INA ALLAH YA KE?

nau, i

INA ALLAH YA KE?
(Nazari Akan Daukakar Allah Bisa Al’arshi A Ra’ayin Magabata Da Na Bayansu)

Download
karubuta zuwaga shugaba wannan shafi

karin bayani

 INA ALLAH YA KE?

(Nazari Akan Daukakar Allah Bisa Al’arshi A Ra’ayin Magabata Da Na Bayansu)

Na

Baban Ramla

Muhammad Mansur Ibhamin

Fassarar

Baban maryam

Aminu Ibrahim Al marawi

Bugawa da Yaxawa:

Mu’assatu Ahlilbaiti Wassahabah, Nigeria

(C) 2005

 DAGA TSOKACIN MALAMAI

A Cikin kitabul Arshi Imamuz-zahabi ya ce:

“Hadisin kuyanga ya qumshi abubuwa guda biyu:

Na Daya: Babu laifi Musulmi ya tambaya, Ina Allah yake?.

Na Biyu: Amsar tambayar ita ce; ya na sama.

To mai musun xayan biyun nan (tambayar ko amsar) yana jayyaya ne da al Musxafa (SAW)”.

Shi kuwa alkali Abdul-wahhab, Bamalike a sharhin da ya yi wa Muqaddimar Risala ta Xan Abu Zaidi alqairawani ga abin da ya ce:

“Sifaita Allah maxaukakin sarki da sifar xaukaka a Al’arshi shi ne tsintsar biyar nassi, da miqa wuya ga Shari’ah da gaskata Allah ga abin da ya sifaita kansa da shi.”

A tashi gudummawa, Imamu Abdul-qadir Al-jilani, cikin littafinsa ‘Algunyatu’ cewa ya yi:

“ya cancanta a sifaita Allah da cewa ya xaukaka a Al’arshi ba tare da wata kwana-kwana ba. Tabbas Allah ya xaukaka a Al’arshi”.

Mujaddadi Sheikh Usman xan Fodio yace:

“Babu wani abin suka ga cewa, Allah ya na sama. Don ayoyi da hadisai masu tarin yawa su ne suka fayyace hakan”. (Al-jami’u li fatawi Ash-sheikh Usman).

Sheikhul Islami Xanu Taimiyya shi kuma cewa yayyi:

“wanda duk ya ce Allah ya na ko ina da zatinsa, ya kauce ma tafarkin Littafin Allah da Sunnar manzonsa da abin da malaman farko suka yarda da shi, kuma ya sava ma xabi’ar da Allah ya halicci mutane a kanta” (Majmu’ul fatawa).

Sai kuma Sarkin Musulmi Muhammadu bello wanda a cikin huxubarsa ta jumu’a ya ke cewa:

“kuma na shaida da cewa babu abin bauta da cancanta sai Allah shi kaxai ba ya da abokin tarayya, masani ga abubuwan da ke tattare da na rarrabe, wanda ya xaukaka a Al’arshi, xaukaka wadda ta dace da shi ba tare da misaltawa ba’.

Shi ma Sheik Abubakar Mahmud Gummi ya bada tasa gudummawar a inda ya ce:

“Allah ya xaukaka akan Al’arshi, xaukaka wadda ta dace da shi….”. (Alqur’ani mai girma tare da tarjamar ma’anoninsa zuwa harshen hausa).

 GABATARWA

Da sunan Allah, mai rahama mai jinqai.

Godiya ta tabbatar ma Allah wanda ya xaukaka akan Al’arshinsa can a tsololuwar sama. Kuma ya sanya yaqini cikin zukatan bayi masu tsoronsa, sai kuma ya jarrabi waxansu da samun rabo, wasu kuma da tavewa.

Na shaida cewa babu abin bauta da can-canta sai Allah shi kaxai bai da abokin tarayya, shaidar wanda ya gaskata tashin alqiyama da tsayuwa gaban Allah.

Kuma na shaida cewa Annabi Muhammadu bawansa ne, manzonsa ne, wanda shi ne mai ba da shaida ga wannan al’umma wadda za ta bada shaidun wasu gaban Allah, shi aka aiko da bayanai na shiriya na yanke hanzari da jayayya. Tsira da aminci su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa dukkansu har zuwa ranar tsayuwa[1].

Bayan haka, Allah mabuwayi ya kammala addininmu, ya cika ni’imarsa a garemu, ya kuma zavi musulunci ya zame mana hanyar rayuwa.

Cikar wannan addinin da kammalarsa alama ce babba mai nuna cewa, manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai bar duniya ba sai bayan da ya gama fayyace ma wannan Al’umma dukkan abin da ta ke da buqata da shi game da lamarin addini, ya warware ma ta zare da abawa ta hanyar bayanai gamsassu waxanda su ke filla filla ta yadda bai bar wani marufi da wani zai zo ya buxe ba.

Daga cikin mafiya girman abubuwan da Manzon Allah ya fayyace akwai, faxakar da al-umma game da sanin sunayen Allah da siffofinsa, saboda wannan shine rukuni na farko wanda saninsa ya zamo tilas, kuma ba zai yiwu a yi sakaci da shi ba. Anan ina son mai karatu ya biyo ni a hankali domin mu tantance wasu qa’idodi na wannan mas’ala kafin shiga cikin zurfin bayani:-

Qa’ida ta farko.

 Littafin Allah da Sunnar manzonsa Almustafa (SAW), sune tushe da mavuvvugar Aqidar Musulunci ba qiyasce-qiyascen son zuciyar mutane ba, domin babu wanda yafi Allah sanin zatinsa kamar yadda babu wanda ya zarce Manzon Allah daga cikIn halittu a wajen ubangijinsa.

 Haka kuma babu wani taliki wanda ya fi kyawon nasiha da hikimar bayani kamar Annabi (SAW). To a duk lokacin da ya tabbata cewa, Alqur’ani mai girma ya sifaita Allah mabuwayi da wata sifa ko kuma Sunnar Annabinsa Almustafa Amintacce ta tabbatar da wannan sifar, ya zama wajibi ne ga musulmi ya miqa wuya kawai. Wannan itace tsarkakewa mafi dacewa ga zatin Allah mabuwayi. Allah maxaukakin sarki yace:

 “ Kuma ba ya kamata ga mumini namiji ko mace idan Allah ya hukunta wani al’amari da manzonsa ya kasance suna da zavi a cikin lamarinsu. Kuma wanda ya sava wa Allah da Manzonsa, to ya vace, vacewa bayyananna” Al-hazab : 36

Qa’ida ta biyu

 Sanin cewa sababban manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi da iyalansa, ba su jahilci ma’anonin sifofin Allah ba kamar yadda ba su yi gardama ba wajen sifaita shi da su, saboda ma gamsuwarsu da abinda Allah ya sifaita kansa da shi ba su ma tambayi manzon Allah (SAW) komai ba dangane da wannan. Alhali kuwa sun sha tambayarsa gameda hukunce-hukunce kamar yadda alQur’ani ya kawo tambayoyin da suka yi masa akan Ganima, Marayu, Jinjirin wata, giya da caca, haila da makamantansu. A nan ba zai yiwu mu fahimci cewa, sanin hukuncin haila yafi sanin sifofin Allah matsayi a wajen Sahabbai (RA) ba, domin kuwa ai da sanin sifofin Allah ne sonsa da girmama shi ke kammaluwa[2]. Don haka da akwai damar karkata ma’anar waxannan nassosi da suka zo qarara “ta hanyar yin tawili” da babu abinda zai hana su himmantuwa zuwa ga tambayar yadda za’a tawilanta su fiye da yadda suka himmantu wajen tambayar wasu rassa na Shari’a. kuma baya halatta garemu mu saki hanyarsu mubi turbar malaman falsafa wanxada kamar yadda Shehu Ahmadu xan Abdulsalami ya bayyana su; “An ba su hazaqa ba’a basu tsarkin zuciya ba, an kuma basu fahimta amma babu zurfin ilmi. Kuma aka sanya masu wani irin ji da gani da zukata. Sai dai kash! jinsu da ganinsu da zukatansu duk ba su amfane su ba ga komai, domin sun kasance suna musunta Ayoyin Allah, kuma abin da suka kasance suna aikatawa na izgili game da shi ya wajaba a garesu:[3]

Qa’ida ta uku:

 Sanin cewa, tabbatarwa da Allah (SWT) sifofinsa na zati ko wasu sifofi na ayukkansa ba jingina nakkasa ko gajiyawa da rashin kamala ne ga Allah Maxaukakin Sarki ba, ai daman sifofin Allah dukkansu sifofi ne na kamala gare shi kuma babu inda suka yi kama da sifofin halittu.

 A nan sai dai mu gane cewa, Allah mahalicci ya na da sifofin da suka dace da girmansa da kamalarsa. Mu kuma halittu muna da sifofi irin waxanda suka dace da irin kasawarmu da gajiyawarmu da buqatarmu. Kamar yadda Allah yace: “Wani abu bai zama kamar tamkarsa ba, kuma shi ne mai ji, mai gani”. Suratush Shurah

Kuma Allah (SWT) ya ce: “lalle ne mu, mun halitta mutum daga xigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi saboda haka muka sanya shi mai ji mai gani”. Suratul Insan Ayah ta (3)

 A nan Allah maxaukakin sarki ya sifaita kansa da sifofin Ji da gani irin yadda ya dace da girmansa da xaukakarsa da cikar sarautarsa, amma shi jin mutun da ganinsa ya taqaita ne ga irin kimarsa da yanayin halittarsa da gajiyarwarsa. Don haka wannan ba zai sa mu kore ma Allah sifofinsa ba, mu ce ai su ma halittu su na da waxannan sifofi kuma ba za mu sifaita Allah ba da sifofin halitta.

Qa’ida ta hudu:

 Dalilin da ya sanya mutane ke savani game da sha’anin tauhidi shi ne don sun nisanci nazari da karatun alqur’ani mai girma da hadissan Annabi (SAW) da kuma rashin lura da zantukan malaman da suka gabata game da mas’alar tauhidi. A madadin haka sai suka rungumi littafan falsafa a matsayin littafan da suke dogaro da su a wajen sanin Allah mai girma a sakamakon haka sai suka yi nisa daga shiriyar Alqur’ani mai girma da Sunnar Annabi (SAW) da kuma bayanan magabata. Bari in baka misali daga xaya daga cikin malaman tafsiri da suka gabata kamar Imamul Nasa’i da Abu Hatim da Albagawi ko waxanda suka zo bayansu irinsu Hafiz Axxabari da Xanu Kasir dukkansu sun sallama wa Allah da manzonsa game da sifofin Allah ba tare da wani tawili ba.

Duba ma a cikin littafan Hadisi, misali ka duba Kitabul Tauhid da ke cikin Sahihul Buhari ba ka tava ganin ko da birbishin tawili game da sifofin Allah maxaukakin sarki, a maimakon haka zaka rinqa ganin hanya sambai wajen tabbatar ma da Allah siffofinsa kammalallu. Duba inda ya ke cewa:

Babin (Al’arshinsa ya kasance ne akan ruwa) (kuma shi ne ubangijin Al’arshi mai girma) game da ma’anar kalmar istawa Abul Aliya ya ce: ya xaukaka zuwa sama, ya xaukaka kenan (sai ya xaukaka su): ya halicce su (sammai). Mujahid ya fassara ma’anar istawa da cewa xaukakuwa ne akan Al’arshi[4].

A wani wajen kuma Imamul Buhari cewa ya yi:

“Babi game da faxar Allah maxaukakin sarki (mala’iku da ruhi (Jibril A.S.) suna takawa zuwa gare shi) Suratul Ma’ariji. Da faxar Allah mabuwayi (zuwa gare shi magana mai daxi ta ke hawa, kuma aiki na kwarai yana xaukarta) Suratul fajir 10. Malam Abu Hamza yace: an karvo daga xan Abbas (RA) cewa, lokacin da Abu Zarri (RA) ya samu labarin bayyanar Manzon Allah (SAW) sai ya ce ma xan uwansa “je ka binciko mini labarin wannan mutun mai raya cewa saqo na zo masa daga sama”, kuma Mallam Mujahid yace: (wal amalus salih) aiki na qwarai yana daga magana mai daxi. Ana cewa (zil-ma-ariji) mai matakala da nufin cewa mala’iku suna takawa zuwa ga Allah[5].

Kamar yadda yake a cikin wannan sahihin littafi na Buhari da ire-irensa, hadisai da yawa da bayanan magabata akan wannan mas’alar sun isa su gamsar da duk masu neman sani, da kuma a ce sun yi riqo da su da ba a juyar da su ba zuwa ga xemuwa ta hanyar kauce ma sifaita Allah da abinda ya sifaita kansa da shi zaton wai in sun yi haka sun jingina ma Allah nakkasa, saboda haka sai su tabbatar ma sa da kamala daga cikin qwaqwalensu ba daga Littafinsa ba.

Qa’ida ta biyar

 Sanin cewa musulmi ba su yi savani game da zatin ubangiji da sifofinsa masu tsarki ba waxanda ke cikin alqurani da Sunnah, sai bayan shigowar litaffan girkawa na falsafa a garuruwan musulmi. Saboda haka ba a tava samun cewa magabatan wannan al’umma sun yi furuci da kalmomi irin waxanda qungiyoyin falsafa suke yawo da su ba waxanda ba su da tushe daga littafin Allah da Sunnar manzonsa[6], musamman irin maganar “jiha” da “bagire” da “tawili” da ire-irensu. Daga cikin waxanda suka yi fice wajen karkata da kauce ma tafarki madaidaici da qoqarin cin gyaran alqur’ani da Sunnah da ijima’in malamai sune, mu’utazilawa waxanda, baya ga karkatar da ma’anar ayoyi da su ke yi basu tsaya nan ba sai da su ka rikirkita duk hadisan da su ka sava ma tsare tsarensu na son rai ta yadda duk yadda Hadisi ya taka martabar inganci za su yi watsi da shi, su qaryata shi, ko su illanta shi, ko su bashi wata gurvatacciyar ma’ana wai da sunan “tawili”. Sha’aninsu ya tsallake nan ma, ya kai ga qoqarin sukar wanda ya ruwaito Hadisin ko da kuwa sahabi balantana tabi’i ko na bayansa.

Kuma suna yin haka ne kamar yadda muka faxi tun farko don su samu damar tabbatar da miyagun aqidunsu tare da cewa, suna amfani da wasu hadisai marasa tushe da kuma masu rauni a inda suke son qarfafa wani ra’ayi nasu, sai su riqa ji-ji-ji don su qarfafa mazahabarsu ta mu’utazilanci[7].

Irin wannan salon yaqi da Sunnah da mu’utazilawa suka bi sun share hanya ne ga sashen musulmi waxanda ke fankama da biyar ilmin falsafa a matsayin wani nau’in gane Allah maxaukakin sarki da kuma addininsa. Wannan kuwa shi ya ja su zuwa ga karkatar da akalar nassoshin Alqur’ani mai tsarki, suka yi watsi da hadisan manzon Allah (SAW) masu ximbin yawa.

Kuma ta wannan qofar ce jahamiyyawa suka kunna kai suka rinqa bayyana da zantukan da ba za su xauku ba. Wannan ne ya sa Imamu Abdullahi xan mubarak (RA) ya ce, “Mu kan faxi maganganun yahudu da nasara, amma maganganun jahamiyya ba su faxuwa”[8].

Abinda na ke so mai karatu ya fahimta a nan shi ne, wannan bincike an aiwatar da shi ba da nufin keta mutuncin kowa ba. An yi shi ne kawai da nufin ba da kariya ga Aqidar musulunci da musulmin wannan al’umma na farko da bayyanar da kishi zuwa ga Allah da Sunnar Annabi (SAW).

Kuma ina sane da cewa, akwai daga cikin malamai wanda ba da daxewar nan ba ya yi rubutu akan wannan mas’ala, sai dai abinda ya rubuta ya ci karo da ingantacciyar Aqida, kuma ya yi wa zantukan magabata wasu irin fassarori ba dai dai da yadda su ke nufi ba. Amma kuma Allah ba zai fasa biyansa ladar kyakkyawar niyyarsa ba. Kuma muna roqon Allah ya shiryar da mu da shi akan hanya madaidaiciya. A nan ina gayyatarsa zuwa karatun wannan bincike da sharaxin shimfida adalci wajen karatun don tantance gaskiya.

Fatata ita ce, da ni da wannan malami da sauran musulmi duka Allah ya saka mu cikin jerin (..waxanda ke sauraren magana, sa’annan su bi mafi kyawonta. Wadancan su ne Allah ya shiryar da su kuma wadancan su ne masu hankali). Suratuz Zumar 18.

A qarshe ina roqon Allah mai girma da xaukaka da ya tsarkake mani wannan aiki kuma ya karve shi, domin shi mai ji ne, kuma mai amsa addu’a.

Allah ka karvi aikina

kada ka tave gurina

Gyara dukkan lamurrana

Kan ka izo min ajali[9].

Allah yayi daxin tsira da aminci da albarka ga annabinsa muhammadu da mutanen gidansa da dukkan sahabbansa.

An kammala wannan Muqaddima a Sakkwato

Ranar 14 ga Safar 1425B.H[10]

 ABINDA YA WAJABA A TSAYU A KANSA GAME DA

SIFOFIN ALLAH

Abin da yake wajibi a kan kowane musulmi game da sifofin Allah maxaukakin sarki shi ne miqa wuya da yankewa kai tsaye cewa, Allah mai girma da buwaya abin sifantawa ne da dukkan sifofin kammaluwa, kuma abin tsarkakewa ne daga dukkan sifofin tawaya, kuma shi kaxaitacce ne a sifofinsa daga dukkan halittu.

Wannan ba zai samu ba sai ta hanyar tabbatar ma sa abinda ya tabbatar wa kansa ko kuma manzonsa (SAW) ya tabbatar masa game da sifofinsa ba tare da canza lafazinsa ko ma’anarsa ba, kamar yadda ba zai kyautu ba a vata ma’anar sifofin haka kuma ba mu iya kore ma Allah mai tsarki dukkansu ko wani sashe daga cikinsu.

Kuma za a barsu a yadda suke, ba za a kamanta su da wani abu ba, sai dai a tabbatar musu da kamannin da Allah ya ayyana su da shi, sannan ba a kamanta su da sifofin abubuwan halitta.

Yana da kyau a sani cewa shi fa mutun musulmi game da sifofin Allah ya na kafuwa ne a kan tushe guda uku kamar haka:

Tushe na farko:

Tsarkake Allah maxaukakin sarki daga kowace irin nakkasa da kuma nisanta sifofinsa daga kamanceceniya da sifofin halittu. Dalilin wannan tushe shi ne cewar Allah maxaukakin sarki:

﴿ لَيسَ كَمِثلِهِ شَيء وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلبَصِيرُ١١﴾ [الشورى:11].

“Wani abu bai zama kamar tamkarsa ba”. Suratus Shura:11.

﴿فَلَا تَضرِبُواْ لِلَّهِ ٱلأَمثَالَ ﴾ [النحل : 74].

“Kuma kada ku bayar da waxansu misalai ga Allah”. Suratun Nahl:74.

﴿وَلَم يَكُن لَّهُ كُفُوًا أَحَدُ٤﴾ [الإخلاص : 4].

“Kuma ba ya da wanda ya kasance tamka a gare shi”. Suratul Ikhlas:4.

Tushe na biyu:

Yin imani da dukkan sifofin da suka tabbata ga Allah maxaukakin sarki a cikin Alqur’ani da Sunnah ba tare da yin tsallake ba ko yin watsi da sashe abar sashe, kuma ba tare da yiwa Allah qari da ragi ba, ko kautar da ma’anoninsu.

﴿ ءَأَنتُم أَعلَمُ أَمِ ٱللَّهُ ﴾ [البقرة : 140]

“shin ku ne mafiya sani ko Allah?” Albakara:140.

﴿ أَم تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعلَمُونَ٨٠﴾ [البقرة : 80] ؟!.

 “ko kuma kuna faxin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah” Suratul Baqara:80.

Tushe na uku:

Yanke tsammani daga riskuwar ko kewaye haqiqanin sifofin. Abin da ke nuna wannan shine zancen Allah maxaukakin sarki:

﴿يَعلَمُ مَا بَينَ أَيدِيهِم وَمَا خَلفَهُم وَلَا يُحِيطُونَ بِهِ عِلما١١٠﴾ [طه :110].

“Ya na sanin abin da ke a gaba gare su da abin da ke bayansu, kuma ba su kewayewa da shi ga sani”. Suratu Xa Ha:11.

Da wani zai yi tambaya game da kamar wata sifa daga sifofin Allah mai tsarki da xaukaka yace: yaya Allah ya ke ji? Ko yaya ya ke gani? Ko yaya ya xaukaka? ko yaya ya ke sauka zuwa saman duniya a qarshen dare? Ko yaya ya ke dariya ko fushi? Ko yace ya hannun Allah ya ke? Da dai sauran ire-iren waxannan tambayoyi, sai mu kuma mu ce ma shi kai gaya muna ya ya Allah yake? Idan ya ce, ban sani ba. Sai mu ce masa ya ya wanda ya kasa sanin kamannin zatin Allah zai san yadda sifofin zatinsa suke[11].

A cikin tafsirins dai dai inda Allah maxaukakin sarki yace,

﴿ ثُمَّ ٱستَوَى عَلَى ٱلعَرشِ ﴾الأعراف:54].

 “sa’an nan kuma ya xaukaka akan Al’arshi” A’araf:54

Mallam Muhammad Al-Amin As-shinqidi, cewa yayi:

A wannan aya mai daraja da ire-irenta waxanda ke magana game da sifofin Allah, kamar inda ya ke cewa:

﴿ يَدُ ٱللَّهِ فَوقَ أَيدِيهِم ﴾ [الفتح : 10]

“Hannun Allah na bisa hannayesu”. Suratul Fathi:10

“Mutane da yawa sun ruxe ba su famince su ba, ruxuwar da ta janyo vacewarsu da kuma rabuwarsu zuwa gida biyu: Waxansu su ka yi watsi da sifofin, waxansu kuma su ka kamanta su da na sifofin bayi. Allah mai girma ya xaukaka daga abin da suke kwatanta shi. Ga shi kuwa Allah maxaukaki bai bar muna komai dunqule ba face ya warware muna shi. Hasali ma sai da Allah mabuwayi ya fayyace muna cewa hanyar gane gaskiya game da ayoyin da suke siffanta shi hanyoyi biyu ne kawai kamar haka:

Hanya ta Farko:

 Tsarkake Allah mai girma da buwaya daga kamanta shi da sifofin halittu.

Hanya ta Biyu:

 Yin imani da dukkan abinda Allah ya siffanta kansa da shi ko siffar da Manzonsa (SAW) ya sifaita shi da shi, don babu wanda ya fi Allah sanin zatinsa, kamar yadda babu mai iya sifaita shi fiye da yadda ya sifaita kansa.

﴿ ءَأَنتُم أَعلَمُ أَمِ ٱللَّهُ [البقرة : 140]

“shin ku ne mafi sani ko Allah?” Albakara:140.

Kuma bayan shi Allah babu mafi sanin zatinsa da sifofinsa fiye da Manzonsa tsira da aminci su tabbata a gare shi wanda akansa ne Allah yace:

﴿وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلهَوَى٣ إِن هُوَ إِلَّا وَحي يُوحَى٤﴾النجم].

“Kuma ba ya furuci da son zuciya. (Maganarsa) ba ta zamo ba face wahayi ne da ake aikowa”. An-Najm 4

 Don haka duk wanda ya kore ma Allah wata sifa da ya tabbatar wa kansa da ita a cikin littafinsa mai daraja ko wadda Manzonsa mai tsira da aminci ya tabbatar ma sa da faxar cewar wai ya yi haka ne don ya kakkave ma Allah abinda bai dace da shi ba, to ya na fassara cewa shi ya fi Allah da Manzonsa sanin abinda ya dace da Allah da wanda bai dace ba, wannan kuwa wata sabuwar hauka ce da qiran qarya, tsarki ya tabbatar ma Allah!

 Kuma duk wanda ya qudurta cewa tabbatarwa Allah sifofinsa, kamanta shi ne da sifofin halittu to shi ne farkon wanda ya kamanta Allah da wata halitta kuma shi mavarnaci ne, rikitacce, vattace.

 Amma wanda ya tabbatar wa Allah abinda ya jingina ma kansa ko Manzonsa tsira da aminci su tabbata a gare shi da sharaxin ya tsarkake Allah mai girma, bai kamanta shi da kowa ba, haqiqa, shi ne mumini, lafiyayye, wanda ya ba Allah sifofinsa na girma da kamala da tsarkakewa, kuma ya kuvutar da kansa daga halaka. Ayar da Allah ya bayyana haka qarara ita ce inda ya ke cewa:

﴿ لَيسَ كَمِثلِهِ شَيء وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلبَصِيرُ١١﴾ [الشورى : 11]

“wani abu bai zama kamar tamkar sa ba, kuma shi ne mai ji, mai gani.” Suratush-Shura: 11

 Anan Allah mabuwayi ne da kansa ya kore ma zatinsa siffar ko wane irin abu inda yace “wani abu bai zama kamar tamkarsa ba”. Kuma a cikin ayar sai ya tabbatar ma kansa sifar kammaluwa da girmamawa yana mai cewa “kuma shi ne mai ji, mai gani”. To a cikin jerin wannan ayar bayan ya kore ma kansa kama da wani abu ai siffanta kan shi ya yi da siffofin girma da cika[12] (Su ne ji da gani ba irin na halittu ba).

 XAUKAKAR ALLAH AKAN HALITTUNSA

 Allah maxaukakin sarki yace:

﴿ وَهُوَ ٱلعَلِيُّ ٱلعَظِيمُ٢٥٥﴾البقرة : 255]

“Kuma shi ne maxaukaki, mai girma.”

Suratul-baqara:255

 Kuma ya ce:

﴿سَبِّحِ ٱسمَ رَبِّكَ ٱلأَعلَى١﴾[الأعلى : 1]

 “Ka tsarkake sunan ubangijinka mafi xaukaka.”

Suratul-A’ala:10

Muslim da waninsa sun ruwaito Hadisi daga khuzaifa (RA) cewa, Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi da mutanen gidansa ya kasance yana karanta:

"سبحان ربي الأعلى"

“tsarki ya tabbata ga ubangijina mafi xaukaka.”

a cikin sujudarsa,[13]

 Kenan Allah shi ne maxaukaki ta ko wace fuska. Shi maxaukaki ne a zatinsa, maxaukaki ne a matsayinsa da cancantarsa, maxaukaki ne a rinjayensa da qarfinsa akan bayinsa. Idan ka ce guda xaya ake nufi ban da sauran, to, ka ba mu dalili.

Sheikh Hafizu Xanu Ahmad al-Hakami wanda ya rasu shekara 1377 B.H. Allah ya yarda da shi ya ce:

“Sunayen Allah “Al-Aliyyu” (Maxaukaki) da kuma “Al-A’la” (Mafi xaukaka) sun bayyana cikar xaukakar Allah ta ko wace fuska tun daga xaukakarsa a kan al-arshinsa; birbishin dukkan halittunsa, xaukaka mabayyaniya, a dai dai lokacin da kuma shi ne mai tsaronsu ya na sane da duk abin da su ke aiwatarwa, ilminsa ya zagaye komai, babu abin da ake iya voye masa komi qaramcinsa, kama ya zuwa xaukakar Allah ta fagen qarfi da rinjaya, domin kuwa tabbas babu mai iya rinjayar Allah ko ya yi jayayya da fito-na-fito da shi, kuma ba a yi masa kishiya kuma ba mai hana faruwar abin da ya zartas. Kai dukkan kowa da komi qanqantacce ne ga girmansa, yofintacce, mai duqawa zuwa ga girmansa, a qarqashin ikonsa. Har zuwa ga xaukakar sha’anin Allah don kuwa dukkan sifofin cika da kamala tabbatattu ne a wajensa kamar yadda dukkan sifofin tawaya korarru ne ba su jinginuwa ga zatin Allah mai girma da xaukaka.

 To dukkan waxannan ma’anoni da fuskokin xaukaka suna tafiya ne liqe da junansu xaya ba zai rabu da xaya ba[14].

 INA ALLAH YA KE?

Allah maxaukakin sarki yace:

﴿وَهُوَ ٱلقَاهِرُ فَوقَ عِبَادِهِ ﴾ [الأنعام : 61]

“kuma shi ne mai rinjaya bisa ga bayinsa” Suratul-An’am: 61.

Ita kuma game da sifar mala’iku, yace:

﴿يَخَافُونَ رَبَّهُم مِّن فَوقِهِم ﴾ [النحل : 50]

 “Suna tsorun ubangijinsu daga bisansu”. Suratun-Nahli: 50.

Don haka, lalle zatin Allah mai girma da buwaya ya na saman bayinsa, kuma duk wanda ya musanta hakan muna binsa bashin dalili:

﴿ قُلْ هَاتُوا بُرْهَانَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ ﴾.

 “kace ku kawo dalilinku idan kun kasance masu gaskiya”. Suratul Baqara: 111.

Ga abinda mujaddadi Shehu Usmanu xan Fodiyo Allah ya rahamshe shi ya ce: “Mas’ala: Ba a sukar batun cewa Allah ya na sama, domin ayoyi da hadisai masu yawa sune suka bayyana hakan qarara, abin suka shi ne faxin hakan ba tare da nufin tsarkakewa ba[15].

Tambayi hankalinka na asali, a ina kake jin Allah ya ke? Tambayi kurma da bai yi karatu ba. Tambayi yara qanana me ya sa su ke cewa, kiski ya na zagin Allah don ya xaga kansa a sama? Tambayi wanda ya ke cikin matsuwa a ina ya ke jin zuciyarsa ta tasar ma? Zuwa ina masu addu’a na dukkan addinai su ke kai hannayensu? Wannan fixirar da Allah ya halicci bayi akanta kenan, matuqar ba su gurvatu da bidi’ar falsafa ba.

Da wannan hujja ne Sheikh Abu Ja’afar Al-hamdani ya rinjayi wani abokin jayayyarsa, wani babban failasufi, Ustaz Al-juwaini wanda aka fi sani da Imamul Haramaini, a lokacin da Hamdani ya gabatar masa da waccan hujja sai ya rikice ya zabura ya buga kansa ya na cewa: “Hamdani ya rikitani! Ya rikitani!!. Imamu xanu Abil izzi shi ya kawo wannan qissa a sharhinsa da ya yi ma littafin aqidar Xahawiyyah[16]

Shi ma Imamu Abul Hasan Al-Ash’ari da wannan ne ya kafa hujjarsa a cikin Littafinsa mai suna Al-Ibanatu[17]. Ga abin da yace: “Mun ga Musulmi dukkansu idan suna addu’a suna xaga hannayensu ne zuwa sama, saboda Allah mai girma da buwaya ya xaukaka ne akan Al-arshi, shi kuwa Al-arshi ya na can qolin sammai, ba don cewar Allah (SWT) na saman Al-arshin ba da ba su xaga hannayensu zuwa can, kamar yadda ba ka ganinsu suna kife hannayensu zuwa qasa yayin yin addu’ar[18]

Sha’arani, xaya daga cikin daxaxxun masana, ya gamsu da wannan bayanin. Ga abin day ace kamar yadda Mujaddadi Shehu xan Fodiye Allah ya lullube shi da rahamarsa ya ciranto:

“In aka ce, mi nene cewa sanin Allah maxaukakin sarki wajibi ne? Amsa anan ita ce: Saboda shi sanin Allah wani lamari ne da ake isa gare shi cikin sauqi, ba ka ganin yadda idan mutun ya abka a cikin matsuwa nan take sai ka ga ya na jinginuwa zuwa ga abin bauta a cikin qan-qan da kai ya na komawa gare shi don a warkar da shi daga matsalar sa? anan ne zuciyarsa ta ke yin saduda har ya tada kai ya na kallon sama, babu qyabtawa don can ne alqiblar miqa addu’a ga dukkan halittu, kuma dukkan wannan ya na faruwa ne ga mutun a xabi’ance ba tare da wani ya koya masa ba, ya na mai neman mahaliccisa da ya yaye damuwarsa, ya kuma taimake shi.”

“Kuma Irin wannan kan faru ko a cikin dabbobin gida da na dawa za ka ga idan abin tsoro ya same su kamar rashin ruwa ko ciyawar kalaci idan sun fara jin qanshin halaka sai su rinqa tayar da kai zuwa sararin sammai don nufin neman agaji ga mahallici. Qananan yara ma, sau da yawa idan wani abin takaici ya samesu sai su xaga yatsun hannunsu (manuni) zuwa sama suna masu kai koke ga Allah. Irin wannan halaye ne fuskanta sama da ke faruwa ga dabbobi, abu ne wanda aka halicce su da shi a cikin jininsu. Su ke nan da ba su da hankali balantana mutum mai qwaqwalwar hankali, wannan itace fixirah (Halittar Allah) wadda alqur’ani da Hadisi suka bada, labarinta.[19]

 TABBAS ALLAH YA NA SAMA

 Allah mai girma ya ce:

﴿أَأَمِنْتُمْ مَنْ فِي السَّمَاءِ أَنْ يَخْسِفَ بِكُمُ الْأَرْضَ فَإِذَا هِيَ تَمُورُ (16) أَمْ أَمِنْتُمْ مَنْ فِي السَّمَاءِ أَنْ يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا فَسَتَعْلَمُونَ كَيْفَ نَذِيرِ (17)[الملك].

“Shin ko kun amince cewa, wanda ke cikin sama ba zai iya shafe qasa tare da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza? Ko kun amince cewa, wanda ke cikin sama ba zai iya sako muku iskar guguwa ba? To, za ku san yadda (aqibar) gargaxina ta kasance? Suratul Mulk 16-17

Abin nufi da Allah yace yana cikin sama shi ne yana akan sama. Kamar yadda ya ce:

﴿ فَسِيحُوا فِي الْأَرْضِ ﴾[التوبة:2] أي على الأرض

“Saboda haka ku yi tafiya cikin kasa”. At-Tauba: 2. ya na nufin akan qasa. Da kuma inda ya ce:

﴿لَأُصَلِّبَنَّكُمْ فِي جُذُوعِ النَّخْلِ﴾[طه:71]

“kuma lalle zan tsire ku a cikin itacen dabino”. D. H: 71 ya na nufin akan dabino.

Xanu Abbas (RA) ya fassara ayar da cewa, ba ku jin tsoron azabar wanda ke sama in kun sava masa?[20]

Ya zo a cikin Muwaxxa da Sahihu Muslim cewa: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace ma kuyanga: Ina Allah ya ke? Sai ta ce : a sama. Sai ya ce ma mai gidanta, ka ’yantar da ita domin ita mumina ce”.[21]

Imamuz Zahabi (RH), a cikin Littafinsa mai suna “Al’uluwwi Lil Aliyil-Azim” a qarkashin wannan Hadisin na kuyanga, ya ce: A kwai abu biyu da Hadisin ke karatarwa:

Na xaya:

A shari’ance, Musulmi ya na iya tambayar “Ina Allah ya ke?”

Na Biyu:

Amsar tambayar ita ce, ya na sama. Kuma duk wanda ya musanta xayansu (tambayar ko amsar) ba kowa ya ke wa musu ba face Almustafa tsira da Amincin Allah su tabbata a ga reshi.[22]

Imamu Abul-Hasan Al-Ash’ari (RH) ya ce: Shi dai Al-arshi ya na a can saman sammai ne duka, wannan shi ne dalilin da ya sa Allah maxaukakin sarki ya ce:

﴿أَأَمِنْتُمْ مَنْ فِي السَّمَاءِ ...﴾[الملك].

“Shin ko kun amince cewa wanda ke cikin sama……..”.

Saboda a nuna cewa Allah ya xaukaka ne kan Al-arshi, wanda shi kuma yana a kan sammai ne. A Larabce duk abin da ya xaukaka a na kiransa sama, shi kuwa Al-arshi yana qolin sammai. Don haka wannan aya ba tana nufin ne Allah ya na cikin sararin sammai ba. Sai dai ya na kan al-Arshin wanda shi kuma yake a birbishin sammai. Kamar yadda wata a cikin sammai ya ke garwaye da sub a duk da haka Allah ya ce ya na a cikin sammai in day a ke cewa:

﴿ وَجَعَلَ الْقَمَرَ فِيهِنَّ نُورًا ﴾ [نوح :16]

 “Ya sanya wata a cikinsu, ya na mai haskawa”. Suratu Nuh: 16.[23]

 XAUKAKAR ALLAH A AL-ARSHINSA MAI GIRMA

Allah maxaukakin sarki ya ce:

﴿إِنَّ رَبَّكُمُ اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ﴾ [الأعراف : 54] [يونس : 3].

 “Lalle Allah ne Ubangijinku wanda ya halicci sammai da qassai a cikin kwana shida, sa’annan kuma ya xaukaka a kan Al’arshi ya na gudanar da lamari”. Suratu Yunus: 3

Kuma maxaukakin sarki ya ce:

﴿تَنْزِيلًا مِمَّنْ خَلَقَ الْأَرْضَ وَالسَّمَاوَاتِ الْعُلَا (4) الرَّحْمَنُ عَلَى الْعَرْشِ اسْتَوَى (5)[طه].

(An saukar da shi) saukarwa daga wanda ya halitta qasa da sammai mai rahama, ya xaukaka a kan Al-arshi”. D.H.: 4-5

Duba qarin haske akan wannan aya cikin tafsirin Imamul Bagawi.[24] Wuraren da Allah maigirma da buwaya ya ambaci xaukakarsa a kan Al-arshi bayan ya kammala halitta sammai da qassai sun kai wurare guda bakwai a cikin Al-qur’aninsa mai girma ayoyi da suka gabata na daga cikinsu, sannan akwai aya ta 59: a Suratul-Furqani, da aya ta 4 a Suratus Sajadah; haka kuma da aya ta 2 a Suratur Ra’adi, ai kuma aya ta 4 a cikin Suratul-Hadidi.

 A bangaren Hadissai kuwa, limaman masu ruwaito Hadissai, Imamul-Bukhari da Muslim, sun ruwaito daga hadisin Abu Hurairata (RA) ya amso daga Annabi (SAW) ya ce: “da Allah ya yi nufi yin halittu, sai ya rubuta cikin Littafin da ke wurinsa a Saman Al-arshi cewa, Lalle ne rahamata ta rinjayi fushina”.[25]

Alkalin nan bamalike mai suna Abu Muhammad Abdulwahab xan Aliyu xan nasar Albagadadi; wanda ya rasu a shekara 422B.H., Allah ya yi masa rahama ya yi sharhi akan wannan batu da ya ke bitar kalaman mai Risala (Malam Xan Abu Zaidi Al-qairawani), a dai-dai inda mai Risalar ke cewa: “Kuma shi (Allah) da zatinsa, ya na saman Al’arshinsa mai girma, amma ilminsa ya game ko’ina”. A nan sai alqalin ya ce:

“Lalle sifaita Allah maxaukakin sarki da sifar xaukaka a Al’arshi shi ne matuqar biyar nassi da miqa wuya ga Shari’ah da gaskata Allah ga abin da ya sifaita kansa da shi. Kuma ba ya halatta a buga masa misali game da hakan domin Shari’a ba ta misalta komai ga irin wannan ba kamar yadda annabi (SAW) bai misalta shi ba kuma Sahabbai ba su yi tambaya game da hakan ba”[26].

Sai kuma Al-hafiz Az-Zahabi Allah ya yi masa rahama. Ga abin da yace:

“Waxannan siffofin fa na xaukaka da zuwan Allah a ranar alqiyama da kuma saukowarsa zuwa saman duniya, dukkansu sahihan nassoshi ne suka zo xauke da su. Daga nan ne malaman farko suka ciro suka miqo ma mafassaran bayansu, kuma ba su karkatar da ma’anar nassoshin ba balantana maganar yin watsi da su, a maimakon hakan, sun bayyanar da matuqar qyamarsu ga masu tawilin waxannan sifofin tare da cewa dukkansu sun san sifofin basu da kama da na halittu kuma sun san cewa, shi Allah wani abu bai zama kamar tamkarsa ba balantana a iya kwatantawa ko ayi wani ja-in-ja game da hakan. Yin haka ko matsayin martani ne ga Allah da manzonsa. Yin kwatance ko karkatar da fassara kuma shisshigi a cikin al’amari[27].

MA’ANAR ISTIWA’I A LARABCI DA SHARI’AH

 A harshen labarci kalmar (Istiwa’) ta qunshi fassarori da dama sai dai ko wace ma’ana a kan dube ta inda aka yi amfani da ita, akwai inda kalmar za ta zo ita kaxai, wani lokaci kuma tare da “wawun” ko kuma tare da “ila” ko “ala”. Ga misalansu kamr haka:

1) Idan lafazin “Al-istiwa’” ya zo shi kaxai ba tare da rakiyar wani harafi ba fassararsa ita ce cika da kammaluwa, kamar inda Allah ta’ala yace:

﴿ وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُ وَاسْتَوَى آَتَيْنَاهُ حُكْمًا وَعِلْمًا﴾[يوسف:14] .

“Kuma a lokacin da ya kai qarfinsa, kuma ya kammala, mun ba shi hukunci da ilmi” Suratul- Qasas:14.

2) Wani lokaci kalmar na zowa tare da “Wawun”, a nan ba ta banbanci da “sawa’un” ma’anarta daidaitar abu biyu, kamar a ce ‘Istawal-ma’u wal khashabu’, watau zurfin ruwa ya yi dai-dai da ciyawa.

3) Amma idan aka jingina harafin “Ila” ga lafazin Istiwa’i to, ma’anar ta kan canza zuwa ‘nufata’ ko kuma tasar ma wani abu, kamar in da Allah subhanahu ya ce:

﴿ ثُمَّ اسْتَوَى إِلَى السَّمَاءِ وَهِيَ دُخَانٌ فَقَالَ لَهَا وَلِلْأَرْضِ اِئْتِيَا طَوْعًا أَوْ كَرْهًا..﴾ [فصلت:11].

 “Sa’annan ya nufata zuwa ga sama alhali kuwa ita (a lokacin) hayaqi ce, sai ya ce mata, ita da qasa “ku zo bisa ga yarda ko a kan tilas” Suratu Fussilat:11.

4) A yayin da aka dabaibaye kalmar “Istiwa’” da harafin “Ala” sai ta xauki ma’anar hawa da xaukaka kamar inda Allah ta’ala ya ce:

﴿ لِتَسْتَوُوا عَلَى ظُهُورِهِ ثُمَّ تَذْكُرُوا نِعْمَةَ رَبِّكُمْ إِذَا اسْتَوَيْتُمْ عَلَيْهِ..﴾ [الزخرف:13]

“Domin ku hau a kan bayansu (jiragen ruwa da dabbobi) sa’annan ku tuna ni’imar ubangijinku idan kuka xaukaka a kansu”. Suratuz-zukhruf:13.

Kuma Allah mabuwayi yace:

﴿ وَاسْتَوَتْ عَلَى الْجُودِيِّ ﴾ [هود:44].

 “ kuma (jirgin) ya xaukaka a kan dutse”.

Suratu Hud:44.

Idan muka duba ayoyi bakwai na alqur’ani da suka bayyana “Istiwa’in” Allah akan Al’arshi za muga dukkansu sun zo ne da wannan siga ta qarshe, wato tare da rakkiyar harafin “Ala”[28].

Don haka ne malaman farko na wannan al’umma suka yi fassara daidai da ma’anar da muka cirato, cewa, Allah ya xaukaka ne akan Al’arshinsa. Mun cirato wannan daga Sahihul Bukhari kiabut-Tauhid, daga Abul Aliyah da Mujahid (Manyan Tabi’ai kuma almajiran Xan Abbas RA).[29]

Shi ma Hafiz Ibnu Hajar ya cirato daga Ibnu Baxxal Allah ya yi masa rahama cewa: “Ingantacciyar ma’ana ga kalmar ‘Istiwa’i’, ita ce, maganar mabiya Sunnah, domin Allah subhanawu wa ta’ala ya ce:

﴿سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ﴾[النحل:1]

“Tsarki ya tabbata a gare shi, kuma ya xaukaka daga barin abin da suke shirki da shi”. Suratuz-zumar: 67[30]

Al-hafiz Ibnu Hajar ya ce: Malam Bagawi ya hikaito daga Xan Abbas (RA) da mafiya yawan Malaman tafsiri, cewa, sun fassara ma’anar (Istawa alAl’arshi) da kalmar “Irtafa’a” ya xagu. Malaman lugga kamar Abu Ubaid da Farra’u da wasunsu su ma sun yi magana mai kama da wannan.[31]

Muna tabbatar wa Allah xaukaka a Al-arshinsa kamar yadda ya tabbatar wa da kansa kuma kamar yadda manzonsa (SAW) ya tabbatar masa ba tare da jirkitawa to karkatar da ma’anar ba, kuma ba tare da misaltawa ba. Yin hakan, shine mazhabar malaman farko managarta yardar Allah ta tabbata a garesu.

 MARTANI GA MASU TAWILI GA KALMAR ISTIWA’I (XAUKAKA)

Masu tawilanta wannan sifar ta Allah “Istiwa’i” (xaukaka akan Al’arshi) sun kasu gida biyu:

TAWILI NA FARKO:

Daga cikinsu akwai masu fassara ta da ma’anar Istila’i (rinjaya), wai kalmar “Istiwa’i” a wajensu a na yi mata qarin harafi xaya ne don ta yi daidai da abinda su ke ganin ya dace da Allah (Rinjaya a maimakon xaukaka). Wannan ra’ayin ya samo asali ne daga wani mutum mai suna Jahamu xan safwan.[32] Kasancewar wannan fassara tasa ta ci karo da fassarar tarsashin masana harshen larabci da Shari’ah ya sa malamai suka qaurace ma ra’ayinsa mafi girman qauracewa, suka wallafa littafai akan yi masa raddi. Daga cikin waxanda su ka yi masa raddi har da jagoran Ahlus Sunnah Wal Jama’ah, Imamu Ahmadu xan Hambali (Allah ya jiqansa).

Wani abin da malaman harshen larabci su ka lura da shi kuma shine, ita wannan kalmar da Jahmu ya musanta kalmar Allah da ita “Istila’i” larabawa ba su amfani da ita sai akan wanda ya yi rinjaye bayan ya gamu da jayayya. Mashahurin Malamin Arabiyyan nan da ake ce ma Ibnul-A’rabi ya gamu da wani malami mai irin wannan fassarar, sai yace masa. Ahir! ko ka san cewa shi Istila’i (rinjaya) ba ya faruwa sai an samu ja-in-ja? Wane ne yake iya ja-in-ja da Allah?.

Masana sun nemi masu wannan fassarar da su kafa hujja daga littafin Allah ko Sunnar Manzon Allah (SAW), amma abin ya gagare su. Daga maganganun larabawa ma ba su samu wata hujja ba sai wani baiti qwara xaya da aka jingina shi ga wani Banasare (kirista) wanda yayinsa ya shuxe a zamanin daular Banu Umayyah, sunansa: “al’Akhxal”. Shi dai wannan mayaqin ya shahara da adawa da musulunci da yi masa izgili, sannan da sukar lamiri ga musulmi. Bil hasili ma wasu masana suna da ra’ayin cewa, shi an canza masa waqrsa ne ba haka ya faxe ta ba. An dai samu qwararrun malamai da su ka hutar da mu mai da martani kan amfani da baitin nasa, kamar Ibnu Taimiyyah[33] da almajirinsa Ibnul qayyim[34].

Akwai bayanai masu dama na malamai kan wannan waxanda wannan xan qaramin rubutu ba zai iya xauka ba[35].

TAWILI NA BIYU:

 Masu tawili na biyu su kuma sun canza ma’anar Al’arshi ne da aka sani, suka ce, Al’arshi ya na nufin Mulki ne, don haka a wajensu cewar Allah ya xaukaka a Al’arshi tana nufin shi mai mulki ne kenan.

Bayanan da suka zo daga alqur’ani da Hadisi su na nuna kuskuren wannan tawili qarara, domin shi Al’arshi nassi ya bayyana shi a matsayin karaga ce mai innuwa wadda ake iya dafawa, har ma a shiga cikin innuwarta.[36] Kai ba haka ba ma Allah maxaukaki ya bayyana mana cewa, mala’ikku su na tallabe da Al’arshin nasa. Ga abin da Allah mai girma da buwaya ya ce:

﴿وَيَحْمِلُ عَرْشَ رَبِّكَ فَوْقَهُمْ يَوْمَئِذٍ ثَمَانِيَةٌ﴾ [الحاقة : 17]

“Kuma )wasu mala’iku) takwas na xauke da Al’arshin ubangijinka a sama dasu a wannan ranar”. Suratul-hakkah;17.

Kuma da inda ya ce:

﴿الَّذِينَ يَحْمِلُونَ الْعَرْشَ وَمَنْ حَوْلَهُ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ﴾ [غافر : 7]

“waxanda ke xaukar Al’arshin da waxanda ke kewayensa, su na tasbihi game da gode wa ubangijinsu”. Suratu Ghafir:7.

Sai kuma inda Allah mai tsarki ya ce:

﴿وَتَرَى الْمَلَائِكَةَ حَافِّينَ مِنْ حَوْلِ الْعَرْشِ﴾ [الزمر : 75].

“kuma kana ganin mala’ikku suna kewaye a sassan Al’arshi”. Suratuz-zumar: 75.

 Al’arshi fa shi ne mafi girman halittu, wanda Allah bai halicci abin da ya kai girmansa ba. Kuma Allah ya halicce shi ne tun kafin halittar sammai da qassai * kamar yadda Allah ta’ala ya ce:

﴿وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ وَكَانَ عَرْشُهُ عَلَى الْمَاءِ﴾ [هود : 7]

“Kuma shi ne wanda ya halicci sammai da qasa a cikin kwanaki shida, kuma Al’arshinsa ya kasance a kan ruwa”. Suratu Hud: 7.

haka kuma shi wannan Al’arshin ya na da qafafuwa kamar yadda Hadisi ya zo cewa:

“sai na ga (Annabi) Musa rike da qafa xaya daga cikin qafafuwan Al’arshi”.[37]

Tambaya a nan ita ce, shin mulkinsa ne yake kan ruwa? Ko mulkin ne mala’ikun suka tallabe? Kuma har wayau shine suka kewaye? Ko kuma shi Annabi Musa ya riqe qafar mulki ne? Wannan wace irin ruxuwa ce?

  ALLAH YANA TARE DA MU, YA NA KUSA DA MU

 Babu cin karo a tsakanin abinda ya gabata na xaukakar Allah a Al’arshi da cewa yana tare da halittunsa, ko kuma ya na kusa da su. Allah Tabaraka wa ta’ala yace:

﴿وَهُوَ مَعَكُمْ أَيْنَ مَا كُنْتُمْ﴾ [الحديد : 4]

“Kuma shi (Allah) ya na tare da ku a duk inda kuka kasance”. Suratul Hadid:4.

 Abinda ya zama wajibi shi ne mu fahimci wannan tarayyar kamar yadda malaman farko suka fahimce ta. Domin mu fahimci nassin daidai da su sai mun lura da siyaqin ayoyin da ke wannan bayani, Mu karanto farkon ayar da ta gabata mana don mu sha labari:

﴿هُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِي الْأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا وَهُوَ مَعَكُمْ أَيْنَ مَا كُنْتُمْ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ﴾ [الحديد : 4]

“Shi ne wanda ya halitta sammai da qasa a cikin wasu kwanaki shida, sa’annan ya xaukaka akan Al’arshi, yana sanin abin da ke shiga cikin qasa da abinda ke fita daga gareta, da abinda ke sauka daga sama da abinda ke hawa cikinta. Kuma shi yana tare da ku, a duk inda kuka kasance. Kuma Allah mai gani ne ga abin da kuke aikatawa”. Suratul Hadid: 4.

Muna iya lura cewa, farkon wannan ayar ya tabbatar da abin da muka faxa, cewa Allah ya xaukaka akan Al’arshi bayan halittar sammai da qasa. A tsakiyarta sai ya tabbatar da cewa, ilminsa ya kewaye dukkan halittu, kuma ya na tare da su. Daga qarshe sai ya fassara wannan tarayyar da cewa: “Kuma Allah mai gani ne ga abinda kuke aikatawa”.

Bayanin wannan aya ya yi daidai da abin da Annabi (SAW) ya ke faxa a cikin addu’arsa, inda yake cewa:

"اللهم أنت الصاحب في السفر ، والخليفة في الأهل"

“Ya Allah kai ne aboki a tafiya, kuma Halifa ga iyalai”[38].

Mun fahimta kenan cewa, Allah maxaukaki ya na tare da matafiya a lokacin tafiyarsu, kamar yadda ya ke tare da iyalan matafiyan a cikin garuruwansu da cikin gidajensu.[39] Ko kai ka na fahimta ne cewa kenan zatin Allah ya na garwaye da zatotan matafiya da na iyalansu?

To, idan haka ka fahimta a wannan aya, ya ka fahimci ita kuma wannan?

﴿مُحَمَّدٌ رَسُولُ اللَّهِ وَالَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ﴾ [الفتح : 29]

“Muhammadu manzon Allah ne, kuma waxannan da ke tare da shi…”. Suratul fathi: 29.

A nan ma waxanda ke tare da Manzon Allah sun shige a cikin zatinsa kenan? Ko kuwa ana nufin waxannan da ke tare da shi a Imani?.

Ga wata ayar ita ma mai kama da wannan:

﴿إِلَّا الَّذِينَ تَابُوا وَأَصْلَحُوا وَاعْتَصَمُوا بِاللَّهِ وَأَخْلَصُوا دِينَهُمْ لِلَّهِ فَأُولَئِكَ مَعَ الْمُؤْمِنِينَ﴾

 [النساء :146]

“Sai fa waxanda suka tuba, kuma su kayi gyara, kuma su ka tsarkake addininsu saboda Allah, to, waxannan suna tare da muminai”. Suratun Nisa’i: 146.

Ashe muna iya fahimtar cewa, suna tare da muminai ne a cikin imani da soyayya. Don haka ne ma a wata ayar Allah ya ce mana:

﴿وَكُونُوا مَعَ الصَّادِقِينَ﴾ [التوبة : 119]

“Kuma ku kasance tare da masu gaskiya”. Suratut Taubah; 119.

Kuma yace:

﴿وَارْكَعُوا مَعَ الرَّاكِعِينَ﴾ [البقرة : 43]

“Kuma ku yi ruku’i tare da masu ruku’i”. Suratul-Baqara: 45.

 Sai mu koma ma ayarmu ta farko. Allah ya na tare da mu a duk inda muka kasance. Ba mu iya voye ma Allah duk in da muka shiga. Maxaukaki ne akanmu, Masani ne ga halinmu, Mai gani ne ga lamurranmu. Don haka ko da yaushe ya na tare da mu[40].

Wannan shi ne abinda ayar ta ke nufi. Saurari wannan fira da ta gudana a tsakanin Imamul Madini (Malamin Imamul Bukhari) da wani almajirinsa.

Almajiri: “Gafarta Malam me ne ra’ayin jama’ah game da ganin Allah”? (jama’a, ya na nufin Ahlus Sunnah).

Al Madini: “Sun yarda da cewa ‘yan Aljanna suna ganin Allah a lahira, sun kuma tabbatar da cewa Alqur’ani maganar Allah ce, kuma Allah ya na sama a kan Al’arshi”.

Almajiri: “To, me za ka ce game da faxar Allah maxaukakin sarki:

﴿مَا يَكُونُ مِنْ نَجْوَى ثَلَاثَةٍ إِلَّا هُوَ رَابِعُهُمْ﴾[المجادلة:7]

“Wata ganawa ta mutum uku ba zata kasance ba face Allah shi ne na huxunsu…”? Suratul Mujadala: 7

Al Madini: “Karanto farkon ayar, sannan ka je har qarshenta”.

Al Majiri: (Sai ya karanto wannan aya):

﴿أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ مَا يَكُونُ مِنْ نَجْوَى ثَلَاثَةٍ إِلَّا هُوَ رَابِعُهُمْ وَلَا خَمْسَةٍ إِلَّا هُوَ سَادِسُهُمْ وَلَا أَدْنَى مِنْ ذَلِكَ وَلَا أَكْثَرَ إِلَّا هُوَ مَعَهُمْ أَيْنَ مَا كَانُوا ثُمَّ يُنَبِّئُهُمْ بِمَا عَمِلُوا يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّ اللَّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ ﴾[المجادلة:7]

“Ashe ba ka ga cewa lalle Allah ya na sane da abinda yake a cikin sammai da abinda ke cikin qasa ba?. Wata ganawa ta mutum uku ba zata kasance ba face Allah shi ne na huxunsu, Haka ma mutum biyar face shi ne na shidansu, haka ma abinda bai kai haka ba, ko abinda ya wuce shi, face yana tare da su a duk inda suke. Sa’annan zai ba su labari da abin da su ka aikata a ranar alqiyama. Lalle Allah masani ne ga dukkan kome”. Suratul Mujadala: 7.

Al Madini: “Daga farkon ayar har qarshenta ta na magana ne akan kewayewar sanin ubangiji”.

Almajiri: “Malam a qara min bayani”.

Al Madini: “A farkon ayar Allah yace, yana sane da komai a cikin sammai da kuma cikin qasa. Don haka sai yace, ya na tare da mu a duk in da mu ke. Sannan ya jaddada mana cewa, shi masani ne akan kome”.

Almajiri: “Malam na gamsu sosai. Allah ya saka da alheri”.[41]

Bayan haka kuma Allah tsarkakakken sarki, ya bayyana mana ya na tare da annabawansa da waliyyansa (masoyansa). Yace, ya na tare da masu gaskiya, da masu taqawa, da masu haquri da kuma masu kyautatawa. Wannan taren ita kuma daban ce. Ga wasu daga wuraren da Allah ya faxe ta kafin mu bayyana ma’anarta:

﴿إِنَّ اللَّهَ مَعَ الَّذِينَ اتَّقَوْا وَالَّذِينَ هُمْ مُحْسِنُونَ﴾[النحل:128]

“Lalle Allah yana tare da waxanda suka yi taqawa da waxanda suke su masu kyautatawa ne”.

Suratun nahl: 128.

﴿إِنَّ اللَّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ﴾[البقرة:153 والأنفال:46]

“Lalle Allah ya na tare da masu haquri”.

 Suratul Baqarah:153 da Suratul Anfal: 46

﴿وَأَنَّ اللَّهَ مَعَ الْمُؤْمِنِينَ﴾[الأنفال:19﴾

“Kuma lalle,Allah ya na tare da mummunai”. Suratul Anfal: 19

﴿فَلَا تَهِنُوا وَتَدْعُوا إِلَى السَّلْمِ وَأَنْتُمُ الْأَعْلَوْنَ وَاللَّهُ مَعَكُمْ وَلَنْ يَتِرَكُمْ أَعْمَالَكُمْ﴾[محمد:35]

“Don haka, kada ku yi rauni ku kira zuwa ga sulhu, alhalin ku ne maxaukaka, kuma Allah ya na tare da ku, kuma sam, ba zai tauye maku aikinku ba”. Suratu Muhammad: 35

Ma’anar Allah ya na tare da waxanda aka lissafa shi ne, ya na taimakonsu da qarfafa su kamar dai yadda ya ce ma annabi Musa da xan uwansa annabi Haruna (AS):

﴿قَالَ لَا تَخَافَا إِنَّنِي مَعَكُمَا أَسْمَعُ وَأَرَى﴾[طه:46]

 (Allah) Yace, lalle ni ina tare da ku, ina ji, kuma ina gani”.[42] Suratu X.H :46.

 Har ila yau dai wannan tarayyar ba ta nufin cewa Allah da zatinsa ya na garwaye ne da zatin annabi Musa da annabi Haruna. Sai dai ya na tare da su domin ya na jinsu, ya na ganinsu, yana kuma taimakonsu da kariyarsu daga duk wani sharrin da fir’auna da mutanensa za su qulla ma su.

Sanin haka ne ya sa annabi Musa (AS) da Banu Isra’ila su ka ce mi shi, lalle fa fir’auna da mutanensa za su kewaye mu, sai ya ce: “Kayya! Lalle ne, ubangijina yana tare da ni, zai shiryar da ni”. Suratus-Shu’ara; 62.

Irin wannan tsagwaron imani na annabawa ne kuma ya sa Annabinmu Muhammadu (SAW) yace wa Abubakar Siddiqu a lokacin da suke a cikin kogo: “kada ka yi baqin ciki, lalle ne Allah ya na tare da mu”[43] Suratut Taubah: 40.

 Ya na kuma da kyau mu sani cewa, Shi bawa a wasu lokuttan ya fi kusanci zuwa ga ubangijinsa fiye da wasu lokuttan. Abin da zai tabbatar da wannan kuwa shi ne Hadisin Abu Huraira (RA) wanda ke cikin Sahihu Muslim daga Annabi (SAW) ya ce: “Bawa ya na fin kusantar ubangijinsa ne a lokacin da ya ke cikin sujada”[44].

Idan ka fahinci wannan sarai, za ka gane cewa, babu wani takin saqa a tsakanin kusancin Allah da xaukakarsa. Allah yana tare da halittunsa baki xaya ta fuskar sanin zahirinsu da baxininsu. Ya na kuma tare da kevavvun bayinsa, tare ta musamman, domin ya na qaunarsu, ya na taimakonsu, ya na qarfafa su, ya na kare su. Shi kam littafin Allah har abada babu cin karo a tsakanin ayoyinsa. Malaman Sunnah sun fahimci haka. Don haka maganganunsu bisa hanya su ke. Wanda ke son ya gano inda maganganu ke cin karo da junansu, sai ya leqa a cikin kalaman ‘yan bidi’a[45].

 BANBANCIN TAFWILI DA TAWILI

Kalmar “Tafwili” an ciro ta ne daga ‘fawwala ilahil amra’, ya mayar da lamari gare shi, sai yadda ya ce. Ga addu’ar Annabi (SAW) ya na cewa: ‘wa fawwaltu amri ilaika’ “kuma na jingina al’amarina gare ka”[46].

Amma malaman falsafa abinda suke nufi da tafwili game da sifar Allah mai girma da xaukaka shi ne, abin da suke jingina wa magabata na kame baki daga fassara sifofin Allah, wai domin ba su san ma’anarsu ba. Har suka ce, saninsu ga waxannan kalmomi bai wuce sanin da bobayi ke yi ma kalmar larabci ba idan sun ji an faxe ta. Babu shakka wannan ya nuna cewa, malaman falsafa sun jahilci magabatan wannan al’umma waxanda su ne halittun da suka fi kowa sanin Allah. Kuma wannan magana ta qumshi tuhuma iri biyu. Tuhuma ta farko ga malaminsu (Annabi SAW) shi da bai sanar da su ba (a cewarsu), ta biyun kuma ga almajiran (Sahabbai) da su ka kasa tambaya. Waxannan tuhumomin ko suna nuna tsananin rashin sanin girman Manzon Allah (SAW) daga falsafawa.

Abin da tarihi ya tabbatar shi ne, faxar magabata da suke cewa game da siffofin Allah: “ku bar su yadda su ka zo”. Amma basu tava samun wani qunci ba wajen sifaita Allah da abinda ya sifaita kansa. Wannan ma’anar tafwili kenan.

Shi kuma ‘Tawili’ asalin kalmarsa ita ce ‘Awlu’, wadda take nufin ‘Ruju’u’ (karkatowa da komawa). Abinda ma ya sa ake ce ma na xaya ‘Awwalu’ saboda shi ne farkon qidaya, duk abinda ya zo daga baya yana komawa ne zuwa ga re shi.[47] Wani lokaci ana amfani da kalmar tawili a matsayin kalmar tafsiri kamar yadda Imamu al Tabari ya keyi. A cikin alqur’ani kuwa, kalmar tawili ta zo ne da nufin makomar lamari a qarshensa.[48]

To, amma duk waxannan ma’anonin ba su failasufi ya ke nufi da tawili ba. Shi dai a gurinsa a kautar da ma’anar lafazi wadda aka sani a bashi wata baquwar ma’ana shi ne tawili.

A nan malamai sun fayyace al’amarin kamar haka:

1. Idan aka yi tawilin kalma saboda wata karvavviyar hujja da ta yi nuni ga yinsa, hujjar ta alqur’ani ce ko ta Hadisi, to wannan ba ya da laifi. Kuma malaman fiqihu su na amfani da wannan.

2. Idan kuwa aka yi tawili saboda wata hujja maras qarfi, to, wannan tawilin shi ma ba ya da qarfi, kuma ba’a karvarsa.

3. Idan tawili ya kasance ba ya da dalili sam, sai dai ganin ya dace daga wani mai yaba kaifin tunaninsa. Anan ne malamai su kace, ba a amfani da shi domin addini ba wasa ba ne. Kuma wanda aka aiko ya yi bayani duk ya fi mu hankali da kaifin tunani.

A wannan na ukun tawilin sifofin Allah ya faxo. Domin in ban da tunanin failasufi babu wata hujja sam, ta yin tawilinsu, tun da har Annabi (SAW) da magabatan farko ba suyi ba.

Daga nan ne sanannar qa’idar nan ta malamai ta zo cewa, “duk abinda ya zo cikin Littafin Allah da Sunnar manzonsa (SAW) ba ya halalta a kauce ma zahirin ma’anarsa sai da dalili mai tilasta yin haka[49].

MAGABATA BA SU TAFWILI, BA SU TAWILI

Ko alama, malaman da suka gabata basu tafwili kamar yadda ba bu ruwansu da tawili. A maimakon haka, su na tabbatar ma Allah ne da sifofinsa kamar yadda ya sifaita kansa.

Amma abin mamaki shine ganin yadda wasu ke jingina Aqidar tawili da tafwili ga malaman da suka gabata. Ga alama irin waxannan mutane ba su gama sanin su wa ye magabata ba. Wani sa’ilin ma ka najin suna furta cewa, wai “Salaf” magabata, sune mufawwila, watau masu kame baki suyi shuru dalilin jahilcinsu ga sanin ma’anar sifofin Allah. Su kace, su ko “Khalaf” malamai na bayansu, sune ‘ma’awwila’, masu karkata ma’anar nassi. Don haka sai su qara da cewa, hanyar Salaf ta fi tsira, ta Khalaf ko ta fi nuna qwarewa.[50]

Gaskiyar Allah kam ita ce, magabata “Salaf” su ne mafifita ilmi da fasaha. Malaman bayansu kuma su na bisa siraxinsu. Wanda duk ya yi vaton hanya har ya faxa gidan falsafa to, shi ya kai kansa.

Dubi yadda Allah ya tsarkake mana Salaf (Ina nufin Sahabbai), ya wanke su tas, daga dukkan vata da xemuwa da ruxani, yace, su ne su ke akan shiriya madaidaiciya. Har ma ya ja kunnenmu da qyaci mai qarfi akan barin hanyarsu. (Duba Suratun Nisa’i: 115). To, ya za’a yi wani ya zo ya nuna mana ya fi su qwarewa a sha’anin sanin Allah?

Alhafiz, Az-Zahabi (Allah ya rahamshe shi) yace: “Daidai da lafazin da bai buqatar a fassara shi, magabata sun fassara shi balantana ma lafazi mai muhimmanci. Haka kuma duk wata aya ko Hadisi da ke xauke da bayanin sifofin Allah ba a samu inda suka yi tawilinta ba, tare da kasancewarsu mafi muhimmancin abubuwa a cikin addini, da kuwa yi musu tawili wani abin tinqaho ne babu shakka da ba a riga su yinsa ba.”

Zahabi yaci gaba da cewa, “Wannan shi ya tabbatar da cewa, karanta su da barinsu da ma’anarsu da aka sansu da ita, shi ne gaskiyar da ba ta neman ado, ba wai ba su wani tawili ba. Saboda haka, mu yi imani da su tare da koyi da magabata.[51]

TAFWILI YA SHA BANBAN DA HANYAR MAGABATA

 Ya na da kyau mu banbance a tsakanin hanyar magabata, ita ce, tabbatar da sifofin Allah, da abin da ‘yan falsafa ke kira tafwili.

Su dai magabata su na tabbatar da sifofin Allah ne, suce, mun san ma’anarsu, amma mu na kame baki daga ba da misali, ko kwatantawa. Domin ba mu kewaye sanin Allah ba balantana mu faxi yanayin sifofinsa, kamar yadda ya ce:

﴿وَلَا يُحِيطُونَ بِهِ عِلْمًا﴾[طه:110]

 “kuma ba su kewayewa da shi ga sani’. Suratu X.H:110 [52].

Su kuma masu da’awar tafwili cewa su ke, kar ma a fassara su baki xaya. A bar su a matsayin wani yare wanda ba’a gane ba.

To, shi kenan idan dabinon aljanna ba irin na duniya ba ne, sai ka ce, to, ba dabino ba ne? Ko giyar aljanna ita ma ba giya ce ba? Duk abin da ke cikin aljanna bai yi tarayya da na duniya a komi ba ban da suna. Haka babban masanin Alqur’ani, Ibnu Abbas (RA) ya faxa da ya ke fassara faxar Allah Ta’ala:

﴿فَلَا تَعْلَمُ نَفْسٌ مَا أُخْفِيَ لَهُمْ مِنْ قُرَّةِ أَعْيُنٍ جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ﴾[السجدة:17]

“Saboda haka wani rai bai san abin da aka voye musu ba na sanyin idanu’ (a aljanna). Suratus Sajdah: 17.

Ga wasu ‘yan misalai a gurguje masu tabbatar da hanyar magabata:

Mu fara daga gidan Manzon Allah (SAW). Mai xakinsa, uwar mummunai, Zainabu xiyar Jahshu (RA) ta kan ce da shi “Ni fa Allah ne ya xaura aurena da kai, tun a saman Al’arshinsa”. A wata ruwayar “Ni fa a sama Allah ya xaura aurena da kai”[53]. Kana zaton cewa Zainab Allah ya yarda da ita ta jahilci ma’anar cewa, Allah ya na saman Al’arshi?.

Ita kuma uwar mummunai Aishatu (RA) ta furta cewa: “Allah da ke kan Al’arshi ya san ban ji daxin kashe khalifa Usman ba”[54]. Ina tafwili yake a cikin maganarta?

 Sai qanen Manzon Allah (SAW), Abdullahi xan Abbas, shi kuma ga abin da yace ma ita Aishar (RA): “Ke ce fa mafi soyuwar mata ga manzon Allah (SAW), kuma shi ba ya son abin da ba ya da tsarki. Ga kuma Allah ya saukar da labarin barrantarki daga birbishin sammai bakwai?[55]. Shi ma xan Abbas ya na tafwili ne, bai san ma’anar Allah na sama ba?

Mu je zuwa dai. Umar xan Khaxxabi (RA) yace ma Khaulatu xiyar Sa’alabah: “Allah ya ji koken wannan mata a birbishin sammai bakwai”[56].

Har wayau a lokacin halifancin Umar xin ne, ya zo a Birnin Sham, sai gwamnansa ya neme shi da ya hau ingarman doki don ya yi kwarjini ga idon mutane, sai Umar ya ce masa: “ku kuna lura da nan ne, amma al’amari a can yake! Sai ya nuna sama”[57]. To, shi ma Sarkin Musulmi Umar (RA) bai san inda Allah yake ba ke nan?.

 Mu saurari bayanin xaya daga cikin masanan Alqur’ani a zamanin Sahabbai, shi ne Abdullahi xan Mas’ud (RA), ga abin da ya ke cewa: “Al’arshi ya na a saman ruwa ne, shi kuwa Allah yana saman Al’arshi, kuma ba abinda ke voye masa daga ayukkanku”.

Su dai Sahabbai malaminsu ne su ke biya. Don ko shi ne yace masu: “ba za ku amince min ba alhali ni amintacce ne ga wanda ke a sama?[58]. Kuma yace masu: “Na rantse da wanda rayuwata ke hannunsa, babu mutumin da zai kira matarsa zuwa ga shimfixa ita kuma ta qiya masa face, wanda ke a sama ya yi fushi da ita har sai lokacin da mijinta ya huce da ita”[59].

Haka kuma yace masu: “Allah mai rahama ya na tausayin masu tausayi, ku ji tausayin na qasa, wanda ke a sama ya ji tausayinku”[60].

 Me zai hana Sahabbai su tabbatar da cewa, Allah na sama kenan, tun da haka ne malaminsu ya karantar da su? Babu shakka Hadisai masu ximbin yawa ne suka tusgo a kan tabbatar da wannan ma’ana. Kuma akansu ne dukkan Sahabbai da Tabi’ai su ka tafi, daga nan har illa ma sha Allahu, kafin vullar ilmin (ko kuma jahilcin) falsafa a qasar musulmi. Nemi littafin Shamsuddin al Zahabi mai suna: “Kitabul Arshi” da kuma xaya littafin nasa mai suna: Al’uluwwu lil Aliyil gaffar za ka samu cikakken bayani[61].

 FASSARAR MAGANAR IMAMU MALIK:

(AL ISTIWA’ﷻ‬ MA’LUMUN)

 Ruwayoyi sun zo daga magabata daga cikin Sahabbai da Tabi’ai, har ma Rabi’atu mashahurin malamin na Imamu Malik, da shi kansa ma Malik, (Allah ya yarda da su baki xaya) cewa, ko wannensu an tambaya shi game da yadda Allah ya xaukaka akan Al arshi. Ga kuma amsar da ko wannensu ya bayar:

“Xaukaka abu ne sananne, hankali bai gano yadda Allah ya yi tasa, Imani da ita kuma wajibi ne, wannan tambayar kuwa bidi’a ce”. A wata ruwaya, malam Rabi’atu ya qara da cewa: “kuma sako ne daga Allah, manzo ya isar da shi, gaskata shi ya zama tilas”[62].

Wannan gamsasshen bayani na malamai ya gamu da daga rashin fahimta daga vangaren ‘yan tawili, sai su ka jefa shi a gidan tafwili. Don haka in za su kafa hujja akan cewa, magabata ba su san ma’anonin sifofin Allah ba, sai ka ji sun ce, ai ga abinda Imamu Malik yace.

 Mai karatu kuwa da ya sake nazarin maganar malaman da mu ka akan siraxi take, babu nuna jahilci a cikinta. Xaukaka abu ce sananniya, don ko ma’anarta a fili take ba voye ba. Kwatanta yadda xaukakar Allah take shi kuma abinda ba za’a iya kai gare shi ne ba, domin ya zaka kwatanta wanda ba ka tava gani ba kuma ba ya da tamka bale ka kwatanta da tamkar tasa? Gaskata Allah da manzo da su ka faxi waxannan sifofi shi wajibi ne. Wannan tambayar ita kuma bidi’a ce wadda ta vulla bayan zuwan falsafa. Kafin haka ba wanda ya ke tambayar ya Allah ya yi kaza? ko kuma ya sifar Allah iri kaza ta ke? Allah ya xaukaka daga a kewaye da saninsa.

Ga abin da Shehun Malami Muhammadul Aminu As Shinqixi ya faxi a cikin littafinsa “Rihlatul Hajji ila baitillahi”:

“Babu shakka cewa, bin hanyar Littafin Allah da Sunnar manzonsa shi ne mafi aminci musamman game da abinda ya shafi bayanin sifofin Allah maxaukakin sarki, domin hankali bai iya kai ga tantance su, kamar yadda Allah yace:

﴿يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلَا يُحِيطُونَ بِهِ عِلْمًا﴾ [طه :110]

(Allah) ya na sanin abinda ke a gaba gare su da abinda ke bayansu, kuma ba su kewayewa da shi ga sani” Suratu X.H :110.

Malam Shinqixi ya ci gaba da cewa, Wannan bayani da muka yi na tabbatar ma Allah sifofinsa ba tare da misalce misalce ba shi ne abin da Imamu Malik Allah ya rahamshe shi ke nufi da faxarsa ta cewa, xaukaka sanannen abu ce, ba a voye take ba. Amma ba a san yadda kwatancinta ya ke ba. Ya na nufin cewa, wannan duk balarabe ya san ma’anarta, kuma Imani da ma’anar xaukaka ga Allah wajibi ne ba tare da sauran shisshigi ba.

TAWILI WANI SALO NE NA TASHBIHI

 Abinda mu ke son mu faxakar akansa anan shi ne, tawilanta sifofin Allah shi kansa ya samo asali ne daga kamanta Allah da halittu. Wannan kamantawar ita ce ta zaburar da su zuwa ga yin tawili don kauce ma wannan varna. An yi gudu ba a tsira ba ke nan. Amma shi wanda ya bi sahun malaman farko ya tsaya a inda Allah ya tsayar da shi, babu wani abin da zai sa shi yin tawili. Wannan kuwa a fili ya ke. Alhamdu Lillahi. Don haka ne Malam Nu’aimu xan Hammad (daga cikin malamai tsararrakin Imamu Malik) yace: “Duk wanda ya misalta Allah da wata halittarsa to, ya saki hanya. Wanda kuma ya musunta abinda Allah ya sifaita kansa da shi, shi ma ya yi vaton kai, kuma sifaita Allah da abinda ya sifaita kansa da shi kuma manzonsa ya tabbatar bai tilasta yin kwatance”[63].

MARTANI AKAN WASU SHUBHOHI

Babbar hujja ga masu tawili ita ce, wai an samu wasu magabata sun yi. Don kuwa ga gulbin ilmi da kansa Abdullahi xan Abbas ya na cewa game da wannan aya:

﴿وَالسَّمَاءَ بَنَيْنَاهَا بِأَيْدٍ﴾ [الذاريات : 47]

 “Kuma sama mun gina ta da wani irin qarfi”. Suratuz Zariyat: 47.

Qarfi anan wai tawili ne, domin ayar hannaye ta faxa ba qarfi ba. Sai muka koma ga tafsirai don muga me nene gaskiyar wannan lamari?

Ga abinda muka samu:

Malaman tafsiri sun bayyana kalmar “aidin” a matsayin kalma xaya wadda ta ke nufin qarfi. Don haka ba ta da alaqa da kalmar “Yadaini” ko “Aidi” waxanda suka zo a cikin wasu ayoyi. Kenan sam wannan aya ba ta cikin ayoyin da suka tabbatar ma Allah da sifar hannaye. Kuma sauran malamai ma sun ba ta fassara irin ta Abdullahi xan Abbas (RA)[64].

Daga nan zamu fahimci cewa, xan Abbas ba ya kore ma Allah cewa, ya na da hannaye, kamar ya faxa a cikin Suratul Fathi:

﴿إِنَّ الَّذِينَ يُبَايِعُونَكَ إِنَّمَا يُبَايِعُونَ اللَّهَ يَدُ اللَّهِ فَوْقَ أَيْدِيهِمْ﴾ [الفتح : 10]

“Lalle waxanda ke yi maka mubaya’a Allah ne suke yi wa mubaya’a. Hannun Allah na bisa hannayensu” Suratul Fathi: 10.

Da kuma inda Buwayayyen Sarki yake cewa:

﴿بَلْ يَدَاهُ مَبْسُوطَتَانِ يُنْفِقُ كَيْفَ يَشَاءُ﴾ [المائدة :64]

“A’aha hannuwansa biyu shimfixaxxu ne, ya na ciyarwa yadda yake so”. Suratul Ma’ida: 64.

Da kuma inda yake cewa Iblisu:

﴿مَا مَنَعَكَ أَنْ تَسْجُدَ لِمَا خَلَقْتُ بِيَدَيَّ﴾[ص:75]

“Me ya hana ka, ka yi sujada ga abin da na halitta da hannayena biyu”? Suratu Sad: 75.

Da dai ire-iren waxannan ayoyi masu ambatar sifofin Allah daban daban. Babu wanda ya isa ya jingina ma Abdullahi xan Abbas (RA) wata fassara ga waxannan ayoyi ban da ma’anar da ta zo qarara a cikinsu. Amma a waccan ayar “Al’aidu” lafazi ne guda, ba jam’in hannu ne ba, ma’anarsa kuma itace qarfi kamar yadda muka faxa. Ga wasu wuraren ma in da wannan kalma ta zo (ba ga ubangiji ba) amma kuma ba’a fassara ta da hannaye ba. Allah Ta’ala yana cewa:

﴿وَاذْكُرْ عَبْدَنَا دَاوُودَ ذَا الْأَيْدِ إِنَّهُ أَوَّابٌ﴾[ص:17]

 “Kuma ka ambaci bawanmu Dawuda ma’abuci qarfi (wajen ibada). Suratu Sad: 17.

Ga kuma wata ayar:

﴿وَاذْكُرْ عِبَادَنَا إبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ أُولِي الْأَيْدِي وَالْأَبْصَارِ﴾[ص:45].

“Kuma ka ambaci bayinmu Ibrahimu da Ishaqa da Yaquba ma’abuta qarfi (wajen bin umurnin Allah) da kuma basira”.[65] Suratu Sad: 45.

Sai kuma wata shubha ta ‘yan tawili wadda ta ke jingina wannan irin xanyen aiki na sauya ayoyin Allah zuwa ga xan Abbas, a inda Allah ya ke cewa:

﴿يَوْمَ يُكْشَفُ عَنْ سَاقٍ﴾ [القلم : 42]

 “Ranar da za a kuranye qwauri”. Al qalam: 42.

A tafsirinsa ga wannan aya Imamul Buhari ya ruwaito Hadisi ne daga Abu Sa’id Alkhuduri (RA) wanda yace ya ji Annabi (SAW) ya na cewa:

 “ubangijimu zai kuranye qwaurinsa, kuma daga nan ne muminai duka za su yi masa sujada. Sai abar waxanda ke yin sujada a duniya da nufin riya, idan suka tafi wurin yin sujada sai bayansu ya sandare”.[66]

Fassarar Ibnu Abbas anan ta zo ne kamar haka:

1- Al-hafiz Ibnu Kasir[67] ya hikaito daga Ibnu Abbas game da wannan aya cewa, rana ce ta tsanantar lamari da firgici da shiga cikin tsoro a wurin tsayuwa (Alqiyama)”.

2- A wata ruwaya, “wani lokaci ne da za a kuranye al’amari a kuma bayyana ayukka”.

3- Ruwaya ta uku ita ce, “Za a kuranye wani lamari babba”.

4- Ruwaya ta huxu, “Ita ce ranar tsayuwa, ranar da ake tsananin matsuwa da damuwa”.

Duk a cikin waxannan fassarori babu abin da ya ci karo da fassarar Annabi (SAW). Bayanai ne kawai masu sifaita ita wannan rana da ubangijinmu zai kuranye qwaurinsa, kuma ita rana ce babba, wadda ke cike da ban tsoro, da abubuwan firgita da damuwa.

Ga wani qarin haske akan ayar daga Abu Musa (RA) wanda ya ji Annabi (SAW) ya ce: “za a kuranye ne daga wani irin haske babba sai a faxi ana sujada gare shi”[68].

To, hanyar mabiya Sunnah anan ita ce, mun gaskata Manzon Allah game da abin da ya faxa. Mun yarda Allah Mai girma ya na da qwauri waxanda suka dace da irin zatinsa, masu haske da kwarjini, waxanda zai nuna mana ranar alqiyama, kuma mu surmuya mu yi sujada muna masu girmama shi. Ya Allah ka sanya mu a cikin waxanda kake cewa game da su a ranar nan:

﴿لَا يَحْزُنُهُمُ الْفَزَعُ الْأَكْبَرُ وَتَتَلَقَّاهُمُ الْمَلَائِكَةُ هَذَا يَوْمُكُمُ الَّذِي كُنْتُمْ تُوعَدُونَ﴾[الأنبياء:103].

“Firgita babba ba ta damar da su. Kuma Mala’ikku su na tarbonsu (su na cewa), wannan shine wuninku da ku ka kasance ana yi muku alqawali”. Suratul Anbiya’: 103.

Amma ka ga shi mai tawili anan zai ce maka, ni kam ina tsarkake Allah daga ace ya na da qwauri. Wannan sifar ‘yan adam ce. Sai mu ce masa, fara tsarkake tunaninka daga kamanta zatin Allah da na mutane, sai ka gano sifofinsa ba irin nasu ba ne. Kada ka qaryata Allah ga abin da ya faxa.

Kuma shi mai tawili ya qi tsayawa wuri guda. Don kuwa in cewa Allah ya na da qwauri ko hannu kamanta shi ne da halitta, to cewa ya na ji, ya na gani fa?. Shi ya sa Muwaffaquddini Ibnu qudamata Al-maqdisi (Allah ya yi masa rahama) yace, bayan da ya ambaci wasu sifofin Allah:

“Ire-iren waxannan sifofi da suka zo ta hanya ingantacciya, mu muna yin imani da su, bamu watsi da su, ba mu jayayya, ba zamu karkatar da bayyanannar ma’anarsu ba, kuma ba za mu misalta su ba da sifofin halittu. Haka kuma ba mu fassara su kamar yadda ‘yan bidi’a ke yi. Kuma muna sane cewa ba bu tamka ga Allah. Kamar yadda yace: “Wani abu bai zama tamkarsa ba, kuma shi ne mai ji, mai gani”. As-shura:11[69].

SHUBUHAR JAHA DA MUHALLI

Rashin lafiyar tawili ciwo ne da ya dabaibaye ‘yan bidi’a ta ko ina. Duk sadda aka kira xayansu zuwa ga imani da sifofin Allah da tabbatar masa da xaukaka akan Al’arshinsa xaukaka wadda ta dace da shi sai kaji sun ce, ana son ne a shata ma Allah jaha ko muhalli. Amsarsu a nan a taqaice ita ce kamar haka:

1. Mu ba mu gani ba a cikin Littafin Allah ko Sunnar Manzon Allah (SAW) in da wannan kalmomi su ka fito. Ya zamu tabbatar ma Allah ko mu kore masa abinda bai sanar da mu kome ba akansa? Magabatan musulmi ba su furta kome game da jaha ko muhalli ba. Don haka mu muna xari-xarin sakin waxannan lafuzza zuwa ga Allah ta hanyar korewa ko tabbatarwa[70].

2. Amma za mu tambaye ku, domin su waxannan lafuzza ana iya qudurta ma’ana mai kyawo ga resu, ana kuma iya qudurta marar kyau, ya danganta ga manufar mutum. To, ku me ku ke nufi da su? Idan kuna nufin sama ita ce jiha, to, Allah ya tabbatar ma kansa. In kunce Al’arshi shi ne muhalli, kuma ba mu ne muka faxa ba, mai sama ne ya faxa. Amma idan wani abu kuke nufi da jaha da muhalli baya ga waxannan, to, wannan rikicinku ne , kuma ba mu da hannu a ciki.

3. Babu rufa-rufa game da cewa, duk abinda gaskiya ta jawo shi ma gaskiya ne, kamar yadda yaye-yayen qarya duka qarya ne. Idan kuna ganin faxin gaskiyar Allah wadda shi ne ya faxe ta shi ke jawo tabbatar ma Allah jaha da muhalli, to, ku kai qara ga Allah don daga wurinsa ne gaskiyar ta fito. Mu a wurinmu da hankulanmu da naku duka ba su ne alqalai ba game da sha’anin ubangiji[71].

4. Kun ce mana tsarkake Allah ku ke yi daga muhalli da jaha don haka ne ba ku yarda yana sama ba. To, kuma kun ce yana ko’ina! Kash!. Ku kuma kun yi masa muhallai da jahohi kenan!! Wannan tumqa da warwara ba ku da maganinsa sai komawa ga maganar mahalicci da ajiye gajeren tunanenku gefe xaya.

Wata sabuwa kuma, su kan ce, to, idan kun ce Allah ya na bisa Al’arshi, to, kafin ya halicci Al’arshi fa ya na ina? Mu ma sai mu mai da muku wannan tambaya. Domin ba mu da banbanci a cikinta.

In kun ce, ya na nan in da ya ke tun daxai, tun kafin ma ya halicci Al’arshi. Sai mu ce, daga ina ku ka samo wannan? Shi dai Allah cewa yayyi:

﴿إِنَّ رَبَّكُمُ اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ﴾ [الأعراف : 54] [يونس : 3].

 “Lalle Allah ne Ubangijinku wanda ya halicci sammai da qassai a cikin kwana shida, sa’annan kuma ya xaukaka a kan Al’arshi”. Suratu Yunus: 3

Ashe xaukakarsa akan Al’arshi ta zo ne daga bisanin halitta abin ya faxa. Mun dawo dai har yau ba mu da amsar wannan tambaya. Kuma daman tambayar taku ce. Mu ba ruwanmu da wannan. Mun dai gaskata Allah ga abin da ya faxa. Allah ya tabbatar da mu akan shiriya.

LIMAMAN MANZHABOBI SUN BI SAHUN MAGABATA[72]

 Su ma manyan limaman mazhabobin nan manya guda huxu tuni sun bi sahun malaman da suka gabata wajen tabbatar ma Allah da sifofinsa kamar yadda suka zo a Alqur’ani da Sunnah. Ba a samu wani savanin ra’ayi ba tsakanin limaman guda hudu, Abu Hanifa, Maliku, Shafi’i, da kuma Ahmad (Allah ya sadar da su da rahamarsa baki xaya).

 Ga abin da Sheikh Muhammad Al-amin As-Shinqixi Allah ya yi masa rahama ya ke cewa a game da wannan:

“Mazhabar da ke kuvutar da mabiyanta daga masifar rikirkita ma’ana da kwatance kwatance, ita ce mazhabar malaman da suka gabaci wannan al’umma na daga cikin Sahabbai da qarnonin da aka yi ma shaidar alheri[73], da kuma limaman mazhabobi da dukkan malaman Hadisi. Babu shakka wannan ita ce gaskiyar da ba qura a lullube da ita, kuma hakan ya ratayu ne a kan nisantar abubuwa guda biyu: sune gurvata ma’ana (yana nufin tawili) da kuma kwatance-kwatance. Don haka dole ne a gane cewa dukkan sifar da Allah ya tabbatar wa kansa da ita ko sifar da manzonsa ya tabbatar masa da ita, to lalle wannan sifar ta tabbata a gare shi ta fuskar kammala girmansa da xaukakarsa ta yadda ba zata iya yin kama da sifofin bayi ba sam”. Kamar yadda Allah maxaukaki yace:

﴿وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ﴾[الإخلاص:4]

“Kuma babu xaya da ya kasance tamka a gare shi”.

 Suratu Ikhlas: 4[74].

 Imamu Abu Hanifa ya tsananta hukunci akan duk wanda ya musunta cewa Allah ya na sama, har ya kai ga kafirta shi. Dalilinsa kuwa shi ne, Al’arshi dai ya na sama, shi kuma Allah ya faxa mana ya na akansa a inda yace:

﴿الرَّحْمَنُ عَلَى الْعَرْشِ اسْتَوَى﴾ [طه:5].

“Mai rahama, ya xaukaka a kan Al-arshi”.[75].

 Suratu X.H.: 5

Shi kuma Imamu Malik cewa ya yi: “Tabbas Allah ya na a sama, kuma ilminsa ya kewaye ko’ina”[76].

 Shi kuma Imamus Shafi’i ga abin da yace: “Maganar Sunnah wadda ni ke a kanta kuma wadda naga malaman Hadisi irinsu Sufyanu da Maliku suke a kanta ita ce, tabbatar da cewa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma muhammadu manzon Allah ne, (haka ya ci gaba da jero aqidar har inda yace), “kuma Allah ya na a saman Al’arshinsa wanda ke a samaniyarsa, ya na kusantar bayinsa yadda yake so, kuma ya na saukowa zuwa ga samar duniya yadda ya so”[77].

Shi kam Ahmadu xan Hanbali har ma Littafi ya wallafa akan bayanin Aqidarsa irin ta Sahabbai da Tabi’ai, a ciki kuma ya tabbatar ma Allah sifofinsa a bisa yadda su ka dace da shi da girmansa. Sunan littafin nasa “Ar-Raddu Alal Jahamiyyah”.

A yayin da kuma xansa hambali[78] ya tambaye shi game da ayar da muka gabatar wadda Allah yace, “wata ganawa ta mutun uku ba za ta kasance ba face Allah shine na huxunsu” Suratul Mujadala: 7, sai Imamus Shafi’i yace: “Ana nufin ilminsa ya kewaye dukkan kome. Ubangijinmu kam yana a saman Al’arshi ba tare da iyakancewa ba ko sifaitawa[79].

BA MUTASHABIHI, BA MAJAZI A SIFOFIN ALLAH

 Abin da aka san ma’anarsa a fili shi ne “Muhkam”, wanda ma’anarsa ba ta filo qarara ba ana kiransa “Mutashabih”. Akwai tarin abubuwa waxanda Allah ne kawai ya ke da ilmi game da su, kamar sanin lokacin tsayuwar alqiyama da fitowar Dujjal da sanin tabbatacciyar fassarar harrufan da ke farkon wasu surorin Alqur’ani. Waxannan su ake kira Mutashabihi.[80]

“Majazi” shi kuma, wani lafazi ne da aka ajiye a wurin da ba na shi ba. Savanin “Haqiqa”, lafazin da aka ajiye a wurinsa. Misalin wannan shi ne, a kira mutum da sunan zaki saboda qarfinsa. Wannan Majazi ne. Zaki na ainihi shi ne “Haqiqa” in ji su.[81]

 Idan mu ka duba ma’anar Mutashabihi da Majazi da ta gabata, muna iya gane cewa, ba su dace a ayyana sifofin Allah mabuwayi da su ba. Ba shi ma a cikin ladabi mu ce Allah ya faxa mana abinda bai da ma’ana ko abin da aka xora shi a inda ba wurinsa ba.

Duk wanda yace, sifofin Allah Majazi ne kuwa, sai ya amsa tambaya, waxanne ne a cikin sifofin nasa ya xauka Majazi? Dukkan sifofin Allah ba su da ma’ana, tamkar yadda ba’ajame bai san ma’anar haruffan larabci ba? Duk sifofin Allah da su kazo cikin “Suratul Ikhlas” da farkon “Suratul Hadid” da qarshen “Suratul Hashri” da cikin “Ayatul Kursiyyi” da kuma cikin ayoyi masu ximbin yawa waxanda suka zo da bayanin sifofin Allah Mahalicci duk ba a sansu ba? ko ba su da ma’ana? Kenan ba a san ma’anar Allah ya na Ji, da Gani, da Magana, kuma ya na da Rayuwa, da qudura, da Irada ba da sauransu!. Wannan magana ba ta da wani magabaci na kirki da ya tava furta ta.

 Da yawa daga cikin malamai masu tantance ilmi sun mayar da martani game da wannan gurvataccen ra’ayi.

Misali a cikin ‘Alkashfu an manahijil adilla’ bayan da ya ambata wasu ayoyin alqur’ani game da sifofin Allah, Malam Ibnu Rushdi, Bamalike, cewa yayi:

“…da ire-iren waxannan ayoyi waxanda idan aka ce a yi masu tawili za a sauya Shari’ah dukkanta. Idan ko a ka ware wasu aka ambace su da sunan Mutashabihatu to dukkan Shari’ah za ta koma Mutashabiha, saboda dukkan shari’o’i sun tabbatar da cewa Allah ya na sama, kuma daga can ne wajensa mala’iku ke saukowa da wahayi zuwa ga Annabawa”[82].

Wani Malami shi ma Bamalike, Ibnu Abdil Barri, Allah ya rahamshe shi yace a cikin sharhinsa akan Muwaxxa ta Imamu Malik:

“Ahlus Sunnah dukkansu sun tabbatar ma Allah da sifofinsa waxanda suka zo cikin Alqur’ani da Sunnah, kuma sun yi imani da su hakanan yadda suka gansu a bisa haqiqaninsu, sai dai basu misalta kome daga cikinsu, kuma basu ware wata sifa ba suka yi mata iyaka. Amma su ‘yan bidi’a da jahamiyyah da mu’atazilah da kharijawa dukkansu sun musunta barin sifofin a haqiqaninsu kamar yadda suka zo”[83].

Sa’annan ya qara da cewa:

“…da za a biye musu akan ra’ayin cewa, wai sifofin Allah majazi ne da an kore dukkan sifofin Allah. Haqiqa Allah ya fi qarfin ya yi maganar da za a ce wai larabawa basu iya ganewa, musamman ga irin lafazin dukkan mai saurare ke iya ganewa. Lafazin Istiwa’i kam sananne ne ga harshen larabawa, shi ne xaukaka akan abu da tabbatuwa akansa”[84].

MALAMAI SUN MUSANTA CEWA ALLAH YA NA KO’INA

 Malamai ba su gushe ba suna musu tare da mayar da martani ga mugun ra’ayin Al’jaham xan Safwan mai cewa, wai Allah yana ko’ina tun a farkon bayyanar wannan ra’ayin.

 Dagag cikinsu kuwa akwai Alhafiz Abu Umar Xan Abdul bar Almaliki (463H), a cikin littafinsa At-tamhid sharhin Al-muwadda dai-dai Hadisi na takwas, Hadisin Xan shahab dagag Abi Salma daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi dagag Annabi Tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da sahabbansa da iyalansa ya ce: “a cikin kowane dare ubangijinmu yana saukowa zuwa ga sama’un duniya…” a nan ne malamin ya fayyace cewa: “malaman Hadisi ba su yi savani ba game da tabbaci da ingancin wannan Hadisi…” kuma a cikinsa a kwai dalili karara cewa Allah mai girma yana a saman bakwai ne a kan Al’arshisa, kamar dai yadda jama’a suka tabbatar. Kuma Hadisi ne hujja gare su a kan Jahamawa da Mu’utazilawa, dama su jahama wa su suka ce wai Allah ba shi a kan Al’arshi amma ya na a ko’ina[85]. Daga nan ne sai malamin ya ci gaba da gargado dalilaida hujjoji masu gamsar da cewa Allah ya xaukaka a Al’arshiya shimfida bayani mai faxi waxanda bai rage komai ba, Allah yayi masa sakayya da alheri haka kuma daga cikin malaman akwai Al-imamu Abu Muhammad Abdulkadir xan Abi Salih Aljili wanda ake jingina wa darikar kadiriyya (561H)[86]. A cikin Littafinsa ‘Algunya li dalibi darikil hak’ ya ce: “Allah ya na a jahar xaukaka ya xaukaka a Al’arshi, ya tattara mulkinsa, ya kewaye komai da ilminsa zuwa gare shi magana mai dadi ke hawa” Faxir:10. “yana shir a’’amari daga sama zuwa kasa, sa’annan ya taka zuwa gare shi a cikin yini, wanda gwargwadonsa shekaru dubu ne ga abinda kuke lissafawa” As-sjada;5. don haka baya halatta a sifaita shi da cewa yana ko’ina sai dai ace yana sama a kan Al’arshi kamar yadda yace: “mai rahama, ya xaukaka a kan Al’arshi” D.H:5. dai-daine kuma a ambaci cewa ya xaukaka ba tare da wani tawili ba wata xaukakawa ce ta zati a kan Al’arshi. Kuma cewa Allah subhanahu wa ta ala, ya kasance akan Al’arshi abu ne da aka ambace cikin dukkan littafan da Allah ya saukar ga Annabawan da ya aiko ba tare da wani kwatantawa ba[87]. Daga cikinsu kuma akwai Shehu Islam Abul Abbas Ibnu Taimiyya Allah ya yi masa rahama (728) ya ce: “duk wanda ya furta cewa, Allah da zatinsa ya na ako’ina, babu shakka ya saba ma Littafin Allah da Sunnah da ijima’in malaman da na gabaci wannan al’umma[88]. Kamar yadda maganar sa ta saba ma tunanin da Allaha ya halitta bayi a kansa don bautarsa, haka kuma ya sabama tataccen hankali. Sai Alhafiz Xan Kasir Allah ya yi masa rahama (774H) bari inkawo ma abin da ya faxi a cikin tafsirinsa inda Allah ya ce: “kuma shi ne Allah a cikin sammai kuma a cikin qassai yana sanin asirinku da bayyanenku, kuma yana sanin abinda kuke yina tsirfa” Al-anam:3. a nan sai lmalam yace: malamai sun yi muhawara game da fassarar wannan aya bayan sun yi itikaki ga yima jahamiyyawa musun maganarsu mai muni ga Allah tsarki ya tabbatar masa cewa wai yana a ko’ina wanda a ganinsu abin da ayar ke nuni da shi ke nan. Iingantacciyar fassarar ayayr kam, inji shi itace kamar haka: “Allah shi ne wanda abin roko a cikin sararin sammai da qassai, dukkan bayinsa dake sama da kasa shine abin kadaitarwa da bauta gare su shi ne Allahnsu da suke roko a cikin halin samu da rashi in banda wanda ya kafirta a cikin aljannu da mutane” a hakan wannan ayarta yi kama da ayar da a cikinta Allah yace: “kuma shi ne wanda ke abin bautawa a sama, kuma abin bautawa a kasa” Az-zukhruf:84. abin nufi shine Allah shine abin bautar halittun dake a cikin sama’u kuma abin bautar halittun da ke cikin kasa shi yasa a waccan ayar yace: “yana sanin asirinku da bayyanenku” ko ta wane hali ke nan[89].

Fassara ta biyu itace: ayar ta na nufin cewa: “Allah shi ne wanda ya san dukkan abinda ke cikin sammai da qassai game da abubuwa dake asirce da bayyana, don haka maganar sa da yace yana sanin alika ta da inda yace cikin sammai kuma da cikin kasa, kuma yana sanin abin da kuke yi na tsirfa.

Magana ta uku: kuma a cikin kasa yana sanin asirinku da bayyanenku, wannan fassara itace zabin Xan Jarir[90].

 LIQA MA MAGABATA TAJSIMI DA TASHBIHI

BA SABUWAR QARYA CE

Daga cikin dadaddiyar cutar ‘yan tawili itace, sun dade suna jifar malaman Hadisi da na Sunnah da cewa wai su masu kwatanta Allah ne (mushabbaha) kuma masu jingina jki ne ga Allah (Mujassama). Alhali su malaman Sunnah suna qoqarin yin uzuri a gare su kamar dai karin maganar nan da ake cewa “jefar ni da dutsi in jefe ka da kan dawo”.

Ma’abuta tawili sun bada kaimi kwarai wajen jingina qarya da kazzuffa ga malaman Hadisi da Sunnah. Shi ya sa Alhafiz Abu Umar Xan Abdul-barr Almaliki, Allah ya yi masa rahama ya fayyace cewa: “duk AhlusSunnah sun tabbatar ma Allah da sifofinsa waxanda suka tusgo cikin Alku’ani da Sunnah sunyi Imani da dukkansu, kamar yadda suka taho a haqiqani, sai dai basu kwatanta komai daga cikin sifofin kuma na ruwansu da iyakance wa ga sifar. Amma su ‘yan bidi’a da jahamiyyawa da mu’utazilawa da hawarijawa har ko yaushe sun kasance ne suna musu kuma ba su yarda da sifofin kamar yaddda suka zo a haqiqaninsu har ma suna zargin wanda ya tabbatar da sifofin kamar yadda suka zo da cewa wai mushabbihi ne, kuma suna zaton cewa hakan da suke yi suna ba Allah kariya ne”. Gaskiya yar lamari shine abinda jama’a da shugabannin Sunnar da suka gabata wannan an al’umma suka tafi akansa. Godiya ta tabbata ga Allah[91]. Bari mu kawo misali da wata qarya wadda wani gwarzon yawon shakatawa Xan Baduda ya fesa Shehun Musulumci Ibnu Taimiyya, ga yadda yace: “wata ranan ina a Damashka (siriya) sai na isko shi a ranar juma’a akan mumbari ya na ta yi musu wa’azi har ya kai ga ce musu: Allah ya na saukowane zuwa sama’un duniya kamar yadda ku ka ga ina saukowa daga wannan minbari sai ya rinka saukowa akan mtakan minbari[92]. Ni kuwa sai na ce wannan qarya kam mun tone ta, domin kamin ya yi wannan magana a cikin Littafin ya faxi cewa ya isa ne a Damashka a ranar Alhamis tara ga watan ramadan a she kara ta dari bakwai da ishirin bayan hijira 9/9/720H shi kuwa[93] Ibnu Taimiyya yana tsare a kurkuku tun ranar 22/7/720 na hijira kuma ba a sake shi ba sai ranar 10/1/721H[94]. wannan ya nuna cewa ranar da xan baduda ya ce ya ga Ibnu Taimiyya akan minbari ranar tara ga azumi ramalan ba gaskiya bane domin a dai-dai wannan ranar Ibnu Taimiyyaya na da kwana 47 cur a gidan kaso. To a mimbarin gidan wa ya ganshi ya na huxuba da a cikinta ya misalta saukowar Allah da saukarsa daga kan mimbari? Kuma wani abin mamaki shine wannan qiren qaryar da aka jingina ga Ibnu Taimiyya ta kwatanta Allah tashbihi shi ne abin da Ibnu Taimiyya ya yi faxa da shi har iyakar tsawon rayuwarsa, duk mai karatun Littafin Ibnu Taimiyya da basira zai shedi,haka misali a nan shi ne a cikin risalarsa zuwa ga jama’ar tadmur da ‘Alfatawal Hamawiyya da Al’Aqidatul wasidiyya’ da dai sauran littafansa Allah ya yi masa rahama ga abin da ya ke cewa a cikin farkon Littafinsa, Al’Aqidatul wasidiyya. Yana daga cikin yin imani da Allah a yarda da sifofin Allah waxanda ya sifaita kansa da su cikin littafansa a kuma kamar yadda manzonsa Muhamma (SAW) ya sifaita shi ba tare da kar katar da ma’anar ko bata ta ba, kuma ba tare da kwatantawa ko misaltawa ba[95]. A’a du dai ahlusSunnah wal jama’a suna imanine da cewa shi Allah: “wani abu bai zama kamar tamkarsa ba kuma shi mai ji ne mai gani” Asshu’ura:11. Ba su kore ma Allah sifofin da ya sifaita kansa da su ba su karkatar da magana daga bagirenta basu kutsawa cikin sunaye da ayoyin Allah su kamanta Allah, ba su misalta sifofinsa da sifofin halitarsa, domin shi Allah mai tsarki babu kama ga sunansa ba shi da tamka ba shi da kishiya kuma ba a kiyasta shi da halittarsa[96]. Haka kuma lika ma jama’ar salafiyya attajsim, watau Aqidar yima Allah jiki, duk wannan labarin cin kanzon kurege ne qarya ce wadda aka dade ana sheka ta ga shehun musulunci Ibnu Taimiyya, da Abu isma’ila al harawi al’ansari Allah ya yi musu rahama, wannan shi ne abin da Alhafiz Az-Zahabi ya tabbatr a cikin Tazkiratul Huffaz[97]. Sharrin yan bidi’a da kimlimbibinsu ya kai ga wata ranansuka malmula wani gumki karami da tagalla suka kai a karshen dardumar da Ibnu Taimiyya ke salla suka turbude, daga na suka kai kararsa ga suldan Alab Arrislan cewa a tuhumi Ibnu Taimiyya domin ya na bautar gumukkane ya na raya cewa irin wannan surar ta gunkin ita ce ga Allah baya da shi sultan ya yi bin cike sai ya gano cewa qarya ce da sharri a ka kulla ma sheikh shi bai san da sun turbude wannan gunki a karkashin dardumar sa ba a nan ne shehun musulunci ya jayo cikin farin ciki da falalar ni’imar Allah babu abinda ya same shi su kuma yan bidi’a mafaryata suka dawo cike da kyacewar dawo cike kyacewar sarki Allah sannan da fushi tare da gintsewar sultan.

AQIDAR IMAMU ABUL-HASSAN AL’ASH’ARI[98]

Malaman tarihi dukkan su sun tabbatar da cewa, shi imamu Abul Hassan Aliyu xan Isma’il Al’ash’ari almajiri ne ga Abu Ali Al-juba’i limamin mu’uta zilawa – shi ya auri uwarsa wanda daga nan ne ys koyi ilmin falsafa har ya zurfafa daga baya kuma sai Allah yayi masa budi na alheri inda ya ganar da shi gaskiya sai ya gano ga hanayar da mazhabar malamain Hadisi har ya kalubalanci malaman na sa da hujjoji daga Alqur’ani mai girma har yau game da shi, asheikh Muhibuddin Al’khadib yace: “ tun a farko ya taso ne akan mu’utazilanci wajen Al-juba’i daga nan sai Allah ya falkar da shi a dai-dai lokacin da yake cikin samartakarsa dai-dai shekarar 403H A wannan lokaci ne ya yi shelar dawowarsa daga rakioyar mu’utazilawa, sannan ya bude ma kansa sabon shafin rayuwar addini akan Aqidar ingatacciya, yana mai cike da nishadi a cikin nazarce-nazarce da rubuce-ruuce tre da bayar da darussa ya na mayar da martani ga gungun mu’utazilawa ya kamo ma tafarkin magabata, kubutacce daga kowanre irn jidali da tawili wannan shi ne abinda ya zaba wa kansa har zuwa karshen rayuwarsa, yaci gabada tabbatar ma Allah dukkan abin da ya tabbatar wa kansa na daga sifofi da sauran abubuwan gaibi waxanda ya zama wajibi akan bawa da yayi imani da su kawai ba tare da jayayya ba.

A nna ne ya wallafa littafi game da hakan, kamar Littafinsa mai suna Al’ibana wanda yanzu hakan ya yadua hannnuan musulmin duniya harma malamai sun badatavacin cewawannan Littafin sa shi ne Littafin na karshe wanda wanda ya rubuta, (Dubi tarjamarsa a Shazaratuzzahab).

Don haka duk abinda aka jingina gare shi na Aqidar ash’ariyya Abul-hassan Al-ash’ari ya riga ya wanke kansa ta hanayar bayanin da yayi na dawowa da rakiyar masu tawili a ckin Littafisa na Al’ibana[99].

Malamai da dama sun daba shedar dawowar Imamu abul-hassan Al-ash’ari zuwa ga Aqidar malamanda suka gabata, daga cikinsu akwai Al-makrizi wanda ya bayyana hakan a Littafin sa al’kadad[100]. Haka kuma, Alallama Ahmad xan Muhammad Addihlawi shima ya faxi makamancin hakan a cikin Littafinsa tarikhu Allil hadis[101]. A nan wanda duk ke son ya san matsayar imamu Abul-hassan Al-ash’ari da mazahabarsa ta karshe, sai ya duni bayninsa na cikin Al’xana inda yake cewa: “Raarrabewa ga bayanin mabiya sunana ma’abuta gaskiya” idan wani yace, tunda kun musulunta maganar mu’utazilawada Alkadariyya da Aljahamiyya da Aljaruriyya da Rafilawa (yan shi’a) da Murji’awa, to ku gaya muna takumagana wadda ku ke biyar addiniku da ita, amsa itace: mu maganar da muke rikon addininmu da ita itace maganar ubangijimu da Sunnar annabinmu da fassarar Sahabbai da Tabi’ai da limaman Hadisi, da wannan muke riko… kuma tabbas Allah ya xaukaka a saman Al’arshi, saboda shi yace: (mai rahama ya xaukaka a saman Al’arshi) idan kuma wani yace: mi za ku c eke nan game da AlIstiwa’i? Amsarsa itace kamar haka: lalle tabbas Allah ya xaukaka asaman Al’arshinsa[102].

 AQIDAR SHEHU USMAN XAN FODIO

 Duk wanda ya ratsi Littafin Shehu usman fodiyo, Allah ya yi masa rahama, dole ne ya san yadda shi shehun ke nuna matukar kamna ga manzon Allah (SAW) kuma zai fahinci yadda xan fodiyo ke biyyar Sunnarsa tare da girmamawa ga sahabban bai da tabi’ar[103]. Ainda ya nun acewa,ita Aqida wajibi ne a dauko ta daga Littafin Allah da Sunnah kuma maganar da ya yawaita faxinta na cewa: “wannan addini an gina shi ne bisa ga basira” da kuma yawan maimaita faxin. Alhairi duka ya rataya ga biya, shi kuma sharri ya tattarau ga bidi’a.

 Ga kuma abinda yace a wani waje: ”daga cikin alamomin mabi Sunnar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da iyalansa da sahabbansa, itace yin imani ga dukkan abinda manzon ya zo dashi da yi masa da’a da lizamtar nuna kamna da koyi da halayensa tare da bibiyar ayukka da bayanansu”[104].ya kuma ciranta daga xanul hajji yana cewa: “idan har ka fahimci hakan, to ya zama wajibi gareka kabi Littafida Sunnah da Sahabbai da Tabi’ai da na ba yansu da biyar tafarkinsu na Sunnah don sune mutanen da manzon Allah yayi ma shedar ta alheri sai mu aikata abin da suka aikata mu kuma yi watsi da abinda ba su yi ba. Wajibi ne ga mai lalaben tafarkin tsira ya yi bincike game da tarihinsu da halayensu. ya kuma yi tsukaci ga bayanai da ayukansu, ya kafa idanunsa ga resu don ya samu damar bin abinda su ke bi ya juya baya ga abinda masu kirkiresuka kirkiro bayan shudewarsu,da zaran ya ga wani sabon abu y ace, da yinsa alheri ne da sun riga yemu yinsa, babu shakka duk wanda ya shiga hanyarsuzai isa inda suka kai amma wanda duk ya karkace hanyarsu, sai muce masa tafi can”[105]. Allah ya haskaka zuciyarsa da basirarsa, Malam Alfakihani ya kai matuka wajen nuna zuwa ga rikoga Sunnah da shiriyar malaman farko a inda yace: “mun sani cewa, Annabi mai tsira da aminci; bai mutuba sai bayan ya shimfida addini ya yi bayani cikakke game da shi, ya kafa ginshikayensa da bayananin ka’idoji da rukunnasa duka da bayani a kansu filla-filla. Duk abin da ake nema na bayai game da hukunce-hukunce guda biyar said a ya yi shi haka kuma game da tafsirin Littafin Allah maxaukaki sarki da Sunnar manzosa da kuma ta Sahabbai. Dukabinda ke kunshe a cikin Littafi ko Sunnah ko abinda malamanfarko daga cikin Sahabbai suka aikata shine, abinda Allah ke son mu yi addini da shi, kuma duk abinda ya saba masa ya zama bidi’a da bacewa domin da wannan abin alheri ne da manzon Allah mai tsira da aminci, ya yi muna bayaninsa, domin yawan kawadayinsa ga nasiha ga al’ummada son alheri ga remu Allah ya saka masa da mafi ficin alherin da ake sakawa annabawa da shi, kuma ya sanya mu daga cikin al’ummarsa wadda ke biya ga Sunnarsa harmu zama cikin gungun jama’arsa da fallalar Allah tare da ni’imarsa. A karshen wannan jawabi ne Shehu ya ce: wanna Magana ce mai kyawo ainun kuma ta ishi duk wani shiryayye[106].

 Bayan irin wadanan bayanai ba zai yiwu ba misilta a zuciyar mu cewa: Shehu Usman xan Fodiyo ya karkace daga tafarkin waxannan malaman farko managarta zuwa ga wani sansanin yan bidi’a. sai dai abin da ya dace mu sani a nan shine, littafan dake a hannu Shehu masa magna akan wannan babi da yawansu akwai falsafa cikin su domin sau da yawa zaka ji ya na ciro bayanai dagag cikin sharhin Sanusi da kuma Al-lakani a ittihaful murid haka kuma daga Al-hassanul yasi Al-mukhadarat, da Ahmad xan Zakari Mahsalul-Mukasidi da Al-manjuri a sahrhinsa na Littafin daya gabata, da Ad dagugi, a shafi yatul kulub da Al-jawari’i a Aqidatul Muwahiddin da Al-wansharibi a Al-mi’iyarul mu’urab da kuma Abdul-wahab. As’sha’arani a Al-kawa’idul kashiyya da sauran irin waxannan malaman da suka zo daga bayawaxanda suka arosalon fahimtar tauhidi ga malaman falsafa.[107]

 Amma kuma duk mutum mai adalci yidan ya yi la’akari da irin bayanin da shi Shehu ke bijirowa dasu a bayan irin waxannan wurare zai gamsu cewa shi bai ba fassarorin falsafa muhimmmanci ba dubi misalign ta’alikin da ya zo da shi bayan ya kawo maganar Sanusi ta cikin Al-umda sharhin kubra, inda yace: “ abin da ya zama waji bi ga al’umma shi net a san ma’anonin tushen addini ta hanyar nasosshinLittafi da Sunnah ba ta hanyar ilmin kalami (falsafa ba)[108].

 Sauda ya yawa za ka same shi a wurare daban dabam yana lizamtar da yin hukunci da Littafin Allah da Sunnah game da masa’alolin sifaita ba ya kulawa da amfani da hankali kawai ko falsafa: dubio misali a inda ya ke cewa: mas’ala: mutane da yawa sun kutsa kansu cikin falsafa game da ayoyi Almuta shabihat da masu Magana game da sifofin Allah suna fassararsu da hankalinsu sun bace kuma sun batar da mutane, a abinda ya fi dace wag are su shi ne su kyautata ladabi ga Allah ta’ala da manzonsa mai tsira da aminci, su kawo bayani ayoyin kamar yadda suka zo daga wajen Allah maxaukakin sarki domi babu wanda a kaji ya yi tawilin waxannan ayoyi daga cikin malaman farko don haka yi musu ta wili a yanzu munana ladabi ne ga Allah mabuwayi kamar yadda yin hakan yana kawo cikas ga bayyana haqiqani abin da Shari’a ta kunsa ta hanayar tawili abin da yake gaskiya shi ne malami ya fito fili karara ya haskaka zukata bayinn Allah yabi da su ta hanyar da zasu agirmama Allah hara cikin birnin zuciyarsu[109].

 Daga nana sai malam, Allah ya lullube shi da rahamarsa ya ci gaba da cewa: Mas’ala: Ba abin suka bane jingina ma Allah kasancewa sama ga komi, domin ayoyi masu yawa da hadisai sun bijiro da wannan bayani, abin suka shine mutun ya kadurta hakan ba tare da tsarkake Allah ba[110]. A karshe sai ya rufe da cewa: Duk lafazin da Shari’a ta jingina ma Allah shi, muma za mu jingina masa abinda kuwa ba ta jingina masa ba babu ruwannu da shi abinda malaman Sunnah suka bayyana[111].

 To wannan shi ne yasa muka samu tabbacin cewa lalle wannan babban mujaddadi yana tare da mazhabar malaman farko Allah ya yarda dasu.

AQIDAR SHEHU AHMAD TIJJAN

 TSOKACI GAME DA SABUWAR QASIDA

 Koda yake, ban so in ce komi ba game da wata takardar kasida wadda wasu yan’uwa suka rubuta daga makarantar Sheikh Muhammad Mujtava Gyalgyal wadda ke dauke da sunan Sheikh Muhammad Bello xan Muhammad xan Umar qofar Atiku, mai take kamar haka fadakar da mumini cewa Allah bai da muhalli. A cikin wannan bincike nawa na so in kame baki ainun game da wasu bayanai dake cikin takardar don kaucema masu son biyar son zuciya yan Karin gishiri gudun kar su yi amfani da wata dama su bunkasa mummunar kasuwancinsu na bata sahu da dillancin yada kiyayya a tsakanin malamai.

 Daga baya sai na lura cewa kuma ya zama tilas in tunatar da makaranta wasu abubuwa da suka zama dole a tunatar da game dasu waxanda suka bayyana a cikin kasidar yin hakan kuma bai zama ketawa ba ga alfarmar ka’idojin bincike da amanar ilmi. Baslantana ma game da irin sain da na yiwa dan’uwa Sheikh Muhammad Bello da abokanin karatunsawaxanda suke a sani na masu tsananin kwadayine a fagen laluben gaskiya da tsayuwa a kanta masu Magana suna cewa: gaskiya ina laifin ki? Haka kamar ina sane da abinda na riga na gabatara cikin wannan bincike ya isa ya gamsu d duk wanda Allah ya haskaka zuciyar sa amma da yake ance: “ko kana da kyawo ka kara da wanka” sai na fahinci cewa, biciken zai kara yin armashi idan na yi masa marufi da fadakarwa game da wasu sassa na cikin kasidar da bayanin ta ya gabata, kamar haka:

 Wuri na farko:

 Inda aka bude shafin kasidar da wani Hadisi wanda suka iza ga Imamul Baihaki kuma aka yanke ma Hadisin dayen hukuncin da cewa karbabbe ne, al hali kuwa Hadisin na Almikdam xan Ma’adi yakrib ne Allah ya yarda dashi, Hadisi yana cewa “idan kuna ba mutane labari (game da ubangijisu) ka da ku faxi abinda da ke tada hankalinsu[112], kuma ya wahalar da su” wannan Hadisi laifi ne (mai rauni) baya halatta a kafa hujja da shi balantana ma a iya jingina shi ga mason Allah tsira da amincin su tabbata a gare shi. Da iyalansa, Hadisi ya na daga cikin ruwayoyin dailami waxanda suke a cikin musnadul-firdausi 1/1/107 kuma ya tusgo a cikin firdausi akhabar lamba ta 1031 da Xan Addi a Littafin sa Alkamil fid du’afa’i 7/80 da Abul Hassan Al kazirina a Mijlisun minal amali (2/198) da Al harawi a zammul kalam 3/81.

 Hadisin kuma yana da illoli buyu daya da ga ciki itace game da Alwalid xan Kamil Albalji wanda ke cikin sarkar Hadisin a game da shi, imam Azzahabi a cikin Almizan[113], yace: Abul fath Al’azdi ya raunana shi, haka kuma kamin shi a kwai Abu hatim wanda ImamulBuhari yace, a kwai mamaki ya lamarinsa a cikin Attahazib, Alhafiz Ibnu Hajar ya ce (Alwalid) ya na ruwaito hadisai masu katsatsin isnadi Xan Alkaddan yace: bai da cikakken adalci[114].

 Illa tabiyu itace ruwayar almajirinsa Bakiyyatu xan Al-walid daga shi Al-walid din weanda ga sanshi da tadalinsul taswiya mafi sharrin tadalibi, wandahar ma malamai sun ce, hadisan bakiyya duka ba su da tsabta a yi hattara da su[115]. Sannan kuma ruwayoyin dalilami na cikin musnadu firdausi da na xan Addi cikin kitabud du’afa’i da ire-irensu an rigaya ansansu da rauni harma imamu Jaluddin Assayudi Allah ya ya yi masa rahama ya yanke cewa, iza Hadisi gare su kadai ya isa a fahimci raunin shi a cikin Al-jami’ul kabir kuwaga abinda ya cea inda ya ke bayani game dqa alamomi ga littafan da ake iza Hadisi a cikin su kamar haka: idan ina nufin jingina Hadisi ga ukuili a Littafin Addu’afa’u sai in ce (uk) xan Addi a Al-amil (DA), Alkhadib (HD) idan a cikin tarihinsa ne idan kuwa ba haka bane zanyi bayani idan daga xan Asakiru ne cikin tarihinsa (KR) dukkan Hadisin da na tara a waxannan wurare guda hudu gami da wandana iza ga hakim Altirmizi cikin (Nawudirul Usuli) ko a cikin tarihin na Ahakim ko cikin masnadul firdausi na Dailami daka Hadisi ne la’ifi mai rauni da zaran ka ga na ciro Hadisi daga waxannan wurare, kada ka jira sai ance ma Hadisin bai ingantava[116].

 Kaga idan ka dora wannan Hadisin da yan’uwa suka bude shafin kasidarsu da shi akan waxannan ma’aunayye na masana kimiyyar Hadisi zaka ka gano kuskuren a fili na cewa wai Hadisi ne karbabbea madadin mai rauni yar babbe. Amma fa duk da haka ina sara ma marubuta kasidar domin ko ratsa Littafin da suka yi har suka kinkimo wannan Hadisi suka dasa cikin kasidar hakan yayi amfani. Sai dai kuma mi zamu iya fahimta daga cikin Hadisin idan ma a ce yana da inganci? Shi Hadisin yana karantar da cewa ne kada mu karantar da mutane abinda ya fito daga Allah da manzonsa tsita da amincin Allah su tabbata a gare shida iyalansa da sahabbansa, game da bayani sifofin Allah maxaukakikin sarki? To idan har lamarin ya zama haka awajen wa zamau karbi bayanin ma’anonin waxannan sifofi matukar muka bar Allah da manzonsa? Zai yiyu ace bayanin da ya fito daga Allah da manzonsa (SAW), shi zai firgita hankali ko ya zama wani tsanani? A ina tsananin yake? Kuma wa zai firgita in ba wanda yake falsafarilmin kalami ya riga ya radashi ba.

WURI NA BIYU:

 Bayan sun bijiro da wannan Hadisi sai suka ci gaba da cewa, da kuma iyalansa da sahabbansa waxanda da suka yi da’a ga Allah da manzonsa masu aiki da abin da ya zo cikin saukakakken Littafinsa mai kunshe da bayani masu kame bakin su ga ayoyin sifofin cikinsa (masu rikitarwa) masu kama da juna da kuma waxanda suka zo bayansu suka bi sahunsu na kame baki suna masu tawili ga sifofin Allah don tsarkake shi ga dace da shi ba na sifofin halittu. Ina ganin akwai kurakurai bartkatar acikin wannan jumla ailmance, na daya: misaltawa da suka yi ga ayoyi masu bayanin sifofin Allah da cewa mutashabihati ne (masu kama da juna), masu rikitarwa to idan har haka ne, ina Al-muhkamat, (ayoyi bayyanannu) suke idan har sifofin Allah sun kasance mutashabihai? Ai (sune mafi yawan littafin domin ba ka samun surar da ba ambaci sifar Allah ba a cikinta.

 Babban misali a nan shi ne, dukkan farkon surori dari da ishirin da hudu na cikin Alqur’ani an bude su da ‘Bismillahir Rahamanir Rahim’ (da sunan Allah mai rahama mai jimkai)in ban da Suratul tauba do haka, bisimilla itama ta na kunshe ne da sifar Allah maxaukakin sarki, wannan shi ne ya sa xan Rushd yake cewa: “idan a ka ce a za’ayi tawilin ayoyin sifatu, to dukkan Shari’a sai an yi tawilinta idan kuma aka ce wai a ayoyin sun fada cikin Al-mutashabihatu (masu kama da juna) masu rikitarwa, to dukkan Shari’ar ta zama haka nan sabo da dukkan shari’o’i sun yi ittifaki game da cewa Allah yana a sama kuma daga wajensa ne, mala’ukuke saukowa annabawa da wahayi[117].

NA BIYU:

 Sun jingina Sahabbai, Allah ya yarda dasu zuwa ga tafwili (kame baki) kuma ma’anar tafwili ta gabata gare ka a cikin wannan littafi wanda ke nua cewa Sahabbai sun jahilci mafi muhimman abu game da lamarin addini shi ne sanin Allah maxaukakin sarki da sifofinsa da sunayensa wanda bai dace ace an jingina Sahabbai da sauran magabata da irin wanna mugun abu ba, bayan kuwa sune suka fito da fassarar sifofin Allah maxaukakin sarki waxanda aka sanshi da su kuma bayan ya gabata gare ka dalla-dalla a babi mai bayani game da banbanci tsakanin tafwili da barin misalta Allah na cikin wannan Littafi, bayani malamai magabata ya wadace ka a can wanda kuma ked a bukatar fadada nazarinsa game da wanna sai ya leka Littafin Azzahabi ‘Al’uluwilil Aliyul Gaffar’ da Littafin Albaihaki ‘Al’asma’u wassifal’ da ire-irensu na daga cikin Littafin malaman Hadisi, ko kuma ma ya buda kitabul Tauhidi a cikin sahihul Buhari da Littafin Al’i’itisam bisSunnah duk daga cikinsa zai samu gamsuwa in Allah yaso.

NA UKU:

 Sur kuma rarraba tabi’ar zuwa gida biyu da masu tafwili (kame baki) da masu tawili, abinda wannan ke nunawa shi ne, ashe su Tabi’ai basu gamsu ba da mazhabar Sahabbai yardar Allah ta tabbata a gare su game da bayanin sifofin Allah maxaukakin sarki a mai makon hakan sun makirkiro ma kansu wata sabuwar mazhaba suka kara da ita don kowannesu ya zabi id yake son bi sai yabi Allah ya tsaresu da yin haka!

 Ya ya ake kwatanta waxannan mafiya alherin karnuka da ina wanna kazamin aikina jefa savani a cikin babbar mas’ala ta tauhidi ko alama mu abin da muka sani shi ne su Tabi’ai masu riko ne da nassoshi tabbatattu a cikin Littafin da Sunnah, kuma sam, basu tava karkacewa a kansa ba ko da misalign dan yatsa, su basu san wani abu ba da ake kira falsafa a zamaninsukuma su ba su tava jahiltar ma’anoni ba balantana har suyi tafwili kuma babu abin da ya rikitasu bale ace sun yi tawili, Allah ya yi masu rahama.

WURI NA UKU:

 Shi ne, inda suka katsao Maganar zarka shi a cikin Littafin sa Al-burhan shi kuma ga abinda y ace: ‘ mutane sun yi savani game da (sifar Allah waddata zo) cikin ayoyi da hadisai harsun rabu zuwa gida uku:

NA DAYA:

 Cewa kada ayi tawilin komi abar ta (sifar Allah) kamar yadda ta zo karar, wannan juma’a su ne ake kira Almutashabiha[118].

NA BIYU:

 A na iya yi mata tawili sai dai barinsa shi yafi saboda mutsarkake Aqidarmu daga yin tashbihi (misaltawa) da ta’adili (bata ma’ana)sai muce: babu wanda ya san ma’anarta sai Allah wannan ita ce maganar malaman farko (Assalaf)[119].

NA UKU:

 A na yi mata tawili amma irin tawili wanda ya dace da shi[120], sai kuma ya ce: Magana ta farko dai batacciya ce, amma na karshe duka an samo su ne daga Sahabbai. A nan ne masu kasidar suka takaita maganar Azzarkashi sai suka dora tubalin kasidarsu bisa ga bayaninsa suka ce, a kan wanna Magana ta Azzarkashi, da waxanda suka rigaye shi cikin malamai muka fahimci cewa malaman Sunnah sun rabu zuwa hanaya biyu ingantaciiya kamar haka: Ta farko, hanyar tafwili da ta tawili amma ita ta farko bata da kyawo watau ita ce wadda suka zana wa suna da hanyar masu tashbihi. Ni kuma sai n ace,ai shi malam zarkashi ba shi da ga cikin malaman farko, ya rayune a karshen karni na takwas ya rasu a shekararhijira ta 794H tambaya a nan ita ce waxannan malamai ne suka rigaye shi kuma suka yi dai-dai da si ga wannan ra’ayi na karkasa musulmi zuwa waxannan rabe rabe? Ku kawo muna ko da sunann malami guda ne.

 Haka dai suka bi malam Zarkashi a kan wanna ra’ayi har ma suka ce: wai uwar mumunai Ummu Salma Allah ya yarda da ita da shugabanni da kuma Auza’i da Is-haqa xan Rahawaihi da Maliku, Allah ya yi masa rahama wai duk suna cikin masu yin Tafwili kamar yadda suka sanya Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, a cikin wannan layi.

 A vangaren malamai masu tawili kuwa suka ce, akwai Abdullahi xan Abbas (RA) da Imamu maliku qila sun manta da cewa tuni sun riga sun saka Imamu maliki (RA) a cikin rukunin masu tafsiri tun a farko. Suka qara da cewa, limamai kamar su Ahmad xan hambali Sufyanus-sauri, Abdul-Hussan Al’ashari, Imamul Buhari, Tirmizi, Xan maja da Sheikh Muhammad nasiruddin Albani wai, a lokaci guda suna tafwili da tawili!!.

 Ni kuwa ban san yadda zai yiwu ba a ce jahiltar wani abu da saninshi su zauna cikin zuciyar mutum xaya a lokaci guda!!! Daga nanne suka bada misali da Shehu Usman xan Fodiyo (RA) game da wannan matsayi.

 A nan ne gizo ya yi saqa, domin kuwa a cikin qasidar ta su duka, dai-dai wannan wurine kuskure ya yi kaka-gida wanda tun farko wannan bincike gyara akan hakan ya wakana ga abinda suka ce:

 SHASHE NA HUXU:

 Malaman musulunci sun kasu ne zuwa gida biyu kacokan; da masu tafwili da masu Tawili duk wanda bai shigo cikin waxannan kashi guda biyu ba to ya faxa cikin gungun mujassama. Wannan magana ba bata da gaba balantana baya, domin kuwa mun sancewa shi Tafwili da Tawili basu bayyana ba cikin garuruwan musulmi sai a cikin qarni na uku, a dai-dai lokacin bukin haihuwar falsafar girkawa wadda ta yaxu a duniya. To idan kuwa haka ne za mu ji labarin haqiqani aqidar musulmi kami zuwan wannan likaci na bayyanar falsafar girka, shi ta ina uwar muminai Ummu Salma (RA) da Abdullahi xan Abbas (RA) suka gamu da wannan falsafa har suka samu lambar ta fito a cikin rukunin da kasance a cikinsa?.

 A wajen wane ne suka karanto wannan falsafa wadda ke Littafin Allah da Sunnar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agr shi da iyalansa?

 Malam auzai da maliku da Ahmad duka almajiran malaman falsafa ne? don haka akoma a yi nazarin sake lalen wannan karkasa malamai gida biyu da aka yi karfin halin yi.

SASHE NA BIYAR:

 Shi kuwa game da gefen hujja ne, a inda suka ba maganar magabata fassarar da ba ta dace da ajingina ga re su ba wanda suke xauka cewa wannan shi ne tsarkaka wa mafi dacewa ga zatin Allah mai girma ga misali:

Na xaya:

 A inda suka jingina ma Uwar Muminai Ummu Salma (RA) cewa ta kasance, cikin masu yin tafwili ba su kawo ruwayoyin da za a iya gaskata su ga tuhumarsu ba sai magana guda wadda suka ce Zarkashi ya ce: an karvo cewa Ummu Salma (RA) ta kame bakinta ga maganar da akatambaye ta game da Istiwa’i (xaukaka) a inda ta yi farat ta amsa da cewa: “xaukaka abu ne sananne amma ba a san yadda yake ba, kuma yarda dashi dole ne kuma tambaya game dashi bidi’a ne”.

 Idan ba a manta ba, mun ambaci cewa irin wannan magana ta Ummu Salma (RS) da yawa wasu magabata sun faxe ta, sannan abinda ruwayar ke nuni a kansa shine hani ga tambayar yadda xaukaka take, kuma da a ce Ummu Salma (RA) ta jahilci ma’nar Istiwa’i (xaukaka) da ba t ace abu ne sananne ba amma an tambaye tane game da kaifiyya (yadda) xaukakar ta kasance, kuma har kwannan gobe amsar da ta bayar ita ce mafi dacewa ga dukkan xan bidi’ar daya mai-maita irin wanan tambaya. Allah ya yarda da Ummu Salama.

Na Biyu:

Shine a inda suka jingina ma imamul Anza’i tafwili, sun ambata cewa sun cirato daga Azzarqashi inda yace: an tambayi Malam Anza’i game da tafsirin ayar da t ace: “mai rahama ya xaukaka a saman Al’arshi” sai y ace wanda ya tambaye shi: haka ne, ina ganin kai batacce ne. To ai shi wanan a zahirisa ya nuna cewa tambayar ta gudana ne a kan yadda xaukakar ta kasance, shi ya Malam Anza’i ya bada irin amsar da malaman farko ke bayarwa tare da tabbatar da ita siffar kamar yadda ta zo domin ga abin da y ace: “mai rahama ya xaukaka a saman Al’arshi” haka yake kamar yadda yace a nan yana ufi ba tare da wani tawili ba, sannan a ya ci gaba da cewa: ina gani cewa kai batcce ne. kuma babu shakka cewa mai tambayar yadda sifofin Allah sukeya abka cikin vata kamar dai yadda MalamAnza’i ya tabbatar.

Na Uku:

 Sun kuma jingina tafwili ga Imamu Is-haqa xan Rahawaishi wanda xaya ne daga cikin limaman Hadisi suka ce Az-zarqashi y ace: an tambayi Xan Rahawaii game da xaukakar (Allah a Al-arshi) shi a tsaye ne ko a zaune (ya xaukaka)? Sai ya amsa cewa: idan a tsaye ne, gajiya ba zata shafe shi ba balantana a ce har ya zauna kuma idan ma a zaune ne haka abin zai kasance irin wannan tambaya ba tad a amfani.

 To a nan ma ka ga cewa a fili mai tambaya yana tambayar yadda alah ya xaukaka ne, a inda yace, a tsaye ne ko a zaune? Kuma irin wannan tambaya ai bidi’a ce.

 A kwai ban-banci mai girma tsakanin ‘yan bidi’a masu laluben a tsaye ya xaukaka ko a zaune, da masu magana ma’anar ita kanta xaukaka wadda aka sani da xaukaka da cirata, domin shi ne, fassararAl’Istiwa’i a inda su waxancan ke qorafin a fayyace musu yadda haqiqanin xaukaka aka yita.

 Sannan kuma shi, Malam Ishaqa xan Rahawaishi shi ya cirato cewa Malamaisun yi ijima’i game da cewa Allah ya na a sama a kan Al’arshi kuma yana sane da komai har abinda ke as qarqashin qasa ta bakwai. A na samun wanan bayani a Kitabul uluwwi da kuma cikin Littafin Assiya a inda aka kawo tarjamarsa[121]. A nan ina qarfafa zaton cewa ‘yan’uwa marubuta wannan qasida ba su ga waxannan bayaqnai ba kamin rubutasu da ba su kawo abinda suka kafa hujja da shi a matsayin dalili ba.

 Da haka aka tambayi Is-haqa cewa, mai zaka ce game dad a maganar Allah maxaukakin sarki cewa: “wata ganawa ta mutum uku ba zata kasance ba face Allah ne shi ne na huxu xinta” (Al-mujadala 7) sai yace: duk inda ka kasance, Allah ya fi jijiyar wuyanka kusanci da kai amma fa yana saman halittunsa, abin da zai tabbata maka da wannan a fili shine maganar alah da ya ce: “ mai rahama ya xaukaka a saman Al’arshi” (D.H.5)[122].

Na huxu:

 Shi wannan duk ya fi sauran fitowa a fili shi ne inda suka cirato jingina tafwili ga imamu maliki (RA) daga Xan Al-jauzi daga Abdullahi xan Wahbin wanda ya ce: wata rana muna a wajen maliki xan Anas sai wani mutum ya shigo y ace masa: ya baban Abdur-rahman! Ance “mai rahamaya xaukaka aAl’arshi” kamar yaya? Sai Imamu Maliki ya yi shiru ya na tunanin nauyin wannan tambaya wadda ta damar da shi, sai kuma ya tadakai, ya ce: lalle “mai rahama ya xaukaka kamar yadda ya sifaita kansa, kuma ba’a tambaya game da yadda ya xaukaka. Ina ganin kai mugun mutun ne xan bidi’a sai ya bada umurni a ka fitar da mutumin da inda yake.

 A nan, kai xan’uwa mai daraja sai ka yi nazarin irin wannan amsa tad a Maliki (RA) ya bayar musamman inda yace: “mai rahama ya xaukaka a Al’arshi ne kamar yadda ya sifaita kansa”. To mai musulmi zai iya qarawa bayan wannan? Babu shakka irin wannan amsa ita ce wadda Malamanfarko ke bayar wa domin barin sifaita Allah kamar yadda suka zo to ta ina tafwili yak e a nan?.

Na Biyar:

 Haka kuma idan ka juya zuwa ga abinda suka naqalta daga Sheikh Abubakar Mahamud Gumi zaka ga cewaduk tafiyar guda ce, domin shima cewa ya yi: “mai rahama ya xaukaka a kan Al’arshi” xaukaka wadda ta dace da girmansa. Abin nufi a nan shi ne, ba mu san yadda xaukakar ta kasance ba. Bari ma in bijiro maka da wani bayani, da ya yi a cikin rufewar tafsirinsa wanda su suka cirato daga suka cirato daga rashi ainda ya ke bayyana manhajarsa waddaya bi a tafsirinsa, ga abinda y ace:

 “A bangaren da ya shafi baya nan ayoyin sunaye da sifofin alah, na bi saun aqidar malaman farko a inda na amfana da Littafin Shehul Islam, Muhammadu Xan Abdulwahab da kuma faxarkar war Sheikh Abdul-aziz Xan Baz, xaukansu Allah ya saka musu da mafificin alheri…[123].

Yanzu kuma bari mu leqa Littafin Sheikh Muhammadu xan Abdul-wahab mu jimi yake cewa domin mu samu damar yi masa adalci, ga maganarsa kamar haka:

“Sanannen abu ne ga musulmi duka cewa, Allah madxaukakin sarki shi ya fi kowasanin kansa don haka idan harya zana wa kansa wani suna ko ya sifaita kansa da wata sifa gardama ta qare kenan. Haka kuma Manzon Allah, Muhammadu xan Abdullahi, (SAW) ya fi kowa sanin Allah wanda hakan shi[124]. Zai sa idan ya ambaci wani suna ko sifa ya jingina ga Allah ba wanda zai yi jayayya da shi, wannan shine abin da hankaliya yarda da shi, kuma abinda hujjoji ingantattu suyka tabbatar domin tataccen hankali shi ke fahimtar abin da Manzon Allah mai tsira da aminci ya zo da shi ba tare da gardama ba, kuma dama Littafin Allah da Sunnah sune ma’auni[125].

A nan sai in ce duk wanda ke son ya tabbatar da cewa Sheikh AbubakarGumi Salafi ne mabiyi sauran Malaman farko kuma ya tabbatar da cewa malamin ba ya da qawance da wani Tafwili ko tawili to ya koma ya dubi Al-qur’ani mai girma da kuma tarjamar ma’anoninsa zuwa ga harshen hausa wanda ya rubuta, ya gani, shin zqai ga wurin da ya yi tawilin Al-yad (hanu) da misalign ni’ima da rahama ko iko ko wani abu da ya yi kama da haka wanda ya shafi falsanci?.

Na shida:

 A inda suka jingina ma Abdullahi xan Abbas (RA) Tawili saboda fassarar da ya yi ga ayar: “ranar da za’a kuranye qwauri a inda ya ce: domin al’amari ne mai tsanani”.

 Mun riga mun yi bayani a babin cewa, tawili yanki ne yashbihi, mun ce wannan ayar tuni Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa ya fassarata kuma harm un ambaci fassarorin da shi Abdullahi xan Abbas (RA) ya yi game da ayar wanda dukkan su basu kauce ma fassarar da Annabi ya yi ba, ta kowace fuska, kuma babu tawilia xaya daga cikin fassarorin domin tawili shine. Juya akalar ma’anar lafazi daga zahirinsa zuwa wani wuri kuma ba shi ya faru ba a nan.

 Amma a fassasarar sa ga ayar da Allah maxaukakin sarki ya ce: “kuma sama, mun gina tad a wani irin qarfi”. (Az-zariyati:47) cewar da ya yi ana nufin da qarfi shima wannan ba tawili bane domi kalmar Al’aidi anan kalma ce, tilo ba jam’i ba ne na yaxu (hannu). A kwai irin t ace inda Allah ya ce: “da kuma ayyuba ma’abuci qarfi” abin da ake nufi da ‘al’aidi a harshen larabci shi ne: qarfi. To ina tawilin da ake zaton anyi anan? Abinda ya kamata a sai a nan shine, gaba xaya waxannanayoyi basu daga cikin ayoyin sifatuna Allah mai girma da xaukaka.

Na Bakwai:

 Inda suka jingina ma Imam Sufyanu Asauri cewa shima ya na tawili saboda a cikin tarjamarsa a Littafin siyasu A’alamin Nubala’i ance, a lokacin da mu’adan ya tambaye shi game da ma’anar zancen Allah maxaukakin sarki, “kuma shi ya na tare da kai a duk inda kukakasance”. Sai ya ce ana nufin, tare da ilminsa. A nan sai ince ai wannan itace fassarar dukkan malaman farkoga dukkanin ayoyi masu nuna tarayya kuma waxannan ayoyi masu tabbarda cewa Allah ya na tare da halittarsa, musulmin da kafiri, ba ta da wani tawili domin a bayyane ta keg a fili kamar yadda muka zo da bayani a babin “tabbatar da tarayya”.

 Kamar dai misalign tarayyarallah ta musamman ga waliyansa wadda ita ma a fili take ba buqatar kawo wani tawili, na karkata lafzi daga zahirinsa. Don haka a fahimci maganar Imamu Sauri ga wannan aya da kyau. Abin mamaki anan shine, a lokacin da suka ciro wannan magana daga reshi sun yi haka ne don kansu ne ka wai amma su kansu ba su amfani da irin wannan magana ta shi daxa ta tawilice ko kuma ba tawili ba ne? abin da zai nuna maka haka shi ne, ba su zube dukkan maganar ba wadda aka ce an ciro daga reshin, bari ku ji yadda take:

 “an tambayi sufyanu game da hadisai masu bayanin sifofin sai ya amsa da cewa: haka suke kamar yadda suke”[126].

Na Takwas:

 Sun ambaci cewa: Ahmad xan Hanbal, yana tawili, da hujjar wani ta’aliqi na Zahabi wanda shima bai ambaci isnadin maganar ba don mu iya gane ingancin maganar ko rashin ingancin ta a inda yace: an karvo daga Abdul-Hassan Abdul-Malik Al-Maimuni, cewa: wani mutun ya so ya ga imamu Khalaf Al-bazzar (RA) game da Hadisin da ya bada labarin sa cewa: “Allah bai halicci wani abu ba wanda yafi Ayatul kursiyyu girma” shi kuwa Imamu Ahmad sai yace: bai dace gare shi ba ya rinqa kawo irin waxannan hadisai a dai-dai wannan likaci, ya na nufin lokacin da suka sami jarrabawa game da maganar halitta Alqur’ani.

 A nan ne sai shi Imamu Az-Zahabi ya ambaci cewa shi Imamu Ahmad da aka tambaye shi game da wannan Hadisi mai cewa: “a cikin sama da qasa Allah bai halicci abinda ya fi ayatul kursiyyu girma ba”. sai ya ce halittar da ake magana ta shafi sama da qasa ne kawai da sauran banda Alqur’ani.

Bari in rufe idanu game da binciken sahihan cin wannan qissa ko rauninta sabo da rashin isnadin ta ba zai bada damar yanke hukunci a kanta ba, amma dai duk da haka, a cikinta babu abinda ke nuna tawili domin a farkon qissar ta nuna cewa, shi imau Al-bazzar ya na bada labarin wani Hadisi ne mai cewa: Allah bai ba wanda ya fi Suratul baqara girma wannan magana itace ta xauki hankalin’yan bidi’a har suka ce, shi Alqur’ani ba maganar Allah bane halittar Allah ne. sai imamu Alhamad ya nuna qyamarsa ga faxin irin wannan magana. Idan ka koma ga ta’aliqin imamu zahabi zakak isko abin da na bayyana maka dalla-dalla game da wannan qissar da izinin Allah[127].

Idan kuwa a na magana imau Ahmad game da Hadisin sai in ce, ban ga alaqarsa ba da maganar maganar tawili?

Sai kuma Hadisin da ke cewa: “A ranar Alqiyama, Suratul baqara za ta zo…” shi ma ya na magana ne game da sifar Allah idan wannan su ke so mi ya sa ba za su koma ba ga tafsirin ayar da Allah ke cewa: “ kuma ubangijin ka ya zo…” (Alfajr:22), don su ga yadda malaman farko dukkansu Allah ya yi musu rahama su ke fassara wannan aya?.

Na Tara:

 Sun jingina tawili ga imamu Buhari (RA) wanda yinhakan abu ne mai bada mamaki domin Littafin imamu Buhari game da wannan mas’ala bayyane yake kamar rana ban san abinda ya sa suka yi watsi da dukkan abinda ke cikin ingantaccen Littafinsa ba a babin tauhidi wanda dukkan sa ya na tabbatar da sifofin Allah ne mi ya kaisu zuwa har su tsinto muna ruwanya daga Al-baihaqi cewa, Buhari ya yi tawilin ma’anar dariya? A duk ingantaccen Littafin ma na a gani a wane babiza a samo abu mai kama dad a shi? Kuna so kuce tawili shi ne mazhabar Buhari? Sannan kuma duba a gani shi kansa imamul Baihaqi wanda aka ce ya citaro wannan magana mi ce ce ta shi mazhabar?

 Bari mu buxa Littafi mu gani mai suna: “Al-asma’u wassifatu” dukkan wannan Littafi na imamu baihaqiya na qumshe ne da bayanin tabbatar ma Allah maxaukakin sarki da sififinsa, mi ya hana su zuwa ga wannan Littafi su xebo?[128].

Na Goma:

 A inda suka jingina tawili ga imamu Abu Isa Attirmizi, wanda wannan ya fi maganar da ta gabace shi bada mamaki barium dubi maganar sa inda ya fassara; “sai ya sanar da su kansa” sai ya ce, ai ya bayyana gare su. To a ciki wannan mi ne n eke nuna tawili?

 To kuma yaushe imamu Attirmizi ya faxo cikin malaman baya masu tawili? Bari mu dubi Littafinsa Assunan da kuma ta’aliqin hadisan dake cikin sa don mu gano salafiyyar da suka liqa ma yin tashbihi.

 Zan taqaitu ga bada misali guda kacokan, daga cikin babin zakka inda ya kawo Hadisin Abu Hurairat (RA) inda ya xaga Hadisin ya na cewa: “Lalle Allah ya na karvar sadaka kuma ya na amsarta ne da hannunsa na dama sai ya ruvanya ma xayan ku ita kamar yadda xayanku ke renonta yadda loma zata zama misalin uhudu” sai ya ce sanin gaskiyar hakan sai an duba Littafin Allah mauwayi inda ya ce: “shin ba su sani ba, cewa lallai Allah ne ya ke karvar tuba daga bayin sa, kuma yana karvar sadaqoqinsu,” (taubati:104). Da kuma in day ace: “Allah yana shafe Albarkar riba, kuma yana qara sadaqoqi”. (Baqara:276).

Abu Isa Attirmizi, yace: wannan Hadisi ne mai kawo, ingantacce. Haka kuma an ruwaito irin wannan daga Aisha (RA) daga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa. Kuma malamai da yawa, sun tavatar da irin waxannan hadisai masu bayyana sofofin Allah da saukowarsa akowane dare zuwa sama’un duniya, sun tabbatarda cewa ba zai yiyuba a musan ta waxannan hadisai, za a yi imani da su ba tare da wata tuhuma ko tambayar buga misali ba.

Haka kuma an ruwaito daga Maliku xan Anas da sufyanu xan Uyaina da Abdullahi xan Mubarak, dukkan su sun fayyace cewa: za a bar waxannan sifofi kamar yadda suka tusgo ba tare da tambayar buga misali ba.

Wannan kuwa shine, abida masa daga cikin mabiya Sunnah suka tafi a kansa. Amma, sun yi watsi da waxannan ruwayoyi har ma suka ce wai wannan tashabihi ne. Alhali kuwa Allah maxaukakain sarki da kansa ne ya yi bayani a wurare da dama cikin Littafinsa cewa, yana da hannu, ya na ji, ya na gani, dukkansu waxanda suka dace da zatinsa. Amma duk da haka sai jahamiyya suka yi tsayin gwamin jaki suka ce, su dole sai sunyi tawilin waxannan ayoyi anan ne suka fassara ayoyi savanin yadda malamai suka fassara har ma suka ce, wai Allah bai halicci Annabi Adamu da hannunsa ba domin hannun da aka ambata a wurin a na nufin karfi ne. Amma malam Is-haqa xan Ibrahim cewa, ya yi, tashabihi ya na kasancewa ne a lokacin da mutun ya ce: hannu ya yi kama da hannu na ko ya ce, jin ya yi kama da nawa ji, amma idan mutun zai ambaci sifofin hannu da ji da gani kamar yadda Allah ya ambacesu ba tare da ya kamantasu da na wani abu ba. Wannan ba a kiransatashabihi sam, domin Allah ya ce: “wani abu bai zama kamar tamkarsa ba. kuma shi mai ji ne mai gani”[129].

Na Goma Sha Xaya:

 Wannan wuri ya fi dukkan sauran wura ban al’ajabi domin a nan ne suka jefa malamin Hadisi na wannan zamani kuma kingin mazan xauri a fagen sanin sirrin Hadisi da biyar Sunnah, malam Muhammadu Nasiruddin Albani (RA) Buharin lokacinsa kamar yadda su suka furta.

 Sun inganta malamin ciki gungun masu tafwili da tawili a waje sifar Al’Istiwa’i (xaukaka), hakan ya faru ne garesu ta hanyar guntsuro sashen maganarsa a cikin Littafin da Al-majirinsa, Muhammad xan Ibrahim ya rubuta game da fatawowinsa. Ko da ya ke a dai-dailokacin da na ke wannan bincike Littafin ba ya kusa da ni, amma na rubuta su yi adalci wajen ciro maganarsa ba domin sashen ta suka xebo suka baro sashen da ba shi suke so ba. Amma ina qarfafa, zaton cewa ba cikin ganganci suka ya hakan ba, a kwai yiwur cewar ba a cikin Littafin kai tsaye suka ciro maganar ba, domin ‘yan bidi’a sun daxe da shahara wajen nuna qiyayyaga mabiya Sunnah kamar irin su Qausari da Gumari da Abu Guddu da Saqqaf waxanda duk an shaide su da irin wannan mugun aiki na biyar malama Sunnah da baqar yadiya, kamar dai mutumin da ya katso maganar Allah ne mai cewa: “bone ya tabbata ga masallata”. Sai ya yi tsayinsa nan don ya jefa ruxu ta hanyar nuna cewa Allah maxaukakin sarki ya zargi dukkan masu yin sallahalhali abi ba haka ya ke ba.[130] a nan sai in ce: lalle Sheikh Muhammad Nasiruddin Albani (RA) ya kasance daga cikin mutane mafiya tsanani ga abinda kuka jingina shi gare shi, duk mai karanta Littafinsa da sauraren kasusuwansa zai shedi hakan. Shi ne malamin da ya taqaita Littafin Alhafiz Az-Zahabi mai suna” Al-iluwwu lil Aliyil Gaffar” (Littafin da ya yi bayani kwatta fill game da tabbatar da sifofin Allah ba tare da wani tawiliba) ya mayar da Littafin cikin shafi 76, ya fito da bayanai a cikinsa qarara masu qarfafawa ga mazhabar malaman farko kuma ya fatattaki dukkan wuraren shubuhohin da ake iya liqewa gare su a cikin Littafin musamman abin da ya shafi, maganar tabbatar da jaha da muhalli. Wannan kaxan ne daga cikin abin da ke qunshe a cikin muqaddimar Littafin wanda ta a nan ne mai karatu zai gano irin nauyi da girman qarya da aka sheqa ma Albani (RA) ta jingina masa abin da aka jingina gareshi a cikin qasida.

 Daga cikin bayanin sa ga abin da ya ce: ya kyautu ga mai karatu ya sani cewa, wannan Littafi ya zo da maganin mas’ala mafi haxari a sashen aqida wadda ta tarwatsa haxin kan musulmi, ba yau ba tun ranar da qungiyar mu’utazilawa ta bayyana a duniya, wannan mas’ala kuwaita ce ta maganar xaukaka Allah a kan dukkan halittunsa wadda ta tabbata cikin Littafi da Sunnah game da gari, aqidar da ita ce hankali lafiyyae ke karva.

 Ba ya dacewa ga miusulmi ya yi musu ga tabbatar irin wannan ko da yake tuni sashen wasu karkatattun qungiyoyi daga Sunnah sun buxe ma kansu da sauran mutane babin tawili, ta wannan hanya ne shexan ya shimfixa gavar zarensa sabo da tsananin gabar sag a mutum na neman kange shi ga hawan tudun mun tsira da kuma hanya madaidaiciya[131].

 Daga nan ne kuma sai buga misalai guda biyu daga cikin wuraren da mamayan Malaman farko suke yin tawilinsa kamar haka:na xaya a in da Allah ya ke cewa: “kuma ubangijinka ya zo alhali mala’iku na jeer, safu safu”, (Suratul Fajr:22). A nan wai sai suce: “kuma bawan ubangijinka, ko lamarin ubangijinka (ya zo). A wuri na biyu kuma shine inda suke tawilin Al’Istiwa’i (xaukaka) sai su ce Al’Istila’i )rinjaya) ya ce: shi a ganinsa ga dalilin da ya ke sa su yin hakan kamar haka: sun jahilci matsayar limaman tafsiri da na Hadisi da na harshen larabci game da irin waxannan fassarori, harma suka tafi a kan cewa, ma’anar kalmarIstiwa’i tan a nufinrinjaya akan Al’arshi ba xaukaka ba, kuma suka ce wanan shi ne abinda malamai suka yi ittifaqi akan sa irinsu Imamu Is-haqa xan Rahawaihi da kuma Alhafiz xan Abdulbar, abin mamaki basu sani ba malaman da suka kawo matsayin dalili gare su, hujja ne a kansu a cikin wannan babi. Wannan ne ya sa hark o yaushe za mug a cewa, da yawa daga cikin malaman da suka zo daga baya suna suna sava ma tafsirin malaman farko game da ma’anar ayoyin Al I’stiwa’ da suuran ayoyida hadisai masu bayani game da sifofin[132].

 Yanki na farko wand azan rufe da shi a cikin bayaninsa, shi ne wata magana mai kyawo wadda ya yi a qarqashin bayanin da ya ciro daga Shehul Islam Ibnu Taimiyya in da ya ce “a sani fa cewa, babu wani nassi ingantacce ko tunani wanin hankali tatacce wanda ke cin karonhaifar malaman farko. Anan ne sai Albani yace: ni kuwa sai n ace: game da ingantaccen nassiidan ka dubi abin da ke cikin Littafin da ke hannunka na Al-hafiz Zahabi zaka samu yaqinin cikakke cewa, ayoyin Alqur’aniduka da hadisai da bayanan malaman farko dukkan su, sun yi nuwafaqa kan cewa, Allah mai girma ya na a saman Al’arshinsa da zatinsa, sama da halittarsakuma ya na tare da su da ilminsa.

 Har wala yau kuma za ka tantance cewa, cikin yardarm Allah dukkan limaman mazhaba bobbin da ake biya tare da mabiyansu na farko-farko, da ma dukkan waxanda suka bi tafrkinsu a vangaren masu bi musu har saukowa zuwa qarni na shida na hijira dukkan fatawowinsu sun gamu kan tabbatar cewa Allah ta’ala ya xaukaka a saman Al’arshinsa da halittarsa kamar yadda yake sama da kowane muhalli, kuma kamar yadda wannan shine sananne gama gari daga manzon Allah tsira da amincin alla su tabbata a gareshi da iyalan sad a sahabbansa, haka kuma dukkan malaman farko da limaman Hadisi da na faqihu da na tafsiri da malaman harshen larabci da sauransu duk sun yi itifaqi a kansu.

 Shakka duk wanda ya bibiyi zantukansu zai tabbatar da hakan. Yawan malaman da suka tafi a kan wannan tafarki sun wuce a qidaya yawansu ba maganar dari biyu ba ne kamar yadda marubucin ya bayyana Allah ya yi masa rahama, ya kawo sunayen wanxanda idanunsa ya sami kaiwa ga resu kawai. Da zarar xalibi mai tsoron Allah tare da neman gaskiya, ya gamu da bayanansu zai sakankance cewa ba zai yiwu ba irin yawan waxannan jama’a haxuwarsu ta zama a kan vata, kuma a nan ne zaka gano vacewar duk wanda ya kauce musu[133].

KAMMALAWA

 Yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai gairma, wanda kyauwawan abubuwa ke kammaluwa da ni’imarsa.

 Bayan haka, babu shakka, cewa, manyan-manyan abubuwa da ke sanya Imani ya qaru shine Ilmin sanin Allah da sunayensa da siffofinsa, kuma karkacewa ga abinda ya danganci Allah da sunayensa da siffofinsa itace babbar karkata mafi hatsari.

 Na tabbata cewa, xan’uwa mai karatu, tafarki na gaskiya game da wannan matsala ya bayyana gare ka, bayan zagayen da aka yo dakai na yawon bada idanu a cikin faxin Littafin Allah mai girma da Sunnar manzonsa musxapha, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da kuma guraben malaman farko Allah ya yarda da su, don yanzu ka tantance wannan tafarkin da suke a kansa game da wannan matsala mai girman hatsari, mai jefa mutum a talalaviya bayan ta rikita tunaninsa.

 Yanzu bari mu taqaice wannan manhaji (Tafarkin) malam acikin tushe guda uku:-

Tushe na xaya:

 Dole ne a tsarkake Allah mai girma daga kowace irin tawaya kuma a nisanta kamanta siffofinsa da siffofin halittu. Dalili game da wannan shi ne maganar Allah ‘Ta’ala da ya ce: “wani abu bai zama kamar tamkarsa ba” “kuma kada ku buga misallai ga Allah” “kuma babu xaya da ya kasance tamka a gareshi”.

Tushe na biyu:

 Wajibine a yi imani da dukkan siffofin Allah mai girma waxanda suka zo tabbace cikin Littafin Allah da Sunnah ba tare da yin tsallake ba, kuma ba za’a yimasu ragi ko qari ba ko canza ma’anonin su (ku ne kuka fi sani ko Allah)?

Tushe na uku:

 Yanke tsammaninsanin ainihin yadda waxannan sifofi suka kasance. Saboda Allah mai girma ya ce: “Yana sanin abin da ke a gaba gare su da abin da ke bayansu, kuma ba su kewaye da shi ga sani”.[134] (D.H 110)

 Haka lamarin ya ke, domin shi Ilmi sanin siffofin Allah, yanki ne a sanin zatinsa, idan kuwa har babu mai iya faxin yadda haqiqanin zatin Allah mai girma yake babu ta hanyar da za’a iya sanin yadda sifofinsa suke. Daga nan ne za’a iya qara tantance xewa, wani abu bai zama tamka ga zatinsa ko ga sifofinsa kamar dai yadda Allah wanda girmansa, sha’aninsa ya buwaya ke cewa: wani abu bai zama kamar tamkarsa ba, kuma shi ne mai ji, mai gani (Shura:11). Daga nan ne zata bayyna gare ka cewa, duk yadda aka so a shafi ma wannan aqida, tatacciya wani kashin kaji ko a gurvata ta, ta hanyar wasu shubuhohi, hakan ba zai yi wani tasiri ba kamar yadda ba zai iya cutar da kyawon aqidar da kome ba. Don haka abinda ya rage, shi ne, biyar hanyar ga skiya ba tare da damuwa da qaramcin mabiyanta ba.

 Gaskiya hanyar ta ba ta da karkata; amma mahankata kawai ka saninta. Ina roqon Allah mai karimci, ubangijin Al’arshi mai girma, ya shiryar dam u ga hanya madai-daiciya. Madalla da kasancewarsa majijivincin lamurra kuma mai taimakon. Tsira da amincin Allah da sallamawar da albarkoki su tabbata ga Annabinsa, kuma badaxayinsa Muhammadu da matansa da zuriyarsa da sahabbansa da mataimakansada duk wanda ya bi hanyarsa har zuwaranar sakamako.

 MANAZARTA

(1) Al’ashari, Imam Abul hassan “Al’ibana an usuliddiyana”. Ta qasidimSheikh Hammad xan Muhammad Al’ansari, Bugun Al’jami’atul Islamiyya, Madinatul Munawwara, 1431. Hijira.

(2) Assayuxi, Imam Jalaluddin. “Al’itiqanu fi ullumil qur’an”. Tahaqiq, Abdul-muna’aim Ibrahim, maktavatu Nazzar Musxapha Al’baz Riyad, Saudiyya, Bugu na Biyu. 1424. Hijira/2003, Miladiyya.

(3) Abu Zahara, “Ibnu Taimiyya: Hayatuhu wa asarahu – Ara’uhu wa fiqihuhu”. Darul fiqr Al’arabi, Alqahira, 1991. Miladiyya.

(4) Xan Qayyim “Ijtima’aul juyushik Islamiyya ala gazawil mu’axxila ti wal jahamiyya”.

(5) Abu Yusuf, Muhammad xan Ibrahim, A’hawimin fatwa As’sheikh Albani. Maktavatul ilmiyya Litturas, sabon Bugu na xaya, 1421, Hijira/2001, Miladiyya.

(6) Xan Qayyim Al’jauziyya Adilatu Uluwillah, ala Khalqihi Mina Kitabio WasSunnah wa aqiwalus salafil umma. Taqidamu wa tialiqu, Muhammad xan Ahmad Sayid Ahmad Maktavatus Suwaxi, Jidda Saudiyya Bugu na xaya, 1412, Hijira/ 1991 Miladiyya.

(7) Sheikh Usman xan fudi, Ir’shadu ahalit Tafaridi wal ifraxi ilsawa’issirax. Makhadud, daga cikin kayan gado na mahaifi na, Sheikh Ibrahim xan Abdurrahaman xan Usman Almasini.

(8) Asshanqixi, Sheikh Muhammadul Amin xan Muhammadul Mukhtar Adwa’ul Bayan fi idahil qur’ani bil qur’an. Maktavatul Ibnu Taimiyya, Alquhira, Misra, 1408, Hijira/1988, Miladiya.

(9) A hakami Sheikh Hafiz xan Ahmad I’ilamus-Sunnah Al manshura li’iitiqadix da’ifatin Najiya Almansura. Dirasatul wa tahaqiqu Ahmad Ali Alush Mudkhali, Maktavatur Rashid, Riyad Saudiyya Bugu na huxu, 1416, Hijira/1996, Miladiya.

(10) Dr. Muhammad Nu’aim yasin Al’iman: Arkanuhu, haqiqatuhu, Nawaqiduhu. Maktavatus-Sunnah, Alqahira, Misra bugu na xaya 1412, Hijira/1991 Miladiya.

(11) As’shaibanu, Muhammad xan Ibrahim Auraqim majmu’atun min hayati Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya. Maktavatul Ibnu Taimiyya, Kuwait, Bugu ba daya 1409, hijira/1989 Miladiya.

(12) Ad’dumashqi, Imam Al’hafiz Abul-fida, Isma’ilxan Qasir Abidayatu wan Nihaya. Tahaqiqi At’turas Darn Ihyait Turasul Islami wa Mu’assasatut Tarihil Arab, Beirut, Lebanon, 1413, Hijira/1993 Miladiya.

(13) Ad’dihilawa, Allama Ahmad xan Muhammad, Tarikhu Ahlil Hadis. Tahaqiqu, Aliyu xan Hassan xan Abdul Hamid Al-halbi, maktavatul, Guraba’ul Asariyya, Madina, Saudiyya Bugu na Xaya, 1418, Hijira.

(14) Az’zahabi, Alhafiz Tazkiratul Huffaz.

(15) Ustaz falih xan Mahadi Al’mahadi At’tuhufatul Mahadiyya Sharhur Risala At’tadamiriyya. Bugun Al’jami’atul Islamaiyya, Madinatul Munawwara, Bugu na Biyu 1406, Hijira.

(16) Al’hafiz Abul fida’i Isma’il xan Qasir Tafsirul Qurr’anil Azim. Darul Ma’arifa, Beirut, Lebanon, Bugu na Farko, 1408, Hijira/1987 Miladiya.

(17) Allamatus sham, Muhammad, bahajatul baixar Hayatu Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya. Beirut, Labanon, 1391 Hijira.

(18) Abdullahi xan Ahmad xan Haribu, As’Sunnah. Tahaqiqu, Muhammad xan Said xan baisuni, zagalul, Darul Kutubil Ilmiyya, Beirut, Labanon, bugu na biyu 1414, Hijira/1994, Miladiyya.

(19) Al’’asqalani, Hafiz shahabud’din Ahmad xan Aliyu Ibnu Hajar Tahazidut Tahazib. Daru Sadir, bugu na farko 1327. Hijira.

(20) Al’qurxubi, Hafiz Abu Umar Yusuf xan Abdullahi xan Mahammad xan Abdul’bar, An’numari. At’Tamhid Lima fil Muwaxxa’a. tahaqiqu, Abdullahi xan Assidiq, da wasu, musawaratul maktavatut tijariyya, makka, Bugun Al’amagarib 1399, Hijira/1979, Miladiya.

(21) Al’masini Allamatul Hajj Usman, Aljami’ul hawi Ligalibi mafi kutubil mujaddad As’sheikh Usman xan Fodiyo. Wanda jikansa Alhaji Aminu Tafidaya yaxa, rubutun Dahiru xan Muhammad, Al’Bukhari, Shekara 1987, miladiya.

(22) Annasa’i Imam Abu Abdur-rahaman Ahmad xan Shu’aibu Sunan An Nisa’i (Almujtava). Darul fikr, Birut, Lebanon, Bugu na biyu 1421, Hijira/2001, Miladiya

(23) Alganimani, Sheikh, Abdullahi xan Amuhammad, Sharhu Kitabut tauhid min Sahihul Bukhari. Maktavatud dar, Al’madinatu Munawwara Bugu na Xaya 1405 Hijira.

(24) Al’bagadadi, Almaliki, Imam Alqadi Abi Muhammad Abdull’usahab xan Ali xan Uasan Sharhu Aqidatil Imamumalik As’sagir Abi Muhammad Abdullah Xan Abi Zaidi Alqirawani. Sahhahahu, Allamat Abu Uwais Muhammad Abu Khaira Al’husaini At’taxawani, (Takharij) Abul Fadl badr Al’umrani Axxanji, Darul Kutub Al’Ilmiyya, Beirut, Lebanon, Bugu na Xaya 1423 Hijira/2002 Miladiya.

(25) Sheikh Usman xan Fodiyo Almatul Muttabi’in li Sunnahti rasulil lahi (SAW). Tahaqiq Abdullahi Muhmmadusifawa wanda Milestone suka yaxa, Sokoto.

(26) Al’waqil Sheikh Abdur-rahaman Sifatul Ilahiyya bainas salaf wal khalaf. Daru lina, Damnahur,misra, Bugu na biyu, 1413 Hijira/1992 Miladiya.

(27) Gumi Sheikh Abubakar Muhamud, Raddul Azhan Ila Ma’anil qur’an. Mu’assafatu Gumi Lihijara, Kaduna, Nijeriya 1408, Hijira/1987, Miladiya.

(28) Imamu Ahmad xan hanbal Ar’raddu ala Az’zanadiqa wal jahamiyya, maxaba’atus-salafiyya, Alqahira, 1393, Hijira.

(29) As’shanqixi, Sheikh xan Muhammad Al’amin xan Muhammad Almukhatar, Aljukni Rihilatul Hajja Ila Baitillahi Haram. Daru Ibnu Taimiyya Alqahira.

(30) Ibnu baxuxa, Rihilatu Ibnu baxuxa, Tuhufatun Nazzar fi garabil Amsar wa ajaibil Asfar. Darul kuttub Al’lubanani, Beirut.

(31) Al’bani Nisirud-din, Silsilatu AHadisib Sahiha. Maktavatul Islam Beirut, Lebanon, Bugu na Biyu 1402, Hijira.

(32) Albani, Sheikh Muhammad Nasiruddin, Silsilatul Anadisid Daifa wal Maudu’a wa Asaraha Assayi’i alal Umma. Maktavatul ma’arifi Riyad, Bugu na Biyu,1420, Hijira/2000, Miladiya.

(33) Attirmizi, Imam Abu Isa Muhammad xan Isa xan Sura, Sunan Attirrmizi. Takharij siddiq Jamil Al’axxar, Darul Fikr, Beirut Lebanon Bugu na xaya 1422 Hijira/2002 Miladiya.

(34) As’sajistani, Imam Au Daud Sulaiman xan Al’ash’as, Sunanu Abi Dauda. Takharij Siddiq Jamil Al’axxar, Darul Fikr, Beirut, Lebanon Bugu na xaya, 1421 Hijira/2001 Miladiya.

(35) Az’ahabi Imam, Shamsuddin Siyaru A’alamin Nubala’i. Tafqiq, Shu’aibu Al’arna’ux da wasu mu’assasatur Risala, Beirut Lebanon Bugu na Huxu 1407, Hijira/1986, Miadiya.

(36) Al’lalaka’i, Axxabari Imam, Alhafiz Abul qasim, itibatullahi xan Alhassan xan mansur sahrhu usuli iitiqadi AhlisSunnah wal jama’a minal kitab wasSunnah wa ijama’issahabati wattabi’in wa man ba’adahum. Kulawar Muhammad, Abdussalam Shehu, Darul Kutubi Ilmiyya, Beirut, Lebanon, Bugu na xaya, 1423, Hijira/2002,Miladiya.

(37) Alhanafi, Allamaxan Abdul 12, Sharhul Aqidatux dahawiyya. Tahqiqi jama’atun minal ulama’a, Takhari, Muhammad Nasiruddin Albani Al’maktabul Islam, Beirut Lebanon Bugu na huxu 1391, Hijira.

(38) Al bagawi Imam Abu Muhammad, Alhassan xan Mas’ud, SharhusSunnah. Tahqiqu Shu’aibu Al’arna’ud, Almaktabul Islami, Beirut, Lebanon Bugu na Biyu, 1403, Hijira/1983, Miladiya.

(39) Al’amin Muhammad Ahamad, Sharhu Muqaddimati ABi Zaid Alqirawani fil Aqida. Maktavatu Dar’il Maxabu’atil Hadisi, Jadda, Saudiya, bugu na xaya, 1412, Hijira 1991 Miladiyya.

(40) Al’bukhari Imam Abu Abdullah Mhammad xanIsma’ail Sahihul Bukhari. Takharij, Siddiq jamil Al’axxur, Darul fikr, Beirut, Lebanon, Bugu na xaya 1422, Hijira/2002, Miladiya.

(41) Alqushairi, Imam Abul Husain Muslim xan Al’hajjaj, Sahihu Muslim. Kulawar Siddiq jamil Aladdar. Darul fikr, Beirut Lebanon Bugu na xaya, 1421, Hijira/2000, Miladiya.

(42) Alwakil Sheikh Abdur’rahaman. Assifatul Ilahiyya bainas-salaf wal khalaf. Maktavatul lia, damnahur Misra Bugu na biyu 1413, Hijira/1992, Miladiyya.

(43) Albani Sheikh Muhammad Nasiruddin, Daifu Aljami’us-sagir wa ziyadatuhu. AlmaktabulIslam, Bugu na biyu 1408,Hijira 1988, Miladiya.

(44) An nasir, Abul Hassan Aliyu Al’Hussain Rija’ul fikr wad’da’awati fil Islam. Darul Qalam Kuwait, Bugu na huxu 1407, Hijira/1987,Miladiya, juzu’i na biyu.

(45) As’sili, Dr. Sayid Abdul Aziz, Al’qaidatus-salafiya bainal Imamu Xan Hanbal wal Imam Ibnu Taimiyya. Darul mannar, Alqahira, Bugu na biyu 1416, Hijira/1995, Miladiya.

(46) Abu luz Sheilh Abdullah xan Abdur’rahaman xan Jubrin, Al’qidatul Wasixiyya ma’a Ta’aliqatiz-zakiyya. Kulawar Abu Anas Aliyu xan Hussain Alharsul wadani, Riyad Saudiyya, 1421, Hijira.

(47) Al’jilani Al husani Sheikh Abdulqadir Al gunya lixalibi xariqil haqq. Al’maktabus-shu’abiyya,

(48) Al’asqalani, Hafiz Ahmad xan Ali Ibnu Hajar, Fathul Bar bi sharhi sahihul Buhari. Ta’aliqu Sheikh, Abdullah xan Baz,Al’maktabutt-tijara, Makkatul Mukarrama 1414, Hijira/19993, Miladiya.

(49) Ad’duilami, Hafiz Shirawi xan Shahardar, Fir dausil Akhabar bi Ma’asunil Khadab Almukhraj ala Kitabis-shuhab. Darul fikr, Beirut, Lebanon, Bugu na xaya 1418, Hijira/1997, Miladiya.

(50) Al’fairuz a badi, allamaa allugawi Majadudin Muhammad xan ya’aqub Al’quamusul Muhid. Tahaqiq, makatabut turas fi Mu’assasatur Risala Beirut, Bugu na biyu, 1407, Hijira/1987, Miladiyya.

(51) Xan qayyim Aljaujiyya, Allama, Shamsuddin, Al qasidatun Nuniyya, Alkafiyatus-shafiya fil intisar lifirqatin Najiya. Kulawar Abdullahi xan Muhammad Al’amairi daru Xan Huzaima, Bugu na xaya, 1416, Hiira/1996, Miladiyya.

(52) Az-Zahabi, Hafiz, kitabul Arshi. Tahaqiq Muhammad Hassan Muhammad Hassan Isma’il darul kutubil Al’imiyya Beirut, Lebanon bugu na daya 1424, Hijira/2003, Miladiya.

(53) Lum’atul iitiqadilhadi ila sabilir rashad. Sharhin SheikhMuhammadxan Salih, Tahaqiqin Abi Muhammad, xan Abdul maqasud, maktavatu dabariyya, Riyad, Bugu na Uku, 1415, Hijira/1995, Miladiya.

(54) Az’zahabi, Hafiz Shamsuddin Mukhta sarul Uluwi Lil Aliyil Gaffar. Tahaqiqin Muhammad Nasiruddin Albani, Makatavatul Islama Bugu na Biyu 1412, Hijira/1991, Miladiyya.

(55) Al’ifiriki, Allam Abul fadl Jamaluddin Xan manzur, Lisanul Arab. Daru sadir bugu na Shida 1417, Hijira/1997, Miladiya, 11/32.

(56) Al hakami Sheikh, Hafiz xan Ahamad. Mukhtasaru Ma’arijilqabuli wanda Hishamxan Abdulqadir xan MuhammadAl uquda ya taqaita, Darus-safawa, Alqahira, Bugu na Biyar 1418, Hijira.

(57) Majmu’ul fotawi darul wafa’i Almansura, Misra bugu na xaya 1418,Hijira/1997, mildaya.

(58) Al’fauzan faxilatis Sheikh salih xan fauzan xan Abdullahi Mujmalu Aqidatis-salafis-salih. Darul Asima Riyad Saudiyya, Bugu na Xaya 1412,Hijira.

(59) Imam xan qayim Aljauziyya Mukhtasarus-suwaiq Arrisala alal jahamiyya wal Mu’axxila. Wanda Sheikh Muhammad xan Al’muusili ya taqaita, a cibiyar bincike da fatawa ta yaxa, Riyad saudiyya.

(60) Ad’daram, Imam Hafiz Abi Muhammad Abdullahi xan Abdur-rahaman, Musnad Ad’durami, sunanud darami. Tahaqiqin Hussain Sulaim asad Ad’darani, Darul Mugni, Riyad Saudiyya, Bugu na xaya 1421, hijira/2000, miladiya.

(61) Alahshari, Sheikh ABul Hassan Ali xan Isma’il Maqalatul Islamiyya Tahoqiqin Muhammad Muhyiddin Abdul Hamid, Maktavatun Nahada, Almisiriyya, Bugu na biyu 1389, hijira/1969, Miladiya.

(62) Al’muntaqa min manhajil iitidal. Wanda Az’zahabi ya taqaita, tahaqiqin Muhibbuddin Alkhabib

(63) As’shanqixi, Sheikh Muhammad Al’amiri, man’ul-jawazAl’majaj fil Manzil Litta’abbbudi wal iijaz. Maktavatu Ibnu Taimiyya, Alqahira.

(64) As’shanqixi, Sheikh Muhammad Al’amin Minhajun wa dirasatun li’ayatil Asmal wassifat. Bugun jami’ar Musulunci, Madina, Al’munawwara, 1400, Hijira.

(65) Az’zahabi Hafiz Abu Abdullahi. Mizanul iitidali fi naqadir Rijali. Tahaqiqin Ali Muhammad Albajawi Darul Fikr, Beirut.

Fassara ta kammala a daren Laraba, 6/4/2005.

Godiya ta tabbata ga Allah maxaukakin sarki.

﴿وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ مَعَ الْمُتَّقِينَ﴾[التوبة:36 والأعراف: 123 والبقرة: 194]

“Kuma ku sani, tabbas, Allah ya na tare da masu taqawa”. Suratul Baqarah:194, Taubah: 36, da A’raf:123.[1] An xebo wannan gabatarwar ne daga littafin Hafiz Zahabi mai suna ‘kitabul arshi,’ tahaqiqin Muhammad Hasan Isma’ila, Darul-kutubil Ilmiyya, bereut, Lebanon, bugun farko, 2003/1424 hijira. shafi na 11.

[2] Abul Ma’ali Al-juwaini yace: Abinda muke yarda da shi a matsayin ra’ayi gamsasshe kuma abinda muke addini da shi a matsayin aqidarmu shine, biyar magabatan wannan al-umma. Kuma yankakken dalilinmu akan hakan shine, domin zamowar Ijima’in wannan al’umma hujja ce miqaqqiya da ake bi, Idan kuwa har da tawili abin qwarai ne da sun himmantu da shi fiye da himmantuwarsu ga rassan addini. Tun da kuwa har zamanin sahabbai da tabi’ai ya qare ba su yi tawili ba, babu shakka rashin yin tawili shine abin biya.” A duba: littafin Al-Aqidatul Nizamiyyah na Abubakar Xan Al-arabi, Maxaba’ar, Alarnaux, ta Alqahira, 1948, shafi, 23, da kitabul-Arsh, na Hafiz Azzahabi, shafi 151

[3] Majmu’atu Tafsiri shaikhul Islam 1/468 

[4] Sahihul Buhari, Kitabut ta’anid, babi na 22.

[5]  Sahihul Buhari, Kitabut tauhid, babi 23.

[6] Duba sharhin da Sheikh Abdullahi xan Muhammad Alginiman ya yi wa kitabul Tauhid na cikin sahihul Buhari wanda aka buga a maktabutud daril Madinatil muna wara bugu na farko anyi shi a 1405 Hijira. Mujalladi na 1/9 – 20 kuma siyaru a alamin – Nubala’I wajen tarjamar Imamu Ahmad xan Haubah 11/236.

[7] Duba littafin Al aqlaniyyuna Afrakhul Mu’utazilatil Asariyyuna na Aliyu xan Hasan xan Aliyu xan Abdulhamid Al halabiy Al asariy, maktabatul guraba’u Al asariyya, Madina, bugu na farko 1413AH/1993CE shafi 176.

[8] Al tamhid lima fil muwatta minal ma’ani wal Asanid na hafiz Abu Umar Yusuf xan Abdullahi xan Muhammad xan Abdul Barri An namiri Al qurxubi, tahaqiqin Abdullahi xan Siddiq da wasu malamai, maktabatul tijariyyah, makkah, kofe daga bugun al magrib, 1399AH/1989CE, 7/346. Malam Waki’u yace: an kafirta Bishirul marisi domin game da sifaita Allah (SWT) an ji shi yana cewa, Allah yana cikin komai. Da a ka tambaye shi cewa yana nufin har cikin hular da ke a kansa? sai ya ce e qwarai, aka ce har a cikin cikin jaki? yace Na’am. Tir! Allah kam ya xaukaka daga abinda karkatattu ke jingina masa, xaukaka kuwa mai girma.  

[9] An ciro wannan ne daga waqen ad Dawudi na larabci wanda ya rasu a shekara ta 467BH

[10]  Wanda ya qarfafi fito da wannan aiki, kuma ya kula da bugunsa na farko shine shaqiqin mai littafin, marigayi Malam Nasiru Ibrahim. Kuma Allah ya yi ma sa rasuwa ‘yan watanni kaxan bayan da wannan littafin na larabci ya fito a sarari. Muna roqon Allah Ya saka masa da mafificin alherinsa, ya dausaya qabarinsa, ya sanya aljanna firdausi ta zamo makomarsa.

[11] -Al-Imanu : Arkanuhu, Haqiqatuhu, Nawaqiduhu, na Dakta Muhammad Nu’aim Yasin, makabatus Sunnah, bugun farko 1412B.H./1991M. shafi 15-18

[12] Duba Adwa’ul bayan fi idahil qur’ani bil qur’an, na Sheikh Muhammad Al-Amin xan Muhammad Al-Mukhtar ash-shinqixi, maktabatu Xan taimayya, Al-qahira, Misra, 1408B.H./1988M., (2/272 - 273).

[13] Sahihu Muslim, kitabu salatil musafiri, Babin mustahabbancin tsawaita karatu a sallar dare (772) (203).

[14] A’lamus Sunnah al Manshurah li I’itiqadil xa’ifatil najiyatil mansurah, na Sheikh hafiz Ahmad Alhakami, tahaqiqin Ahmad Aliyu Allush madkhali, Maktabatul rushd, Riyad, Saudi Arabiya. Bugu na huxu 1416-B.H./1996M. shafi na 74.

[15] Al jami’ul Hawi li galibi ma fi kutubil mujaddadi al Sheikh Usmanu xan Fodiyo, na Al Haji Usmanu Almasini, wanda jikansa Alhaji Aminu tafida ya buga da rubutun hannun Dahiru xan Muhammadu Buhari, Sakkwato, Shekarar 1978M. Shafi na 131.

[16] Sharhul aqidatil xahawiyyah, shafi na 325-326. Ustazu Al-juwaini ya na cikin sahun malamai da suka yi zurfi cikin ilimin falsafa (Ilmul kalam) amma daga baya ya yi nadama har ma ya yi wa xalibansa kashedi game da ilmul kalam ya na cewa: “kada ku kuskura ku shagaltar da kanku da ilmin falsafa ko ni da na san zan sami kaina cikin wannan hali na ruxuwa da ban shagalatu da ilimin falsafa ba” Duba littafin Naqdul Manxiq, Shafi na 61. Wani abin da ke qara nuni ga komowarsa ga tafarkin gaskiya shi ne, a lokacin da kalamin Imamu maliku ya kai ga kunnensa inda ya ke cewa “xaukaka abu ne sananne” sai ya bayyana gamsuwarsa ga maganar har yace ya zama wajibi mu bar ayoyin sifofin nan kamar yadda suka tuzgo. Idan ka duba “Al Qa’idatun Nizamiyyah a shafi na 23 za ka ga Abu Ja’afar Al-hamdani duk ya tattaro ayoyi da Hadissai masu maganar Allah na sama da ire iren waxannan sifofin na Allah, sannan yace, waxannan nassoshi da ire-irensu duka za mu faxe su akan yadda suka zo, ba wani tawili.

[17] Zamu yi magana akan wannan bawan Allah “Ash’ari” wanda masu cewa, Allah na ko ina ke jingina kansu ga mazhabarsa alhali ko shi ba aqidarsa kenan ba.

[18] - Al-Ibanatu An usulil diyanati, shafi na 120.

[19] Al’adar yara it ace, duk qadangaren da suka ga yana xaga kai sama rannan za su aika lahira. Sannan idan suka lafta masa bulala ya mimmiqe ya na xaukar rai sai su yi sauri xaga kansu su kalli sama suna cewa: Na riga ka dibin Allah. Don suna ganin cewa a lokacin idan ya xaga kansa sama to qararsu zai kai ga Allah. A nan ne sai su riga shi kai uzuri ga Allah !

Wani lokaci kuma idan aka cuci yaro, ya tabbata an fi qarfinsa, sai ya ce: “Allah na bisa na gani”. Shi kuma kurma ko da da kurunta a ka haife shi idan yana so ya yi ratsuwa ko ya mai da lamari ga Allah sai ka ga ya xaga hannu ya nuna sama.

            Duk wannan Allah ne ya gina halittarsa a haka ya shiryar da su sanin inda yake da zatinsa ba tare da saninsu da wani dalili na qur’ani ko Hadisi ba. Allah ya sa mu gane Allah. (Daga mai fassara).

            Xanu Abdul-Barr Bamalike Allah ya rahamce shi ya ce, daga cikin hujjar cewa shi Allah mabuwayi ya na a saman Al’arshi, qolin qololuwar sammai bakwai; shi ne ganin cewa, dukan wani mai kaxaita Allah daga cikin larabawa ko Ajamawa da zarar baqin ciki ya sauka ga xayansu suna xaukaka fuskokinsu ne zuwa sama don neman taimako ga Allah (SWT). Shahararre wajen malamai har ma da jahilai babu bukatar ayi ta zubo dalilai akanshi, abu ne da ya fi qarfin Musuntawa ga ko wane Musulmi. Kuma sai ya kafa hujja da Hadisin kuyanga wanda Maliku ya ruwaito cikin Almuwadda da Muslim a ingantaccen littafesa. Duba At-Tamhid, 7/134         

[20]  Duba Tafsirin Qurxubi, (16/215)

[21] Malik ya ruwaito shi cikin Al-muwadda (kitabul Itki wal-wala’I, babin; ma yajuzu minal Itk fir-rkabil-wajibati, 2/776-777) Da Ahamad cikin Al-Mujnad (2/291,3/222,388,389 5/447,448,449) Da Muslim cikin As-sahih (K. Al-janaiz h, 53) Da Abu Dauda cikin As-salat, H. 930 da cikin Al-Iman wan-Nuzur, babin Ar-Rikabu Almuminatu cikin As-Sahawu, babin Alkalmu fis-Salati 3/14-19   

[22] Mukhtasaru Al-Uluwwi Lil-Aliyyil-Jaffar,shafi 81  

[23] Al-Ibanatu an Usulil-Diyanati. (20)

[24] Duba: Mu’alimut-Tanzil’ na Al-bagawi mai Ta’alikin Abdullahi xan Ahamad xan Az-zayyad. Bugu jiha’zal-Irshad, Wat-Taujihi bil-harsil-wadani, Ar-Riyad 1421 Hijira, 1/457

[25] Al-Imamul Bukhari ya fitar da wannan Hadisi a wurare 6, a cikin littafinsa. Wuwi na faro a Kitabu Bad’il-Wahyi, lambar 3194 sai a Kitabut-Tauhid, Lambobi 7404, 7422, 7453, 7553, da kuma 7554 ta hanyoyi daban-daban dukkansu sun tabbatar da cewa wannan littafen ya na wurin Allah a birbishin Al-arshi. Shi kuwa Muslim ya fitar da Hadisin ne ta hanyoyi guda uku a cikin kitabut-Tauhid, Lambar Hadisin 2751. 

[26] Sharhu Aqidatil Imami Malik As-sagir, Abi Muhammad Abdullahi Xan Abi Zaidin Alqairawani, na Imamu Abu Muhammad Abdulwahab xan Aliyu al Bagadadi Al-Almaliki, wanda Malam Abu Uwais al Kharrati ya sahhaha, kuma  Abul fadl badar Al-umrani ya yi bitar hadissansa, Bugun Darul kutubil ilmiyyah, Beirut, Labanon, Bugun farko, 1423H /2002M. Shafi na 28

[27] Siyaru A’alamin Nubala’i (11/376)

[28] Amma banda ayar Dakhan don ita ta zo ne da harafin Ila ita kuwa babu ambaton Al-arshi tare da ita, rinjayayyar magana game ita, ita ce bata daga cikin ayoyin sifatu

[29] Duba sahihul-Bukhari, K. At-Tauhid, babi Lamba ta 22

[30] Fathul Bari: 3/406.

[31] Duba littafen da ya gabata.

[32] Shi dai Jahamu ya yayo wannan ra’ayin ne daga Ja’adu xan Dirham daga wani xan uwan Labidu xan A’sam, bayahuden nan da ya yi wa Manzon Allah (SAW) sihiri, har Allah ya saukar ma manzonsa da magani cikin surori biyu na qarshen alqur’ani. 

[33] Al’aqidatus salafiyya bainal Imami Ibnin Hambal wal Imami Ibnu taimiyyah, na Dakta Sayyid Abdul-aziz As-Sili. Darul Manar, Alqahira, bugu na biyu, 1416H/1995M. shafi na 298.

[34] Duba Alqasidatun Nuniyyah, mai suna Alkafiyatus-Shafiyah fil intisari lil firqatin Najiya, na Shamsuddin Ibnul qayyim, wadda Abdullahi xan Muhammad Al-umair ya kula da ita, bugun Daru ibni khuzaimah, na farko, 1416H 1996M shafi 157.

Wannan waqar ta kai baiti kusan dubu shida, kuma dukkanta tana fayyace sha’anin aqida ne bisa tafarkin magabata. Haka kuma waqar ta maida martani cikin tsanaki ga dukkan karkataccin aqidodi.

[35] Duba littafin da sunansa ya gabata, shafi na 91. Da kuma sharhinsa na Sheikh Muhammad Khalil Harras, (1/179-180), da Mukhtasarus-sawa’iqil-mursala, shafi na 306, da Taudihul kafiyah, na sheikh Abdurrahaman xan Nasir as-Sa’adi, shafi na 61, da Taudihul maqasidi na Xan Isa (1/197-398).

[36] Kamar yadda ya zo a Hadisin “Allah zai sanya mutane bakwai a cikin inuwar al’arshinsa.

*Sheikh Abubakar Mahmud Gumi yace: Farkon Halitta, Al’arshi ko ruwa, ruwa da Al’arshi suna gaba da sammai da qasa. Sa’annan aka halicci qasa daga ruwa kuma aka mayar da ruwa hayaqi aka halicci sama. Sa’annan kuma aka mulmula qasa a cikin surar qwai. Allah ne mafi sani. Tarjama320

[37] Sahihul Buhari, kitabul Khusumat, babi 1, Hadisi na 2411 da Kitabul tauhid babi na 22 Hadisi na 7427. Kuma ka duba Hadissai masu lambobi kamar haka:  3408, 3414, 4813, 6017, 6018, 7472. Sannan da Sahihu Muslim, Kitabul Fada’il, babi 42, Hadisi na 2373, sai dai a cikin ruwayar Muslim ba’a ambaci qafafuwa ba, amma a xayan ruwayarsa ya zo da lafazin “sai ga Annabi Musa riqe da gefen al’arshi”.

[38] Sahihu Muslim, Kitabul Jana’iz, babi na 75, Hadisi na 1342 wanda a ka karbo daga Abdullahi dan umar Allah ya yarda da shi.

[39]  Wata xan sha huxu ba ya rabuwa da kai idan ka yi tafiya, ya na kuma can tare da iyalanka a gida, da ma sauran dukkan masu na shafin kwalli. Allah ya xaukaka daga a buga masa misali.

[40] Majmu’u fatawa Sheikhil Islam Ibni taimiyyah, (5/23-232), a kuma koma ga As-Sifatul Ilahiyyah bainas salafi wal khalaf, na Sheikh Abdur Rahman Al-Wakil, daru linah, damnahur, Misra, bugu na biyu, 1413H/1992M. shafi na 129-130.

[41]  Duba wannan firar a littafin da muka ambata a sama, da kuma cikin Sharhin Aqidatux Xahawiyyah.

[42] Gajeruwar fahimta ga wannan aya da ire-irenta ta sanya wasu sufaye ke cewa, Allah ya na ko ina, har su na raya cewa yana sauka ya shiga cikin jikin komai (Al hulul). Amma ina suka ga hujja a nan? Dukkan dalilan nan hujja ne a kansu, in da za su rabu da son zuciya.

[43] Ahmad ya ruwaito shi 2/421, da Muslim a Kitabus-salati, Hadisi na 215, da 482, da Nasa’i a`cikin Kitabut Taxbiq, Hadisi na 1137 daga Abu Hurairata (RA).

[44] Shi yasa ma aka umurci mai sujada ya karanta (Subhana Rabbiyal A’ala) a daidai lokacin da ya kai qolin qanqan da kansa ga Allah, ya faxi cewa, Allah shi ne mafi xaukaka. Duba Majmu’ul fatawa (5/236-237).

[45] Wani failasufi yace ma wani Ahlus Sunnah, ai saukowar da Allah ya ke yi a qarshen ko wane dare zuwa samar duniya, ba shi ne ya ke saukowa ba, umarninsa ne ke saukowa. Sai Ahlus Sunnah ya ce, to, daga wurin wa umarnin zai sauko, tun da ba ka yarda Allah ya na sama ba?!

[46] Lisanul Arab, na Abul Fadli jamaluddin, Al’ Ifriqi, Daru Sadir, bugu na shida, 1404B.H/1998M (7/210).

[47] Duba littafen da sunansa ya gabata 11/23 da Alqamusul Muhix, na Muhammad xan Ya’qub Al fairuz abadi, Tahaqiqin maxaba’ar Mu’assasatur Risala, Beirut, bugu na biyu, 1407B.H./1987M shafi na 839.

[48]   Duba misali Surorin Kahfi: 58, 78, 82, Nisa’i: 59, Yunus :36, A’raf :52-53, Yusuf: 39, 44, 37, 100, Sajdah: 17 da kuma Al-imrana: 7.

[49] Manhajun wa dirasatun li ayatil Asma’i was-sifati, na Sheikh Muhammad Al-Amin As-Shinqixi, Bugun Jami’ar Musulunci ta Madina, 1400B.H., shafi na 18-19.

[50] Jauharatul Tauhid mai hashiyar Abajuri shafi 55 saidai abin lura anan shine, su nassoshi bayyanannu ba su da wani rikici ga mutane masu basira da hankali mai tsarki, amma zukatan da ke ciki rashin lafiya  wadanda falsafa ta dabaibaye dole ne su samu kansu cikin rudu, kuma da wahala su iya gano cewea Allah ya na da sifofin da suka dace da girmansa wadanda ko shakka babu sun saba ma sifofin mutun da halayensa.

[51] Siyaru A’alamin Nubala’i (10/506-506).

[52] At Tamhid na xan Abdul-Barri 7/149

[53] Sahihul Bukhari, Kitabut Tauhid, babi na 22, Hadisi na 7420.

[54] Darami ya ruwaito shi a littafen Ar Raddu Alal Jahamiyyah da isnadi ingantacce. Duba: (1/27).

[55] Duba littafin da ya gabata, shafi 27 – 28, da kuma Kitabul Uluwwi na Zahabi. Albani kuma yace, isnadin Hadisin ingantacce ne a kan sharaxin Muslim. Mukhtasarul uluwwi shafi 130.

[56] Tafsirul Qur’anil Azim, na Ibnu Kasir, Darul ma’arifi, Beirut, Lebanon, bugu na farko 1407B.H/1987M (4/133)

[57] Musnad na Darimi, shafi na 105, da littafen Ar-Raddu alal-Jahmiyyah, shafi na 26 game da isinadin shi, Alhafiz Zahabi ya ce, kamar rana ya ke, shi kuwa Albani yace, isnadin sa a kan sharadin Buhari ne da Muslim. Mukhtasarul Uluw, shafi na 103. Abdullahi xan Ahmad xan hanbali a cikin kitabus-Sunnah da Baihaqi a littagin Al Asma’u Was Sifat, 104 da Ibnu Khuzaima 70 da Lalaka’i a Sharhu Usulli I’tiqadi Ahlis Sunnah (1/213) da Ibnul qayyim a cikin Ijtimaul-juyushil Islamiyyah shafi na 100 da kuma Ibnu Abdil barr a cikin At Tamhid (7/139).

[58]  Sahihul Buhari K. Almagazi, babi 62 Hadisi 435 da Sahihu Muslim, K Az Zakati, babi 47, Hadisi 1064.

[59] Sahihu Muslim K An-Nikah, babi 19 Hadisi 1436

[60] Sunan Abi dawuda, K Al’adab, babi 66, Hadisi 4941, da Sunan At Tirmizi, K Albirri Was-silati, babi 16, Hadisi 1931. Tirmizi ya ce, wannan Hadisi mai kyawo ne ingantacce.  Duba qarin bayani akan darajar Hadisin a cikin Silsilatus Sahiha, 922.

[61] An samu kwafin wannan littafe na asali da rubutun hannun Ahmad xan Zaidu Almaqadisi a inda ya ambata cewa, shi kuma ya xauko daga rubutun hannun mawallafin littafen. An aka buga shi a Indiya shekarar 1306B.H. kuma daga bugun Indiya ne Jama’atu Ansaris Sunnah ta alqahira su ka buga shi tare da ta’aliqin Abdur-Razzak Afifi a shekarar 1357B.H. sannan sai Maktabus Salafiyyah ta madina ta yaxa shi a shekarar 1388B.H. qarkasin kulawar Ustaz Abdur-Rahman Usman. Sannan Shehu Muhammad Nasirruddin ya  rairaye littafin ya fitar da ruwayyoyinsa masu inganci kaxai, Maktabul Islami ya buga shi. Daga baya kuma an samu wani sabon bugu wanda Muhammad Hassan Isma’il ya kula da shi. Shi kuma Maktabul Ilimiyyah ne ya buga shi a shekarar 1424B.H/2003M.

[62] As-Sunnah, na Lalaka’i, (1/92), da A’uluwwu, na Zahabi, 132. Malamai da dama sun inganta shi

[63] Imamuz Zahabi ne ya ruwaito shi cikin kitabul uluw kuma ya inganta shi dubi shafi 184.

[64] Duba Tafsirul Qur’anil Azim na Ibnu Kasir 2/254 da Tafsirin Imamut Tabari 7/27.

[65]  Duba qarin bayani a Mufradatul Qur’an, na Asfahani, (1/85).

[66]  Sahihu Buhari K Tafsiril Kur’an babi 2 Hadisis na 4919 daga Hadisi Abu Sa’id kuma  har wa yau Buhari ya fitar da shi cikin kitabul tauhid babi 24 Hadisi 7439 cikin  wani Hadisi mai  tsawo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da  iyalansa acikin Hadisin ya ce  “sai ubangijimu ya kuranye kwabrinsa dukan muminai suyi mai sujada ga Allah sai domin riya to idan  ya je ganin yin sujada sai bayan ya sandare a sahe guda”

[67] Tafsirul Kur’anil Azim na Hafiz Ibnu Kasir, Darul Ma’rifah, Beirut, Lebanon, bugu na farko, 1407B.H/1987M (4/435).

[68] Duba littafe na sama. Sai dai wannan ruwaya ta na da rauni inji Ibnu Kasir.

[69] Lum’atul i’tiqad Al hadi ila Sabilir Rashad, Sharhin Sheikh Muhammad Ibnu Salih, Tahaqiqin Abu Muhammad xan Abdul Maqsud, Maktabar Xabariyyah, Riyad, Saudi Arabia, Bugu na uku, 1415B.H/1995M. shafi na 61.

[70] Shi yasa muna iya cewa Allah mai hikima ne amma ba mu iya cewa, mai hankali ne. Kuma muna iya cewa, Ibrahim (AS) badaxayin Allah ne amma bamu iya cewa abokin Allah ne. Haka kuma muna cewa ya na da Al’arshi (Kujerar mulki) bamu iya cewa ya na da gado. Ko da yake dukkansu suna iya karvar ma’ana guda amma saboda ladabi  ga Allah maxaukakin sarki ba zai yiwu ba mu ambace shi da suna ko sifar da bai ambatarwa kansa ba.

[71] Alhafiz Abu Umar xan Abdulbarri bamalike yace: “Hujjar da suke kafawa (ya na nufin ‘yan tawili) da cewa inda ya na a wani muhalli da kenan ya yi kama da halittu domin abin da duk muhalli ya kewaye to, halitta ne. Wannan ba ya lazimtar ubangiji. Kuma ma wannan magana ba ta da ma’ana, domin shi Allah, wani abu bai zama kamar tamkarsa ba daga cikin halittarsa, kuma ba a qiyasta shi da komi, sannan ba a kamanta shi da mutane. Musulmai da ma duk masu hankali sun yarda da cewa “hankali bai iya fahimtar wani samammen abu sai a muhalli. To, amma kuma shi Allah akwai shi tun babu muhallin. To, wanda a haka ya za’a qiyasta shi da wani abu a halittunsa? Allah ya girmama ga abin da azzalumai ke faxi zuwa gare shi girma kuwa babba” At-tamhid (7/135 - 136).

[72] Don qarin bayani game da sanin sahihiyar aqidar limaman mazhabobi huxu da suka gabata sai ya duba littafin Usuluddin, na Ustaz Abu Xahir Albagdadi (1/313) da littafin Iqazu Himami ulil Absar, na Salih Alfullani, shafi na 50 da kuma Tarikhu Ahlil Hadis na Dahlawi, shafi na 35 -43.

[73]  Qarnonin da aka yi ma shaidar alheri su ne qarnuka guda uku na farkon musulunci, wato Sahabbai da masu bi musu da masu bi musu. Don Annabi (SAW) yace, su ne mafi alherin jama’a.

[74] Rihilatul Hajji ila baitillahil haram, na sheikh Muhammad Aminu As-shinkixi, Daru Ibn Taimiyya, Alqahira, shafi na 63.

[75] Kitabul Arshi, shafi na 70 – 71 amma wannan magana ta Imamu hanifa ta yi tsanani da yawa. Shi kam Zahabi (Allah ya yi masa rahama) da ya zo maganar Qatada (wani mashahurin malami wanda santsi ya kama shi ya faxa cikin aqidar qadariyya) Zahabi  cewa ya yi “Akwai yiwuwar Allah  ya yi uzuri ga irinsu Qatada wadanda suka sami kansu cikin ramin bidi’ah wajen qoqarinsu na son tsarkake Allah da girmama shi, domin Allah mai hukunci ne da adalci mai tausayin bayinsa, kuma babu mai tambayarsa ga abinda ya aikata. (Duba: Siyaru a’lamin Nubala’i 5/271). Har wa yau bayan da ya ciro ire-iren waxannan maganganu masu tabbatar da waccan bidi’a daga shi Qatada sai yace; munyi uzuri ga reshi da duk ire-irenshi. Idan kam Allah ya yi musu uzuri to, madalla. Idan kuwa ya yi musu azaba, to Allah baya zaluntar bayi. Halitta da al’amari duka nasa ne. (Siyaru a’alamin Nubala’i 5/277)

[76] Kitabul Arshi, 71.

[77] Isbatul uluwwi, na Ibnu qudama, lamba 108, da Kitabul Arshi na Zahabi, shafi na 39. Kuma a duba tarjamar Imamus Shafi’i wadda ke cikin Siyaru a’alamin Nubala’i (10/79).

[78]  Hambali xan Shafi’i malami ne. Kuma An sa masa sunan kakansa ne.

[79] Lalaka’i ya fitar da shi a Sharhu Usulis Sunnah (3/160-161) da Zahabi a Kitabul Arshi, shafi na 97 da Ibnul Qayyim a Ijtima’ul Juyushil Islamiyya, shafi na 201.

[80] Al Itiqanu fi ulumil Qur’an, na Imamu Jalaluddin A Suyuxi, tahaqiqin Abdul Mun’im Ibrahim, maktabatu Nazar Musxafa Al baz, Riyad, Saudi Arabia, bugu na biyu, 1425B.H/2003 (2/675).

[81] Wannan qa’ida ta rarrabe magana zuwa “Haqiqa” da “Majaz” ya na cikin bidi’oin Mu’utazilah da jahamiyyah. Kuma ba wata masaniya game da wannan kafin qarni na uku bayan Hijira. Dubi Majmu’ul fatawa, na Shehul Islam Ibnu Taimiyyah (6/301–374) da Mukhtasarus Sawa iqil mursala, na Ibnul qayyim, (1/75–76) da Man’u jawazil majaz fil munazzali lit ta’abbudi wal i’jaz, na Shinqixi da kuma  Tafsirin Adwa’ul Bayan, nasa (10/...) da sharhin Muqaddimar Risala, na Sheikh Al-amin Alhaji Muhammad, Shafi 109.

[82] Al-kashfu an manahajil adilla, shafi 60 a kuma duba Assifatul ilahiyya bainas-salafi wal khalaf, shafi 127, da Majmu’u fatawa Sheihul Islam Ibnu Taimiyya 13/294-313.

[83] duba littafi da sunansa ya gabata 7/145

[84] At-tamhid na Ibnu Abdil Barr (7/131).

[85] Duba littafen da ya gabata 7/128.

[86] Akwai tarjamarsa cikin Siyaru A’alamin Nubala’i na Imamu Shamsuddin Zahabi, tahaqiqin Shu’aibu Al’arna’ud tare da wasu mu’assasatur risala,Beirut Lebanon, bugu na hudu 1406.H/1986M 20/43-9-451. ya na daga cikin manyan malaman Sunnah wadanda ake bugun gaba da su, kamar yadda tarihinsa ke shedun haka,Allah ya yi masa rahama. Imamuz-zahabi ya kai mutuka wajen yabonsa, da yake ambaton akidarsa ta salafiyya sai da ta kai yace: a cikin manyan waliyyan Allah ba a zarce Shehu Abdul kadir ba a fagen halaye ba karamomi sai dai da yawansu ba su inganta ba, har ma daga cikinsu akwai abubuwan da basu yiyuwa a takaice da shi Shehu Abdulkadir sha’aninsa ya na da girma amma wannan ba ya hana  a iya kama kuskurensa, wasu labaran ma da aka jingina masa na karya ne Allah shi ne gwani. Duba siyaru A’alamin Nubala’i 20/450-451. 

[87] Algunya li dalii darikil hak na Shehu Abdulkadir Aljelani, Al-maktabatus-shu’ubiyya, shafi 54-57 a takaice, kuma Imamuz-zahabi ya ciro wannan maganar daga shi Shehu Abdulkadir a cikin kitabul arsh 154 harma ya yi masa addu’a.

[88] Majamu’ul fatawa, Darul wafa’i Almansura, Misra bugu na daya 1418H/ 1997M 5/230

[89] wannan itace fassarar da shehu musulunci Ibnu Taimiyya ya Allah ya rahamshe shi ya karfafa a cikin Majmu’ul fatawa 2/404.

[90] Tafsirul Kur’anil Azim darul ma’arifa Beirut Lebanon bugun farko, 1408H/1987M 2/127-128.

[91] At-Tamhid na Xan Abdul-barr 7/145.

[92] Rihilatu Xan Baduda mai suna Tuhfatun Nazzar fi gara’ibil amsar wa aja’ibilabfar, darul kutabil luba nani; beirut shafi 68.

[93] Shafi na 61

[94] duba Albidaya wan niyya na Imamu Alhafiz Abdul-fida’i Isma’ila Ibnu Kasir Addamasliki tahaqiqin maktabi tahaqiqit turas, darul ihya’it tunas al-islami da mu’assasatul  tarihil Arabi Beirut lebanon 1413H/ 1993M 14/97 da littafen Ibnu Taimiyya hayatuhu wa asruhu ara’uhu wa fikihuhu, na Imamu Muhammad Abu Zahara, darul fikril arabi alkahira 1991M shafi 71, da hayatu sheikh Islam Ibnu Taimiyya na Allahmatussham Muhammad bahjatul baidar, almaktabatul islam beirut lebanon 1391H shafi 44 da auraku majmu’at min huyati shehu islam Ibnu Taimiyya na muhammad xan ibrahin Asshaibani maktabatu Ibnu Taimiyya alkuwait bugu na daya 1409H/1989M shafi 58-59 da Rijalulu fikr wadda’awati fil islam na abul hassan aliyu alhussaini annadwi darul kalam alkuwait bugu na 4 1407H 1987M juzu’i na biyu shafi na 90.

[95] At-taharifi (karkata ma’ana) shi ne, sauya lafazi daga ainihinsa da ma’anarsa ta haqiqa zuwa wani waje. Ta’adili kuwa (bata ma’ana) sonce ma Allah sifofinsa da sunayensa ko abinda suke nuni a kansa, Attakyif, (kwatantawa) kuwa itace kamanta iyakance ma Allah sifa daga sifofin sa. Attamsil (misaltawa) shine buga ma Allah misali ta hanayar sifaitasa da wata sifa ta halittu. Duka dai Allah ya girmama ga surutun azzalumai girma mai nis.

[96] Al’akidatul wasidiyya ma’a ta’alikatuz-zakkiyya na Absharkh, Abdullahi xan Abdur-rahaman xan Jabirin kulwar Abu Anas Aliyu xan Husain Abu lauz, wanda, Jihazul irshad wat taujih bil harsil wadan suka watsa, riyad assaudiyya 14/21H shafi 81-92.

[97] Tazkiratul Huffaz 3/358.

[98] Sunansa shine Aliyu  xan Isma’il xan Ishaka xan Salim  xan Isma’il xan Abdullahi xan Alburda xan abi Musa Al-ash’ar, an haife shi  a shekarar 270H. ya rasu  a shekarar 324H, ya bar gadon  littafai manya masu amfani, daga daga  cikinsu kuwa akwai littafen  Al’ibana da Al-lam’u karami da babba  wadanda duk a cikinsu ya bayyana akidar magabata ya kuma mayar da martani ga maiya bidi’a irjn, jaha miyyu  da rafidawa da mu’utata zilawa da ire-iren su ga abinda wani yace: accikin wakar  sa game daa Abul-Hassan da ace bai rubuta komi ba a  rayuwarsa sai littafen Al’ibana da sun wadatar da shi amma shi mutun ne wanda yayi zurfi a cikin fannonin ilimi da rubuce-rubucen tarbiyya wadanda suka tasarma dari biyu dukkansu masu matukar amfani da shiriya ga al’umma. Malamai dana gabata masu yawa sun anbaci littafensu kamr yadda sheikh Hammad Al’ash’ari limamin malaman Hadisi na madina a lokacinsa Allah yayi masa rahama.

[99] Duba A-muntaka min hajil’ihidal wanda  azzahabi ya takaita,  tahaqiqin Muhibbuddin Al’khadib, ta’aliki mai lamba 2.

[100] Al-khadad lil makrizi 3/358-359.

[101] Tarikhu Ahlil Hadis, shafi 74-77.

[102] Al’ibanatu fi Usuliddiyana shafi na 52-53 da shafi na 119.

[103] Dubi misali wannan a wasikatul wan litabyini dalilatil wujubi ittaba’il 8 kitabi wasSunnahati wal ijma’i, da littafen  Baynul Bidi’a shaidaniyya allati ahada sahan nasu fi tiazaz zamani da  Kitabu Ihhyasus-Sunnahti wa lihmadul bida da dai sauransu.

[104] Alamatul muttabi’ina lisSunnahti rasulillah (SAW), tahaqiqin Abdullahi Muhammad sifawa wanda moilestone ya yada shafi na 1.

[105] Ihya’usSunnah wa ikhmadul-Bidi’a.

[106] Al-majimul hawi shafi na 170-171.

[107] A gani na da ace Shehu Usman xan Fodiyo Allah ya yimasa rahama tun a farko ya sadu da kitabus Sunnah na imamu Ahmad xan Hanbal (T.241H) da Ar-radu Alal Jahamiya da kitabus Sunnah na xan Abi Asim (T.287H) da kitabus Sunnah  na Abdullahi xan Ahmad (T.290H) da kitabut tauhid wa ma’arifati sifatir rabi azza wa jal na Xan Huzaima (311H) da kitabut tauhid na xan Mundah da kitabul akidati  na xan Abu ja’afar Al dahawi (T.321H) da littafen “Albaihaki al’asma wassifat” da kitabusshari’ati fisSunnah na Abubakar al’ajuri (T.360H) da littafen Alla’laka’i (T.418H) sharhu usulu i’itikadi AhlusSunnah wal jama’a da littafen  assuna na Khilali da  sharhin Sunnah na Aldagawi (T.516H) da kitasbu xan kudama (T.620H) fi isbatil uluwi fi akidati ahlisSunnah da assharhu wal ibana  na xan Badda da al ibanana Abul hassan al ash’ari da kitabul arsh na zahabi (T.748H) da istima’ul juyushil islamiyya na Xan Al kayyim (.751H) da  ibdalut tawilat na Abu ya’ala da ire-irensu da cikin littafan da ke bayani akan tafarki  malaman Hadisi babu  shakka da ace ya samesu da babu abinda zai hana shi kafa hujja da su. Saboda muhimmancin su a wannan babi. Allah ya yi masa sakayya da alhairi game da namijin kokarinsa na yaki da kafirci  da bautar gumaka da jihadin san a turmuza bidi’a, kuma Allah ya hada mu tare da shi a  Aljannarsa kuma si Allah mai iko ga yin haka.    

[108] Irshadi ahalit tafridi wal ifradi ila sawaiis-sirad rubutun hannu wanda na same shi a cikin litaffan mahaifi na sheikh Ibrahim xan Abdur-rahman xan Usman Almisini Allah ya yi masa rahama.

Duba shafi na 14.

[109] Aljami’ul hawi, shafi 130-131.

[110] Duba littafen daya gabata shafi na 131.

[111]Duba shafi na 102 a littafen da ya gabata.

[112] Yadda aka kawo Hadisin a cikin kasidar shine: “kada ku gaya musu abinda ke azabtarwa” wannan wani kuskure ne,.

[113] Mizanul i’i tidal fi nakdirrijal hafiz shamsuddin Abu Abdulahi Azzahabi tahaqiqin Aliyu Muhammad Albukhari. Darul fikri Beirut 4/344.

[114] Tahazibul Tahazib na Hafiz sharhuddin Ahamad  xanhajar Al’askalani, daru sadir, bugun farko 1327H,11/147.

[115] Duba Taharijin wannan Hadisi a Silsilatul AHadisid da.

[116] Al-jami’ul kabir na Assayudi, shafi na 2.

[117] Al-kurshfu an manahajil adilla, 60.

[118] A a wannan kam ita ce tsintsar mazabar malaman farko (Assalaf)kuma duk wanda ya jingina su ga Almutashabihaya yi musu kazafi.

[119] Wannan shi ne tawili (kame baki) wanda ke nuna cewa, sahabbai Allah ya yarda da su sun jahilci sashen mafi girma da muhimmanci bangaren addini shine sanin zatin Allah da sunayen sad a sifofinsa.

[120] Wannan ga zatonsu ken an amma kuma aishi Allah mai girma da manzon sa sun fi su sani kuma sun fi fasaha da sanin abinda ke tsarkake Allah mabuwayi don haka ita hanyar tsarkake Allah a na gane tan e hanyar ilmi ba hankali ba don ba a iya game kammalar Allah sai ta hnyar Allah da manzonsa.

[121] Duba Muktasarul uluwwi shafi na 194, da Siyaru A’alamin Nubala’i 11/370.

[122] Siyaru A’alamin Nubala’i 11/370.

[123] Raddul Azhan Ila-ma’anil qur’an na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi mu’assasatu Gumi Lit-tijara, Kaduna Nijeriya.

[124] 1408.H/1987M/2/828

[125] Ad-durarus-saniyya bugu na daya, 2/70.

[126] Siyaru A’alamin Nubala’i 7/274. kuma basu ciro maganar da mai ta’aliqin wannan littafe ya kawo ba daga Alhafiz Xan Jarir Ad’xabari a cikin tafsirinsa game da ayar “kuma shi yana tare da ku a duk inda kuka kasance”, sai yace, abin da Allah ta’ala ya ce anan shine, Allah yana  lura da abinda kuke  ciki shiga duk inda kuka shiga, ya na sane da ayukkan ku da jujuyarku da makomarku, amma shi ya na a kan Al’arshisa wanda yake a saman samai bakwai. Duba littafen da sunansa ya gabata an ciro wannan ne daga jumi’ul bayani na Ad’xabari 27/216.

[127] Siyaru A’alamin  Nubala’i 10/578.

[128] Amma kuma ya kyatu mu yi uzuri ga ‘yan uwa marubuta wannan qasida,  yana yiwuwa hannunsu  bai samun kaiwa ga wannan littafe ba, qila sun ciro waccan magana ce ta hanyar Assaqaf, mutumin da aka shaida da rawar kai da tsananin ta assubaci, amma kuma idan haka ne in ce musu “ku tambayi ma’abuta sani idan ku ba ku sani ba” in kuma qara dqa cewa: “…idan fasiqi ya zo muku da labari to ku nemi bayani”

[129] sunan At-tirmizi , Kitabu Az-zakat daga manzon Allah (SAW), babi na 28H. 662.

[130] Daga baya na samu ganin littafen ta hannun wani xalibina, Allah ya saka mas da alhairi. Makatabar Ilimiyya Lit-turas, ita ce ta buga shi a 1421H./2001M. da na duba littafen sai naga abin da na fadi shi ya tabata. A cikin sa shehu Albani a bayana wata tambaya, ya fara bada amsar kamar haka: lalle wannan tambaya ta zo a cikin ingantaccen littafen musulim… sai ya ambaci Hadisin kuyanga, daga nan sai ya ce: mu kam muna koyi ne da tafarkin manzon Allah (SAW) wannan hanya ita ce abin biya a gare mu, kuma muna sane cewa daga cikin mutane a kwai wanda ba zai  iya bada amsa irin wadda wannan kuyanga ta bayar ba, da za ka ce da shi, a ina Allah ya ke? Abinda zai fara shiga a zuciyarsashine kyamar irin wannan tambaya alhali kuwa nuna kyama ga wannan tambaya kafirci ne domin tamkarnuna kyama ne ga tambayar da ta fito daga bakin manzon Allah, (SAW). Haka dai malam Albani ya ci gaba da bayani irin na kariya ga akidar salafiyya kamar yadda akasanshi da wannan aiki. Amma da yake ya tsawaita bayani game da tambaya ta biyu a kebe wannan shi ya bada damar da wasu ‘yan bidi’a suka yi amfani da ita na yanko abin da suke da sha’awa gare shi a cikin bayanisa wanda  shi ba shi ne manu farsa ba wanda ta sanadiyyar haka ne masu wannan kasida suka tsinto maganar ba tare da komawa asalin littafen ba wanda a sanadiyyar hakan ya sa suka sha talalabiya.  Wannan shi ne, zaton da nayi zuwa garesu da farcewa idan suka sami ganin wannan littafe za su gaugauta duba shi a karo na biyu don su gane kurensu na abinda suka jingina malamAlbani (RA) dashi. Haka kuma duk mai sha’awar ya san ingantacciyar akidar Albani kuma ya gano cin mutuncin da aka yi masa na jingina shi ga yin tafwili da tawili ga siffofin Allah to ya ratsi littafensa ta hanyar karanta su kuma ya saurari kasusuwan wa’azojinsa, kuma ni ina da littafensa fiye da littafin da kasusuwansa fiye da dari.     

[131] Mukhtasarul uluwwi lil Aliyil Gaffar, shafi 22.

[132] Duba littafen da ya gabata shafi, 23-226.

[133] Duba littafe da sunansa ya gabata.

[134] Allah ya san kome ga halittunsa, su kuwa ba su iya kewayewa da sanin kome game da shi. (sheikh Gumi).

kafofi:

shafin intanet na saidul fawa id

Nau'uka na ilmi: