta ba. Xan Shi’ar ya ce wai, gwamnan da Usmanu Raliyallahu Anhu ya tura Masar, wato Abdullahi xan Sa’ad xan Abu Sarhu, ya shakewa mutanen qasar zaiti, har sai da suka kai qarar zaluncin da yake masu ga halifan. Amma maimakon ya kwatar masu haqqinsu, sai ma ya qara xaure mashi gindi. Ta hanyar rubuta masa takarda a asirce a kan Ya ci gaba da aikinsa yadda ya saba. Alhali kuwa yaja kunnensa a rubuce bainar jama’a.

To mu ba duk mai hankalin daya dubi wannan magana ya san qarya ce aka yi wa Usman Raliyallahu Anhu kuma da aka zarge shi da haka, saida ya sha billahil - lazi a kan bai ji bai gani ba. Kuma kasan a qa’ida duk abin da ya faxi gaskiya ne, ko bai rantse ba. Iyakar abin da ya tabbata dai shi ne, magatakardarsa Marwanu xan Hakamu ne ya rubuta wannan takarda ta biyu, bada saninsa ba. Su kuwa Misirawa, suka ce: to in gaskiya ne ya ba su Marwanun su kashe. Shi kuwa ya ce: atafau.

To ka ga kashe Marwanu a matsayinsa na kawai wanda ya yi sojan gona bai halatta baza shari’an ce, bai cancanci kisa ba. Kenan qin bayar dashi da halifan yayi dai – dai ne. Kai! Wajibi mane. idan kuwa akwai wani tawili da zai halatta kashe shi, ba wajabtawa ba… to shima qin bayar dashi xin halas ne. babu kuwa wani dalili da zai wajabta kashe shi, in ba ijtihadi ba.

To tafi ma, mu qaddara cewa halifan ya hana a tabbatar da wani abu daya wajabta. Ai idan baka manta ba kuma shi halifan ga vatacce ne a wurin Allah tabbas.

To sai me kuma?

Wata shahararrar qarya kuma da xan Shi’ar ya tafka a cikin wannan magana, itace cewa da ya yi wai halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ya yi umurni da kashe Muhammad xan Abubakar. Ka ji kai.

Wannan magana ko shakka babu qarya ce. Domin kuwa duk wanda ya san Usman da irin dattako da adalcin daya shahara dashiya ba zai yi horo da irin wannan aiko kan wani ma, ba Muhammad ba. Kai ba a tava jin yayi irin wannan aika- aika ba.

To tafi ma halifan ya ce a kashe shi. A matsayin Usman Raliyallahu Anhu na nagartaccen shugaba, yana da damar yin haka. Don wajibi ne a kansa, yakare mutuncin talakawansa. Ta hanyar kashe duk wanda, ba a iya hutawa daga fitinarsa sai ta haka. Kuma wannan ba abin suka bane. kuma shi yafi cancanta da a yi wa xa’a idan yayi horo da hakan ba waxanda suka so kashe mansuranu ba. A matsayinsu na ‘yan tawaye. Kuma mavarnata, waxanda ba suda ikon kashe kowa, ko zartarwa kowa da hukunci. Waxanda kuma iyakar hujjarsu ita ce, an zalunci tane, keda haqqin haninta wanda ya zalunce shi ba. Balle har ya kashe shi daxa.

Ko shakka babu Muhammadun nan da kake ji, ya dace da kisa sosai, savanin maroranu. Don fitina da sharri da matsalolin da koyaurshe a gindinsa babusu a na muh’d. Kuma irin shaharar da Marwanu yayi a fagen ilimi da kishen addini shi bayyi taba. tunda har hadisai da dama ke akwai a cikin shihalu na Marwanun. Kuma ma har fatawa malamia kan yi da wasu maganganunsa. Wasu ma na jin yayi tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Qarya ta farko a wannan magana, itace cewa halifa Usman ne Raliyallahu Anhu ya kai Mu’awiyah sham bayan rasuwar xan’uwansa Yazidu xan Abu Sufyanu. Wanda ke gwamna a qasar. Shi kuwa halifa Usmanu Raliyallahu Anhu da yazo, sai ya barshi a sham xin a matsayinsa na gwamna. Kuma Mu’awiyah yayi abun a zo a gani, a wannan qasa ta sham. Don tarihin rayuwarsa ya tabbatar da cewa yana daga cikin gwamnonin da talakawansu ke matuqar godewa, da tsananin so.

A gaida sarkin sarakuna xan Abu Sufyanu. Baban Yazidu hafizin qur’ani.

Ta tabbata a cikin ingantaccen hadisi cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: zavavvu daga cikin shuga banninku, sune waxanda kuke so, suke kuma son ku. Kuma kuna yi masu addu’ar alheri suma suna yi maku. Kuma mafi sharrinsu, sune waxanda kuke qi suna kuma qinku. Kuna la’antar su, su ma suna la’antar ku.

Duk abin da za ka ji ance Mu’awiyah yayi, to ya faru ne bayan kisan gillar da aka yi wa halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ita kuwa wannan fitina ruwan dare ce game duniya, ba shi kaxai ta shafa ba. Hasali ma Mu’awiyah shi mafi neman salama da zaman lafiya, fiye da sauran waxanda abun ya shafa. Don baka haxa shi da Ashtar An-nakha’I ko Muhammadu xan Abubakar ko Abdullahi xan Umar xan Khaxxabi ko Abul-a’awar as-sulami, ko Hashim xan Hashim al-Murkali, ko Ash’asu xan kasu al-qiniki, ko Busru xan Abu Azda’ata da wasunsu daga cikin magoya bayansa da magoya bayan Ali Raliyallahu Anhu duk yafi dama sosai.

Haka kuma xan Shi’ar ya ce, halifa Usman ya kai Abdullahi xan Amir Basra, inda gwamnan ya aikata miyagun abubuwa yadda yaso.

Martani:

Duk abin da wannan gwamna ya aikata na zunubi, ai yana kansa. Mi ya gano halifa Usmanu Raliyallahu Anhu? tunda babu wanda ya ce ya yarda da ayyukan Abdullahi. Kuma tattare da hakan rayuwar gwamnan cike take da kyawawan ayyuka, waxanda suka sa mutane na matuqar sonsa iyakar zarafi.

Haka kuma xan Shi’ar ya soki lamirin halifan da naxa Marwanu da ya yi, tare da xauko masa wuqa da nama, a sha’anin mulki. Har ya daka masa hatiminsa. Wanda wai a qarshe hakan ta zama sanadiyar kashe shi halifan. Tare da jefa al’umma cikin fitina.

Martani:

Marwanu, shi kaxai, ba shi ne sanadin kashe halifan ba. Abubuwa ne da dama suka haxu. Waxanda suka haxa da qorafe-qorafen da ake yi kan shi Marwanun, da kuma kasan cewar halifan ya sha ruwa sosai shekaru sun miqa. Wanda hakan taba su gwamnonin damar yin wasu abubuwa ba tare da saninsa ba musamman waxanda ake qorafi a kansu amma sanda yawa yake ba Marwanun umurnin canzawa wasu daga cikinsu wuraren aiki ko tuve ma wasu. Shi kuma wani lokaci ya zartar. Wani lokcin kuma ya doje. Mun riga mun fexe buru’I wannan magana har wutsiya.

Sannan kuma wani abu da zai qara tabbatar maka da cewa cin amanar Usman Raliyallahu Anhu aka yi har aka kashe shi, shi ne, yayin da ‘yan inna da suke qorafi a kansa, saida ya wayar masu da kai a kai. Kai! Har saima da a qarshe, ya yarda da zai tuve duk wanda ba su so . kuma zai danqa mabuxan Baitul’mali hannun wanda suke so. Ya kuma tabbata masu cewa babu kwabo xaya daya tava xauka daga Baitil malin yaba wani, face ya nemi yarda da shawarar sauran Sahabbai. Kai har dai suka yi kwatakyas. Hakan tasa Sayyida Aisha Raliyallahu Anha cewa: basu kashe shi ba saida suka matseshi kamar yadda ake matse tufa, suka raba shi da komai.

Allah ya isa!

Iyakar abin da ake cewa shi ne wai, sun kama wata takarda ne, a kan hanya dasa hannun halifan, inda a ciki wai ya yi umurni da a kashe su. A qarshe kuma halifan ya rantse masu da Allah a kan cewa baida masaniya da wannan takarda. Suka ce to, lalle ko maruranu ne ya rubutata. Saboda haka lalle abasu shi su kashe. Shi kuwa halifan, ya ce, atafau.

Wai a kan haka ne suka kashe shi.

To, mu qaddara cewa wannan labari gaskiya ne, marwanu ya rubuta takardar, kuma halifan yaqi bayar da Shi a kashe. To,ai wannan bai isa halatta jininsa ba, balle a kashe haka kaddan. Don ko shi Marwanun zunubinsa kawai na shirya a kashe sune, in har ta tabbata ya yi hakan, amma ai gurin nasa bai cika ba, balle. Niyar kashe mutum ba tare da wanzarwa ba, bata wajabta kashe mai ita. Ka ga kenan ko Marwanun bai cancanci kisa ba balle halifan.

Amma, eh! Gaskiya ne irin wannan ya kamata a ladabta shi, a kore shi, a kuma yi kaffa - kaffa dashi. Ko wani abu mai kama da haka. Amma a ce a kashe shi, wala.

Haka kuma xan Shi’ar ya soki lamirin halifa Usmanu Raliyallahu Anhu da cewa yana kwasar dukiyar Baitul-mali yana ba danginsa da makusantansa. Wai akwai ma lokacin da yaba wasu Quraishawa dake auren ‘ya’yansa mata dinari dubu.

Martani:

Ina xan Shi’ar ya samo wannan magana? Ba muna musun irin kyautar da halifan ya shahara da ita ne ba. Domin kuwa ko tauraruwar sarfa ta sanda zamansa. Gaskiya ne halifa Usmanu Raliyallahu Anhu na cikawa makusantansa aljifansu. Amma kuma da kowa yake, shi ba indararo bane, kaba daji ruwa gida bai sha ba. A’a shi a duk lokacin daya ba Albasa ruwa sai ya ba yalo. A’a ba musu muke ba. Wannan adadi da xan Shi’ar ya faxa, shi muke son mu ji maqaryacin malamin daya gaya masa shi.

Wannan magana ko shakka babu qarya ce. Ba Usmanu Raliyallahu Anhu ba, babu wani halifa daga cikin shiryayyun halifofin Manzo, daya tava kyautar irin wannan maqodan kuxi. Halifa Mu’awiyah shi ne tarihi ya tabbatar da cewa ya bi sawun halifa Usmanu a fagen kyauta. Toko shi iyakar adadin abin da aka riwaito, daya kan ba waxanda yake lallashi don su bi shi bai tava wuce dirhami dubu xari ko dubu xari uku ba. Kamar yadda ya tava ba Hassan xan Ali Raliyallahu Anhu an kuma riwaito cewa ma Hassan xin kawai ne ya tava dacewa da irin wannan babbar riba. Wasu malama na jinma Mu’awiyah ya sha gaban Usmanu Raliyallahu Anhu a irin wannan kyauta ta lallashi.

Eh! Gaskiya ne halifa Usman Raliyallahu Anhu na irin wannan kyautawa makusantansa, wadda har taja masa fitinu. Amma kuma mun riga mun kawo hojjojunsa a kan haka. Za mu kuma qara warware matsalar nan gaba kaxan.

To kuma duk aje ma wannan. A taqaice dole ne kowane shugaba ya gyara tsakaninsa da wasu mutane, don su ji daxin bashi kariya daga duk wanda ke son cuta masa. Musamman idan bai sami irin yadda Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma suka samu ba, na kasancewar talakawansu tare dasu fai da voye.

Wannan shi ne uzuri na farko daya kamata a yi wa halifa Usmanu Raliyallahu Anhu idan ana yi wa Allah.

Uzuri na biyu kuma da ake iya yi wa halifan shi ne: a matsayinsa na ma’aikacin gwamnatin musulunci, kuma wanda ke hidimar dukiyarta,to yana da haqqi na musamman a ciki. Don cewa Allah Ta’ala yayi: da masu aiki a kansu (9:60) a kan wannan dalili ne gaba xayan musulmi suka yi ittifaqi a kan cewa komi wadatar wanda ke hidimar irin wannan dukiya, to yana da haqqi a cikinta. Kuma ba laifi bane don ya karve shi.

Haka kuma xan Shi’ar ya ce wai: xan Mas’ud na ganin la’anin halifa Usman Raliyallahu Anhu saboda irin waxannan xabi’u nasa, harma yana kafirta shi.

To duk mai hankali da ilimi yasan wannan magana qarya aka yi wa xan Mas’ud babu wani malami daga cikin malamai manaqalta sirrin riwaya daya tava riwaito irin wannan magana. Hasali ma, abin da suka riwaito xan Mas’ud xin na cewa, a lokacin da aka naxa halifa Usmanun Raliyallahu Anhu shi ne: mun naxa mafi girman daraja. Bamu bayar ba.

Wani kuma abin da ke qara tabbatar da kasancewar wannan magana ta xan Shi’ar qarya, shi ne, kasancewar shekarun farko na halifancin Usman Raliyallahu Anhu babu wanda aka ji yana sukar lamuransa a cikinsu. Sai da aka kai ga kashin qarshe na shekarun, sannan aka fara jin qorafe -qorafe a kansa dangane da wasu abubuwa, da masu qorafe -qorafen keda uzuri a cikin wasu daga cikisu. A yayin da kuwa halifan ne keda uzuri a cikin mafi yawansu.

Wannan qorafi da xan Shi’ar ke son mayar wa wani abu, wanda xan Mas’ud keyi a kan halifa Usmanu, na daga cikin waxannan qorafe - qorafe. Abin da ya faru kuwa shi ne xan Mas’ud ya daxe yana hushi da halifan, saboda danqa aikin sake rubuta Alqur’ani da ya yi ga Yazidu, maimakon ya danqa masa. Bayan haka kuma ya umurci Sahabbai da shafe nasu Qur’anan, su bar aiki dasu, su dawo ga wanga da Yazidu ya rubuta daga baya. Kuma sai mafi yawan Sahabbai suka goyi bayan halifan: suka bar xan Mas’ud. Ka ji iyakar abin da ya faru. Amma zancen kafirtawa, bamu da wannan labari: kai, babu shi sam.

To kuma idan dai har ana son gaskiya, zancen halifan shi ne abun xauka. Bana xan Mas’ud ko Amru ko Abu Zarri ba, ko waninsu. Don babu wanda darajarsa daga cikinsu ta kai ta Usman Raliyallahu Anhu kamar yadda dalilai da dama suka tabbatar.

Wannan ta vangaren su kenan. To vangaren kuwa wanda abin bai shafa ba. Amatsayinsa na xan kallo, kamata yayi ya fahimci, halifa ne ya kamata ace yana fushi da xan Mas’ud, ba shi yayi da shi ba. Amma saboda dattakonsa bai yiba, balle a riwaito. Ko kuma idan ya tashi bayar da labarin mas’ala, ya tsetsefeta, tsetstsefewa irin ta masu ilimi da adalci. Idan kuwa matsayinsa bai kai na haka ba, to ya tsaya ga faxar darajojinsu da kishen addininsu, ya fita batun yin alqalanci tsakaninsu. Don yayi kaxan. Sauran abin da ya gudana tsakaninsu na yaya da ja-in-ja, kuma, ya barwa Allah sani.

Kuma bisa wannan dalili nema, malamai su kayi umurci musulmi dasa ido kawai, da kame baki daga duk abin da ya gudana a tsakanin Sahabbai. Domin kuwa Allah ba zai tambaye mu a kan al’amarin ba.

Kuma a qoqarin qarfafa wannan mataki na kame baki ne, Umar xan Abdul’aziz ke cewa: tunda Allah ya sabani da hannu cikin zubar da wadancan jinane na musulmi, toba kuwa zan tsoma halshena cikinsu ba.

Wani magabancin kuma abin da yake cewa shi ne, abin da Allah Ta’ala ya ce: waccan, wata al’umma ce,ta riga ta shige, tana da abin da ta sana’anta, kuma juna da abin da kuka sana’anta. Kuma baza a tambaye kuba daga abin da suka kasance suna aikatawa(2:134).

Amma kuma ka sani, haka ba zata hana, idan wani xan bidi’a ya tsiru yana sukar lamirin wadancan magabata, da abin da basu jiba basu gani ba, a tashi a yaqe shi, ta hanyar amfani da ilimi da adalci, har a karya lagonsa.

Haka nan kuma abin da xan Shi’ar ya ce, wai Amru ya ce: Usmanu Raliyallahu Anhu ya kafirta, kafirci mabayyani. Har kuma Hassan xan Ali Raliyallahu Anhu ya kwave shi. A qarshe kuma wai Alin Raliyallahu Anhu ya cewa Amrun “ sai dai idan kaine ka kafirce wa Ubangijin da Usman Raliyallahu Anhu ya yiimani dashi.

Duk waxannan maganganu, qarairayi ne, da basu tava faruwa ba a tarihin musulunci.

Wannan kenan. Haka kuma cewar da ya yi wai, hawan Usmanu Raliyallahu Anhu keda wuya sai yasa aka yi wa xan Mas’ud dukan tsiya har ransa ya fita. Wannan magana qarya ce bai sa ittifaqin ma’abuta ilimi.

Babu abin da ke tsakanin halifa Usmanu da xan Mas’ud Raliyallahu Anhu sai alheri. Domin haka ne ma a lokacin da Usmanun Raliyallahu Anhu ya zama halifa, bai xauke shi daga Kufa ba, inda yake, har sai da hukuncin Allah ya gudana kansa. Amma ba Usmanu ne Raliyallahu Anhu ya kashe shi da duka ba.

To kuma ko da ta tabbata cewa halifan yasa an yi wa xan Mas’udun dama Amru dukan, wannan ba zai zama abin suka gare suba, har shi halifan. Domin dukansu ‘yan aljanna ne tun duniya. Mun kuma shedi haka. Kuma suna daga cikin manya -manyan waliyan Allah masu taqawa.

Kuma ko bayan haka, mun riga mun yi bayanin cewa abu ne mai sauqi sosai waliyen Allah ya aikata laifin da zai cancantar masa da wata azaba ta shari’a, balle gargaxi (ta’azur).

Tomu dawo ga zancen Ammru. Wanda xan Shi’ar ya ce wai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce shi wata fata ne daga cikin fatun idonsa Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma yake jin wasu la’ananu ‘yan tawaye za su kashe. Waxanda ke fatar Allah ba zai sasu cikin jirgin cetonsa ba a ranar qiyama.

Ina son ka xan kalli wannan magan da kyau.

Iyakar abin da ya inganta daga cikinta shi ne, cewa Annabi ya ce: Ina jin wasu la’anannu ne ’yan tawaye za su kashe shi to kuma ko ita wannan kalma wasu malamai sun raunana ta, a matsayin hadisi. Daga cikin malaman kuwa akwai: al-Husaini al-Karabisi da wasunsu. An kuma riwaito imamu Ahmad shima ya raunana hadisin. Ka ga da sakal kenan.

Sauran abin da kuma ba wannan magana ba, a cikin hadisin, duk qarya ce, karanta aka yi a matsayin toliyar zamba. Babu wani malami daga cikin malamai masana isnadi da ya riwaito ta.

To kuma majata ta tabbata Manzon ya faxi duk tarkacen da xan Shi’ar ya faxa. Hakan ba zata daxa Ammarun da komai ba. Balle ta hana a hukunta shi, idan ya yi wani laifi.

Dubi matsayin da nana Fatima keda shi a wurin mahaifinta Sallallahu Alaihi Wasallama. Wanda harta tabbata a cikin ingantaccen hadisi cewa ya ce: ko shakka babu Fatima jinina ce. Duk abin da ya tava ta ya tava ni.

Amma kuma tattare da ha kan manzon ya tabbatar wa duniya, a cikin wani ingantaccen hadisi, da cewa: da Fatima ‘yar Muhammadu zata yi sata wallahi sai na yanke hannunta.

Haka kuma ta tabbata Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na matuqar son Usamatu, wanda har ya ce a wani ingantaccen hadisi: ya Ubangiji kasan inason Usamatu. Saboda haka ya Allah kaso shi. Ka kuma so duk wanda ke sonsa.

Amma kuma tattare da haka Manzon yayi matsananci hushi tare da kakkausan kashedi gare shi, a lokacin daya dahe wani mutum bayan ya furta kalmar shahada. Ya ce masa: ya kai Usamatu! Ya zaka kashe shi bayan ya ce: la’ilaha illal-lah?

Usamatu ya ce: haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya riqa maganar nan yana ta konkoma ta a kaina, har saida naji ina ma dai a ce sai a ranar ne na musulunta!.

To haka abin yake, babu wanda halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ya zartar wa wani haddi ko gargadi bisa jahilci ko zalunci. kuma shi yafi cancanta da a yi masa uzuri, a kuma bashi kariya.

a cikin waxannan masallolin bias ga Ali Raliyallahu Anhu

Bayan wannan kuma xan Shi’ar ya soki lamirin halifa Usmanu Raliyallahu Anhu da cewa wai, ya dawo da Hakamu xan Abdul-Abi a wurinsa, da xansa Marwanu a garin Madina. Bayan manzo Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya koresu tsawon rayuwansa. Kuma halifa Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma suka qi maikar dasu, sai shi. Har ma ya naxa Marwanu a matsayin magatakardansa. Alhali kuwa Allah Ta’ala ya ce: Ba zaka sam mutane masu yin imani da Allah da ranar Lahira suna soyaya da wanda ya savawa Allah da Manzonsa (58:22).

Wannan magana ko kaxan babu qanshin gaskiya a cikinta. Domin dai Hakan xin nan xan Abi, na xaya daga cikin mutane dubu da suka Musulunta ne, ranar da aka ci garin da yaqi. Kaji wanan ko? Sannan shi kuma Marwanu, xansa, shekarunsa a lokacin basu wuce bakwai ko aqalla ko akasansa ba da kaxan. Ka ga yazo ne matuqa. Wanda ba wani zunubi kansa da zai sa har Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kore shi a kauran kanoli. Kuma a wannan lokaci ba a ba fursunoni yaqin da aka sallama damar zama cikin garin Madina, balle ace an kore Hakim daga cikinta. In har korace, sai dai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, ya kore shi daga Makka ba Madina ba. Idan kuwa har kaddarata sa aka bashi damar zama Madina. Kuma kora tazo, to sai dai a kora shi zuwa Makka. Amma da mafi yawan ma’abuta ilimi babu yarda da koransa akayi. Abin da suka ce dai ya tafi ne a ra’ain kansa.

Ka ga dawowa da shi bisa wannan lokaci ba lafi bane.

Sannan shi kuma Marwanu mun riga mun gaya muku cewa yaro ne qarami a wannan lokacin ko da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu Marwanu bai balaga ba, bisa litaffin ma’abuta cikin qololuwan shekarunsa a wannan lokacin ba sufi goma ba to ya za’ace Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kori shi wannan lokaci.

To a kan me?

Kuma tarihi ya tabbatar da cewa qoriya da samartakar Marwanu duk na musulunci ne bai da voye; mutun ne mai yawan karatun al-qurani da neman ilimi fiqihun addini. Haka rayuwarsa ta xore a kan nagarta har lokacin da fitinoni suka kuma kai. To don Allah meye laifin wanda ya haxamu na wannan matsayin magatakardarsa?

Wani abin la’akari kuma shi ne ko da wannan fitina ta faru, ba a kan Marwanu kawai ta tsaya ba; tabi ta kan har waxannda suka fi shi daraja. Kuma baya cikin waxanda suka savawa Allah da Manzonsa. Shi kuma Mahaifinsa yana daga cikin fursunoni da aka saka masa in gantacen imani. Wasu kuwa abin nasu gashi nan dai. Duk kuwa zunubin da ake yi wa mai shita’aziri, ba wajabta kasancenwarsa munafiki a voye.

Haka kuma idan baka manta ba xan Shi’ar ya ce wai halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ne ya kori Abu Zarri zuwa Rabzah, bayan ya yi masa dukan tsiya. Alhali kuwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce shi ne mafi gaskiyar zance a duniya. Kuma Allah ya yi wa Manzon wahayi da cewa yana son wasu Sahabbansa guda huxu, kuma yana horonsa dashi ma yaso su. Kuma na qarshen waxannan Sahabbai shi ne Abu Zarri.

Allah da iko shike. Kai ka ji wannan tsari.

To mu dai iyakar abin da muka sani, kuma wanda za mu mayarwa ‘yan shi’an nan martani dashi, shi ne: Abu Zarri shi ne a qashin kansa ya bar birnin Madina ya koma Rabza. Saboda rikittan dake faruwa tsakaninsa da mutane. Sakamakon qoqrin da yake yi na tilasta masu zama zahidai. Shi mutum ne salihi mai zuhudu. Wanda kuma ke jin zuhudu wajibi ne. kuma duk abin da mutum ya rage hannunsa bayan buqatarsa ta yini ta biya. Allah zai yi masa azaba dashi gobe qiyama. Harma da Allah ya karvi na Abdulrahamu xan Aufu. Aka samu ya bar dukiya. Sai Abu Zarri ya yanke hukunci cewa Allah zai yi masa lalas da ita gobe qiyama a wuta. To ashe kai ka je.

To kuma da yawa halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ke qoqarin ganar da Abu Zarri, ta hanyar ilimi cewa al’amani ta ba haka ba. A haka har watarana ka’abu ya tsoma baki ya kuma goyi bayan lafiya, har Abu Zarri xin ya kai masa duka. Kuma wani abu mai kama da haka ya tava faruwa tsakaninsa da Mu’awiyah a kan haka a sham.

Sannan kuma wannan ra’ayi na Abu Zarri ya savawa abin da gaba xayan halifofi shanyayyu da sauran Sahabbai da tabi’ai suke a kai.

To kuma uwa uba ya savawa abin da ingantattar sunnar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta tabbatar. Kamar inda Manzon ke cewa: babu zakka a cikkin abin da ba kai auziqi ko zandi ko awaki biyar ba.

Ka ga a nan Manzon ya tabattar da halarcin aje abin da bai kai xayan biyu ba, ba kuma tare da an fitar masa da zakka ba. Kuma ko da mai shi baya da buqata dashi. ai buqatar ba sharaxi bace a nan.

Bayan wannan kuma jumhuran Sahabbai sai suka fasara waccan kalmar ta “kanzin” dukiyar dake jawo azabar Allah gobe qiyama ga mai ita, da cewa itace. Dukiyar da ba a fitar da haqqin Allah daga cikinta. Komai yawan ta ko qanqancita.

Ka ga kenan Abu Zarri ya jefa kansa a wannan lokaci, a cikin matsalar son wajabta wa mutane abin da Allah bai wajabta masu ba. Ya kuma ga laifin mu a kan abin da Allah bai ga yayi ijtihadinsa ne. kuma Allah zai bashi lada a kai, kamar yadda zai bayar ga takwarorinsa ijtahidai.

To a kan wannan dalili ne Abu Zarri ya ga bari ya batse kansa, ya koma Rabza. Ba don Usmanu Raliyallahu Anhu nada wani mugun nufi a kansa sannan kuma maganar kasancewar Abu Zarri xin alfahari ne ba. Kuma hakan bata nuna cewa darajarsa ta fita kowa. Hasali ma, a ingantacen hadisi, shi mumini ne mai rauni kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbatar, inda ya ce: ya kai Abu Zarri! Na riga na gane kai mutum ne mai rauni. Duk da yake kuma ina so maka abin da nake sowa kaina. Amma ina ganin bai kamata a shugabantar da kai ko da a kan mutum biyu ba. Ko a baka dukiyar maraya.

Wani hadisin kuma dake qara walwale wannan, tare da fitowa da matsayin Abu Zarri na haqiqa, savanin wancan da xan Shi’ar ke son qaraba mana shi ne, cewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wani igantacen hadisi: mumini mai kaza da kaza shi ne mafi alheri da soyuwa a wurin Allah, bisa ga mumini raunana. Amma kuma akwai alheri aikin kowanensu.

To ka ga idan haxa hancin waxannan hadisai biyu wuri xaya, sai kace: muminai ‘yan majalisar shura, irinsu Usmanu da Ali da Abdurahama xan Aufu, waxanda suka cancanji zama halifofi da sonransu, shi ne muminai kafata kuma masu kazar - kazar. Shi kuma Abu Zarri da takwarorinsa, masu cikin hali da halittarsa sune raunana. Kenan waxannan sunfi shi falala.

Shi kuwa wannan hadisi, a cikin wannan lafazi da xan Shi’ar ya kawo, hadisi ne mai rauni. Kai! Qagagge ma, don babu wani isnadi da zai iya xaga darajarsa.

Ka ji wannan!

To yanzu kuma mu dawo ga cewar da ya yi wai halifa Usmanu ya keta alfarmar shari’ar Allah, tunda bai kashe Ubaidullahi xan Umar ba, wanda ya kashe Hurmuzanu, bawan Ali Raliyallahu Anhu bayan kuma ya musulunta. Kuma wai saboda haka Alin (Sarkin Musulmi) yayi tsaye a kan shi ko sai ya zartar wa Ubaidullahi da hukuncin Allah. Amma wai a qarshe Mu’awiyah ya bashi mafaka.

Sannan kuma wai, inji xan Shi’ar, halifa Usmanu Raliyallahu Anhu yaso yayi ko oho da hukuncin shan giya. Wanda ya hau kan Walidu xan Uqbata. Sai da Ali Raliyallahu Anhu ya xaukarwa abin matakin soja; ya zartar da hukuncin a kansa, ya kuma rufe caftar da cewa: Ai ba ta yiwuwa a tozartar da hukuncin Allah ina raye.

Martani:

Wannan magana ko shakka babu bakar qarya ce. Domin kuwa ba haka kawai halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ya ki kashe Ubaidullahi makashin hurmuzanu ba. Akwai dalili a kan haka, da kuma hujja karvabba. Bari ka ji yadda al’amrin ya kasance. Wanda na yi imani da Allah, ba ni ba, ko kai za ka yi wa halifa Uzuri.

Abu na farko da ya kamata ka sani shi ne: shi dai Hurmuzanun nan, xaya ne daga cikin Farisawa da Kisra ya waqilta su yaqi musulmi. A qarshe Allah ya nufi aka kama shi a matsayin fursunan yaqi. Da aka zo dashi gaban zakin halifofi Umar xan khaxxabi sai ya musulunta. Halifan ya ce: mun karvi musuluncinka, mun kuma ‘yanta ka. Kana ji da kyau ko?

To a lokacin da bamajushen nan, Abu lu’ulu’ata bawan Mugirata xan Shu’ubata ya yi wa halifa Umar Raliyallahu Anhu kisan gilla. Musulmi suka zurfafa bincike, sai aka gano cewa akwai abota mai kauri tsakaninsa da hurmuzanu. Harma an gansu, suna kus-kus-kus kafin kashe halifan. Aka kuma tabbatarwa Ubaidullahi xin da haka. A haka sai Hurmuzanu ya zama babban wanda ake tuhuma da hannu a cikin kisan halifan.

Wannan tuhuma ta kara qarfi matuqa, da aka yi la’akari da labarin da Abdullahi xan Abbas ya bayar cewa, kafin shexar Umar ta fita Raliyallahu Anhu ya ce masa: Ai ga irinta nan. Kai da mahaifinka kun fi kowa son a sakarwa illiyin Farisa mara sa cika birnin Madina.

Jin haka sai Abdullahi xan Abbas xin ya cewa halifan: To in ka yarda yau muna aika gaba xayan su lahira. Umar ya ce: Ai bata yiwuwa tunda har an wayi gari sun ari harshen ku sun kuma shiga addinin ku.

To ina son kaxan dubi wannan magana da kyau. Ka ga idan dai har xan abbas, a matsayinsa wanda ya yi wa Abdullahi xan Umar fintinqau a fagen sanin makamar addini da kishinsa. Ya kuma fi shi martaba, zai nemi iznin yi wa gaba xayan illiyin Farisa dake Madina kisan qare dangi, saboda kawai ana tuhumarsu da fasadi. Me zai hana Ubaidullahi sakankancewa da hallaccin kashe Hurmuzanu a kan abin da ya aikata? Babu.

Bayan da aka gama tabbatar da hannun Hurmuzanu a cikin aika -aikar, sai halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ya shawarci mutane a kan dacewar yin layya dashi. Sai wasu Sahabbai suka ce, hakan bai dace ba

a halin yanzu. Saboda jiya - jiya ne aka aika mahaifinsa lahira. Idan shi kuma aka aika shi yau, to hakan na iya zama abun faxi ga musulmi.

Ka ga kenan a taqaice, kamar wata shubha ta kama zuqatan waxannan Sahabbai, har suke jin jinen Hurmuzanu bai gama halatta ba, takwana. Wato rasa gane matsayinsa tunda tuhuma ce ake masa; shin yana kawai cikin ‘yan hadin baki waxanda jininsu baya halatta, koko cikin ‘yan damu aka yi, waxanda suka cancanci kisa?

Ka ji bilinbiton da waxannan Sahabbai suka sami kansu a ciki. Amma dai sauran mafi yawansu sai suka tafi kan cewa jininsa ya halatta. Domin wannan kisan ‘gilla da aka yi wa halifa Umar Raliyallahu Anhu duk malamai sun sakasu a cikin babin tawaye. A qa’ida ko da ‘yan hadin baki da ‘yan damu akayi, a wannan babi duk hukuncinsu xaya.

A kan haka duk wanda ya taimaka, ko da da magana ne, a cikin wannan kisa da aka yi wa halifa Umar Raliyallahu Anhu to a wurin waxannan Sahabbai (jumhuru) wajibi ne ya baqunci lahira. Ta kuma tabbata cewa hadin baki a cikin kisan halifan. (Umar Raliyallahu Anhu)

To ka ga a haka kisan Hurmuzanu ya wajaba illa dai shugabanin jama’a ne keda haqqin zartar masa da hukuncin. Sai Ubaidullahi yayi azarbabi ya riga malam masallaci ya gama dashi. Amma kuma duk da haka halifan nada cikakkar dama ta yafewa wanda ya riga sarkin yankansa ga mai laifi.

Ka ji yadda al’amarin ya faru a haqiqa.

Bayan wannan sai kuma xan Shi’ar ya ce wai sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya xaura niyar kashe ubaidullahi saboda kashe Hurmuzanun da ya yi.

To ka ga wannan magana, ko da ta inganta, bai kamata ‘yan Shi’ah su buga taba, da suna da hankali. Domin zata fito da gwarzon nasu ne (Ali Raliyallahu Anhu a matsayin wanda bai san makamar addini ba (fikhu) Dama haka halinsu yake; sawa zagi rigar yabo.

To kuma ma wai, ina suka samo cewar Alin Raliyallahu Anhu yayi niyar kashe Ubaidullahi, koma har ya kashe shi? Yaushe Aliyu Raliyallahu Anhu ya samu wannan faraga? Wanda bai fita ruwa bana matsar ragga?

Kuma ya za a yima Ali Raliyallahu Anhu ya iya kashe Ubaidullahi a matsayinsa na wanda ya sami goyon bayan dubban musulmi harma da Mu’awiyah. Wadanda kuma ke jin Ubaidullahi ya cancanci kowace irin kariya a matsayin mayar da hannun baiwa ga wanda ya miqo shi. Kuma kasawar da Alin Raliyallahu Anhu ya yita tunvuke Mu’awiyah kawai, ta tabbatar da cewa ba kofar da zai iya bi balle ya isa ga Ubaidullahi balle ya kashe shi. Bama zai fara wannan tunani ba.

Kuma wani abin mamaki, da zai tabbatar maka da cewa ‘yan Shi’ah na qaryar kare hukuncin Allah Sallallahu Alaihi Wasallama suke yi shi ne yin kunnen uwar shege da suka yi da maganar jinin halifa Usmanu Raliyallahu Anhu tare da halatta shi. Tattare da kasancewarsa jagoran musulmi (Imamu) kuma wanda aka yi wa bushara da aljanna. Wanda kuma shi da danginsa su ne mafifitan halitta bayan Annabawa.’yan Shi’ah suka xauki kashe sa da aka yi kamar an kashe kare. Amma sai gashi suna qoqarin kifar da duniya a kan kawai an kashe Hurmuzanu. Kuma a matsayin wanda ake tuhuma da nifaqa da yi wa Allah da Manzonsa tawaye, da xaurewa fasadi gindi a duniya.

Halifa Usmanun nan da kake ji Raliyallahu Anhu Sahabin da ‘yan Shi’ah suka yi wa wannan riqon sa kainar kashi, dattijo ne na qarshe. Riwayoyi mutawatirai sun tabbatar da cewa ya fi kowa gudun zubar da jinin wani. Shi ne kuma mutum mafi haquri da yafewa wanda yaci mutuncinsa. Kuma irin yadda ya kau da kai tare da tsare alfarmar waxanda suka kai masa takakka don su kashe, tattare kuma yasan nufinsu, ba duk mutum ke iya haka ba.

Sai da musulmi suka yo angaya daga ko ina, suka bashi shawarar lalle ya xaura yaqi da waxannan mutane. Amma gogan naka; salihi uban dattijai, ya kafa kai ga kasa ya ce, atafau, kada wanda ya yaqe su; duk wanda ke jin maganarsa ya kauda kansa. Harma an riwaito cewa ya ce wa bayinsa duk wanda ya kama kansa na ‘yanta shi.

Ganin cewa halifa Usmanu baya da niyyar sassautawa daga wannan mataki daya xauka sai musulmin dake tare dashi, suka ce to yayi hijira mana ya koma Makka. Ya ce: Allah ya sauwake. Ba zai zama wanda ya keta alfarmar xakin Allah ba. Suka ce to ya tafi sham. Ya ce: Barin Madina; garin hijira baya yiwuwa gare ni. Suka ce: To lalle koka yaqe su ya ce: ina! Ko alama. Ba zan yarda in zama farkon wanda ya raka Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama da fasa garken al’ummarsa da takobi ba.

Ko shakka babu, wannan haquri da jaruntaka da halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ya nuna, ta hanyar yi gaba da gaba da mutuwa, na daga cikin manyan darajojin da musulmin duniya ke girmama shi a kai. Duk kuwa wanda ya soki lamarinsa da cewa wai ya halatta zubar da jinin musulmi tunda yaqi kashe Ubaidullahi. Duk wanda ya ce haka, to a taqaice yana sone ya buxe kofar sukar lamarin Ali Raliyallahu Anhu da abin da yafi wannan girma. Domin idan magatta Ali Raliyallahu Anhu suka qirdadi wannan magana, suka kuma hankalto cewa kyale Ubaidullahi da halifa Usmanu Raliyallahu Anhu yayi, abune dake da madogara a shari’a. To sai suce ba kowa ne ya keta alfarmar hukuncin Allah ba, banda Ali Raliyallahu Anhu tunda shi ne yaqi hukunta makasan halifa sukutum (Usman Raliyallahu Anhu) waxanda babu wani tawili da zai kasa halatta, jininsu. Wanda ko shakka babu keta alfarmar hukuncin Allah a cikin yin biris da wannan haddi tafi zama varna bisa ga yin biris dashi acikin wancan. Domin ko alama alfarmar Hurmuzan bata kai ta halifa Usmanu ba Raliyallahu Anhu.

To idan kuwa har za a yi wa Ali Raliyallahu Anhu uzuri, a kuma ba shi kariya. Ta hanyar la’akari da kasancewarsa mujtahidi kuma maras wuqa a hannu tare da nama. Babu abin da zai hana a sakawa Usman Raliyallahu Anhu irin wannan riga. Don ya mafi cancanta da ita.

Haka kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai halifa yaso yin biris da haddin da yahau kan Walidu xan Ukbata. Wai sai da Ali Raliyallahu Anhu yayi tsaye ya zartar da hukuncin a kansa. Qarya ce yake yi wa duka su biyun.

Abin da ya tabbata a ingantaccen hadisi, kamar yadda muka ambata a baya, shi ne; halifa Usmanu Raliyallahu Anhu shi ya umurci Ali Raliyallahu Anhu da bulale Walidu haddi. Qarshe kuma shi Alin Raliyallahu Anhu ya hana a yi masa bulala tamanin. Aka tsaya ga arba’in. Ka ga da ya bari an yi tamanin xin halifa ba zai ce uffan ba. Don hakan ma sunna ne. Ka ga kenan Ali Raliyallahu Anhu ya tausayawa Walidu a matsayinsa kuma na wanda ya savawa Allah.

Wannan kenan. Wani abin kuma dake qara tabbatar maka da jahilcin wannan xan Shi’a, da kasancewarsa mugun maqaryaci, shi ne cewar da ya yi wai bayan tsayar da wancan haddi da Ali Raliyallahu Anhu yayi, sai ya ce: Bata yiwuwa a tozarta hukuncin Allah ina raye.

Tumun fari, wannan magana qarya ce.

To kuma ko da mun qaddara kasancewarta gaskiya, to za ta zama wani babban abunda ya kamata a yabi halifa Usmanu dashi ba Ali Raliyallahu Anhu ba. Domin halifan bai yi girman kan qin karvar shawarar Ali ba Raliyallahu Anhu balle ya hana shi zartar da hukuncin. Tattare da kuma yana da ikon yin haka. Kuma a matsayinsa na halifa idan yaga dama, Ali Raliyallahu Anhu bai isa yasa ko hana shi abin da yaga damar yi ba.

Wannan magana tabbas haka take. Don Ali Raliyallahu Anhu nada irin wannan iko a a kan halifa Usmanu Raliyallahu Anhu da bai bari ya aikata abubuwan da ‘yan Shi’ah suka xauka abubuwan kunya ba. Amma ka ga bai hana shi ba. Tattare da kasancewar sa Ma’asumi, mai iko a kan komai. Kamar yadda ‘yan Shi’ah suka yi imani. Ka ga kenan reshe ya juye da mujiya; sukar lamirin ta koma kan Ali Raliyallahu Anhu.

Saurarawa Ali da Usman zaiyi Raliyallahu Anhu idan har hakan ta tabbata, don zartar da wannan hukunci, na kawai tabbatar da dattako da kishin addini da adalci da halifan ke dasu ne, amma ga mai hankali.

Haka kuma halifa Usmanu ya naxa Walidun nan gwamnan Kufa. Abin da ‘yan Shi’ah ke ganin bai halatta ba. To ka kuwa ga inda hakan haramun ne, kamata yayi ace Ali Raliyallahu Anhu ya hana halifan yin haka. Tunda har yana da ikon yin haka ko? Tunda kuwa har bai hana shi ba, kenan ya yarda da naxin a matsayin halas. Ko kuma bai da ikon hana shi xin. In har hakan bata halasta, a nasa gani.

Idan kuwa haka ta tabbata, kenan Ali Raliyallahu Anhu bai zartar da hukuncin can ba, bayan Usmanu Raliyallahu Anhu yayi biris dashi, in har hakan ta tabbata. Tunda ta tabbata bai iya hana shi komai, don yana ji yana gani ya naxa Walidun.

Ka ga kenan a hankalce, da halifa Usmanu bai so ba, bata yadda za a yi Ali Raliyallahu Anhu ya iya zartar da hukuncin. Idan kuwa ya zartar dashi ne, tare da yardar halifan. Ka ga halifan ya tabbata mai kishin addini. Wanda ba zai tozartar da wani hukunci daga cikin hukunce - hukuncen Allah ba.

Karka yi mamaki yadda ‘yan Shi’ah nan ke tafe suna qwangaba qwanbaya. Haka sunka saba.

Bari kaji wata wautar da tunqa da walwala. Xan Shi’ar ya ce wai: haka kuma halifa Usmanu ne Raliyallahu Anhu ya qirqiro da bidi’ar kiran sallar, da wanka na ranar jumu’a. Har aka wayi gari ya zama kamar sunna.

Ka ji magana kamar ta ilimi.

Martani:

Idan dai wannan ijtihadi da halifa Usmanu Raliyallahu Anhu yayi bidi’a ne, to Ali Raliyallahu Anhu ko na daga cikin waxanda suka goya masa baya a kanta, a lokacin rayuwar halifan da bayan rasuwarsa. Don haka ne ma da Alin Raliyallahu Anhu ya zama halifa bai kashe wannan kiran sallar ba.

Kamar yadda ya tuve waxanda bai yarda da su ba, daga cikin ma’aikatan Usmanu Raliyallahu Anhu wanda har Mu’awiyah na daga cikinsu. Amma abin ya faskara. Ka kuwa san kashe kiran sallah, da wasu ayyuka masu kama da shi, da ake jin bidi’a ne, a Kufa yafi sauqi matuqa bisa ga qoqarin tuve wadancan ma’aikata, daxa balle yaqar su. Abin da ya gagari Alin Raliyallahu Anhu

Kuma ko shakka babu, da Ali Raliyallahu Anhu ya kashe irin wannan kiran sallah a Kufa, da duniyar musulunci taji. Ka ga kenan ba bidi’a bane har a cikin littafin fiqihun Ali Raliyallahu Anhu.

Nasan kangararrun (‘yan Shi’ah) na iya cewa: to ai dole ya bari aci gaba da yi nai. Don ko cewa yayi a daina mutane baza su yarda ba.

Ka ji wawaye.

To ai hakan, dalili ne dake nuna cewa mutane harda magoya bayan Ali Raliyallahu Anhu waxanda suka taya shi yaqi, irin su: Ammaru da Sahlu xan Hanifu, da wasunsu daga cikin ‘yan sahun farko a musulunci, duk sun goyi bayan halifa Usmanu Raliyallahu Anhu a cikin ganin dacewar wannan kiran sallah, da tahowarsa a kan qari.

Wani abun ban mamaki ma duk, bai fi cewa mutanen nan (‘yan Shi’ah) dake sukar lamarin halifa Usmanu Raliyallahu Anhu a kan wannan kiran sallah da ya taho dashi. Kuma gaba xayan musulmi; da suka haxa da Muhajirun da Ansaru, suka mara masa baya. Sune mutanen da suka kara lafazin “Hayya Ala Haril Amal” a cikin kiran sallar. Abin da ba a tava ji zamanin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya furta ko ya yi umurni dashi ba. Kuma babu musulmin da baisan cewa kiran sallar da Sahabi Bilalu da xan Ummu Makatum keyi a masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a Madina. Da wanda Abu Mahazura keyi a Makka, da Sa’adu al-Kurzu a Quba a, duk bai qunshi wannan xan Shi’ar lafazi ba.

Ka ga kenan wannan qari nasu shi ne bidi’a kuma vatatta, ba kiran wanka ba. Don gashi musulmi ba riwaito lafazin nasu ba, amma sun riwaito wanda ya inganta.

Haka kuma xan Shi’ar ya ce wai gaba xayan musulmi sun raba gari da halifa Usmanu Raliyallahu Anhu wanda hakan ta zama sanadiyar ya rasa ransa. Kuma wai ma sukan yi masa arashi da cewa, bai halarci yaqin Badar ba. Kuma ya gudo daga na Uhudu. Kuma ba tare dashi aka yi Bai’atur - Ridhwanu ba. Kuma wai labari a kan haka sufi qarfin kididdiga.

Maratani: Idan xan Shi’ar na nufin raba gari na gama gari. Waton gaba xayan mutane sun juya wa halifa baya. Suka halatta jininsa, ta hanyar haxa waccan yar qungiya, da bata kowane irin taimako don xaukar ran halifan, to babu wanda bai san wannan magana qarya bace. Domin wasu ‘yan kwarorin mutane ne, azzalumai suka yi masa tawaye, suka kuma kashe shi. Kuma da sauran musulmi sun sami goyon bayan halifan a kan yaqar Makosan da Mussarsu ta kyankyami kasari.

Kuma wani abin da ke tabbatar da cewa wannan magana qarya ce, shi ne cewar da xan Zubairu yayi: Allah dai ya la’anci makasan Usmanu Raliyallahu Anhu sun masa shigar sauri ne kamar yadda varayi keyi. Amma duk da haka nan wasunsu basu shaba. Sauran kuma suka nemi sa’ar hasken taurari.

Wato yana sone ya ce: ‘yan tawayen sun kai kutsa kai ne suka kashe halifan cikin dare. Bayan mafi yawan musulmi sun sallame shi. Amma sauran mutanen gari sun ga shigowar su. Sai dai ba su yi tsammanin kashe shi za su yiba. Don babu wata alama tare dasu da ke nuna hakan.

Ka ga ashe kenan wasu ‘yan tsiraru ne suka raba garin dashi ba kowa ba.

Idan kuwa xan Shi’ar na nufin gaba xayan musulmi su raba gari ne da halifan, rabawa irin wadda ta taqaita ga qin amincewa da duk abin da ya aikata kawai. Ko kuma ga abubuwan da ake sukar lamarinsa a kansu kawai. To ko a hakan ya shara shegiyar. Domin kuwa tarihi ya tabbatar da cewa babu wani abu da wasu musulmi suka savawa halifan a cikinsa, face adadin da yafi nasu yawa ya amince dashi a kai. Kai harma daga cikin nagartattun malaman su kan mara masa baya. Haka kuma tarihi ya tabbatar da cewa waxanda suka yarda da halifa Usmanu Raliyallahu Anhu a kan abubuwan da wasu ke qi nasa, sun fi waxanda suka yarda da Ali Raliyallahu Anhu a kan abubuwan da ake ganin lamarisa a kai yawa da girman daraja, ta fuskoki da dama.

Haka kuma ta tabbata cewa waxanda suka yi wa halifan arashi da cewa bai halarci yaqin Badar da Bai’atar-Ridwanu ba, ya kuma gudo daga yaqin Uhudu, wasu ‘yan tsiraru ne kawai daga cikin musulmi, waxanda ba su cika yatsun hannu ba a adadi ba. Kuma halilfan da biyu, shaixan kawai ne ya talalabantar dasu, saboda sashen abin da suka tsirbata. Kuma lalle ne, haqiqa Allah ya yafe laifi daga gare su. Lalle ne Allah mai gafara ne mai haquri (3:155).

To ka ga wannan aya ta hutar da duk mai tsoron Allah. Tunda sarkin ya yafewa duk ma wanda ya kaye a ranar yaqin; ba Usman Raliyallahu Anhu kawai ba. Ga kuma tarin falala da kyawawan ayyukan da halifan yake dasu Raliyallahu Anhu.

 2.79 Maganar Shaharastani Ba Hujja Ce Ba

A wani qoqarin kuma na samar wa soke-soken da xan Shi’ar ya yi wa waxannan manyan halifofi, sai ya lalabu maganar shahraxani ya kafa hujja da ita, da cewa: Duk da tsananin kyamar da shahraxani ke yi wa Shi’ah ‘yan-sha-biyu inji xan Shi’ar, wai an samu yana cewa: Babu wata fitina data gurvata al’ummar musulmi bayan fitinar shexan (Iblis) kamar savanin daya shiga tsakanin Sahabbai a lokacin rashin lafiyar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

Farkon wannan savani kuma inji shahraxani, wai shi ne, abin da Buhari ya riwaito, da isnadinsa, daga xan Abbas, wanda ya ce: Ya yinda rashin lafiyar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qaura aikinta ta tsananta, sai ya cewa Sahabbai ku kawo mani tawada da farar takarda in rubuta muku wasiyyar da baza ku vace ba bayan na qaura. Sai Umar ya ce: ina ganin zafin ciwo ne ya tsananta gare shi. Kuma ai littafin Allah ya ishe mu.

Daga nan sai wuri ya kacame da yaya. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Bai kamata kuna irin wannan yaya da jayayya gabana ba. Kai! Ku dai watse.

To farkon abin da za mu ce a nan, a matsayin martani shi ne: Maganar shahraxani ba hujja bace. Saboda mafi yawan abin da yake faxa, shi da takwrorinsa mawallafa, a cikin: Al-milal Wan-Nihal, maganganu ne da sashensu ke riwaitowa daga sashe. Kuma mafi yawansu, ba a riga an tace jirwayen zantukan waxanda aka riwaito su daga gare suba, aka zubar. Kuma ma mafi yawan su ba su da isnadi. Wani abin la’akari ma shi ne da yawa yakan tsakuro maganganu daga cikin littafan marubuta ‘yan Shi’ah da suka wallafa maqalu kafinsa. Wato irin su: Abu Isah al-Warrak, shahararren marubucin nan na ‘yan Shi’ah. Waxanda basu jin kunyar qarya. Sai kuma Abu Yahaya da waninsa. Haka kuma ya kan tsakuro wasu abubuwa daga cikin littafin Shi’ah Zaidiyya da Mu’utazilawa. Waxanda suka shahara da sukar lamirin da yawa daga cikin Sahabbai saboda haka maganarsa bata isa hujja ba.

To amma mu bamu yi mamakin wannan abu da xan Shi’ar yayi na riqon gurvataccin maganganun malamin a matsayin hujjojinsa ba. Domin kamar an tunkuxi icce ne inda yake son faxuwa. Dama kuma ma’abucin son zuciya na kodayaushe lalaben abin da ya dace da itane ya karva ido rufe. Ba tare da wata kwakwarar hujja dake wajabta masa hakan ba. Nan take kuma ya yi watsi da duk abin da bai dace da ita zuciyar tasa ba, ba bisa wani dalili kwakwara ba.

‘yan Shi’ah kenan. Babu wata qungiya daga cikin qungiyoyi a duniya da tayi sunan qaryata gaskiya da gasganta qarya kamar su. Domin waxanda suka kafa marhabar tasu, da malamanta duk munafukai ne zindikai. Kamar yadda malamai da dama suka tabbatar, take kuma bayyana ga duk wanda ya yi masu kallon tsaf.

A kan haka, kenan ba za ta yiwu ba mu saki samu kama abin da ko ga tozo bai kai ba. Abubuwan da al-qur’ani da sunna da mutawatiran riwayoyi suka daddale, na kyawawan ayyukan Sahabbai da darajojinsu sun yafi qarfin wata gurguwar magana maras asali. Ko burkutu - burkutu su kawar dasu. Balle wadda ke kan turva madaidaiciya. Domin a qa’ida, shakka bata kawar da yaqini. Kuma mu mun riga mun miqa wuya ga duk abin da al-qur’ani da sunna da ijma’in magabata suka tabbatar. Haka kuma duk wata riwaya mutawatira, ko wata dalili na kaifin hankali da zai zo ya marawa waxannan abubuwa da muka yarda da su baya; ya daxa karfafa su, ta hanyar tabbatar da cewa Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sune mutane mafiya daraja a cikin halittar Allah bayan Annabawa. To za mu karvi irin waxannan riwayoyi da hannu biyu - biyu. A waje xaya kuma sukar da za a yi masu ta hanyar amfani da wasu abubuwa da ingancinsu bai tabbata ba, ba zata razana mu ba, balle wadda aka tabbatar da kasancewarta qarya.

Wannan kenan. Sannan kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai, Shahrastani na daga cikin mutane masu tsananin kyamar Shi’ah ‘yan-sha-biyu. Ba gaskiya bane. Kuma ya kawo wannan magana ne don ya yaudari hankalin mai karatu.

Abin da yake gaskiya shi ne: Shahrastani na daga ma cikin mutanen da ake zargi da kasancewa ‘yan Shi’ah Isma’iliyyah. Saboda da yawa yake goyon bayan wata hujja da wata magana tasu. Duk da yake, a haqiqanin gaskiya shi ba xan Shi’ah bane. Tattare kuwa da waxanda ke zargin shi da ita sun kafa hujjoji daga cikin maganganunsa da tarihin rayuwarsa. Amma idan akace malami ne daka tava qida kaxan ya tava karatu; yau Ba ash’are gobe Bashi’e babu laifi.

Daga nan kuma sai cewar da xan Shi’ar yayi, shahrastani ya ce: Babu wata matsala data girka xumar fasadi da varna a duniya bayan wadda Iblisu ya girka, kamar savanin daya shiga tsakanin Sahabbai a lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke jinyar ajali.

Ka ji.

To duk yadda aka kaxa aka raya wannan magana ba ta zama gaskiya; Idan xan Shi’ar na nufin wannan savanin fahimta daya shiga tsakanin Sahabbai a wannan lokaci; shi ne farkon laifin da aka yi wa Allah, to qarya yake yi. Haka kuma ko cewa yayi; a’a, yana dai nufin shi ne savani na farko da aka samu bayan waccan matsala ta Iblisu. Duk dai har yau bai daga ko kaxan daga matsayin maqaryaci ba, saboda dalilai kamar haka:

a)           abin nan daya faru tsakanin Sahabbai a wannan lokaci, ya sha banban da wanccan daya faru ga Iblisu kwata - kwata. Domin wancan batun zuci da iblisu yayi, har ya kasa miqa wuya ga umurnin Allah kai tsaye, bai sa mala’iku suka shiga cikin wani bilinbito ba. Kuma al’amarin bai kai kunnen ‘yan Adamu ba, balle suma su afka cikin koyin rikici da savani.

b)          Banbancin fahimta tsakanin ‘yan ‘Adamu abune mai daxaxxen tarihi; tun zamanin Annabi Nuhu. Hasali ma banbancin fahimta da savani da ake samu tsakanin musulmi, ko kaxan bai kama qafar wanda ya yi ta faruwa a tsakanin al’ummomin da suka gabace mu ba.

C) Idan aka kai wannan abu da ya faru a lokacin wannan jinya ta Manzo, bai kai can ba. Domin babu wani abu mai rikitarwa acikinsa balle; abu ne mai matuqar sauqi da zama ga – ta - sarqi. Domin kuwa ya tabbata a cikin ingantaccen hadisi cewa, kafin wannan lokaci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya cewa Sayyida Aisha Raliyallahu Anhu: kiraman mahaifinki da xan’uwanki. Ina son in rubuta wa Abubakar Raliyallahu Anhu wata takarda don kada mutane suyi wata shakka, balle su sava a kansa, bayan na qaura. Sannan Manzon ya cika da cewa: Alhali kuwa shi ne zavin Allah, wanda kuma muminai za su zava.

Ka ji tushen wancan al’amari.

Kamawar ranar Alhamis keda wuya sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yayi tunanin rubuta wannan magana don qara daddale ta. Har ya ce a kawo masa kayan rubutu. Umar Raliyallahu Anhu ya ce: Anya ba zafin masassara ne ya tsananta a kansa ba.

Ka ga Umar Raliyallahu Anhu bai yanke hukunci a kan matsayin maganar ba, tunda ya yi amfani da kalmar “anya” wadda ke alamace ta “shakku”, da tabbatar da cewa al’amarin ya shige masa duhu ne. Kamar yadda rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta shige masa duhu, har kaxan ya rage ya musanta ta.

Daga nan sai wasu Sahabbai suka ce, kai! Ku samo abun rubutu. Wasu kuma suka ce, kar a kawo. Ganin wannan magana ta Umar Raliyallahu Anhu tayi wannan tasiri a cikin Sahabbai. Kuma ma ba wani muhimmanci wannan rubutu keda shi ba. Ko banza ma ya riga ya faxi abin da yake son rubutawa tun shekaranjiya. Ga kuma wannan kokwanto daya sami Sahabbai daga wurin Allah. Sai Manzon ya fita batun rubutun.

Ka ga kenan abin da wannan ke tabbatar wa, shi ne; wannan wasiyya bata cikin abin da Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya wajabta wa Manzon rubutawa Sahabbai a wannan lokaci, a matsayin sakonsa. Don da wajibin ce, babu abin da zai hana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita batunta, a matsayinta na abin da Allah ya umurce shi dayi. Abu dai ne da shi a karan kansa, yaga ya dace, don yayi maganin wani rikici da kan iya tasowa a kan bakin daya bari na Sahabi Abubakar Raliyallahu Anhu ya gaji halifancinsa.

Wannan itace gaskiyar al’amarin. Amma saboda jahilcin daya yi wa ‘yan Shi’ah kanta, sai sukace wai Manzon yaso ne ya rubuta wasiyyar a kan Ali Raliyallahu Anhu ya maye halifarsa, bayansa kai tsaye. Alhali kuwa babu wani abu a cikin wannan qissa dake nuna haka ta kowane hali. Kai! Ko wancan hadisi sannane a wurin malaman riwaya, baya xauke da wani abu mai ko kama da wannan. Amma ingantattun hadisan dake tabbatar da halifancin Sahabi Abubakar suna da yawa.

Wani abun kuma dake qara tabbatar da jahilcin waxannan mutane, shi ne cewar da suka yi wai itama halifar Ali Raliyallahu Anhu Manzon ya riga ya tabbatar da ita a nassance, ta yadda wanda ya kauce mata ba zai sami wani uzuri ba. Ah! To idan kuwa har haka ne, to rubutu na me? Idan kuwa har yaso ne ya rubuta don kada waxanda suka ji wancan nassi su fandare. To rubutun ba zai yi amfani ba. Don shi ma suna iya fandare masa. Ka ga kamar yadda muka faxa, idan dai har ta tabbata Manzon ya furta waccan magana, to amfani me rubutun zai yi masu? Babu.

Savani na biyu a wannan lokaci, a cewar sharastanin shi ne, rabuwar kan da aka samu tsakanin Sahabbai, bayan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce musu: ku kimtsa rundunar Usamatu. Kuma Allah ya la’anci duk wanda ya bari ta bar shi tasha.

Wai kuma tattare da wannan babbar magana da Manzon yayi, sai Sahabban suka shiga ka-ce-na-ce; wasu na cewa: Lalle ne a aiwatar da wannan umurni. Wasu kuma na cewa: A’a a dai saurara. Ba ku ganin yadda masassarar nan ta tsananta gare shi? Bai kamata mu tafi mubarshi ba. Kuma wai a lokacin da suke wannan muhawara har Usamatu ya sha xamara.

Martani:

Eh! Gaskiya ne wannan abu ya faru. Amma malamai masana sirrin riwaya sun tabbatar da cewa qarya ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai ce: Allah ya la’anci duk wanda wannan runduna ta bari tasha ba. Kuma babu wani isnadi dake tabbatar da cewa ya ce haka. Babu wani littafi na hadisi daya sanda wannan magana asalata. Kuma tarihin musulunci ya tabbatar da cewa imanin Sahabbai ba zai bari su qi fita tare da Usamatu ba, daya fitar. Shi ne da kansa ya ga bai dace su fita a lokacin ba, saboda ganin halin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke ciki na rashin lafiya. Har ya ce masa. Ya Manzon Allah! Ya zan fita in barka cikin wannan hali? In koma ina tambayar fatake yadda ka kwana? Daga nan sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa izinin lalle sai Usamatun ya tafi, ba abin da zai hana shi zuwa. Da kuwa sauran Sahabban da aka shirya subi shi sun bishi. Don ta tabbata babu wanda ya bari jirgin rundunar ya bar shi tasha, lokacin da ya tashi, bayan rasuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sai fa wanda shi Usaman ya yi wa izinin tsayawa saboda wani jihadin.

Sannan kuma kan malamai ya haxu kan cewa babu sunan Abubakar Raliyallahu Anhu cikin jerin sunayen waxanda ya kamata su fita yaqin tare da Usama. Amma an riwaito cewa na Umar Raliyallahu Anhu na ciki. Kuma tuni Barden ya xaura tamantaka yayi shirin fita, da lokacin ya yi.

Amma sai Abubakar Raliyallahu Anhu ya nemi izinin Usaman a kan ya bar masa Umar Raliyallahu Anhu don ya kama masa wani jihadin. Aka kuma yi sa’a kwamandan ya amince. Amma kuma karka manta zaman Sahabi Abubakar halifa ke da wuya, ya dage a kan lalle wannan runduna ta tafi. Amma sauran Sahabbai suka nuna masa haxarin daka iya faruwa a cikin fita tunda wuri haka. Don magabata sun koxa wuqaqensu da jin rasuwar Annabi. Amma duk da haka halifan ya nace a kan wannan Umurni nasa, yana mai cewa: Wallahi ba zan saukar da tutar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya xaga ba. Sai dai kome ke tafasa ya kone.

Tirqashi ka ji maza. A gaida Uban Aisha saxaukin fama.

Haka kuwa aka yi, sai da rundunar ta tafi.

Wannan shi ne ingantaccen tarihin abin da ya faru. Amma sai gashi sarakunan qaryar duniya na yayata cewa wai Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma anga daga cikin waxanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya shata su tafi yaqin tare da Usama. Kuma wai dasisa ce Manzon ya killa masu, don kada su hana Ali Raliyallahu Anhu kaiwa ga halifanci, idan ya cika suna kusa. Ka kuwa san fa mai kera irin wannan qarya sai mafi jahilcin mutane da tarihin Manzon da Sahabbansa.

Abin da ya tabbata shi ne; tsawon kwanukan jinyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Abubakar Raliyallahu Anhu ne keba mutane sallah, da Umurninsa. Kuma kowa ya san haka. Da Annabi yaga dama, yana iya naxa wanda zai gade shi a lokacin. Kuma Sahabbai ba za su qiya masa ba. Kuma ko shakka babu Muhajiruna da Ansaru na yin layya da duk wanda yaqi bin umurnin Allah da Manzonsa. A matsayinsu na waxanda suka yi gwagwarmayar kafa addinin har ya kai gaci.

Umurnin Manzon Allah ba zai tava faxuwa ba matuqar waxannan na raye. Da Manzon yasa Ali Raliyallahu Anhu ya waqice shi ga limancin sallah, ko aikin hajji, ya kuma sa Abubakar da sauran Sahabbai qarqashin ikonsa. Ko ya ce masu: Ga Aliyu nan shi ne na zava ya zama shugabanku (halifa) idan na qaura. Babu wanda ya isa ya ce masa a’a. Kai ka san haka.

A shirye gaba xayan musulmi da Muhajiruna da Ansaru suke suyi masa xa’a da zai ce haka. Saboda babu wanda Ali Raliyallahu Anhu ya kashe wa xan’uwa daga cikinsu balle yaqi shi.

Ah! Kuma inda Manzon na sone ya korewa Ali Raliyallahu Anhu su, don haka ya tura su yaqi tare da Usama. To da abin ya faskara, sai ya ce wa musulmi: kada wanda ya yi wa xayan su bai’as. Shikenan ba mai yi. Babu wani tsoro da zai ji a cikin faxar haka. Saboda tabbacin samun taimakon Allah da yake da shi. Kuma ga Muhajiruna da Ansaru kewaye dashi. Waxanda da zai hore su da kashe iyayensu da ‘ya’yansu, nan take ne.

Kuma ma me yayi zafi tsakanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma wanda tarihi bai sani ba, balle ya faxa, har da haka zata kasance? Ai surar bara’atu ta sauka daga wurin Allah. Ta tona asirin munafukai, ta fito dasu a fili, musulmi kowa ya sansu. Manzo da gaba xayan al’umma suka yi tir da Allah waddai dasu.

Amma aka ci aka suxe, Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma na nan a kan matsayinsu na mafiya zama kusanci ga manzon. Mafiya girma, soyuwa da cuxanya dashi dare da rana. Kuma waxanda suka fi kowa qaunarsa, da biyar umurninsa, da yarda da ra’ayinsa da xaukaka martabar addinin da yazo da shi.

Ka ga a wannan matsayi nasu, ya savawa hankali a ce kuma, suna daga cikin waxanda mutane da surar Bara’atu ta tonawa asiri. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yanke kowace irin hulxa dasu bayan saukar surar. Amma kuma har Allah ya karvi rayuwarsa babu wanda ya keso daga cikin mutane, da girmamawa kamar Abubakar Raliyallahu Anhu .

Bayan wannan kuma sai shaharastanin ya ce: Savani na uku kuma shi ne wanda ya faru a kan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama .

Martani: Eh! Ko shakka babu al’amarin rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yaya shige wa Umar Raliyallahu Anhu duhu a farkon lamari, amma safiya nayi, ya dawo cikin hayyacinsa, ya kuma sakankance cewa dai lalle Manzon Allah ya qaura. Bayan haka kuma ya tabbatarwa sauran musulmi da cewa, matakin da ya hau jiya kuskure ne. Kuma daga nan sai kura ta kwanta komai ya koma daidai. Kuma lafazin hadisin na haqiqa ya savawa yadda shahrastani ya shimfixa al’amarin.

Abin da yazo a cikin Buhari da Muslim, a hadisin da aka riwaito daga xan Abbas, wanda ya ce: Umar na cikin magana, sai ga Abubakar Raliyallahu Anhu ya fito, ya ce: saurara Umar, zauna. Umar yaqi ya zauna. Sai ganin haka, mutane suka mayar da hankali ga Abubakar Raliyallahu Anhu don suji abin da zai faxa. Suka fita batun Umar Raliyallahu Anhu sai Abubakar Raliyallahu Anhu ya ce: Bayan haka, ku sani, duk wanda ke bautawa muhammadu, toya sani Muhammadu ya rasu. Duk kuwa wanda ke bautawa Allah to ya sani Allah baya mutuwa. Kuma Allah Ta’ala ya ce: kuma Muhammadu bai zamo ba face manzo, lalle ne manzani sun shuxe a gabaninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, za ku juya akan duga - duganku? (3:144)

Xan Abbas ya ce: Wallahi kai kace mutane basu tava sanin Allah ya saukar da wannan aya ba, sai yau da Abubakar ya karanta masu ita. Nan take kuma sai kowa ya riqe ta yana maimaita a zuci, lavvansa na mui –mui - mui.

Ya ce kuma : xan masayyibi ya bani labarin cewa Umar Raliyallahu Anhu ya ce: wallahi qarewar Abubakar karatun wannan aya keda wuya sai gavvaina suka yi sanyi., har kafafuna suka kasa xauka ta. Nan take na faxi zaune na kuma tabbata lalle dai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu.

Ka ji haqiqanin abin da ya faru.

Sannan kuma savani na huxu, kamar yadda Shahrastanin ya ce, wai shi ne wanda ya faru a kan halifanci. Ya ce kuma shi ne savani mafi muni a tarihin musulunci, daya tarwatsa kan al’umma. Domin babu wata qa’ida ta musulunci da aka zare takubba aka ba hamata iska saboda ita, a tsawon zama, kamar yadda aka yi a kan halifanci.

Martani: Wannan magana babban kuskure ce. Domin kuwa –Alhamdu - Lilahi- babu wani yaqi da aka yi a kan halifancin Abubakar ko Umar ko Usmanu Raliyallahu Anhu kai! Ko cacar baki har hanci ya yi zafi, ba a tava yiba a zamaninsu a kan halifanci, balle a kan wani abu na addini. A sane muke da cewa Ansaru sunyi waxansu ‘yan maganganu. Amma kuma da manyan mutane suka yi masu kashedi, nan take kowa ya nabba a. Ka ga ba wani rikici a nan. Don babu mai musun cewa girman darajar mutane irin su Ubaidu xan Huzairu da Abbadu xan Bushrin da wasunsu tafi ta Sa’ad xan Ubaidata, a tsurar ruwan zatin kansu da girman gida. To sune suka sa baki magana ta kare.

Babu wani mutum xaya daga cikin manyan gidajen Ansaru, waxanda Buhari da Muslimu suka riwaito, ta fuskoki da dama cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbatar da girmansu da cewa: mafi alheri daga cikin gidajen Ansaru, sune:

1.   Gidan bani Najjar

2.   Gidan bani Abdul-As’hal

3.   Gidan bani Hashi

4.   Gidan bani Sa’idata

Amma kuma akwai alheri a cikin gaba xayan gidajen Ansar inji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama to babu wani daga cikin gidaje uku masu daraja ta farko (1-3) da aka ji ya yi wata jayayya a kan halifancin. Hasalima manyan mutane daga cikin Bani Najjar, irin su: Abu Ayyuba al-Ansarida Abu Xalhatu, da Ubayyu xan Ka’abu da wasunsu duk Abubakar suka a zava.

Haka kuma Usandu dan Hudhainu, barden da ya jagoranci rundunar Ansaru a ranar da aka ci garin Makka da yaki, yana hagu ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama Abubakar Raliyallahu Anhu na dama. Wanda kuma daya ne daga cikin Gidan Bani Ashhal, shina daya daga cikin Ansarun da suka hada kan al’umma a kan yi wa Abubakar Raliyallahu Anhu bai’a.

Waxanda kawai suka yi cijiya; suka ki yin wannan bai’a a lokacin da kowa ya yi, s;u ne: Sa’ad dan Ubbadata da Hubbatu dan munzir, da wasu ‘yan tsirarun mutane. Ko su kuma sun gano sun yi kuskure. Daga baya suka dawo suka yi wa Siddiqu mubaya’a, ban da Sa’adu dan Ubbadata shi kam cewa ya yi, atafau.

Amma kuma wannan abu da Sa’ad ya yi, ba abin mamaki ba ne. Domin shi ba ma’asumi bane balle. Amma dai mutum ne salihi. Kuma yana da laifuka, waxanda wasunsu sananni ne ga musulmi. Kuma ana fatar Allah ya gafarta masa su. Musamman tunda ya sami shiga sahun ansaru na farko ga shiga musulunci. Waxanda kuma Allah ya yi wa albishirin aljanna tun duniya. Kari a kan yarda da amincewa da ya yi da su.

Kuma cewar da shahrastani ya yi wai gaba xayan Ansaru sunyi ittifaqi a kan Sa’ad din ya walkice su, ya zama halifa, maganace maras tushe balle makama. Domin abin ada ya tabbata daga bakin ma’abuta ilimin riwaya, da kuma tabbataccin hadisai duk sun tabbatar da kasancewar maganar karya bisa ittifaqi. Duk da yake shahrastani da ma kantansa ba maqaryata ba ne a karan kansu. Amma tabbas suna tsakuro abubuwa daga cikin littafan manyan maqaryata ba tare da sun sani ba.

Haka nan kuma abin da wasu ke yaya tawa, an cewa duk wannan rikici da ake ta yi a kan halifanci, wai Ali Raliyallahu Anhu bai da labari. Don yana can ya shagalta da abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umarce shi da yi na yi masa wanka da saka masa likkafani da rufe shi da kuma zaunawa wurin kabarinsa. Wannan magana tabbas qarya ce. Kuma maganar ma ta yi ban hannun smakaho da abin da su kansu suka yi imani da shi. Na cewa a cikin daren ne ankayi jana’izar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba da rana ba wasu kuma suka ce a’a, sai da wani dare ya yi sannan aka rufe shi. Kuma bai umurci kowa da zaunawa wurin kabarinsa ba. Kuma tarihi bai fadi cewa Alin Raliyallahu Anhu ya zauna wurin ba, ko a ra’ayin kansa.

Ya ma za a yi haka ta faru, tunda an nufe Manzon ne a cikin dakin Aisha Raliyallahu Anhu kuma ba ajanabace ga alin?

Sannan kuma ai ‘yan Shi’ar sun gaya mana cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya riga ya gaya wa Ali shi ne magadin halifarsa. Kuma lalle ne ya yi qoqarin ganin haka ta tabbata. To ya za a yi wanda ke da irin wanna aiki; kuma a ce manzon ya umurce shi da tsare kabariunsa. Ko ya yi me? Oho.

Kuma a haqiqanin gaskiya ba Ali Raliyallahu Anhu ne kawai ya yi hidmar jana’izar Manzon ba. Abin da ya tabbata shi ne, shi da Abbas da ‘ya’yan Abbas din, da barwansa Shakran ne da wasu ansaru suka yi masa wanka da saka masa likkafani. Abubakar da Umar da wasunsu kumas suna bakin kofar dakin har aka ci aka sude. Ka ga da su aka yi kenan. Cewar da ake yi suna Bani Sa’adata a lokacin qarya ce kawai.

Abin da kuma ya hana su shiga a kimtsa gawar ta Ma’aiki tare da su shi ne; kasancewar sunna ta tanadi ta kaita irin wannan hidma ga dangin mamaci. Saboda haka ne Ali Raliyallahu Anhu da makamntansa suka rabauta da wannan alheri. Da kumas aka karkare, sai aka ba musulmi dama suka shiga dakin; daya bayan daya don su yi masa salla da ganin ban kwana. Haka suka yi ta yi, maza da mata. Taron da jama’a musulmi suka yi don wannan ibada, sai ta sa dole aka jin kirta rufe gawar har zuwa ranar alhamis.

To kuma ba halifancin halifofi uku na kafin Ali Raliyallahu Anhu wanda aka yi lami lafiya, ko yakin da aka yi lokacin halifa Ali Raliyallahu Anhu ba yaki ne na neman shugabanci ba. Domin mutanen da ke bayan Sayyida Aisha da Mu’awiyah Raliyallahu Anhu a yakokan Basasar da aka yi na Jamalu da siffain da Nahrawan, ba su saxaukantar da rayukansu ne ba, don nada wani halifa ba, Ali Raliyallahu Anhu kamar yadda Mu’awiyah da Xalhatu da Zubairu babu daya cikinsu da ya ce shi ne shugaba ba Ali Raliyallahu Anhu ba. Kamar yadda kuma ba ba qarqashin jagorancion wanimutum da suke jin shi ne halattaccen shugaba, suka yi yakokin mba, kafin sasantawar da aka so yi bisa girman Allah.

Haka kuma babu daya daga cikinwaxannan yakoka na basasa, da aka yi, a kan wata ka’ida ta shugabanci da ake cece-kuce a kanta don tabbatar da sukar lamiri da rashin goyon bayan halifofi uku magabata, da shelantawa duniyar musulunci cewa ba su ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bar wasiya a nassance da cewa su gaji shi ba. Haka kuma su dayan vangaren, ba suna yakin ne don suna jin Ali Raliyallahu Anhu bai cancanci zama halifan ba. Ko alama ba haka al’amurran suka gudana ba.

‘yar ja yayyar da ta shiga tsakanin mutane a kan wannan al’amari, kamar wadda ke tsakaninsu ce da ‘yan Shi’ah da Harijawa da mu’utazilawa da sauransu. Amma babu wani sahaboi da ya shiga ytakin;don kawai jayayyar shugabanci. Babu wanda ya kushe shugabancin Ali Raliyallahu Anhu ko ya kafirta shi, ko ya kafirta duk wanda ya jibince shi, shi da Usman Raliyallahu Anhu.

Ka ga kenan, idan ka fahimci wannan karatu da na shinfida maka, zaka fahimci cewa duk wanda ya ce farkon damtsen da aka ware, aka ba hamata iska a tsakanin musulmi wa-su-wa-su, har anka hada da kaifin takobi, ya faru ne kawai saboda kokuwar shugabanci, makaryaci ne na kinkarawa. Wanda leka kundin tarihin Sahabban kawai, ba tare da an shiga cikinsa ma sosai ba ke tabbatar da haka.

Kuma duk wanda ya kalli waxannan yake-yake da idon basira da tsoron allah, zai tabbatar da cewa yake-yake ne na Basasa, da Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya jarabci Sahabban da su a matsayin “fitina” kuma a kan haka ne mafi yawan malamai masu tsoron allah suka kwana. Kuma idan har ta kama sauran su yi wani sharhi a kai, ba su kan wuce cewa: Yakoka ne da suka faru tsakanin ‘yan santsi da ‘yan tabo a cikin Sahabban ba.

Ka ga a ta kai ce an yi yakokan ne bisa karvabben tawili, na garin dacewar saurara wa wanda bai gama zama shugaba ba. Amma ba don wata ka’ida ta addini ba.

Iyakar fassarar wannan lamari kenan. Kamar yadda da a ce lokacin da aka nada halifa Usmanu Raliyallahu Anhu wasu Sahabbai sun ja daga har haka ta sa ya yake su. To matsayin yakin dazai yi da su din daya da wanda Ali Raliyallahu Anhu ya yi da wadannasn. Eh! Matsayinsu daya mana, tattare kuwa da kasancewar babu wata rashin jituwa tsakaninsu a kan wata ka’ida ta addini.

Ka ji matsayin waxannan yakoka. Amma yaki na farko da aka yi a tarihin musulunci, a kan wata ka’ida ta addini shi ne wanda Harijawa suka tayar tsakaninsu da Sahabbai. Sanadiyar wasu akidu da suka qirqira waxanda suka saba wa akidar musulunci, kuma wannan yaki na daya daga manya-manyan yakoka a tarihin musulunci. Kuma da ma nassosa mutawatirai sun ambace shi kamar cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: wasu ‘yan tawaye za su yi amfani da wata tsaga da za ta faru a garin musulmi, su yi wa musulunci tawaye. Amma vangaren da ya fi gaskiya daga cikin musulmin ne za su kashe su.

Haka kuma shi Ali Raliyallahu Anhu a karan kansa, bai yaki kowa don ya kwaci shugabanci ba. Kuma babu wanda ya yake shi don ya kwace shugabanci daga hannunsa. Kamar yadda babu daya daga cikin: Sayyida Aisha ko Xalhatu ko Zubairu ko Mu’awiyah da Sahabbansa, ko Harijawa, da ke jin shi ya fi cancanta da halifanci a kan Ali Raliyallahu Anhu Hasali ma gaba xayan al’umma na matukar ganin girmansa da zamansa mafificin daraja bayan halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ya kaura. Haka kuma suna jin babu wani Sahabi da bai zama wajibi gare shi, ya cire wa Ali Raliyallahu Anhu hula ba,a lokacin Usman Raliyallahu Anhu babu gagarabadau a cilkin Sahabban sai shi. Wanda hakan ta sa babu wanda ya ji wani kaikayi, da aka ce shi ne halifa, balle ya yi wata jayayya, da husuma don qoqarin nuna fifikon cancantar wani a kansa. Ba a sami ko daya daga cikin irin wannan ba, balle dada zancen shaya daga. Kamar dai yadda Akayi halifancin Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma cikin lumana da kwanciyar hankali.

A ta kaice dai, abin da muke son tabbatar wa da wannan jeka-ka-dawo shi ne: duk wanda ke da masaniya da tarihin Sahabbai ingantacce, tabbas ya san cewa babu wani rikici da ya faru tsakaninsu a kan halifancin Abubakar da Umar da Usmnu Raliyallahu Anhu balle yaki .

Haka kuma ba a sami waxanda suka yi wata jayayya ba, don qoqarin jtabbatar da akwai wanda ya fi Ali Raliyallahu Anhu cancanta da halifanci a lokacin sa. Duk da yake akwai wasu mutane da aka tilastawa yi wa dayan halifofin huxu bai’a. Wannan dole na, kuma ba abun mamaki ba ne. Domin ko annabcin Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama sai da aka tilasta wasu karvar sa, balle halifancin wani Sahabi.

Haka kuma ta tabbata cewa Sahabbai ba su yaki junansu a kan halifancin Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhu ba. Kai! Ko cacar baki ba su yi ba. Halifancin dai da aka zubar da jini a kasa shi ne na Ali Raliyallahu Anhu ka ga idan har zubar da jini a kan shugabanci abun kunya ne, to ba wanda hakan za ta shafa sai wanda hakan can ta faru tsakanin al’umma kan shugabancinsa.

To kuma wannan ita ce hujjar hawarijawa a kan matsayin da suka xauka na kin yaarda da al’amarin Ali Raliyallahu Anhu kuma wannan hujja tasu, ta fi ta ‘yan Shi’ah qarfi, su kuma a matsayin da suka xauka na kai Sahabi inda Allah bai kai shi ba. Haka kuma takubbansu sun fi sauka madaidaicin wuri bisa ga na ‘yan Shi’ah. Kamar yadda addininsu ya fi nasu inganci. Saboda su Harijawa ba maqaryata ba ne kamar ‘yan Shi’ah. Amma kuma duk da haka ta tabbata daga bakuna da daman gaske, daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bisa kuma ittifaqin Sahabbai cewa Harijawa batattu ne, kuma abin da suke kansa bidi’a ne. Dada Balle ‘yan Shi’ah waxanda hauka da jahilci da rashin kishin addinin su, da jaruntakarsua fagen kiren karya da rashin kuzarinsu da rashin tsentseni, kai da suffan tuwarsu da duk wasu miyagun halaye, suka tabbata.

Ko shakka babu Harijawa su ne qungiya mafi yaji, da wasu da takobi a kan wuyan mutane. Amma duk da haka ba su yaki kowa a kan halifancin Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma ba. Hasali ma suna daga cikin duban jama’ar da suka yarda da shugabancinsu, suks kuwa bi su.

Wannan kenan.

Sannan kuma Shaharastani ya ce: Matsala ta biyar wai ita ce ta Fadak da abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bari na kayan gado a duniya.

To, ita wannan mas’ala ba matsala ba ce. Domin kuwa ta tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mu Annabawa ba a gadon mu. Duk abin da muka bari duniya sadaka ne”.

To, abin da ya kamata a sani a kan wannan mas’ala shi ne; mas’ala ce ta banbancin fahimta a farfajiyar shari’a. Kuma ba ma wani savani da za a iya cewa akwai a cikinta. Don bai kai wanda ke cikin gadon ‘yan‘uwan juna tare da kaka namiji ba. Ko na kaka mace tare da danta ba. Ko kuma wanda ke cikin shamakance Uwa da ‘yan‘uwa biyu ke yi. Ko xaukar matsayin kaka namiji da Uwa kamar na Uba. Da kuma wasu mas’aloli na gado, masu kama da waxannan, da malamai suka sami banbancin fahimta a kai.

Sannan kuma ita ma mas’alar Fadak, mas’ala ce ga-ta-sarai. Domin kuwa ai Ali Raliyallahu Anhu ya zama halifa bayan haka nan, Fadak da sauran garuruwan musulunci duk suka koma qarqashin ikonsa. Amma bai damqa ta hannun ‘ya’yan Fatima ba, a matsayin wani abu da ‘yan Shi’ah ke iqirarin wai Abubakar Raliyallahu Anhu ya ba mahaifiyarsu. Haka kuma bai karvo wani abu da aka bai wa matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da ‘ya’yan Abbas ba, da sunan gado.

Ka ga ke hakan na nuna cewa shi kansa alin Raliyallahu Anhu bai tare da ‘yan Shi’ah a cikin wannan zargi da suke yi wa halifofin. Domin da yana jin cewa abin da suka aikata da abin da Manzon ya bari zalunci ne, lalle da ya walwale shi. Domin kuwa yana da ikon yin haka. Kuma hakan ma shi ne abu mafi sauki gare shi, bisa ga fuskantar Mu’awiyah da rudunarsa da sunan yaki. Ko shakka babu Alin Raliyallahu Anhu ba zai yaki Mu’awiyahn ba, tattare da irin sharrin da hakan za ta haifar. Kuma a lokaci xaya ya kasa qwato wa magadan Annabi wannan xan abin duniya ba. Abin da yake iya yi cikin qyaftawa da bisimillah.

Bayan wannan kuma sai malamin ya ce wai kuma matsala ta shida ita ce: Yaqar waxanda suka hana zakka da halifa abubakar ya yi. Wannan ma ya vata wa al’ummar Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama suna. Wai ma saboda tsinkayo haka ne da halifa Umar Raliyallahu Anhu ya hau gado ya dage kai da fata ya mayar ma su da waxanda aka kamo daga cikinsu a lokacin yaqin. Ya kuma saki gaba xayan waxanda aka xaure a dalilin haka.

Ka ji abin da Shahrastani ya ce, kuma xan Shi’ar ya riwaito.

To duk wanda ya san tarihin musulunci ya san wannan magana shegiyar qarya ce. Domin kuwa halifa Abubakr Raliyallahu Anhu bai yaki waxannan mutane ba, sai da Umar Raliyallahu Anhu ya yarda da shi, bayan sun kara wa juna ilimi a kan mas’ala. Kamar yadda Buhari da Muslimu suka riwaito daga Abu Hurairata cewa:

Umar ya ce Abubakar Raliyallahu Anhu: ya kai halifan Manzon Allah! Ya zaka yaki waxannan mutane, alhali Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: An umarce ni da in yaki mutane, matukar ba su yi imani da babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah ba, kuma ni Manzon ne. Amma idan suka furta wannan kalima jinai nai da dukiyoyinsu sun haramta gare ni. Sai fa a kan wani hakki na shari’ah. Hisabinsu kuma na wurin Allah?

Sai Abubakar Raliyallahu Anhu ya ce masa: Ah! To ai cewa ya yi: sai fa a kan wani hakki na shari’ah ko? Ti ai zakka hakki ne na shari’ah. Tunda kuwa haka ne. Wallahi da za suki ba ni ko da ragwamar Raqumi da sukan ba Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zan yake su a kan haka.

Daga nan sai Umar Raliyallahu Anhu ya ce: wallahi, daga nan ne na fahimci Allah ya gama haskaka qirjin Abubakar a kan wannan yaqi. Na kuma sakan - kance da cewa lalle bisa hanya yake.

Ka ga kenan wannan hadisi ya tabbatar mana da cewa Umar Raliyallahu Anhu yayi itifaqi da halifa Abubakar Raliyallahu Anhu a kan wannan yaqi. Haka kuma sauran Sahabbai ma sun yarda da shi a kai. Kuma yaqin yayi amfani matuqa . saboda mutanen sun dawo sun yarda da kasancewar ci gaba da fitar da zakkar wajibi a kansu. Bayan can dauri sun fandare. Sannan kuma a ingantaccen tarihin yadda yaqin ya kasance, ba a kama kowa daga cikinsu aka ribace ba. Ba a kuma xaure kowa daga cikinsu ba. Kai hasalima babu wanda aka tava xaurewa a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kona Abubakar Raliyallahu Anhu a Madina. Balle har a ce halifan ya mutu ya bar ‘yan fursuna. Qarya ne.

Daga nan kuma sai shahashtanin ya ce wai, matsala ta bakwai itace: zaven Umar Raliyallahu Anhu da halifa Abubakar Raliyallahu Anhu yayi a matsayin wanda zai zama halifa bayansa. Wai har wasu mutane suka qorafa cewa: Abubakar ka naxa mana mutum mai kaushi hali da hushi!

Martani:

Harwayau dai, wannan mas’ala ba ta isa a kira ta mas’ala ba domin kuwa ba ga Umar Raliyallahu Anhu aka fara ba. Wasu Sahabbai sunyi irin wannan qorafi a kan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a kan ya shugabantar da Zaidu xan Harisata da xansa Usamatu a kansu, a wasu lokutta. Kuma wasu mutane da yawa sun yi qorafi da suka a kan wasu da halifa Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma suka ba riqon wasu kasashen musulmi.

To kuma shi wannan qorafi, da waccan magana da malamin ya ce an faxa a kan Umar Raliyallahu Anhu ai ba kowa ne ya yi ba banda Xalhatu. Shi ma daga baya yayi nadama. Har ma aka wayi gari yana cikin sahun mutanen da ke matuqar girmama halifa Umar xin Raliyallahu Anhu kamar yadda masu qorafin can a kan jagorancin Zaidu da Usamata suka yi nadama a kai, kuma suka gyara saboda girman Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Bayan wannan kuma sai malamin ya ce, wai kuma matsala ta takwas ita ce kafa kwamitin da halifa Umar Raliyallahu Anhu yayi, don ya zavi halifa bayansa. Wanda wai kuma a qarshe bayan an yamutsa gashin baki, manbobin suka haxu a kan Usmanu Raliyallahu Anhu a matsayin halifa.

Martani:

Wannan magana na xaya daga cikin maganganun da malamai masana sirrin riwaya, suka haxu a kan kasancewarsu qarya tuburan. Domin kuwa babu wanda ya nemi tayar da hankali a kan halifancin Usmanu Raliyallahu Anhu saboda wai bai yarda ba. Illa dai Abdurrahamanu xan Aufu ya xauki tsawon kwana ukku yana tattaunawa da mutane. Inda yabi har matan Sahabbai a gidajensu, yana neman shawarar su. A qarshe aka tabbatar masa da cewa an gamu da Usman ya zama halifa Raliyallahu Anhu. To kuma ko da akwai wanda ke qyamar halifan a zuciyarsa, ba a samu wanda ya riwaito hakan ba. Kai! Hasali ma dai babu abin da aka faxa a kan wannan al’amari, da ya kawo kunnenmu.

Amma kuma duk da haka, ba mu cewa wani bai yi wani qorafi ba, koda a zuci. Tunda irin wannan al’amari na neman shawara wurin jama’a ya gadi haka.

Sannan kuma malamin ya ce wai ko bayan waxannan matsaloli. Wasu matsalolin sun faru da dama. Waxanda suka haxa da: Mayar da Hakamu xan Umayyata da halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ya yi a Madina, bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kore shi. Wanda har mutane ke yi masa laqabi da “Zakkar Manzo”. Kuma wai halifan ya yi haka ne, tattare da neman halifa Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma da ya yi, a lokacin halifacin da su yi wa Hakamu xin afuwa. Amma abun ya faskara. Kuma ma wai halifa Umar Raliyallahu Anhu bai tusaya ga qin yi masa Afuwa ba. Har qarawa yayi da shi gaba, daga inda yake zaune a Yamen, da tsawon zango arba’in.

To abin da za mu ce a nan shi ne: Wannan mas’ala ba ta isa a kira ta savani ba. Abin da har za’a xauka a kai shi da nisa. Balle a ambace ta matsala. Idan kuwa har aka yi haka. To kenan, duk wani hukunci da wani halifa ya yanke, wasu Sahabbai suka saba da shi a fahimtar abun ya zama “matsala” kenan ko?

To dama irin wannan, har gwamma a ambaci banbance-banbancen fahimtar da aka samu tsakanin Sahabban, a kan wasu mas’alolin gado da saki da wasu mas’aloli irinsu. Waxanda suka fi inganci a riwaya, da amfani ga mutane. Eh! Waxannan mas’aloli da ire - irensu su ne mafi inganci mana, da tabbata. Saboda ma’abuta ilimi sun riwaito su. Wanda kuma har yau mutane na bitar su, tare da amfanuwa da taskokin da ke cikinsu na ilimi, a matsayinsu na duwatsun murhun shari’a, da ake iya qara wa juna ilimi a cikinsu.

Savanin irin waxannan qananan abubuwa, daba su isa a kalli banbance - banbancen fahimta a cikinsu, a matsayin wani abu daya cancanci tautaunawa don qara wa juna ilimi ba.

Amma fa duk wannan sharhi da muke yi muna yin sa ne, tattare da yaqinin da muke da shi a kan cewa duk waxannan abubuwa da ya faxa game da Hakam, qorarsa, laqabinsa, nemar masa afuwa, qiyawa da qarawa dashi gaba, duk qarya ce.

Idan kuwa xan Shi’ar ko shi shahrastanin naji zancen gaskiya ne, to su gaya mana asalin wanda ya riwaito shi, da isnadinsa, da lokacin da ya tafi yeman xin, da dalilin da ya sa aka iza qeyarsa can. Alhali Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa mazauni a Xa’ifa, kamar yadda suke cewa. Gashi kuma ya tafi Yemen xin zama kusa ga Makka da Madina.

Eh mana! A gaya mana dalilin da zai sa a matsa dashi can bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya aje shi kusa dashi. A gaya mana.

To kuma duk aje wannan. Ma’abuta ilimi sun tabbatar cewa, wannan magana da ‘yan Shi’ah ke yayatawa, ta cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya kore Hakamu zuwa Xa’ifa ba gaskiya ba ne, shi ne ya tafi a son ransa. Sannan kuma wani abu da zai tabbatar ma ka da cewa maganar tatsuniya ce. Shi ne kasawar waxanda suka ce Manzon ya yi masa korar, daga ambaton wani isnadi ingantacce, a kan yadda al’amarin ya faru dalla-dalla.

Sannan kuma malamin ya ce, wai daga cikin matsalolin, akwai korar da halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ya yi wa Abu Zarri zuwa Rabaza. Da aurar wa Marwanu xan Hakamu ‘yarsa da ya yi. Tare da dunqule wasu ganimomi biyar da aka samo daga Afrika, ya danqa masa. Waxanda qimarsu ta kai dinari dubu xari biyu.

Martani:

Ita maganar Abu Zarri da barin garin Madina da ya yi, mun riga mun yi bayani a kanta dalla-dalla a baya kaxan.

Wannan kenan. Sannan kuma me ya haxa aurarwa Marwanu da ‘yarsa da al’amarin musulmi, balle ace hakan ta haifar da wata matsala a tsakaninsu? Sannan zancen ganima biyar ta Afrika da yaba shi, daga ina aka samo ta? Abin da suke faxa can farko shi ne halifan yaba shi dinari dubu biyu. Ka ga an sami savani nan take. To kuma ko a haka, ai kowa ya san waccan ganima ba ta kai wannan qima ba.

Bayan wannan kuma sai ya ce: Kuma daga cikin matsalolin akwai bayar da mafaka da halifa ya yi ga Abdullahi xan Sa’adu bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya halarta zubar da jininsa. Wai ma kuma halifan ya naxa shi gwamnan Masar bayan haka.

Martani:

Idan xan Shi’ar na nufin har zuwa lokacin da halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ya tura Abdullahi xan Sa’ad xin Masar a matsayin gwamnansa, jinin nasa na nan halattace. Kamar yadda maganar tasa ke nunawa, to qarya yake yi. Kuma hakan ta qara tabbatar da kasancewarsa jahilin tarihin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin kuwa gaba xayan mutane; soja da farar hula a fagen sani sun yi ittifaqi, a kan cewa, an karvi tubar Abdullahi xan Sa’ad. Suka ce bayan da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya shelanta halartar zubar da jinin waxansu mutane da dama, a ranar da aka ci garin Makka da yaqi. Kuma a cikin mutanen nan har da Abdullahin nan. Bayan xan lokaci sai Usman Raliyallahu Anhu ya taho dashi wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya roqar masa afuwa. Shi kuma yayi mubaya’a. A qarshe kuma ya kulle amana da musulmi; ta a faxi a tashi tare. Daga nan sai jininsa ya koma haramtacce.

Sannan kuma malamin ya ci gaba da cewa: Kuma halifa Usmanu ya naxa kwamandan Askarawansa, Mu’awiyah xan Abu Sufyanu gwamnan Sham. Ya kuma kai Sa’ad xan Abu waqqasi Kufa. Ya kuma maye gurbinsa da Abdullahi xan Amru daga baya. Ya kuma tura Walidu xan Uqubata Busrah.

To abin da za mu tabbata wa xan Shi’ar a nan shi ne, halifa Umar xan Khaxxabi ne farkon wanda ya naxa Mu’awiyah gwamnan Sham bayan rasuwar xan’uwansa Yazidu xan Abu Sufyanu, wanda ke gwamna a can. Iyakar abin da halifa Usmanu Raliyallahu Anhu ya yi shi ne tabbatar ma sa da ci gaba da riqon Sham xin tare da haxe masa baki xayan sassanta. Kuma Mu’awiyah ya zauna da mutanen wurin zama na madalla; tarihin zamansa dasu cike yake da abubuwa masu faranta rai. Wanda hakan ta sa talakawan nasa ke matuqar girmama shi, da qaunar shi.

Ka ga ashe Mu’awiyah ya sami babban rabo musamman idan aka yi la’akari da abin da ya tabbata a cikin Buhari, a ingantaccen hadisin da aka samo daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama wanda ya ce: Zavavvu daga cikin shugabaninku sune waxanda kuke so, suke kuma son ku. Kuke kuma yi masu fatar alheri, suma suke yi maku.

Kuma tabbas tarihi ya tabbatar da cewa talakawan Mu’awiyah Raliyallahu Anhu suna matuqar sonsa tare da yi masa addu’a da fatar alheri. Haka shima, son da yake masu ne yasa ya riqa su da aminci, har ma yake masu fatar dauwama cikinsa ko bayansa.

Shi kuma zancen abin da ya faru tsakanin Sa’id xan Asi, wanda halifa Usman Raliyallahu Anhu ya naxa gwamnan Kufa, da talakawan nasa, abu ne sababbe. Mun riga mun faxa maku cewa su miyagun mutane ne asalatan. Babu gwamnnan daya tsira daga qorafe - qorafensu. Sa’ad xan Abu Wakkas, da Abu Musa al-Ash’ari da Ammaru xan yasir da Mugirata xan Shu’ubata duk sun zauna da mutanen Kufa, a matsayin gwamnoninsu. Amma babu wanda ya kwashe lafiya dasu. Sun shahara da irin wannan matsala. Illa dai abin nasu yafi qamari a lokacin halifa Usmanu Raliyallahu Anhu amma kuma ko Ali Raliyallahu Anhu bai tsira daga sharrin suba. A matsayinsa na wanda shima yaba makusantansa muqamai kamar yadda Usman Raliyallahu Anhu yayi.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: kuma shahrastani ya ce: matsala ta tara kuma ita ce wadda ta faru a zamanin Sarkin Musulmi Ali Raliyallahu Anhu wadda ta haxa da: Tashin da Xalhatu da Zubairu suka yi zuwa Makka, bayan an zaxi Ali Raliyallahu Anhu a matsayin halifa har kuma an yimasa bai’a, da kuma xaukar sayyida Aisha Raliyallahu Anhu da suka yi kan Raqumi zuwa Busra. Da kuma dagar da suka shiga da halifan. Wadda aka sani da suna “Yaqin Basasar Raqumi”. Da kuma savanin da ya shiga tsakaninsa da Mu’awiyah Raliyallahu Anhu wanda a qarshe ya haifar da “Yaqin basasar Siffin”. Da kuma warewar da Amiru xan Asi ya yi wa Abu Musa al-Ash’ari.

Sai kuma savani daya faru tsakanin halifan da la’anannin Marikawan nan a Nahrawan.

Amma dai a taqaice, duk waxannan abubuwa da suka faru, Ali Raliyallahu Anhu shi ne mai gaskiya. Sai gashi kuma mutane irin su: Ash’as xan Kaisa da Mus’ir da Fadqi at-Tamini da Zaidu xan Huswain ad-da’i da wasunsu dake tare dashi, sun yi masa tawaye da sunan Harijawa. Bayansu kuma, duk a zamanin nasa aka sami “Gulatu” irin su Abdullahi xan Saba’i. Waxannan qungiyoyi biyu sune mafarkacin kowace irin fitina da varna. Kuma a haka sa maganar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yayi a kansa ta tabbata. Inda ya ce: mutum biyu za su halaka a kanka; wanda ya wuce wuri a cikin sonka da wanda ya zurfafa a cikin qinka.

Xan Shi’ar ya kammala wannan magana da cewa: don Allah ka dubi maganar wannan mutum (Shaharastani) da idon basira. Za ka fahimci cewa waxannan tsoffin bariki (halifofi uku kafin Ali Raliyallahu Anhum) su ne ummul-haba’asin duk wata fitina da ta faru a tarihin musulunci. Kar ka daxa kar ka qara.

Martani:

Eh; to. Wannan ra’ayinka ne. Amma a qashin gaskiya, duk wanda ya dubi wannan magana ta Shahrastani da idon adalci. Zai fahimci cewa marubucin ya shirya littafin ne kawai don ya tallata Shi’ah. Kamar yadda muka riga muka vulguta maku tun farko. Ah! To idan ba haka ba. Ai ya ambaci Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhu fiye da sau shurin masaki. Amma baice “suke da gaskiya ba”. Amma nan take, daya kawo kan Ali Raliyallahu Anhu sai ya yanke hukuncin cewa shi ne mai gaskiya. Kamar dai an naxa shi Alqalin alqalai.

Ka kuwa san ga al’ada, idan ba wata manufa kega marubuci ba, a matsayinsa kuma na mai bayar da labari, to baya wuce faxin abin da kowa yayi, da abin da aka yi masa. Amma duk wanda kaji ya kutsa wannan duhun daji, daga cikin musulmi. A qarshe kuma ya buye ga cewa: Gaskiya na tare da Ali, yana kuma tare da ita Raliyallahu Anhu su kuwa Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhu to!---. Ka tabbata xan Shi’ah ne.

Kuma wani abin da ke tabbatar maka da cewa wannan magana qarya ce shi ne, cewar da Shahrastanin ya yi wai: Sai da aka daddale magana a kan zaven Ali Raliyallahu Anhu har aka yi masa bai’a. Sannan qura ta muske. Alhali kuma a haqiqanin gaskiya mafi yawan musulmi, har daga cikin mutanen Makka, ba su yi masa mubaya’a ba. Fita batun waxanda ke nesa. Irin mutanen Sham da Masar da Magrib da Iraqi da Khuransa.

Irin wannan magana ta haxuwar kan jama’a gaba xaya, bata faxuwa a kan Ali Raliyallahu Anhu kamar yadda take faxuwa a kan halifa Usmanu Raliyallahu Anhu wanda ba a sami mutum xaya daya qi goyon bayansa ba.

Wani abun kuma dake tabbatar da rashin gaskiyar Shahrastani a cikin wannan magana shi ne, sukar lamirin daya yi wa xalhatu da Zubairu da Aisha Raliyallahu Anhu ta hanyar wanka da kamar jirwaye. Ba tare da ya fito da al’amarin fili yadda ya faru ba. Alhali kuwa ma’abuta ilimi na qwarai, sun kwana da sanin cewa Xalhatu da Zubairu basu fita da nufin su yaqi Ali ba Raliyallahu Anhu Abin ya zamar masu dole ne, a matsayin kariyar kai. Haka suma mutanen Sham basu fita da niyar yaqar saba. Allah kawai ya qaddara haka ta faru. Shi Alin Raliyallahu Anhu ba nufinsa ne ya yi yaqi da waxancan ko waxannan ba. Qaddara ce kawai ta riga fata.

Malaman da suka naqalci zahiri da baxinin tarihin musulunci, sun bayyana cewa yaqin Raqumi ba yaqi ne ba. Rikici ne kawai na cikin gida. Koka ce masa “Yaqin Basasa” kamar yadda muka ambace shi a farko.

Dalili kuwa inji malaman shi ne; gaba xayan vangaroran biyu sun haxu ne, domin daddale yarjejeniyar da suka yi. Da shata yadda za a yi a kama makasa halifa Usmanu a hukunta su. Don a sami zaman lafiya; kowa yabar jin qaiqayi a ransa. A cikin wannan dufulomasiyya, sai makasan nasa, dake cakuxe cikin musulmi, suka tabbata cewa, idan suka yarda aka zartar da wannan yarjejeniya, lalle kashin su ya bushe. Saboda haka bari su sake tayar da wata fitina kamar yadda suka tayar da ita farko.

Sai nan take, suka kai farmaki kan Xalhatu da Zubairu da mutanensu. Su kuma suka yo kukan kura don su kare kansu. Sai makasan suka yi tururuwa, daga cikin jama’ar Ali Raliyallahu Anhu da cewa ga su Xalhatu nan za su far ma su. Nan take sai kuma Ali Raliyallahu Anhu ya sa qaimi, mutanensa, har da su makasan, suka rufa masa baya, a matsayin su ma masu kariyar kai, aka yi karon battar qarfe.

Subhanallahi. Allah ka kiyashe mu da halin munafukai.

Iyakar guri da niyyar kowane vangare kenan; kariyar kai. Amma ba yaqi ba.

To tunda ko har haka ne. Ka ga al’amarin sai hamdala da hauqala. Kuma kame baki daga gareshi shi yafi. Tunda Alqur’ani da Sunnah sun bayyana cewa, su zavavvu ne a wurin Allah, na kirki ne, ‘yan aljanna.

 2.60 ‘Yan Shi’ah na Taimakon Kafirai a Kan Musulmi

Bari mu fara da inda xan Shi’ar ke cewa: “Ka dubi maganar wannan mutum da idon basira da adalci. Za ka tabbatar cewa waxannan tsoffin bariki, yana nufin halifofi uku na farko, su ne ummul haba’isin wannan fitina”.

Martani:

 Zancen fitina a cikin musulunci, ko na-goye ya kwana da sanin cewa, ‘yan Shi’ah ne mafarinta. Babu wata fitina ko wani sharri da ya faru ga wannan al’umma, face ka taras da cewa su ne kanwa uwar gami a ciki. Domin kuwa ai wutar fitinar farko da ta kama a tarihin musulunci, su ne suka hasa ta, don su ne suka kashe halifa Usmanu Raliyallahu Anhu.

 Imamu Ahmad ya riwaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: “Fitinu uku, duk wanda ya tsira daga cikinsu to, shi ne tserarre. Mutuwata, da kisan wani halifa a kan zalunci, da kuma Dujjal”.

 Wannan kenan. Wani abu kuma dake tabbatar da kasancewar maganar wannan xan Shi’ah qarya shi ne, duk wanda ya bibiyi diddigin tarihin qungiyoyi a duniya, zai tabbatar cewa, Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama mutane ne da Allah Subhanahu WaTa’ala ya shaida a cikin Alqur’ani da kasancewa mafiya alheri daga cikin halitta, kamar inda yake cewa:

﴿كُنتُم خَيرَ أُمَّةٍ أُخرِجَت لِلنَّاسِ تَأمُرُونَ بِٱلمَعرُوفِ وَتَنهَونَ عَنِ ٱلمُنكَرِ وَتُؤمِنُونَ بِٱللَّهِ وَلَو ءَامَنَ أَهلُ ٱلكِتَبِ لَكَانَ خَيرا لَّهُم مِّنهُمُ ٱلمُؤمِنُونَ وَأَكثَرُهُمُ ٱلفَسِقُونَ١١٠﴾ آل عمران: ١١٠

Kun kasance mafi alherin al’umma, wadda aka fitar ma mutane; Kuna umurni da Alheri, kuma kuna hani daga abin da ake qi, kuma kuna imani da Allah (3:10).

 Su ne mutanen da suka fi kowa son zaman lafiya. Domin kuwa ba a tava samun jama’a wadda kanta ya haxu a kan shiriya, da faxaka da nisantar fitina da savani da rarrabuwar kai, a tarihin duniya kamar su ba.

 Haka kuma kundin tarihin ya tabbatar da cewa ‘yan Shi’ah sun fi kowa nisa daga shiryayyar qungiya wadda Allah ke taimako.[59] Hakan kuwa ta faru ne a sakamakon kasancewarsu mafiya jahilci da zalunci daga cikin qungiyoyin shexan, waxanda ke iqirarin kasancewa cikin musulmi masu mayar da gaba gabas su yi sallah.

 Haka kuma ya tabbata cewa, zavavvun wannan al’umma su ne waxancan Sahabbai. Sun kuwa samu wannan sheda da matsayi a sakamakon kasancenwarsu shafe zane a fagen zama tsintsiya maxaurinki daya, a cikin shiriya da addinin gaskiya. Tare da yin matukar nesa-nesa daga xai-xaicewa da zaman 'yan marina. Duk kuwa wani abu na tasgaro da kasawa, da wani zai ce ya faru daga waxannan mutane, ba zai wuce ajizanci irin na xan Adamu ba. Kuma da za a kwatanta shi da wanda ya faru daga wasunsu, za a taras da bai taka kara ya karya ba.

Fita batun duk wani abu da mutum zai qaddara a cikin zuciyarsa, ya kuma nace a kan kasancewarsa, alhali Allah Subhanahu WaTa’ala bai halicci mai irin wannan abu a cikin qanana da matsa kaita da manyan bayinsa ba. Kamar abin da waxansu ke cewa, wai lallai ne shugaba ya kasance ma'asumi. Wasu kuma su ce, a’a, ko dai bai kai ma'asumi ba, ya kasance xan qwarya-qwarya. Kai wasu ma za ka taras suna jin cewa, ya kamata duk yadda malami ko shehi ko shugaba ko sarki ya qasura, tattare da yawan iliminsa da kishin addininsa da yawan ayyukansa. Duk da haka su a wurinsu lalle ne ya kasance ya san komai, ta yadda ba ya kure a cikin kowace irin mas’ala. Ya kuma fita daga layin mutane, ta yadda babu abin da zai vata masa rai balle ya yi fushi. Kai da yawa daga cikin irin waxannan mutane ma ke gurin shugaba ya siffanta da wata sifa da ko Annabawa albarka.

Ka ga wannan ya sava wa hankali. Domin kuwa ai Allah Subhanahu WaTa’ala umurtar Annabi Nuhu da Muhammadu Alaihimus Salamu Ya yi da su ce:

﴿وَلَا أَقُولُ لَكُم عِندِي خَزَائِنُ ٱللَّهِ وَلَا أَعلَمُ ٱلغَيبَ وَلَا أَقُولُ إِنِّي مَلَك وَلَا أَقُولُ لِلَّذِينَ تَزدَرِي أَعيُنُكُم لَن يُؤتِيَهُمُ ٱللَّهُ خَيرًا ٱللَّهُ أَعلَمُ بِمَا فِي أَنفُسِهِم إِنِّي إِذا لَّمِنَ ٱلظَّلِمِينَ٣١﴾ هود: ٣١

Kuma ba ni ce muku a wurina taskokin Allah suke, kuma ba ina sanin gaibi ba ne. Kuma ba ina cewa ni mala’ika ne ba. (11:31).

 Amma kuma tattare da wannan magana, sai ka taras da jahilai daga cikin mabiya na gurin shugabansu ya kasance masanin duk abin da za’a tambaye shi, mai iko a kan duk abin da za’a nemi ya yi. Ya kuma wadatu daga duk wasu buqatu irin na ‘yan Adamu; wato ya dai zama kamar mala’ika. Irin wannan guri da fata da wasu mabiya ke yi wa shugabanninsu, daidai yake da fatar da Harijawa ke yi wa al’umma baki xaya, wato kada wani ya aikata wani zunubi daga cikinsu. Wanda kuwa duk ya aikata, to a wurinsu ya kafirta kuma xan wuta ne har abada.

Da wannan matsayi na Harijawa da wancan na ‘yan Shi’ah da wasunsu daga cikin qungiyon bidi'a, duk vata ne. Allah Subhanahu WaTa’ala bai halacci irin waxannan mutane ba, balle ya shari’anta irin waxannan siffofi.

Harwayau kuma dai, muna qara nanatawa. ‘Yan Shi’ah su ne matattarar vata da danbarwa, fiye da kowace qungiya daga cikin qungiyoyin da ke jingina kansu ga wannan al’umma. Kamar yadda su kuma ma'abuta hadisi da tantagaryar Sunnah, su ne matattarar shiriya da sawaba da rahama fiye da kowace qungiya daga cikin qungiyoyin wannan al'umma. Wanda hakan ta sa duk motsin da za su yi, lalle ne ya kasance taimako ga sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama don ba su da kowa sai shi. Shi ne shugaba a garesu na qarshe. Ba su sauraren maganar kowa, sai idan ta yi muwafaqa da tashi. Kuma fatarsu kodayaushe ita ce taimakon addinin Allah da sunnar Manzo.

To, ka ga a hankalce, idan Sahabbai da ma’abuta hadisi da tantagaryar sunnah, sun kevanta da kasancewa ma’abuta shiriya da addinin gaskiya, mafiya nisantar qungiyoyi daga shiriya su ne masu zagin su.

A haka kenan, ta bayyana ga dukkan mai hankali cewa, maganar wannan xan Shi’ah shirme ne kawai irin wadda babu mai kafa hujja da shi sai jahili. Haka kuma ta bayyana cewa marubucin, son rai ne yake bi, illa iyaka. Ga shi kuma bai san kome ba a cikin fannin riwaya. Matsayinsa bai wuce na masu bada qissoshi a cikin masallaci ba.

Su dai ‘yan Shi’ah an sani cewa, munafukai ne da suka shigo musulunci da nufin gurvata shi. Saboda haka suka qirqira qarairayi, suka haifar da miyagun ra’ayoyi don cimma wannan manufa tasu, ta qasqanta duk wanda ke kan tafarki madaidaici. Saboda haka suka fara da kashe halifa Usmanu, wanda shi ne xaya mafarin qirgar fitina. Bayan haka sai suka koma suka kewaye Ali Raliyallahu Anhu da sunan so da qauna gare shi da 'yan gidan Manzon Allah, alhali kuwa manufarsu ita ce girka sanwar fitina a tsakanin musulmi.

 Wannan dalili ya sa za ka taras da 'yan Shi’ah kodayaushe suna goyon bayan kafirai da waxanda suka yi ridda. Kamar yadda suka goyi bayan Banu Hanifata mabiyan Musailamatul-Kazzabi, suka ce wai musulmi sun zalunce su, a qarqashin shugabancin Abubakar Raliyallahu Anhu kamar yadda marubucin ya ce. Haka kuma za ka same su suna goyon baya da jin-jina wa kasurgumin kafirin nan Abu lu’uluatal Majusi wanda ya kashe sayyidina Umar.

 Bari kaji yadda abin ya kasance: An riwaito cewa, Abu lu’uluata ya nemi halifa Umar ne da ya sa baki tsakaninsa da masu karvar haraji, don a sassafta ma shi. Halifa Umar ya yi niyyar sa bakin, amma kafin haka sai qiyayyar da ke kimshe cikin zuciyar Bamajushen zuwa ga musulunci da musulmi ta yunquro masa. Sai kawai ya kashe halifa Umar, saboda ya xaukar wa kafirai fansar fatattakar da Umar xin ya yi masu lokacin da ya ci qasashensu, inda ya karkashe shugabanninsu ya kuma rarrabe dukiyoyinsu a tsakanin musulmi.

Ka ji aika-aikar da Abu Lu’ulu’ata ya yi. To, don Allah kai kana ganin akwai wanda zai kalli irin wannan bawa da gashi a ka, balle har ya koxa shi, in ba mafi girman kafirce wa Allah da Manzo daga cikin mutane, da qiyayya da musulunci, da kai matuqa ga jahiltar al’amurransa ba?.

To, mu fita batun ma wannan, da duk wani abu da a ke ji ko ake karantawa wanda ya faru tsawon shekaru, duk mai hankali da ya dubi abin da ke faruwa yau a zamaninsa, da wanda ya faru jiya kaxan na fitinu da sharri da varnace-varnace a cikin musulunci, zai taras da cewa ‘yan Shi’ah ne suka haddasa mafi yawansa. Zai kuma tarar da cewa aikinsu kenan: duk abin da zai jefa wannan al’umma cikin wutar fitina da sharri da varna, to suna lale marhabin da shi.

Mu mun sheda, mun kuma ji ta lafiyayyun hanyoyi, abin da ya faru a wannan zamani namu. Mun ga irin yadda Jankizkhan sarkin kafiran Turkawa ya danno, da irin mugun abin da ya faru ga musulunci, na mamayewar da kafirai mushrikai suka yi wa qasashen musulmi. Suka taka dangin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Hashimawa da Banul Abbas yadda suke so. Suka kashe na kashewa, suka raunata na raunatawa. Suna da ribaci mata muminai suka halatta farjojansu. Qananan yara kuwa suka shigar da su cikin addininsu, tare bautar da su.

Wannan duk ban da karkashe malamai da suka yi da fitattun makarantan Alqur’ani da wargaza masallatai. Daga sai suka samu damar xaukaka darajar gidajen gumaka waxanda suke yi wa laqabi da Al-Bazkhanat, da wuraren ibadar Yahudawa da ‘yan mishan. Kai da waxansu abubuwan da dama, waxanda ba su da daxin faxi.

Kuma duk mai hankali ba ya shakkun cewa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zai dawo duniya, ya ga wannan illa da ta faru ga al’ummarsa lalle zai yi baqin ciki fiye da wanda zai yi, a kan musulmi biyu da suka shaya daga tsakaninsu saboda tabbatar da mulki na gari. Dalili kuwa shi ne su waxannan yaqe-yaqe na basasa, babu wani vangare daga ciki da aka ribace matansa, ko aka keta alfarmarsa. Kuma ba su qari wani kafiri da komai ba. Kamar kuma yadda ba su rosa wasu shari’o’i mutawatirai, bayyanannu na musulunci ba.

Ka dubi girman wannan al’amari. Ya kuma faru bisa ga gayyata da tallafi na musamman daga ‘yan Shi’ah. Haka kuma mutane sun sheda a lokacin da Holaku Sarkin kafiran Turkawa ya shiga qasar Sham a shekara ta 658H. ‘Yan Shi’ah da ke cikin Sham a birane da qauyuka, waxanda suka haxa da mutanen Halab da maqwabtanta da na Dimashqu da kewayenta, su ne suka zama manya-manyan dakarun da waxannan kafirai suka yi amfani da su ga tabbatar da mulkinsu, bayan sun roshe na musulmi.

Haka abin ya kasance a lokacin da Holakon ya isa qasar Iraqi, ya kashe halifa da musulmin da Allah ne kaxai ya san adadinsu. Babba da yaro, kowa ya san cewa a wannan lokaci, wazirin halifan ne, wato Ibnul-Al-qami xan Shi’ah da mutanensa suka mara wa wannan kafiri baya, suka taimake shi ta hanyoyi daban-daban, na voye da na bayyane. Waxanda faxarsu ba za ta yiwu ba, ko wani sarki ya ci ya fita.

Haka kuma an tabbatar mana da cewa, ‘yan Shi’an sun ci gaba da kasancewa tare da Jankizkhan, don musulmi na ganin su tare kodayaushe, a cikin sasannin Sham da sauran garuruwa.

 Kai! Babu wani lokaci da musulmi za su shaya daga da Nasara, face ‘yan Shi’ah sun yi qawance da Nasaran, tare da ba su kowace irin gudunmuwa gwargwadon ikonsu. Suna baqin ciki da qyamar su ji an ci wani gari na Nasara da yaqi. Kamar yadda suka qyamaci cin garin Akka da ire-irensa. Kai kama hannun Nasaran ma suke yi suna nuna masu inda musulmi suke. Akwai ma wani lokaci da aka yi qanfar rudunar musulmi a Sham, a shekara ta 599H. Ganin haka sai ‘yan Shi’ah suka bazu a cikin garuruwa suna ta varna da masha'a ta hanyar kashe Ahlus-Sunnah da qwace dukiyarsu. Tare da kaxa tutar da ke xauke da hoton kuros a sama, da kururuta fifikon Nasara a kan musulmi. Qarshe ma har ribace musulmi da dukiyoyinsu da makamansu suka xora yi suna kai wa Nasara abokan gaba, a Qubrus da wasu garuruwa.

 Mutane da yawa sun shedi waxannan abubuwan da makamantansu. Wanda kuwa bai ganar wa idonsa ba, ya ji ta hanyoyi mutawatirai. Wallahi da zan ambaci gaba xayan abin da na gani da wanda na ji a kan wannan lamari da wannan littafi ya gagari kundila. Na kuma tabbata mutane da yawa sun san wasu abubuwa filla-filla na wannan labari, waxanda ban sani ba.

Taimakon da ‘yan Shi’ah ke yi wa kafirai a kan masulmi da irin yadda suka fi qaunar ganin kafirci da kafirai sun bice hasken musulunci da musulmi abu ne da ya fi rana bayyana idan ta fito.

Mu qaddara cewa musulmin da ‘yan Shi’ah ke wannan matsananciyar gaba da su, azzalumai ne kuma fasiqai, waxanda kuma ke bayyanar da nau’o’an bidi’o’i waxanda suka fi zagin Ali da Usmanu Raliyallahu Anhuma nauyi. Duk da haka, da a ce ‘yan Shi’ah mutane ne masu hankali, kamata ya yi su auna irin sharrin da wannan aiki nasu zai haifar, da alherin da ke cikin rashin yin sa.

Ai ka ga su Ahlus-Sunnah, da yake mutane ne masu cikar hankali, tattare da abin da suke faxa na kasancewar Harijawa da ‘yan Shi’ah da wasunsu daga cikin mutanen bidi'a karkatattu, ba su tava taimakon kafirai a kan xaya daga cikinsu ba, balle su guraci rinjayen kafirci da kafirai fiye da yadda wata ‘yar qaramar bidi'a za ta bayyana. Don sun san haka rosa kai ne.

Su kuwa ‘yan Shi’ah da xai haka suke. Idan suka sami sa’a ba su iya ba. Dubi abin da suka haifar na varna a zamanin daular sarki Khudabandah, wanda aka rubuta wa wannan littafi, da muke martani a kansa. Sharrin da waxannan mutane suka qulla a wannan lokaci, da ya tabbata ya kama qasa sosai, da gaba xayan shari’o’in musulunci sun kwanta dama! Sai dai da yake ta Allah ba tasu ba; kullum suna qoqarin bice hasken Allah ta hanyar amfani da kaifin halsunansu, amma Allah na daxa tabbatar da haskensa, ko da kafirai sun qi.

Su kuwa halifofi da sauran Sahabbai su ne tushen duk wani alheri da musulmi ke ciki a yau har Allah Ya naxe qasa. Su ne suka yi jihadi fi sabillillahi, har hasken imani da musulunci da Alqur’ani da sauran fannonin ilimi, da ibadodi suka kammala, dashensu ya haxu ya yi kyau ya barbaje. Musulmi suka yi galaba a kan kafirai, kalmar Allah ta xaukaka, aljanna ta tabbata ga musulmi wuta ta nisanta daga gare su. Gaba xaya aikin da Sahabban can suka yi na yaxa addini, shi ne ya tabbatar da wannan.

A kan haka babu wani mutum da ya yi imani da Allah face Sahabbai nada kamisho da falala a cikin haka har rana ta qarshe. Kai su kansu ‘yan Shi’ah, duk wani abu na alheri da suke cikinsa, sun same shi ne albarkacin waxannan Sahabbai. Su kuma halifofin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shiryayyu, su ne kan gaba a sahun wannan alheri da aka samu ta hanyar Sahabbai. Domin kuma a duniya da lahira babu wani Sahabi da ya kamo qafarsu a fagen aikata alheri da dasa shi. To, ta yaya za a wayi gari yau a ce mana su ne mavuvvugar sharri, su kuma ‘yan Shi’ah wai su ne mavuvvugar alheri?

Alhali kuwa sanannen abu ne cewa, shi wannan xan Shi’ah yana bisa turbar waxancan ‘yan Shi’ah ne, ta qin jinin Sahabbai. Ashe wannan ba yana nuna kasancewarsu mafi sharrin waxanda Allah Ya toshe wa basira ba?:

﴿ فَإِنَّهَا لَا تَعمَى ٱلأَبصَرُ وَلَكِن تَعمَى ٱلقُلُوبُ ٱلَّتِي فِي ٱلصُّدُورِ٤٦﴾ الحج: ٤٦

Domin haqiqa makanta ba ta idanu ba ce, amma makanta (ta gaskiya) ita ce makantar zukata waxanda ke cikin qiraza (22:46).

 3.0 ZANGO NA UKU: DALILAI NA HANKALI

Xan Shi’ar ya ce: Fasali na uku wanda zai yi magana a kan dalilan da ke tabbatar da cancantar sarautar Sarkin Musulmi Aliyu xan Abu Xalib, shugaba bayan wucewar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Duk da yake waxannan dalilai na da matuqar yawa, ta yadda ba za a iya qididdige su ba. Saboda haka za mu ambaci mafi muhimmanci daga cikinsu, ta hanyar karkasa su gida huxu. Inji shi:

Waxannan dalilai guda biyar ne. Na Farko: Lalle ne duk wanda zai shugabanci al’umma bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a matsayin Imamu, to, ya kasance ma'asumi. Wannan dalili kuwa shi zai tabbatar da cancantar Aliyu Raliyallahu Anhu da wannan kujera.

“Dalilinmu a kan goshin wannan magana inji xan Shi’ah, wato wajabcin samar da shugaba ga jama’a da zancen kasancewarsa ma'asumi shi ne: Kasancewar mutun wata halitta da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya sa wa son zama cikin taro, ta yadda rayuwarsa za ta yi qunci da tasgaro matuqa, idan ya ce zai rayu shi kaxai. Saboda buqatunsa na samun abin ci da sha, da sutura da wurin bacci kodayaushe, ba za su samu tabbatuwa ba, matuqar ya yi tsinbirin gata. Dole ne yana da buqata da gudunmawar wasu mutane irinsa, waxanda kowane daga cikinsu, har da da shi kansa, zai tsare wa xan’uwansa wata daga ta waxancan buqatu. Ta wannan hanya ce kuwa kawai jinsin xan adam zai iya ci gaba da wanzuwa a bayan qasa”.

“Irin wannan haxuwa kuwa, wuri xaya da nufin zama, ta gadi haifar da qeta da son kai. Ta yadda wasu daga cikin mazaunan za su yi qyashin abin da ke hannun wasu har ma su yi gurin gushewarsa ko dawowarsa a hannunsu ta hanyar qwace ko yaudara. Wanda hakan kan haifar da qunci da tajin-tajin da tashin fitinu. Ka ga a irin wannan yanayi, dole ne a samar da shugaba ma'asumi wanda zai hana mutane zaluntar juna da wuce iyakoki. Ya tabbatar da ganin kowa ya tsaya wurinsa tare da qwato wa wanda aka zalunta haqqinsa daga wanda ya yi zalunci da kuma sadar da kowane haqqi ga mai shi. Duk kuwa wanda zai hau wannan matsayi, lalle ne ya kasance ba ya kuskure ko mantuwa ko savo. Idan kuwa ya kasa cika waxannan siffofi, to zaune ba ta qare ba. Don har yau dai al’ummar na da buqata da wani shugaban ba shi ba. Domin kuwa toshe kafafen kurakuran a cikin al’umma ne dalilin da ya sa aka naxa shi, To, idan har kuwa shi ma irinsu ne, an yi faxuwar guzuma kenan ka ga dole a nemo wani shugaba wanda ba ya kuskure. Idan shi ma ya bi hanyar na gabansa, to babu hus. Haka al’amarin zai ci gaba da tafiya yana kwan-gaba kwan-baya”.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: “Shi kuwa abin da qirjin wannan magana ya qunsa, wato ma'asumancin Aliyu Raliyallahu Anhu a matsayin shugaba abu ne bayyanane. Domin kuwa babu xaya daga cikin Abubakar ko Umar ko Usmanu wanda ma’asumancinsa ya tusgo bisa haxuwar malamai. Amma ta tabbata cewa Ali Raliyallahu Anhu ma'asumi ne. Saboda haka shi ne ya kamata ya zama magajin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na farko”.

Martani:

Gaba xayan waxannan maganganu; goshin da qirjin, vatattu ne. Bari mu fara da farko, inda ya ce: Dole ne a samar da shugaba ma'asumi wanda zai hana mutane zaluntar juna da wuce iyakoki, ya tabbatar da ganin kowa ya tsaya wurinsa, tare da qwato wa wanda aka zalunta haqqinsa daga wanda ya yi zalunci, da kuma sadar da kowane haqqi ga mai shi. Ya kuma ce, duk wanda zai hau wannan matsayi, lalle ne ya kasance ba ya kuskure ko mantuwa ko savo.

To a nan sai mu ce: Mu ma Ahlus-Sunnah mun yarda da wannan dalili da ke wajabtar da samar da shugaba ga jama’a. Amma inda gizo ke saqa shi ne, wane ne ma'asumin? Amsa a nan ita ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma wajibi ne a kan kowane mutum a kowane zamani ya yi xa'a da biyayya gare shi. Kuma Alhamdu lillahi, abin da ke hannunmu na horo da hani, waxanda ya yi wa al’ummarsa, ya fi cika da kamala a kan abin da xaixaikun shugabanninku suka sani na horo da hani, waxanda voyayyen imaminku ya yi.

Ko shakka babu, shugabanci da ma'asumancin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama su ne mafiya bayyana da tabbata. Kuma ga shi babu wani daga cikin al’ummarsa wanda ya jahilci horace-horace da hane-hanen da ya yi. Magana ta qare. Wannan shi ne matsayinmu.

Su kuwa ‘yan Shi’ah, qololuwar abin da za su gaya maka a kan sha’anin nasu ma'asumin shi ne har yanzu bai riga ya bayyana ba, ana nan ana ta dakon isowarsa. To, ba wannan ma kawai ba. Babu wani mutum a duniya ko da kuwa daga cikin ‘yan Shi’an, da zai bugi qirji ya ce ya san wani horo ko hani daga wannan imami na voye, kamar irin yadda gaba xayan al’umma suke da cikakkar masaniya da shari’o’in da Manzonsu Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo masu da su. Ta yadda ba su da buqata da wani shugaba wanda ba shi ba. Ko wani Wanda zai yi labu da wasa da abubuwan da wannan addini nasu ya qunsa. Domin kuwa duk abin da suke da buqata da shi, don gudanar da ayyukan addini, Manzon ya riga ya zazzage masu shi. Ba kamar xaixaikun masu da’awar wancan shugaba ma'asumi ba, waxanda ba su san komai dangane da shi ba ko da an qaddara samuwarsa. Har yau dai baya ga Aliyu Raliyallahu Anhu babu wani daga cikin imaman can da ake wa gogen ma’asumanci, da ya tava jagorantar mutane a zahiri. Sai ko Al-Hasan da ya yi na wata shida.

 Muna da cikakkar masaniya kuma yankakka, cewa akwai mabiyan wannan imami voyayye, a qasar Yaman da Khurasana da waxansu qasashe, da ba su san abu xaya wanda ya yi umurni ko hani da shi ba. 'Yan korensa ne kawai ke wasa da hankalin mutane.

 Amma ka ga waxanda suka gaji ilimin da Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo wa duniya da shi, sun san komai a cikinsa filla-filla. Kuma suna sanar da sauran mutane shi tsakani da Allah; ba ragi ba qari, fiye da yadda waxanda ke waqen bin Ali Raliyallahu Anhu suka san matsalar da irin yadda suke isar da ita ga duniya. Iyaka kawai abin da suke qoqarin tabbatarwa shi ne wajabcin samar da shugaba ma'asumi a raye.

To, muna tabbatar masu da cewa, wannan magana tasu vata ce, ta fuskoki kamar haka:

Fuska ta farko: Ba a tava samun wani shugaba, a inda aka fito, da waxannan sifofi da suka zayyana ba. Haka kuma a wannan zamani namu. Wanda dai ke da waxannan sifofi shi ne wanda ko a wurin mabiyansa sunansa Malam-na-Voye, balle a wajen masu hankali a cikin al’umma. Su a wurinsu sunansa Malam-babu.

To duk kuwa wanda yake haka, babu wani abu daga cikin manufofin shigabanci, da ke iya tabbatuwa ta hanyarsa, asalatan. Kai duk wanda ma za a shugabantar wa mutane, ko da kuwa iliminsa da adalcinsa ba su taka kara sun karya ba, matuqar dai ga shi a sarari, to ya fi fa’ida gare su bisa ga irin wannan da babu wata hanya da zai iya amfanar da su da ita da komai.

Ko da kuwa mabiyan shi wannan ma'asumin voye, sai sun nemi gudunmawar wasu mutane a kan wasu al’amurra nasu. Waqen kasancewarsa majivincin al’amuransu kawai suke yi. Amma idan suka tashi neman wani agaji sai su nema daga wani qasurgumin kafiri ko azzalumi. Idan kuwa har wannan ma'asumi da ake jira ya kasa amfanar da ko waxanda suka yi imani da shi a cikin wani sha’ani nasu na duniya ko lahira, ba ta yadda za a yi ya iya tabbatar da wani abu na gallar shugabanci da manufofinsa ga wani.

To, idan ko har babu wata manufa daga cikin waxannan manufofi na shugabanci da ke iya tabbata ta hanyar Malam-na-Voye, to, kuma ba mu da buqatar tabbatar da hanyoyin rashin yiwuwar haka. Domin kuwa ba don guga tana guga ake sayenta ba. A’a sai don a jawo ruwa da ita. To idan kuwa har ta tabbata cewa babu wata rijiya a gari da ke da ko xigo na ruwa, to zancen guga vata lokaci ne. Kamar dai a ce ne ga mutane na buqatar agajin abinci da abin sha masu kama kaza. Kuma qabila kaza ce kawai ake iya samun su daga gare su. Amma kuma tarihi ya tabbatar da cewa ko veran masallaci ya san da zaman wannan qabila saboda tsananin rashi da talauci. Ka ga ai ba magana.

To kamar haka ne babu wata fa’ida da za’a samu a cikin neman duk wani abu da ake da masaniyar babu shi. Ko kuma biyayya ga wanda ba ya da amfani ko masoso. Ai ana buqatar shugaba ne don xayan abubuwa biyu: Ko dai don wani ilimi da ya kevanta da shi, don ya isar da shi ga mutane ta hanyar karantarwa. Abu na xaya kenan. Na biyu Kuma, ko don ya taimaki mutane da qarfin mulkinsa a kan aiki da wani ilimin da suka riga suka sani.

 To, shi wannan Malam-na-Voye da ake jiran bayyanarsa, ba ya iya amfanar da al’umma da xayan waxannan abubuwa biyu. Duk ma abin da suke da shi na ilimi, sun same shi ne daga cikin zantukan waxanda suka gabace shi. Ta fuskar aiki kuwa, sukan nemi gudunmawar musulmi ne, a cikin abubuwan da kansu ya haxu da nasu a ciki. Idan kuwa ba su sami haka ba, sai su nemi gudunmawar kafirai da zindiqai da makamantansu.

 Kar ka yi mamakin wannan magana tawa. Idan ba ka sani ba, Allah bai halicci mutane mafiya ragganci da jahilci kamar waxannan mutane ba, tattare kuwa da gogen da suke yi na kasancewa mabiyan ma’asumi. Alhali kuwa ita wannan kalma ta ma’asumi na nufin siffantuwa da cikakken ilimi da qarfin iko na aiwatarwa. Amma su, da ilimin da ikon ba su da ko xaya. Hakan kuwa ita ke tabbatar da koruwar duk abin da suke waqa. Kuma babu xaya daga cikin shugabannin da aka yi, wanda manufofin shugabanci suka tabbata ta hannunsa albarkacin xaya daga cikin waxancan imamai goma sha biyu. Idan kuma ka cire Ali Raliyallahu Anhu ka yi qasa da lissafi, za ka taras cewa, babu wani abu na ilimi ko kishin addini da suka qarar da mutane da shi, fiye da yadda takwarorinsu ke iyawa da yi. Abin da Zainul Abidina da xansa Baqiru da jikansa As-Sadiq suka kasance suna karantar da mutane a zamaninsu, daga cikin abin da Allah ya sanar da su, bai fi wanda sauran malaman zamaninsu ke karantarwa ba. Kai akwai malaman da ma suka fi su ilimi da amfanar da jama’a a wancan zamani. Babu wani ma’abuci ilimi da bai san haka ba.

To, ko da ma za a qaddara cewa sun fi kowa ilimi da kishin addini a wancan zamani, ai wannan ba wani abu ne ba. Domin tarihi bai ambaci wani tasiri da ma’abuta ilimi da kishin addini suka yi, a fagen tabbatar da mutane a kan gaskiya da hana su varna, ta hanyar amfani da qarfin iko ba, kamar yadda ma’abuta mulki suka yi.

 To, sauran imamansu bayan ukun da muka ambata, musamman ma dai biyun na qarshe, ba su da wani ilimi da tarihi ya tabbatar da al’umma ta qaru da shi, ko wani qarfi da ta yi shinge da shi. Matsayinsu bai fi na sauran Hashimawa ba, waxanda mutane ke gani da gashi a ka don kusancinsu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da fuskar dangantaka. Ilimin da su ke da shi na abubuwan da suke da buqata da su a musulunci, bai fi na sauran takwarorinsu ba. Shi ne kuma irin ilimin da fararen hula daga cikin musulmi ke da shi.

Amma abin da ma’abuta ilimi suka kevanta da shi na sannai, su ba su sami wani rabo daga cikinsa ba. Saboda haka ne ma ba a yi almajircin ilimi a wurin su ba, kamar yadda aka yi ga waxancan uku na farko. Da kuwa mutane a lokacinsu sun san akwai abin, da sun je nemansa. Amma ka san ba wanda ya san abin da ya ke buqata kamar mai neman ilimi

Wani abu da zai tabbatar maka da haka shi ne, duk wanda ke da ilimi da girman asali, za ka tarar da asalin ya taimaka ga kwararowar mutane zuwa gare shi don su qaru. Ai ka ga da yake xan Abbas na da tarin ilimi, al’umma ta ji ta kuma fa’idantu da shi. Kuma babba da yaro kowa ya ji sunansa.

Haka Imamus-Shafi’i, nasabarsa ta Quraishawa ta qara fitowa da shi fili, ilimin da ya ke da shi na fiqihu da sauran fannona ya bayyana, aka qaru da shi.

Amma da zarar mutum ya tarar da babu abin da yake nema a wurin da ya yo qarere, ko tashen batun ba zai yi ba. Yau da za a cika duniya da waqen cewa ai wane qwararren malami ne a fannin likitanci ko Nahawu, aka cicciva shi har wasu daga cikin masana likitanci ko Nahawu suka ziyarce shi. Amma suka tarar da cewa bai san abin da suke nema a cikin waxannan fannoni ba. za su koma inda suka fito ne. Ka ga koxa shi da xaukaka sunansa da jahilai suka yi bai daxa shi da komai ba.

Wannan kenan. Kuma sai Shi’ah ‘yan-sha-biyu suka tsallaka suka je wurin Mu’utazilawa suka aro wasu aqidu da suka danganci siffofin Allah da makamantansu. Ita kuma matsalar shugabanci sai suka azizita ta har ta fi Annabta matsayi a wurin su.

Suka ci gaba da cewa: Al’adu da shuxewar kwanuka sun tabbatar mana da sanin cewa, a duk lokacin da jama’a suke qarqashin jarumin shugaba wanda ake tsoro, ake kuma yi wa biyayya ko ba don Allah ba. Sai don iya shugabancinsa da shinfixa hannayensa. Haka ta fi sa su kasancewa mafi zama kusa ga shiriya da nisantar varna. Balle daxa idan babu shugaban baki xaya, sai a wayi gari qunci da yamutsi sun mamaye su, su kuma zama nesa qwarai daga shiriya.

To, ka ga wannan matsala ita ce kanwa uwar gami, a cikin sha’anin sa hankali gaba a cikin addini. Sanannen abu ne da ba mai musun sa, sai wanda ya jahilci halin rayuwa, bai kuma san qa’idar xorewar zaren tunani a cikin kai ba. Daga nan sai suka ce: Idan kuwa har hakan za ta taimaka ga xauke nauyin hukunce-hukunce, ai kuwa tabbatar da wanzuwarsa ya zama wajibi. Don haka sai suka ambaci siffofin shugaban, waxanda suka haxa da ma'asumanci da waninsa.

Wasu daga cikinsu suka tambayi kansu da cewa: Ah, to idan mun ce shugaba rahama ne da taimako ga xauke nauyin shari’a, to ai ba mu tare da shi yanzu! Ba kuwa yadda za a yi luxufi da taimakon wanda ba ya nan ya wanzu. Idan kuwa har ta tabbata ba za a iya samun wannan luxufi ba matuqar dai imamin yana fake, ga kuma nauye-nauyen shari’a sun tabbata, kenan cewar da muka yi shugaba luxufi ne a cikin addini ta tashi. Kuma ba mu da bakin sake sharxanta ma'asumancin wani shugaba.

Sai kuma suka ba junansu amsa da cewa, a’a, ai muna nufin ne luxufin wancan shugaba da ke fake, na samuwa ne ga waxanda suka san da zamansa, suna nan bayyane. Waxanda kawai wannan luxufi ba zai sama ba, su ne waxanda ba su yarda da kasancewarsa imaminsu ba. Kamar dai yadda luxufin sanin Allah ba zai samu ga wanda bai san shi ba.

A qarshe suka ce: Qaryar waccan tambaya ta qare, sanadiyyar wannan bayani. Saboda haka suna nan kan bakarsu na kururuta wajabcin ma’asumancin shugaba.

Kawowarsu nan ke da wuya sai aka ce masu: To, idan kuwa luxufinsa na iya saduwa da ku yana faken kamar yadda zai sadu da ku idan ya bayyane, kenan wajibi ne ku wadatu daga bayyanarsa, don ba ta da wani amfani. Sai kawai ku ci gaba da biyayya gare shi yana faken har ku mutu. Mun kuwa san wannan ba shi ne manufarku ba.

Sai suka sake karvawa da cewa, ai abin da muke nufi da saduwar luxufinsa ga waxanda suka yi imani da kasancewarsa shi ne ta hana su kusantar miyagun ayyuka. Kamar yadda kuma za su ci gaba da kasancewa idan ya bayyana. Amma ita bayyanar tasa za ta wajabtar da wani abu da ba wannan ba. Wato bayyanarsa za ta kwave hannuwan azulumai daga taushe muminai da suka yi. Ta kuma karve dukiyoyin da masu iko suka qwace ta mayar wa masu su da abinsu. Ba wannan kawai ba, za ta kuma kawar da azzulaman daulolin da mu ba mu iya kawarwa, sai da taimakon wannan imami na voye.

To a nan sai a tuna wa ‘yan Shi’ah cewa: Kar fa ku manta, shugaban nan da kuka ce luxufi ne, shi ne wanda hankulla da al’adun rayuwa suka sheda. Wanda kuma kuka ambata da cewa duk lokacin da jama’a suke qarqashin mulkin jarumin shugaba wanda ake tsoro, ake kuma yi wa xa’a ko ba don Allah ba. Hakan za ta sa su kasancewa mafi zama kusa da shiriya, da nesa-nesa da varna. Bayan wannan kuma kuka sharxanta kasancewarsa ma'asumi. Kuka kafa hujja da cewa, saboda da ita ne kawai shugabancin nasa zai iya tasiri. Amma kuma sai ga shi gaba xayan imaman da suka kasance kafin wannan da ake jira, babu xaya daga cikinsu da ya taka wannan rawa; babu wanda ya kasance mai qarfin iko da zartarwa daga cikinsu. To qaqa kenan? Kun ga maganar can taku ta zama sharholiya.

 Tsawon kwanukan da Ali Raliyallahu Anhu ya yi yana halifa, abubuwan da ya gudanar na halifanci da zartarwa ba su kai na waxanda suka gabace shi ba. A yayin da sauran waxanda da suka biyo bayansa daga cikin imaman naku babu wanda ya gudanar da wani abu na iko da zartarwa.

To, daxa balle shi wancan bawan Allan na voye, wanda babu ko harafi xaya na abin da ya gudanar, domin ko ganin sa ba a tava yi ba.

Yau da waxanda suka yi imani da samuwarsa, za su ji cewa, fiye da shekaru 460 kenan da ya faku, kuma saboda jin tsoro ne ba zai iya bayyana ba, balle ya gudanar da hukunce-hukunce. Kuma kodayake can fake xin ba ya da ikon bayar da wani umurni ko hani, to, za su fahimci cewa ashe saboda haka ne qunci da varna suka yi kanta a cikinsu. Kuma a qashin gaskiya haka ne; babu wani bananci a cikin wannan magana.

A kan wannan dalili ne kake ganin qungiyoyin ‘yan Shi’ah sun fi kowace qungiya kasancewa cikin qunci da varna, da yawan savani ta hanyar kace-nace, da bankaura. Irin yadda kashe-kashe da savani da zaluntar juna ke gudana tsakaninsu, ko tsakanin waxanda ke qarqashin jagorancin kafirai albarka. Daxa balle waxanda ke cikin taragon musulmin direba. To idan ka dubi wannan sai ka ga wane luxufi ne waxannan mabiya na wannan “Malam-na-Lave” suka samu?

 Shi dai imani da kasancewar Allah Ta’ala samamme, rayayye, mai iko a kan komai, yana kuma horo da yin xa’a gare shi tare da tanadin lada ga wanda ya yi, yana kuma hani daga savo, tare da shirin azabtar da wanda bai ji bari ba. Imani da waxannan abubuwa na daga cikin manya-manyan abubuwan da ke sa tsoron Allah da kwaxayin rahamarsa a cikin zukata. Ta yadda sanin zai kasance tafarkin samun lada da jinqayinsa. Daga nan sai ka ga an dage a kan aikata abubuwan da ya yi umurni da su, da nisantar waxanda ya hana. Za ka taras da duk wanda ya kai wannan matsayi yana samun tashin hankali a duk lokacin da ya savi Allah ko a kan kuskure ne. Saboda ya kwana da sanin cewa Allah masani ne kuma mai iko. Kuma sunnarsa ta riga ta gudana a kan saka wa masu biyayya da alheri da azabtar da waxanda suka kangare. To, ya za a kwatanta wannan sani na Ubangiji da yake da wannan xinbin fa’ida da sanin Malam-na-Boye?

 Duk mutumin da aka san babu shi fiye da shekaru xari huxu, kuma bai iya azabtar da kowa ko da da baqar magana, ba ya kuma da abin da zai ba wani na lada. Hasali ma tsoron mutane yake yi, saboda haka yake fake; ba zai iya fitowa ba, balle ya bayar da wani umurni ko hani. Sanin akwai irin wannan mutum ba zai sa a aikata abin da ya yi horo da shi, ko a bar abin da ya hana ba. A maimakon haka ma sanin da ake da shi na kasancewarsa da tsoron da yake da shi, za su sa ne kawai a daxa kutsa kai cikin miyagun ayyuka. Musamman ma kasancewa an xauki tsawon lokaci ba a ji ya karrama wani ko ya gyara wa wani zama ba.

 To mu qaddara ma yakan bayyana sau xaya bayan kowace shekara dari ya xan zartar da wani xanyen hukunci. Ba zai kama qafar xaya daga cikin shugabanni a fagen luxufi ba, ko da kuwa bayan kowace shekara goma ce yake bayyana, ko ma ce bayan kowace shekara xaya. Ba dai zai kama qafar shugabannin da ke tare da jama’a kodayaushe ba a fagen amfanarwa, tattare kuwa da abin da ke tuzgowa daga gare su na zunubbai da zalunce-zulunce a wasu lokutta. Sun dai tsayar da shari’ar Allah, ta hanyar zartar da hukunce-hukunce na horo da zuba qoqari a cikin kwaxaitar da jama’arsu ga yin ayyukan xa’a, fiye da yadda wanda ba ya ko bayyana gare su daga bana sai baxi. To daxa balle wanda ya salwanta sukutum; masu hankali suka tabbatar da rashin wanzuwarsa. Waxanda ke waqen akwai shi xin ma, suna da yaqinin cewa, kasasshe ne, matsoraci; bai ma tava tavuka wani abu irin wanda xaixaikun mutane ke tavukawa ba, daxa balle irin abin da shugabanni ke yi.

 To wace irin jaruntaka ce ko kwarjini irin wannan mutum ke da su, da har za a shakkarsa? Wane iko ke ga irin wannan balle har ya shimfixa hannunsa a kan mutane, ko ya zama mai taimaka masu ga kasancewa mafi zama kusa ga shiriya!

 Duk wanda ya yi xan batun zuci a cikin wannan lamari, zai tabbatar cewa jahilci da girman kai da wautar waxannan mutane sun isa. Ganin irin yadda suka sakankance da kasancewar samun luxufin wannan mahaluqi na voye, tattare kuma da kasancewarsa kasasshe, kamar yadda wai za su sami luxufin nasa ko da bayyana ya yi. Kuma wai sakamakon amincewa da kasancewarsa samamme a cikin halin nasa na kasawa da tsoro, a can faken, daidai yake da kasancewarsa a fili, kuma a cikin halin maza kuta da aminci. Wai kuma tsurar ruwan zatin wannan masaniya luxufi ce a karan kanta ga wanda ya siffanta da ita, kamar sanin Allah Subhanahu WaTa’ala. Tirqashi wani aiki sai jahili.

Fuska ta biyu:

Muna son mu ji ta daga bakinku ku ‘yan Shi’ah. Shin cewar da kuka yi, dole ne a samar da shugaba ma'asumi wanda zai tsare aikata waxancan abubuwa da kuka ce kalmar luxufi ta qunsa, na nufin wajibi ne ga Allah Subhanahu WaTa’ala Ya halicci mutum mai waxancan siffofi ya kuma tabbatar da samuwarsa. Ko ko a’a wajibi ne ga mutane su yi masa bai’a a matsayin shugaba bayan Allah Ya samar da shi?

Idan kuna nufin wajabci na farko, to qaryarku ta sha qarya. Domin kuwa Allah Subhanahu WaTa’ala bai halicci mai irin waxancan siffofi ba. Qul xin abin da kuke iya cewa shi ne, ai Ali Raliyallahu Anhu ma'asumi ne. Amma ai ko shi xin, tarihi ya tabbatar da cewa Allah Subhanahu WaTa’ala bai arzutta shi da wata halitta a cikin jikinsa ko rundunarsa ba, wadda za ta iya ba shi damar aikata irin waxancan abubuwa da kalmar ta luxufi ta qunsa a wurin ku.

 Ku da kanku ma, kuna faxa wa duniya cewa sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya kasance mai rauni kuma audugar kasuwa, wanda aka zalunta a zamanin halifofi uku na kafinsa. Kuma a daidai lokacin da ya haxa runduna don xaukar fansa, sai aka s