WANKAN TSARKI (JANABA) ()

Malan Aliyu Muhammad Sadisu

Yayi Magana ne akan yadda ake wakan janaba wada sanisa wajibine gakowane Musulmi mace da namiji

  |

  WANKAN TSARKI (JANABA)

  [Hausa هوسا-]

  Malan Aliyu Muhammad Sadisu

  2014 - 1435

  غسل الجنابة

  [Hausa هوسا-]

  الشيخ : علي محمد السادس

  2014 - 1435

  WANKAN TSARKI (JANABA)

  Shinfida: Bayan da bayanai suka gabata akan abinda ya shafi karamin hadasi wanda yake ya takaitune ga tsarki da kuma alwala, sannan bayanai suka zo akan abinda ya shafi kadan daga cikin hukunce-hukuncen alwala, to a yanzu za'a yi bayani ne akan abinda ya shafi babban hadasi wanda yake bai tsaya ga tsarki ko alwalaba a'a, shi tsarkinsa shine ayi wanka shine an tsarkaka, wadannan abubuwa da suke wajabta wanka suna da yawa za mu yi iya kokari damin mu kawo su daki-daki, da fatan Allah ya yi mana jagora, amin.

  (1) Janaba: Janaba dayace daga cikin abubuwan da suke wajanta wanka, wanda yake hanyoyin kasantuwa da janaba sune kamar haka:

  (a) Fitar Mani: Idan maniyyi ya fita daga mace ko namiji to wanka ya wajaba, amma kafin wankan ya wajaba sai ya zama maniyyin ya fitane ta hanyar jin dadi, kamar kallo ko wasa ko tabe-tabe ko jingina…' amma idan ya fita ba ta hanyar jin dadiba ya fitane ta hanyar wahala, kamar ya taka wuta ko harbin kunama ko kuma watar lantarki ta ja shi…' to wannan wanka bai wajaba a kanshiba saida kawai ya yi alwala. Shi wannan fitar maniyyi da ake Magana akan shi ko dai ya fita a farke ko kuma ya fita ana bacci, idan ya fita ana farke shine ake maganar an ji dadi ko ba'a ji ba, amma idan ya fita ana baccine to ba wata maganar jin dadi wanka ya wajaba.

  (b) Shigar Azzakari Cikin Farji: Idan kan kaciyar namiji ya bace cikin gaban mace to wanka ya wajaba. Anan ba'a maganar an fitar da mani ko ba'a fitarba, da zarar hakan ya faru ko macen ce ta fitar amma namijin bai fitarba ko kuma namijin ne ya fitar amma macen bada fitar ba ko ma dukansu basu fitarba wankadai ya kamasu su duka, da wanda ya fitar da wanda bai fitarba, tunda ba maganar fitarwa ake yi ba maganar saduwace, amma inda wasa aka yi ba saduwa ba to wanda ya fitar shi wanka ya wajaba a kanshi.

  Idan aka yi saduwa sannan aka kara yi to idan an tashi wanka wanka guda kawai za'a yi, koda an yi saduwar sau gomane sannan ake so ayi wanka to wanka guda za'a yi ba wanka goma ba.

  Idan mutum ya sadu da mace kuma yake so ya jinkirta wankan janaba zuwa an jima to abinda zai yi shine ya yi tsarki sai ya yi alwala, domin alwalar tana rage kaifin janaba, sannan kuma tana kara kuzari lokacin da ake so akara saduwar.

  Idan mutum ya sadu da mace sai bai fitar da maniyyi ba wanka ya wajaba akanshi kamar yadda bayini ya gabata, to bayan ya yi wankan sai kuma ya ga maniyyi ya zubo, to anan idan wata sabuwar sha'awace ta fitar da wannan maniyyin wani wankan ya kama shi, amma idan janabar da ya yi wa wankace maniyyinta ya zo yanzu to alwala kawai zai yi.

  Abayan da suka gabata mun yi bayani na babbancin maniyyi da kuma maziyyi, sannan kuma da banbance-banbancen maniyyin mace da na namiji. Sannan mu sani wadannan bayanai sun shafi maza da mata, sannan kuma ka'ida ta musulunci itace bayanin abubuwa a yadda suke, domin kada a ga maganganun sun yi tsauri, mahalline na bayanin hukunce-hukunce.

  Fitar maniyyi a farke ko ta hanyar nafarki, kamar mutum ya yi mafarkin yana saduwa da mace, ko mace ta yi mafarkin namiji yana saduwa da ita to wannan al'amari yana tabbatar da abubuwa kamar haka; abu na farko wannan wanda ya fitar da maniyyin janaba ta hau kanshi, abu na biyu; idan wannan shine fitar maniyyinsa na farko to ya sani daga wannan lokacin ya balaga, saboda haka hukunce-hukuncen musulunci sun hau kanshi ko kanta.

  Idan mutum ya yi mafarkin yana saduwa da mace, ko mace ta yi mafarkin ana saduwa da ita, sannan kuma ya farka bai ga maniyyi ba to ba wata janaba akanshi, saboda haka ba zai wanka ba kuma zai yi tsarkiba saboda hakan.

  Wadannan kadan kenan daga cikin bayanan da suka shafi janaba, kuma dole a tashi tsaye domin a karantar da mutane, wani da ake Magana da shi cewa yake yi shi bai san idan mutum ya sadu da matarsa wai sai ya yi wankaba, wai abinda ya dauka shine wanda ya yi zina shine wanda zai yi wanka. Wannan jahilci har ina!.

  Abubuwan Da Janaba Ke Hanawa: Bai halatta ga wanda yake da janaba ba ya shiga masallaciba, ko kuma ya karanta Alkur'ani ba, sai aya daya ko biyu domin neman tsari.

  Mutumin da yasan ba zai iya taba rowan sanyi ba to malamai sunce kada ya kusanci iyalinsa sai ya tanadi abinda zai dumama rowan dashi, kamar hita, risho ko itace…'.

  (2) Daukewar Jinin Al'ada: Abu na biyu cikin abubuwan da suke wajabta wanka shine daukewar jinin al'ada, kenan idan jinin al'adar mace ya dauke to abu na farko dake gabanta shine wanka. Bayanai akan abinda ya shafi jinin al'ada da hukunce-hukuncensa da alamar daukewarshi da izinin Allah za su zo nan gaba, mudai sani idan jinin al'ada ya dauke to dole mace ta yi wanka, kuma zuwan jinin al'ada lamace dake nuna wannan mai jinin ta balaga musamman ace shine zuwansa na farko a wurinta, bayanai dai za su zo da izinin Allah.

  (3) Daukewar Jinin Biji: Wannan shine abu na uku daga cikin abubuwan da suke wajabta wanka, watau daukewar jinni haihuwa, da zarar mace ta ga jinin haihuwa ya dauke mata ko da ranar data haihune to wanka ya wajaba akanta domin ta fara sallah, ba wanda yace sai mai jego ta yi kwanaki arba'in kafin ta kama sallah, shima bayai akan jinin biji zai zo da izimin mai duka shine Allah, kawai mu sani anan daukewar jinin haihuwa yana wajabta wanka.

  (4) Mutuwa: Mutuwa tana wajabta a yiwa wanda ya mutu wanka, shi kuma bayanai kan abinda ya shafi wankan da yadda ake yinsa zai zo ne alokacin da za'a kawo bayanai kan jana'iza da izinin Allah, kuma Allah ya kaimu lokacin, abinda ake so a fahimta anan shine idan mutum ya mutu to dole ayi mishi wanka sai dai idan shahidine da ya rasu a fagen fama.

  (5) Musulunta: Wannan yana cikin abinda malamai suka karawa juna sani, shin idan wanda ba musulmiba ya musulunta wajibine sai ya yi wanka? Wasu sukace wajibine domin Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya umarci wasu da suka musulunta da su yi wanka, su kuma wadanda sukace ba wajibi bane wankan sunce ba'a ruwaito cewa Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya umarci dukkan wadanda suka musulunta da cewa kowa sai ya yi wanka ba.

  Kammalawa: A yanzudai munsan abubuwan da idan yada daga cikinsu ya faru to wanka ya wajaba, kuma mun sami takaitaccan bayani akan abinda ya shafi janaba, kama daga hanyoyin da ake samunta, bayanan da zasu zo nan gaba za su kun yadda wankan tsarki yake, wato wankan janaba da kuma na daukewar jinin al'ada (haila) da bambance-bancen dake cikin su, Allah ya kai mu lokacin da sauran kwana da kuma imani.

  Rbutawa :

  Malan Aliyu Muhammad Sadisu