Qalubale Ga ‘Yan Shi’ah: TAMBAYOYI 70 Waxanda Ba Su Da Amsa

Download
karubuta zuwaga shugaba wannan shafi

karin bayani

 Qalubale Ga ‘Yan Shi’ah: TAMBAYOYI 70 Waxanda Ba Su Da Amsa

Daga

MUHAMMAD MANSUR IBRAHIM

Jami’ar Uthmanu Xan Fodiyo, Sokoto

Xaukar Nauyin Bugawa

CIBIYAR AHLUL BAITI DA SAHABBAI TA NAJERIYA

Titin Ahmadu Bello, Sakkwato

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yabawa

Daga

Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

Rahimahullahu Ta’ala

Waxannan kalmomi sun fito daga bakin Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam a qarshen karatunsa na Tafsiri da yake gabatarwa a Masallacin Jum’ah na Uthman Bin Affan da ke Gadon Qaya a ranar Juma’ah 15 ga Muharram 1428H wanda ya zo daidai da 2 ga February 2007M. Sati goma kenan cif (kwana 70) kafin abinda Allah ya rubuta masa na samun kyakkyawan qarshe. Allah ya jiqan sa, ya saka masa da alheri.

Ga abin da ya ce:

 “Akwai wani kaset na Malam Mansur Tambayoyi 70 waxanda basu da amsa, duka na ‘yan Shi’ah ne. Ina tafiya akan hanya daga Sokoto zuwa nan Kano na saurari kaset xin kab, gaba xayan sa.

 A qashin gaskiya, ga yaren Hausa ban tava jin wata lacca da aka yi ba wadda ta gamsar game da Shi’ah irin ta. Gamammiyar amsa wadda Ilhama ce kawai. Hasara ce gaggaruma a ce baka ji wannan kaset ba.

 Don haka, da na zo da su, da kaina na ba wa ‘yan uwa, na ce ayi qoqarin a buga su, dukkan masu kaset da suke zuwa masallaci a raba masu su samu kofi kofi don yaxa shi a tsakankanin jama’a. Kuma na nemi shawarar shi Malam Mansur cewa, ya fitar da shi a maida shi littafi. Ya yi nazari ya dawo da su kaset xaya nan gaba.

 Amma gaskiya, kaset xin ya yi, matuqa. Allah ya saka masa da alheri.

Don haka, ba wai ina tallar kaset xin a madadin masu kaset xin ba. Wannan gaskiya in xalibin ilmi bai same shi ba ya yi hasara.

 Ni dai na qaru, qaruwa mai yawa, gaskiya tsakani da Allah. Akwai ababen da na san su ya qara jaddada min su. Akwai ababen da ban tava sanin su ba sai bayan ya faxe su.

 Don haka, kaset ne mai matuqar muhimmanci. Ku neme shi! Ku neme shi!! Ku neme shi!!! Ina jaddada maku”.

Bismillahir Rahmanir Rahim

Gabatarwa

Waxannan tambayoyi an gabatar da su ne a Masallacin Sarkin Musulmi Bello da ke Sokoto ranar Jumu’ah 14 ga watan Zul-qidah 1427BH, wanda ya zo daidai da 2 ga watan Disamba 2006M. Na qalubalanci ‘yan Shi’ah da waxannan tambayoyi ne, ina basu tabbacin idan suka amsa kashi xaya daga cikin goma na tambayoyin to, zan shelanta komawata zuwa ga aqidarsu.

An dai shirya wannan haxuwa ne a qarqashin kulawar Cibiyar Ahlul Baiti da Sahabbai. Cibiyar da ta xauki alqawarin bayyana ma mutane gaskiyar Allah game da matsayin almajiran Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da iyalansa. Domin kuwa waxannan bayin Allah kamar yadda Allah ya sifaita su abu xaya ne. Rayuwarsu kuma iri guda ce; ‘yan’uwan juna ne, masu qauna da taimakon juna. Aqidarsu xaya, jagoransu xaya, manufarsu a rayuwa kuma guda ce tilo. Ita ce, bin tafarkin shugabanmu ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallama.

Waxannan tambayoyi da ire-iren su sakamakon dogon nazari ne da malaman Sunnah suka sha yi akan addinin Shi’ah da kuma arangama a tsakanin su da ‘yan Shi’ar tun a tarihi mai nisa. Kamar yadda shehun musulunci xan Taimiyyah ya yi a lokacinsa. Haka ma marigayi Sheikh Ihsan Ilahi na qasar Pakistan da ire-irensu da dama.

Haka ma an gabatar da irin wannan qalubale a wata karawa da tashar Al-Mustaqillah ta shirya a watan azumin 1418H wanda aka rinqa nuna shi kai tsaye, tun daga farkon watan har qarshensa, mutane daga sassan duniya suna kallo. Malaman Sunnah irin su Sheikh Usman Al Khamis da Sheikh Abdurrahman Dimashqiyyah da Sheikh Abul Muntasir Al-Balushi ne suka kara da ayoyin Shi’ah, suka kuma qalubalance su da ire-iren waxannan tambayoyi. Ana kuma iya samun wasu daga cikin waxannan tambayoyi a layukan Ahlus-Sunnah da dama a duniyar gizo, musamman ma dai layin alburhan.com da wylsh.com da fnoor.net da makamantansu.

Na samu wani littafi da Sheikh Sulaiman xan Salihu Al-Kharashi ya wallafa mai suna As’ilatun Qadat Shababas Shi’ati Ilal Haqqi sati xaya bayan gabatar da wannan lacca. Shi ma dai tafiyarmu iri xaya ce, kuma madogarar ma guda ce; ita ce; biyar daddagin littafan Shi’ah da maganganun malumansu na da na yanzu.

Daga cikin abin da ya qara mani qarfi akan jefa waxannan tambayoyi har da sanin cewa, wakilan Shi’ah na Jihohi da ma wasu qananan hukumomi da dama sun samu wani horo na wata shida a qasar Iran. Kuma ba da daxewa ba ne suka dawo, da abin da suke ganin cewa ilimi ne. Don haka na so in qalubalance su da waxannan tambayoyi ya’allah ko zasu gane shirmen da ke cikin wannan aqidar da aka koya masu.

Fatar da muka yi ita ce, su tsarkake niyya a wajen fuskantar waxannan tambayoyi. Kyakkyawan zatonmu ne cewa, gaskiya suke nema koda yake basu shiryu zuwa gare ta ba. Idan har Allah ya sa suka hankalta to, wajibi ne su dawo ma hanya, su koma kan turbar gaskiya; tafarkin Sunnah.

Kafin na rufe wannan gabatarwa dole ne in yi godiya ga Allah maxaukakin Sarki da ya sawwaqe wannan nazari. Sannan in miqa godiya ga Barrister Muhammad Nasiru Sidi Kaduna wanda shi ne ya juyar da kaset xin ya mayar da shi a rubuce. Na yi bitar aikin ga baki xaya na mayar da shi a salon rubutu maimakon salon tsarin magana. Haka kuma na qara wasu tambayoyi bakwai akan saba’in na farko, na kuma kasa tambayoyin kashi goma duk dai da manufar qara bada dama ga su ‘yan Shi’ah don su yi nazarin da, wataqila ya ja su zuwa ga gaskiya.

Allah ya yi muna muwafaqa.

 Baban Ramlatu,

 Muhammad Mansur Ibrahim

 A Sakkwato, 01/06/1429H – 06/06/2008M

 Kashi Na Farko

Shi’ah Da Musulunci

Tambaya Ta Xaya:

Wannan tambaya ta ginu ne akan faxar Allah Subhanahu Wa Ta’ala a cikin Suratul Ma’idah aya ta 4 in da Ya ce:

ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَالمائدة: ٣

Ma’ana:

A yau na cika maku addininku, na kammala maku ni’imata akan ku, sannan na zavar muku musuluncin nan ya zama shi ne addininku.

Wannan aya ta sauka ne a ranar Arafah, 9 ga watam Zul-hajji, a shekara ta 10 BH kwana 97 kenan kafin cikawar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan ya nuna kenan ayar ta sauka ne bayan da Manzon Rahama ya yi shekaru ashirin da uku yana kira zuwa ga musulunci. Bayan kuma kafuwar daular musulunci da shekaru goma.

Da yake addinin Shi’ah, aqidarsa da siyasarsa, da yunqurin tawayensa duk sun bayyana ne bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Tambaya a nan: Shin Shi’ah tana cikin addinin da aka kammala ranar Arafah ko tana wajen sa? Idan har tana cikinsa to, ya aka yi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai faxe ta ba? bai gina addininsa akan ta ba? bai karantar da almajiransa ita ba? Idan kuma bayan addini ya kammala ne ta zo, to me ye amfaninta?

Tambaya Ta Biyu

Sanin mu ne cewa, lokacin da Sayyidina Uthman ya yi shahada gaba xayan musulmi sun yi mubaya’a ga Aliyu xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu. Aka miqa masa ragamar mulki babu jayayya. Sai daga baya ne da ya yanke shawarar saukar da wani gwamna daga cikin gwamnonin da ya iske. Gwamnan kuma yana da goyon bayan jama’a a yankinsa sosai, kuma yana ganin yana da alhaki wajen fansar xan gidansu da aka kashe, shi ne sayyidina Uthman. Sannan ne rashin fahimta ya shiga a tsakaninsu. Sannan ne kuma ‘yan ta’adda suka hasa wutar yaqi a tsakaninsu.

Tambaya anan, da Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya karvi ragamar mulki, me ya sa bai bayyana shi’anci ba? Don me bai fito da wani sabon Alqur’ani ba? Me ya sa bai shar’anta mutu’ah ba? Me ya sa bai xauko haqqin nan na Fatima da kuka ce an qwace na gonar Fadak ba, ya miqa ma zuri’arta? Me ya sa bai goge Assalatu Khairun Minan Naumi da kuka ce bidi’ar sahabbai ce ba? Me ya sa bai qara Ashhadu Anna Aliyyan Waliyullahi a cikin kiran sallah ba, tunda yin haka addini ne a wurin ku? Me ya sa bai sava ma ko abu xaya wanda halifofin nan uku suka yi ba?

Ashe, wannan bai nuna qarara cewa, Aliyu Raliyallahu Anhu Ahlus-Sunnah ne, ba xan Shi’ah ba? Kuma yana da cikakkiyar biyayya da qauna ga magabatansa na halifofi savanin yadda kuke tsegumi?

Tambaya Ta Uku

Kulini a cikin Al-kafi (1/397): yayi wani babi wanda ya sanya ma suna: “Idan Imamai suka xaukaka, (ma’ana in Shi’ah ta kafa gwamnati) to, za ayi hukunci irin na Yahudawa”. Ya kuma ci gaba da cewa: “…ba zasu tambayi hujja ba, ba za su karvi shedu ba”. (Kenan zasu yi ta kisan duk wanda ba xan Shi’ah ba, ko yana da gaskiya ko baya da ita).

A cikin “Biharul Anwari” (52/354) Majlisi cewa yayi: “Idan Mahadi ya bayyana zai zo da sabon al’amari (sabon addini), da sabon littafi, da sabon hukunci”. Haka shi ma Nu’umani ya kawo wannan cavin magana a cikin Kitabul Ghaibati shafi na 154.

 A cikin Kitabul Ghaibati har wa yau: Wai Ja’afar As Sadiq yace: “Kamar ina ganin Mahadi a lokacin da zai bayyana a xakin Ka’abah tsakanin Rukunul Yamani da Maqamu Ibrahim, yana mubaya’a ga mutane bisa ga zasu bi sabon littafi ba Alqur’ani ba”. Wannan magana akwai ta kuma a cikin “Biharul Anwari” (52/135).

Har wayau Majlisi a cikin “Biharul Anwari” yana cewa: “Mahadi idan ya bayyana, mutane da yawa in suka ga irin kisan da yake ma al’umma, sai sun yi burin bai bayyana ba”. Ya ce: “… mutane da yawa sai sun rinqa cewa, kai! wannan ba iyalin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba ne. Idan da cikin iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne ai da ya tausaya!”.

Tambaya anan itace: Me ya sa Mahadinku idan ya bayyana zai yi amfani da shari’ar Yahudu? Ina shari’ar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wadda ta shafe sauran shari’o’i? Me ya sa za a bar Alqur’ani? Ashe wannan ba hujja ne ba akan cewa, asalin addininku yahudanci ne ya haxu da majusanci sannan aka lulluve shi da maguzanci kuma aka bashi sunan musulunci?

Tambaya Ta Huxu

 Mene ne dangatakar addininku da harshen Farisanci? Domin mun lura cewa, harshen larabci ba shi da wata qima a wurin ku. Kuna fifita Farisanci da Farisawa akan ko wane harshe da ko waxanne irin mutane. Kafin ku yi gardama bari in bada ‘yan misalai don bayyana abin da nike nufi;

Littafanku suna nuna cewa, Mahadinku, idan ya bayyana, zai halaka quraishawa, ya karkashe larabawa. Sannan daga cikin sunayensa akwai Khisru Majus Sarkin Majusawa! Daman kuma kun ce, Kisran Farisa wanda ya yaga wasiqar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama don cin mutunci zai shiga wuta amma an haramta ta akan sa. Littafanku suna nuna muhimmancin Salmanul Farisi akan kusan duk Sahabbai. Abu lu’luata, bamajusen da ya kashe Umar kuna girmama shi, kuna ziyartar qabarinsa.[1] Al Gharithi ma a cikin gabatarwar littafinsa Aqdud Durar Fi Baqri Baxni Umar cewa ya yi, Abu Lu’ulu’ata ya cancanci rahama duk da kasancewar sa ba musulmi ba. Kuma ziyarar qabarinsa da yi masa addu’a na daga cikin mafi girman ayyukan lada saboda muhimmancin aikin da ya yi na kashe sayyidina Umar, surukin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama!

Duba yadda Al-Ahqaqi a cikin littafinsa Risalatul Islam shafi na 324 yake kuka akan wai, qazamai, shaixanai, macuta – a cewar sa – suka yi wa tsarkakakkun ‘yan matan Farisa (majusawa) a lokacin da aka buxa ta. Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama fa kenan!

Karbala kuma ta cikin Farisa tafi birnin Makka da na Madina daraja a wurin ku. Har ma darajar Ka’aba idan aka kwatanta ta da darajar Karbala kamar abin da allura zata xebo ne in aka tsoma ta a cikin teku. In ji Majlisi a Biharul Anwar (98/106).

Bugu da qari kuma qasar Iran a yau, harshen da ta yarda da shi shi ne Farisanci kamar yadda ya zo a tsarin mulkinta. Wannan kuma ba zai bada mamaki ba in aka san cewa, mafi yawan Marji’an Shi’ah waxanda su ne mujtahidai masu bada fatawa a mataki na duniya duk bobayi ne; basu jin larabci. Irin su: Khumaini da Khamene’i da Rafsanjani da Khatami. Kai! Har da Sistani Sayyidul Muhaqqina na wannan zamani a wurin su! A shekarun baya ne tashar AlJazeerah ta yi wata fira da jagoran Shi’ah na Najeriya, sai ga shi ana fassara masa larabcin don ya bada amsa da turanci! Ko ba a lura ba?!!! Sai na ce, to, ai shi larabcin Aljazeerah ana yin sa ne da wasali! Ko ba a lura ba?!!!

Kashi Na Biyu

Tambayoyi Akan Imamah

Addinin Shi’ah ya ginu akan cewa Aliyu xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu shi ne Imami na farko. Akan haka ne ma ake kiransu Imamiyyah. Suna ganin cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wasici da shi ya ja ragamar al’umma a bayan sa. Sai kuma zuri’ar Aliyu ita za ta gade shi a cewar su.

Akan wannan aqidar tasu ne suke kallon duk sahabban da suka yi jagoranci gabanin sa a matsayin ‘yan qwace, azzalumai, waxanda suka ci amanar Manzon Allah, suka sava wasicinsa.

Wannan al’amari na shugabanci kuwa ‘yan Shi’ah ba su xauke shi da sauqi ba. Domin suna ganin cewa shi ne mafi girman rukunnan addinin musulunci wanda, sauran rukunna basu tsayuwa sai da shi, kuma ba su kai daraja da martabarsa ba. Kai! Wai ma ya wuce matsayin annabta.[2]

Tambaya Ta Biyar

Me ya sa wannan rukunin babba na addini ba’a faxe shi ba a cikin Alqur’ani kamar yadda aka faxi sauran rukunnan da kuke ganin ba su kai darajarsa ba? Ga shi ko Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya fayyace abubuwa daki daki a cikin bayyanannen littafinsa. Mu duba sha’anin sallah misali. Ba kawai ita sallar ba har maganar tsarki, alwalla, taimama, alqibla. Kai! har da zuwa makewayi sai da aka yi maganarsa a Alqur’ani.

Abubuwan da Allah ya wajabta da waxanda ya haramta ba abin da ya rage sai da bayaninsa ya zo a littafi mai albarka. Kamar yadda Allah ya ce:

وَقَدۡ فَصَّلَ لَكُم مَّا حَرَّمَ عَلَيۡكُمۡ إِلَّا مَا ٱضۡطُرِرۡتُمۡ الأنعام: ١١٩

Ma’ana:

Kuma Haqiqa, (Allah) ya fayyace maku abin da ya haramta ma ku, sai fa abinda kuka matsu zuwa gare shi..

Suratul An’am: 119

Kai! Ba ma wajibai da Muharramai ba, har Mustahabbai da Makaruhai sun zo cikin Alqur’ani. Sauran abubuwan da Allah ya halasta ma ya yi maganar su kamar ciniki da rance (bashi) da farauta wadda, har ayoyi huxu aka saukar akan ta.[3]

To, ya aka yi Alqur’ani bai bayyanar da Aliyu a matsayin Imamu ba, har ya kasance babu aya ko da guda xaya wadda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya bayyana a cikinta cewa, Aliyu shine shugaban farko na musulmi bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Me yasa babu sunan Aliyu cikin Alqur’ani, ga kuwa sunan Zaidu varo varo a cikin Suratul Ahzab?

Muna sane da cewa, malaman Shi’ah sun haxu akan cewa, akwai sunan Aliyu a xaruruwan ayoyin Alqur’ani amma sahabbai ne suka cire shi. Kamar yadda zaka gani a mafi tsarkin littafansu; Al-Kafi. Muhimmiyar tambaya ko anan ita ce: Ina ma’anar kariyar da Allah ya ce ya yi wa Alqur’ani?

Tambaya Ta Shida

A ranar da aka ci Makkah Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ari makullan Ka’aba daga qabilar da ake kira Banu Xalhah waxanda, a hannunsu makullin xakin yake. Sun gadi riqonsa daga iyaye da kakanni.

 Da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo sai ya nemi a kawo masa makullin ya buxe Ka’abah. Wannan ya janyo ma Banu Xalhah baqin ciki mai yawa zaton cewa, makullin ya fita hannunsu kenan. Don haka sai suka fashe da kuka. Sai Alqur’ani ya sauka akan wannan magana, in da maxaukakin Sarki Ya ce:

إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تُؤَدُّواْ ٱلۡأَمَٰنَٰتِ إِلَىٰٓ أَهۡلِهَا وَإِذَا حَكَمۡتُم بَيۡنَ ٱلنَّاسِ أَن تَحۡكُمُواْ بِٱلۡعَدۡلِۚ إِنَّ ٱللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُم بِهِۦٓۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ سَمِيعَۢا بَصِيرٗا ٥٨ النساء: ٥٨

Ma’ana:

Allah Yana umurnin ku da ku mayar da amanoni zuwa ga masu su. Kuma idan kuka yi hukunci a tsakanin mutane to, ku yi hukunci da adalci. Haqiqa abinda Allah yake muku wa’azi da shi mai kyau ne. Haqiqa Allah ya kasance Mai ji ne, Mai Gani.

Akan haka ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya mayar da makullin nan ga Banu Xalhah, har ma ya yi wani jawabi mai tabbatar masu da wannan haqqin ila yaumil qiyamati, in da ya ce:

"خذوها يا بنى طلحة خالدة مخلدة فيكم إلى يوم القيامة، لا ينزعها منكم إلا ظالم"

Ma’ana:

Ku karvi wannan makullin ya Banu Dalhah, ya zauna dimun a hannunku, ba mai karvar sa daga wurinku sai in ya yi zalunci. Daga nan kuwa har ranar tashin qiyama.

 Tambaya: Idan ya kasance akan makullin Ka’abah, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wannan irin jawabi varo-varo don tabbatar da haqqin masu shi, haqqi na kulawa ba na mallaka ba.. Me ya sa bamu samu wani wasici da wani bayyanannen jawabi ba akan wannan Imamanci na Ali Raliyallahu Anhu da kuke faxi? Me ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi irin wannan maganar ba, misali ya ce:

Ku karvi wannan shugabancin ya Banu Ali, ya zauna dimun a hannunku, ba mai karvar sa daga wurinku sai in ya yi zalunci. Daga nan kuwa har ranar tashin qiyama.

Me ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi haka ba? Sha’anin makullin nan ya fi muhimmanci ne akan wannan babban rukunin addini – a cewar ku – ko yaya?

Tambaya Ta Bakwai

Kun ce Imamai Ma’asumai goma sha biyu ne. idan mun tambaye ku hujja, sai kuce mana saboda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa mayafinsa ya lulluve Ali da Fatima da Hasan da Husaini ya ce:

"اللهم هؤلاء أهل بيتى فأذهب عنهم الرجس وطهرهم تطهيرا"

Don haka, tun da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya tsarkake su, to, a cewarku ma’asumai ne. Me ya sa baku ce Fatima Ma’asumiya ba ce? Ai tana cikin zanin ko? Idan kuma kun ce ma’asumiya ce to, bamu ga sunanta cikin Imamai ba tunda wannan hadisi dalilin Imama ne a gurin ku! Ina kuma sauran Imamai tara a wannan ayar ko wannan hadisin?

Tambaya Ta Takwas

A zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, mutane da yawa sukan zo su musulunta. Idan sun musulunta kuma sai su koma garuruwansu. Da yawa- yawansu sau xaya ne suka haxu da shi Sallallahu Alaihi Wasallama, ko kuma sau biyu ko sau uku. Ire- iren waxannan bayin Allah basu tava jin labari game da Imamar Aliyu Raliyallahu Anhu da zuri’arsa ba. Basu tava jin cewa Aliyu Raliyallahu Anhu shi ne wasiyyin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba, kamar yadda ku ‘yan Shi’ah kuke cewa.

Tambaya anan: Shin musuluncinsu kammalalle ne ko ragagge? Musuluncinsu yana da rangwame ko kuwa? Idan kun ce musuluncinsu yana da rangwame, me ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai kammala masu ba, ya bayyana masu wannan muhimmin al’amari? Idan kuwa kun ce kammalalle ne, to meye amfanin wannan magana da kuke yi cewa addini bai kammala sai an yarda da shugabacin Aliyu Raliyallahu Anhu?

Ko dai kuna ganin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya taqaita ne kamar yadda Khumaini yake gani a cikin Kashful Asrari yana ganin “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai ida saqon Allah game da Aliyu ba kamar yadda ya ida saqon Allah game da nasa Manzancin”?

Tambaya Ta Tara

‘Yan Shi’ah sun ce, Aliyu Raliyallahu Anhu shi ne Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ba wa wannan haqqi, kuma waxanda suka zo kafin sa qwace suka yi, to, Me ya sa Aliyu ya shiga cikin kwamitin mutum shida waxanda a cikinsu za a zavi shugaba lokacin da Sayyidina Umar Raliyallahu Anhu zai cika?

Ga yadda abin ya faru: Lokacin da ajali ya riski Sayyidina Umar, bayan sukar da aka yi masa da wuqa yana sallah, ya kuma haqiqance mutuwa zai yi. Umar ya bayyana sunayen mutane shida da zasu zavi shugaba guda xaya daga cikin su. Ya kuma yi sheda cewa, dukkan su sun cancanta, sun kuma gama lafiya da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Waxannan mutane shida dai su ne; Uthmanu xan Affana da Ali xan Abu Xalibi, da Abdurrahman xan Aufu da Xalhatu xan Ubaidullahi da Zubairu xan Awwamu da kuma Sa'adu xan Abu Waqqasi. Ya xiba masu wa’adin kwana uku su bayyana shugaba daga cikin su. Sannan ya kafa gwamnatin wuccin gadi.

A zaman farko na wannan kwamiti dai aka samu jituwa akan mutane su uku su janye su bar uku. Xaya kuma, wanda shi ne Abdurrahman xan Aufu ya janye akan a bar shi ya zava daga biyun da suka rage; Ali ko Uthman. Ya kuma zavi Uthman bayan ya kwana uku yana shawara da jama’ar musulmi.

Tambaya anan: Me ya sa Ali Raliyallahu Anhu yaqi gaya masu cewa, daman shi ne Allah Ya zava, kowa ya janye? Don me ya shiga cikin wannan kwamiti in ya san an yi ne don a qwace masa haqqinsa? In ma har ya san yana da wasici daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ina amfanin yin takara?

Tambaya Ta Goma

Idan har abin da kuke faxa gaskiya ne cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi fatar Ali ya gade shi har ma wai, ya yi yunqurin nuna wa sahabbai haka. Gashi kuwa mun sani cewa, a tsarin musulunci shugaba shi ke bada sallah. To, Me ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai umurci Aliyu Raliyallahu Anhu da ya bada sallah ba ko da kuwa sau xaya ne kafin rasuwarsa?

 A namu littafai ko a naku, a tarihinmu ko a naku, ko akwai inda aka ce Aliyu Raliyallahu Anhu ya bada sallah ko da guda xaya ce, a rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kafin cikawar sa?. Da namu littafin da naku duka sun faxi Abubakar Raliyallahu Anhu ya bada sallah. Amma ba inda aka faxi Aliyu Raliyallahu Anhu ya bada sallah. Don me? Kuma kun ce shine shugaba, shine wanda aka yi wa wasici!.

Tambaya Ta Sha Xaya

Me ya sa Sayyidina Aliyu Raliyallahu Anhu ya karvi muqamai a lokuta daban- daban a zamanin khalifancin Sayyidina Umar Raliyallahu Anhu? Misali, lokacin da Umar xin zai je baitul Maqadisi don ya karvi makullan masallaci na uku mai alfarma bayan da aka ci nasarar garin a qarqashin jagorancin Khalidu xan Walidu. A lokacin Sayyidina Umar ya naxa Ali a matsayin gwamnan Madinah. A wancan lokaci kuwa gwamnan Madina a matsayin mataimakin shugaban qasa ne. Domin kuwa shi zai gadi Sarkin Musulmi idan qaddarar ajali ta riske shi; ya jagoranci gwamnatin riqon qwarya kafin musulmi su sake zaven shugaba.

Me ya sa Aliyu Raliyallahu Anhu ya karvi zama mai bada shawara, sannan gwamna a qarqashin gwamnatin da ku ‘yan Shi’ah kuke ganin ta cewa gwamnati ce kafira? Duba Nahjul Balagah, shafi na 325 da 340.

Haka ma lokacin da Umar zai je yaqin qasar Iraqi - kafin daga bisani ya yanke shawarar dawowa, ya sa wakili - Aliyu ne ya naxa a matsayin Gwamna. Salmanul Farisi ma haka, ya yi gwamna a Mada’in zamanin Umar, kamar yadda Ammar xan Yasir ya yi masa gwamna a Kufa. Waxannan su biyun kuwa na hannun daman Ali ne. Duba: Siyaru A’lamin Nubala’i (1/547 da 422).

Aliyu kuma har wayau, ya yi Alqalanci a zamanin Sayyidina Umar. Ya aka yi bai ce: “Ni ne shugaba” ba. Don haka, ni ba zan karvi muqami a qarqashinka ba?

Tambaya Ta Sha Biyu

Me ya sa Ali xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu bai hau mimbarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba ko da sau xaya ne a rayuwarsa don ya bayyana ma jama’a wannan haqqen nasa? Alal misali yace: “Ya ku jama’ah! Ku tuna Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurce ni da in jagorance ku. Don haka ku kauce ma waxannan “azzalumai”? Idan har halifofin nan uku da suka gabace shi azzalumai ne, kamar yadda kuke cewa?

Tambaya Ta Sha Uku

Ashe Aliyu Raliyallahu Anhu ba jarumi ba ne? Ina jaruntarsa da muka sani? Me ya sa bai yaqi waxanda suka qwace haqqin da Allah ya saukar masa ba? A cikin littafan Shi’ah ana cewa daga saman sammai bakwai Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya aiko da Imamar Aliyu Raliyallahu Anhu kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala shi ya kira shi Amirul Mumina kamar yadda ya zo a cikin mashahurin littafinku Al-Kafi na Kulini. To, Me ya sa Aliyu Raliyallahu Anhu bai fito ya yi jihadi don kare wannan haqqin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya aiko masa ba? Ko akwai inda aka bayyana ya ja daga da waxannan magabatan nasa, ko ya nemi goyon bayan jama’a don ya yaqe su kamar yadda jikansa Husaini ya yi sadda ya qudure cewa, Yazidu azzalumi ne?

Tambaya Ta Sha Huxu

 A cikin Nahjul Balagha shafi na 136 - xaya daga cikin littafai madogara a wurin Shi’ah - an faxi cewa Aliyu Raliyallahu Anhu ya roqi a yafe masa shugabanci lokacin da Sayyidina Uthman Raliyallahu Anhu ya cika. Saboda ganin irin musibar da ake ciki. ‘Yan juyin mulki sun taso daga Kufah, yawan su bai zarce mutum dubu biyu ba kacal. Kuma an bar su sun ci karensu ba babbaka saboda Sayyidina Uthman Raliyallahu Anhu ya hana a yaqe su. Daga qarshe sun kai hari ga Sarkin Musulmi, kuma suka kashe shi a cikin gidansa, a birnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, alhalin yana shugaba, Khalifan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Ga abinda aka ce a cikin Nahjul Balagah daga Aliyu xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu:

"دعونى والتمسوا غيري فإنى لكم وزير خير منى لكم أمير"

Ma’ana:

Ku bar ni ku je ku nemi wani. Domin ayi wani shugaba in taimaka masa ya fi maku alheri akan ni in shugabance ku.

Tambaya anan zuwa ga ‘yan Shi’ah: Me ya sa Aliyu bai karvi wannan haqqin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya saukar masa daga sama ba? Tsoro ya ji ne? wa yake tsoro bayan Allah Subhanahu Wa Ta’ala? Idan a da can an zalunce shi, me yasa yanzu da dama ta samu ta tabbatar da umurnin Allah bai yi amfani da ita ba? Ko dai daman can qarya ne babu wannan umurni da kuke faxa?

Tambaya Ta Sha Biyar

Me ya sa kuka hana Imamah a gidan Al-Hasan? Kuka bar ta kawai a gidan Husaini. Ga dai jerin Imaman naku a yadda suka zo a littafanku, ba ko mutum xaya daga gidan Hassan in ban da shi Hasan xin kansa:

1.         Ali xan Abu Xalib

2.         Hasan xan Ali

3.         Husaini xan Ali

4.       Ali xan Husaini (Zainul Abidin)

5.         Muhammad xan Ali xan Husaini (Al-Baqir)

6.         Ja’afar xan Muhammad xan Ali xan Husaini (As-Sadiq)

7.         Musa xan Ja’afar xan Muhammad xan Ali xan Husaini (Al-Kazim)

8.         Ali xan Musa xan Ja’afar xan Muhammad xan Ali xan Husaini (Ar-Ridha)

9.         Muhammad xan Ali xan Musa xan Ja’afar xan Muhammad xan Ali xan Husaini (At-Taqiyyu)

10.       Ali xan Muhammad xan Ali xan Musa xan Ja’afar xan Muhammad xan Ali xan Husaini (An-Naqiyyu)

11.       Al-Hasan xan Ali xan Muhammad xan Ali xan Musa xan Ja’afar xan Muhammad xan Ali xan Husaini (Al-Askari)

12.       Muhammad xan Hasan xan Ali xan Muhammad xan Ali xan Musa xan Ja’afar xan Muhammad xan Ali xan Husaini (Mahadi).

 Me ya sa duk gaba xaya Imaman naku jikokin Husaini ne kawai? Me ya sa babu zuriyar Hasan a cikin su? Ashe ko babu qamshin gaskiya a cikin zargin da ake muku cewa, ko Husainin ma don yana surukin Kisra na Farisa ne shi ya sa kuke azizita shi, kuke kuma azzama zuriyarsa don sun gama jini da Kisra “Sarkin bautar wuta”?

Abinda tarihi ya bayyana shi ne, lokacin da aka ci Farisa a halifancin Sayyidina Umar, aka kuma kama ‘yar Kisra shugaban Farisa Shaharbanu a cikin fursunoni, sai Sayyidina Umar ya yi gatancin ba da kyautar ta ga Husaini. Kuma zuri’ar Husaini duka ‘ya’yan ita wannan baiwar Allah ne xiyar Sarkin majusawan Iran. Kuma akan qiyayyar da majusawa ke yi wa musulunci, da galabar da musulunci ya ci wajen ruguza addininsu da rosa mulkin kakanninsu shi ya sa suka kafa addinin Shi’anci. Kuma suka gina shi akan ‘yan gidanci, suna masu jingina shi ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama amma ta wajen zuriyyarsa mai dangantaka da Yazdajrid, Kisran Farisa. In kun ce ba haka ba ne, to, ku bayyana mana abinda ya fifita zuriyyar Hussaini akan ta Hassan wanda ya sa har kuke ta suka ga zuriyyar Hassan kamar yadda ya ke a littafanku da dama, irin; Tanqihul Maqal na Mamaqani (3/142) da A’yanus Shi’ati (1/26) da Biharul Anwar (27/212) da Kitabu Sulaimi ibni Qais shafi na 288.

Tambaya Ta Sha Shida

Imaminku na goma sha biyu wanda kuke ce ma Mahadi, yau sama da shekaru dubu yana voye a cikin kogo wai, a cewar ku. To, mene ne dalili? A Iraqi ko wace shekara sun sanya rana don haxuwa ana kuka ana hargowa ana neman ya fito don ya ceci al’umma daga azzalumai! Akwai ma wasu fatawowi da aka yi daga baya bayan nan, a layukan yanar gizo (Intanet) masu nuna cewa, a yawaita varna sosai domin idan varna ta yawaita, to, lalle ne Mahdi zai bayyana.

Tun can asali don me ya voye? Mun sani kuna cewa, wai saboda tsoron azalumai, a lokacin daular ‘ya’yan gidan Abbas a wancan lokaci. Don su ne ya vuya. To, me ya hana ya bayyana daga bisani bayan sun gushe kuma har ma an samu ‘yan Shi’ah sun kafa gwamnati a qarqashin daular “Ubaidiyyuna” da wadda suka kafa bayan ta waxanda ake kira “Faximiyyuna”? Ga kuma “Buwaihiyyuna” da “Safawiyyuna”? Kai! Ko a wannan zamanin namu ma ga Iran nan wacce ta mallaki har makaman qare dangi. Anya Mahadin da ke tsoron azzalumai zai iya kau da zalunci?

Tambaya Ta Sha Bakwai

A lokacin haihuwar Mahadin naku, kun ruwaito cewa wasu tsuntsaye sun sauko daga sama suka rinqa kaxa fika- fikansu suna yi masa fita, suna shafar kansa, suna shafa fuskarsa sannan su tashi. Wasu kuma su dawo suyi haka sannan su tashi. Da aka gaya ma mahifinsa, wai, sai ya yi murmushi ya ce ai mala’iku ne suka zo daga sama suna neman albarkarsa. Sannan idan ya bayyana sune mataimakansa. Tambaya anan: Idan mala’iku su ne mataimakansa me ya sa ya voye: wa yake tsoro kenan?

Tambaya Ta Sha Takwas

A littafanku na Shi’ah an ce, Allah ya tsawaita rayuwarsa ne – shi Mahadi - “Don buqatar da talikai suke da ita zuwa gare shi”. Kamar yadda Ibnul Muxahhir ya ce, a cikin Minhajul karamati.

Tambayarmu anan, Idan akwai wanda buqatar da talikai suke da ita zuwa gare shi ta kai matsayin a qara masa tsawon rayuwa har irin wannan, Me ya sa ba a qara ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba? Ko kuwa dai a gurin ku Mahadin yafi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ko an fi buqatuwa zuwa gare shi?

Tambaya Ta Sha Tara

‘Yan Shi’a kun yi amanna cewa, Imamanku sha biyu, a cikin su har da Hasan da Husaini duk sun san gaibi, kuma ba wanda zai mutu cikin su sai a lokacin da ya zava, kamar yadda ya zo a mafi tsarkin littafanku Al-kafi. To, me ya sa Husaini ya kai kansa zuwa ga mutuwa? Me ya sa lokacin da aka sanya wa Al-Hasan guba yaci abincin? Ya san gaibi yaci guba? Ya kashe kansa ne? Mun fa sani Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya kashe kansa xan wuta ne”. Kuna son ku ce, Al-Hasan ya kashe kansa ne da ya ci abincin alhali ya sani cewa, da akwai guba a cikin sa?

Tambaya Ta Ishirin

Kun ce Hasan da Husaini ma’asumai ne. Haka ma sauran cikon imamanku goma sha biyu. Wannan maganar, malamanku sun haxu akan ta. Sun kuma zayyana ta a littafansu kamar, Ikmaluddini na Saduq da Aqa’idul Imamiyyatil Ithna-Ashariyyah na Zanjani, da Aqai’dul Imamiyyah na Muzaffar da Al-hukumatul Islamiyyah na Khumaini. Bisa ga haka, kun ce ba su kuskure, ba su tuntuve, ba su talalaviya. Mawaqinku na Gadan Qaya har ya qara maku da na sha uku in da yace:

Zazzakiyyu mujaddadi ne

Ma’asumi shi kaxai ne

Duk Amir ma mabbiyi ne

Mai iya fitinuwa ku gane

Ba zagin Umara’u nai nufi ba.

 Tambayarmu anan: A cikin waxannan ma’asuman guda biyu, wa ya yi daidai? Al-Hasan ne ko Al-Husaini? Al-Hasan dai ya xauki mulkin nan da aka yi masa mubaya’a, ya miqa shi ga Banu Umayyah, ta hannun Mu’awiyah. Al-Husaini kuwa yunquri ya yi na amshe wannan mulkin daga hannunsu. A wurin wannan yunqurin ne ma aka kashe shi. Wa ya yi daidai cikin su?

Kar mu manta cewa, Al-Hasan a lokacin da ya bada mulki dubun dubatar mutane ke tare da shi, waxanda ke iya bada rayukansu wajen kariyar sa. Kuma sun ma riga sun naxa shi. Al-Husaini kuwa ba shi tare da kowa sai iyalinsa da wasu kaxan daga danginsa da basu wuce mutane saba’in ba, akasarinsu mata ne da yara. Wasu kuma da suka ga aradu a fili sulalewa suka yi. Waxanda suka yi yaqi a tare da shi basu kai mutum hamsin ba. Amma dai duk da haka ya nace sai ya qwaci goriba ga hannun kuturu!

 Wane ne akan sawaba a cikinsu? Wanda yana cikin dubun dubatar mujahidai ya ce ya fasa, ya sakar ma Babu Umayyah? Ko wanda ya ce sai ya qwato mulkin daga Banu Umayyah ko da ba shi tare da kowa?

A wurinmu, su, ba ma’asumai ba ne. Kuma Al-Hasan shi yafi zama daidai domin Manzon Allah da kansa ya yabi wannan aikin nasa a lokacin da ya bada bushara cewa, za ayi hakan. Ga abin da Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wannan jikan nawa shugaba ne. Watarana Allah zai sanya shi ya zamo dalilin gyara a tsakanin wasu manyan rundunonin musulmi biyu masu faxa da juna”. Annabi ya kira su musulmi duk da faxan da suka yi, domin faxa ne na rashin fahimtar juna, ba faxa ne na kafirta juna ba. Husaini kuwa babu shakka ya yi kure da rashin karvar shawarwarin da masu nazari suka ba shi, qaddara ta sanya ya yi kuskuren lissafi, domin faxa da gwamnati mai ci, dogaro da ‘yan Shi’ah, mayaudara, masu alqawullan qarya in ba qaddara ba ba abin da zai kawo shi. ‘Yan Shi’ar nan dai kafin haka su ne suka kashe Ali, suka kashe Al-Hasan.

Duk da haka, Husaini kafin a kashe shi ya yi la’asar. Ya kuma gane cewa, lallai ‘yan Shi’ah sun yi masa ingiza mai kantu ruwa. Don haka, ya nemi ya koma abin sa, ko ya kama hanyar fagen fama, ko ya kai kansa a wurin Yazidu ya yi masa mubaya’a kamar wada sauran musulmi –cikin su har da Ahlulbaiti da Sahabbai- suka yi. Hana masa ko xaya daga cikin waxannan buqatu guda uku shi ya sa ya yi yaqi ba tawaye akan gwamnatin ba. Don haka, an zalunce shi, kuma ya yi shahada in Allah ya so. Waxanda suka kashe shi kuwa zasu gamu da fushin Allah, idan basu tuba ba.

Shahadar Husaini dai wata ni’ima ce da Allah ya ba shi kamar yadda ya bai wa xan uwansa Al-Hasan don a xaukaka darajojin su, su kai ga matsayin da maxaukakin sarki ya nuface su da shi. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxi cewa, su ne jagororin matasan Aljanna. Kafin cikawar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Al-Hasan da qanin nasa duk yara ne. Babu wanda ya yi jihadi ko xaya a cikinsu. Amma bayan samun wannan shahada, maxaukakin sarki ya basu abinda suka rasa.

Wannan ita ce aqidarmu Ahlus-Sunnah. Ku kuma ‘yan Shi’ah muna jiran amsarku: Wa yayi daidai, wa ya yi kuskure a cikin su?

Tambaya Ta Ashirin Da Xaya

A cikin Al-kafi (1/252) kun ce: “Imamai goma sha biyu sun san ranar da zasu mutu, kuma ba wanda zai mutu daga cikin su sai da zavin kansa.” Amma kuma a cikin Biharul Anwari (43/366) sai kuka ce: “Babu wani Imami daga cikin su face ya mutu ta hanyar an kashe shi, ko an sa masa guba”.

Mu a sanin mu, wanda duk ya kashe kansa xan wuta ne. Don haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce. To, a lokacin da ake sanya ma Imamanku guba, sun sani suka ci, suka kashe kansu? Ko basu sani ba? Ko dai labarun naku duk qarya ne kawai? Ina nufin ruwayar kulini da ta Majlisi.

Tambaya Ta Ashirin Da Biyu

Kuna cewa Husaini ya mutu da qishirwa, har yana cewa, “Duk kuka sha ruwa, ku tuna da ni”. A qasashen da Shi’ah ta yaxu, sukan ajiye ruwan sha a muhimman wurare, sai su rubuta cewa, “Sha ruwa ka tuna qishirwan Husaini”.[4]

Tambayarmu anan: Ashe bai san gaibi ba? Bai san qishi zai kama shi ba? Me yasa bai zo da ruwa wadatacce ba? Ashe ba Allah y ace, in zamu yaqi mu riqa makami ba? Muna riqa makami mu bar guzuri ne? Duba Suratul Anfal aya ta 60, Allah cewa ya yi, mu yi tanadi in zamu yaqi. Akwai tanadin da yafi na rowan shag a wanda har qishirwa zata kashe shi?

Mu a aqidarmu, Husaini bai san abin da zai faru gare shi ba sai da qaddara ta ingiza shi zuwa ga hukuncin da Allah ya rubuta masa. Ku ko da kuka ce ya san gaibi muna jiran naku bayani.

Kashi Na Uku

Imani Da Alqur’ani

Tambaya Ta Ashirin Da Uku

‘Yan Shi’ah kuna zargin Sahabbai da canza Alqur’ani. Kuma riwayoyi waxanda basu qirguwa sun tabbatar da haka a cikin amintattun littafanku. Kuna ganin Alqur’anin da ke hannun musulmi a yau wai, xan jabu ne. Domin ko sahabbai sun voye na gaskiya a cewar ku. Misali, a cikin Biharul-Anwar (24/305) an ce: Baban Abdullahi, Ja’afarus Sadiq Alaihis Salamu ya ce;

نزل القرآن أرباعا: ربع فينا، وربع فى عدونا، وربع سنن وأمثال، وربع فرائض وأحكام. ولنا كرائم القران.

Ma’ana:

Alqur’ani ya sauka kashi huxu ne: Kashi na farko akan mu ya sauka (Ahlul-baiti), kashi na biyu akan maqiyanmu (Sahabbai), kashi na uku kuwa wasu sunnoni ne da kuma wasu karin maganganu, kashi na huxu shine wasu farillai da wasu hukunce-hukunce. Kuma darajojin da ke cikin Alqur’ani namu ne.

To, ka ji fa! wai har kashi xaya cikin huxun qur’aninku karin magangannu ne. Daga nan ne suke tuhumar sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa sun voye kashi na xaya da na biyu na Alqur’ani. Domin in zaka xauko wannan Alqur’ani namu daga farkonsa wato suratul Fatiha zuwa qarshensa; Suratun Nasi, sura xari da goma sha huxu, ayoyin nan dubu shida da xoriya, ba inda zaka ga an faxi wata xibar albarka ga sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, sai dai faxin darajarsu. Don haka sai suke tuhumar sahabbai da cewa sun voye wannan.

Tambaya anan: Da Sahabbai suka voye Alqur’ani, shi ina Aliyu Raliyallahu Anhu? Me ya sa shi bai bayyana ba? Ko su kaxai Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya umurce su da suyi bayani, amma shi Ali Allah bai umurce shi ba? Idan ya bayyana a ina yake? Ina abinda ya bayyana xin? Ina sabon Alqur’anin? Ku kawo mana shi in kuna da gaskiya.

قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ البقرة: 111 والنمل: ٦٤

Tambaya Ta Ashirin Da Huxu

Idan Sahabbai sun voye kashi biyu daga cikin kashi huxu na Alqur’ani saboda suna gudun a bayyana darajar Ahlul-Baiti, to, Me ya sa basu voye hadisan da suka bayyana darajar Ahlul-Baiti ba? Suna nan cikin littafanku, suna kuma cikin littafanmu. Amma a nan ba zan bada misali da naku ba (littafan Shi’ah), bari in bada misali da namu (littafan Sunnah) waxanda muke gadara da su.

 Duk a cikin littafai na duniya in ban da Alqur’ani, mu mabiyan Sunnah muna ganin babu littafi mai daraja da inganci kamar littafin Bukhari da na Muslim. To, ga ‘yan misalai daga darajojin Ahlulbaiti a cikin su.

Misali na xaya: Hadisin Wilaya:

"من كنت مولاه فعلى مولاه"

Ma’ana:

Duk wanda na kasance abin jivintarsa to, Aliyyu ma abin jivintarsa ne.

Muna iya cewa, kacokan, aqidar Shi’ah ta dogara ne a kan wannan hadisi. Hadisin yana nan cikin Bukhari, kuma riwaye ce ta sahabbai fiye da ashirin. Hadisi ne mutawatiri. Sahabban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sun yarda da shi, kuma sun faxe shi, kuma mu Ahlul-Sunna mun yarda da shi. Abinda bamu yarda ba shi ne, irin qarairayi da qarin gishirin da kuke yi ma shi.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxi wannan hadisi a Gadir-Khum a kan hanyarsa ta dawowa Madina bayan gama hajjinsa na bankwana. Su ‘yan Shi’ah sai suka ce, Gadir-Khum matattara ce wurin da Jama’a ke rabuwa na kowane gari su yi garinsu. Wai, don haka ne ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya zavi wannan wurin wanda kowa da kowa na nan kafin a rabu don ya sanar da mutane, ta hanyar wannan hadisi cewa, Ali shi ne magadinsa.

Don tunvuke wannan tatsuniya daga asalinta sai na bi diddigi, nayi bincike, na tambayi masana a qasar Saudiyya, inda na gano wurin da Gadir-Khum yake. Abinda na gano kuwa shi ne, nisan wurin daga garin Makkah Kilomita xari biyu da hamsin (250) ne, akan hanyar zuwa Madina.

Don Allah Jama’a ya za ayi ace sai an ci kilomita xari biyu da hamsin daga Makka sannan mahajjata zasu rabu? Mutanen Xa’ifah alal misali, garinsu bai wuce kilomita arba’in ba daga Makka. Mutanen Iraqi su kam ma ba abinda zai bishe su hanyar Madina. Domin suna hannun riga ne da ita. Mutanen Kufah da na Basrah da wannan yankin duk ba sa isowa Gadir-Khum in sun bar Makka zuwa garuruwansu. Saboda haka, Ghadir Khum ba mararraba ba ce.

Idan kuma da Annabi yana son jama’a kowa da kowa yaji wannan bayani ne me ya hana ayi shi ranar Arafa; ranar da kowa ma yana nan, har ‘yan cikin garin Makka?

Gaskiyar magana ita ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai da ya bari kowa ya tafi, mutanen Madinah kawai suka rage, sai ya tsoratar dasu daga wasu maganganu da yaji suna faruwa. Domin Aliyu xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu, ya shugabanci wata runduna, sai ya samu rashin jituwa da wasun su. Domin ya hana su amfani da kome cikin ganimar da aka samu har sai an koma Madina. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wannan jawabi don ya sanar da su matsayin Ali su daina qyamar sa. Duk wanda ko ke qyamar Aliyu Raliyallahu Anhu xan wuta ne.

Ahlul-Sunnah sun yarda cewa, wanda ke qyamar Aliyu Raliyallahu Anhu xan wuta ne. Kuma ba zaka tava samun Ahlul-Sunnah guda xaya ba da yake qyamar Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu. Ka je duk in da musulmi masu karva sunan Ahlus-Sunnah ka gani, Aliyu nawa zaka samu a cikin su? Muna qyamar sa muke sa sunansa?

Tambayarmu kenan ita ce: Me ya sa sahabbai basu voye wannan hadisi ba, har aka samu sama da mutum 20 a cikin su sun ruwaito shi? Kuma babbar darajar Aliyu Raliyallahu Anhu yake bayyanawa, in dai har su ne masu voye ayoyin Alqur’ani tsoron kada girman Ali da sauran Ahlul-Baiti ya bayyana?

Misali na Biyu:

Hadisin Kisa’u. Shi ma kusan rabin ruwayoyin Shi’ah suna dogara ne a kansa. Hadisin yana cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya lulluve Fatima da Mijinta da xiyanta Al-Hasan da Al-Husaini, sannan sai yace:

اللهم هؤلاء أهل بيتى فأذهب عنهم الرجس وطهرهم تطهيرا

Ma’ana:

Ya Allah! Waxannan iyalan gidana ne. Ina roqon ka tafiyar da qazanta daga gun su, kuma ka tsarkake su, tsarkakewa.

Wannan hadisin, muna iya kiran sa rabin addinin Shi’ah, saboda yawaitar dogaron su akan sa. Wa ya riwaito wannan hadisi? Uwar muminan dai A’isha da takwararta Ummu Salamata su ne suka ruwaito shi.

Misali Na Uku: Hadisin Matsayin Ali

أنت مني بمنزلة هارون من موسى

Ma’ana:

Matsayinka a gurina kamar matsayin Annabi Haruna ne ga Annabi Musa.

Haruna qanin Musa ne kamar yadda Ali ya ke qanin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama. Amma waxancan su biyu annabawa ne. Ali kuma ba Annabi ne ba. Sai dai hadisin ya bayyana cikakken matsayin kusanci da Sayyidina Ali yake da shi.

Wa ya ruwaito wannan hadisin? Amsa ita ce, Sa’adu xan Abu Waqqas wanda ‘yan sha biyu ke ganin sa a matsayin wanda ya yi ridda don ba ya son Ali. Kuma Hadisin yana nan cikin ingantaccen littafin Bukhari (3505)

Misali Na Huxu: Hadisin da yace,

لأعطين الراية غدا رجلا يحب الله ورسوله ويحبه الله ورسوله يفتح الله على يديه

Bayanin Hadisin

A ranar da za ayi yaqin Khaybara Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, idan an wayi gari gobe zan bada tuta ga wani mutum guda wanda yana son Allah Subhanahu Wa Ta’ala da Manzonsa Sallallahu Alaihi Wasallama kuma Allah da Manzonsa na son shi. Allah kuma zai yi masa buxi, ya bashi nasara.

Saboda girman wannan bushara a wannan rana kowa ga kansa yake so. Sayyidina Umar ya ce, a ranar sai da ya riqa tsalle yana son Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gan shi don ya kira shi ya bashi wannan tuta. Ana haka ne sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kira Ali ya ba shi tutar.

Wa ya riwaito wannan hadisi? Amsa ita ce, Sa’adu xan Abu Waqqas da Salamatu xan Akwa’u ne suka riwaito shi. Kuma yana cikin ingantaccen littafin “Bukhari”. Me ya sa waxannan sahabbai basu voye wannan darajar ta Aliyu ba, alhalin sun voye sashen Alqur’ni don kar a bayyana darajarsa a cewar ku?

Misali Na Biyar: Hadissan falalar Fatima da ‘ya’yanta:

Suna da yawa; kamar cewa ita ce: سيدة نسآء أهل الجنة “Fisrt Lady” ta ‘yan Aljanna mata. Da kuma falalar ‘ya’yanta; Al-Hasan da Al-Husaini, cewa sune: سيدا شباب أهل الجنة “Shugabannin matasan Aljanna. Da kuma cewa Al-Hasan shugaba ne, Allah Subhanahu Wa Ta’ala zai sulhunta qungiyoyi biyu na musulmi masu faxa da juna saboda shi. Da bayanin irin qaunar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yake ma Al-Hasan da Al-Husaini, da xaukarsu da yake yi yana tawan su, yana yi masu addu’a yana cewa: اللهم إنى أحبهما فأحبهما “Ya Allah! Haqiqa ni, ina son su. Don haka, kai ma ka so su.

 Waxannan hadisan an samo su ne daga Usamatu xan Zaidu, da Bara’u xan Azibu da Anas xan Maliku da Abdullahi xan Umar. Kuma duk suna cikin Sahihul Bukhari. Me ya sa basu voye waxannan hadisai ba?

Falalar Ahlul-Baiti gaba xaya, da kasancewar son su wajibi ne, qyamar su kuma halaka ce. Duk Sahabbai suka riwaito su. Don me suka voye ayoyin Alqur’ani gudun bayyana darajar Aliyu da Fatima da Hasan da Husaini, sannan suka bayyana waxannan hadissai? Me ya sa haka? Ko dai shi Alqur’anin Allah bai tsare shi ba ne? To, ya aka yi ya tsare hadisi daga irin abin da bai tsare Alqur’aninsa daga gare shi ba a ganin ku? Ku sake tunani ya ku mutanena!

Tambaya Ta Ashirin Da Biyar

Sanin kowa ne cewa, sahabbai su ne suka cirato mana Alqur’ani daga bakin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallama. Alqur’ani kuma mutawatiri ne, bi ma’ana adadi mai xinbin yawa ne suka jiyo shi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba ‘yan qwarorin mutane ba. Qira’oi guda goma ne aka sani a duniya, ko wanensu yana da riwaya biyu ta almajiransa kuma duk maruwaitan su Ahlus-Sunnah ne.

A duniyar yau, Qira’ar malamai uku aka sani; Nafi’u da Asim da Abu Amril Basri. Qira’ar Nafi’u ta shahara da riwayar Warshu da ta Qalun. Qira’ar Asim ta shahara da riwayar Hafsu. Shi kuma Abu Amril Basri riwayar Duri ce aka fi sani a karatunsa. Kuma duk wani Alqur’ani da aka buga a duniya – ko a Iran ne – da xayan qira’oin nan uku ne. Kai! Mafi yawa ma dai riwayar Hafsu ce aka fi sani wadda ya karvo ta daga Asim daga baban Abdurrahman As-Sulami da sahabbai: Uthmanu xan Affan da Ali xan Abu Xalib da Zaidu xan Thabitu da Ubayyu xan Ka’abu.

Tambaya anan: Ina qur’anin Ahlul-Baiti wanda suka ruwaito daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Ina ruwayarku ta Ali xan Abu Xalib? Ina ruwayar Al-Hasan da ta Al-Husaini da ta Zainul Abidina?

Ina qira’ar Ridha idan ya karvo daga Kazim daga Sadiq daga Baqir?

Ina ta Askari daga Naqiyyu daga Taqiyyu?

Ba kun ce su ne hujjar Allah akan talikkai ba?

Ba su ne Allah ya naxa su don su shiryar da mutane ba a cewar ku?

Sun karantar da kome amma ban da Alqur’ani?

Ya zaku dogara ga karatun da kafirai – a wurin ku – suka cirato daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama?

Bincike ya tabbatar da cewa, ba wata riwaya ta karatun Alqur’ani daga Ahlul-Baiti sai guda xaya, ita ce; riwayar Hamza Az-Zayyat (malamin Sunnah) wadda ya karvo daga Sadiq daga Baqir daga Zainul Abidin. To, ina riwayar ‘yan Shi’ah ga wannan tilawa? Me ya sa Zayyat ne kawai (malamin Sunnah) ya riwaito ta? Ya aka yi Kazim bai riwaito ta daga Sadiq ba? Ko a ce: Askari ya karvo ta daga Naqiyyu daga Taqiyyu daga Kazim daga Sadiq? Ita kanta wannan qira’ar a yanzu labari ce, domin babu ta. Me ya sa baku nemo ta ku buga Alqur’ani da ita tunda ita kaxai ce ta fito daga Ahlul-Baiti?

Muna son ku fito mana da qira’a mutawatira, ko ma ba mutawatira ba wadda ta fito daga Ahlul-Baiti daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Tambaya Ta Ashirin Da Shida

 Qur’anin Fatima da kuke cewa. Labarinsa ya zo a cikin Al-kafi -kafi kafiri varna- (1/239): Wai wani ya shigo a gidan Abu-Ja’afar Alaihis Salamu yace, ina so in maka tambaya amma ka duba waje idan ba kowa! Ya ce, sai ya xaga labulen da ke tsakaninsa da wani gida, sai ya ce, yi duk tambayar da kake so babu abin tsoro. Kowa bai jin ka. Imami Ma’asumi ya ce; “Haqiqa muna da wani Alqur’ani mai suna Alqur’anin Fatima. Alqur’ani ne wanda yayi girman Alqur’anin nan naku sau uku. Wallahi ko harafi xaya na Alqur’aninku babu a cikinsa”.

Ikon Allah! Ashe ma naku Qur’anin ba ya da bismillah?!

Tambayarmu anan, shin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya san da wannan Alqur’ani na Fatima ko bai san da shi ba? Idan ya san shi me ya sa ya voye ma sahabbai shi? Me ya sa ya voye ma Al-ummarsa? Gashi ko Allah Subhanahu Wa Ta’ala yace

۞ يَٰٓأَيُّهَا ٱلرَّسُولُ بَلِّغۡ مَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۖ وَإِن لَّمۡ تَفۡعَلۡ فَمَا بَلَّغۡتَ المائدة: ٦٧

Idan kuma kun ce bai sani ba, ya aka yi ku kuka sani a yanzu?

 Haqiqanin gaskiya, wani malami na Shi’ah ana kiransa Al-Xabarsi ya tona asirin Shi’awa a lokacin da ya wallafa wani kataferen littafi wanda ya sa masa suna Faslul Khixabi fi ithbati tahrifi kitabi Rabbil Arbabi “Rarrabe zance don tabbatar da cewa lallai an chanja littafin Ubangijin Ubangizai”.

 A cikin sa sai da ya kawo sama da ruwaya dubu biyu na ‘yan Shi’ah waxanda ke tabbatar da wannan Alqur’anin namu ba na qwarai ba ne a wurin su. Wai an canja shi! A ciki ya kawo maganganun fuqaha’un Shi’ah, da Muhaddithuna da Mufassiruna da dai sauran duk waxanda su ‘yan Shi’ah ke gadara da iliminsu. Daga qarshe ya ce qarara: “Ya wajabta a qudurta cewa, Alqur’anin da ke hannun mutane ba na qwarai ba ne”.

Wannan shi ya sa Sayyid Hashimul Bahrani, a cikin littafinsa Al-Burhan, a muqaddimar fasali na huxu, shafi na 49 yake cewa: “A gurina kasancewar wannan magana qarara bayan an binciki labarin a littafan hadissai, akan haka ya wajaba a hukunta cewa lalura ne in kana xan Shi’ah ka yarda cewa Alqur’ani an canja shi. Yana daga cikin manya-manyan manufofi cewa, lallai an qwace khalifanci ga Ali Raliyallahu Anhu. Ku yi tunanin wannan magana”. In ji shi. To, mun yi tunani kuwa mun gano qarya ce.

 Ni’imatullahil Jaza’iri – wani mashahurin malamin Shi’ah - da yake maida martani ga masu cewa Alqur’ani daidai yake, ga abinda yake cewa: “Duk wanda ya yarda cewa, Alqur’anin nan gaba xaya wanda ke hannunmu Jibrilu ne ya sauko da shi to, ya qaryata ruwayoyi waxanda suke mutawatirai daga shugabanninmu da abokanmu. Don haka shi ba xan Shi’ah ba ne. (Duba Littafin Al-Anwarun Nu’umaniyyah 2/357).

 Kada mu tafi da nisa, a cikin Al-kafi (1/26) ga abinda yake cewa: “Duk wanda ya xauka cewa akwai Alqur’ani kammale a gurin wani mutum, to wannan shine babban maqaryaci. Domin ba wanda ya tara Alqur’ani ya haddace shi, yadda Allah ya saukar da shi in ba Aliyu ba da Imamai – na zuri’arsa – a bayansa”

Al-Khu’i, shi ma wani hamshaqi ne da ake ji da shi daga malaman Shi’ah na wannan zamani da muke ciki. Idan ka duba kittafin Lillahi Summa lit Tarikh shafi na 67-68, zaka sami abinda yake cewa kamar haka: “Na umurce ku da ku riqe wannan Alqur’ani da ake da shi a yanzu har sai lokacin da Alqur’anin Fatima ya sauka”.

Allahu Akbar! Ayi wa Alqur’ani riqo na wuccin gadi? Ina na din- din- din? Babu dai Alqur’anin na Fatima a hannunsu. In ma ba a cikin qwaqwalensu ba babu inda Allah ya saukar ma Fatima da wani Alqur’ani wanda ya kevance ta.

 ‘Yan Shi’ah dai ba wannan Alqur’ani na Fatimah kaxai suke cewa suna da shi ba. Suna da wani Alqur’ani mai suna Al-jami’ah, bayaninsa ya zo a cikin Al-kafi (1/239) da Biharul Anwari (26/25).

 Sannan suna da wani Alqur’ani mai suna An-Namus. An faxe shi a cikin Biharul Anwari (25/117). Suna da wata takarda wadda suka ce ita ma sauko da ita aka yi daga sama, sunan ta Al-Abixah ta zo a cikin Biharul Anwari (26/37). Suna da kuma wanda suke kira Zu’abatus Saifi ta zo a cikin Biharul Anwari (26/56).

Haka kuma suna da wani littafi mai suna Al-jafar shi ma sun ce Allah ya sauko musu da shi. Ya zo a cikin Usulul Kafi (1/24).

Tambaya anan (Ta 27): Da yake mun tabbatar da cewa, littafanku a cike suke da sukar Alqur’ani da zargin Sahabbai cewa sun sa son ransu a ciki. To ko kuna da wata riwaya guda xaya daga Imamanku wadda ta gyara wannan magana, misali ta ce, Alqur’ani cikakke ne ba a canza kome ba a cikin sa? Ni ina cewa, “Babu wannan riwaya ko wuri xaya a cikin littafanku”. Idan kun qaryata ku kawo mu gani!

Tambaya (Ta 28): Lokacin da Ali ya karvi halifanci me ya sa bai fito da waxannan littafan ba? Idan a zamanin Abubakar da Umar ko Uthman Raliyallahu Anhum ba shi ke mulki ba, kuma tsoro yake ji, to a nasa zamanin fa? Me ya hana ya fito da su don ya xora mutane kan miqaqqiyar hanya? Kun ce yana da Alqur’ani wanda aka jeranta kamar yadda Allah ya saukar da shi, ba kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa Sahabbai suka tsara shi ba. Wato, wanda yake farawa da Iqra’ ya kuma qare da Alyauma Akmaltu Lakum.. Kuma kun ce Aliyu kaxai yake da shi. Me ya sa bai bayyana shi ba a zamanin mulkinsa?

Kashi Na Huxu

 Sauran Halifofi Tambaya Ta Ashirin Da Tara

Ya zamo mutawatiri, abinda duk al’umma ta faxa cewa, Ali Raliyallahu Anhu akan minbarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, lokacin da yake Khalifah, ya sha cewa, “Mafificin wannan al’umma bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, shine Abubakar sannan Umar, Tambaya anan, Me ya sa Aliyu ya yabe su? Kuna iya cewa, ai taqiya ce. To, me ya sa ku ba zaku yi taqiyyar ba? Duk ku ci gaba da taqiyya mana, kamar yadda ya yi, sai a huta, a zauna lafiya!

Tambaya Ta Talatin

Me ya sa aka rufe Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a xakin wadda kuke ganin ta kafira, tare kuma da waxanda a ganin ku, su ma kafirai ne? A wurin ku sun ma fi fir’auna kafirci! Me ya sa Allah bai kare shi daga wannan ba? Sun zauna da shi a duniya su ne mafi kusancin mutane zuwa gare shi. Ga su kuma a yanzu su ne mafi kusancin mutanen duniya a gare shi. Amma kun ce a lahira basu tare da shi! Me yasa Allah ya haxa su?

Ina Ali yake a lokacin da za a rufe Manzon Allah har ya bari aka rufe shi a xakin A’isha? Ina yake lokacin rufe Abubakar, haka ma lokacin rufe Umar? Me yasa bai hana ba? Ko kuwa duk jaruntarsa da muka sani a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta sassafce tun daga cikawar Manzon Allah?

Tambaya Ta Talatin Da Xaya

‘Yan Shi’a kun ce, halifofi uku na farko bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kafirai ne. Me ya sa Ali Raliyallahu Anhu ya yi musu mubaya’a? Me ya sa kuma ya yi jihadi tare da su? Me ya sa ya yi yaqi a qarqashin su?

Wasu malamanku sun ce, wai, yana son ya kare fitina ne. To Me ya sa ya yi yaqin basasar Jamal? Me ya sa ya yi na Siffin? Yaqar da ya yi ma su Nana Aisha Raliyallahu Anha da su Xalhatu da Zubairu da xinbin jama’ar musulmi da ke tare da su, da kuma yaqar da ya yi wa Mu’awiyah da mutanen Sham har aka yi hasarar mutane musulmi sama da 70,000 akan sun qi yin mubaya’a gare shi a matsayin sarki don su basu zave shi ba, wannan shi ba wurin kare fitina ba ne, sai yaqar Abubakar da Umar don ya karvi haqqinsa da Allah ya umurce shi - a tunaninku - na halifanchi?

Mu a wurinmu Aliyu bai yi laifi ba a duk waxannan yaqoqan. Domin fitina ce Allah ya kawo ta a lokacin. Kuma idan fitina ta bayyana, ba mai iya ganin hanyar da zai bi sai wanda Allah ya taimake shi. Abinda ya faru ke nan. Shi ya sa sahabbai da sauran jama’a a wancan lokaci suka kasu kashi uku: Masu mara masa baya don ganin yana da haqqi, da Masu goyon bayan mutanen Sham bisa dalilin jan haqqi na jinin Sayyidina Uthman, da kuma masu shiga tsakani da suka ce, waxancan vangaroran biyu sun auka cikin fitina. Wannan kashi na uku shi ke da rinjayen sahabbai, kuma daga baya kusan kowa ma ya raja’a ga wannan ra’ayi – har shi kansa Sayyidina Ali – in banda ‘yan Sha biyu. Don haka abubuwan da suka auku, qaddarar Allah ce.[5]

Amma muna bin ku bashin hujjar da ta sa ya yi wannan yaqi amma bai yaqi Abubakar da biyu na bayansa ba don ya karvi haqqensa a cewar ku.

Tambaya Ta Talatin Da Biyu

Ku ‘yan Shi’ah kuna ganin cewa, halifofi uku sun qwace mulki saboda kwaxayin duniya. Suka hana wanda Allah ya zava, kuma Manzon Allah ya bayyana don kawai son su ci duniya.

Tambayarmu anan (Ta 32): Me suka samar wa kansu na duniya da suka yi mulkin? Wane ne a cikinsu ya tara dukiya? Domin kuwa duk mun sani cewa, Sayyidina Umar Raliyallahu Anhu ko da ya mutu ana bin sa bashi mai xinbin yawa wanda duk qabilarsu bata iya biya masa, sai da aka nemi taimakon dangi na nesa, Quraishawa sannan aka biya bashinsa. Sayyidina Abubakar da Sayyidina Uthman dukan su attajirai ne; hamshaqan ‘yan kasuwa tun kafin bayyanar musulunci. Kuma ko wannen su sai da ya qarar da dukiyarsa wajen taimakon musulunci kafin qarshen rayuwarsa.

A cikin su wane ne ya sanya xansa ya gade shi? Idan har sun qwace mulki ne don suna kwaxayin duniya, to, basu da ‘ya’ya ne? Ashe ku ‘yan Shi’ah ma ba cewa kuke yi Aliyu ne ya naxa xansa Al-Hasan ba? Me ya sa Abubakar bai naxa xansa “Abdurrahaman” ba? Me yesa Umar bai naxa xansa “Abdullahi” ba? Me ya sa Uthman bai wakilta xansa “Abanu” ba?

Tambaya ta 33: Wace duniya su kuma sauran Sahabbai suka nema da barin wasicin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Mene ne Abubakar ya ba su, ko ya yi alkawalin ba su wanda ya sa suka bar Allah da Manzo domin shi, alhalin su ne waxanda suka bar kowa da komi domin Allah har sai da Allah ya saukar da cewa, ya amince mu su kamar yadda ya zo a cikin Suratul Ma’ida:100 da wasu ayoyi?

Idan kuka gamu da wani cikin khawarij waxanda ke tuhumar sayyidina Ali ya ce maku, ai banda zubar da jinainan musulmi ba abin da mulkin Ali ya tsinana, alhalin mulkin halifofi uku na farko cike ya ke da nasarorin musulmi akan kafirai. A lokacinsu ne ma aka buxe manyan daulolin kafirci, aka shigar da qasashensu a cikin musulunci. Ga Uthmanu an kawo masa takakka a Madina don a yaqe shi amma ya kame hannunsa har aka kashe shi bai kashe kowa ba, bai kuma bari an kashe ba. Shi ko Ali ya tashi ya tafi har Kufa da Basrah don ya yaqi waxanda basu yaqe shi ba. Kawai dai sun ce, ba su yi masa mubaya’a sai an biya tasu bukata. Illa iyaka. Me zaku ce masa?

Ga wata kuma: Idan xan khawarij ya ce maka Allah ya taimaki halifofi uku a duk yaqoqan da suka yi don suna kan gaskiya, amma bai taimaki Aliyu ba a nasa yaqoqa har aka zo aka kashe shi ba wata nasara da ya samu saboda shi ba shi akan gaskiya. Wace amsa zaku ba shi?

Gaskiyar Allah ita ce, ba wanda yake iya kare Ali daga tuhumomin khawarij sai mu Ahlus-Sunnah da muka yarda da sauran halifofi, muka kuma xauka cewa, duk nasarar da suka samu Ali yana hannu a cikin ta. A nasa lokacin kuma qaddarori ne na Ubangiji suka gudana a yadda Allah ya nufe su ba a son ransa ba. Irin duk zarge-zargen da ‘yan Shi’ah ke yi ma halifofi su ne khawarij ke wa Ali. Kuma kariyar Ali tafi wuya. Kamar yadda duk falalar da suke son tabbatar wa Ali tafi sauqin tabbata ga magabatansa.

Tambaya Ta Talatin Da Huxu

‘Yan Shi’ah kuna zargin Sayyidina Umar da cewa lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zai cika ya ce, a kawo takarda ya rubuta ma mutane abin da ba zasu vace ba a bayansa har abada. Kuka ce, yana so ne ya yi masu wasici na qarshe akan wanda zai gade shi. Anan sai Sayyidina Umar ya hana a kawo wannan takarda.

A cikin littafanku na Shi’ah har cewa kuke yi, wai, ya ce: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita hayyacinsa”. Amma a littafanmu ingantattu babu wannan magana. Abin da ya zo a cikin Bukhari da makamantan sa shi ne, cewa ya yi: “Zafin ciwo ya dami Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kada ku qara masa zafi. Alqur’ani ya ishe mu”.

 Ku, ‘yan Shi’ah kuna zargin sayyidina Umar da cewa, ya sava umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, don haka a wurin ku ya kafirta. Kuma ya vatar da al’umma, tunda ya hana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya isar da saqonsa na qarshe. Ya sanya Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya mutu da wannan baqin ciki na rashin isar da saqo.

Tambayarmu (Ta 34): Ina Aliyu yake a wannan lokaci? Me ya sa shi bai zabura ya cika umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba? Ko sayyidina Umar kawai abin ya shafa? Kuma yafi shi qarfi ne? Ko ya rinjaye shi? Me ya sa bai yaqe shi anan ya yi jihadi don tabbatar da manufar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba?

A wata riwaya cikin Musnad na Imamu Ahmad cewa aka yi, lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wannan magana, sayyidina Aliyu ne ya yi fararat ya ce; “Ya Manzon Allah! Ni, ina iya riqewa. Faxi maganar ko wacce ce. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ina yi muku wasici da riqe Sallah, kada kuyi sakaci da ita. Sai Zakkah, ku fitar da ita kamar yadda Allah ya umurce ku, bisa ga bayanan da nayi muku. Ina kuma yi muku wasici da abinda damanku ta mallaka (yana nufin bayi) ku kyautata masu.[6]

To, ashe kenan idan har littafin ba a kawo ba, wane ne ya hana? Wanda ya ce, a bari zai riqe? Ko wanda ya ce, a sassauta wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ciwo ya tsananta masa?

Wannan magana dai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yita ne a safiyar Juma’ah kamar yadda ya zo a nassin riwayar. To, (Tambaya Ta 35) Me ya sa a sauran wunin Juma’ah bai sake cewa a kawo wannan takarda ba? Har ranar Asabar ta zo ta wuce, Lahadi ma haka, har litinin ta zo wadda a hantsinta ya cika?

Tambaya Ta 36: Wannan abin da Manzon Allah zai faxi, kuka ce ya mutu da haushinsa, wai a cikin addini yake ko a wajen sa? Idan a cikin addini yake, kuna nufin kenan addini bai cika ba tun da Manzon Allah ya yi wafati ba a bari ya faxe shi ba? Idan kuma ba a cikin addini yake ba, to, mene ne na damuwa?

Tambaya Ta 37: Shi wannan saqon dole ne sai a rubuce za a bar shi? Me ya hana a faxe shi kowa ya ji don ya zama yankan hujja?

Tambaya Ta 38: Wa ya sanar da ku abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yake son ya yi wasici da shi tun da har bai faxe shi ba, kuka zo kuna ce mana wai, halifanci ne yake son ya damqa ma Sayyidina Ali?

Tambaya Ta 39: Tunda kun ce sayyidina Umar ya sava ma umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ya kuma yi ridda akan haka. To, shi kuma Sayyidina Ali da aka ce ya share sunan Manzon Allah na manzanci ya sanya sunansa na yanka a ranar Hudaibiyyah ya ce ba zai yi ba fa? Shi sayyidina Aliyu mene ne ya yi anan?

A wurin mu Umar da Aliyu duk basu yi laifi ba. Abinda suka yi kuma ya yi dai-dai. Umar dai ya tausaya ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, yace kada a wahalar da shi. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbatar da hakan, don bai sake cewa kome akai ba. Aliyu kuma ya bayyanar da girmamawar sa ga sunan manzanci na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ya ce shi ba zai goge Rasulullahi ba. Manzon Allah kuma bai musa ba, sai ya karva ya goge da kan sa. Idan dai Umar da ya ce kada a kawo takarda ya yi ridda ta sava umurni a ganin ku, to, Ali da ya sava umurnin gogewa me ya yi? Ko ko dai mudu biyu kuke awo da su, kuyi ciko da buhuna iri biyu?

Tambaya Ta Arba’in

‘Yan Shi’a kuna zargin Sayyidina Uthmanu da son danginsa (Banu Umayyata) da kuma fifita su akan sauran jama’a wajen muqamai da sauran ayyukan gwamnati. Har ma kuna yi masa laqabi da “Sodangi” wai don a cewar ku, ya nuna ma sauran jama’a wariya.

Tambaya anan: Idan son dangi laifi ne, Me ya sa Ali Raliyallahu Anhu da ya yi mulki ya naxa nasa dangi? Kuma ma su wane ne ya naxa? Zamu fara. Bismillahi! Gwamnan da ya naxa a Basrah shi ne, Abdullahi xan Abbas xan Abdul-Muxxalibi, (Da mahaifinsa Abbas da Abu-Xalibi; mahaifin Ali wa da qani ne). A Yaman kuwa sai ya naxa Ubaidullahi xan Abbas, qanen wancan na Basrah. A Makkah ya naxa Quthamu xan Abbas, qanen waxancan biyun. A Madina ya naxa Ma’abadu xan Abbas, xan autan waxancan ukun.

Subhanallahi! Gwamna huxu duk ‘ya’yan gida xaya? Kuma duk qannen Sarkin Musulmi?

To, ba su kaxai ne dangin Ali a muqaman gwamnati ba. Domin kuwa gwamnansa na Khurasana ma xan yarsa ne. Shi ne, Ja’adatu xan Hubairata. Mahaifiyarsa ita ce, Ummu Hani’i yar Sayyidina Ali. Ba shi kaxai ba. Gwamnansa na Masar shi ne, Muhammadu xan Abubakar Siddiqu. Kar ka ce wannan ba danginsa ba ne. Domin wace ce mahaifiyarsa? Mahaifiyarsa ita ce, Asma’u xiyar Umaisu wadda take aure da Sayyidina Ali a daidai wannan lokaci da ya naxa shi. Sayyidina Ali ya aure ta ne bayan mutuwar mijinta halifa Abubakar.

To, fa! Yaya kenan? Ba a naxa dangi aka yi haka?

Muna son ku sani cewa, a wurin Ahlus Sunnah, sam, Sayyidina Ali bai yi laifi ba. Haka shi ma Sayyidina Uthman. Domin a muqami buqatar ake wanda ya cancanta ko xan wane ne shi, kuma ko daga ina ya fito, in musulmi ne mai cancanta. To, amma ku da kuke zargin sayyidina Uthmanu sai ku faxa mana kariyar da zaku wa sayyidina Ali don mu duba, watakila mu ma da ita zamu kare sayyidina Uthman. Tare da haka, hanzarin sayyidina Uthman yafi qarfi, saboda dalilai da dama. Daga cikin su har da kasancewar shi, ba fara naxa su ya yi ba, ya isko magabacinsa ne sayyidina Umar ya naxa su, shi kuma bai ga wani dalilin cire su ba don kawai sun haxa zumunta da shi. Na biyu, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kansa ne ya sunnanta naxa ‘yan gidan Umayyata. Domin idan ka lissafa ma’aikatansa babu qabilar da kai yawan ta Umayyata a cikin waxanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya naxa. Amma bai cika naxa Banu Hashimu ba, danginsa shi da sayyidina Ali, ballantana ya yi gwamna huxu ‘yan gida guda.

Tambaya Ta Arba’in Da Xaya

A cikin littafan Shi’ah Kamar Kashful Gummah na Arbali, da Biharul Anwari na Majlisi da Al-manaqib na Khuwarizmi duk an faxi cewa Sayyidina Uthman Raliyallahu Anhu shi ne ya tallafa wa Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu da kuxin da ya yi sadakin matarsa Nana Fatima xiyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Tambaya: Me ya sa Aliyu Raliyallahu Anhu ya karvi wannan tallafi daga mutanen da ku a gurin ku maqiyan Allah ne, kafirai?

Tambaya Ta Arba’in Da Biyu

Me ya sa Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya tura ‘ya’yansa Hasan da Husaini Raliyallahu Anhuma suka je kariyar Sayyidina Uthman Raliyallahu Anhu a lokacin da ‘yan tawaye suka zo zasu kashe shi? Wannan magana tana a littafan Sunnah da na Shi’ah baki xaya.

 Misali duba Tarikhul Umam na Xabari daga cikin Sunnah, a cikin tarihin abinda ya auku a Shekara ta talatin da biyu. Da kuma Murujuz Dhahab na Mas’udi (2/344).

 Me ya sa Ali Raliyallahu Anhu ya tura ‘ya’yansa, wasiyyansa – a wurin ku – don su kare wanda kuke ganin shi kafiri ne, mai qwacen haqqen iyalan gidan Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama? Me ya sa bai bari ayi masa juyin mulki ba, shi kuma sai ya samu damar karvar haqqinsa da aka qwace?. Idan kun ce, wannan maganar ba gaskiya ba ce, shi bai tavuka kome bad a aka zo kasha sayyidina Uthman, to, wace amsa zaku ba Khawarij masu tuhumar cewa, shi Alin ne ya sa aka kashe Uthman don ya hau mulki? Me zaku ce masu?

Tambaya Ta Arba’in Da Uku

Kun ce sayyidina Mu’awiyah kafiri ne. Me ya sa Al-Hasan ya miqa masa ragamar shugabancin musulmi, ya mayar da shi halifan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Bayan cikawar sayyidina Ali fa mutanen kufa - magoya bayan Ali – sun haxu akan yin mubaya’a ga Al-Hasan. A gurin ‘yan Shi’ah ba zavin mutanen Kufa ne ba, naxi ne daga Sarki mai barin gado shi ne sayyidina Ali. Ya naxa xansa don ya gade shi. Abinda Abubakar da Umar da Uthman basu yi ba. Ko ya aka yi dai, Al-Hasan ya zamo shugaba mai faxa a ji a birnin Kufa. Amma bayan wata shidda sai ya gayyato Mu’awiyah, ya ba shi mulkin, da fatar yin haka zai sa a zauna lafiya. Ya kuma tilasta jama’arsa, mutanen Kufa akan yi masa xa’a.

Al-Hasan – ma’asumi a gurin ku – ya shugabantar da kafiri ne akan al’ummar musulmi? Ko kuwa dai sayyidina Mu’awiya musulmi ne, ku ne kuke masa qazafi?

Kashi Na Biyar

Sahabban Manzon Allah

Sallallahu Alaihi Wasallama

 ‘Yan Shi’ah suna qudure cewa, duk sahabbai sun yi ridda bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai kaxan daga cikin su. Wasun su suna cewa, uku ne suka rage. Wasu su ce huxu. Har dai mafi nisa an samu masu cewa, goma sha uku. Akan haka duk surukan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama basu cikin waxannan. Haka ma matayensa da sauran danginsa.

Tambaya Ta Arba’in Da Huxu

Idan sahabbai sun yi ridda, daga wane addini suka yi ridda? Daga addinin Shi’ah ne? Ko daga wane addini? Domin ridda tana nufin canza addini. To, a da su Shi’ah ne suka dawo Sunna ko kuwa? Idan kun yarda babu Shi’ah a lokacinsu, to daga me suka yi ridda? Idan kun ce, ai musuluncin ne dai suka bari, to, suka koma wane addini?

Tambaya Ta Arba’in Da Biyar

Wace amsa zaku bayar da wani zai ce maku wannan addini ba zai yiwu ayi aiki da shi ba tunda ko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasa samar da waxanda zasu tsayu akan addinin su dage har mutuwarsu akan sa?

Waxannan fa su ne waxanda Allah ya shedi qoqarin su, ya yaba ma aikinsu, ya tsarkake zukatansu, ya bada sanarwar ya yarda da su, duk a cikin Alqur’ani. To, idan sun kasa dagewa akan addini wane ne zai iya dagewa akan sa?

Tambaya Ta Arba’in Da Shida

 ‘Yan shi’ah kuna zargin sahabbai da cewa, ranar Hudaibiyya sun qi bin umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama saboda ya karvi yin sulhu da Mushrikai alhalin su basu ji daxi ba. Suna ganin cewa, suna da qarfi, suna bisa gaskiya, ga kuma ayar Alqur’ani tayi musu bushara da cewa, lalle zasu shiga masallaci mai alfarma. Gashi sun zo an ce basu shiga. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa hannu ga yarjejeniyar komawa gida, wadda kuma ta qunshi wasu sharuxxa marasa daxi. Sun haxa da cewa, duk wanda ya musulunta idan ya tafi Madina, Annabi ya mayar da shi. Amma idan wani sahabi ya so ya yi ridda, to, Manzon Allah ba shi da ikon hana shi. Duk dai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Na yarda”.

Sahabbai a wancan lokaci sun yi amanna cewa, wannan sulhu ba zai tabbata ba. Allah zai saukar da wahayi ya wargaza shi. Don haka da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurce su da yanka dabbobinsu, su kwance haramarsu, sai suka yi zamansu jiran ko Allah zai shiga tsakani a cikin wannan lamari. Sai daga bisani bisa ga shawarar iyalinsa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwance haramarsa, ya yanka dabbarsa. Ganin haka, komawa ta tabbata kenan, sai duk sahabbai suka yi abin da ya yi.

To, su ‘yan Shi’ah sai suka fassara wannan da cewa, wai, sahabbai sunyi ridda; sun qi bin umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Tambayarmu anan, a wannan rana ina sayyidina Aliyu ya ke? Ko bai samu fita Hudaibiyya ne ba? Da namu littafai da naku duk sun ce, yana wurin. To, ya aka yi? Me ya sa bai bi umurnin ba koda shi kaxai ya fita daga sahun masu ridda? Iya Tambayar kenan. Kuma duk amsar da kuka bayar game da hujjarsa to, ita ce hujjar Abubakar da Umar da Uthman da ma duk sauran waxanda ke halarce a wannan rana. Illa iyaka.

Tambaya Ta Arba’in Da Bakwai

‘Yan Shi’ah kuna sukar Zubairu xan Awwamu. Kun ce wai, ya yaqi Aliyu Raliyallahu Anhu a yaqin basasar Jamal saboda yana qyamar sa. Tambayarmu anan: Ashe kun manta ne, ko kun yi kamar kun manta cewa, lokacin da aka kafa kwamitin shura na mutum shida, waxanda Sayyidina Umar yace a zavi halifa a cikin su, Zubairu shi ne ya zabura ya ce na bar ma Aliyu haqqina? A lokacin da Xalhatu ya ce, na bar ma Uthmanu, Shi kuma Sa’adu xan Abu Waqqasi ya ce, na bar ma Abdurrahamani xan Aufu. Me ya sa Zubairu Raliyallahu Anhu ya bar ma Aliyu nasa haqqi na halifanci idan yana qyamar sa?

Tambaya Ta Arba’in Da Takwas

Matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kansu basu tsira ba daga bakinku ya ku ‘yan Shi’ah. Da Hafsah da Aisha Allah ya yarda da su sun haxu da miyagun kalamai da qazaman maganganu daga wurin ku. Alhali kuwa su ne mafi soyuwar matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa gare shi. Gashi dai varo- varo a cikin At-Tafsirus-Safi (2/720) da Biharul- Anwar (22/33) da As-Siraxul Mustaqim na Bayadi (3/165), da Aqaidul- Imamiyyah na Zanjani (3/85) da ma kusan duk littafan Shi’ah kun ce waxannan tsarkakakkun matan Manzon Allah kafirai ne. Allah Subhanahu Wa Ta’ala ko ya na cewa:

لِلۡخَبِيثِينَ وَٱلۡخَبِيثُونَ لِلۡخَبِيثَٰتِۖ وَٱلطَّيِّبَٰتُ لِلطَّيِّبِينَ وَٱلطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَٰتِۚ أُوْلَٰٓئِكَ مُبَرَّءُونَ مِمَّا يَقُولُونَۖ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ ٢٦ النور: ٢٦

Ma’ana:

Miyagun mata na miyagun maza ne, miyagun maza kuma na miyagun mata ne. Kuma tsarkakakkun mata na tsakakakkun maza ne, tsarkakakkun maza kuma na tsarkakakkun mata ne. Waxancan su ne waxanda ake barrantawa daga abin da (masu qazafi) ke faxi. Suna da gafara da arziki na karimci.

‘Yan Shi’ah ku zamo masu hankali ayi magana da ku. Mutumin da ya zo ya same ka, ya ce, duk waxanda ka auro ‘ya’yansu ‘yan iska ne. Matanka kuma fajirai ne. Sa’annan waxanda ka aura ma naka ‘ya’ya ba mutanen kirki ba ne. Kuma kai malami ne da duk almajiranka ba mai tsoron Allah sai wane da wane. A tsawon shekaru 23 da ka yi tare da su basu amfana da kome ba sai yin ridda da kauce ma umurnin Allah! Don Allah wannan mutum wa yake nufin ya ce da shi “Mutumin Banza”?

Kashi Na Shida

 Iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Tambaya Ta Arba’in Da Tara

Me ya sa kuka sanya Fatima ita kaxai cikin Ahlul-Baiti ban da sauran ‘ya’yan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Mine ne laifin Zainab da Ruqayyatu da Ummu Kulthumi da Abdullahi da Ibrahim da ma babban yayansu Al-Qasim? mahaifinsu Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya son su ne? Ko shi ya kore su daga cikin iyalansa?

Tambaya Ta Hamsin

Me ya sa kuka fitar da matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama su ma daga iyalan gidansa?

Ya ku ‘yan Shi’ah! Kuyi ma kanku adalchi. Duk wanda aka ce ya kira iyalansa, ya zo da kowa ya baro matarsa, don Allah kuwa yayi ma iyalansa adalchi? Yayi ma matarsa adalchi? Me ya sa baza kuyi ma matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama adalchi ba?

Idan muka koma a Alqur’ani zamu ga ayar da ta sauka akan Ahlul-Baiti da matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama take magana. Haka ita ma ayar da tayi maganar iyalan gidan Annabi Ibrahim da matansa take. Haka iyalan gidan Annabi Luxu matarsa ake nufi. Iyalan Annabi Musa haka. To, don me su matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama?!!! Haba wannan tsana, haba wannan qiyayya, don Allah ku rage musu ita mana!!!

Kashi Na Bakwai

Alaqa Tsakanin Iyalan Annabi Da Sahabbai

Tambaya Ta Hamsin Da Xaya

Dukkan mu mun sani cewa, musulunci ya yi umurni da mu zavi na kirki wajen aure da kuma aurarwa. Akan haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurce mu da, mu zavi surukai na gari.

To, me ya sa shi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya je ya yi aure gidan “yan iska” a cewar ku? Ya je ya auri xiyar Sayyidina Umar, wanda a gurin ku xan zina ne? Kamar yadda Bahrani ya faxa a cikin Al-Kashkul (3/212). Kai! A cikin littafin Jaza’iri – daga cikin malamanku –Al Anwarun Nu’umaniyyah (1/63) cewa ya yi, wai, Umar yana da wani ciwon hauka, wanda kuma ba ya kwanta masa sai da ruwan maza. Ma’ana wai, sai an yi liwaxi da shi sannan hankalinsa ya kwanta! Wal iyazu billahi! Wallahi ba don faxin kafirci a matsayin labari ba kafirci ba ne da bamu halasta ko hikaito wannan magana. Amma tana nan a cikin littafinku inda muka faxa.

Tambayarmu dai ita ce: Me ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi surukuta da shi? Yanzu xayanku zai yarda a ce uban matarsa “Xan iska” ne, ko “Mazinaci” ko “Xan Liwaxi”?

Tambaya Ta Hamsin Da Biyu

Me ya sa Ahlul-baiti suka yi surukuta da Sahabbai? Me ya sa Sahabbai suka yi surukuta da iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, alhalin a cewar ku, su maqiyan juna ne? Addinin da ake koya ma ‘yan Shi’ah shi ne cewa, sahabbai sun muzguna ma Ahlul-baiti, sun zalunce su, sun takura masu. Don haka yanzu ma neman masu haqqinsu ne suke yi. Kuma akan haka suke yawaita ziyarar qaburburansu suna addu’a, wai Allah ya yi masu baqar isa ga maqiyansu, cewa da Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama! Me ya sa suka yi surukuta da junan su? Bari mu xan bada misalai kaxan;

Idan muka soma daga asali Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kansa su wa ye surukansa? Duk matan nasa goma sha xaya ‘ya’yan wa ye? Idan ma ka xauka sauran ‘ya’yan sahabbai ne ba to, Aisha Raliyallahu Anha xiyar wa ce? Hafsatu fa?

Shi kuma su wa ya aurar wa nasa ‘ya’yan? Da yawan mu basu san cewa ba Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana da ‘ya’ya huxu mata, kuma duk ya aurar da su. Xayar kawai aka sani, ita ce, ‘yar autar su Fatima. Amma duk ukun a gidan Banu Umayya ya aurar da su. Baban Asimu xan Rabi’u shi ne surukin farko da Manzon Allah ya aurar ma ‘yarsa Zainab. Xan gidan Umayyah ne. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuma da kansa ya yabe shi, inda yake cewa; “Mun yi surukuta da shi mun ji daxi. Ya kuma yi mana alqawari ya cika”.

Sauran ‘ya’yan biyu kuwa, Ruqayyatu da Ummu Kulsumi duk sayyidina Uthmanu ne aka aura ma su, xaya bayan xaya. Duk a tarihin ‘yan adam kuwa ba’a tava samun wanda ya kulle qofar gidansa da ‘ya’yan Annabi biyu ba in ban da xan gidan Umayyah, Sayyidina Uthman Raliyallahu Anhu. Shi ya sa malaman tarihi ke ce masa Dhun Nuraini, Mai haske biyu. Don kuwa duk wanda ya auri xiyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya samu haske. Amma shi Uthmanu biyu ya samu.

A yanzu bari mu bada ‘yan misalai na surukuta da Ahlulbaiti a vangaren gidan Uthman xin kawai. Sauran bayanin sai a duba littafan da muka wallafa akan wannan.[7] Bari kuma mu fara da babban xansa Abanu xan Uthman, wanda shi ya auri Ummu-Kulthum ‘yar Abdullahi xan Ja’afar xan Abu-Talib. Sai kuma Musa xan Abanu, jikan Sayyidina Uthman Raliyallahu Anhu kenan. Shi kuma ya auri Ummul-Qasim xiyar Alhasan, jikanyar Alhasan xan Aliyu xan Abu Xalib.

 Haka kuma wani jikan na Sayyidina Uthman; Zaidu xan Asim xan Uthman, ya auri Sukainatu xiyar Husaini xan Ali. An ce, a cikin tarihin larabawa ba’a tava kyakkyawar mace irin Sukainar nan ‘yar Husaini ba, sai ko A’ishatu xiyar Xalhatu xan Ubaidullahi.

Abdullahi xan Abanu xan Uthman shi ma ya auri Fatima ‘yar Husaini xan Ali, qanwar Sukainatu.

Duka wannan auratayyar Ahlulbaiti da gida xaya na Sahabbai kenan, shi ne gidan Sayyidina Uthman xan Affan, xaya daga fitattun Banu Umayyah.

Aje wannan magana a yanzu. Ko ka san cewa, Yazidu xan Mu’awiyah, wanda ‘yan Shi’ah ke zargi da kisan Husaini, yana aure ne da ‘yar tsatson Ahlulbaiti, ita ce Ummu Kulthum xiyar Abdullahi xan Abbas xan Abdul Muxxalib, kuma har ta haifa masa ‘ya’ya biyu; Amru da Abdullahi?.

Anya kuwa akwai adawar nan da kuke faxa a tsakanin Ahlulbaiti da sauran musulmi? Ko kuwa dai kuna gurvata tarihi ne kawai?

Tambaya Ta Hamsin Da Uku

Me ya sa Sayyidina Ali ya aurar da ‘yar cikinsa ga Sarkin Musulmi Umar xan Haxxabi? Ashe ba shi ne kuka ce ya tashi kashe uwarta don ta nemi haqqinta na gado ba? Ko dai shi ma tasa sakayyar kenan da Sayyidina Ali ya yi masa akan nasa xanyen aiki? A gurinku Sayyidina Umar “Xan Zina” ne. Can ga bakinku! Kun tuhumce shi da abubuwan da harshen duk musulmi na qyamar ya hikaito su akan surukin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, surukin Ali Raliyallahu Anhu, alqalami ma na jin nauyin rubuta tuhumominku akan sa. Kun kafirta shi, har ma kun ce yafi shexan shexanci. Malaminku Ni’imatullahil Jaza’iri cewa ya yi, a ranar alqiyamah shexan ma sai ya saki baki yana kallon azabar da ake wa Umar! To, ya aka yi sayyidina Aliyu ya xauki xiyarsa ya aura masa? Ko don ita Nana Fatima mahaifiyarta ba ta da rai ne?

Labarin yadda aka xaura wannan aure dai ya zo a littafanmu na Sunnah da ma naku na Shi’ah. Kamar Al-kafi fil furu’i da Tahzibul Alhkami na Tusi.

Ummu-Kulthum ‘yar Ali ta Haifa ma sayyidina Umar ‘ya’ya biyu: Zaidu da Ruqayyah. Su biyun kuwa suna alfahari da cewa, su ‘yan gidan halifofi biyu ne; Umar ne uban su, Ali ne kakan su.

To, idan Aliyu ma’asumi ne ya aka yi ya aurar da xiyarsa ga kafiri? Ba ku da mafita sai xayan biyu anan; Ku yarda Umar ba kafiri ba ne. Da haka kuwa duk aqidarku ta wargaje. Ko kuma ku ce Aliyu ba ma’asumi ne ba. A nan ma dai aqidar taku ta wargaje. Dama dai mu mun san yanar gizo ta fi ta albarka.

Tambaya Ta Hamsin Da Huxu

Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya auri mata da yawa kuma sun haifa masa ‘ya’ya da dama bayan rasuwar uwargidansa Nana Fatima Raliyallahu Anha. Zan yi tambaya bayan sharhi mai xan tsayi daga cikin littafanku na Shi’ah.

 Ba zan so in jera sunayen iyalansa da mutanen gidansa daga littafan sunna ba. Don haka, bari mu duba cikin Kashful Ghummah na Arbali da Biharul Anwari na Majlisi, tun da yake suna cikin fitattun littafan Shi’ah. Ga jerin sunayen matansa da ‘ya’yansa daga cikin waxannan littafai.

 Da farko, Sayyidina Ali ya auri Ummul Banina ‘yar gidan Haramul-Kalbi. Ita ce kuma ta haifa masa Abbas da Ja’afar da Abdullahi da Uthman.

 Sannan Ya auri Laila ‘yar gidan Mas’udut-Tamimi. Ta Haifa masa Abdullahi da Abubakar. Duk ‘ya’yan xakunan nan biyu sun yi shahadah tare da wansu Husaini a karbala.

 Sannan kuma ya auri Asma’u ‘yar gidan Umaisu, xaya daga cikin matan da suka yi wa sayyidina Abubakar Raliyallahu Anhu wanka (takaba). Bayan rasuwar sa ne kuma da ta cika idda sayyidina Ali ya aure ta. Kafin haka, a lokacin da mai xakin Ali, ita ce Nana Fatima Raliyallahu Anha ta rasu wannan Asma’un ce, matar sayyidina Abubakar tayi mata wanka. Duk wannan yana a cikin littafan Shi’ah. Kafin ta auri waxannan sadaukai kuma sarakai, Asma’u ita ce ta wanki Ja’afaru xan Abu Xalib yayan Ali Raliyallahu Anhuma. Ta kuma haifi “Muhammad” a duk gidajen nan da tayi aure guda uku. Shi dai Ali bayan ta haifa masa Muhammad, sai ta sake haifa masa Yahaya da kuma Aunu. A cikin ‘ya ‘yanta ba wanda ya bar zuri’a.

 Sannan Ali ya auri Ummu Habiba ‘yar gidan Zama’atu. Dalilin auren ta kuma shi ne, Ali ya fita yaqi a zamanin halifancin Sayyidina Abubakar, a qarqashin tutar Khalidu xan Walidu Raliyallahu Anhu, inda suka kai farmaki a wani wuri da ake kira Ainut Tammari a qasar Iraqi. A can ne Ali ya samu ganimar wannan baiwar Allah. Daga bisani ya xiyauta ya, kuma ya aureta. Ta haifa masa Ruqayyatu da Umar. Xanta, Umar kuwa ya yi tsawon rai, don sai da ya shekara talatin da biyar 35 a duniya.

 Sannan Ali ya auri Ummu sa’idu ‘yar gidan Urwatu xan Mas’udus-Saqafi, sanannen sahabin nan na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Ita ta haifa masa Ummul Hasan da Ramlatul- Kubra.

 Sannan ya auri Umamatu ‘yar Baban Asimu xan Rabi’u. Ita kuma jikanyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ce ta wajen babbar ‘yarsa Zainab. An ce ma, Nana Fatima ce Raliyallahu Anha, ta yi masa wasicin ya aure ta gaf da rasuwar ta.

Umamatu dai ita ce wadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ke xaukar ta, a lokacin da yake sallah. In ya yi sujada sai ya aje ta, in ya tashi tsaye kuma ya sake xaukar ta, a lokacin tana qarama.

Umamatu ta haifa ma Ali Muhammadul- Ausax. Na biyu kenan daga cikin Muhammad uku da Aliyu Raliyallahu Anhu ya haifa.

 Sannan ya auri Khaulatu ‘yar gidan Ja’afar Al-hanafiyah. Ita ma dai a zamanin halifancin Abubakar ne, a kuma yaqoqan da aka yi na Ridda ya same ta a cikin ganima. ‘Yan Shi’ah dai har yau basu yarda cewa, Ridda mutane suka yi ba. A cewar su tawaye ne aka yi ma Abubakar Raliyallahu Anhu. To, ko mene ne dai Ali Raliyallahu Anhu ya bada rayuwarsa a wajen yaqar su. Har ya ribanto wannan baiwar Allah wadda ta haifa masa Muhammadul-Akbar wanda aka fi sani da Ibnul Hanafiyyah. Kuma yana cikin Imamai ma’asumai a wurin wasu vangarori na Shi’ah.

 Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ko da ya cika yana da mata huxu 4, da kuyangi goma sha tara 19. Daga cikin ‘ya’yansa mata banda waxannan da muka faxa, akwai; Ummu Hani’i da Maimunatu da Zainabul Kubra da Ramlatus-Sugra da Ummu Kulthumis-Sugra da Fatimah da Ummu Khadijah da Ummul Kirami da Ummu Ja’afaru da Ummu Salamata da Jumanatu. Duka- duka ‘ya’yansa maza goma sha huxu (14) mata goma sha bakwai (17). Da yawa daga cikin su sun yi shahada a Karbala.

Zuri’ar sayyidina Ali ta yaxu ne kawai ta wajen: Al-Hasan da Al-Husaini. Al-Husaini xin ma ta hanyar Zainul-Abidina, wanda shi ne mai rabon ganin baxi daga cikin ‘ya’yan Husaini da suka zo Karbala. Dalili kuwa bai riqa makami ba don ba shi da lafiya. Su kuma ‘yan ta’adda sai basu ce masa uffan ba, ballantana su kashe shi. Da Muhammad Ibnul Hanafiyyah da Abbas da Umar su ne suka haifi zuri’ar da ta yaxu bayan Sayyadi Ali.

Tambaya anan (Ta 54): Me ya sa Ali Raliyallahu Anhu ya sa ma ‘ya’yansa na tsatsonsa waxanda kuma ya haife su ne bayan rasuwar Nana Fatimah, a zamanin halifancin Abubakar da Umar da Uthman, ya sa masu sunayen halifofi masu ci a lokacin? A cikin ‘ya’yansa da muka zana har da Abubakar da Umar da Uthman. Waxannan ‘ya’yan nasa duk sunayensu sun zo a cikin Kashful Ghummati na Arbali da Biharul Anwari na Majalisi waxanda suna cikin madogara a littafan Shi’ah.

Don Allah xan uwa mai hankali ka tava jin wani bayahude ya sa ma xansa suna Muhammadu? Ko hankali yana xaukar cewa, Muhammadu ya sa ma xansa suna Jacob? A nan Najeriya ‘yan Shi’a da dama sun sauya sunayensu daga Abubakar da Umar da Uthman don kauce ma sunayen mutanen banza a cewar su. Jiya jiya wallahi, jiya Alhamis wata baiwar Allah ta zo gidana ta bayyanar da tuban ta. Ta bayyana min cewa, sunanta Aisha, amma har ta canza suna. ‘Yar nan Jihar Sakkwato ce. A yanzu ta sake koma ma sunanta na asali.

Ya aka yi Aliyu Raliyallahu Anhu ya sa ma ‘ya’yansa sunan maqiyan Allah Subhanahu Wa Ta’ala a gurin ku? Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu duk a cikin Quraishawa shi kaxai ne wanda aka samu ya sanya sunayen halifofi uku gaba xaya: Abubakar da Umar da Uthman. A zamaninsa ba a tava samun baquraishen da ya yi wannan ba. Saboda yana qaunarsu ya sanya ma ‘ya’yansa sunayensu ko saboda yana qyamar su?

Ku ‘yan Shi’ar Najeriya kuna ta canza sunayenku. Kuma muna da masaniya cewa, kuna samun shawarwari daga qasa mai tsarki a gurin ku. Domin da yawa mun ji labarin waxanda suka je Iran suna da sunan Abubakar ko Umar sai aka basu shawarar canza sunayen, domin a cewarsu wai, babu alheri ga duk mai irin wannan suna!

Tambaya (Ta 55): Me ya sa kuka qago bidi’ar qaurace ma waxannan sunaye bayan can da magabatanku suna sa waxannan sunaye?

Alal misali, a duba littafin Al-kafi, mafi tsarkin littafan duniya a wurin ku. Mu fara duba muqaddimarsa, su wane ne suka ruwaito duk ilmin da kuke jinginawa ga Ahlul-baiti?

Bari in zavo muku kaxan daga cikin sunayen: Mufaddal ibnu Umar, Ahmad ibnu Umar Al-halabi, Umar ibnu Aban, Umar ibnu Uzainah, Umar ibnu Hanzalah, Musa ibnu Umar, Abbas ibnu Umar.

Me ya sa duk waxannan magabatan naku ba su canza sunayensu ba, amma ku kuke canzawa? Kuma tun can farko sun sanya waxannan sunayen ne don suna qaunar sahabi Umar ko don suna qyamarsa?

Tambaya (Ta 56): Me ya sa Ali Raliyallahu Anhu ya halalta wa kansa saduwa da fursunoni mata waxanda aka qwato su bisa ga zalunci a gurinku? Duk yaqoqan da aka yi a lokacin Abubakar da Umar da Uthman a wurin ‘yan Shi’ah zalunci ne. Me ya sa su waxanda aka kamo xin Ali ya halalta ma kansa su?

Tambaya Ta Hamsin Da Bakwai

‘Yan Shi’ah kun ce Abubakar ya cuci Nana Fatimah, ya hana ta gadonta. Mawaqinku na gadon qaya akan haka yana cewa:

Ku tuna da na can gabanku

Ko Sahabbai an irin ku

Masu sharri yafi naku

Sun yi wa Imam Ali “Ku”

Fatima basu bar ta ta natsa ba.

Sun qazaf gun maigidanta

Ita kuma gadon ubanta

Suka danne, suka qi bata

Sun yi yaqi da maigidanta

Wai kan bai yo mubaya’a ba

 Kun ce sayyidina Abubakar ya danne mata haqqi, sai da tai kuka ga Manzon Allah, ta rinqa zuwa wurin qabarinsa tana zubar da hawaye, tana cewa, “Ya Manzon Allah! na kawo qara gare ka”! Kuma wai, sai da ta je kasuwa ta ci mutuncin halifa Abubakar tare da sayyidina Umar! Abin da ya jawo har Umar ya shure ta, ya zubar mata da cikin da take xauke da shi.

Wannan cikin da aka zubar har kun bashi suna “Muhsinu”. Mu kuwa a sanin mu “Muhsinu” yaronta ne da ta haifa, kuma har ya fara rarrafe, sannan Allah ya karvi ransa.

Tambaya (Ta 58) anan: Abubakar ya qwace haqqin fatima tana a matsayin matar wa? Aliyu ba shi ne Asadul Usudi gamji mai wuyar karo ba? Ba shi ne shugaban jarumawa ba? Me ya sa bai qwato mata haqqinta ba? Akan Abubakar ya sa an zubar da cikin xansa shi ya sa ya yi masa sakayya ya auri matarsa a bayan cikawarsa, ya riqa nasa xan (Muhammadu xan Abubakar) ya yi renon sa a cikin gidansa, kuma da ya zama shugaba ya naxa shi Gwamna?

Tambaya (Ta 59): Shin wannan gonar ta Fadak, kyauta ce Annabi ya ba ta ko gado ne zata yi? Idan kyauta ce, to, ya aka yi Manzon Allah ya bata kyauta, alhalin ga Zainab bai bata ba? Ga Ummu Kulthum, ita ma da ranta da lafiyarta a lokacin, don kuwa sai da ta yi shekaru uku bayan khaybar sannan ta rasu, a shekara ta tara bayan hijira. Ma’ana har kusa-kusan wafatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tana duniya. To, me ya sa bai basu ba, ya ba Fatima? Ashe Manzon Allah ba shi ne ba ya ce ma Bushairu xan Sa’adu a lokacin da ya so ya ba wa xansa Huzaifa kyautar gona har ya ce Annabi ya zo ya yi shaida, Annabi ya tambaye shi: “Kana da wasu ‘ya’yan”? Ya ce: “eh”. Ya ce: “to, duk ka basu irin wannan kyautar?” Ya ce: “A’a”. Sai Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa: “Ni ba na shedun zalunci”. (Sahihul Bukhari 2456, Sahihu Muslim 3058).

Idan kuma kun ce, kyauta ce aka bata, to, gonar tana hannunta ne Abubakar ya zo ya qwace? ko kuma ba ta a hannunta ne, a sadda take son ta karve ta ne ya hana ta? Domin a qa’idar Shari’ah, idan aka baka kyauta baka karva ba har wanda ya baka ita ya mutu, kyautar ta tashi, babu ta.

Idan kuma kun ce, wannan gonar ba kyauta ba ce, gado ne, to, ina sauran magada da basu ja haqqinsu ba? Ko kun manta Abbas baffan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne, kuma shi ne wanda zai shamakance Ali a matsayinsa na xan baffa daga gadon Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama in har akwai gadon?

A wurin masana, ba a gadon Annabawa. Domin ruwaya ta tabbata daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama akan haka. Daga cikin waxanda suka riwaito hakan kuwa har da sayyidina Ali shi kansa da Abbas da wasu mutum shida daga cikin Asharatul Mubassharuna bil Jannah, waxanda suka haxa da; Abubakar, Umar, Uthman, Abdurrahman xan Aufu, Zubairu xan Awwamu, da Sa’adu xan Abu Waqqasi. Gaba xayan su sun ruwaito Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mu Annabawa ba a gadon mu. Abin da duk muka bari ya zamo sadaka ga musulmi”.

Mun yarda cewa, Fatima ta nemi Abubakar ya bata gado, domin bata san da wannan bayanin ba. Ba laifi ta yi ba. Shi kuma halifa Abubakar bai bata gadon ba, don Annabi ne ya hana ta. Shi ma bai yi laifi ba. An ruwaito cewa, ba ta ji daxin hakan ba. To, amma saboda me? Ba a yi mata bayani ba? Ko dai bata gamsu ba? Mu Ahlus-Sunnah laluben uzurinta da nema mata hanzari muke yi. Amma ina laifin Abubakar?

Cewar da kuka yi tayi jayayya da Abubakar, har tayi faxa da shi a kasuwa. Shin wa kuke son kuce xan iska ne? Ko Fati mai tuwo tashar mota zata yi faxa da sarkin Musulmi ta tsira da mutuncinta? Ko a kasuwar bacci ta kaduna aka ji wata Fati tayi faxa da lumo; sarkin kasuwa ai ba za ace ta yi bajinta ba! Ko dai kun manta Abubakar aminin mahaifinta ne tun suna yara? Kuma ashe ba shi ne mutum na farko da ya gaskata mahaifinta daga wajen gidansa ba? Ba shi ne Abokin tafiyarsa a lokacin hijirarsa zuwa Madina ba? Ba surukinsa ne uban matarsa ba? Kuma duk dai Fatima ta yi yajin ci masa mutunci a kasuwa?

A cikin littafin Al Bidayah wan Nihayah na Ibnu Kathir an ce, Abubakar Raliyallahu Anhu, yaje ya nemi ya fahimtar da ita bayan da ya san cewa, ranta bai yi daxi ba. Tare da izinin mijinta ya shiga har xakinta ya bata haquri, ta ce da shi: “Ba kome. Na haqura”. Haka kuma sayyidina Abubakar ya hannunta wannan gonar ga Aliyu da Abbas a matsayin su na jigon iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama domin su gudanar da sha’aninta kamar wada shi da kansa Sallallahu Alaihi Wasallama yake yi sadda yana raye, ba a matsayin gado ba.

Tambaya (Ta 60): Ina labarin wannan gona bayan zamanin halifofi guda uku? Domin ko idan gonar haqqin Fatima ce, to, ya kamata Ali ya hannunta ta ga magadanta waxanda su ne, shi kansa da ‘ya’yansa na wajenta. To, bamu ji samatar wannan magana ba a zamanin mulkinsa. Ina labarin ya kwana a tatsuniyarku?

Tambaya (Ta 61): A cikin littafanku an ce, mace bata gadon qasa, bata gadon fili. Kulaini a cikin Al-kafi fil furu’i (7/127) ya yi babi mai suna “Mata basu gadon komai a fili”. A cikinsa ya kawo ruwaya daga Baban Abdullahi wanda aka Tambaya: “Shin mata me suke gado? Sai ya ce: “Ana basu kuxin laka, da kuxin gini, da kuxin icce. Amma qasa ko gona da fili basu da komai na gado a cikin su. Tambaya anan: Don me Fatima ta je neman abinda bata da gado a cikin sa? Wannan ruwayar har wayau akwai ta a cikin At-tahzib na Tusi (9/254).

Tambaya (Ta 62): A cikin ruwayoyinku kuka ce: “Duk abinda yake na Manzo ne, to, bayan Manzon na Imamu ne”. Kamar yadda ya zo a cikin Alkafi, kitabul hujja, (1/476). To don me Fatima ta zo neman abinda yake na Imamu ne? Abubakar kuwa shi ne Imamun. In kun ce, a’a, to, me ya sa Aliyu bai je neman ba, tunda yake shi ne Imamu a gurin ku?

Kashi Na Takwas

 Daga Tafsirin Alqur’ani Tambaya Ta Sittin Da Uku Allah Subhanahu Wa Ta’ala Yana cewa:

لَّقَدۡ رَضِيَ ٱللَّهُ عَنِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذۡ يُبَايِعُونَكَ تَحۡتَ ٱلشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمۡ فَأَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ عَلَيۡهِمۡ وَأَثَٰبَهُمۡ فَتۡحٗا قَرِيبٗا ١٨ الفتح: ١٨

Ma’ana:

Haqiqa, Allah ya yarda da Muminai a lokacin da suke yi maka mubaya’a a qarqashin bishiya. Kuma Allah Ya san abinda ke cikin zukatansu, don haka ya saukar musu da natsuwa, kuma ya basu tukuici da buxi wanda yake kusa kusa.

 Suratul Fathi: 18

Tambaya anan (Ta 64): Shin da Allah ya ce ya yarda da muminai, ya aminta da su, su wa ke da wannan takardar sheda? Kuma me shedar take nufi? Su ‘yan wuta ne kenan ko ‘yan aljanna? Ashe duk duniya ba ta yarda ba da cewa, halifofin nan uku na cikin waxanda wannan aya ta sauka akan su, suka samu wannan sheda? Waxanda Allah ya xaukaki addininsa da su, kuma har ya faxi ya amince masu, ya yarda da su, daidai ne a zage su? Da Allah ya ce ya san abin da ke cikin zukatansu don haka ya basu tukuicin buxi ba da vata lokaci ba. Wannan abin da ke cikin zukatansu munafinci ne ko Imani? Wane irin tukuici ne ya basu? Xaukakar addini ne ko rushewar sa?

Tambaya Ta Sittin Da Biyar: Kuma Allah maxaukaki yana cewa:

وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ فِيكُمۡ رَسُولَ ٱللَّهِۚ لَوۡ يُطِيعُكُمۡ فِي كَثِيرٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِ لَعَنِتُّمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ حَبَّبَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡإِيمَٰنَ وَزَيَّنَهُۥ فِي قُلُوبِكُمۡ وَكَرَّهَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡكُفۡرَ وَٱلۡفُسُوقَ وَٱلۡعِصۡيَانَۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلرَّٰشِدُونَ ٧ الحجرات: ٧

Ma’ana:

Ku sani haqiqa Annabi yana a cikin ku. Da zai yi muku xa’a a cikin al’amurra da yawa da kun wahala.[8] Amma kuma Allah shi ya soyar maku da imani, ya qawatar da shi a zukatanku. Kuma Ya qyamatar da kafirci da fasiqanci da savo a gare ku. Waxancan su ne shiryayyu.

 Suratul Hujurat: 7

Tambaya guda xaya ce a nan, Allah na gaya mana abinda ke cikin zukatansu na imani, ku kuma kun ce mana a zukatansu munafukai ne. Allah ya ce shi da kansa ya sanya masu sha’awar gaskiya da qin qarya, ku kuma kun ce su ne suka xaure wa qarya gindi. Shin kun fi Allah sani ne?

Kashi Na Tara

Makokin Hussaini

Tambaya Ta Sittin Da Shida

Wa ya kashe Husaini? Na tabbata zaku yi fararat, ku ce: “Yazidu”!. Sai in ce, ina hujja?

Mu koma ma littafanku. Su ne alqalai a yau a tsakanin mu. Littafan Shi’ah sun wanke Yazidu tsabal daga wannan xanyen aiki!. Ku saurara!

A cikin A’ayanus Shi’ah kashi na farko, shafi na 34, Sayyid Muhsinu Al Amin ya ce: “Mutane 20,000 suka yi mubaya’a ga Husaini cikin mutanen Iraqi…” su wa kenan? ‘yan Shi’ah! “…Sun yaudare shi, sun yi fito na fito da shi, alhali suna da mubaya’arsa ga wuyayensu, suka kashe shi”.

To, tun da ‘yan Shi’ah ne suka kashe shi wa zaku tada ma hankali?

Imamu Zainul Abidin[9], ga abinda yake ce wa ‘yan Shi’ar Kufah kamar yadda ya zo a cikin Al-Ihtijaj (2/32): “Shin kun manta ku kuka rubuta wasiqu kuka yaudare shi, kuka ba shi alqawari mai qarfi daga wurin ku, sannan kuka yaqe shi, kuka tozarta shi? Da wane ido zaku kalli Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana ce muku: “Kun yi yaqi da zuriyata, sannan kun keta alfarmata. Ku baku cikin al-ummata!”.

A wani wurin (2/29) ga abin da yake cewa: “Yan Shi’ah suna kukan an kashe iyayena. To wa ya kashe su in ba su ba?”.

Wani abin al’ajabi shi ne, in ka duba sunayen waxanda suka halarci kisan Husainin, da ma waxanda suka sa hannunsu ga kisan nasa, kai! Har da wanda ya cire kansa bayan an kashe shi, da gwamnan da ya haxa rundunar ya tura ta, zaka tarar duk sunayen waxanda suke cikin rundunar Ali ne ranar Siffin! To, su wa kenan ba ‘yan Shi’ah ba?

Daga cikin malaman Shi’ah da suka tabbatar da wannan magana cewa, ‘yan Shi’ar da suka kira Husaini su ne suka kashe shi har da; Kazim Al Ahsa’i a cikin Ashura shafi na 89 da Abbas Al Qummi a cikin Nafathul Mahmumi shafi na 365 da Tusi a cikin Muntahal Amal (1/485) da Murtadhal Mutahhari a cikin Al Malhamatul Husainiyyah (4/94).

Yanzu da yake mun tabbatar da cewa, ‘yan Shi’ah ne munafukai suka kashe Husaini sannan suka dawo suna yi masa makokin qarya.. Bari mu bada labarin a yadda ya ke. Bismillahi.

Abinda ya faru shi ne; mutanen Kufah bayan da suka lura da abinda suka yi, sai suka fito suka yi wata runduna mai suna Jundut Tawwabin, rudunar masu tuba. Wai yanzu sun tuba, sun gano sun yi ma Allah laifi!. Husaini yana zaman sa lafiya a amintaccen gari; Makka, suka aika da wasiqa xauke da sa hannun mutum 15,000 ko 20,000. Shi kuma da yaga an shirya, ga masoyansa can ba abin da suke jira sai isowar sa ayi juyin mulki. Ya shirya ya fita, ya kuma qi sauraren duk shawarwarin da aka yi ta ba shi akan yin hattara da alkawullan ‘yan Shi’ah. Kafin ya tafi kuwa sai da ya aike da xan baffansa Muslimu xan Aqilu aka yi masa tarbo na ji da faxi, shi kuma ya aika masa da alamar koren haske.

Tafiyar xan saqon Muslimu ke da wuya sai lamari ya juya; reshe ya jirkice da mujiya. ‘Yan Shi’ah sun miqa Muslimu an tsire shi. Ina ma ace wannan labari ya kai ga Husaini! Kash, qaddara ta riga fata.

Husaini ya iso kusa da Kufah, a wani wuri mai suna Karbala. Tsammanin Husaini ne ya tarar da dubun dubatar masu tarbon sa. Amma sai ya ga fuskokin da ya sani a cikin rundunar mahaifinsa. Sun zo don su tarbe shi? A’a, don su kashe shi! Kuma haka aka yi xin, bayan duk hanyoyin sulhuntawa sun ci tura.

Tambaya Ta Sittin Da Bakwai

Me ya sa kuke kuka, kuke hargowa, kuke tsaga jiki, har da marin fuska a ranar ashura wai, don tuna mutuwar Husaini? Hala ba ku tuna mutuwar Al-Hasan? Ba kun ce, ya fi shi daraja ba?. Ba ku tuna mutuwar babansu Aliyu? Kai! Me ya sa ba ku tuna mutuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Wa ya tava jin ‘yan Shi’ah sun yi makokin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Me ya sa suke makokin Husaini?

Tambaya Ta Sittin Da Takwas

Me ya sa duk a littafanku da laccocinku da bayananku da jaridunku da website xin ku, idan kuna maganar makokin Husaini, baku sa sauran ‘yan uwansa da suka yi shahada tare da shi a Karbala?

Bari mu koma cikin littafanku mu gani. Ai ba shi kaxai ya yi shahada ba a Karbala. A cikin Al-Irshad na Mufid shafi na 194 da kuma Muntahal Amal (1/240) da Jala’ul Uyun na Majlisi shafi na 582 duk an faxi cewa, Abubakar xan Ali xan Abu Xalib da Umar xan Ali xan Abu Xalib da Uthman xan Ali xan Abu Xalib da Abubakar xan Hasan xan Ali xan Abu Xalib da Umar xan Husaini xan Ali xan Abu Xalib duk waxannan sun yi shahada a Karbala. Me ya sa baku faxar su? Don sunayensu ne da ba kwa so? Ko me ya sa haka?

Tambaya Ta Sittin Da Tara

Idan wannan marin fuska da kuke yi da fitar da jini addini ne, to, me ya sa ba ayi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Me ya sa Ali Raliyallahu Anhu bai yi irin wannan makokin ba lokacin da Nana Fatima ta cika? Kai! Me ya sa Aliyu Raliyallahu Anhu bai yi shi ba lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rabu da duniya?

Tambaya Ta Saba’in

Shi wannan makokin da ku ke yi ranar ashura sunnah ne ko bidi’a? Kafin ku ce komi, bari mu koma cikin littafanku mu gani.

 A cikin Mustadrakul Wasa’il da Nahjul Balagah akwai wata magana da Sayyidina Ali ya yi inda yake cewa - a lokacin rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama – ya ce: “Wallahi ya Manzon Allah! in ba don da kai ne ka yi umurni da haquri ba, ka hana ayi raki, da mun zubar da hawayen da ke jikinmu saboda mutuwarka. Amma tunda ka hana ba zamu yi ba”. A cikin littafin Al Khisal na Saduq, a shafi na 621 da kuma cikin “Wasa’ilus Shi’ah” ga abin da Ali Raliyallahu Anhu yake cewa, “Duk wanda ya xauki hannunsa ya buga ga cinyarsa idan musiba ta cim masa to, duk ya ruguza aikinsa”. To, ka gani! Ashe ‘yan Shi’ah dama duk kun ruguza aikinku baku sani ba!!

A cikin Muntahal Amal shafi na 248 Al-Husaini xin kansa, wanda suke ma kuka a cewar su, yana ce ma ‘yar uwarsa Zainab ‘yar Ali: “Na gama ki da Allah, idan aka kashe ni to, kada ki yaga rigarki. Kada ki tsaga fuskarki. Kada ki kira waiyo Allah”. to ku ‘yan Shi’ah don Allah mine ne kuke yi?

A cikin Furu’ul Kafi na Kulaini (5/557) ga wasicin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yake yi wa xiyarsa Nana Fatima: “Idan na cika don Allah kada ki tsaga fuska, kada ki saki gashi. (mata a da sukan yi haka, su daina gyaran kansu idan uba ko xa ko miji ya rasu). Sannan kar ki kira waiyo Allah. Kada kuma ki gayyato duk wata mai kukan mutuwa”.

To, ku ‘yan Shi’ar yau don me kuke marin fuskokinku? idan ko marin fuska addini ne me ya sa masu rawunnan nan da manyan alkyabbu basu cire ruwannansu da alkyabbunsu su mari nasu fuskoki? Ba ku lura suna yaudarar ku ne da fatawoyin da su basu aiki da su?

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Kukan mutuwa na cikin ayyukan jahiliyyah”. Majlisi da Xabarsi – daga cikin malamanku - sun ruwaito Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yace: “Akwai muryoyi biyu da Allah yake qyama, mai yin su kuma duk inda yake Allah ya la’ance shi: hargowa idan musiba ta sabka, da waqa (music) idan farin ciki ya samu.

To, ya kenan, ya ku ‘yan Shi’ah?

Kashi Na Goma

 Auren Wuccin Gadi (Mutu’ah) Da Taqiyyah (Munafunci) da Sauran Miyagun Xabi’un ‘Yan Shi’ah Tambaya Ta Saba’in Da Xaya

‘Yan Shi’ah kun cika littafanku da yabon Mut’ah, auren wuccin gadi. Kun samar da xinbin lada ga wanda duk ya yi ta. Kuma kun ce, tana cikin sunnonin Imamanku, har da cewa, wanda ya yi Mut’ah sau xaya, ya cimma darajar Hussani, wanda ya yi sau biyu, ya cimma darajar Al-Hasan, wanda ya yi sau uku, ya cimma darajar Ali, wanda ya yi sau huxu, wai ya cimma darajar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama!. Haka Hadisin naku ya zo a cikin Tafsiru Manhajis Sadiqina na Sayyid Fathullahil kashani (2/198).

A cikin Man la Yahduruhul faqihu, xaya daga cikin Kutubul Arba’ah, littafai huxu mafi daraja a wurin ku, kun ce Baban Abdullahi Ja’afarus Sadiq – xaya daga cikin Imamanku – ya ce: “Mut’ah addinina ce, kuma addinin iyayena ce. Duk wanda ya yi ta, ya bi addininmu, wanda ya musanta ta ya musanta addininmu”. Har wayau a (3/356) na wannan littafi, an tambaye shi, wanda ya yi Mut’ah ko yana da lada? Sai ya ce: “Idan ya yi Mut’ah yana neman lada daga Allah, to, babu wata kalmar da zai faxa mata sai ta zama lada”. “…Idan ya kusanceta kuma Allah zai gafarta masa zunubansa. Idan ya gama ya yi wanka duk xigon ruwan da ya hau jikinsa an gafarta masa zunubansa”.

Kar ka yaudaru da cewar su wai, Mut’ah magani ce ga matsalar zawarawa. Khumaini, a cikin Tahrirul Wasilah yana ganin cewa, halal ne ma ayi Mut’ah da jinjira mai shan nono, wato ya rungume ta, ya sanya zakarinsa a tsakanin cinyoyinta, yana sumbantar ta, yana jin daxi da ita! Idan kuma ta kai shekara bakwai ba komai ayi komai da komai! Majlisi kuma a cikin Biharul Anwar (100/312) ya ce ba a buqatar shedu! Aure mai tsawon minti goma! Haxuwa xaya, sai biyan sadaki, sai sirrantawa, sai saduwa. Shi kenan aure ya qare. Ba shedu, ba sanarwa, ba xaurawa. Babu gado, babu saki, babu idda. Ku faxa mana banbancin wannan da abin da karuwai ke yi. Gaya min don Allah duk garin da wannan mugunyar xabi’a ta yaxu a cikin su, wa zai natsu da rayuwar ‘ya’yansa da qannensa da har matansa na aure? Tsakanin ka da allah xan Shi’ah kana jin daxin ayi wannan da xiyarka? Kana son ayi da mahaifiyarka? Ka yarda ayi shi da qanwarka?

A kuma cikin sa har wayau (3/366) wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce; “Duk wanda ya yi Mut’ah sau xaya, ya aminta daga fushin Allah. Wanda ya yi sau biyu kuwa za a tada shi cikin mutanen kirki. Wanda ya yi sau uku zai gwamatse ni a cikin Aljannah”.

Tambaya a nan (Ta 72): Me nene ma’anar hadisin da ya zo cikin Biharul Anwari (100/308) cewa, an tambayi Baban Abdullahi Ja’afarus Sadiqi a game da hukuncin auren Mut’ah, sai ya ce: “Kada ka qazantar da kanka da ita”? Haka kuma mene ne ma’anar faxar sayyidina Ali da ta zo a cikin Wasa’ilus Shi’ah (21/12) a lokacin da Ali ya ji Abdullahi xan Abbas yana fatawar halalcin Mut’ah, ya ce masa “Kai vataccen mutum ne. Domin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya haramta auren Mut’ah, ya haramta cin naman jakan gida ranar Khaibar”.[10]

Tambaya Ta 73:

A iya saninmu waxancan darajoji da falaloli na auren Mut’ah da malamanku suka faxa duk sun kuvuce ma Imamanku goma sha biyu. Kamar yadda Nana Fatima bata samu wannan falalar ba. Don haka, mu bamu iya tambayar ku cewa, sau nawa suka yi Mut’ah? kuma da wa suka yi? Sannan ‘ya’ya nawa suka bari na Mut’ar? Bamu iya waxannan tambayoyi. Amma idan kuna da wata amsa akai, to, bamu hana ku faxi ba.

Tambaya Ta Saba’in Da Huxu

‘Yan shi’ah kuna sujada akan turba, kuma kun ce, duk qasar da ke duniya ba wadda ta kai tsarkin ta. Ita ce qasar da aka kashe Husaini, kuma wai, tafi qasar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yake kwance a cikin ta, kuma wai, tafi Al-Arshin Ubangiji daraja.

Tambaya: Ko Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tava yin sujada akan ta? Idan kun ce eh, mun san qarya kuke yi. Idan kun yarda bai tava yi ba, to kun fi Annabi ne? Ruwayoyinku na Shi’ah suna cewa, Jibrilu Alaihis Salamu ya xebo qasar Karbala ya zo wa Manzon Allah da ita, ya ce, wannan ita ce qasar da za a kashe jikanka Husaini a kanta. Ruwayoyin suka qara da cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi kuka a wannan lokacin. To amma kun ce itace tafi tsarki, to me ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi sujada gare ta ba, gashi kuwa Jibrilu Alaihis Salamu ya kawo masa ita?

Tambaya Ta Saba’in Da Biyar

A cikin Wasa’ilus Shi’ah (3/598) cewa aka yi: “Wajibi ne ayi sujada da gavvai takwas; Goshi, da Hanci, da Tafuna biyu, da Guiwoyi biyu, da Tafuna hannuwa guda biyu. To, Me yasa wannan qasar baku yo guda takwas ba? Kun yi watsi ne da wannan nassin? Ko kuwa dai daman duk abin son rai ne da shirme?

Tambaya Ta Saba’in Da Shida

Me ya sa mazanku da matanku ke sa baqaqen kaya? Kada wannan Tambaya ta ba ku mamaki. Domin Abu Ja’afar Al Qummi a cikin babban littafinsa Man la Yahduruhul Faqihu xaya daga cikin littafai huxu mafi tsarki a wurin ‘yan Shi’ah (1/232) da kuma cikin Wasa’ilus Shi’ah (2/136) Ali Raliyallahu Anhu yayi wasici ga almajiransa cewa: “Kada ku sa baqaqen kaya, domin tufan fir’auna ne”.

A cikin Tafsirus Safi mai littafin ya ce, a inda yake tafsirin:

وَلَا يَعۡصِينَكَ فِي الممتحنة: ١٢

Wai, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi mubaya’a ga mata cewa “Kar su sa baqaqen kaya, kada kuma su dinga tsaga tufafinsu idan anyi mutuwa, kada suce wayyo Allah”. Ku gaya ma malamanku su canza baqaqen alkyabbu su sa farare mana! Ai daman Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba abinda yake so a cikin sutura kamar fararen kaya. To, me yasa malamanku ke son baqaqe?

Ku tuna fa wannan tafsirin na daga cikin littafanku har ma a muqaddimarsa cewa ya yi: ya kira littafinsa Safi ne, wai tatacce, domin ya tankaxe shi, ya rairaye ta yadda, ba riwaya ko xaya ta Ahlus-Sunnah a cikinsa. To, ga abin da ya ce akan baqar sutura!

Don Allah a duniya akwai matan da ke sa baqaqen kaya kamar matan ‘yan Shi’ah? Me ya sa matanku suke sa baqaqen kaya?

Tambaya Ta Saba’in Da Bakwai

Kun ce Taqiyya addininku ce kuma addinin Imamanku. Wanda ya bar ta kamar wanda ya bar sallah ne. Duba Biharul Anwar (75/421). Anan Sokoto mun ga Taqiyyar a fili. Domin kuwa mafi yawan waxanda suka zo nan Masallacin Sarkin musulmi Bello, suka yi rantsuwa akan cewa sun bar Shi’ah, ta tabbata duk qarya su ke, taqiyya ce.

Ga wani nassi da nike so ku bani amsa akan sa. Yazo a cikin Nahjus Sa’adati xaya daga cikin muhimman littafanku (2/339) cewa, Sayyidina Ali ya shigo da baqin ciki, yana sassaka, yana cewa: “Ya zaku yi da wani zamani ya da yake tafe? A lokacin za a qi aiki da hukunce-hukuncen Allah? Za a rinqa sace dukiyar jama’a, ayi qiyayya da masoyan Allah, ayi soyayya da maqiyan Allah. Sai suka tambaye shi: To, ya zamu yi idan wannan lokaci ya cim mana? Sai yace: “Ku zamo kamar yadda sahabban Annabi Isah Alaihis Salamu suka zamo. An yanka naman jikinsu da zarto. An gicciye su akan katako aka karkashe su. Sannan ya ce: “Mutuwa akan xa’ar Allah tafi rayuwa akan savonsa”

Tambaya anan: Idan har wannan magana gaskiya ce, -kuma mu, mun san gaskiyar ce- to, ina amfanin taqiyya kenan?

Kammalawa

Daga qarshe, waxannan tambayoyi saba’in da bakwai, kaxan ne daga cikin abin da zai yiwu a tambayi ‘yan Shi’ah. Kuma ina rantsuwa da Allah ban yi nufin cin mutuncin kowa da waxannan tambayoyin ba, balai cin zarafi ko izgili. Fatata dai ‘yan Shi’ah ku yi tunani ku dawo ma hanya mu tafi tare bisa ga sunnar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kamar yadda Allah ya ce wa Manzonsa:

قُلۡ يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ تَعَالَوۡاْ إِلَىٰ كَلِمَةٖ سَوَآءِۢ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ أَلَّا نَعۡبُدَ إِلَّا ٱللَّهَ وَلَا نُشۡرِكَ بِهِۦ شَيۡـَٔا وَلَا يَتَّخِذَ بَعۡضُنَا بَعۡضًا أَرۡبَابٗا مِّن دُونِ ٱللَّهِۚ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقُولُواْ ٱشۡهَدُواْ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ ٦٤ آل عمران: ٦٤

Ma’ana:

Ka ce: “Ya ku mutanen littafi! Ku taho zuwa ga kalma mai daidaitawa a tsakaninmu da ku; kada ku bauta wa kowa sai Allah. Kuma kada ku haxa kowa da shi. Kuma kada sashenmu ya riqi sashe abin bauta baicin Allah. To, idan sun juya baya sai ku ce: “Ku yi shaida cewa, lalle ne mu masu miqa wuya ne (ga Allah). Suratul Ma’ida:64

Wal Hamdu Lillah.[1]  Qabarin da suke ziyarta a garin Kashana ta qasar Iraqi ba na gaskiya ne ba. Domin kuwa Abu Lu’ulu’ata tun randa ya kashe Umar a Madina aka kashe shi. To, ya za ayi kabarinsa ya koma Iraqi? Wa ma zai san wurin kabarin irin wannan la’ananne, tun da yake ba ma musulmi ba ne balai a kai shi maqabartar musulmi? Amma su ‘yan Shi’ah suna da tatsuniyoyi irin nasu da suke hikaitowa akan abin da ya maida shi Kashana. Mu dai muna magana da masu hankula ne.

[2]  Duba alal misali; Usulul Kafi (1/227) da sharhinsa As Shafi Sharhul Kafi (5/28) Biharul Anwar (26/82) da Wada’iun Nubuwwah shafi na 114 da Aslus Shi’ati Wa Usuluha shafi na 58.

[3]  Duba: Suratul Ma’ida: 1, 94, 95, 96.

[4]  Abin haushi abin dariya, ‘yan hizbullahwi da ke Lebanon, basu bari Ahlus-Sunnah a qauyukan da su ‘yan Shi’ar ke da rinjaye su sha ruwan rijiyar burtsatse da qungiyar ta yi. Don me? Wai su ji qishirwa su tuna da qishirwar Husaini da aka kashe shi da ita. Waxannan bayin Allah su, basu da wannan tarihin. Basu ma san wai, wane Husaini ne aka kashe ba, kuma yaushe? Sai suka kira su, suka ce, don Allah ku gaya mana nawa ne diyyar Husainin nan naku da aka kashe, mu biya ku a zauna lafiya?!

[5]  Duba cikakken bayanin wannan a littafinmu na biyu a jerin “Baraden Musulunci” mai suna “Qaddara ta riga Fata” wanda maxaba’ar Ihsan ta Jos suka buga a shekarar 2006.

[6]  Wannan wasiyya akwai hikimomi a tattare da ita. Kuma tana nuna hangen nesa da (M) ya yi cewa, bayi zasu xaukaka sosai, kuma ‘ya’yansu zasu shugabanci al’ummar musulmi. To, idan ba a kula da sub a har tarbiyyar ‘ya’yansu ta vaci, al’ummar musulmi zata xanxana kuxarta.

[7]  Duba alal misali, Alaqa Tsakanin Ahlulbaiti da Sahabbai, Na Sheikh Saleh Ad Darwish, Fassarar  Muhammad Mansur Ibrahim. Da kuma Su Wane Ne Masoyan Ahlulbaiti? Na Muhammad Mansur Ibrahim, Fassarar Aliyu Rufa’I Gusau, Bugun Cibiyar Ahlulbaiti da Sahabbai, Sakkwato.

[8] Saboda qoqarin kai matuqa da sahabbai suke yi wajen ibada kamar yadda suka nace sai su sadar da azumi; su daina sahur da buxin baki, amma Annabi ya hana su. Kamar kuma yadda Annabi ya kauce ma qiyamullaili a masallaci da ya ga kuzarinsu ya yi yawa akai don, kada a wajabta ta sai tayi ma al’umma na baya gare su nauyi. Da ire- iren su.

[9] Xan Husaini ne. Da shi aka je Karbala, amma saboda ba shi da lafiya bai yi yaqi ba. Su kuma ‘yan ta’addar da suka gan shi a kwance, sai suka qyale shi don yana da rabon ganin baxi.

[10]  Wannan hadisi yana cikin Bukhari da Muslim, amma mun kawo shi da daga Wasa’ilus Shi’ah don kafa ma ‘yan Shi’ah hujjah. Kuma shi ne gaskiya cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya haramta auren Mut’ah har abada. Amma to, don me waxancan qarairayin da muka gabatar daga maganganunsu? Kuma maganar da ake ji cewa, an halatta ta sannan aka haramta, aka sake halattawa aka haramta, ba haka take ba kamar yadda Ibnu Taimiyyah ya yi sharhi a cikin Minhajus Sunnati.