Hukuncin Sihiri Da Bokanci

nau, i

HUKUNCIN SIHIRI DA BOKANCI
DA ABINDA YA KE DA ALAKA DA SU

Download
karubuta zuwaga shugaba wannan shafi

karin bayani

Hukuncin sihiri Da Bokanci

da abinda ya ke da alaka da su

Wallafar:

Sheikh Abdul'aziz dan Abdullahi dan Baz

Fassarar

Khadija Ahmad Yahya

Dubawar

Aliyu Muhammad Sadisu

Gabatarwar Wanda Ya Duba

Da sunan Allah mai yawan rahama kuma mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad ﷺ‬ da iyalansa da kuma sahabbansa baki daya.

Hakika wannan littafi na; 'Hukuncin sihiri da bokanci da abinda ke da alaka da su' wanda wannan babban malami kuma imami Abdul'aziz dan Abdullahi dan Baz – Allah ya yi masa rahama- ya wallafa, kuma wannan baiwar Allah malama Khadija Ahmad Yahya ta fassara shi zuwa harshen Hausa, hakika littafi ne mai matukar muhimmanci a kowanne lokaci musamman a wannan lokaci da bokaye da 'yanduba da masu rufa ido da sauransu suka yawaita, kuma a wasu wuraremma su ake kira malamai.

Wannan littafi ya tattauna kuma ya magance wadannan abubuwa, kama daga hukuncin masu asiri da hukuncin wadanda suke zuwa wurin bokaye da 'yanduba.

Malam ya yi bayanin hanyoyin warware asiri da aka yi wa mutum ta hanya shar'antacciya, kuma ya tattauna maganar shigar aljani jikin mutum da kuma fitar da shi wanda malam ya tabbatar da hakan da dalilai na ayoyi da hadisai da kuma maganganun magabata, sannan malam ya tabbatar da rashin ingancin maganar wadanda suke ganin ba hakaba.

Allah ya sakawa wannan malami da alkhairi da kuma wacce ta fassara shi, sannan kuma da duk wanda ya taimaka wurin yaduwar wannan littafi.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma'aikin Allah ﷺ‬ da iyalanshi da kuma sahabbansa baki daya, amin.

Aliyu Muhammad Sadisu,

[email protected]

بسم الله الرحمن الرحيم

Dukkan godiya ta tabbataga Allah Shi kadai, tsirada Amincin Allah su tabbata ga wanda babu wani Annabi a bayansa, bayan haka.

Lura da yawaitar bokaye da su ke ikirarin bada magunguna, su ke kuma yin maganin ta hanyar sihiri ko bokanci, da kuma yawaitarsu a sashin wasu mutane wayanda jahilci ya mamayesu – sai na ga – ya dace – inbayyana hakan ababin yin nasiha don Allah sannan kuma bayin sa, saboda hatsari mai girma – dake cikinnsa – ga addinin musulunci da musulmai saboda abinda ke cikinsa na – ratayuwa ga wanin Allah da kuma sabawa manzonsa.

Kuma lallene mutum musulmi ya tafi wajen likita a rashin lafiya na cikin jiki ko kuma na raunuka ko kuma ko makamantan haka, domin ya bincikan masa rashin lafiyasa, kuma ya yi masa magani na abinda ya dace dashi daga magungunan da suka halasta a shari'ance yadda kima aka san shi a ilimin magunguna, domin hakan yana cikin babin ruko da dalilai wanda aka saba kuma baya nuna cewa ba'a dogara ga Allah ba, kuma hakika Allah ya madaukakin sarki ya saukarda da cuta kuma ya saukar da magani tare da ita, wanda yasan hakan ya sani wanda kuma ya jahilci hakan ya Jahilta, sai dai shi–Allah tsarkakken sarki bai sanya warakar bayinsa cikin abinda ya haramta mu su ba.

Hukuncin Sihiri Da Bokanci Da Abinda Suka Kunsa

Baya halatta ga maralafiya ya je wajan bokaye da suke ikirarin sanin abubuwan da ke boye, wai don ya gano masa rashin lafiyansa, kamar yadda baya halatta ya gasganta su cikin abinda su ka bayar da labarin sa ba, domin su suna maganine ko kuma su kirawo aljanu domin su taimaka mu su akan abinda su ke so, to wadannan hukuncinsu shi ne 'kafirci' idan sun yi ikirarin – ilimin gaibi, hakika Muslim ya ruwaito cikin ingantaccan littafinsa, lallai Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

((من أتى عرافا فسأله عن شيء لم تقبل له صلاة أربعين يوما))

Ma'ana: “Duk Wanda ya je wajan dan'duba sai ya tambaye shi wani abu to ba za'a karbi sallar sa ba ta kwana arba'in". Kuma daga Abuhuraira Allah ya kara masa yarda daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:

((من أتى كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد صلى الله عليه وسلم)).

رواه أبو داود وخره أهل السنن وصححه الحاكم عن النبي صلى الله عليه وسلم بلفظ ((من أتى عرافا أو كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد صلى الله عليه وسلم)).

Ma'ana: “Duk wanda ya je wajan boka sai kuma ya gasganta abinda ya ke cewa, to hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi".

Abu dawud ya ruwaito shi kuma ma'abota littattafan sunnah hudu sun fitar da shi, kuma Hakim ya ingantashi daga Annabi tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi da lafazin:

“Duk wanda ya je wurinan dan'duba ko boka sai ya gaskanta abinda yake cewa to hakika – ya karficewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi".

Kuma daga Imran dan Husaini Allah ya karama sa yarda ya ce: Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce:

((ليس منا من تطير أو تطير له أو تكهن أو تكهن له أو سحر أو سحر له، ومن أتى كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد ﷺ‬)). رواه البزار بإسناد جيد

Ma'ana: “Baya cikimmu duk wanda ya ke yin camfi ko a ke yi masa camfi ko ya yi bokanci ko ake yi ma sa bokanci, ko ya yi sihiri, ko ya sa ayi mishi sihirin, duk kuma wanda ya je wajan boka sai ya gaskantashi a aduk abinda yake cewa to hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi". Bazzar ne ya ruwaito shi da Isnadi mai kyau.

A cikin wadan nan hadisai masu girma akwai hani game da zuwa wajan 'yan'duba da bokaye da masu sihiri (asiri) da makamantansu, da kuma hukuncin tambayarsu da kuma hukuncin gasganta su da bayanin narkon azaba akan haka.

A binda yake wajibi ga shuwagabanni da 'yanhiziba da wasunsu, na daga wadanda su ke da ikon fada aji shi ne su hana zuwa wajan bokaye da 'yanduba da maka mantan su, da kuma hana masu zuwa da wasu abubuwa maka mantan haka a kasuwanni da sauran wurare, da hana mu su zuwa wajan su, kuma baya halatta ka rudu da gaskiyarsu asashin wasu al'amura, ko yawaitan masu zuwa wajensu, hakika su Jahilai ne baya halatta mutane surudu dasu?.

Domin hakika manzon Allah tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hani akan zuwa wajan su da kuma tambayar su da gaskanta su, domin abinda ke cikin haka na muni maigirma da hatsarin da ya ke babba da mumunar makoma kuma domin lallai su makaryatane fajirai, kamar yadda ya ke cikin wadannan Hadisai dalili ne cewa boka kafirine da mai asihiri domin su biyun basu cimma manufar su sai ta hanyan yi wa aljanu hidma da bauta musu koma bayan Allah kuma wannan kafurcewa Allah ne da kuma yi masa tarayya – tsarkakken sarki.

Kuma mai gasganta su cikin abinda su ke cewa na sanin gaibu ya kasance kaman su ne, kuma dukkan wanda ya karbi wadannan al'amura na abinda su ke bayarwa to hakika Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya barranta da shi, kuma baya halatta ga musulmi ya yarda da abinda su ke rayawa cewa magani ne.

Domin lallai wannan yana daga cikin bokanci da rudar da mutane, kuma wanda ya yarda da hakan to hakika ya taimaka musu akan barnarsu da kafircin su.

Hakanan kuma baya halatta ga wani mutum musulmi ya jewajansu – domin ya tambayesu gameda wanda.

Zai aurar da dansa ko wani makusancinsa ko kuma abunda ke iya kasancewa tsakanin ma auratan biyu da danginsu na soyayya da cika alkawari ko kuma kiyayya da rabuwa da makamantan haka;domin wannan yana daga cikin gaibi wanda babu wanda yasansu sai Allah tsarkakke mada'au kaki.

Kuma sihiri yana daga cikin abubuwa haramtattu na kafirci kamar yanda Allah mai girma dad au kaka yace cikin sha'anin mala' I kunnan biyu cikin suratul Bakarah:

﴿وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتلُواْ ٱلشَّيَطِينُ عَلَى مُلكِ سُلَيمَنَ وَمَا كَفَرَ سُلَيمَنُ وَلَكِنَّ ٱلشَّيَطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحرَ وَمَا أُنزِلَ عَلَى ٱلمَلَكَينِ بِبَابِلَ هَرُوتَ وَمَرُوتَ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِن أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحنُ فِتنَة فَلَا تَكفُر فَيَتَعَلَّمُونَ مِنهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَينَ ٱلمَرءِ وَزَوجِهِ وَمَا هُم بِضَارِّينَ بِهِ مِن أَحَدٍ إِلَّا بِإِذنِ ٱللَّهِ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُم وَلَا يَنفَعُهُم وَلَقَد عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشتَرَىهُ مَا لَهُ فِي ٱلأخِرَةِ مِن خَلَق وَلَبِئسَ مَا شَرَواْ بِهِ أَنفُسَهُم لَو كَانُواْ يَعلَمُونَ١٠٢﴾

Ma'ana: “Kuma basu sanar da kowa ba balle suce: mu fitina kawai ne, saboda haka ka kafirta," balle har suke rarrabwa tsalanin mutum da matarsa das hi daga gare su. Kuma su (masu yin sihirin) basu zama masu cutar da kowa da shiba, face da iznin Allah. Kuma suna neman ilimin abin da yake cutar da su, kuma baya amfaninsu, kuma lallai ne, sun sani tabbas wanda ya saye shi, baya da wani rabo lahira. Kuma tir da abinda suka sauar da raukansu da shi, da sun kasance suna sani)). Suratul Bakara, aya ta: 102

Sai kuma waccan ayar maigirma da ta yi nuni akan cewa lallai masu sihiri suna raba tsakanin mutum da matarsa. Kamar yadda ta yi nuni kuma cewa lallai sihiri baya tasiri don karan kansa ta fuskar amfanarwa ko cutaruwa, sai dai yana tasiri ne da iznin Allah wan ya riga ya kaddara kuma ya kasantar, domin lallai Allah tsarkakke madaukaki shi ne ya halcci alkhairi da sharri, hakika cutar ta yi girma kuma zaluncin ya yi tsanani ga wadannan masu kirkirar, wadanda su ka gaji wadan nan ilimomi daga mushrikai su ka zo suka rikita masu raunin kwakwale da su, lallai mu daga Allah mu ke kuma lalle mu gare shi zamu koma, Allah ya isar mana kuma madalla da wakili wanda yake shi ne Allah.

Kamar yanda ayar mai girma tayi nuni akan cewa hakika wadanda su ke neman ilimin sihiri ba komai suke nema ba mai amfanar da su ba a wajan Allah na rabo, kuma wannan alkawarin narkon azaba mai girma ya na nuni akan tsananin hasarar su a nan duniya da lahira, kuma lallai su sun sayar da kawunan su da mafi karancin kudi, don hakane Allah mai girma da daukaka ya zargesu akan haka fadarsa da ya ce:

﴿ وَلَبِئسَ مَا شَرَواْ بِهِ أَنفُسَهُم لَو كَانُواْ يَعلَمُونَ١٠٢﴾

Ma'ana:“Tir da abinda suka siyar da rayukan su da shi da sun kasance suna sani". Suratul Bakara, aya ta: 102.

Muna rokon Allah lafiya da aminci daga sharrin masu sihiri da bokaye da sauran masu……'

Kamar yadda muke rokon sa daya tsare musulmai daga sharrin su, kuma ya da tarda mahukuntan musulmai da wa'azantuwa daga gare su, da tabbatar da hukuncin Allah a kan su, domin bayi su huta daga cutarwarsu da kuma ayyukan su munana, lallai shi mai yawan kyauta ne mai karamci.

Kuma hakika Allah ya shar'anta wa bayinsa abinda za su tsare kawunan su dashi daga sharrin sihiri, ga banin aukuwarsa, kuma ya fayyace musu abinda za su yi magani da shi bayan aukuwan sa, domin rahama daga gareshi zawu garesu, da kuma kyauta tawa daga gareshi zuwa gare su, da kuma cika ni'imarsa a garesu.

Abinda zai biyo baya yanzu shi ne bayanin abubuwanda ake kare kai dasu daga hatsarin sihiri ga banin aukuwansa, da kuma abubuwanda ake magani da su bayan aukuwarsa na al'amuran da ya halatta a shar'ance.

Amma abubuwan da ake kare kai dasu daga hatsarin sihiri gabanin aukuwansa mafi mahimmancin sa da kuma amfani shi: Neman kariya dayin zikirori na shari'a da kuma addu'o'i da neman tsari wadanda suka tabbata asunnah, yana daga cikin haka karanta 'Ayatul kursiyyi' a bayan kowaCce sallar farilla bayan zikirori na shari'a bayan ka sallame daga sallah, yana daga cikin haka karanta ta yayin bacci, kuma Ayatul kursiyyi ita ce aya mafi girma, Ita ce fadansa tsarkakke:

﴿ٱللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ ٱلحَيُّ ٱلقَيُّومُ لَا تَأخُذُهُ سِنَة وَلَا نَوم لَّهُ مَا فِي ٱلسَّمَوَتِ وَمَا فِي ٱلأَرضِ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشفَعُ عِندَهُ إِلَّا بِإِذنِهِ يَعلَمُ مَا بَينَ أَيدِيهِم وَمَا خَلفَهُم وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيء مِّن عِلمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرسِيُّهُ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضَ وَلَا يَُودُهُ حِفظُهُمَا وَهُوَ ٱلعَلِيُّ ٱلعَظِيمُ٢٥٥﴾

Ma'ana: “Allah, babu wani abin bautawa da cancanta sai shi, Rayayye, mai tsayuwa da komai, gyangyadi ba ya kamashi kuma macci baya kamashi, shi ke da abinda ya ke cikin sammai da abinda ke cikin kassai, wanene yake yin ceto awurinsa sai dai da Izininsa? Yana sane da abinda yake gabansu da abinda ke bayansu, kuma ba su kewayewa da komai daga Ilimisa, sai dai da abinda ya so, Kursiyinsa ya yalwanci sammai da kasai, Kuma shine madaukaki mai girma". Suratul Bakara, aya ta: 255.

Daga cikin haka kuma akwai karatun Suratul Ikhlas da falaki da Nasi, a Karshen dukkan salloli na farilla, da kuma karanta wadannan surori sau uku – uku afarkon yini bayan sallar asuba kenan, acikin farkon dare bayan sallar magariba (ko ma tun bayan sallar la'asar) da kuma lokacin bacci, yana daga cikin haka kuma karanta ayoyi biyu na karshen suratul Bakarah – a farkon dare sune kuma fadarsa Allah madaukaki.

﴿ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَا أُنزِلَ إِلَيهِ مِن رَّبِّهِ وَٱلمُؤمِنُونَ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَئِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لَا نُفَرِّقُ بَينَ أَحَد مِّن رُّسُلِهِ وَقَالُواْ سَمِعنَا وَأَطَعنَا غُفرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيكَ ٱلمَصِيرُ٢٨٥﴾

Ma'ana: “Manzon Allah yayi Imani da abinda aka saukar zuwa gareshi daga Ubangijinsa, da muminai, Ko wannansu ya yi imani da Allah, da mala'ikunsa, Ba mu rarrabewa a tsakanin daya daga manzanninsa, Kuma (Muminai) su kace; “Mun ji kuma mun yi biyayya (muna neman) gafararka, Ya Ubanginmu! Kuma zuwa gareka makoma take". (Suratul Bakarah, aya ta:285) zuwa karshen surar.

Kuma hakika ya Inganta daga manzo Allah tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi lallai yace;

((من قرأ آية الكرسي في ليلة لم يزل عليه من الله حافظ، ولا يقربه شيطان حتى يصبح)).

Ma'ana: “Duk wanda ya karanta 'AyatulKursiyyi' cikin dare ba zai gushe ba yana da wani mai tsare shi daga waurin Allah, ba kuma wani shaidani da zai kusance shi har gari ya waye)).

kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi lallai shi ya ce:

((من قرأ الآيتين من آخر سورة البقرة في ليلة كفتاه)). والمعنى والله أعلم: كفتاه من كل سوء.

Ma'ana: “Duk wanda ya karanta ayoyi biyu daga ayoyin karshen Suratul Bakarah a kowanne dare sun isar masa". Abin nufi Allah shi ne masani; 'Sun isar masa daga kowacce irin cuta'.

Kuma yana daga cikin haka yawaita neman tsari dafad'in:

((أعوذ بكلمات الله التامات من شر ما خلق))

Ma'ana: “Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda ya halitta (mai sharri))".

Cikin dare da yini, da kuma yayin da suka sauka a wani masauki ginanne ne ko kuwa a sararine ko a yanayi na teku, domin fadar Annabi tsira da damincin Allah su tabbata a gare shi cikin hadisin da ya gabata: ((Duk wanda ya sauka awani masauki sai yace: “Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda ya halitta babu abinda zai cutarda shi har ya tashi daga wannan wurin)).

Yana daga cikin haka kuma musulmi ya karanta wannan addu'ar aduk farkon yini da kuma farkon dare sau uku (Wato bayan sallar asuba da bayan sallar la'asar):

((بسم الله الذي لا يضر مع اسمه شيء في الأرض ولا في السماء، وهو السميع العليم)).

Ma'ana: “Da sunan Allah wanda babu abunda ya ke cutawa (idan ya hada) da sunan sa a kasa ko a sama, kuma shi mai jine masani)".

Domin Ingancin kwadaitarwa akan haka daga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, kuma lallai hakan dalili ne na amintuwa daga dukkan cuta.

Sannan kuma wadannan zikirori da neman tsari yana daga cikin mafi girman dalilai wurin kariya daga sharrin masu sihiri da wanin su na dukkanin sharri ga duk wanda ya yi ruko da su da gaskiya da imani da amincewa ga Allah da dogaro gareshi da kuma gamsuwa da abinda yake nuni agare shi, kuma su na daga cikin mafigirman makami domin gusar da sihiri bayan aukuwarsa tare da yawaita kaskantar da kai ga Allah da rokonsa tsarkakke da ya ye maka cututtuka kuma ya gusar kuma gusar maka da dukkanin cuta.

Kuma daga cikin uddu'oin da suka tabbata daga gareshi tsira da mincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yi wa sahabbansa addu'oi da su:

((اللهم رب الناس أذهب البأس، واشف أنت الشافي لا شفاء إلا شفاءك لا يغادر سقما)).

Ma'ana: “Ya Allah Unbangjin mutane, ka tafiyarda cuta kuma kawarkar kaine mai warkarwa babu waraka sai dai warkarwar ka, warakar da ba ta barin wata cuta". Za'a karanta wannan ne sau uku.

Yana daga cikin haka addu'ar da Mala'ika Jibrilu u ya yi wa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi Ita ce fadarsa:

((بسم الله أرقيك من كل شيء يؤذيك، ومن كل نفس أو عين حاسد، الله يشفيك، بسم الله أرقيك)).

Ma'ana: “Da sunan Allah nake maka addu'a daga dukkan abinda ke cutar da kai da kuma sharrin dukkan wata rai ko ido mai hassada, Allah ya warkar da kai, da sunan Allah na ke maka Addu'a". kuma zai ta maimaita hakanne har sau uku.

Kuma yana daga cikin magungunan sihiri bayan aukuwar sa kuma shi maganine mai amfani ga na miji idan ya kasa tarawa da iyalinsa, ya sami ganyan magarya kore guda bakwai sai ya dan dandaka su da dutsen ko makamacin sa, sai ya zuba cikin wani botikin ruwa wanda zai ishe shi yin wanka, sai ya karanta Ayatulkursiyyi, da suratul Kafirun da Kulhuwallahu da Faki da Nasi, da Ayoyin sihiri wadanda suke cikin Suratul A'araf su ne kuma fadarsa madaukaki:

﴿وَأَوحَينَا إِلَى مُوسَى أَن أَلقِ عَصَاكَ فَإِذَا هِيَ تَلقَفُ مَا يَأفِكُونَ١١٧ فَوَقَعَ ٱلحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعمَلُونَ١١٨ فَغُلِبُواْ هُنَالِكَ وَٱنقَلَبُواْ صَغِرِينَ١١٩﴾

Ma'ana: “Kuma muka yi wahayi zuwa ga Musa cewa: Ka jefa sandar ka, sai gata tana lakumar abin da suke karya da shi! Gaskiya ta auku, kuma abinda suke aikatawa ya baci. Sai aka rinjayesu acan, kuma su ka juya suna kaskantatu". Suratul A'araf, aya ta: 117-119.

Da kuma wasu ayoyi cikin suratu Yunus, aya ta saba'in da tara zuwa ta tamanin da biyu, wato fadin Allah mai girma da daukaka:

﴿وَقَالَ فِرعَونُ ٱئتُونِي بِكُلِّ سَحِرٍ عَلِيم٧٩ فَلَمَّا جَاءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَى أَلقُواْ مَا أَنتُم مُّلقُونَ٨٠ فَلَمَّا أَلقَواْ قَالَ مُوسَى مَا جِئتُم بِهِ ٱلسِّحرُ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبطِلُهُ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصلِحُ عَمَلَ ٱلمُفسِدِينَ٨١ وَيُحِقُّ ٱللَّهُ ٱلحَقَّ بِكَلِمَتِهِ وَلَو كَرِهَ ٱلمُجرِمُونَ٨٢﴾

Da wasu ayoyi cikin Suratu D.H aya ta sittin da biyar zuwa ta sittin da tara, wato fadin Allah madaukakin sarki:

﴿قَالُواْ يَمُوسَى إِمَّا أَن تُلقِيَ وَإِمَّا أَن نَّكُونَ أَوَّلَ مَن أَلقَى٦٥ قَالَ بَل أَلقُواْ فَإِذَا حِبَالُهُم وَعِصِيُّهُم يُخَيَّلُ إِلَيهِ مِن سِحرِهِم أَنَّهَا تَسعَى٦٦ فَأَوجَسَ فِي نَفسِهِ خِيفَة مُّوسَى٦٧ قُلنَا لَا تَخَف إِنَّكَ أَنتَ ٱلأَعلَى٦٨ وَأَلقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلقَف مَا صَنَعُواْ إِنَّمَا صَنَعُواْ كَيدُ سَحِر وَلَا يُفلِحُ ٱلسَّاحِرُ حَيثُ أَتَى٦٩﴾

Kuma bayan karanta wadan nan abubuwan da aka ambata a cikin ruwa, zai sha sau uku sai ya yi wanka da sauran da hakane cutar zata gushe in Allah yaso. Kuma idan bukata ta kai ga ayi hakan sau biyu ko fiye da hakan to babu laifi har dai cutar ta gushe.

Kuma wannan yana daga cikin magungunan sihiri kuma shi ne ma mafi amfanuwar maganin, kuma a yi kokari har a gano wurin da aka boye asirin a cikin kasa ko tsauni ko madai ina ne, idan aka gano sai aka fitar da shi aka bata shi to asirin ya baci kenan.

Wannan shi ne abinda ya sauwwaka na bayanin al'amuran da ake kare kai dasu daga sihiri da kuma wadanda ake magani dasu, Allah shi ne majibinci da kuma cewa. Amma maganinsa da aikin masu sihiri wanda ya ke kusantar da su zuwa ga Aljanu ta hanyar yanka ko waninsa da abubuwan neman kusanci to wannan bai halattaba, domin hakika yana daga ayyukan shaidan kai yana daga cikin tarayya mafi girma.

Abinda yake wajibi, shi ne takatsan-tsan daga hakan, kamar yadda baya halatta ayi maganin sihirin ta hanyar tambayar bokaye da 'yanduba da masu tsafe-tsafe da kuma yin aiki da abinda su ke fada, domin lallai su ba su yi imani ba, kuma hakika su makaryatane kuma fajirai suna ikirarin sanin gaibi kuma suna rikitarda mutance, kuma hakika manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi gargadi game da zuwa wajansu, da kuma tambayarsu da gaskantasu, kamar yadda bayani ya gabata akan haka afarkon wannan lttafi, kuma hakika ya inganta daga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi an tambaye shi gameda warware sihiri awajan mai sihirin sai yace: “Yan da cikin aikin shaidan". Imamu Ahmad ya ruwaito shi da Abu Dawud da isnadi mai kyau.

Abin nufi da maganar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, shi abinda mutanen Jahiliyya suke yi shi ne: Tambayar mai sihiri ya warware sihiri, ko kuma warware sihiri da kwatan kwacin sihirin awurin wani mai sihirin.

Amma warwareshi da addu'oi da neman tsari na shari'a da magunguna na halas to babu laifi da hakan kamar dai yadda ya gabata, kuma hakika babban malamin nan Ibnu Kayyim ya fadi hakan, da kuma babban malami Abdurrahman dan Hassan cikin littafin 'Fat'hul-majeed' Allah ya yi musu rahama, kuma wasunsu daga cikin ma'abota ilimi sun fadi haka.

Allah muke roko da ya datar da musulmai da lafiya daga dukkan cututtuka, kuma ya kiyaye musu addinin su, kuma ya'azurtasu da fahimtar addinin, da kuma lafiya daga dukkan abinda ya sabawa shari'ar sa, tsira da amincin Allah su tabbata ga bawansa kuma manzon sa Annabi Muhammad da Iyalan gidansa da Sahabban sa.

SIHIRIN DA MATA TAKE YIWA MIJI

Daga Abdul'aziz dan Baz zuwa ga dan'uwa maigirma, aminicin Allah su tabbata a gareku da rahamar sa da albarkan sa, bayan haka;

Wasikarka da aka rubuta ba tare da (kwanan wata ba), Allah ya isarmaka da shiriyarsa da kuma abinda ya kunsa na amfani na abinda ya sameka yayinda ka yi nufin saduwa da amaryarka, da kuma tafiyarka zuwa wajan babban malamin nan da abinda ya yi maka fatawa da shi da kuma abinda tsohuwar matarka tayi wanda yazamanto dalilin kasa saduwa da maryarka da kuma tambayarka gameda hukuncin haka, wanna nan ya kasance sananne ne.

Amsar Ita ce: Idan tsohuwar matar ka ta tabbatar da wannan aikin, ko kuma hakan yatabbata da shaidu to hakika ta aikata mummunan laifi kuma mai garma, kai, kafirci ne ma da bata, domin wannan aikin na ta sihirine haramtacce, kuma mai sihiri kafirine kamar yadda Allah tsarkakke ya fada: a cikin suratul Bakara aya ta (102) dari da biyu.

﴿وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتلُواْ ٱلشَّيَطِينُ عَلَى مُلكِ سُلَيمَنَ وَمَا كَفَرَ سُلَيمَنُ وَلَكِنَّ ٱلشَّيَطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحرَ وَمَا أُنزِلَ عَلَى ٱلمَلَكَينِ بِبَابِلَ هَرُوتَ وَمَرُوتَ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِن أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحنُ فِتنَة فَلَا تَكفُر فَيَتَعَلَّمُونَ مِنهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَينَ ٱلمَرءِ وَزَوجِهِ وَمَا هُم بِضَارِّينَ بِهِ مِن أَحَدٍ إِلَّا بِإِذنِ ٱللَّهِ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُم وَلَا يَنفَعُهُم وَلَقَد عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشتَرَىهُ مَا لَهُ فِي ٱلأخِرَةِ مِن خَلَق وَلَبِئسَ مَا شَرَواْ بِهِ أَنفُسَهُم لَو كَانُواْ يَعلَمُونَ١٠٢﴾

Ma'ana: “kuma suka bi abinda shedanu suke karanta musu akan mulkin (Annabi) Sulaiman, kuma (Annabi) Sulaiman bai yi kafici ba, saidai shadanune suka kafirce, suna koyawa mutane asiri, kuma ba'a saukar da wani abuba akan mala'iku biya a babila (wato) Haruta da Maruta. Kuma basu sanar da kowa ba balle suce: mu fitina kawai ne, saboda haka ka kafirta," balle har suke rarrabwa tsalanin mutum da matarsa das hi daga gare su. Kuma su (masu yin sihirin) basu zama masu cutar da kowa da shiba, face da iznin Allah. Kuma suna neman ilimin abin da yake cutar da su, kuma baya amfaninsu, kuma lallai ne, sun sani tabbas wanda ya saye shi, baya da wani rabo lahira. Kuma tir da abinda suka sauar da raukansu da shi, da sun kasance suna sani)). Suratul Bakara, aya ta: 102

Kuma waccamma ayar maigirma tana nuni ne akan cewa lallai sihiri kafirci ne, kuma lallai mai sihiri kafiri ne, kuma lallai masu sihiri suna neman ilimin abunda zai cutarda su kuma bazai amfanar da su ba, kuma yana daga cikin manufar su raba tsakanin mutum da matar sa, kuma lallai su ba su da wani rabo awurin Allah ranar alkiyama -abun nufi ba su da rabo wajan tsira-. Ya zo cikin Hadisi ingantacce daga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi lallai shi ya ce:

((اِجْتَنِبُواْ اَلسَّبْعَ اَلْمُوبِقَاتِ، قَالُواْ يَا رَسُولَ اَللهِ وَمَا هِيَ؟ قَالَ: اَلشِّرْكُ بِاللهِ، وَالسِّحْرُ، وَقَتْلُ اَلنَّفْسِ اَلَّتِي حَرَّمَ اَللهُ إِلاَّ بِالْحَقِّ، وَأَكْلُ اَلرِّبَا، وَأَكْلُ مَالِ اَلْيَتِيمِ، وَالتَّوَلِّي يَوْمَ اَلزَّحْفِ، وَقَذْفُ اَلْمُحْصَنَاتِ اَلْغَافِلاَتِ اَلْمُؤْمِنَاتِ)).

Ma'ana: “Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa, sai suka ce; Ya Ma'aikin Allah wadannene? Sai ya ce: Yi wa Allah shirka, da Sihiri (asiri) da kashe rai wacce Allah ya haramta a kasheta saida gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juya baya a lokacin yaki, da yiwa mata muminai masu kamunkai kazafi".

Amma malamin da ya baka magani a gaskiya mai sihiri ne kamar matar, domin hakika babu mai tsinkayar ayyukan sihiri sai dai mai sihirin, kuma shi yana daga masu duba da bokaye da aka sani da da'awar sanin gaibu cikin mafi yawan al'amura, abinda ya ke wajibi ga dukkan musulmi shi ne ya kiyaye su, kuma karya gaskanta su adukkanin binda suke ikirarin sun sani na gaibi domin fadar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

((من أتى عرافا فسأله عن شيء لم تقبل له صلاة أربعين ليلة)) أخرجه مسلم في صحيحه.

Ma'ana: “Duk wanda yaje wajan dan duba sai ya tambayeshi kan wani abu ba za'a karbi sallarsa ta kwana arba'in ba". Muslim ya fitar da shi cikin ingantaccan littafinsa.

Ma'aikin Allah ﷺ‬ Ya sake cewa kuma

((من أتى عرافا أو كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد صلى الله عليه وسلم)).

Ma'ana: “Duk wanda ya je wajan danduba ko boka sai ya gaskanta shi da abinda ya ke cewa to hakika ya kafircewa abinda aka saukar wa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi".

Don haka abinda ya faru daga gareka, kuma ka gayawa shugaban (Hisbah) su dauki matakin da ya dace da su, kuma idan irin wannan matsalar ta sake faruwa da kai to ka tambayi malaman shari'a. Allah ya azurtamu da kai fahimtar addini da kuma tabbata akan shi da kuma kubuta daga abinda zai saba masa, lallai shi mai yawan kyauta ne mai karamci.

Amincin Allah su tabbata a gare ku da rahamarsa da albarkarsa.

HUKUNCIN TAMBAYAR MASIHIRTA DA MASU TSAFE-TSAFE

Tambaya: Wani dan'uwa P.M.B daga Riyadh, yana cewa a cikin tambayarsa: Ana samun wasu mutane a yankin Yaman, ana kiran su (sadat) wadaannan mutane suna zuwa da abubuwa da suka fita daga addini misaln tsafe-tsafe da wasunsu, kuma suna da'awar cewa zasu iya warkar da mutane daga rashin lafiya mai wahala.'

Kuma suna kafa dalili akan haka da sukan jikinsu da wuka ko yanka harsunan su sannan su mayar da su ba tare da wani wani abu ya samesu ba, kuma wadan nan mutanan daga cikinsu akwai masu sallah daga cikinsu kuma akwai mara sa sallah, haka nan kuma suna halattawa kawunan su aure daga wadanda ba danginsu ba, kuma basu yarda wa wani ya aura daga danginsu ba, kuma a wurin Addu'ar ta su ga marasa lafiya suna cewa (Ya Allah ya wane) ma'ana daya daga cikin kakannin su.

Acanda mutane sun kasance suna girmamasu, kuma suna daukarsu wasu mutane ne na daban kuma su mutane ne na kusa da Allah, kai sunama kiransu mutanan Allah, amma yanzu mutanen sun rabu da su: daga cikin su a kwai wadanda basu yarda da su ba, su ne kuma matasa da kuma sashin malamai, daga cikin su kuma akwai wadanda ba su gusheba suna ruko da su, sune kuma masu yawan shekaru (wato tsofaffi) da wadanda ba su da ilimi. To muna rokon ku da ku yi mana bayani akan hakikanin wannan al'amari.

Amsa: To, wadan nan da makamantan su suna daga cikin sufaye wadanda suke da ayyuka munana da kuma kakataccen yanayi, harwayau su na cikin masu duba wadanda Annabi ﷺ‬ ya fada game dasu:

“Duk wanda ya je wajan danduba sai ya tambaye shi akan wani abu ba za'a karbi sallarsa ta kwana ar'bain ba".

Wannan kuma sakamakon da'awarsu ne na sanin gaibu, da kuma hidimar su da suke yi wa aljanu, da kuma bauta musu, da kuma rikita hankulan mutane da abinda suke aikatawa na nau'ukan sihiri wanda Allah madaukakin sarki acikin kissar Annabi Musa u da Fir'auna yak e cewa:

﴿قَالَ أَلقُواْ فَلَمَّا أَلقَواْ سَحَرُواْ أَعيُنَ ٱلنَّاسِ وَٱستَرهَبُوهُم وَجَاءُو بِسِحرٍ عَظِيم١١٦﴾

Ma'ana: “Yace. “Ku jefa", Yayinda suka jefa suka sihirce idanun mutane, kuma suka tsoratar da su, kuma suka zo da sihiri mai girma". Suratul A'araf, aya ta: 116.

Don haka baya halatta aje wurinsu ko tambayar su domin wannan hadisin maigirma, kuma domin fadar Sa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi:

“Duk wanda yaje wajan boka sai ya gaskanta shi da abinda yake fada to hakika ya kafirce wa abinda aka saukar wa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabba a gare shi".

Amma rokonsu koma bayan Allah da neman agajin su ga wanin Allah ko kuma riyawarsu cewa iyayensu da magabatansu suna gudanarda al'amura cikin yanayi, ko kuma suna warkarda marasa lafiya, ko kuma suna karba kira tare, ko sun mutu ko kuma basanan to dukkan wadannan kafurcewa Allah ne mai girma da daukaka, kuma yana daga tarayya mafi girma, abinda yake wajibi yi musu inkari da rashin zuwa wajansu da rashin tambayarsu, da rashin gaskantasu, domin lallai su sun tattara a wannan ayyukan tsakanin aikin bokaye, da 'yanduba, da kuma aikin mushirikai shi ne bautan wanin Allah da kuma neman agaji ga wanin Allah da masu neman taimako daga wanin Allah, daga aljanu ne ko daga matattu da wasunsu, daga wadanda suke dangantuwa zuwa gare su kuma suke riya cewa lallai su iyayansu ne kuma magabatansu ne ko- kuma wasu mutane na daban da suke riya cewa suna da wilaya ko karama, a'a dukkan wadannan yana daga nau'ukan tsafi da kuma ayyukan bokanci da duba wanda yake haramtacce ne cikin wannan shari'ar mai sarki.

Amma abinda ke faruwa na yanayin sukan kawunansu da manyan wukake ko yanke harsunan su to dukkan wadannan rufa ido suke yi wa mutane, kuma dukkan su suna daga nau'uka na sihiri wanda yake harammun ne, wanda nassoshin Alkur'ani da sunnah suka zo da haramcin su, ya kuma yi gargadi akansa kamar yadda ya gabata, bai kamata ga mai hankali ya rudu da hakan ba, kuma wannan yana daga cikin abinda Allah tsarkakke madaukaki ya ce game da masu sihirin Fir'auna:

﴿ يُخَيَّلُ إِلَيهِ مِن سِحرِهِم أَنَّهَا تَسعَى٦٦﴾

Ma'ana: “Ana suranta su a gare shi, daga – sihirin su, lallai suna tafiya da sauri".

Kuma hakika wadan nan sun hada – tsakanin sihiri da shirka mafi girma da kuma neman taimako agun wanin – Allah da kuma da'awar sanin gaibi, da kutsawa cikin ilimin yanayi, kuma wadan nan nau'ukan da yawan su shirka ne mafi girma da kuma kafirci, kuma yana daga cikin ayyukan matsafa wanda Allah ya haramta shi kuma su na da'awar sanin gaibi wanda babu wanda yasanshi sai Allah, kamar yadda Allah tarkakke ya ce:

﴿قُل لَّا يَعلَمُ مَن فِي ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ ٱلغَيبَ إِلَّا ٱللَّهُ وَمَا يَشعُرُونَ أَيَّانَ يُبعَثُونَ٦٥﴾

Ma'ana: “Kace: babu wanda yasan gaibi a cikin sammai da kasa sai Allah". Suratul Naml, aya ta: 65.

To wajibine ga dukkan Musulmai wadanda suka san halayansu da suyi musu inkari, kuma su bayyana wa mutane mumunan ayyukan su da cewa hakika haramun ne da kai karar su wajan shuwagabanni idan suna cikin garin musulunci ne domin a hukunta su da abinda ya dace a shari'a, domin tsari daga sharrinsu da kuma kare musulmai daga barnarsu da rikitarwar su.

Allah shi ne majibincin dacewa.

NEMAN maganiN gargajiya wurin wanda ke amfani da aljanu

Tambaya?

Akwai wasu mutane sunavyin maganin gargajiya a fadarsu, yayin da na je wajan dayan su sai yace dani: Rubuta sunanka da sunan mahaifiyarka sannan ka dawo gobe, yayin da mutum ya dawo wurin na su sai su ce masa: Hakika abu kaza da kaza…. Ya same ka, sai waninsu kuma ya ce: Lallai shi zai yi amfani da maganar Allah ne wurin yin maganin, to menene ra'ayinku cikin irin wadannan mutane? Kuma menene hukuncin zuwa wajansu? (S.A.G –Ha'il)

Amsa:

Duk wanda ya kasance ya na aiki da wadan nan al'amuran wajan magungunan sanin gaibi, to ba ya halatta a nemi magani a wajansa, kamar yadda ba ya halatta aje wajansa ko tambayarsa, domin fadar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cikin irin wadan nan mutanen:

“Duk wanda ya je wajan danduba sai ya tambaye shi akan wani abu to baza'a karbi sallar sa ta darare ar'ba'in ba". Muslim ya fitar da shi cikin ingantanccen littafin sa.

Kuma ya tabbata cikin hadisai masu yawa daga gareshi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hani game da zuwa wajan bokaye da 'yanduba da masu sihiri da kuma hani akan tambayar su da gaskanta su, sai yace:

“Duk wanda ya je wajan boka sai ya gaskanta shi da abinda ya ke fada to hakika ya kafirce wa abinda aka saukar wa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi".

Duk wanda yake da'awar sanin gaibi ta hanyar bugun kasa ko amfani da kasar kabari ko rubutu akan kasa ko tambayar maralafiya sunansa da sunan mahaifiyar sa ko sunan makusantan sa to duk wadan nan suna nuna cewa masu dubane kuma bokaye ne wanda Annabi tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi hani akan tambayar su da kuma gaskanta su.

To wajibine a yi taka-tsantsan da su da tambayar su da yin magani a wurin su koda suna cewa za su yi maganin ne da Alkur'ani domin al'adar lalatattun mutane ita ce boye al'amurra da yaudara to baya halatta a gaskantasu cikin abinda suke fada, kuma wajibine ga duk wanda ya sansu ya kai kararsu wurin shugabanni kamar alkalai – da sarakuna da manyan wurare da jama'a suka kafa, a kowanne gari har a yi musu hukunci da abinda Allah ya hukunta, kuma musulmai su kubuta daga sharrin su da kuma barnar su, da cin dukiyar mutane da barna. Allah muke neman taimakon sa ba bu dabara kuma babu karfi sai ga Allah.

Maganin sihiri A shar'an ce

Tambaya?

Na ji wani mallami yana cewa: Duk wandan ke zaton an yi masa sihiri ya sami ganyan magarya guda bakwai ya sa shi cikin kwarya mai ruwa sai ya karanta surorin neman tsari a cikin ta, da Ayatulkursiyyi, da suratul Kafirun, da kuma fadar sa madaukaki:

﴿ وَمَا أُنزِلَ عَلَى ٱلمَلَكَينِ بِبَابِلَ هَرُوتَ وَمَرُوتَ ١٠٢﴾

“…da abinda aka saukar da shi a kan mala'iku biyu a Babila, Haruta da maruta". Suratul Bakarah, aya ta: 102. Da kuma Suratul Fatiha, to menene ingancin sa? Kuma wanda ke zaton – an yi masa sihiri me zai aikata? Ka amfanar da mu Allah ya amfanarda ku.

Amsa

Babu kokwanto lallai akwai sihiri kuma sashin sa ma rufa ido ne, kuma sihiri da izinin Allah mai girma da daukaka, kamar yadda Allah maigirma da daukaka ya ce dangane masu sihiri: cikin suratul Bakara aya ta dari da biyu:

﴿وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتلُواْ ٱلشَّيَطِينُ عَلَى مُلكِ سُلَيمَنَ وَمَا كَفَرَ سُلَيمَنُ وَلَكِنَّ ٱلشَّيَطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحرَ وَمَا أُنزِلَ عَلَى ٱلمَلَكَينِ بِبَابِلَ هَرُوتَ وَمَرُوتَ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِن أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحنُ فِتنَة فَلَا تَكفُر فَيَتَعَلَّمُونَ مِنهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَينَ ٱلمَرءِ وَزَوجِهِ وَمَا هُم بِضَارِّينَ بِهِ مِن أَحَدٍ إِلَّا بِإِذنِ ٱللَّهِ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُم وَلَا يَنفَعُهُم وَلَقَد عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشتَرَىهُ مَا لَهُ فِي ٱلأخِرَةِ مِن خَلَق وَلَبِئسَ مَا شَرَواْ بِهِ أَنفُسَهُم لَو كَانُواْ يَعلَمُونَ١٠٢﴾

Ma'ana: “kuma suka bi abinda shedanu suke karanta musu akan mulkin (Annabi) Sulaiman, kuma (Annabi) Sulaiman bai yi kafici ba, saidai shadanune suka kafirce, suna koyawa mutane asiri, kuma ba'a saukar da wani abuba akan mala'iku biya a babila (wato) Haruta da Maruta. Kuma basu sanar da kowa ba balle suce: mu fitina kawai ne, saboda haka ka kafirta," balle har suke rarrabwa tsalanin mutum da matarsa das hi daga gare su. Kuma su (masu yin sihirin) basu zama masu cutar da kowa da shiba, face da iznin Allah". Suratul Bakarah, aya ta: 102.

To shi dai sihiri yana da tasiri amma dai da izinin Allah wanda ya riga ya kaddara, domin babu wani abu aduniyar nan face da kaddarawar Allah tsarkakke madaukaki sai dai wannan sihiri yana da magani, hakika ya faru da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, kuma Allah ya warkar da shi, kuma ya tseratar da shi daga sharrin sa, kuma suka sami abinda aka aikata na sihiri sai ya cire shi ya lalata shi, Allah yawarkar da Annabin sa ﷺ‬ daga hakan tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, haka nan ne idan aka sami abinda mai sihiri ya aikata na kulle – kullen igiyoyi ko kuma aka kafa kusa sashinta da sashi ko wanin haka don yin haka yana lalatashi, domin hakika daga cikin dabi'ar masu sihiri shi ne tofi acikin kulle – kulle sai su buga mummunar niyyarsu akan wannan abin, sai abinda su ke nufi ya faru da izinin Allah madaukakin sarki, wani lokacin kuma sai ya bace, kuma Ubangin mu mai iko ne akan dukkan komai, tsarkakke madaukaki.

Wani lokacin kuma ana maganin sihirin ne da karatu, duk daya ne shi da aka yi wa sihirin zai karantawa kan sa karatun idan hakalinsa na tare dashi, ko ko wani ne zai yi masa karatun sai ya tofa masa a kirjinsa ko kuma a wata gaba daga cikin gabban sa, sai ya karanta masa: Suratul Fatiha, Ayatulkursiyyi, Kulhuwallahu, Falaki da Nasi, da kuma ayoyin sihirin nan da aka sani na suratul A'araf, da Suratu Yunus da kuma Suratu D.h.

Daga cikin Suratul A'araf:

﴿وَأَوحَينَا إِلَى مُوسَى أَن أَلقِ عَصَاكَ فَإِذَا هِيَ تَلقَفُ مَا يَأفِكُونَ١١٧ فَوَقَعَ ٱلحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعمَلُونَ١١٨ فَغُلِبُواْ هُنَالِكَ وَٱنقَلَبُواْ صَغِرِينَ١١٩﴾

Daga cikin Suratu Yunus Allah madaukakin sarki ya na cewa:

﴿وَقَالَ فِرعَونُ ٱئتُونِي بِكُلِّ سَحِرٍ عَلِيم٧٩ فَلَمَّا جَاءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَى أَلقُواْ مَا أَنتُم مُّلقُونَ٨٠ فَلَمَّا أَلقَواْ قَالَ مُوسَى مَا جِئتُم بِهِ ٱلسِّحرُ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبطِلُهُ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصلِحُ عَمَلَ ٱلمُفسِدِينَ٨١ وَيُحِقُّ ٱللَّهُ ٱلحَقَّ بِكَلِمَتِهِ وَلَو كَرِهَ ٱلمُجرِمُونَ٨٢﴾

Daga kuma cikin Suratu D.H, fadin Allah madaukakin sarki:

﴿قَالُواْ يَمُوسَى إِمَّا أَن تُلقِيَ وَإِمَّا أَن نَّكُونَ أَوَّلَ مَن أَلقَى٦٥ قَالَ بَل أَلقُواْ فَإِذَا حِبَالُهُم وَعِصِيُّهُم يُخَيَّلُ إِلَيهِ مِن سِحرِهِم أَنَّهَا تَسعَى٦٦ فَأَوجَسَ فِي نَفسِهِ خِيفَة مُّوسَى٦٧ قُلنَا لَا تَخَف إِنَّكَ أَنتَ ٱلأَعلَى٦٨ وَأَلقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلقَف مَا صَنَعُواْ إِنَّمَا صَنَعُواْ كَيدُ سَحِر وَلَا يُفلِحُ ٱلسَّاحِرُ حَيثُ أَتَى٦٩﴾

Kuma sai ya karanta: س﴿قُل يَأَيُّهَا ٱلكَفِرُونَ١﴾ har zuwa karshe.

Kuma ya karanta ﴿قُل هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ١﴾ الإخلاص: ١ har zuwa karshe.

Sai kuma ya karanta ﴿قُل أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلفَلَقِ١﴾ الفلق: ١ har zuwa karshe.

Sai kuma ya karanta ﴿قُل أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ١﴾الناس: ١ har zuwa karshe.

Kuma abinda ya fi shi ne ya maimaita “Kul huwallahu da Falaki da kuma Nasi sau uku". Sannan ya yi masa Addu'an waraka:

((اللهم رب الناس أذهب البأس أنت الشافي لا شفاء إلا شفاءك شفاء لا يغادر سقما))

Ma'ana: “Ya Allah Ubangijin mutane ka tafiyar da cuta kuma ka warkar shi, kai ne mai warkarwa babu waraka sai warakarka warakar da ba ta barin wata cuta".

Sai ya maimai ta wannan addu'ar sau Uku.

((بسم الله أرقيك من كل شيء يؤذيك، ومن شر كل نفس أو عين حاسد، الله يشفيك، بسم الله أرقيك))

Ma'ana: “Dasunan Allah na ke yi maka Addu'a daga dukkan abinda ke cutarda kai, kuma daga sharrin dukkan wata rai ko idanu na mai hasada, Allah ya warkar da kai, da sunar Allah na ke maka Addu'a".

Zai mai – maita ta sau uku. Hakanan kuma zai masa Addu'a da:

((أعيذك بكلمات الله التامات من شر ما خلق)).

Ma'ana: Ina neman maka tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda ka halitta (mai sharri)". ya maimaita hakan sau uku ya fi.

Kuma ya yi masa Addu'ar waraka da samun lafiya, idan ya fada kuma cikin Addu'arsa:

Dukkan wadannan suna daga cikin magunguna masu amfani, idan ya karanta wadan nan Addu'oi cikin ruwa sannan wanda aka yi wa sihirin ya sha ruwan kuma ya yi wanka da sauran ruwan, to wannan yana daga cikin dalilan waraka da samun lafiya da Izinin Allah.

Kuma idan ya sa ganyan magarya guda bakwai cikin ruwan bayan ya daka ganyan wannan ma yana daga dalilan waraka, kuma hakika dayawa an gwada hakan kuma Allah yasa an dace, kuma Allah ya sa sun warke, to wannan maganine mai amfani kuma mai amfanarwa ga dukkan wanda aka yi wa sihiri, haka nan kuma wannan maganin ya na da amfani ga wanda ya kasa saduwa ga iyalinsa, saboda – mutum ya kasa saduwa da ita kuma aka yi wadan nan Addu'rin Allah zai datar da shi da izinin Sa, dai daine ya karanta da kansa ne ko kuma wanine ya karanta masa ko kuma ya karanta a cikin ruwane, sannan ya sha ruwan kuma ya yi wanka da sauran – dukkan wadan nan suna da amfani ga wanda aka yi wa sihiri da wanda aka hana masa saduwa da matar sa, da izinin Allah.

Dukkanin wadan nan suna daga cikin dalilai da Allah tsarkakke madaukaki shi ne mai warkarwa shi kadai, kuma shi mai ikone akan dukkan komai, a hannunsa ne madaukaki waraka da cuta suke kuma dukkan komai da ikon sa ne da kaddarawar sa tsarkakke, kuma ya inganta daga manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi lallai shi yace:

((ما أنزل الله داء إلا أنزل له شفاء، علمه من علمه وجهله من جهله)).

Ma'ana: “Allah bai saukar da wata cutaba face ya saukar da maganinta, wanda ya sani ya sani kuma wanda bai sani ba bai saniba".

Kuma wannan falala ce daga gareshi tsarkakken sarki madaukaki. Allah ya sa mu dace ya kuma shiryar da mu hanya madaidaiciya.

FAYYACE GASKIYAR MAGANA GAME DA SHIGAR ALJANI JIKIN MUTUM DA KUMA MAIDA MARTINI GA MASU MUSANTA HAKAN.

Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah ﷺ‬ da iyalansa da sababbansa da wadanda suka shiryu da shiriyarsa.

Bayan haka: hakika wasu jaridun cikin gida sun yadu da ma wasun su cikin watan Sha'aban a wannan shekarar, abin nufi shekara ta dubu daya da dari hudu da bakwai (1407h) hijira, takaitattun maganganu da masu tsayi na abinda ya faru daga sanarwar wani aljani wanda ya shiga jikin wata mace muslma a birnin Riyadh ya yi na musuluntar sa a wurina bayan da na gayawa dan'uwa Abdullahi Ibn Mushirif Alumari wanda ke zaune a Riyadh, bayan da ya karanta wa wacce aljanin ya shiga jikinta ayoyi kuma ya yi magana da aljanin ya tsoratar da aljanin Allah ya kuma masa wa'azi ya kuma gayamasa cewa zalunci haramun ne kuma zunubi ne mai girma, kuma ya kirashi zuwa ga musulunci, yayin da ya gaya masa cewa shi kafiri ne yana bin addinin buda, sai ya nemi da ya fita daga jikinta sai ya yarda da kiran da aka yi masa, sai ya musulunta a nan wurin Abdullahi da aka ambata, sannan wannan Abdullahi ya yi kwadayi da shi da 'yan'uwan matar su zo wajena da matan har inji musuluntar aljanin, sai ko suka zo waje na, sai na tambaye shi dalilin da ya sa ya shiga jikinta, sai ko ya gayamin dalilin sai ya yi magana a harshen matar sai dai maganar na miji ne ba maganar mace ba, ita kuma tana kan kujerar da ke kusa da ni, dan'uwanta da yar'uwarta da Abdullahi Ibnu Mushrif da wasu manyan malami suna wurin su na jin maganar aljanin, kuma hakika ya bayyana musuluntar sa afili, kuma ya ce shi mutumin indiya ne yana bin addini buda ne, sai na yi masa nasiha kuma na yi masa wasiyya da jintsoron Allah, kuma ya fita daga jikin matar sannan kuma ya daina cutarda ita, sai ya yarda da hakan kuma yace: Ni na yarda da musulunci, kuma na yi masa wasiyya da ya kira jama'rsa zuwa ga musulunci bayan da Allah ya shirye shi, sai ya yi alkawarin hakan, sai ya bar jikin matar ya wuce, maganar karshe da ya yi it ace: “Assalamu Alaikum".

Sannan matar ta yi magana da harshen ta da ta saba, kuma ta ji sauki tahuta da gajiyar da ita da ya yi.

Sannan bayan wata guda ko fiye da hakan ta dawo suka dawo wurina tare da 'yan'uwanta biyu, sai ta ce mi ni; ita yanzu ta sami sauki, kuma shi bai sake dawo mata ba, kuma godiya tatabbata ga Allah, sai kuma na tambaye ta game da abinda ta ke ji yayin da aljanin ke tare da ita sai tace; ta kasance tana miyagun tunani wanda ya sabawa shari'a kuma tana ji kamar takoma Addinin Buda da kuma karanta littattafan da aka rubuta akansa, amma kuma bayan da Allah ya kubutar da ita daga gareshi sai wadan nan tunanin suka gushe daga gareta kuma ta dawo yanda ta ke, sai ta yi nisa daga wadanca tunanin mai karkatarwa.

Kuma hakika labari ya iso min daga babban malami Ali Dandawi cewa lallai shi ya musanta faruwar irin wannan Al'amarin kuma ya ce wannan aikin jujal kuma karyane, ya ce kuma zai yiwu ya zamanto maganar da aka nada ce a kaset tare da matar sai ba ta furta hakan ba. kuma tabbas na nemi kaset din da aka nadi maganar ta sa kuma na san me ya fada, na ji matukar mamaki akan yadda ya ce hakan an nada ne a kaset tare da cewa na tambayi aljanin tambayoyi masu yawa kuma ya amsa, yaya mai hankali zai yi zaton cewa kaset zai tambaya kuma ya amsa, wannan mummunan kuskurene da kuma wawantar da kwakwale, kuma yake cewa a cikin maganar ta sa musuluntar aljani a hannnun mutum ya sabawa fadin Allah madaukakin sarki cikin kissar Annabi Sulaiman u.

﴿قَالَ رَبِّ ٱغفِر لِي وَهَب لِي مُلكا لَّا يَنبَغِي لِأَحَد مِّن بَعدِي إِنَّكَ أَنتَ ٱلوَهَّابُ٣٥﴾ص: ٣٥

Ma'ana: “Kuma ka ba ni mulki wanda ba ya kamata da kowa daga baya na". Suratu S. aya ta: 35.

Babu kokwanto wannan kuskure ne daga gareshi kuma Allah ya shirye shi, kuma fahimta ce wacce take ba ta daidai ba, musuluntar aljani a hannun mutum baya sabawa addu'ar Annabi Sulaiman u, hakika jama'ar aljanu masu yawa sun musulunta a hannun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Kuma hakika Allah ya bayyana hakan cikin Suratul Ahkaf da Suratul Jinni, ya tabbaa cikin Bukhari da Muslim daga hadisin Abuhurairata Allah ya kara masa yarda daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi tabbas ya ce:

((إن الشيطان عرض لي فشد علي ليقطع الصلاة علي فأمكنني الله منه فذعته، ولقد هممت أن أوثقه إلى سارية حتى تصبحوا فتنظروا إليه، فذكرت قول أخي سليمان u ﭽ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﭼ ص: ٣٥

Ma'ana: “Hakika shaidan ya bijirto mini sai kuma ya matsamin don ya yanke min sallah ta, sai Allah ya taimakeni akansa sai na tunkude shi da karfi, kuma hakika na yi niyyar in daure shi a ginshiki har ku wayi gari ku gan shi, sai na tuna da addu'ar dan'uwana Sulaiman amincin Allah ya tabbata a gare shi. “Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuma ka bani mulki wanda baya kamata da kowa daga bayana". Sai Allah ya mayar da shi yana kaskantacce". Wannan lafazin Bukhari kenan, kuma lafazin muslim:

((إن عفريتا من الجن جعل يتلفت علي البارحة ليقطع علي الصلاة، وإن الله أمكنني منه فبقد هممت أن أربطه إلى جانب سارية من سواري المسجد حتى تصبحوا تنظرون إليه أجمعون أو كلكم ثم ذكرت قول أخي سليمان: ﴿ وَهَب لِي مُلكا لَّا يَنبَغِي لِأَحَد مِّن بَعدِي إِنَّكَ أَنتَ ٱلوَهَّابُ٣٥﴾ ص: ٣٥

Ma'ana: “Hakika wani mugun aljani ya kama waige na a daren nan da ya wuce domin ya yanke min sallah, sai Allah ya taimake ni akansa sai na tunkunde shi da karfi, hakika na yi niyyar in daureshi a gefen ginshiki daga cikin ginshikan masallaci har ku wayi gari ku gan shi baki daya ko dukkan ku, sannan sai na tuna zancen dan'uwana Sulaiman u. “Ubangiji ka gafarta mini kuma ka bani mulki wanda baya kamata da kowa daga baya na". Sai Allah “Ya mai da shi (aljanin) yana kaskantacce".

Kuma Nasa'i ya ruwaito shi a sharadin Bukhari daga Aisha Allah ya kara mata yarda, hakika Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana sallah sai shaidan ya zo masa sai Annabi tsirada amincin Allah su tabbata a gare shi ya kama shi, sai ya kada shi ya makure shi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

((حتى وجدت برد لسانه على يدي ولولا دعوة سليمان لأصبح موثقا حتى يراه الناس)).

Ma'ana: “Har na ji sanyin harshen sa a hannu na, dabadun addu'ar Sulaimanu ba da ya wayi gari a daure har mutane su ganshi". Ahmad ya ruwaito shi daga hadisin Abu Said akwai a cikin sa:

“Sai na mika hannu na bangushe ba ina makurar sa har na ji sanyin yawunsa a tsakanin wayannan yatsu na, babban yatsa da mai bin sa".

Kuma Bukhari ya fitar cikin ingantacce littafin sa ya kuma yi masa ta'aliki ya karfafashi a mujalladi na hudu shafi na 487, daga Fat'hulBari daga Abihuraira Allah ya kara masa yarda lallai shi ya ce:

“Manzon Allah ﷺ‬ ya wakiltani da in tsare zakkar Ramadan sai wani mai zuwa ya zo mini, sai ya kama satar abincin sai na kamashi na kuma ce na rantse da Allah sai na kaika gun manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya ce: Ni mabukaci ne kuma ina da iyali kuma ina da bukata mai tsanani, ya ce: Sai na keleshi sai da gari yaw aye sai Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: “Ya Abuhurairata yaya ka yi da bakon ka na jiya da daddare?". Sai na ce:

“Ya Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koka tsanin bukatarsa saboda yawan iyali, sai ko na tausaya masa sai na rabuda shi, sai Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce: “Lallai shi ya yi maka karya ne amma zai da wo". Sai na tabbata cewa zai dawo domin fadar da Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi- sai na yi ta dakonsa sai ya zo yana satar abincin, sai ko na kama shi sai na ce:

Lallai sai na kai ka gun Manzan Allah ﷺ‬, sai ya ce: Ka barni hakika ni mabukaci ne kuma ina da iyali ba zan dawo ba, sai na tausaya masa dai na rabu da shi sai da gari ya waye Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Ya Abahuraira yaya ka yi da bakonka na jiya da daddare"?. sai na ce: Ya Ma'aikin Allah ya koka bukata mai tsanani da kuma iyalai, sai ya ce:

Lallai shi sam karya ne karo na uku sai ya dawo, sai na jira shi a karo na uku sai ya dawo yana satar abincin, sai na kamashi sai na ce: Lallai sai na kai ka gurin Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, wannan karo na uku ke nan, kuma shi ne na karshe kai kana cewa ba zaka dawo ba sai kuma ka dawo, ya ce; ka barni zan koya maka wasu kalmomi da Allah zai amfanar da kai da su, sai na ce:

mecece? Yace: Idan ka zo wurin kwanciyarka to ka karanta 'Ayatulkurisiyyi' har karshen ayar, domin lallai kai ba za ka gushe ba da wani mai tsaro daga wurin Allah, kuma shaidan ba zai kusance ka ba har gari ya waye, sai na sake shi, sai da gari ya waye Manzan -Allah tsirada amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce da ni: “Yaya ka yi da bakonka na jiya da daddare? sai na ce: Ya Ma'aikin Allah -tsirada amincin Allah su tabbata a gare shi- cewa ya yi; Tabbas zai koya min wasu kalmomi da Allah zai amfanar da ni da su, sai na kyale shi, ya ce:

(mecece?) Na ce; ya ce dani 'idan ka zo wurin kwanciyarka karanta 'Ayatulkursiyyi' daga farkonta har ka kai karshen ayar, kuma ya ce ba za ka gushe ba da wani mai tsaro daga wurin Allah, kuma shaidan ba zai kusanceka ba har gari ya waye, kuma su sahabbai sun kasance masu kwadayin abun alheri ne, sai Annabi tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce:

“Amma lallai shi ya fada maka gaskiya, sai dai shi makaryacine, kasan wanda kake Magana da shi tun tsawon dararen nan uku ya Abahuraira?" na ce: A'a yace: “Wannan shaidanne".

Kuma hakika Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya bada labari cikin Hadisi Ingantace wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito, daga Safiyyah -Allah yakara mata yarda- lallai Annabi ﷺ‬ ya ce: “Shaidan yana gudana a jikin da'adam magudanar jini".

Kuma Imamu Ahmad ya rawaito cikin “Musnad" Mujalladi na hudu 4 shafi na 216, da Ingantaccin isnadi, lallai Usman dan Abil As t ya ce: Ya ma'aikin Allah shaidan ya shamakan ce tsakanina da sallah ta da tsakanin karatu na, ya ce: “Wannan shaidan ne ana kiransa “Khanzab", idan ka ji motsinsa to kanemi tsarin Allah daga gareshi sai ka yi tofi a hagunka sau uku", ya ce: Sai na aikata hakan sai Allah mai girma da daukaka ya tafiyar min da shi.

Kamar yadda ya tabbata a cikin Hadisai ingantattu daga Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- hakika kowanne mutum akwai wani makusanci na mala'ika tare da shi, da kuma wani makusanci na shaidanai har da Annabi ﷺ‬ sai dai Allah ya taimake shi akansa sai da alkhairi.

Kuma hakika littafin Allah mai girma da daukaka da sunnar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da haduwar bakin al'umma sun yi nuni akan yiwuwar shigar aljani jikin da'adam, da kuma cutar da shi, to tayaya zai halasta ga wanda ake dangantawa da ilimi ya musanta haka ba tare da ilimi ko wata shiriya ba sai dai makauniyar koyi ga sashin 'yan bidi'a, wadanda suke sabawa ma'abota sunnah akan karantarwar magabata, to Allah ne abin neman taimako kuma babu dabara kuma babu karfi sai ga Allah.

Kuma ni zan ambata maka ya kai mai karatu abinda ya sawwaka daga maganganun ma'abota ilimi akan haka in Allah ya so:

Bayanin Malaman Tafsiri Allah ya yi musu Rahama A FadaR allah madaukaki sarki:

﴿ٱلَّذِينَ يَأكُلُونَ ٱلرِّبَواْ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِي يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيطَنُ مِنَ ٱلمَسِّ ٢٧٥﴾ البقرة: ٢٧٥

Ma'ana: “Wandanda su ke cin riba ba su tashi (daga kabari), face kamar yadda wanda shaidan ya ke dimautarwa daga shafa ya ke tashi".

Abu Ja'afar dan Jarir Allah ya yi masa rahama yace: Cikin fassarar wannan ayar ga abinda ya nassanta; Abinda ake nufi da hakan shaidan ya bata masa hankali a nan duniya, shi ne kuma wanda ke makurarsa ya kada shi akasa, abin nufi hauka kenan.

Kuma Imamul Baghawi Allah ya yi masa rahama ya ce cikin fassarar wannan ayar da aka nassanta: Hauka. Ana cewa aljan ya shafi mutum, to kuma shi wanda aljani shafa ne, idan ya kasance mahaukaci.

Kuma Ibnu Kasir Allah ya yi masa rahama ya ce cikin fassarar wannan ayar da aka ambata: Wato ba za su tashi daga kaburburan su ba a ranar alkiyama sai dai kamar yadda wanda ke farfadiya da kuma kifar da shi da shaidan yake yi, hakan ya nuna cewa lallai shi yana tashi mumunan tashi.

Kuma Abdullahi dan Abbas Allah ya kara musu yarda ya ce: Mai cin riba ana tayarda shi ranar alkiyama mahaukaci yana makure". Ibn Abi Hatim ya ruwaito shi ya ce; kuma an ruwaito daga Awf dan Malik dan Sa'id dan Jubair da Suddi da Rabi'i dan Anas da Katadah da Mukatil dan Hayyan kwatan kwacin hakan…'

Abinda muka ciro daga zancansa ya kare Allah ya yi masa rahama.

Kuma Kurtubi Allah ya yi masa rahama ya ce cikin fassarar wannan ayar;

Cikin wannan ayar akwai dalili akan rushewar maganar wanda ya musanta bugun aljani ta bangaran aljani, ya kuma rika cewa yana daga cikin dabi'ar mutum kuma lallai shaidan ba ya shiga jikin mutum kuma baya shafar sa.

Maganganun malaman taf'siiri cikin ma'anar wannan ayar suna da ya wa wanda ke bukatar shi zai same shi.

Kuma Shehul Islam Ibnu Taimiyya Allah ya yi masa rahama ya ce a cikin littafin sa:

“Bayyanannun hujjojii akan gamewar manzancin (Manzan Allah) ga dukkanin mutane da aljanu" wanda ke cikin majmu'ul Fatawa Mujalladi na 19 shafi na 9 zuwa na 65 ga abinda ya fada bayan maganar da ta gabata:

'Don haka ne wasu bangarori daga cikin mu'utazila suke musun su, amma ba su musanta samuwar aljani ba, saboda domin wannan – na farkon – be bayyana ba cikin hadisan Ma'aikin Allah ﷺ‬ kamar yadda – na biyun – ya bayyana ba, dudda cewa sun yi kuskure akan haka. Don hakan Al'ash'ari ya ambata a cikin maganganun Ahlussunna Wal Jama'a lallai su suna cewa hakika aljani ya na shiga jikin mara lafiya, kamar yadda Allah madaukaki ya fada cikin wannan ayar da ta gabata cikin Suratul Bakara aya ta 275, wato fadin Allah mai girma da daukaka:

﴿ٱلَّذِينَ يَأكُلُونَ ٱلرِّبَواْ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِي يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيطَنُ مِنَ ٱلمَسِّ ٢٧٥ البقرة: ٢٧٥

Kuma Abdullahi dan Ahmad dan Hambali yace: Na ce ya baba wasu mutane suna riya cewa lallai aljani baya shiga jiki sai ya ce: Ya da na karya suke yi, shi ne wanda ke magana da harshen sa, kuma wannan maganar an fayyaceta a mahallinta.

Ya sake cewa kuma – Allah ya yi masa rahama a mujalladi na 24 a littafin “Fatawa" –Shafi na 276 – 277 ga nassin abinda ya fada:

“Samuwar aljani tabbatacce ne a Alkur'ani da Hadisan mazon Allah ﷺ‬ da haduwar bakin al'umma da suka gabata da manmanyan malamansu, haka nan kuma shigar aljanin cikin jikin mutum tabbatacce ne da haduwar bakin manyan malamai ma'abota sunnah da Jama'a Allah madaukaki ya ce a cikin ayar da ta gabata cikin Suratul Bakara, aya ta 275, wato fadin Allah madaukakin sarki:

﴿ٱلَّذِينَ يَأكُلُونَ ٱلرِّبَواْ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِي يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيطَنُ مِنَ ٱلمَسِّ ٢٧٥ البقرة: ٢٧٥

Ya zo cikin Bukhari daga Annabi tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi: “Lallai shaidan yana gudana a jikin dan Adam a magudanar jini".

Abdullahi dan Imamu Ahmad dan Hambali ya ce: Na tambayi baba na; Lallai fa wasu mutane suna cewa hakika aljani ba ya shiga jikin maralafiya, sai ya ce: Ya da na karya suke yi, shi ne wanda ya ke magana da harshen sa, kuma wannan abinda ya fada al'amarine shahararre, hakika kuma shi yana buge mutum sai ya yi magana da harshen da ba'a sanin ma'anarsa, sai a doke shi duka mai kafri irin dukan da idan an yi wa rakumi shi to da ya nuna babbar alama mai girma, tare da hakan shi maralafiya ba ya jin dukan ko maganar da ake masa, kuma shi maralafiyan ya kan ja mai lafiya kuma ya ja shinfidar da yake zaune akan ta kuma ya yi ta jujjuya abubuwa ya ta shi daga wannan wurin zuwa wancan wurin sai wasu al'amuran da ba wannan ba su yi ta faruwa wanda ke wajan yake kallo zai fahinici cewa lallai wannan mai magana da harshen mutum mai motse – motse da wannan jikin wani jinsi ne na daban ba mutum ba ne.

Kuma babu wani cikin al'ummar musulmi da ya musanta shigar aljani jikin maralafiya wanda ya musanta haka ya kuma yi ikirarin cewa lallai shari'a na karyata hakan to hakika ya yi wa shari'a karya, kuma babu wasu dalilai na shari'a da suka kore hakan..

Kuma Ibnul Kayyim Allah madaukaki ya yi masa rahama ya ce cikin Littafinsa 'Zadul Ma'ad' a mujalladi na 4 shafi ta 66-69 ga nassin: Sai rashin lafiya ta bugun aljani ya rabu gida biyu; bugun aljani daga rayuka miyagu dake kasa, da bugun Aljani daga cudanya mara kyau, na biyun shi ne likitoci suke magana akan sa akan dalilin sa da kuma magananin sa.

Amma bugun aljani na rayuka (miyagu dake a kasa) shugabannin su da kuma masu hankulan su sun tabbatar da shi ba sa koreshi, kuma suna tabbar da cewa lallai maganin sa dai-dai yake da rayuka madaukaka masu daraja mafi alkhairi ne ga wadan nan rayukan ashararai miyagu sai ya tunkude gurabun su kuma ta ci karo da cututtukansu kuma ta lalata su.

Kuma hakika ya nassanta hakan da fitila a sashen littatafan sa, kuma ya ambaci sashin magun-gunan bugun aljani ya ce; wannan kawai yana amfanarwa ne ga bugun da dalilin sa cudanya ne da asalin sa, Amma bugunda ke kasancewa daga rayuka to wannan maganin baya amfanar da shi.

Amma jahilan likitoci da kangararrun su da makamanta su da wadanda su ke kudurta munafinci to wadan nan sune suke musun bugun rayuka, kuma basa yarda da cewa lallai bugun aljan yana tasiri a jikin marafiya ba, kuma babu komai yake tareda su ba sai dai jahilci, in ba haka ba babu wani aiki na likitanci dake inkarin haka, ji da kuma abinda ka gani suna tabbatar da hakan, kuma yadda suke mayar da mafi rinjayan kurakuran su eh, hakan gaskiya nau'i na kasan al'amuran ba wai a bakidanyan su ba, har dai ya kai ga cewa;

''Wasu zindikaan likitaci sun zo basa tabbatar da wani bugun aljan ba sai kawai bugun cudanya shi ka dai, duk kuwa wanda ke da hankali da sani akan wadan nan rayuka da tasirin su zai yi dariya saboda jahilcin wadan nan da kuma raunin hankulan su.

Kuma maganin wannan nau'in yana kasancewa da al'amura biyu ne; Al'amari na bangaran maralafiya da al'amari na kuma bangaren maimagani, wanda yake bangaran maralafiya yana kasancewa da karfin ransane, da gaskiyar fuskantar sa ga wanda ya halicci wadannan rayukan wanda yake shi ne kuma Ubangijin rayukan, ta hanyar neman ingantaccen tsari wanda ya dace da zuciya da kuma harshe.

Domin tabbas wannan nau'in abun yaka ne, kuma mai yaki baya samun cin nasara wurin abokin gabarsa da takobi sai da al'amura guda biyu; ya kasance takobin lafiyayye ne a karankansa, kuma ya kasance mai taimakon mai karfine, to duk lokacin da daya daga cikin su ya saba to takobin ba zai yi wani amfani mai yawa ba, to yaya idan aka rasa al'amuran gaba dayan su?, sai zuciya ta lalace game da rashin tauhidi da dogaro ga Allah madaukakin sarki da kuma tsoron Allah da shiryarwa babu wani makami a tare da shi.

Na Biyu daga bangaren mai maganin, ya kasance akwai wadan nan al'amura biyu a tare da shi, kuma harma daga cikin masu magungunan akwai wanda ke wadatuwa da fadain ((Fita daga jikin shi)) ko kuma ya ce: ( بسم الله) ko kuma ya ce: (لا حول ولا قوة إلا بالله)

kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana cewa:

“Fita makiyin Allah, Ni manzon Allah ne"

Kuma na ga malamin mu ya kan aikawa maralafiyan wanda zai yi magana da ran dake cikin sa, sai ya ce: Malam ya ce da kai ka fita, domin lallai wannan baya halatta a gareka. Sai mara lafiyan ya farfado, sai dayawa kuma malam din yakan yi masa magana da kansa.

Wani lokacin kuma aljanin yak an kasance kangararre ne sai yafitar da shi da duka, sai kuma maralafiyan ya farfado sannan kuma ba zai ji zafin dukan ba.

kuma hakika mun gani mu da karankammu da ma wasu mung a hakan daga wurin malam sau da yawa, har inda yake cewa: Adunkule dai wannan nau'in na cuta da maganin sa babu mai inkarinsa sai dai masu karancin kaso na ilimi da kuma hankli da sani.

Kuma mafi yawan miyagun rayuka – ajanu – na samin shiga ne ga karancin fuskantar addini da kuma rushewar zuciyar su da kuma harsunan su na hakikanin zikirori da neman tsari da neman kariya wadanda Annabi ﷺ‬ ya karantar ma su kara imani, sai mummunan rai (aljanu) su hadu da mutumin da ya nesantar da kansa – daga Addu'oi – kenan babu wani makami atare da shi, mai yiwu wa ma yana tsirara sai hakan ya yima sa mummunan tasiri. Nan maganarsa ta kare Allah yayi masa rahama.

Daga abinda muka ambata na dalilan Shari'ah da haduwar bakin ma'abota ilimi na daga ma'abota sunnah akan fahimtar magabata akan yiwuwar shigar aljani jikin dan'adam – ya bayyana ga mai karatu rashin ingancin zancen wanda ke musanta hakan (wato suke musanta shigar aljani jikin dan'adam) da kuma kuskuren babban Malamin nan Aliyu dandawi akan Inkarin sa da hakan.

Kuma hakika ya yi alkawari cikin maganar sa cewa zai karbi – gaskiya a duk lokacinda aka nunar da shi, maiyiwuwa zai dawo ya karbi gaskiyar – bayan ya karanta abinda muka – ambata, kuma muna rukon Allah da ya shiryar da mu da kuma shi, ya kuma datar damu.

Kuma daga cikin abinda muka ambata za'a san cewa lalle abinda jaridar Nadwah ta ruwaito a bugunta na ranar: 14/10/1407h (11/6/1987) shafi na 8 daga Dr. Muhammad Arfan cewar: Hakika ita kalmar Junun (wato hauka) ta boyu a kamus din likitanci, da yadda wai ya ce; lallai shigar aljani jikin mutum da maganarsa da harshen sa lallai hakan fahimtace ta Ilimi akan kuskure dari bisa dari (100%).

Dukkan wadannan magana tasa ba daidaiba ce – kuma hakan ya farune sakamakon karancin ilimin al'amuran shari'a da kuma abunda – ma'abota ilimi na Ahlussunnah a kan fahimtar magabata, kuma idan wannan al'amarin ya boyu ga yawancin likitoci to hakan bai zama hujja akan rashin samuwar sa ba, saidai hakan yana nuni ne akan jahilcin su mai girma na abinda wasun su suka sani da cikin fitattatun malamai da aka sani akan gaskiya da rikon amana da basira game da al'amuran Addini, kai wannan fa shi ne Ijma'in malaman Sunnah wadan da suke fahimtar ilimi akan fahimtar magabata, kamar yadda Shehul-Islam Ibnu Taimiyyah ya ruwaito hakan da dukkan ma'abota ilimi, kuma aka ruwaito daga Abul Hassan Al'ash'ari; cewa lallai shi ya ruwaito hakan ne daga ma'abota Sunnha da jama'a, kuma an ruwaito hakan kuma daga Abul Hassan Ash'ari babban malami Abu Abdullahi Muhammad Ibnu Abdullahi Asshabli Al'hanafi wanda ya rasu a shekara ta 799 (bayan hijira) a cikin littafin sa: (AAKAMUL MARJAN FI GARA'IBIL AKH'BAAR WA AHKAMUL JA'AN) cikin babi na hamsin da daya a cikin wannan littafin na sa.

Haka kuma tabbas ya gabata cikin maganar Ibnul Kayyim -Allah ya yi masa rahama - cewa lallai Kwararrun likitoci da masu hankulan cikin su sun tabbatar da hakan, kuma ba su kore faruwar shi ba, sai dai kawai wadanda suka musanta hakan a bangaren likitoci su ne kuma jahilan cikin su da kaskantattun su da kuma zindikan su.

To, ka sani ya kai dan'uwa mai karatu kuma ka yi ruko da hakikanin bayani na gaskiya da muka yi maka, kar ka rudu da jahilan likitoci da wasun su, ko da wanda ke magana cikin wannan al'amarin ba tare da ilimi ba kuma ba tare da basira ba saidai kawai bin jahilain likitoci da wasu daga cikin 'yanbidi'a – na Mu'utazilah da wasun su, wurin Allah muke neman taimako.

Fadakarwa

Hakika abinda muka ambata a baya na hadisai ingantattu daga Manzon ﷺ‬ da maganganum malamai da suka yi akan cewa; Yin magana da aljani da yi masa wa'azi da tunatar da shi da-kiran sa zuwa ga shiga addinin musulunci da kuma amsawar aljani hakan bai sabawa abinda Allah madaukakin sarki ya fada ba game da Annabii Sulaiman u cikin [Suratu Swad aya ta 35, wato fadin Allah madaukakin sarki (Annabi Sulaimanu y ace):

﴿قَالَ رَبِّ ٱغفِر لِي وَهَب لِي مُلكا لَّا يَنبَغِي لِأَحَد مِّن بَعدِي إِنَّكَ أَنتَ ٱلوَهَّابُ٣٥﴾ ص: ٣٥

Ma'ana: “Ya Ubangiji ka gafarta mini, kuma ka bani kyautar mulki wand aba wanda zai sami irin sa a bayana, lalle kai ne mai yawan kyauta".

Hakanan kuma umarnin aljanin da ya yi da kyakkyawan abu da kuma hana shi da ya yi da mummuna da kuma dukan sa da ay yi domin ya ki fita daga jikinsa dukkan wadan nan ba sa sabawa ayoyin da muka ambata, sai dai hakan ma wajibi ne ta han'yar tunkude zalunci da taimakon wanda aka zalunta, da kuma umarni da kyakkyawa da hanin aikata mummuna kamar yadda ake aikata hakan ga mutum, kuma ya riga ya gabata cikin hadisi ingantacce lallai Annabi tsirada amincin Allah su tabbata a garaeshi ya ce:

((ذعتُّ الشيطان حتى سال لعابه))

Ma'ana: “Na makure shaidan har saida yawun sa ya gudana". A hannun sa mai darajar, kuma Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

((لولا دعوة أخي سليمان لأصبح موثقا حتى يراه الناس))

Ma'ana: “Da badun addu'ar dan'uwana (Annabi) Sulaiman ba to da ya wayi gari a daure har mutane su gan shi". A cikin riwayar Muslim kuma daga hadisin Abuddarda'i daga Annabi tsir da Amincin Allah su tabbata a gareshi lallai ya ce:

((إن عدو الله إبليس جاء بشهاب من نار، ليجعله في وجهي، فقلت: أعوذ بالله منك. ثلاث مرات، ثم قلت: ألعنك بلعنة الله التمة – فلم يستأخر- ثلاث مرات، ثم أردت أخذه، والله لولا دعوة أخي سليمان لأصبح موثقا يلعب به ولدان أهل المدينة))

Ma'ana: “Lalle makiyin Allah lblis ya zo da harshen wuta don ya sa shi a fuska ta sai na ce: lna neman tsarin Allah daga gare ka (sau uku yana fadin hakan), sannan na ce: Ina la'antarka da la'anar Allah cikakka- sai bai motsa ba, sau uku, sannan na yi nufin in kama shi, na rantse da Allah badun addu'ar dan'uwa na (Annabi) Sulaiman ba da ya wayi gari a daure yaran madina su yi wasa da shi".

Hadisai a wannan ma'anar suna da matukar yawa, haka kuma maganganun malamai, kuma ina fatan cikin abinda muka ambata zai wadatar kuma ya gamsar ga dukkan maineman gaskiya, ina rokon Allah da sunayen Sa kyawawa da siffofin Sa madaukaka da ya datar da mu da sauran musulmai ga fahimtar addini da kuma tabbata akan akan addinin, kuma ya yi mana baiwa bakidayam mu da dacewa da gaskiya cikin dukkaninnmaganganummu, da kuma ayyukammu, kuma ya tsare mu da kuma dukkan musulmai daga magana akan Sa (Shi Allah) ba tare da ilimi ba, ya kuma tsaremu daga musanta abinda ba mu da ilimi a kan sa, lallai shi ne majibincin haka kuma mai iko akan hakan.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawan Sa kuma Manzon Sa Annabimmu Muhammad da Iyalan gidan Sa da kuma Sahabban Sa da mabiyan Sa da kyautatawa.

Nau'uka na ilmi: