Shiriyar Annabi Yabo Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Shi Gameda Ƙanan Yara Da Matasa

nau, i

Shiriyar Annabi Yabo Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Shi Gameda Ƙanan Yara Da Matasa

Download
karubuta zuwaga shugaba wannan shafi

karin bayani

Shiriyar Annabi Yabo Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Shi Gameda Ƙanan Yara Da Matasa

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa, kuma muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da kuma zunubban ayukkanmu. Duk wanda Allah ya shiryar dashi babu mai ɓatar dashi, kuma wanda duk Ya ɓatar babu mai shiryar dashi. Kuma ina shaidawa babu abin bautawata da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne, Allah yayi daɗin yabo a gare shi da iyalansa da sahabbansa, kuma yayi daɗin aminci, aminci mai yawa.

Bayan haka:

Kuji tsoron Allah -Yã ku bayin Allah- Haƙiƙanin jin tsoro, kuma ku zama a faɗake dashi cikin ɓoyenku da gãnawarku.

Yã ku musulmai:

Allah madaukaki ya sanya wani ƙarfi tsakanin rauni biyu a cikin rayuwa; wannan ƙarfi shine ginshiƙi a cikin rayuwa, kuma ana cin ribarsa a lahira, kuma shekarun samarta sune ƙarfin dake biyo bayan rauni, a cikinsu ne ruruwar azama take, da kuma daukakuwar himma, amfaninsu a cikin tsawon zamuna mai yawa ne, Mutanen Ibrahim -aminci ya tabbata a gare shi- sukace gameda shi:

﴿سَمِعْنَا فَتًى يَذْكُرُهُمْ يُقَالُ لَهُ إِبْرَاهِيمُ ﴾ [سورة الأنبياء: 60]

«Munji wani saurayi yana ambatonsu, ana kiransa ibrahim» [Suratul Anbiya: 60], kuma ya faɗa gameda Yahya -aminci ya tabbata a gare shi-:

﴿وَآتَيْنَاهُ الْحُكْمَ صَبِيًّا﴾ [سورة طه: 12]

«Kuma mun bashi fahimtar littafi da aiki da hukunce-hukuncensa alhãli yana ƙaramin yaro» [Suratu ɗaha: 12], Ibnu Katheer Allah ya jiƙansa yace: «watau: fahimta, da ilimi, da dagewa, da azama, da fuskantar alheri, da duƙufa kansa, da yin ƙoƙari cikinsa, alhãli yana ƙarami, mai ƙarancin shekaru».

Kuma Allah maɗaukaki yace gameda mutanen kogo:

﴿إِنَّهُمْ فِتْيَةٌ آمَنُوا بِرَبِّهِمْ وَزِدْنَاهُمْ هُدًى﴾ [سورة الكهف: 13]

«Lallai su samari ne da sukayi imani da Ubangijinsu, kuma muka ƙara musu shiriya» [suratul kahfi: 13], Ibnu katheer Allah ya jiƙansa yace: «Allah maɗaukaki ya ambaci cewa su samari ne; da sune matasa, kuma sune sukafi karɓar gaskiya, kuma sukafi bin tafarki sama da dattawa, don hakane ya kasance mafi yawan masu amsama Allah da manzonSa matasa ne».

Kuma daga cikin bakwai ɗin da Allah zai sakasu cikin inuwarSa ranar tashin Alƙiyama: «Matashin da ya tãso cikin biyayya ga Allah» (Bukhari da muslim suka ruwaito shi).

Kuma tarihin Annabinmu muhammad –yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- tare da ƙananan sahabbai da matasansu shine mafi girman tarihi, ya ƙanƙan da kai garesu, kuma ya zauna tare dasu, kuma ya ziyarcesu, kuma ya ilmantar dasu, ya ɗaga himmominsu, sai al'umma mafi girma ta fito daga cikinsu.

Yana daga ƙanƙan da kansa -yabo da aminci su tabbata a gareshi-: «idan ya wuce wasu ƙananan yara yana yi musu sallama» (Muslim ya ruwaito shi).

Ibnu Baɗɗal -Allah ya jiƙansa- yace: «Sallamar Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi ga ƙananan yara, yana gada cikin halayensa masu daraja, da ladabinsa maɗaukaki, da ƙanƙan da kansa».

Kuma ya kasance mai tsananin kwaɗayi ne kan koyar dasu, Jundub ɗan Abdullahi –Allah yarda dashi- ya ce: «Mun kasance tare da Manzon Allah –yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- alhãli mu samari ne masu jin ƙarfi – watau: mun kusa balaga-, sai muka koyi imani kafin mu koyi Alqur'ani, sa'annan sai muka koyi Alqur'ani sai muka ƙara samun imani dashi» (ibnu majah ya ruwaito shi).

Kuma ya kasance yana dasa aƙida a zukatansu, Ibnu Abbas -Allah ya yarda dasu- ya ce: «Na kasance a bayan Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- wata rana, sai yace: Yã kai yaro, lallai ni zan koyar da kai wasu kalmomi; ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sãme Shi a gabanka, idan zaka ka roƙa, to ka roƙi Allah, kuma idan zaka ka nemi taimako, to ka nemi taimakon Allah...» Har zuwa ƙarshen Hadisin, (At-tirmizi ne ya ruwaito shi).

Kuma yana tausasawa wajen koyar dasu, ta hanyar nau'antar da hanyoyinsa, wani lokaci yakan kama hannuwansu, Mu'ãzu -Allah yarda dashi- ya ce: Manzon Allah –yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kama hannuna wani lokaci, sai yace: «Lãllai ni ina sonka, sai mu'ãzu yace: kuma nima wallahi ina sonka, Yace: shin bazan koya maka wasu kalmomi ba, da zaka rinƙa faɗarsu a bayan kowace sallarka, yace: eh, Yace: kace Allahumma A'inni ala zikrika wa shukrika wa husni ibadatika» (Bukhari ya ruwaito shi a cikin al-adabul mufrad), wani lokacin yana ɗora tafukansu tsakanin tafukansa, Ibnu Mas'ud Allah ya yarda dashi ya ce: «Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya koyar dani –alhãli tafi na yana tsakanin tafukansa- Tahiya, kamar yadda yake koyar dani sura daga Alqur'ani» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi), wani lokacin yakan kama kãfaɗunsu, Abdullahi ɗan Umar -Allah ya yarda dasu- ya ce: «Manzon Allah –yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kama kãfaɗata, sai yace: Ka kasance a cikin duniya kamar kai bãƙo ne, ko kuma mai ƙetare hanya» (Bukhari ya ruwaito shi).

Kuma saboda tausasawarsa wajen koyarwa sun kasance suna zuwa wurinsa, suna ce masa ka koyar damu, Ibnu Mas'ud -Allah ya yarda dashi- yace: «Nace ya manzon Allah ka koyar dani daga wannan zancen –watau: daga Alqur'ani, sai ya shafa kaina yace: lallai kai yaro ne abin a koyarwa» (Ahmad ya ruwaito shi) sai ya kasance ɗaya daga cikin makarantan wannan al'umma.

Kuma yana haƙuri wajen koyar dasu; Jabir -Allah ya yarda dashi- ya ce: «Manzon Allah –yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana koyar damu addu'ar neman zãɓi cikin al'amura, kamar yadda yake koyar damu surah daga Alqur'ani» (Bukhari ya ruwaito shi).

Kuma yana daga sanya ƙaunarsa a zukatansu da yakeyi; ya kasance yana goya su a baya idan ya hau abin hawansa tare da cewa manyan sahabbai suna nan, «Sai ya goya Usamatu -Allah yarda dashi- kan abin hawa- daga Arfa zuwa Muzdalifa, sannan ya goya Fadlu ɗan Abbas daga Muzdalifa zuwa mina» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Kuma ya kasance yana kwadaitar dasu kan Ibãda, Ya cema Abdullahi ɗan Umar -Allah ya yarda dasu -alhãli shi a wannan lokacin yana yaro-: «Abdullahi mutum ne abin madallah dashi, da dai ya kasance yana sallah cikin dare!, sai Abdullahi ya kasance, bayan haka baya bacci daga dare sai ɗan kaɗan» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Kuma ya kasance yana fuskantar dasu da mafi taushin bayani, yace ma Khuraimunil Asadi -Allah ya yarda dashi-: «Kai mutum ne abin madallah da kai, ya Khuraimu, da ba don wasu ɗabi'u biyu tattare dakai ba, Nace menene su ya manzon Allah? Yace: jan kwarjallenka, da sassautar da gashinka» (Ahmad ya ruwaito shi).

Kuma ya kasance yana tausasa masu, kuma yana tambayar su gameda iyalansu, Mãlik dan Huwairith -Allah ya yarda dashi- ya ce: «Munzo wajen Annabi –yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- alhãli mu muna yan matasa- watau: matasa- waɗanda suke tsarakun juna, sai muka zauna a gurinsa kwana Ashirin, sai ya gane muna shauƙin iyalanmu, sai ya tambayemu wa muka bari don kula iyalanmu, sai muka bashi labari, -kuma shi ya kasance mai tausayi ne mai jin ƙai- sai ya ce: Ku koma zuwa ga iyalanku; ku koyar dasu kuma ku umarcesu, kuyi sallah kamar yadda kuka ganni ina yin sallah» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Kuma Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- alhãli shine babban mutum ne, ya kasance yana ma yara ba`a, Mahmudu ɗan Ar-rabi'u -Allah ya yarda dashi- ya ce: «Na kiyaye lokacin da Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- yayi wata gumtsa ya fesata a fuskata, alhãli ina ɗan shekara biyar, watau:- Annabi –yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya shigar da ruwa cikin bãkinsa, sai ya fitar dashi a kan fuskar yaron, ta fuskar wasa» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Banda haka ma; ya kan tambayesu gameda tsuntsayensu, kuma yana masu alkunya don tausasa masu, Anas -Allah yarda dashi- ya ce: «Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana cuɗanya damu, har yana fadama wani ɗan'uwa na ƙarami, Ya baban Umair! Mai ya faru da Nugair- tsuntsu ne ɗan ƙarami-?» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi). Ibnu baɗɗal -Allah ya jiƙansa- yace: «Ya kasance -yabo da aminci su tabbata a gare shi- yana zolayar yara kuma yana masu wasa, domin ayi koyi dashi cikin haka, cikin zolayarsa ga yara akwai sassauto da rai wajen ƙanƙan da kai, da kore girman kai daga gareta».

Kuma ya kasance yana riƙe su a tare dashi da hannunsa har zuwa gidansa, domin ciyar dasu, Jabir ɗan Abdullahi –Allah ya yarda dashi- yace: «Manzon Allah –yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya riƙe hanuna wata rana izuwa gidansa, sai ya fito masa da wasu gutsuts-tsirin biride watau: karyayyun gurasa» (Muslim ya ruwaito shi).

Kuma idan suka shigo gidan yana masu izini da sauraron maganar da akeyi a gidansa, Ibnu Mas'ud -Allah ya yarda dashi- ya ce: Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce min: «Izininka a gurina, shine a ɗage labule, -watau: idan kaga labulen ƙofa ɗage, to ka shigo ba tare da an baka izini-, kuma ka saurari zancen boye na –watau- sirrina- har sai na haneka –watau: gameda shigowa» (Muslim ya ruwaito shi).

Kuma ya kasance yana ci tare dasu, yana koya musu ladduban abinci, Umar ɗan Abi salamah Allah yarda dasu- ya ce: «Na kasance ƙarƙashin kulawar Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- watau: Renonsa- kuma hannuna ya kasance yana zamewa a cikin akushi –watau: Yana yawo acikin akushin yana kaiwa dukkan ɓangarorinsa-, sai yace min: Ya kai yaro! Ka ambaci sunan Allah, kuma kaci da damanka, kuma kaci daga gabanka» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Kuma yana amsa gayyatar ƙananan sahabbansa da kuma matasansu, Abdullahi ɗan Busr Al-mãzini -Allah ya yarda dasu- yace: «Mahaifina ya aikeni zuwa ga Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi-, domin gayyatarsa zuwa cin abinci, sai ya taho tare dani, a yayin da na kusa zuwa gida sai nayi sauri, sai na sanar da mahaifã na, sai suka fito suka tari Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi-, kuma sukayi maraba dashi» (Ahmad ya ruwaito shi).

Idan labarin rashin lafiyar ɗaya daga cikin ƙananan sahabbansa ya iso gareshi yana zuwa dubashi, Zaidu ɗan Arƙam -Allah yarda dashi- ya ce: «Wani ciwon ido ya sameni, sai Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- yazo duba ni» (Ahmad ya ruwaito shi).

Kuma ya kasance -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana lura da hankaltar kowane ɗaya daga cikinsu sai ya fuskantar dashi da abinda zai amfani kansa da al'ummarsa, Yayinda ya tunkaro -yabo da aminci su tabbata a gare shi- garin Madina, yaga zaidu ɗan thabit -Allah yarda dashi- alhãli shi yana ƙasa da shekaru goma sha biyar, ya iya rubutu, sai ya sanya shi daga marubuta wahayi, kuma ya hangi basira tattare dashi sai ya nemi koyan yaren yahudawa daga gare shi, domin ya fassara masa abinda ake rubutawa a harshensu, Zaidu -Allah ya yarda dashi- ya ce: «Sai na koyi rubutunsu dominsa, kwana sha biyar bata wuce min ba, har sai da na ƙware acikinsa, sai na kasance ina karanta masa rubuce-rubucensu idan suka rubuto gare shi, kuma ina bada amsa a madadinsa idan zai rubuta» (Ahmad ya ruwaito shi).

Kuma ya kwaɗaitar da ƙananan sahabbansa Kan koyon littafin Allah, sai yace: «Ku koyi Alqur'ani daga mutum huɗu: daga ɗan Ummi Abdin –watau: Ibnu Mas'ud-, da kuma Mu'azu ɗan Jabal, da kuma Ubayyu ɗan Ka'ab, da kuma Salim maulan Abu Huzaifa» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Kuma ya kasance yana yabonsu, kuma yana bayyana matsayinsu, ya saurari karatun Salim maulan Abu Huzaifa -Allah ya yarda dashi- alhãli yana yaro ƙarami, mai daɗin murya da karatun Alqur'ani, sai yace: «godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya irin wannan cikin al'umma ta!» (Ibnu Majah ya ruwaito shi).

Kuma Yaga fahimta tattare da Mu'azu -Allah ya yarda dashi-, sai yace: «Mafi saninsu ga halal da haram mu'azu ɗan Jabal» (Ahmad ya ruwaito shi).

Kuma ya kasance yana bayyana soyayyarsa ga ƙananan sahabbansa da kuma matasansu, kuma yana furta musu hakan, domin ya bayyana matsayinsu a gurinsa garesu da kuma wasunsu, Yace gameda Zaidu ɗan Haritha -Allah ya yarda dashi-: «Haƙiƙa yana daga mafiya soyuwar mutane gareni, kuma lallai wannan ma –watau ɗansa Usamatu- yana daga mafiya soyuwar mutane gareni bayansa» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Kuma ya ga yaran mutanen madina da mãtansu sun taho, sai yace: «Allah ya sani cewa; ku ɗinnan kuna daga mafiya soyuwar mutane gareni» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Kuma ya kasance yana addu'a ga ƙananan sahabbai na alheran duniya da lahira, saboda sonsu da karramasu, Ibnu Abbas -Allah yarda dasu- ya ce: «Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi-, ya jawo ni gare shi, sai yace: Yã Allah ka sanar dashi littafi» (Bukhari ya ruwaito shi), kuma yayi Addu'a ga Anas -Allah yarda dashi- da faɗinsa: «Yã Allah ka yawaita dukiyarsa da ƴaƴansa, kayi masa albarka cikinsu» (Bukhari daMuslim suka ruwaito shi).

Kuma ya kasance yana keɓancesu da wasu sirrika banda wasunsu, saboda aminta dasu, -Anas Allah yarda dashi- ya ce: «Annabin Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya sirranta wani sirri gareni, har yanzu ban ba wani labarinsu ba, kuma haƙiƙa Ummu Sulaim-itace mahaifiyarsa- ta tambaye ni gameda shi, ban bãta labarinsa ba» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Kuma ya kasance yana basu amanar manyan al'amura, ya shugabantar da Attab ɗan Asid -Allah ya yarda dashi- ga garin Makkah, sai ya gudanar taron hajji, kuma ya jagoranci musulmai hajji, shekara ta takwas, alhãli shi yana ƙasa da shekara ashirin.

Kuma mafi yawan wanda suka ruwaito hadisin Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- bayan Abu huraira -Allah ya yarda dashi- mutum biyar ne cikin ƙanan sahabbai: Anas, da Jabir, da Ibnu Abbas, da Ibnu Umar, da Aisha -Allah yarda dasu-, dukkansu suna daga ƙananan sahabbai.

Kuma wanda yabo da amincin Allah sun tabbata a gare shi ya kasance yana shãwartar ƙananansu a cikin abinda ya keɓance shi na al'amura masu girma, domin a lokacin da akayi ƙazafi ga Nana Aisha- ya tura zuwa ga Aliyyu ɗan Abi Ɗalib, da Usamatu ɗan Zaidu -Allah ya yarda dasu- a yayinda wahayi yayi jinkiri yana shãwartar su. (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Kuma a majalisarsa yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi yana darajtasu kuma yana ɗaukaka sha'aninsu, tare da cewa manyan sahabbai suna nan: «An kawoma Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- abin sha, sai ya sha daga gareshi, kuma a dama dashi akwai wani yaro, a hagun dashi kuma akwai dattawa, sai yacema yaron: Shin zaka bani izini in fara ba waɗannan?, sai yaron yace: A'a wallahi! Bazan fifita wani ba da rabona daga gareka, sai Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ɗora shi –watau: ya azashi kan hannunsa» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Kuma wanda yabo da amincin Allah sun tabbata a gare shi ya kasance yana ganin girman musiba idan ta sami yãra da matasa, Anas ɗan Mãlik -Allah yarda dashi- ya ce: «Wasu matasa daga mutanen madina mutum saba'in ana ce masu makaranta, sun kasance suna zama a cikin masallaci, sai Annabi ya aike su baki ɗaya, sai aka kashesu a wurin da ake kira rijiyar ma'unah, sai Manzon Allah yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi yayi addu'a kan makasansu har tsawon kwãna goma sha biyar a cikin sallar safiya» (Ahmad ya ruwaito shi, asalinsa hadisin yana cikin Bukhari da Muslim).

Kuma mafi yawan wanda musuluncinsu ya gabata, kuma suka taimaiki Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- a farkon al'amarinsa, shekarunsu tsakanin takwas ne zuwa shekara sha uku, kamar Aliyyu da Ɗalha, da Azzubair -Allah ya yarda dasu-.

Kuma a yayinda Ƙuraishawa suka himmatu da fitar da Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- daga garin Makkah, Al'ansar sunzo daga Madinah, kuma rabinsu duk yara ne, sai sukayi masa mubaya'a a wurin Al'aqabah har sau biyu.

Kuma wanda yabo da amincin Allah sun tabbata a gare shi ya aika yaro matashi zuwa garin madina –a gabãnin yin hijirarsa, yana koyama mutanen garin Alqur'ani, kuma yana fahimtar dasu addini; Mus'ab ɗan Umair -Allah ya yarda dashi-, sai ya sauƙa wurin matashi irinsa As'ad ɗan Zurarah sai ya bashi masauki.

Yayin da Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- yayi azamar yin hijira ya umarci Aliyyu ɗan Abi ɗalib Allah ya yarda dashi alhãli yana matashi ne, daya zauna a gida maimakon yin hijira, har sai ya gabatarwa ya ma mutane haƙƙoƙinsu da ke hannun Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi-.

Kuma a hanyar hijirarsa yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi yara da matasa sun ƙarfafeshi, Abdullahi ɗan Abubakar -Allah ya yarda dasu-; ya kasance yana zuwa masa alhãli yana cikin kogo tareda abokinsa; yana kawo labarin mutanen Makkah zuwa garesu, Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: «Alhãli shi yaro ne matashi, mai saurin fahimta da ɗaukar abinda yaji- watau: Mai basira ne mai saurin fahimta» (Bukhari ya ruwaito shi), kuma Asma'u -Allah ya yarda da ita- ta kasance budurwa ce ƙarama tana ɗaukar abinci da abin sha zuwa garesu.

Yayinda ya isa garin Madinah yaran garin sun tareshi suna masu farin ciki dashi, Al-bara'u -Allah ya yarda dashi- ya ce: «Kuma yara da masu hidima suka rarrabu kan hanya, suna ɗaga murya: Ya muhammadu ya manzon Allah, ya muhammadu ya Manzon Allah» (Muslim ya ruwaito shi).

Kuma yayinda -yabo da aminci su tabbata a gare shi- ya tabbata a cikin Madinah, Sahabban Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- sunyi ta hijira daga Makkah zuwa Madinah alhãli sun kasance matasa ne, Anas -Allah ya yarda dashi- ya ce: «Annabi yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya gabato watau: Madinah-, babu mai furfura –watau: Wanda gashinsa yayi fari- cikin sahabbansa, banda Abubakar» (Bukhari ya ruwaito shi).

Kuma a yaƙin Badar Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya horar da sahabbansa zuwa yaƙi, Ibnu Abbas -Allah ya yarda dasu- ya ce: «Sai matasa sukayi ta rige-rige zuwa gare shi» (Ibnu Hibban ya ruwaito shi), kuma a ranar Hunain matasan sahabbai sun fita babu makami.

Kuma kafin mutuwarsa -yabo da aminci su tabbata a gare shi- ya haɗa wata runduna mai girma domin yaƙar Rumawa a ƙasar Sham, ya shugabantar masu da Usamatu ɗan Zaidu -Allah ya yarda dashi-, shekarunsa sha bakwai da haihuwa.

Saboda mu'amalar Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- ta daban ga yara suka soshi so mai yawa, ya kasance idan ya dawo daga tafiya suna fitowa don tararsa, As-sa'ib -Allah ya yarda dashi- ya ce: «Na fito tare da yara muna tarar Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- zuwa Saniyyatul wada'i –kafar bankwana- a dawowarsa daga yaƙin Tabuka» (Bukhari ya ruwaito shi), Kuma sun kasance suna kwana tare da Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- a cikin gidansa, Rabie'atu ɗan Ka'ab Al-aslami -Allah ya yarda dashi- ya ce: «Na kasance ina kwana tare da Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi-, sai na kawo masa abin alwalarsa da abin bukatarsa, sai yace min: Ka roƙa, sai nace: Ina roƙan abotakarka cikin Aljanna» (Muslim ya ruwaito shi).

Kuma idan sukayi barci cikin gidansa ɗayansu yakan ɗora kansa gurin kan Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- a kan matashinsa, «Ibnu Abbas -Allah ya yarda dasu- ya kwana a wani dare a wurin Nana Maimuna uwar muminai –kuma ita innarsa ce-, ya ce: sai na kwanta bisa faɗin matashin, Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma ya kwanta da iyalinsa bisa tsawonsa»(Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Bayan Haka Yã Ku Musulmai:

Duk sanda ɗabi'un masu girma suka ɗaukaka suna ƙanƙan da kai ga ƙananan yara, yaro an ɗabi'antar dashi ga son wanda ya kusanto shi kuma yake koyar dashi, kuma riskarsa a hadda da fahimta ya kan iya ɗara na manya, kuma Addinin musulunci ya dace da ɗabi'arsu suna sonsa suna son laddubansa da shari'o'insa, da kuma shiriyar Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- tasowarsu kanta, kuma rainasu da kawar da kai daga garesu baya dacewa da halayyar masu hankali.

Ina neman tsarin Allah daga shaiɗan jefaffe

﴿لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَ لِّمَن كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الْآخِرَ وَذَكَرَ اللَّهَ كَثِيرًا ﴾ [سورة الأحزاب: 21].

«Lallai haƙiƙa koyi mai kyau ya kasance gareku acikin al`amarin Manzon Allah, ga wanda ya kasance yana ƙaunar Allah da kuma ranar ƙarshe, kuma ya ambaci Allah dayawa» [suratul Ahzab: 21].

Allah ya min Albarka tare daku cikin Alqur'ani mai girma.


Huduba ta biyu

Dukkan yabo sun tabbata ga Allah kan kyautatawarsa, kuma godiya ta tabbata a gare Shi akan datarwarSa da kuma ni'imominSa, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai bashida abokin tarayya don girmamawa ga al'amarinSa, kuma ina shaidawa Annabinmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, yabon Allah ya tabbata gareshi da iyalansa da sahabbansa, kuma yayi aminci, aminci mai ƙaruwa.

Yã ku Musulmai:

Shiriyar Manzon Allah -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- itace mafi cikar shiriya, kuma hanyarsa itace mafi kamalar hanya, kuma mu'amalarsa itace mafi ɗaukakar mu'amala, yaran yau sune abin burin al'umma, kuma ginshiƙinta, wanda ya nufi alkairi ga masu tasowa to ya lazimci shiriyar Annabi -yabo da amincin Allah su tabbata a gare shi- wajen mu'amalarsa garesu, kuma da kulawarsa ne yabo da aminci su tabbata a gare shi da ƙananan sahabbansa da matasansu ilimi ya koma zuwa garesu, al'umma ta amfana dasu, kuma na daga datarwar Allah ga yara samuwar wani malami garesu da zai ke koya musu Addininsu, kuma ya ladabtar dasu da ɗabi'un Annabawa -aminci ya tabbata garesu-, kuma yana kan majiɓantansu suyi ƙoƙarin samar musu da hakan.

Sannan ku sani lallai Allah ya umarce ku da yin salati da sallama ga Annabinsa...