HANYOYI MASU FA’IDANTAR DA SAMUN KYAKKYAWAR RAYUWA

nau, i

Yayibayanin yadda mutumzaisamuingantacciyarrayuwa a nan duniyada kumalahira.

Download
karubuta zuwaga shugaba wannan shafi

karin bayani

HaNyoyi masu fa'idantar Da SAMUN kyakkyawaR rayuwa

>Hausa <الهوسا -

Sheikh Abdurrahman dan Nasir Assa'adi.

—™

Translator's name: Isah Zubairu

Reviser's name: Aliyu Muhammad Sadisu

GABATARWAR WAN DA YA DUBA.

Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga ma'aikn Allah Annabi Muhammad (ﷺ‬) da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya.

Bayan haka:

Wannan littafi yana bayani ne akan hanyoyin da mutum zai bi domin samun ingantacciyar rayuwa, wacce zata amfane shi anan duniya da kuma lahira.

Littafin ya zo ne a daidai lokacin da ake bukatarsa, domin damuwa wasuwasi kuncin rayuwa… sun yi wa al'umma katutu, kuma littafin ya zayyano hanyoyin da al'umma za su bi domin kaucewa wadannan tashin hankalin da kuma yadda za su sami ingantacciyar rayuwa, Allah ya azurta mu da ita.

Mawallafin wannan littafi shi ne Shehin malamin nan Nasir Assa'adi wanda an kawo takaitaccen tarihin sa a wannan littafin, wanda kuma ya fassara mana littafin daga harshen Larabci zuwa Hausa shi ne dan'uwa malam Isa Zubair.

Allah madaukakin sarki ya saka musu da alheri, amin.

Wanda ya duba fassara.

Aliyu Muhammad Sadisu,

Minna – Nigeria.

[email protected]

بسم الله الرحمن الرحيم

Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai.

Takaitaccan Tarihin Mawallafi

Wannan risalar wacce ke gabammu ta na kunshe da wasu al'amura masu fadi domin samun rabo na hakikani, wanda mutum ke nema, kuma ita risalar tana nesa daga karkata ta mutum, kuma ta dogara a rubun ga wasu al'amura a bisa ga dalilai masu karfi daga Alkur'ani mai girma da kuma bayanin Annabi ﷺ‬ mai hikima, kuma ita da kanta ita ce wacce mutum mai mumini ke buri, kuma zamantakewa ta mummunai ke rayuwa da ita, domin ita ce hanya guda ga tsarin tafiyar da rayuwa abisa ga jin tsoron Allah da kuma neman yardarsa.

Kuma marububucin wannan Risalar shi ne Shehun malami Abdurrahman dan Nasir dan Abdullahi, daga cikin dangin sa'ad. Wanda aka haifa a birnin Unaiz dake Kasim a yankin najad a kasar Saudi Arebiya, lyayansa sun rasu alokacin yana karami sai dai ya kasance yana da kaifin fahimta da zurfin tunani da kuma kwadayin nema ilimi, hakika ya fara haddar Alkur'ani da wurin tun yana yaro harya kammala haddar ya kuma gyara haddar a lokacin yana da shekaru goma sha biyu a rayuwansa, sai ya fara neman wasu ilimomin na addini daga malaman kasarsa da kuma wasu da suka zo kasar, ya yi matukar kokari a wannan tafarkin na neman ilimi har ya samu rabo da kaso mai girma na ilimomi masu yawa.

Ashekara ta ashirin da uku ya hada neman ilimi da kuma karantarwa da bincike wanda ya ci gaba da yin haka har karshen rayuwar sa, hakika malamai da dama sunyi karatu a gaban shi sun kuma amfana da iliminsa.

Daga cikin malamansa akwai:

(1) Shehun malami lbrahim dan Hamd dan Jasir, wannan shi ne ya kasance malamin sa na farko.

(2) Shehun Malami Salihu dan Usman, Alkalin Unaizah ya karanci Usul da kuma Fikhu da Tauhidi da Tafsir da Larabci ya kuma lizimce shi zuwa rasuwarsa, kuma Shehun malamin ya kasance ya lakanci ilimin Usul da Tauhidi da kuma fiqhu da wadacciyar wayewa game da Tauhid, kuma ya shagaltu da littattafai da aka aminta da su, kuma ya bada kulawa ta musamman ga littattafan lbnu Taimiyyah da Ibnu Kayyim, kumar yadda ya kasance ma aboci kulawa sosai game da tafsir da fanoninsa sai ya karance shi har ya zamo gwani acikin shi ya kuma kyautata shi ya zamanto fitace acikin sa.

Yana da wallafe -wallafe a Tafsir kamar haka :-

1- تيسير الكريم الرحمن في تفسير كلام المنان في ثمانية أجزاء.

2- تيسير اللطيف المنان في خلاصة تفسير القرآن.

3- القواعد الحسان لتفسير القرآن.

Kuma daga cikin littattansa da ake matukar bukatar ace ka same su kuma ka amfana da su, banda wadanda aka ambata, akwai:

4- الإرشاد على معرفة الأحكام

5- الرياض الناضرة.

6- بهجة قلوب الأبرار.

7- منهج السالكين وتوضيح الفقه في الدين.

8- حكم شرب الدخان وبيعه وشرائه.

9- الفتاوى السعدية.

10- الحق الواضح المبين بشرح توحيد الأنبياء والمرسلين.

11- توضيح الكافية الشافية (نونية ابن القيم).

12- ثلاثة دواوين خطب منبرية.

Kuma yana da wasu wallafe-wallafen masu yawa a Fiqhu da Tauhidi da Hadisi da Usul da Fatawoyi daban – daban.

Rasuwarsa:

Hakika ya kuma fama da rashin lafiya mai tasnani wanda ya nuna kusantorwar ajalinsa, ya rasu a daren alhamis ashirin da uku ga watan Jumada Sani a shekara ta 1376 da hajirah a birnin Unaizah, kuma ya bar gurbi da bakin cikin mai zurfi a akin zukatan duk wadanda suka san shi, ko suka ji karatun shi, Allah ya yi masa rahama mai yalwa kuma ya amfanar da mu iliminsa da wallafe wallafensa Amin.

Mukaddimar Mawallafin Littafi.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya cancanci dakkan yabo, kuma ina mai shedawa babu abin bauta wa da cancanta sai Allah shi Kadai yake ba shi da abokin ta rayya. Kuma ina shedawa lalle Annabi Muhammad ﷺ‬ bawana sa ne kuma manzon sa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da Iyalansa Sahabbansa.

Bayan haka lalle hutun zuciya da farin cikinsa da gushewar damuwa da bakin ciki su ne abin nema ga kowani mutum, kuma da shi ne ake samun rayuwa mai dadi kuma ake samun farin ciki da murna, a cikin samun haka akwai wasu sabubba na addini da wasu sabubba na dabi'a da kuma wasu na aiki, kuma ba zai yiwu su haduba face sai ga masu Imani, amma ka ga wadanda ba su ba to koda sun same su ta wata fuskar da wani sababin da su ka yi kokarin samun sa to ta kubuce musu ta wasu fuskokin da suka fi amfana kuma suka fi kyawun hali da makoma.

Saidai ni zan ambata a cikin wannan Risalar (takaitaccan littafi) abin da ya zo min na sabubba ga wannan babban abin nem , wanda kowa ke kokari don samun sa.

To daga cikin mutane akwai wadanda suka samu kaso mai yawa sai suka yi rayuwa mai sauki kuma suka rayu rayuwa mai kyau, kuma daga cikinsu akwai wanda ya rasa su baki daya sai ya rayu rayuwa ta kunci da tsanani, kuma daga cikin su akwai wada yake tsatsaki gwargwadon abin da aka da tar da shi, Allah shi ne mai datarwa kuma wanda muke neman taimakonsa abisa ga dukkan alheri ya kuma tunkude mana dukkan sharri.

**** ***** *****

Fasali:

Mafi girman sabubban kuma asalinsu wato tushensu, Shi ne imani da aki na kwarai

1- Mafi girman sabubba akan haka kuma wanda yake shi ne asali wato tushen samun kwanciyar hankali, shi ne imani da kuma aiki na kwarai Allah madaukaki yana cewa:

ﭽ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﭼ النحل: ٩٧

Ma'ana: “Dukkan wanda ya yi aiki na kwarai na miji ne ko mace alhali ya na mai imani to za mu rayar da shi rayuwa mai dadi kuma zamu saka musu da ladansu da mafi kyawun abinda suke aikatawa". Suratun Nahl, aya ta:97.

Sai Allah madaukakin sarki ya bada labari ya kuma yi alkawari ga duk wanda ya hada tsakanin imani da aiki nakwarai da cewa zai bashi daddadar rayuwa, anan gidan duniya da kuma sakamako mai kya nan gidan duniya da kuma gida na har abada (wato aljanna).

Kuma sababin haka a fili ya ke, domin masu imani da Allah ingantaccan imani wanda ke gadar da aiki nakwarai mai gyara zukata da dabi'u anan duniya da lahira a tare da su akwai turaku da jijiyoyi suna karbar dukkan abinda ya zo musu na sabubban farin ciki da annashawa, da kuma sabubban bacin rai da damuwa da bakin ciki.

Saidai kuma suna fata daga Allah irin abin da su ba fata Suratun (Nisa'i :104)", kuma yana samuwa a garesu na taimakon Allah da dadin falalarsa abinda ke tunkude ababen tsoro, kuma Allah madaukaki ya ce:

ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ الأنفال: ٤٦

Ma'ana: “Kuma ku yi hakuri Lalle Allah yana tare da masu hakuri." Surtul Anfal, aya ta: 46.

2- Kyautatawa Halittu; yana daga cikin sabbuba masu kawar da damuwa da bakin ciki, kuma nau'ukan ayyuka na gari dukkansu alheri ne kuma kyautatawa ne, kuma da su ne Allah ya ke tunkude damuwa da bakin ciki daga mutum na gari da kuma fajiri, sai dai mumini ya fi samun rabo mai girma da kyauta, domin shi kyautatuwarsa ta fitone daga ikhlasi da fatan neman lada a wajen Allah, sai Allah ya sawwaka masa aikin alheri domin abinda yake fata na alheri, ya kuma tunkude masa abin ki saboda ikhlasin sa da fatan lada, Allah madaukakin sarki ya ce:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭ ﭼ النساء: ١١٤.

Ma'ana: “Babu alheri a cikin yawancin ganawarsu face wanda ya yi umarni da ayi sadaka ko alheri ko yin sulhu a takanin mutane, to duk wanda ya aikata haka don neman yardan Allah da sannu za mu bashi lada mai girma." Suratun Nisa'i, aya: 114.

Sai Allah madaukin sarki ya bada labarin cewa dukkan wadannan al'amuran alheri ne ga wanda suka fito daga gareshi, kuma alheri yana jawo alheri yana kuma tunkude sharri, kuma cewa mumini mai kwaunar lada Allah zai bashi ladan sa mai girma, kuma yana daga cikin lada mai girrma gushewar damuwa da bakin ciki da wahalhalu da makamantan su.

**** ***** ****

Fasali:

Abubuwan da suke zama sababi na kauda damuwa mai tasowa daga jijiyoyi da yadda zuciya take shagala da wasu abubuwa na bacin rai.

1. Yana daga cikin sabbuban tunkude damuwa mai tasowa mutum ya shagaltu da ayyuka ko ilimi amfani, domin suna shagaitar da zuciya daga barin al'amarin da ya dameta, kuma ma wani lokaci shi kansa, bayayin duba zuwa ga wanda ke samansa kuma sau dayawa murnsa da farincikin sa zai karu abisa ga wanda ya ke ya samu, dukkan ababen nemansa a duniya idan ba'a bashi nasa ba.

Kamar yadda zaka sami wannan wanda baya aiki da hukuncin imani babu wani aiki a tare da shi idan aka jarrabe shi da talauci ko rasa sashen wani abin nema na duniya, zaka same shi a matukar hasara da tabewa.

Wani misalin daban idan sabubban tsoro suka auku masifu suka dami mutum zaka sami mai ingantacen imani yana da tabbatacciyar zuciya, kuma hankalinsa a kwance, yana mai iko akan juya shi a cikin sauki wannan al'amarin da ya same shi, da abinda zai iya na tunani da magana da kuma aiki sai zuciya sa ta natsuwa ga wannan bala'in da ya fada mata, wadannan da wasu halaye ne masu hutar da mutum da tabbatar da zuciyarsa.

Kamar yadda zaka sami mara imani da akasin wannan hali, idan abubuwan tsoro suka auka masa sai zuciyar sa ta takura kuma gabobinsa su murtsike, tunaninsa su murtsike ya kuma tarwatse, tsoro da fargaba su fada masa, kuma tsoro na ciki da shakka na ciki wanda ba za'a iya sinfanta su ba, wannan nau'i na mutane idan sashin wasu sabubba na dabi'a wacce ke neman a kwatanta ta, sau dayawa sai karfinsu ya yi rauni kuma gabobin su ki karba, kuma haka na samuwa ne domin rasa imani wanda shi ne zai sa su suyi hakuri na musamman alokatan kunci da halaye na bakin ciki da damuwa.

To mu sani mebin Allah da kuma fajiri da mumini sannan da kuma kafiri suna yin tarayya a wajan samun gwarzantaka ta jiki da kuma siffa wacce ta sawwaka da rage ababan tsoro, sai dai mumini da kafiri suna yin tarayya a wajan debo gwarzantaka ta jiki da kuma siffa wacce ta sawwaka da rage ababan tsoro, sai dai mumini yakan kebanta da wasu al'amura a sakamakon karfin imani da hakuri da dogaron sa ga Allah da fatan ladansa wadanda suka kara masa gwarzantaka kuma suke sawwaka masa tsananin tsoro suna sawwaka masa masifu kamar yadda Allah madaukaki yace:

“Idan kun kasance kuna jin radadi to ai su ma suna jin radadi, kuma kuna fata daga wurin Allah abinda su ba sa fatan shi". (Nisa'i:)

Ya samu gareshe da kwanciyar hankali, da gushewar damuwa da kuma gushewar bakinciki da shakka da kuncin zuciya da warakar rayuwa har rayuwa mai dadi ta cika a gareshi a wannan rayuwa ta duniya.

Kuma dayan yana karbar abubuwan takama da wuce iyaka, sai halayensa su baci ya kuma aikata su kamar yadda dabbobi suke aikatasu, da zari da kuma handama, kuma dudda haka shi ba mai natsattsiyar zuciya ba ne a'a shi a daddatse ya ke ta bangarori masu yawa, adatse yake ta jihar tsoro daga gushewar ababen da yake son su, da kuma bujere – bujere masu yawa dake haifuwa daga garesu amafi yawan lokaci, da kuma bangaren cewa lalle ita zuciya ba ta tsayawa 'yaka a' a ba za ta gusheba tana bukatar wasu alamura na daban, kuma wani lokaci sukan auku wani lokaci kuma basa aukuwa, kuma idan suka auku abisa ga kaddarawa to shi ma kunci ne ta bangarori da aka ambata, yana karabar abubuwan ki da kunici kuwa, tsoro, da bakin ciki, kada ka yi tambaya game da abinda ke faruwa a gareshi na tabewar rayuwa, da cututukka na tunani, da tsoro wanda zai kwashi mafi munin halaye da mafi firgicin al'amura, domin shi baya fatan wani lada kuma ba shi da hakurin wanda zai lallashe shi kuma ya sawwake mishi, shi kuma dukkan wadan nan an gansu ta hanyar gwadawa, misalin mutum wanda yake cikin wannan nau'in idan ka kula da shi kuma ka sanya shi a bisa ga halin mutane za ka ga banbanci mai girman gaske tsakanin mumini mai aiki da abinda mahalicci ya hukunta da kuma tsakanin mutimin da ba haka yake ba, kuma shi ne lalle addini yana kwadaitawa mutukar kwadaitarwa a bisa ga kana'a game da arzikin Allah da abinda ya bawa bayi na falalarsa da karamcinsa masu yawa.

To munmuni idan aka jarabeshi da rashin lafiya ko talauci ko makaman cin haka na daga manufofi wanda kowanne mutum sukan bujuro mishi, to lalle shi da imanin sa da kuma abinda ke gurinsa na kana'a da yarda gameda abinda Allah ya raba masa za ka same shi mai sanyin idanu ba ya neman wani al'amari a zuciyarsa wanda ba shi da ikonsa, yana dubane zuwa ga wanda ke da murna da kuma sabubban kunci da damuwa da bakin ciki, suna tarbar ababen so da masu sa farin ciki ta hanyar karbar su da yi wa Allah godiya akan su, da yin amfani da su a cikin abinda yake da amfani, idan suka yi amfani dasu a wannan fuskar sai ya haifar musu da farin ciki da kwadayin tabbatuwarsu da albarkarsu da fatan idan masu godiya da wasu al'amura musa girma wadanda alherin su da albarkarsu sai su samu fifiko wanda shi ne saka makon.

Kuma suna karbar ki dama masu cutarwa da damuwa da bakin ciki ta hanyar daidaita su da abinda zai yiwu adaidaita, da kuma sawwake abinda zai yiwu a sawwake shi, da kyakkyawan hakuri ga abinda ba su da makawa a gareshi, kuma da haka ne zai yi sabo da karfi, da abinda ya shafi hakurin da neman lada wadanda abubuwa ne masu radadi da za su rage zafi da su, sai farin ciki da buri mai dadi ya fada mahalinsu da kuma kwadayi a cikin falalar Allah da ladansa, kamar yadda Manzon Allah ﷺ‬ ya fada a cikin ingantaccen Hadisi;

“Akwai abinban mamaki ga al'amarin mumini, lalle al'amarinsa bakidaya alheri ne; idan yalwa ta same shi sai ya yi godiya, idan kuma abin ki ya same shi sai ya yi hakuri sai haka ya zama masa alheri, kuma hakan ba ya samuwa ga kowa sai ga mumini". Muslim ne ya ruwaito shi.

Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bada labarin cewa lalle ribar mumini da alherinsa da ladan ayyukansa suna ninkuwa cikin dukkan abinda auka masa na alheri ko sharri, don haka zaka samu mutum biyu wani abu zai fada musu na alheri ko na sharri sai dayansu ya dara dan'uwansa lada kuma haka na samuwa ne gwargwadon fifikon su a imani da aikata aiki na kwarai.

Kuma wannan da aka siffanta da wadannan siffofi guda biyu yana karbar alheri da shirri da abinda muka ambata na hakuri da godiya ga Allah da abinda yake biyo masu, sai farin-ciki ya samu ya manta sababin da ya samar masa da damuwa da bakin-ciki, sai ransa ya cika da farin-ciki, kuma nishadinsa ya karu, kuma wannan sababin harwayau abin tarayya ne tsakanin munini da waninsa, sai dai mumini ya kan banbanta da imanin sa da ikhlasa da kuma fatan ladansa a shagaltuwar sa da wannan ilimin da ya ke nema ko yake bayarwa, kuma ya aikata alheri wanda yake sanin sa idan ya kasance shi mai ibadah ne, idan kuma ya kasance wani shagali ko al'adah ta duniya sai kyakkyawar niyyar ta mai da ita mai amfani, kuma ya yi nufin neman taimakon Allah akan hakan yi masa biyayyah, to a haka akwai tasiri mai karfi cikin tunkude damuw da bakinciki, sau dayawa za'a jarrabi mutun da damuwa da yawan bacinrai, sai cutututka daban daban sukan fada masa bacin-rai kuma ya dame shi a sakamakon shagaltuwarsa da wani muhimmin al'amari, kuma ya kamata clikni da zai shagaltu cikinsa ya zama daga clbin da zai samu natsuwar zuci ne domin wannan ya fi kira zuwa ga warman manufa mai anfani, Allah shi ne mafi sani.

(1) Yana daga cikin abinda ake debe damuwa da bakin ciki dashi haduwan tunani dukkannin sa akan aikin yau da katse shi daga barin himmantuwa game da lokaci na gaba, da kuma yin bakinciki akan lokacin da ya wuce, kumo don wannan manzon Allah ya nemi tsari (ﷺ‬) damuwa da bakinciki, to bakinciki akan qlamuran da suka shude wadanda bazai yiwusu dawo ba ko acin musu, da damuwa wanda shi kuma yanafaruwa a sababin tsoro a nan gaba, sai bawa ya zamanto dan yi minsa, yana tara kokarinsa da kwazonsa a cikin haka yana wajabta cika aiyyuka, kuma bawa zai debe kewa dashi daga barin bakin ciki da damuwa, kuma Annabi (ﷺ‬) Idan yayi wata addu'a ko ya nunawa alummarsa zuwa ga wata addu'a to shi ya kwadeturwa tare da neman taimakon Allah da fata cikin falalarsa abisa ga kokarida kwazo ciki tabbatarwa ga samuwar abinda yake rook ga samuwasa, da wofintuwa game da abinda ya kasance yana rook ga tunkude shi, domin shi addu'a ya gwame da aiki, to shi bawa zai donga kokari cikin abinda zai amfane shi acikin addini da kuma duniya, kuma ya roki Ubangijin sa basarar bukatansa, kumaya nemi taimakonsa akan haka, kamar yanda mazon Allah tsira da amincin. Allah su tabbata a gareshi yace (Kayi kwadayi abisa ga kuma Idan wani abu ya sameka to kada kace: da ace ni nayi kaza to da kaza da kaza ya kasance sai dai kace, kaddarar Allah ce kume abinda yaga dama ya aikata, domin Ita da ace tana bude aikin shedan. (Muslim ne ya rawaitoshi) sai mazon Allah ya hada umani da kwadetarwa a bisa ga alamura masu amfani acikin kowani hali, da neman taimakon Allah da rashin biyayya ga kasawa wanda she ne kasala mai cutarwa, da kuma tsakanin alamura da suka wuce, da kuma duban kaddarar Allah da hukuncinsa.

Sai ya sanya alamura kasha biyu: Akwai kashin da bawa zaiya samu ko samun wani abu daga cikin sa, ko tunkude. Shi ko sauwake shi, to wannan bawa zai bayyana kokarinsa acikin kuma ya nemi taimakon abin bautar sa. Da kuma kashin da bawa ba zai Iya samu ba, to wannan bawa zai natsu, ya yarda ya kuma sallama gareshi, kuma babu kokwanto lalle kulawa da wannan a salin sababi ne ga farinciki da gushewar damuwa da bakinciki.

**** **** *****

Fasali:

Samun mafi girman sababi na fadin kirji da natsuwa.

(2) Yana daga cikin mafi girma sabbuba ga fadin kirji da samun natsuwa (yawaita ambaton Allah) domin lalle ga haka akwaitasiri mai burgewa a cikin fadin kirji da samun natsuwa da gushewar bakin-cikinsa da damuwarsa Allah madaukaki ya ce ku saurara: da ambaton Allah ne zukata ke samun natsuwa). (Suratur Ra'ad 28). To ga ambaton Allah akwai tasiri mai girma cikin samuwar wannan abin nema a karakansa, kuma don abinda yake fata na ladansa.

(3) Kuma haka kuma bayarda labari game da ni'imomin Allah na bayyane da boye, domin saninsu da kuma bada labarinsa, Allah yana tunkude damuwa da bakin-ciki wadanda su ne mafi daukakan matakai ku mafi daraja harma da bawa ya kasance a halin talauci ko rashin lafiya ko wanin su, daga cikin naui'n bala'i, domin idan ya kwatanta tsakanin ni'imomin Allah wadanda ba su da adadi da tsakanin abinda ya same shi na abinda ba ya so, to wata dangantaka ba zata kasance ba ga abinda ba ya so zuwa ga ni'ima.

A abinda ba ya so da masifu idan Allah ya jarrabi bawa da su, kuma ya yi hakuri ya yarda ya sallama ga hukuncin Allah sai fuskantarta ta yi sauki dawainiyar ta ya ragu, kuma idan lurar mutum ga ladanta da bautawa Allah ta hanyar tsayuwa da aikin hakuri da yarda suka kasance sai ya mayar da mai daci mai zaki kuma zakin ladarta ta mantar da shi dacin hakurinta.

(4) Yana daga cikin mafi amfani abubuwa a wannan maudu'in yin amfani da abinda Annabi (ﷺ‬) ya yi nuni zuwa gareshi a cikin Hadisi Sahihi, ayayin da ya ke cewa:

(Ku yi duba zuwa ga wadanda ke kasa da ku, kuma kada ku yi duba zuwa ga wadanda ke samar daku. Domin shi ne ya fi cancantan kada ku rena ni'imar Allah a gareku". (Bukari da Muslim) ne suka rawaito shi.

Domin shi bawa idan ya sanya wannan ka'idar mai girma a tsakanin idanun sa, to sai ya ga cewa shi ya dara mutane da dama cikin lafiya da abinda ke biye da ita da kuma arziki da abinda ke biye da shi, ko awani halin ma ya tsinci kansa sai damuwar sa da bakin-cikinsa su gushe kuma faricikin sa da rufin asirinsa game da ni'imomin Allah su karu wadanda sun fi wanin sa a cikinsu, na daga wanda bai kashe ba a cikinsu.

Kuma a kowannne lokaci bawa ya yi la'akari da ni'imomin Allah na bayyane da na boye da kuma addini da na duniya zai ga cewa lalle Ubangijinsa ya ba shi alheri mai yawa, kuma ya tunkude masa sharri da dama, kuma babu kokwanto cewan wadannan suna tunkude bakin-ciki da damuwa, ya kuma tabbar da natsuwa da farinciki.

**** **** ****

Fasali:

A kan sabbuba masu samar da farin-ciki da gushewar damuwa da bakin-ciki.

Yana daga cikin sabubba masu samar da farin-ciki da kuma gusar da damuwa da bakin-cikin: Yin kokari wurin gusar da sabbuba masu jawo damuwa, da kuma kokarin jawo sabbuba masu kawo farin-ciki. Hakan na samuwa ta hanyar mance abinda ya gabata na abubuwan ki wadanda ba zai yi wu ga mutum ba ya tunkude su, da sanin sa cewa shi shagaltarwa ne sai ya ki shi daga cikin babin wasa, da kuma abinda ba zai yi wu ba, kuma cewa Lalle hakan shirme ne da kuma hauka ya dorawa kansa tunanin hakan, kuma kamar haka zai yi kokarin cireta daga zuciya don cimma burin nan gaba saboda abinda yake zato na talauci ko tsoro ko wanin su, daga abubuwan ki wadanda yake zaton su a nan gaba cikin rayuwarsa, sai ya sani Lalle al'amura masu zuwa ba a san abinda zai faru a cikinsu ba na alkairi ko na sharri da kuma burace-burace da kuma radadi na cewa suna hannun mabuwayi mai hikima, babu komai wurin tabbatar da alkairan su, da tunkude cutarwarsu, kuma bawa ya sani lalle shi idan ya juyar sai ya ki daga zuciyarsa don al'amarin da yake fuskanta, kuma ya dogara bisa ga Ubangijinsa, sannan kuma ya natsu zuwa gareshi, to idan ya taikata hakan zuriyarsa za ta natsu kuma halayensa za su yi kyau, sai kuma damuwarsa da bakincikinsa su gushe.

(9) Yana daga cikin mafi amfanin kulawa da al'amura masu? Zuwa amfani da wannan addu'o'in wadanda Annabi (ﷺ‬) ya kasance yana rokon Allah da su:

(10) ((Ya Allah ka gyara mini addini na wanda shi ne igiyar al'amarina, kuma ka gyara mini duniyata wacce take rayuwata ke cikinta, ka kuma gyara mini lahirata wacce zuwa gareta ne makomata take, ka kuma sanya rayuwata ta zamanto karuwa ce agareni cikin dukkan alheri, mutuwa kuma ta zama hutu gareni cikin dukkan sharri)). (Muslim).

(11) Kuma kazalika fadarsa: ((Ya Allah rahamarka nake fata, to kada ka wakilta ni zuwa ga karankaina daidai da kiftawar ido, ka kuma gyara mini sha'anina duka, babu abin bautawa da gaskiya sai kai)). (Abu Dawud ya rawaito shi da Ingantacce Isnadi). To idan bawa ya dage da yin wadannan addu'o'in wadanda a cikinsu akwai neman gyaruwar addininsa da kuma duniyarsa, ya yi kuma da zuciya halartacciya, da niyya ta gaskiya tare da kokari cikin abinda ya roka kuma ya yi fata, ya yi kuma aiki donshi, sai damuwarsa ta juya zuwa farinciki.

**** **** ****

Fasali:

Cikin mafi amfanin sabbuban gushewar damuwa da takura idan masibu suka fadawa bawa.

(12) Kuma yana daga cikin mafi amfani sabbuba ga kawar da damuwa da takura idan masifu suka fadawa bawa: Ya yi kokari cikin sawwaka su ta yadda zai kaddara mafi munin halaye wadanda al'amarin zai iya kaiwa garesu, kuma ya yi iya karfinsa akan haka, to idan ya cikata a haka to ya yi kokari wajan sawwaka su saboda abinda zai yi wu gwargwado ya yi su, to da wadannan karfafa da kuma wadannan sawakaka mai amfani bakin cikinsa da damuwarsa zasu kau, sai sabanin hakan ya kasance a gareshi, watau yin kokari wajan jawo amfani da kuma tunkude cututtuka masu sauki ga bawa.

Idan sabbuban tsoro suka fada masa da sabbuban cututtuka da kuma sabbuban talauci da rashi na abubuwan da yake so daban-daban to ya rungumi haka ta hanyar natsar da zuciya da karfafata akan haka, a duk tsananin dake yi wuwa daga cikinsu to karfafa kai abisa ga daukan abubuwan ki ya saukaka kuma yana gusarda tsananinta, musamman idan ya shagaltar da kansa da tunkude su gwargwadon abinda zai iya, sai ya hadu a hakkinsa da karfafa kansa tare da kokarin amfani da wadanda zai shagaltar daga barin himmantuwa da masifun, kuma ya takura wa kansa abisa ga sabon karfinsa wanda ke mikar da abubuwanki tare dogaronsa ga Allah a kan haka, da kyakyawan aminta da shi kuma babu kokwanto lalle a wadannan al'amuran suna da fa'ida mafi girma kan samar da farnciki da kuma kwantar da zuciya tare da abinda bawa yake buri na lada ayanzu da nan gaba, kuma wannan abu ne da aka gani aka jarraba, kuma farawarsa yana ga wanda ya dandane su masu yawa ne kwarai.

**** **** ****

Fasali:

Cikin mafi girman magunguna ga cututtukan zuciya dana jikkuna.

(13) Yana daga cikin mafi girman magunguna ga cututtukan zuciya masu tsanani, kai harma da cututtukan jiki: Karfin zuciya da rashin takuruwarsa ga yawan zato da rudu, wadanda mumunan tunani suke kawowa, domin shi mutum duk lokacinda ya mika wuya ga rudu kuma zuciyarsa ta saba da abubuwa masu tasiri na tsoro daga cututtuka da wanin su da kuma daga fushi da damuwa na sabubba masu radadi da tsoron aukuwan abubuwan ki da abubuwan hakan sai ya jefa shi cikin bakin ciki da damuwa da cututtuka na jiki da kuma na zuciya, da makalkalewa wani ra'ayi wanda ke da gurabunsa mummuna wadanda mutane suka ga ire-iren cutarwar su masu yawa.

(14) Kuma koda yaushe zuciyar ta dogara ga Allah, kuma bai sallamawa yawan zatonsa ba, sannan kuma wasuwasi bai mallake shi ba, ya kuma aminta da Allah, yana kuma fata a cikin falalarsa, sai damuwa da bakin-cikinsa su yaye, cututtuka na zuciya da na jiki su bar shi, sai zuciya ta samu karfi da fadin kirji, wadanda ba za a iya kwatantawa ba, sauda dama asibitoci sukan cika da marasa lafiya na wadannan damuwa da rudu mara kan gado, kuma sauda dama wadannan al'amuran sun yi tasiri a cikin zukatan majiyyata, ballantana masu rauni, kuma da dama ta sa musu dolonci da hauka. Wanda aka tsare shi ne wanda Allah ya tsare ya kuma datar da shi ga yakar kansa, don tabbatar da sabuba masu amfani masu karfafa zuciya, masu tunkude damuwarsa, Allah madaukaki ya ce “duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isar masa". (Talak 3). Abin nufi zai isar masa dukkan abinda ke damunsa na al'amuran addini ko duniya.

To mai dogara ga Allah mai karfin zuciya ne wahamomi ba sa tasiri acikin sa, kuma abubuwa masu faruwa ba sa firgitashi domin saninsa cewa hakan ya faru ne daga raunin zuciya da kuma kasala da tsoro wanda ba shi da hakika, kuma yana sane tare da wannan lalle Allah ya dauki lamani ga duk wanda ya dogara a gare shi da ba shi isasshiyar kariya, sai ya aminta da Allah kuma ya natsu zuwa ga alkawarin sa sai damuwar sa da bakin cikinsa ya gushe sai tsananin sa ya zamo sauki, bakin-cikinsa kuma ya zamo farinciki, tsoronsa ya zamo aminci. To muna rokon Allah lafiya, kuma ya yi mana falala da karfin zuciya da tabbata da dogaro cikakke wanda Allah ya yi lamani ga ma'abotansa da dukkan alheri da kuma tunkude ko wani bala'i da cuta.

**** **** ****

Fasali:

Game da fadar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi:

(15) “Munini kada ya kyamaci mumina, domin idan ya ki wata dabi'arta to fa zai so wata dabi'ar ta ta". (Muslim ne ya ruwaito).

Ga wasu fa'idoji biyu masu girma: Ta farko: Nunarwa zuwa ga yadda za a mu'amalanci mata da makusanci da aboki da ma'aikaci da kuma duk wanda tsakanin ka da shi, akwai alaka da zumunci, mai hankali ya kamata ka tabbatarwa kanka cewar babu makawa za'a samu aiki acikin sa, ko tawaya ko wata alama dake kinsa, to idan ka samu haka to ka kwatanta tsakanin wannan da tsakanin abinda ya wajaba akanka ko ya kamata a gare ka na karfin saduwa da wanzuwa, da kuma manufofi kebantattu dawwamammu, kuma da wannan runtse idanu daga munanan ayyuka da kula da kyawawan abokai alaka dake dawwama kuma take cika kuma ta tabbata.

Fa'idah ta biyu: Ita ce gushewar damuwa da bakin-ciki da wanzuwar kwanciyar hankali da kuma dawwama akan tsayuwa da hokkoki na wajibi da na mustahabbi, da kuma samuwar hutu tsakanin bangarori biyu, duk wand bai kula da wannan abinda manzon Allah ya fada ba tsira da aminci Allah sutabbta a gareshi y ace ba a'a ya sunkuye hukuncin ne sai ya kallaci lefuffuka ya kuma makance daga abubuwa masu kyau to babu m akawa zaiyi damuwa kuma babu makawa abinda ke tsakaninsa da wanda yake saduwa dashi zai gurbace, kuma hakkoki da dama su katse wandada ke akan kowanne daga cikin su.

Kuma akwai mutane da yawa masu karfin himma sukan tilastawa kansu yin hakuri da samun natsuwar zuciya a yayin aukuwar bala'i da abubuwan damuwa. Amma a wurin wasu al'amura marasa daraja kanana sai su dunga bakinciki kuma zuciya ta gurbace kuma sabuba a cikin wannan shi ne cewan su sun dorawa kansu manyan buri sukan kuma rabu da kanana, sai suka cutar da su kuma suka yi tasiri abinda ya shafi hutun su, mai karfin niyya zai dorawa kansa al'amura kanana da manya, kuma ya roki Allah ya taimaka masa akansu kuma ba zai wakilta shi ba ga kansa daidai da kiftawan ido ba, to a wannan lokaci karamin abu zai masa sauki kamar kuma yadda babba zai iya yi masa sauki kuma yawanzu da natsuwar zuciya da kwanciyar hankali a hutunsa.

**** **** ****

Fasali:

Mai Hankalin yana sane cewa Ingatacciyar Rayuwa Ita ce Rayuwar Rabo Da Natsuwa Kuma cewar Ita Gajeruwa Ce.

(16) Game da mai hankali yana sani cewar rayuwa ingantacciya ita ce rayuwar rabo da natsuwa, kuma cewa ita gajeruwa ce kwarai: To bai kamata ba gareshi ya gajarta ta da damuwa da mika wuya ga gurbace-gurbace domin haka ki shiyar rayuwa ce ingatacciya, sai ya yi hakuri mai yawa daga cikin ta, don kada damuwa da gurbace gurbace su kwace masa su, kuma babu banbanci cikin waannan tsakanin mai biyayya da fajiri, sai dai mumini yana da rabo mai girma saboda tabbatar da wannan siffar, da kuma rabo mai amfani anan duniya da kuma lahira.

(17) Kuma ya kamata idan wata damuwa ta same shi ko ya yi tsoron to sai ya kwatanata tsakaninta da ni'imomin da suka tabbata a gareshi na addini da duniya da kuma tsakanin abinda ya same shi na damuwa, to ayayin da ya kwatanta yawan abinda yake da shi na ni'ima to zai bayyana da kuma raunin abinda ya same shi na abinki. Kuma kamar hakadai zai kwatanta tsakanin abinda yake tsoro na aukuwan wani agare shi da tsakanin, da tsakanin farinciki masu yawa sai ba zai bar fariciki mai rauni ya rinjayi babba mai karfi ba, kuma da haka ne damuwar sa da tsoron sa zasu gushe, ya kaddara mafi girman abinda zai kasance na farinciki wadanda zai yi wu su same shi sai ya karfafi kansa ga faruwar haka, idan ya faru, kuma ya yi kokarin tunkude abin da bai auku ba da abinda ya auku ko sawwaka shi.

(18) Kuma yana daga cikin al'amura masu amfani: Ka sani lalle cutarwar muta ne a gareka musamman a munanan maganganu, ba zasu cutar a kai ba, face idan ka shagaltar da kanka acikin damuwa da su. Kuma ta halasta maka yanda zaka mallaki abubuwanda kake ji, to awannan lokaci zata cutar da kai kamar yadda ta cutar da su, idan kuma kai baka damu da ita ba ba zata cutar da kai da komai ba.

(19) Ka sani lalle rayuwarka tana bin tunaninka, to idan ya kansance tunani ne cikin abinda zai dawo maka da alheri, acikin addini ko duniya to rayuwarka mai dadi ce mai rabo, idan kuma ba haka ba to akasin haka ne.

(20) Yana daga cikin mafiya amfanin al'amura da kore damuwa ka lazimtawa kanka cewan ba zaka nemi godiya daga kowa ba face sai daga Allah, to yayinda ka kyautata zuwa ga mai hakki akanka ko wanda ba shi da hakki, ka sani cewa wannan mu'amala ce daga gare shi dan Allah, to kada ka damu da godiyar wanda ka yi wa ni'ima kamar yadda Allah madaukaki ya ce game da hakkin kebabbun bayin sa:

“Abin sani muna ciyar da ku ne don fuskan Allah bamu nufin wani sakamako ko godiya daga gare ku". “Suratu, Insan".

(21) kuma wannan ya kan yi karfi cikin mu'amalar iyali da yara da wadanda alakarka take da karfi da su, to koda yaushe ka lizinta wa kanka kautar da sharri daga barinsu to hakika ka huta, yin riko da abubuwa masu falala kai aiki da su gwargwadon iko banda tsananta wa kai wanda ke haifar da damuwa, kuma ka zamanto tababbe abisa hanyoyin ka na faruwar falala, ta yadda ka shiga hanya lankwasasshiya, kuma wannan yana daga cikin ni'ima kuma rika daga al'amura gurbatattu, al'amura tsarkaka don jin dadi da haka ne tsarkakakken jin dadi zai karu kuma gurbatattun abubuwa su gushe.

(22) Kasanya al'amura masu amfani a gabanka kuma ka yi aiki don tabbatar da su, kada ka yi waiwaye zuwa ga al'amura masu cutarwa don ka kada ka gataltu da haka game da sabbuba masu jawo damuwa da bakinciki, ka nemi hutu da tattara zuciya a bisa ga al'amura masu mahimmanci.

(23) Yana daga cikin al'amura masu amfani: Kayyade ayyuka cikin halinda ake ciki da barin damuwa da lokaci na ga ba, domin su ayyuka idan ba'a kayyade su ba sai sauran ayyuka su taru a gareka, kuma ayyukan nan gaba su dadu a gare shi, sai dabbaka su ya yi tsanani, to idan ka kayyade dukkan komai da lokacinsa zaka zama al'amuran da kake fuskanta da karfin tunani da karfin aiki.

(24) Ya kamata ka zabi ayyuka masu amfani kuma mafiya mahimmci kuma ka tantance tsakanin abinda kake karkata zuwa gareshi, kuma da yadda kake da tsananin kwadayin sa, domin kishiyarsa yana samar da kosawa da damuwa, ka nemi taimako akan haka da tunani mai inganci da kuma shawara, domin wanda ya nemi shawara ba zai yi nadama ba, ka karanci abinda kake nufin aikatawa a natse, to idan maslaha ta tabbata ka dauki aniya sai ka dogara ga Allah, lalle Allah yana son masu dogaro.

(25) Dukkan godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai, kuma Allah ya yi salati ga shugaban mu Annabi Muhammad da iyalansa da sahabban sa.

**** **** ****

kafofi:

Nau'uka na ilmi: