Malan yayi bayanine akan wasu shubha da wasu suke kafa dalili dasu wajan ayyukan bidi a da sauransu da kuma amsa akan wa ainnan dalilai da ma anoninsu na gaskiya da kuma hukumci maulidi da bayani akan wasu shirka da wasu musulmai ke fadawa acikinsu da bada amsoshi akan tambayoyi bayan kowane karatu.
Wanene ya haliccemu kuma don menene ya haliccemu? Komai na nuna cewa akwai mahalicci wanda Shine Allah, Mai cikan tsarki, Mai sunaye kyawawa da siffofi maɗaukaka, Musulmai sunyi imani da Alƙur'ani da littattafai kafinsa, sunyi imani da bayin Allah manzanni dukkansu cikinsu harda Isa aminci ya tabbata a gare shi, kuma Musulunci shine cikakken miƙa wuya ga Allah da kaɗaita Shi da bauta domin samun tsira, to ka musulunta da gaggawa domin ka rabauta.