Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(Kisa) 3/7#

nau, i

Yayi Magana (Kisa) ,da kuma haramcin yin kisa a addini

Download
karubuta zuwaga shugaba wannan shafi

karin bayani

  Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa:

  (3- Kisa)

  [Hausa هوسا-]

  Malan Aliyu Muhammad Sadisu

  2014 - 1435

  السبع الموبقات:

  ( 3- قتل النفس الذي حرم الله )

  [Hausa هوسا-]

  الشيخ : علي محمد السادس

  2014 - 1435

  Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(Kisa)

  Kisa: A yanzu za mu yi bayani akan abu na uku cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakarwa, wannan abu kuwa shine Kisa. Allah madaukakin Sarki ya haramta kisa haka kawai ba tare da dalili na shara'a ba, kuma Ya sanya nau'ukan narkon azaba ga dukkan wannada ya aikata kisa. Karkasuwar Kisankai: Kashi na Farko: Mutum Ya Kashe Kanshi Da Kanshi. Allah Madaukakin sarki Yana cewa a cikin littansa Alkur'ani 'Kada ku kashe kawunanku, lalle Allah Ya kasance mai rahama ne a gareku. To duk wanda ya aikata haka (ya kashe kanshi) dan kiyayya da zalinci to da sannu zamu konashi da wuta, hakanko ya kasance a wurin Allah abune mai sauki" Suratun Nisa'I aya ta 29-30. Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- 'Duk wanda ya kashe kanshi da wani abu to da wannan abun za'a azabtar da shi' hakan nan da ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yake cewa 'Duk wanda ya kasha kanshi da guba to zai zo ranar kiya yana ta hambadar wannan gubar ackin wuta, hakanan duk wannda ya kasha kanshi da wuka zai zo ranar kiya da wuka a hannunsa yana ta caka wa jikinshi a cikin wuta'. Ibnu Kasir ya kawo wadannan hadisai alokacin da yake fassara wadancan ayoyin na da suka gabata. Tabbas wannan yana nuna mana cewa kwata-kwata bai halattaba don mutum ya samu kanshi cikin bakin ciki da damuwa da tashin hankali ya ce zai rataye kanshi kodai a fankar dakinshi ko ya tafi daji ya rataye kanshi a wata bishiya, ko ya fada cikin kogi, ko yah au katuwar kada ya diro, mace ko namiji, Allah Ya tsaremu baki daya amin. Shin Ya Hallata Ayi Masa Sallah? Ya hallata ayi mishi sallah domin bai kafitraba, saidai malamai da masu fada aji basu halarci sallar da binne shi ba, don kada yaba sauran mutane dammar aikata irin wannan danyan aiki, amma bai hana su koka mishi gafarar Allah a inda suke tsakaninsu da Allah. Kashi Na Biyu: Kisan Ganganci: Kisan gangaci shine 'Mutum ya yi nufin kasha wani sannan ya dauki abin da yake kisa ya kashe shi'. Allah madaukakin Sarki Yana cewa " Kuma duk wanda ya kashe mumini da gangan to sakamakonsa Jahannama kuma zai dawwama acikinta kuma Allah Ya yi fushi da shi, kuma Ya tsine masa, kuma Ya yi mishi tattalin azaba maigirma.'' Suratun Nisa'I, aya ta:93. (Allah ya tsaremu, amin) Hukuncin Kisan Ganganci: irin wanna kisan na ganganci Allah madaukakin sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai tsarki inda Allah Ya ke cewa a Suratul-Bakar 'Ya wadanda suka yi imani, an wajabta muku ramuwa dan gane da wadanda aka kashe' Bakara, ayata:178. haka kuma Allah Ya ce 'Kuma mun wajabtamusu acikinta (Attaura) Lalle ana kashe rai idan ran nan ta kashe' (wata rai) Suratul Ma'idah, aya ta:45. Ma'anar Kisasi (wato ramuwa) shine yadda wanda aka kashe ya dandani tacin mutuwa to shima wanda ya yi kisan ya dandana, irin wannan hukuncin shi zai tabbatar da zaman lafiya domin duk mutumin da yasan indai ya kashe to tabbas za'a kashe shi ko shi waye to lalle zai shiga taitayinsa, wanda hakan zai sanya rayuwa ta aminci tsakanin al'umma. Amma farfagandar da ake da sunan kare hakkin dan'adam na cewa shara'ar musulunci ta tsaurara domin bata kula da hakkin dan'adam ba, irin wannan maganar tana nuna jahiltar menene hakkin dan'adam ?! domin ai shima wanda aka kashe dan'amne kuma yana da hakki, yanzu dan ankwatar masa hakkinsa sai ace donme? Yafiya: Idan 'yan'uwan wanda aka kashe suka ce sun yafe, to shikenan ba za'a kashe wanda ya yi kisanba sai ya bada diyya ga su 'yan'uwan wanda aka kashedin, sannan kuma ya yi azumi sittin ajere. Kashi Na Uku: Kisan Kuskure: Kisan kuskure shine 'Kisan da aka yi ba tare da anyi nufiba' kamar maharbi ya hangi barewa bayan ya kamala shiri ya sakar mata kibiya kawai sai kibiyar nan ta wuce ta sami wani can daban yana noma ko ya zo wucewa. Hukuncin Kisan Kuskure: Hukuncin kisan kuskure shine 'Za'a bayar da diyya ga dangin wanda aka kashe, sannan za'a 'yanta baiwa/bawa mummunai, idan ba'a samu ba sai ayi azumin kwanaki sittin ajere, Allah Ya karemu, amin. Tambihi/Fadakarwa: Yana da kyau musan wadanda suke da hakki akan wanda aka kasha: Na farko: Allah Madaukakin Sarki, domin shi ne wanda ya halicce shi sannan wani ya zo ya kashe mishi bawansa ba tare da izinin shiba, hakkin Allah madaukakin sarki shi ne ' wanda yayi kisan ya 'yanta baiwa/bawa' idan ba'a samu ba sai ya yi azumin kwanaki sittin a jere ba tare ta ya shaba, domin Allah Yana cewa:'' …Kuma da 'yanta baiwa (ko bawa) mumina, to duk wanda bai samuba to sai ya yi azumin watanni biyu masubibitar juna don neman tuba a wurin Allah.' Suratun Nisa'I, aya ta: 92. Na biyu: 'yan-uwan wanda aka kasha: Suma 'yan-uwan wanda aka kashe suna da hakki domin an kasha musu dan-uwansu kuma Allah ya basu dammar su tashi su nemi hakkin su, Allah yana cewa a cikin Suratul-Isra'I, a 33 ayata : Kuma duk wanda aka kashe shi a halin an zalince shi to munsanyawa danginsa karfi (na su nemin hakkinsu) to amma kada ayi barna wurin kisa' (ta yadda za'a wanda bai da lefi). Saboda haka duk wanda ya yi kisa da ganganci za su taru shi danginsa su bayar da diyyah ga 'yan-uwan wanda aka kashe, domin Allah Yana cewa ''Bai kasance ga wani muminiba ace ya kashe mumini saidai da kuskure, to duk wanda ya kashe mumin da kuskure to zai 'yanta bai mumina (Hakkin Allah) da kuma diyyah da za'a mikata ga dangin wanda aka kashe sai dai in sun yafe" Suratun Nisa'I, aya ta: 92. Na Uku: Wanda Aka Kashe: Shi kuma wanda aka kashe aranar kiyama zai ruko wuyan wanda ya kashe shi ya zo da shi gaban Allah yace '' Ya Allah tambayeshi akanme ya kashe ni?''. Tambaya: A yanzu idan aka tambayeka akace 'Shin irin mahaukacin lodin da direbobi suke yi a mota, kamar ace mota zata dauki buhu hamsin na kaya sai aloda mata buhu sittin sannan mutane su hau da anje kan kwana ko wani tudu ko gangara sai motar ta balle ayi asarar rayuka wane irin kisane? Kuma way a yi kisan? Allah Ya tsaremu amin. Idan ba'asan wanda ya yi kisaba: Amusulunci idan ba'asan wanda ya yi kisaba to gwamnatice zata bayar da diyya ga 'yan-uwan wanda aka kasha, domin itace wajibin tsare rayukan al'umma ya rataya a wuyanta. Kammalawa: Awannan dantakaitaccan rubutun ya bayyana agaremu yadda musulunci ya baiwa ran bil'adama kulawa, da kuma yadda Ma'aikin Allah ya sanya kisan kai cikin abubuwan da suke halaka wanda ya aikata su. Sannan ya bayyana agaremu cewa koda mutum ya yi kisa anan duniya anbashi kariya ta kowanne irin al'amari to ya sani wannan kariyar bazata anfaneshiba a gaban Allah Madaukakin Sarki. Kenan yanzu dole mutum ya kula da duk irin aikin da za'a sashi da kuma irin alkawarin da za'a yi masa, domin koda ya tsira anan duniya to ya sani fa a kwai lahira, Allah madaukakin sarki yak are rayukan al'ummar musulmi bakidaya, ya tsaremu ya tsare mana imanimmu, amin

  Rbutawa :

  Malan Aliyu Muhammad Sadisu

  kafofi:

  Nau'uka na ilmi: