Mawallafin littafin ya ambaci wadansu gimshikai guda shida, kuma ya yi bayanin abinda ya shafi hakkin Allah akan bayinsa da kuma cewar shi Allah ya umarce su ne da kadaitashi, kuma ya hana su su rarraba ya umarce su da hadin kai, kuma ya maida martini ga rudanin da makiya musulunci suke kawowa.
Malan yayi bayani akan lokutan da addini ya halasta hada salloli biyi da kuma yadda ake hadawa da sallolinda ake hadi tsakaninsu da dalilan dakesa ahada tsakanin salloli biyu.
Malan yayi bayani akan ma anar kiran sallah da lokutan da ya halitta akira sallah da kuma hukunci wanda ke cikin masallaci alokacin kiran sallah da mahimmacinsa amusulinci.