Littafi ne da ya kunshi bayani akan rukunan musulunci da sharuddan Kalmar shahada da kuma tsarin karantar da al’umma, da bayani akan alwala da sallah, da kuma yadda ake shirya janaza da yi mata da tsoratarwa akan shirka, da bayanai akan kyawawan dabi’un musulunci.
Yayi Magana ne akan shika shikai guda uku wanda makamaci kowane Musulmi yasansu sune ilmi da aiki dashi da kira zuwaga allah da kuma hakuri akan cutarwa acikinsa
Yayi Magana ne akan rukunan imani da jajibine Musulmi yayi I mani dasu dakuma mahimmacin imani da allah da mala ikunsa da littaffansa da lahira da sauransu
Littafine da mawallafinsa ya lissafo bayanai masu yawa na dabi’un maguzawa, wadanda tuni musulunci ya yi watsi da su kuma ya bayyana hatsarin da ke cikinsu a addinance da kuma duniyance, abinda yake da matukar muhimmanci kowanne musulmi ya sansu.