Akidar Ahlussunnah Wal Jama’a

nau, i

Littafine da ya tara ingantacciyar akida da ta zama wajibi akan kowanne musulmi ya kudurceta, kamar bayanin shikashikan musulunci da kaddara da abinda ya zama wajibi a sani akan sahabbai.

Download
karubuta zuwaga shugaba wannan shafi

karin bayani

AKIDAR AHLUSSUNAH WAL JAMA'AH

Muhammad Bin Saleh Al'uthaimin

—™

Ibrahim Abdullahi Abubakar

Aliyu Muhammad Sadisu

GABATARWAR WANDA YA DUBA

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya, tsira da amincin Allah su tabbata ga wanda babu wani Annabi bayansa Annabi Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka, wannan littafi mai matukar fa'ida musamman a wannan lokaci mai suna: “Akidar Ahlussunah Wal Jama'a", wanda Shehun Malami Muhammad dan Saleh Al'uthaimin ya wallafa, kuma babban shehun malamin nan Abdul'aziz bin Abdullahi bin Baz ya yi wa gabatarwa, sanna shi kuma Malam Ibrahim Abdullahi Abubakar ya fassara shi zuwa harshen Hausa, hakika littafine da ya kunshi bayana akan abinda ya zama kowanne mutum musulmi ya kudurce ya yi aiki da shi.

Ya yi bayani dalla-dalla akan abinda ya shafi shikashikan Imani daya-bayan-daya, ko ma kace littafin ya kunshi akan ne, da kuma bayanan rukunan Imani da kaddara, da kuma matsayin sahabban ma'aikin Allah ﷺ‬.

Dafatan Allah ya datar da mu ya kuma anfanar da mu, Allah ya yi dadain tsira ga Annabi Muhammad ﷺ‬, da iyalansa da kuma sahabbansa baki daya.

Wanda ya duba

Aliyu Muhammad Sadisu.

[email protected]

GABATARWAR SHEHUN MALAMI IBNU BAZ:

Godiya ta musamman ga Allah shi kadai, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga wanda babu wani Annabi bayansa, da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, hakika na yi nazarin littafin nan na dan'uwa kuma babban malami mai suna Sheikh Muhammad Salih Al'Uthaimin, wanda ya wallafa a kan akida tsayayya a takaice, kuma na ji duk abinda ya kunsa sosai, na same shi shi wannan littafin ya hade duk wani bayani game da akida ta mabiya sunnah da jama'ah, a cikin hanyar tauhidi ( kadaita Allah da bauta) da kuma kadaita shi a cikin sunayansa da siffofinsa (kada a hada shi da kowa a cikinsu) kamar kuma yadda ya yi bayani game da wajabcin bada gaskiya da mala'iku da littattafai da manzanni, da kuma bada gaskiya da ranar kiyama (rayuwa bayan mutuwa).

Ya kuma yi bayani game da wajibcin yarda da kaddara alherinsa da sharrinsa.

Hakika ya ma hada wasu zantuttaka masu amfani da dama dangane da abinda dalibin ilimi da kuma dukkan musulmi yake bukata cikin rukunnan imani guda shida, kuma ya hada bayanai masu amfani matuka dangane da bayani akida wadanda bayanan suke da wuyar samu a sauran littattafai da aka wallafa a wannan na fannin akida.

Allah dai ya saka masa da alheri, ya kuma kara masa ilimi da shiriya, ya kuma amfanar da wannan littafin na shi da sauran litataffan da ya wallafa ya kuma sanya mu mu da shi da sauran 'yan'uwa cikin shiriya kuma masu shiryarwa, masu kira zuwa ga hanyar Allah da basira lalle shi Allah mai ji ne kuma kusa yake (ga mai kiransa).

Shehun Malami Abdul-aziz bin Abdullah bn Bazz.

ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, kuma kyawawan makoma suna ga masu kiyaye dokar Allah, kuma babu kiyayya sai ga azzalumi. Na kuma shaida cewa babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah, Shi kadai yake, ba shi da abokin tarayya bayyananar sarauta ta gaskiya ta shi ce, kuma na shaida cewa lalle (Annabi) Muhammadu bawan sane kuma manzon sane. Shi ne karshen Annabawa kuma shugaban masu kiyaye dokar Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar kiyama.

Bayan haka, lalle Allah ta'ala ya aiko manzonsa Annabi Muhammad (ﷺ‬) da shiriya da kuma addinin gaskiya domin ya zamo jagora ga dukkan talikkai kuma ya zama hujja ga dukkan bayi. Ya bayyana addini da shi (wannan Annabi) da kuma abinda aka saukar na littafi da kuma hadisi na dukkan abin da zai zama gyaruwar bayin Allah da kuma tabbatar da halayensu a cikin addininsu da rayuwarsu: na daga ingantacciyar akida da ayyuka na gaskiya da kyawawan dabi'u da kuma ladubba na karamci. Hakika Annabi ﷺ‬ ya bar mutane akan hanya mai haske wadda darenta yake kamar yininta babu mai bacewa a cikinta sai halakakke.

Sai al'ummar Annabi ﷺ‬ suka tabbata akan haka, daga cikin wadanda suka amsa kiran Allah da manzon sa, kuma sune zababbu daga cikin halittar Allah: daga cikin Sahabbai da Tabi'ai da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa, sai suka tsayu a kan shari'arsa suka yi riko da tafarkinsa kuma suka rike ta da turaman hakora, na abinda suka kudurta na bauta da kyawawan dabi'u da kuma ladubba. Sai suka zamo jama'a da bata gushe ba a kan zahirin gaskiya, kuma ba ya cutar da su duk wulakanta su ko ya sabamasu har al'amarin Allah ya zo suna nan akan haka.

Kuma mu -godiya ta tabbata ga Allah- masu bin karantarwar su da kuma tarihin su ne, ya sa muka yi riko da littafi da kuma Sunnah shiryayya, za mu fadi haka ne don nuna godiya da ni'imar Allah ta'ala da kuma bayanin abin da ya wajaba mumini ya kasance akai.

Allah ta'ala muke roko ya tabbatar da mu da al'ummar musulmi da zance na gaskiya a rayuwar duniya da lahira, ya kuma yi mana baiwa daga gareshi ta rahma, lalle shi ne mai cikakkiyar baiwa.

Kuma saboda muhimmancin wannan maudu'i na Tauhidi da kuma banbance-banbance akidu da mutane suke da shi sai na so in takaita zance na akan akidar mu: Akidar Ahlussunnah Wal Jama'ah itace kuwa: Imani da Allah, mala'iku, littattafai, manzanni, da ranar karshe da kuma imani da kaddararsa ta alheri ko ta sharri.

Allah nake roko ya sanya wannan aiki dominsa, kuma mai dacewa da yardarsa kuma mai amfanuwa ga bayin Allah.

AKIDARMU:

Akidarmu (wato abinda muka kudurce a zuciya) Shine: Imani da Allah da mala'ikkunsa da littattafansa da manzanninsa da ranar karshe da kuma imani da kaddara alherinsa da sherinsa.

Saboda haka mun yi imani da rububiyar Allah ta'ala: watau Allah shi ne Ubangiji mahalicci mamallaki mai kuma juya al'amura bakidaya, kuma mun yi imani da kadaitakar Allah da cewa shi ne abin bauta da cancanta kuma duk abin bauta bayansa bata ne.

Kuma mun yi imani da sunayansa da siffofinsa da cewa shi kadai yake da kyawawan sunaye da kuma siffofi cikakku madaukaka.

Kuma mun yi imani da kadaituwarsa a cikin dukkan haka da cewa ba shi da abokin tarayya a rububiyar sa da uluhiyya haka kuma a cikin sunayansa da siffofinsa madaukaka. Allah ta'ala yace:

﴿رَّبُّ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ وَمَا بَينَهُمَا فَٱعبُدهُ وَٱصطَبِر لِعِبَدَتِهِ هَل تَعلَمُ لَهُ سَمِيّا٦٥﴾

Ma'ana:“Ubangijin sammai da kassai da abinda ke tsakaninsu sai ka bauta masa kuma ka jajirce akan bautarsa, shin ka taba sanin wani mai irin sunansa". (Maryam: 65).

Kuma munyi imani da cewa lalle shi ne:

﴿ٱللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ ٱلحَيُّ ٱلقَيُّومُ لَا تَأخُذُهُ سِنَة وَلَا نَوم لَّهُ مَا فِي ٱلسَّمَوَتِ وَمَا فِي ٱلأَرضِ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشفَعُ عِندَهُ إِلَّا بِإِذنِهِ يَعلَمُ مَا بَينَ أَيدِيهِم وَمَا خَلفَهُم وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيء مِّن عِلمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرسِيُّهُ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضَ وَلَا يَُودُهُ حِفظُهُمَا وَهُوَ ٱلعَلِيُّ ٱلعَظِيمُ٢٥٥﴾

Ma'ana:“Allah wanda babu wani abin bautawa da cancanta sai shi, rayayyene kuma tsayayye, gyangyadi baya kamashi balle bacci, dukkan abinda ke cikin sammai da kassai na shi ne, wa zai yi ceto a wurinsa? Sai da izininsa, yana sane da abinda ke gabansu da bayansu, babu wani abinda zasu sani na daya daga cikin iliminsa sai abinda ya so, kursiyinsa ya yalwaci sammai da kassai, kiyaye su baya gagararsa, kuma shi ne madaukaki mai girma". (Bakara :255).

Kuma munyi imani da cewa shi ne:

﴿هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ عَلِمُ ٱلغَيبِ وَٱلشَّهَدَةِ هُوَ ٱلرَّحمَنُ ٱلرَّحِيمُ٢٢ هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ ٱلمَلِكُ ٱلقُدُّوسُ ٱلسَّلَمُ ٱلمُؤمِنُ ٱلمُهَيمِنُ ٱلعَزِيزُ ٱلجَبَّارُ ٱلمُتَكَبِّرُ سُبحَنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشرِكُونَ٢٣ هُوَ ٱللَّهُ ٱلخَلِقُ ٱلبَارِئُ ٱلمُصَوِّرُ لَهُ ٱلأَسمَاءُ ٱلحُسنَى يُسَبِّحُ لَهُ مَا فِي ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ وَهُوَ ٱلعَزِيزُ ٱلحَكِيمُ٢٤﴾

Ma'ana:“Shi ne Allah wanda babu wani abin bautawa da cancanta sai shi, masanin abinda ke boye da sarari, kuma shi ne mai rahma mai jin kai. Shi ne Allah wanda babu wani abin bautawa da cancanta sai shi, mai mulki mai tsarki mai aminci, mai amincewa mai saukakawa mabuwayi mai karfi mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah daga barin masu shirka. Shi ne Allah mahalicci mai kirkiran halitta mai suranta halitta, kyawawan sunaye sun tabbata a gareshi, abinda ke cikin sammai da kasa suna masa tasbihi (suna tsarkakeshi) kuma shi ne mabuwayi mai hikima". (Hashr :22-24).

Kuma muna imani da cewa mulkin sammai da kasa na shi ne:

﴿لِّلَّهِ مُلكُ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ يَخلُقُ مَا يَشَاءُ يَهَبُ لِمَن يَشَاءُ إِنَثا وَيَهَبُ لِمَن يَشَاءُ ٱلذُّكُورَ٤٩ أَو يُزَوِّجُهُم ذُكرَانا وَإِنَثا وَيَجعَلُ مَن يَشَاءُ عَقِيمًا إِنَّهُ عَلِيم قَدِير٥٠﴾

Ma'ana:“Yana halittar abinda yake so, yana kyautar 'ya'ya mata ga wanda ya so, kuma yana kyautar 'ya'ya maza ga wanda ya so, ko kuma ya sirka maza da mata ('ya 'ya) kuma yana sanya wanda yaso bakarare (wanda ba ya haihuwa), lalle shi mai ilimine kuma mai kaddarawa". (Shurah 49-50).

kuma muna imani da cewa:

﴿فَاطِرُ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ جَعَلَ لَكُم مِّن أَنفُسِكُم أَزوَجا وَمِنَ ٱلأَنعَمِ أَزوَجا يَذرَؤُكُم فِيهِ لَيسَ كَمِثلِهِ شَيء وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلبَصِيرُ١١ لَهُ مَقَالِيدُ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ يَبسُطُ ٱلرِّزقَ لِمَن يَشَاءُ وَيَقدِرُ إِنَّهُ بِكُلِّ شَيءٍ عَلِيم١٢﴾

Ma'ana:“Allah babu wani abinda ya yi kama da shi, kuma shi ne mai ji mai gani. Mabudan arzikin sammai da kassai na shi ne yana bada arziki ga wanda ya so ya kuma sanya kunci ga wanda ya so kuma lalle shi akan dukkan komai masani ne". (Shurah: 11-12).

kuma muna imani da cewa:

﴿وَمَا مِن دَابَّة فِي ٱلأَرضِ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِ رِزقُهَا وَيَعلَمُ مُستَقَرَّهَا وَمُستَودَعَهَا كُلّ فِي كِتَب مُّبِين٦﴾

Ma'ana:“Babu wata halitta da ke bayyan kasa face arzikinta na hannun Allah, yana sane da mazauninta da kuma inda za'a binneta, kuma komai yana cikin littafi mabayyani". (lauhul mahfuz) (Hud: 59).

Kuma muna imani da cewa:

﴿ٱلحَمدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضَ وَجَعَلَ ٱلظُّلُمَتِ وَٱلنُّورَ ثُمَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِم يَعدِلُونَ١﴾

Ma'ana:“Mabudan gaibi suna a hannunsa babu wanda ya sansu, shi ke sane da abinda ke bayan kasa da cikin ruwa, babu wani ganye ko kwayar da zai fadi a cikin duhun kasa face yana sane ita, haka ko da danye ne ko busashe face ya kasance a cikin littafi mabayyani". (An'am: 59).

Kuma muna Imani da cewa lalle Allah shi ne:

﴿إِنَّ ٱللَّهَ عِندَهُ عِلمُ ٱلسَّاعَةِ وَيُنَزِّلُ ٱلغَيثَ وَيَعلَمُ مَا فِي ٱلأَرحَامِ وَمَا تَدرِي نَفس مَّاذَا تَكسِبُ غَدا وَمَا تَدرِي نَفسُ بِأَيِّ أَرض تَمُوتُ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرُ٣٤﴾

Ma'ana:“Kuma a wurinsane kadai sanin lokacin alkiyama, kuma yana saukar da ruwan sama, kuma ya san abindake cikin mahaifa, kuma rai batasan me zata aikata a gobeba, kuma rai batasan a ina zata mutuba, lalle Allah masanine kuma maibada labara". (Lukman:34).

Kuma muna imani da cewa Allah yana magana da duk abinda yaso, lokacin da yaso kuma yadda yaso.

﴿ وَكَلَّمَ ٱللَّهُ مُوسَى تَكلِيما١٦٤﴾

Ma'ana:“Kuma Allah ya yi magana da (Annabi) Musa hakikanin magana". (Nisa'i: 164).

﴿وَلَمَّا جَاءَ مُوسَى لِمِيقَتِنَا وَكَلَّمَهُ رَبُّهَُ١٤٣﴾

Ma'ana: “Kuma lokacin da Musa ya zo mikatin mu kuma Ubangijinsa ya yi zance da shi". (A'araf: 143).

﴿وَنَدَينَهُ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ ٱلأَيمَنِ وَقَرَّبنَهُ نَجِيّا٥٢﴾

Ma'ana:“Kuma mun kira shi ta gyaifen daman dutsen turi, sai muka kusantar da shi domin zantawa". (Maryam: 52).

Kuma muna imani da cewa:

﴿قُل لَّو كَانَ ٱلبَحرُ مِدَادا لِّكَلِمَتِ رَبِّي لَنَفِدَ ٱلبَحرُ قَبلَ أَن تَنفَدَ كَلِمَتُ رَبِّي وَلَو جِئنَا بِمِثلِهِ مَدَدا١٠٩﴾

Ma'ana:“Da koguna zasu zama tawada sa'annan bishiyoyi su zama alkalumma na rubuta kalmomin Ubangiji na da kogunan sun kafe kafin kalmomin Ubangiji na". (Kahf: 109).

﴿وَلَو أَنَّمَا فِي ٱلأَرضِ مِن شَجَرَةٍ أَقلَم وَٱلبَحرُ يَمُدُّهُ مِن بَعدِهِ سَبعَةُ أَبحُر مَّا نَفِدَت كَلِمَتُ ٱللَّهِ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيم٢٧﴾

Ma'ana:“Kuma ko da abinda ke bayan kasa na bishiyoyi su ma su zama alkalumma kuma kogi yana karoshi bayansa kuma koguna bakwai (domin rubuta kalmomin Ubangiji) to kalmomin Allah ba za su kare ba, lalle Allah mabuwayine mai hikima". (Lukman: 27).

Kuma muna yin imani da cewa: Maganganun Allah cikakku ne, wajan bada labarin gaskiya da kuma adalci wajan hukunci, kuma mafi kyawon zance. Allah ta'ala ya ce:

﴿وَتَمَّت كَلِمَتُ رَبِّكَ صِدقا وَعَدلا لَّا مُبَدِّلَ لِكَلِمَتِهِ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلعَلِيمُ١١٥﴾

Ma'ana:“Kuma Kalmar Ubangijinka ta cika da gaskiya da adalci". (An'am: 115). Kuma ya kara da cewa:

﴿ وَمَن أَصدَقُ مِنَ ٱللَّهِ حَدِيثا٨٧﴾

Ma'ana:“Wa ya fi gaskiyar zance kamar Allah"?. (Nisa'i :87).

Kuma muna imani da cewa alkur'ani mai girma zancen Allah ta'ala ne, ya yi zancen gaskiya da shi, kuma ya jefa shi zuwa ga Mala'ika Jibrilu sai Mala'ika Jibrilu ya saukar da shi a zuciyar Annabi Muhammad ﷺ‬:

﴿قُل نَزَّلَهُ رُوحُ ٱلقُدُسِ مِن رَّبِّكَ بِٱلحَقَِّ١٠٢﴾

Ma'ana:“Kace ruhi mai tsarki ne ya saukar da shi daga wurin Ubangijinka da gaskiya". (Nahl: 102).

﴿وَإِنَّهُ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلعَلَمِينَ١٩٢ نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلأَمِينُ١٩٣ عَلَى قَلبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلمُنذِرِينَ١٩٤ بِلِسَانٍ عَرَبِيّ مُّبِين١٩٥﴾

Ma'ana:“Kuma lalle shi (Alkur'ani) saukakke ne daga wajen Ubangijin halittu, ruhi amintacce ne ya saukar da shi a cikin zuciyarka domin ka kasance cikin masu gargadi, da halshen larabci mabayyani". (Shu'ara'i: 192-195).

Kuma muna imani da cewa lalle Allah madaukaki ne akan halittun sa da zatinsa da kuma siffofin sa, domin Allah ta'ala yace:

﴿ وَهُوَ ٱلعَلِيُّ ٱلعَظِيمُ٢٥٥﴾

Ma'ana:“Kuma shi ne madaukaki mai girma". (Bakara: 255) kuma da fadarsa madaukakin sarki:

﴿وَهُوَ ٱلقَاهِرُ فَوقَ عِبَادِهِ وَهُوَ ٱلحَكِيمُ ٱلخَبِيرُ١٨﴾

Ma'ana:“Kuma shi ne mai rinjaye akan bayinsa, kuma shi ne mai hikima mai bada labara". (An'am: 18).

Kuma muna imani da cewa Allah shi ne:

﴿إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضَ فِي سِتَّةِ أَيَّام ثُمَّ ٱستَوَى عَلَى ٱلعَرشِ يُدَبِّرُ ٱلأَمرَ مَا مِن شَفِيعٍ إِلَّا مِن بَعدِ إِذنِهِ ذَلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُم فَٱعبُدُوهُ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ٣﴾

Ma'ana:“Ya halicci sammai da kassai a cikin kwanaki shida sa'annan ya daidaita akan al'arshi (daidaituwar da ta dace da shi), mai juya al'amurrah ne".(Yunus: 3).

Daidaituwa akan al'arshi shi ne daukakar Sa da zatin Sa, daukaka kebabbiya wadda take tare da girmansa, babu wanda yasan yaya yake sai shi, kuma muna imani da cewa Allah ta'ala yana tare da halittunsa alhali kuwa yana kan al'arshi (tarayya da iliminsa) yana sa ne da halayensu kuma yana jin zantuttukansu, yana ganin ayukkansu, yana jujjuya al'amuransu yana azurta talaka, yana dora wanda ya samu karayar arziki, yana bada mulki ga wanda yaga dama, ya kwace mulki daga wanda yaso dukkan alheri daga hannunsa, kuma shi akan dukkan komai mai iko ne.

Duk wanda ya kasance da irin wannan sha'ani tabbas yana tare da bayin sa, ko da yake yana kan al'arshinsa;

﴿ لَيسَ كَمِثلِهِ شَيء وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلبَصِيرُ١١﴾

Ma'ana:“Babu wanda ya yi kama da shi, kuma shi ne mai ji mai gani". (Shurah: 11).

Kuma ba zamu fada kamar yadda hulluyin (masu cewa Allah na shiga komai) daga cikin jahamawa da wasunsu ba, suna cewa lalle shi Allah yana tare da halittun sa, a cikin kasa, kuma muna ganin cewar duk wanda ya fadi haka haka to shi kafiri ne ko batacce, domin ya siffanta Allah da abinda yake tawayaye ne.

Kuma muna imani da abinda Manzonsa ﷺ‬ ya bada labari game da shi cewa lalle shi yana sauka zuwa sama ta duniya (makusanciya) a cikin kowani kashi na uku daga cikin dare sai ya ce: “Wa zai rokeni in karba masa? Wa zai rokeni in ba shi? Wa zai nemi gafara in gafarta masa?. (Bukhari da Muslim suka ruwaitoshi).

Kuma muna bada gaskiya da Allah tsarkakakken sarki zai zo ranar karshe (ranar alkiyama) domin rabewa tsakanin bayi saboda fadinsa madaukakin sarki:

﴿كَلَّا إِذَا دُكَّتِ ٱلأَرضُ دَكّا دَكّا٢١ وَجَاءَ رَبُّكَ وَٱلمَلَكُ صَفّا صَفّا٢٢ وَجِاْيءَ يَومَئِذِ بِجَهَنَّمَ يَومَئِذ يَتَذَكَّرُ ٱلإِنسَنُ وَأَنَّى لَهُ ٱلذِّكرَى٢٣﴾

Ma'ana:“Ina! Lokacin da Allah zai nike kasa matukar nikewa, mala'iku su zo sahu-sahu, sai a zo da jahannama a wannan ranar, a lokacin sai mutum ya tuna da abinda ya aikata". (Fajr: 2-23).

Kuma muna bada gaskiya da shi Allah ta'ala cewa:

﴿فَعَّال لِّمَا يُرِيدُ١٦﴾

Ma'ana:“Mai aikata abin da ya yi nufi ne". (Buruj: 16).

Kuma muna bada gaskiya da cewa nufin Allah kasha biyu ne:

Kauniyah: Wadda take aukuwa da nufinsa amma bai zama dole yana son shi ba, kuma ita ce ke daukar ma'anar mashi'ah (ganin dama) kamar yadda Allah ta'ala yace:

﴿ وَلَو شَاءَ ٱللَّهُ مَا ٱقتَتَلُواْ وَلَكِنَّ ٱللَّهَ يَفعَلُ مَا يُرِيدُ٢٥٣﴾

Ma'ana:“Da Allah ya gadama da ba su yi kasha-kashe ba, amma Allah ya na aikata abin da ya yi nufi". (Bakara 253), kuma ya ce:

Shar'iyyah: Kuma wanda yake shar'i baya lizimtar faruwar abu da nufinsa, amma ba ya kasancewa sai a abinda ake so, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce;

﴿وَٱللَّهُ يُرِيدُ أَن يَتُوبَ عَلَيكُم ٢٧﴾

Ma'ana:“Allah yana nufin ku da tuba…' (yana son ku tuba)". (Nisa'i: 27).

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle nufinsa kauni (wato wanda ya kasantar) da shar'i (wanda ya shar'anta) suna biye ne da hikimar sa, haka kuma duk abin da ya hukunta kasancewarsa ko kuma ya bautar da bayinsa da shi ta hanyar shari'a to lalle ne wannan abun akwai hikima kuma akan daidai da hikimar daidaine mun sani ko kwakwalammu ba su kai ga sanin hakan ba, Allah madaukakin sarki ya ce:

﴿أَلَيسَ ٱللَّهُ بِأَحكَمِ ٱلحَكِمِينَ٨﴾

Ma'ana:“Ashe ba Allah ne mafi hikimar masu hikima?". (Tin: 8).

﴿ وَمَن أَحسَنُ مِنَ ٱللَّهِ حُكما لِّقَوم يُوقِنُونَ٥٠﴾

Ma'ana:“Kuma wa yafi Allah kyakkyawan hukunci ga mutane masu sakankancewa". (Ma`ida: 50).

Kuma muna ba da gaskiya da cewa Allah ta'ala yana da masu jibintarsa kuma suna son shi (Waliiyansa):

﴿قُل إِن كُنتُم تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِي يُحبِبكُمُ ٱللَّهُ وَيَغفِر لَكُم ذُنُوبَكُم وَٱللَّهُ غَفُور رَّحِيم٣١﴾

Ma'ana:“Kace in kun kasance kuna son Allah to ku yi mun biyayya Allah zai so ku". (Ali Imran: 31).

﴿ فَسَوفَ يَأتِي ٱللَّهُ بِقَوم يُحِبُّهُم وَيُحِبُّونَهُ ٥٤﴾

Ma'ana:“Da sannu Allah zai zo da wasu mutane (daban) yana son su kuma suna son Shi (Allah)". (Ma'ida: 54).

﴿ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلصَّبِرِينَ١٤٦﴾

Ma'ana:“Kuma allah yana son masu hakuri". (Ali-Imran: 146).

﴿ وَأَقسِطُواْ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلمُقسِطِينَ٩﴾

Ma'ana:“Kuma ku yi adalci, Allah yana son masu adalci". (Hujurat: 9). Kuma ya ce:

﴿ وَأَحسِنُواْ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلمُحسِنِينَ١٩٥﴾

Ma'ana:“Ku kyautata, lalle Allah yana son masu kyautatawa". (Bakara 195).

Kuma muna bada gaskiya da cewa Allah ta'ala yana yarda da abinda ya shar'anta na daga ayukka da zantuttuka, kuma yana kin abinda ya yi hani da abarshi, Allah madaukakin sarki yace:

﴿إِن تَكفُرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ عَنكُم وَلَا يَرضَى لِعِبَادِهِ ٱلكُفرَ ٧﴾

Ma'ana: “In kuka kafirce to lalle Allah wadatacce ne daga barin ku, amma baya yarda ma bayinsa da kafirci, kuma in kun gode yana yardar muku da haka". (Zumar: 7). Kuma ya ce:

﴿ وَلَكِن كَرِهَ ٱللَّهُ ٱنبِعَاثَهُم فَثَبَّطَهُم وَقِيلَ ٱقعُدُواْ مَعَ ٱلقَعِدِينَ٤٦﴾

Ma'ana:“Sai dai Allah ya kyamace ya aika su, saida tabbatar dasu ya ce; ku zauna tare da mazauna". (Tauba: 46).

Kuma muna bada gaskiya da cewa Allah ya yarda ga muminai da kuma aiki na kwarai:

﴿ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنهُم وَرَضُواْ عَنهُ ذَلِكَ لِمَن خَشِيَ رَبَّهُ٨﴾

Ma'ana:“Allah ya yarda da su kuma sun yarda da (Shi) Allah, wannan lamari ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa ne". (Bayyina: 8).

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle Allah ta'ala yana fushi akan wanda ya cancanci fushinsa kamar kafirrai a wasunsu:

﴿ ٱلظَّانِّينَ بِٱللَّهِ ظَنَّ ٱلسَّوءِ عَلَيهِم دَائِرَةُ ٱلسَّوءِ ا٦﴾

Ma'ana:“Masu zato ga Allah mummuna, a gare su mumuna take kuma Allah ya yi fushi da su". (Fathi: 6).

﴿مَن كَفَرَ بِٱللَّهِ مِن بَعدِ إِيمَنِهِ إِلَّا مَن أُكرِهَ وَقَلبُهُ مُطمَئِنُّ بِٱلإِيمَنِ وَلَكِن مَّن شَرَحَ بِٱلكُفرِ صَدرا فَعَلَيهِم غَضَب مِّنَ ٱللَّهِ وَلَهُم عَذَابٌ عَظِيم١٠٦﴾

Ma'ana:“Kuma duk wanda kafirci ya bude zuciyarsa to fushin Allah ya tabbata a gareshi tare da azaba mai girma". (Nahl: 106).

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle Allah ta'ala yana da fuska wadda ta siffantu da dankaka da karamci:

﴿وَيَبقَى وَجهُ رَبِّكَ ذُو ٱلجَلَلِ وَٱلإِكرَامِ٢٧﴾

Ma'ana:“Kuma fuskar Allah ma'abocin daukaka da karamci zai saura". (Rahman: 27).

Kuma muna bada gaskiya da cea Allah ta'ala yana da hannuwa biyu masu girma:

﴿ بَل يَدَاهُ مَبسُوطَتَانِ يُنفِقُ كَيفَ يَشَاءُ ٦٤﴾

Ma'ana: “Saidai hannuwansa biyu shimfide suke yana ciyarwa yadda ya so". (Ma'ida: 64).

﴿وَمَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدرِهِ وَٱلأَرضُ جَمِيعا قَبضَتُهُ يَومَ ٱلقِيَمَةِ وَٱلسَّمَوَتُ مَطوِيَّتُ بِيَمِينِهِ سُبحَنَهُ وَتَعَلَى عَمَّا يُشرِكُونَ٦٧﴾

Ma'ana:“Kuma basu girmama Allah ba matukar girmamawa, kuma kasa baki daya zai damkarsa ce ranar alkiyama sammai kuma a nade suke a (hannun) daman sa, tsarki da daukaka sun tabbata a gareshi daga barin mushirikai". (Zumar: 67).

Kuma muna bada gaskiya da cewa Allah ta'ala yana da tabbatattun idanuwa biyu, domin fadin sa madaukakin sarki:

﴿وَٱصنَعِ ٱلفُلكَ بِأَعيُنِنَا وَوَحيِنَا ٣٧﴾

Ma'ana:“Kuma ka kera jigin ruwa a gaban idon mu ta hanyar wahayi". (Hud: 37), kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; “Shamakin sa haske ne, da zai kware shi da hasken fuskarsa ya kona duk halittunsa zuwa karshen inda ganinsa ya kai". [Muslim].

Kuma duk Ahlussunnah sun hadu akan cewa yana da idanuwa biyu, kuma abinda yake karfafa hakan shi ne maganar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada game da Jujal ya ce: “Lalle shi yana da ido daya ne kuma Ubangijinku ba mai ido daya ba ne". [Bukhari da Muslim].

Kuma muna bada gaskiya da cewa Allah ta'ala “ganin bayinsa ba ya riskarsa amma ganinsa yana riskuwar su kuma shi mai tausayi ne mai ba da labara". (An'am: 103).

﴿لَّا تُدرِكُهُ ٱلأَبصَرُ وَهُوَ يُدرِكُ ٱلأَبصَرَ وَهُوَ ٱللَّطِيفُ ٱلخَبِيرُ١٠٣﴾

Kuma muna bada gaskiya da cewa muminai zasu ga Ubangijin su ranar kiyama “A ranar wasu fuskoki zasu kasance masu haske, zuwa ga dubin Ubangijin su". (Kiyama: 22-23).

﴿وُجُوه يَومَئِذ نَّاضِرَةٌ٢٢ إِلَى رَبِّهَا نَاظِرَة٢٣﴾

Kuma muna bada gaskiya da cewa Allah ta'ala babu mai kama da shi domin cikar siffofin sa “Babu wanda ya yi kama da shi, kuma shi mai jine mai gani ne". (Shura: 11).

﴿ لَيسَ كَمِثلِهِ شَيء وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلبَصِيرُ١١﴾

Kuma muna bada gaskiya da cewa: “Lalle shi gyan-gyadi ba ya kamashi, balle barci"…. (Bakara: 255).

﴿ لَا تَأخُذُهُ سِنَة وَلَا نَوم ٢٥٥﴾

Domin cikar rayuwarsa da kula da bayinsa.

Kuma muna bada gaskiya da cewa: Lalle shi ba ya zaluntar daya daga cikin bayinsa saboda cikar adalcinsa, kuma shi ba gafalalle ba ne game da ayukkan bayinsa domin cikar kusancin sa da kiyayewarsa.

Kuma muna ba da gaskiya da cewa babu abinda yake gagararsa acikin sammai da kassai domin cikar iliminsa da ikon sa“lalle abin da yake al'amari gare shi shine idan ya yi nufin wani abu sai ya ce masa; Kasance' sai yai ta kasancewa". (Yasin: 82).

﴿إِنَّمَا أَمرُهُ إِذَا أَرَادَ شَيًا أَن يَقُولَ لَهُ كُن فَيَكُونُ٨٢﴾

Da kuma sanin cewa gajiya bata kamashi balle kasala domin cikar karfinsa “Hakika mun halicci sammai da kassai da abinda ke tsakaninsu a cikin kwanaki shida ba tare da gajiya ba".(Kaf: 38).

﴿وَلَقَد خَلَقنَا ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضَ وَمَا بَينَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّام وَمَا مَسَّنَا مِن لُّغُوب٣٨﴾

Wato gajiya da kasala.

Kuma muna bada gaskiya da duk abinda Allah madaukakin sarki ya tabbatar wa kansa ko manzonsa ﷺ‬ ya tabbatar masa na daga sunayen sa da siffofinsa, sai dai mu na barranta daga munanan abubuwa manya guda biyu su ne kuma:

1.Kamantawa:- shi ne mutum ya riya a zuciyarsa ko ya fada da bakinsa cewa siffar Allah ta yi kama da halittarsa.

2.Kamanceniya:- shi ne mutum ya raya a zuciyarsa ko ya fada da bakinsa cewa Allah ga yadda yake.

Kuma muna bada gaskiya da kore duk wani abu da Allah ya kore wa kansa ko manzonsa ﷺ‬ ya kore masa, tare da cewa korewa tana kunshe da tabbatar wa Allah cika game da kishiyar abinda aka kore, kuma muna shiru akan abun da Allah madaukakin sarki ya yi shiru kuma Manzanshi ﷺ‬ ya yi shiru.

Kuma muna ganin lalle tafiya akan wannan tafarki wajibi ne babu makawa akan haka. Kuma duk abinda Allah ya tabbatar wa kansa ko ya kore wa kansa labari ne wanda ya bayar game da kansa, kuma shi ya fi sanin kansa, mafi gaskiyar zance, mafi kyawun zance dukkan bayi babu wanda ya kai iliminsa.

Kuma abin Manzonsa ﷺ‬ ya tabbatar masa dashi ko ya kore masa labarine wanda ya bayar kuma shi ne mafi sanin Ubangijinsa game da mutane, nagartacce mafi gaskiya da kyawun zance ga Ubangijinsa akan sauran halittu.

A cikin zancen Allah ta'ala da kuma Manzonsa ﷺ‬ akwai cika wajen ilimi da gaskiya da bayani wanda babu uzuri ga wani ya yi kokwanto ko ya yi watsi da shi.

FASALI

Dukkan abinda muka dunkule na siffofin Allah ta'ala a fayyace ko kuma a dunkule wanda yake tabbatar wa da kuma wanda yake karewa, Kuma mu masu dalilaine daga littafin Ubangijimmu da kuma Sunnar Annabin mur. Haka kuma sauran malamai magabata da kuma manyan malamai da ake koyi da su da suka tabbata akan shirya wadda suka zo bayan Annabi ﷺ‬.

Kuma muna ganin cewa wajibi ne a tafiyar da Alkur'ani da Sunnar Annabi rakan haka, (siffofin Allah) akan zahirinsu, kuma daukesu akan hakikani yadda suke wanda ya dace da Allah madaukakin sarki kuma mabuwayi.

Kuma muna barranta daga hanyoyin masu canza sunayen Allah da siffofin Sa wadanda suka karkatar da su ba ta inda Allah da Manzonsa suke nufi ba.

Da kuma barranta daga hanyar masu korewa Allah sunaye da siffofi, wadanda suka koresu daga barin abinda suke nunarwa, wanda Allah da Manzonsa ﷺ‬ suke nufi.

Da kuma hanyar mutanen da suka wuce iyaka akan sunayan Allah da siffofinsa, wadanda suka misilta Allah ko suka dorawa kansu hakikanin yanayin yadda suke.

Kuma muna sane da ilimi na yakani da cewa lalle duk abinda ya zo a littafin Allah ko Sunnar Annabi ﷺ‬ cewa gaskiya ne, sashinsu ba ya warware sashi, domin fadin Allah ta'ala: “Ashe ba za ku yi lura a cikin wannan Alkur'ani ba ko da za ku ce daga wanin Allah yake da an samu sabani mai yawa". [Nisa'i 82].

﴿أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلقُرءَانَ وَلَو كَانَ مِن عِندِ غَيرِ ٱللَّهِ لَوَجَدُواْ فِيهِ ٱختِلَفا كَثِيرا٨٢﴾

Kuma domi cewar warwara tana lizimtar karya wajan bada labari, shi kuwa hakan ya nisanta daga labarin Allah da Manzonsa.

Duk wanda ya yi da'awa akan tufka da war-wara atsakanin Alkur'ani da Sunnar mazon Allah ﷺ‬ to wannan ya tabbata ne domin mummunar manufarsa da wata cutar dake zuciyarsa, sai ya tuba zuwa ga Allah madaukakin sarki ya kuma bar wannan rudaddiyar hanyar ta sa.

Kuma duk wanda ya yi tunanin akwai tufka-da-warwara a cikin littafin Allah ko don karancin iliminsa ne to, wannan zai kasance don karancin ilimnsa ne ko don karancin fahimta, ko karancin neman ilimi akan haka, sai ya yi kokarin neman ilimi da kuma lura da la'akari har gaskiya ta bayyana a gareshi, idan kuma gaskiyar ba ta bayyana a gareshi ba, sai ya maida al'amarinsa zuwa ga wanda ya sani, sai ya kame daga fadawa mummunan tunaninsa, sai ya fada kamar yadda masu zurfi a cikin ilimi suke fada: “Mun yi Imani, dukkanasu daga wurin Ubangijinmu".

[Ali-Imran: 7].

﴿ ءَامَنَّا بِهِ كُلّ مِّن عِندِ رَبِّنَا ٧﴾

Daga nan ya san cewa littafin Allah da Sunnar Manzonsa ﷺ‬ babu tufka-da-warwara a tsakaninsu, haka kuma babu sabani a tsakanin su.

FASALI

Kuma muna bada gaskiya da mala'ikun Allah ta'ala da cewa su “Bayi ne masu karamci, ba sa riga Shi (Ubangijinsu) da zancen kuma su da umarninsa ne suke aiki". [Anbiya'i: 26-27].

﴿وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحمَنُ وَلَدا سُبحَنَهُ بَل عِبَاد مُّكرَمُونَ٢٦ لَا يَسبِقُونَهُ بِٱلقَولِ وَهُم بِأَمرِهِ يَعمَلُونَ٢٧﴾

Allah ta'ala ya haliccesu ne daga haske sai suka tsaya domin yi masa da'a da bauta “Ba sa girmankai akan kin yi masa bauta kuma ba sa gajiya, suna tasbihi dare da rana ba sa gajiya". [Ambiya'i: 19-20].

﴿وَلَهُ مَن فِي ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ وَمَن عِندَهُ لَا يَستَكبِرُونَ عَن عِبَادَتِهِ وَلَا يَستَحسِرُونَ١٩ يُسَبِّحُونَ ٱلَّيلَ وَٱلنَّهَارَ لَا يَفتُرُونَ٢٠﴾

Allah ya boye su daga garemu ba ma ganinsu sai dai akwai Allah madaukakin sarki yana bayyanar da su ga wasu daga cikin bayinsa, domi hakika Manzon Allah ﷺ‬ ya ga Mala'ika Jibrilu a asalin halittarsa yana fiffike dari shida ya tokare ko'ina, sa'annan kuma Jibrilu ya zo wa Nana Maryam gyatumar Annabi Isah u da siffar mutum ya yi mata magana kuma ta amsa masa. Kuma ya zo wurin Annabi ﷺ‬ cikin Sahabbansa a siffar mutum wanda babu wanda yasan kamarsa kuma babu alamun tafiya a tare da shi, mai farin tufafi mai bakin gashi, sai ya zauna a wurinsa ya jingina gwaiwarsa akan guiwar Annabi ﷺ‬ ya kuma dora tafin hannunsa akan cinyarsa sai ya yi zance da Annabi ﷺ‬ Annabi kuma ya amsa masa, Annabi kuma ya ba Sahabbansa labarin cewa lalle Jibrilu ne. [Bukhari da Muslim].

Kuma muna ba da gaskiya da cewa lalle mala'iku suna da ayukkansu wanda Allah ya dora musu, daga cikinsu akwai Mala'ika Jibrilu wanda aka dora masa saukar da wahayi, yana saukar da shi ne daga wurin Allah madaukakin sarki zuwa ga wanda Allah ya zaba daga cikin Annabawansa da Manzanninsa.

Akwai kuma daga cikinsu Maka'ika wanda aka dorawa saukar da ruwan sama da kuma fitar da tsiro.

Akwai kuma Israfilu wanda aka dorawa busa kaho a lokacin mutuwa da kuma lokacin tashi.

Akwai Malakul maut (Mala'ikan mutuwa) wanda aka dorawa karbar rayuka a lokacin mutuwa.

Akwai mala'ikan tsaunuka mai kula dasu.

Akwai mala'ika mai tsaran wuta.

Akwai mala'iku wadanda aka wakilta domin tsaron rayuka a cikin mahaifa, wasu kuma domin tsaron 'yan'Adam, wasu kuma domin ayyukansu, kowanne mutum yana da mala'iku biyu. “Daga gefen dama da gefen hagu akwai mai tsaro" babu wani lafazi da zasu furta face akwai Rakib da Atid a tare dashi". [Kaf: 17-18].

﴿إِذ يَتَلَقَّى ٱلمُتَلَقِّيَانِ عَنِ ٱليَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ قَعِيد١٧ مَّا يَلفِظُ مِن قَولٍ إِلَّا لَدَيهِ رَقِيبٌ عَتِيد١٨﴾

Da kuma wasu wadanda aka wakilta domin tambayoyi bayan kiran karshe zuwa makomarsa, sai mala'iku biyu su zo suna tambayarsa game da Ubangijinsa, da kuma Addininsa da Annabin sa sai “Allah ya tabbatar (datar) da wanda ya yi imani da zance tabbatacce a cikin duniya da lahira, kuma Allah yana batar da azzalumai kuma Allah yana aikata duk abinda ya so". [Ibrahim: 27].

﴿يُثَبِّتُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱلقَولِ ٱلثَّابِتِ فِي ٱلحَيَوةِ ٱلدُّنيَا وَفِي ٱلأخِرَةِ وَيُضِلُّ ٱللَّهُ ٱلظَّلِمِينَ وَيَفعَلُ ٱللَّهُ مَا يَشَاءُ٢٧﴾

Kuma daga cikinsu akwai wadanda aka wakilta domin mutanen aljannah “Suna shiga garesu ta kowacce kofa, suna cewa aminci ya tabbata a gareku akan abinda kuka yi hakuri, madalla da kyakyyawar makoma". [Ra'ad: 23-24].

﴿جَنَّتُ عَدن يَدخُلُونَهَا وَمَن صَلَحَ مِن ءَابَائِهِم وَأَزوَجِهِم وَذُرِّيَّتِهِم وَٱلمَلَئِكَةُ يَدخُلُونَ عَلَيهِم مِّن كُلِّ بَاب٢٣ سَلَمٌ عَلَيكُم بِمَا صَبَرتُم فَنِعمَ عُقبَى ٱلدَّارِ٢٤﴾

Hakika Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya bada labarin cewa lalle: “Dakin da ake rayar da shi (Albaitul Ma'amur) da sama ana shigarshi". A wata riwayar kuma “Ana sallah a cikinsa kowace rana Mala'iku dubu saba'in sannan ba za su sake komawaba har abada". [Bukhari da Muslim].

FASALI

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle Allah ya saukar da littattafai domin su zama hujja ga halittu, kuma dalil ga aiki da su, kuma masu karantar da su da hijkima da kuma tsarkakesu.

Kuma muna bada gaskiya da cewa Allah ya saukarwa da kowanne Manzo da littafi domin fadinsa Allah madaukakin sarki:

﴿لَقَد أَرسَلنَا رُسُلَنَا بِٱلبَيِّنَتِ وَأَنزَلنَا مَعَهُمُ ٱلكِتَبَ وَٱلمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلقِسطِ ٢٥﴾

Ma'ana: “Hakika mun aiko Manzannimmu da hujjoji kuma muka saura musu da littafi da abin awo domin ya tsayar da mutane da adalci". [Hadid: 25].

Kuma mu sani daga cikin wadan nan littattafai akwai:

1. Attaurah: wacce Allah madaukakin sarki ya saukar da ita ga Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gareshi, kuma ita ce mafi girman littattafan 'ya'yan Isra'ila (banu Isra'ila) “A cikin ta akwai haske da shiriya, Annabawa suna hukunci da ita wadanda sun sallama ga yahudawa masu binta (masu tsoron Allah) da malamansu game da abinda (aka ce) Ku kiyaye daga cikin littafin Allah, kuma sun kasance masu shaida akan haka".

﴿ فِيهَا هُدى وَنُور يَحكُمُ بِهَا ٱلنَّبِيُّونَ ٱلَّذِينَ أَسلَمُواْ لِلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلرَّبَّنِيُّونَ وَٱلأَحبَارُ بِمَا ٱستُحفِظُواْ مِن كِتَبِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ عَلَيهِ شُهَدَاءَ ٤٤﴾

2. Al'injil: Wacce Allah madaukakin ya saukar da ita ga Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi, wacce ke gasganta Attaurah kuma wacce take cikata “Kuma mun ba shi Injila a cikinta akwai shiriya da haske, kuma mai gasganta wace ga abinda yake gaba gareta (wato abinda ya zo kafin ita, Attaurah kenan) daga Attaurah da kuma shiriya da wa'azi ga masu tsoron Allah". [Ma'ida: 46].

﴿ وَءَاتَينَهُ ٱلإِنجِيلَ فِيهِ هُدى وَنُور وَمُصَدِّقا لِّمَا بَينَ يَدَيهِ مِنَ ٱلتَّورَىةِ وَهُدى وَمَوعِظَة لِّلمُتَّقِينَ٤٦﴾

“Kuma domin in halatta muku wani sashi na abinda aka haramta muku". [Ali-Imran: 50].

﴿ وَلِأُحِلَّ لَكُم بَعضَ ٱلَّذِي حُرِّمَ عَلَيكُم ٥٠﴾

3. Zaburah: Wacce Allah ya baiwa Annabi Dawud tsira da amincin Allah bsu tabbata a garshi.

4. Sulufi: Ibrahim da Musa amincin Allah ya tabbata garesu.

5. Alkur'ani: Mai girma wanda Allah ya saukar ga Annabin Sa Muhammad ﷺ‬ cikamakin Annabawa “Shiriya ga mutane kuma mai hujjoji na shiriya da kuma rarrabewa". [Bakara: 185].

﴿ هُدى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَت مِّنَ ٱلهُدَى وَٱلفُرقَانِ ١٨٥﴾

Sai ya kasance: “Mai gasgantawane ga abinda yake gabaninshi (wato littafan da suka zo kafin shi) na daga littafi, kuma wanda ya shafe su". [Ma'idah: 48].

﴿ مُصَدِّقا لِّمَا بَينَ يَدَيهِ مِنَ ٱلكِتَبِ وَمُهَيمِنًا عَلَيهِ ٤٨﴾

Sai Allah madaukakin sarki ya shafe dukkan littattafan da suka gabace shi da shi, kuma ya dauki nauyin kiyaye shi daga masu wasa da canza ayoyin sa. “Mu muka saukar da Zikiri {Alkur'ani} kuma mune masu kiyaye shi". [Hijr: 9].

﴿إِنَّا نَحنُ نَزَّلنَا ٱلذِّكرَ وَإِنَّا لَهُ لَحَفِظُونَ٩﴾

Domin lalle zai kasance hujja ga mutane baki daya har zuwa ranar tashin alkiyama.

Amma littattafan da suka gabace shi hakika su an yi masu lokaci da iyaka, suna karewa ne da saukar wanda zai shafe su da kuma bayyana abinda ya faru a cikin su na karkatarwa da kuma canzawa (da gurbatattun malamai suka yi) saboda haka su wadannan littattafan ba su kasance wadanda Allah ya yi alkawarin kiyayesu ba, haki canje-canje da kari da kuma ragi duk sun auku a cikinsu. “Daga cikin yahudawa akwai masu karkatar da kalmomi daga wurin da suke". [Nisa'i: 46].

﴿مِّنَ ٱلَّذِينَ هَادُواْ يُحَرِّفُونَ ٱلكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِ ٤٦﴾

“Bone (azaba) ya tabbata ga wadanda suke rubuta littafi da hannuwansu sannan su ce; ai wannan daga wurin Allah ne domin su sayar da shi da kudi kadan, bone ya tabbata garesu na daga abinda hannuwansu suka rubuta kuma bone (azaba) ta tabbata a garesu na daga abinda suka aikata". [Bakarah: 79].

﴿فَوَيل لِّلَّذِينَ يَكتُبُونَ ٱلكِتَبَ بِأَيدِيهِم ثُمَّ يَقُولُونَ هَذَا مِن عِندِ ٱللَّهِ لِيَشتَرُواْ بِهِ ثَمَنا قَلِيلا فَوَيل لَّهُم مِّمَّا كَتَبَت أَيدِيهِم وَوَيل لَّهُم مِّمَّا يَكسِبُونَ٧٩﴾

“Ka ce; wa ya saukar da littafin da (Annabi) Musa ya zo da shi (ya zama) haske da shiriya ga mutane, kuna sanya shi a takardu kuma kuna bayyanasu kuna kuma boye masu yawa."[An'am: 9].

﴿ قُل مَن أَنزَلَ ٱلكِتَبَ ٱلَّذِي جَاءَ بِهِ مُوسَى نُورا وَهُدى لِّلنَّاسِ تَجعَلُونَهُ قَرَاطِيسَ تُبدُونَهَا وَتُخفُونَ كَثِيرا وَعُلِّمتُم مَّا لَم تَعلَمُواْ أَنتُم وَلَا ءَابَاؤُكُم قُلِ ٱللَّهُ ثُمَّ ذَرهُم فِي خَوضِهِم يَلعَبُونَ٩١﴾

“Kuma daga cikinsu akwai wasu bangare suna sanya harsunan su a cikin littafi domin ku yi zaton yana daga cikin littafin alhali kuwa shi ba daga littafin ba ne, kuma suna cewa daga wurin Allah ne kuma shi ba da daga wurin Allah ba ne, kuma suna yi wa Allah karya alhalin suna sane. Baya kasancewa ga mutum dan Allah ya ba shi littafi da hikima da annabta sa'an nan ya ce: ku kasance bayina koma bayan Allah". [Ali-Imran: 78-79].

﴿وَإِنَّ مِنهُم لَفَرِيقا يَلوُنَ أَلسِنَتَهُم بِٱلكِتَبِ لِتَحسَبُوهُ مِنَ ٱلكِتَبِ وَمَا هُوَ مِنَ ٱلكِتَبِ وَيَقُولُونَ هُوَ مِن عِندِ ٱللَّهِ وَمَا هُوَ مِن عِندِ ٱللَّهِ وَيَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلكَذِبَ وَهُم يَعلَمُونَ٧٨ مَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُؤتِيَهُ ٱللَّهُ ٱلكِتَبَ وَٱلحُكمَ وَٱلنُّبُوَّةَ ثُمَّ يَقُولَ لِلنَّاسِ كُونُواْ عِبَادا لِّي مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَكِن كُونُواْ رَبَّنِيِّنَ بِمَا كُنتُم تُعَلِّمُونَ ٱلكِتَبَ وَبِمَا كُنتُم تَدرُسُونَ٧٩﴾

“Ya ku ma'abota littafi, hakika manzammu ya zo muku yana bayyana muka dayawa daga cikin abinda kuke boyewa daga cikin littafi". zuwa fadin Allah “Hakika wadanda suka ce; Lalle Allah to shine kawai Almasihu dan Maryam ne sun kafirta…………". [Ma'idah: 15-17].

﴿يَأَهلَ ٱلكِتَبِ قَد جَاءَكُم رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُم كَثِيرا مِّمَّا كُنتُم تُخفُونَ مِنَ ٱلكِتَبِ ١٥﴾ har zuwa: ﴿لَّقَد كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُواْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلمَسِيحُ ٱبنُ مَريَمَ ١٧﴾

**** **** ****

FASALI:

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle Allah ta'ala ya aika Manzanni zuwa ga mutane, “Masu bushara da tsoratarwa domin kada mutane su kafa hujja da Allah bayan manzanni (sun zo musu) kuma Allah ya kasance mabuwayi ne kuma mai hikima". [Nisa'i: 165].

﴿رُّسُلا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى ٱللَّهِ حُجَّةُ بَعدَ ٱلرُّسُلِ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيما١٦٥﴾

Kuma muna bada gaskiya da cewa na farkon su shi ne (Annabi) Nuhu u kuma na karshen su shi ne (Annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a garesu baki daya, “Hakika munyi wahayi zuwa gareka kamar yadda muka yi wahayi zuwa ga Nuhu da Annabawan da suka zo bayan shi".[Nisa'i: 163].

﴿إِنَّا أَوحَينَا إِلَيكَ كَمَا أَوحَينَا إِلَى نُوح وَٱلنَّبِيِّنَ مِن بَعدِهِ ١٦٣﴾

“Annabi Muhammad bai kasance daya daga cikin Ubannin manzan ku ba, sai dai Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa [Ahzab: 40].

﴿مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَا أَحَد مِّن رِّجَالِكُم وَلَكِن رَّسُولَ ٱللَّهِ وَخَاتَمَ ٱلنَّبِيِّنَ وَكَانَ ٱللَّهُ بِكُلِّ شَيءٍ عَلِيما٤٠﴾

Kuma mafifita daga cikin su su ne (Annabi) Muhammad sa'an nan (Annabi) Ibrahim sa'annan (Annabi) Musa sa'annan (Annabi) Nuhu sa'annan (Annabi) Isah dan Nana Maryam, kuma wadanda Allah ya kebe su a cikin fadin sa madaukakin sarki:

﴿وَإِذ أَخَذنَا مِنَ ٱلنَّبِيِّنَ مِيثَقَهُم وَمِنكَ وَمِن نُّوح وَإِبرَهِيمَ وَمُوسَى وَعِيسَى ٱبنِ مَريَمَ وَأَخَذنَا مِنهُم مِّيثَقًا غَلِيظا٧﴾

Ma'ana: “Kuma ku tuna lokacin da muka riki alkawari daga Annabawa da kuma Kai (Annabi Muhammad) da Nuhu da Ibrahim da Musa da Isah dan Maryam kuma munn riki alkawari mai girma". [Ahzab: 7].

Kuma muna kudurcewa azuciyarmu da cewa lalle shari'ar Annabi Muhammad ﷺ‬ ta shafe sauran shari'o'in wadancan Annabawa wadanda Allah ya kebe su da fadin sa madaukakin sarki:

﴿شَرَعَ لَكُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا وَصَّى بِهِ نُوحا وَٱلَّذِي أَوحَينَا إِلَيكَ وَمَا وَصَّينَا بِهِ إِبرَهِيمَ وَمُوسَى وَعِيسَى أَن أَقِيمُواْ ٱلدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُواْ فِيهِ كَبُرَ عَلَى ٱلمُشرِكِينَ مَا تَدعُوهُم إِلَيهِ ٱللَّهُ يَجتَبِي إِلَيهِ مَن يَشَاءُ وَيَهدِي إِلَيهِ مَن يُنِيبُ١٣﴾

Ma'ana: “Allah ya shar'anta muku addini na daga dukkan abinda aka yi wasiyar shi ga Annabi Nuhu da kuma wanda muka yi wahayinsa zuwa gareka da kuma Musa da Isah, akan cewa su tsayar da addinin (Allah) kuma karku rarraba a cikinsa". [Shura: 13].

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle dukkan manzanni mutane ne wadanda aka halitta, ba su da wani abinda suka kebanta da shi wanda suka mallaka, Allah ta'ala ya ce game da (Annabi) Nuhu kuma shi ne na farkon su:

﴿وَلَا أَقُولُ لَكُم عِندِي خَزَائِنُ ٱللَّهِ وَلَا أَعلَمُ ٱلغَيبَ وَلَا أَقُولُ إِنِّي مَلَك ٣١

Ma'ana: “Kuma bance muku ina da taskar Allah ba, kuma ban san gaibu ba, kuma ba na cewa ni Mala'ikane". [Hud: 31]. Kuma Allah ya umurci Annabi Muhammad ﷺ‬ kuma shi ne karshen su da ya fada musu cewa:

﴿وَلَا أَقُولُ لَكُم عِندِي خَزَائِنُ ٱللَّهِ وَلَا أَعلَمُ ٱلغَيبَ وَلَا أَقُولُ إِنِّي مَلَك ٣١

Ma'ana: “Kuma bance muku ina da taskar Allah ba, kuma ban san gaibu ba, kuma ba na cewa ni Mala'ikane". [Hud: 31].

kuma ya kara cewa da su:

﴿قُل لَّا أَملِكُ لِنَفسِي نَفعا وَلَا ضَرًّا إِلَّا مَا شَاءَ ٱللَّهُ ١٨٨﴾

Ma'ana:“Bana iya mallaka wa kaina wata anfanarwa ko cuta, sai dai abinda Allah yaso". [A'araf: 188]. kuma ya kara da cewa:

﴿قُل إِنِّي لَا أَملِكُ لَكُم ضَرّا وَلَا رَشَدا٢١ قُل إِنِّي لَن يُجِيرَنِي مِنَ ٱللَّهِ أَحَد وَلَن أَجِدَ مِن دُونِهِ مُلتَحَدًا٢٢﴾

Ma'ana: “Ban iya mallaka muku wata cutarwa kuma bana (iya mallaka muku) shiryarwa. Ka ce; Lalle ne Ni babu wanda zai iya tseratar dani daga (azabar) Allah kuma ban da wani wanda zan nemi mafaka a wurinsa bayan Sa (Shi Allah)". [Jinni: 21-22].

Kuma muna bada gaskiya da cewa (Su Annabawa) bayi ne daga cikin bayin Allah, Allah ta'ala ne ya daukaka su da manzanci, ya kuma siffanta su da cewa su (bayinsane na hakika) masu yawan bauta. Kuma da haka ya yabe su a cikin Alkur'ani mai girma, sai Allah madaukakin saki ya ce game da farkonsu:

﴿ذُرِّيَّةَ مَن حَمَلنَا مَعَ نُوحٍ إِنَّهُ كَانَ عَبدا شَكُورا٣﴾

Ma'ana:“Zuriya ce wacce muka dakko tare da (Annabi) Nuhu, lalle Shi (Annabi Nuhu) ya kasance bawa ne mai yawan godiya". [Isra'i: 3]. Haka kuma ya kara cewa game da (Annabin) da yake shi ne na karshen su wato (Annabi) Muhammad ﷺ‬:

﴿تَبَارَكَ ٱلَّذِي نَزَّلَ ٱلفُرقَانَ عَلَى عَبدِهِ لِيَكُونَ لِلعَلَمِينَ نَذِيرًا١﴾

Ma'ana:“Albarka ta tabbata ga wannan da ya saukar da Alfurkan (Alkur'ani) ga bawan sa domin ya zama wa'azi ga talikai". [Furkan: 1]

Kuma ya kara da fadi game da wasu manzannin:

﴿وَٱذكُر عِبَدَنَا إِبرَهِيمَ وَإِسحَقَ وَيَعقُوبَ أُوْلِي ٱلأَيدِي وَٱلأَبصَرِ٤٥﴾

Ma'ana: “Kuma ka ambata (wa mutanen ka) bayin mu Ibrahim da Is'hak da Yakub ma'abota karfi da gani (na zuci)". [Saad: 54].

﴿ٱصبِر عَلَى مَا يَقُولُونَ وَٱذكُر عَبدَنَا دَاوُدَ ذَا ٱلأَيدِ إِنَّهُ أَوَّابٌ١٧﴾

Ma'ana: “Kuma ka ambata wa mutanenka bawan mu (Annabi) Dawud ma'abocin karfi lalle shi mai yawan komawane ga Allah". (Saad: 17).

﴿وَوَهَبنَا لِدَاوُدَ سُلَيمَنَ نِعمَ ٱلعَبدُ إِنَّهُ أَوَّابٌ٣٠﴾

Ma'ana:“Kuma mun yi wa (Annabi) Dawud baiwar (Annabi) Sulaiman, madalla da wadan nan bawa, lalle Shi mai komawane ga Allah". [Saad: 30].

Haka kuma ya fada ga (Annabi) Isah u dan Nana Maryam:

﴿إِن هُوَ إِلَّا عَبدٌ أَنعَمنَا عَلَيهِ وَجَعَلنَهُ مَثَلا لِّبَنِي إِسرَءِيلَ٥٩﴾

Ma'ana: “Shi ba kowa bane sai dai wani bawa ne wanda muka yi ni'ima a gareshi sai muka sanya Shi ya zama misali ga banu Isra'il". [Zukhruf: 59].

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle Allah ta'ala ya cika sakon sa da aiko Annabi Muhammad ﷺ‬, kuma ya aiko shi ne zuwa ga dukkanin mutane, domin fadinsa madaukakin sarki:

﴿قُل يَأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيكُم جَمِيعًا ٱلَّذِي لَهُ مُلكُ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ يُحيِ وَيُمِيتُ فََامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِيِّ ٱلأُمِّيِّ ٱلَّذِي يُؤمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَتِهِ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُم تَهتَدُونَ١٥٨﴾

Ma'ana: “Ka ce; ya ku mutane, lalle ni manzon Allah ne zuwa gareku baki daya wanda keda mallakar sammai da kassai, babu abun bautawa da cancanta sai Shi yana rayawa yana kuma kashewa, ku yi imani da Allah da kuma Manzonsa Annabi kuma Ummiyyi (wanda bai karantawa kuma bai rubutawa) kuma wanda yayi imani da Allah da kuma kalmominsa kuma ku bi shi domin ku samu shiriya". [A'araf: 158].

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle shari'ar Sa ( Shi Annabi Muhammadu ﷺ‬) ita ce addinin musulunci, wannan da Allah ya yarda da shi ga bayinsa kuma Allah ta'ala ba ya karbar wani addini bayan shi (musulunci) domin fadinsa madaukakin sarki:

﴿إِنَّ ٱلدِّينَ عِندَ ٱللَّهِ ٱلإِسلَمُ ١٩﴾

Ma'ana: “Lalle (zababben) addini a wurin Allah shi ne musulunci". [Ali-Imran: 19]. kuma da fadinsa:

﴿ ٱليَومَ أَكمَلتُ لَكُم دِينَكُم وَأَتمَمتُ عَلَيكُم نِعمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلإِسلَمَ دِينا ٣﴾

Ma'ana:“A yau na cika muku addininku kuma na cika muku ni'imata agareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addinin gaskiya". [Ma'idah: 3].

﴿وَمَن يَبتَغِ غَيرَ ٱلإِسلَمِ دِينا فَلَن يُقبَلَ مِنهُ وَهُوَ فِي ٱلأخِرَةِ مِنَ ٱلخَسِرِينَ٨٥﴾

Ma'ana: “Duk wanda ya riki wani addini bayan musulunci to ba za'a karba daga gare shi ba kuma shi a lahira yana cikin masu hasara". [Ali-Imran: 85].

Kuma muna ganin duk wanda yake riyawa cewa akwai wani addini tsayayye kuma karbabbe a wurin Allah bayan musulunci, kamar addinin yahudanci ko nasaranci ko waninsu to shi kafirine kuma za'a neme shi da ya tuba in ya tuba shikenan ida kuma bai tuba ba to za'a kashe shi domin ya kasance wanda ya karyata Alkur'ani.

Kuma muna ganin duk wanda ya kafircewa (ya ki yarda) game da Manzancin Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) wanda ya zo da shi ga mutane baki daya to hakika ya kafirce da dukkanin Manzanni hadda manzancin da yake riya cewar ya yi imani da shi, domin fadin Allah ta'ala:

﴿كَذَّبَت قَومُ نُوحٍ ٱلمُرسَلِينَ١٠٥﴾

“Mutanen Nuhu sun karyata dukkanin Manzanni". [Shu'ara'i: 105]. Sai Allah ya sanya su masu karyata dukkanin Manzanni tare da cewa manzannin basu riga Annabi Nuhu ba, kuma Allah ta'ala ya ce:

﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكفُرُونَ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِ وَيُرِيدُونَ أَن يُفَرِّقُواْ بَينَ ٱللَّهِ وَرُسُلِهِ وَيَقُولُونَ نُؤمِنُ بِبَعض وَنَكفُرُ بِبَعض وَيُرِيدُونَ أَن يَتَّخِذُواْ بَينَ ذَلِكَ سَبِيلًا١٥٠ أُوْلَئِكَ هُمُ ٱلكَفِرُونَ حَقّا وَأَعتَدنَا لِلكَفِرِينَ عَذَابا مُّهِينا١٥١﴾

“Lalle wadanda suke kafirce wa Allah (ta'ala) da Manzonsa kuma suke son su rarraba tsakanin Allah da Manzonsa, kuma suna cewa; mun yi imani da sashi kuma muna kafirce wa sashi kuma suna nufin su riki tsakanin haka a matsayin wata hanya, to wadan nan sune kafirrai na hakika, kuma mun tanadar wa kafirai azaba wulakantacciya". [Nisa'i: 150-151].

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle babu wani Annabi bayan (Annabi) Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) kuma wanda ya yi da'awar Annabta bayan shi ko ya gasganta wanda ya yi, da'awar to shi kafiri ne domin ya kasance mai karyata Alkur'ani da Sunnar Ma'aikin Allah ﷺ‬ da kuma ijma'i musulmi bakidaya.

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle Annabi yana da Khalifofi wadanda suka maye bayansa da ilimi da Da'awah da kuma shugabanci, kuma mafifici da cancantar Halifancin daga cikinsu shi ne Abubakar Siddik sannan kuma Umar dan Khattab sannan sai kuma Usman dan Affan sannan sai kuma Aliyu dan Abutalib Allah ya kara musa yarda gabadaya.

Kuma haka suka kasance cikin halifanci gwargwadon yadda suka kasance a falala a shar'ance, kuma Allah bai kasance – kada ka manta shi ke da cikakkiyar hikima- ba wanda zai zabar wa mutanen da suka fi kowa alheri shugaba ba alhali acikinsu akwai wanda ya fishi alheri da cancantar khalifancin ba.

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle wanda aka fifita daga cikin wadan nan yakan kebantu da wata daraja ta musamman da zai dara wanda ya fi shi a wannan darajar, saidai ba ya cancantar falala ta gabadaya da wannan, domin hakika abubuwan da suke jawo falala ga mutum suna da yawa kuma nau'uka daban-daban.

Kuma muna yin imani da cewa lalle wannan al'ummar ita ce mafi alheri da daraja a wurin Allah maukakin sarki, domin fadinsa madaukakin sarki;

﴿كُنتُم خَيرَ أُمَّةٍ أُخرِجَت لِلنَّاسِ تَأمُرُونَ بِٱلمَعرُوفِ وَتَنهَونَ عَنِ ٱلمُنكَرِ وَتُؤمِنُونَ بِٱللَّهِ وَلَو ءَامَنَ أَهلُ ٱلكِتَبِ لَكَانَ خَيرا لَّهُم مِّنهُمُ ٱلمُؤمِنُونَ وَأَكثَرُهُمُ ٱلفَسِقُونَ١١٠﴾

Ma'ana: “Kun kasance mafi alherin al'umma wadda aka fitar daga cikin mutane kuna yin umurni da kyawawan aiki kuma kuna hana munana kuma kuna imani da Allah". [Ali Imran: 110].

Kuma muna bada gaskiya da cewa lalle hakika fiyayyun wannan al'ummar sune Shabbai sannan Tabi'ai sannan masu bin Tabi'ai.

Kuma muna bada gasikiya da cewa; wata jama'a ba za ta gusheba a cikin wannan al'umma tana tsaye akan gaskiya, ba zai taba cutar da su ba duk wanda ya wulakantar da su ko ya saba musu har zuwa lokacin da al'amarin Allah mai girma da daukaka zai zo (alkiyama).

Kuma muna kudurtawa da cewa duk wani abun da faru na fitina tsakanin su (su Shabbai Allah ya kara masu yarda), hakika ya farune akan wani tawili da ijtihadi a cikinsa, duk wadanda su ka kasance daga cikinsu akan daidai to suna da lada biyu, kuma duk wadanda suka kasance akan kuskure to suna da lada daya, kuma su kowanne kuskure suka yi to Allah ya gafarta musu shi.

Kuma muna ganin cewa wajibi ne kowan nan mu ya kame bakinsa daga anbaton munanan ayyukan su, kuma ba za mu anbace su ba sai da abinda ya cancanta na yabo mai kyawu, kuma don mu tsarkake zukatammu daga reni da hasada ga kowane dayansu, domin fadin Allah ta'ala:

﴿ لَا يَستَوِي مِنكُم مَّن أَنفَقَ مِن قَبلِ ٱلفَتحِ وَقَتَلَ أُوْلَئِكَ أَعظَمُ دَرَجَة مِّنَ ٱلَّذِينَ أَنفَقُواْ مِن بَعدُ وَقَتَلُواْ وَكُلّا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلحُسنَى وَٱللَّهُ بِمَا تَعمَلُونَ خَبِير١٠﴾

Ma'ana: “Ba za su yi daidai ba daga cikinku wadanda ya ciyar kafin budin makka kuma ya yi yaki, wadancan suna da babbar daraja akan wadanda suka ciyar kuma suka yi yaki bayan budin makkah, kuma dukkan su Allah ya yi musu kyakkyawan alkawari (aljannah)". [Hadid: 10]. Kuma Allah ta'ala ya fada game mu:

﴿وَٱلَّذِينَ جَاءُو مِن بَعدِهِم يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱغفِر لَنَا وَلِإِخوَنِنَا ٱلَّذِينَ سَبَقُونَا بِٱلإِيمَنِ وَلَا تَجعَل فِي قُلُوبِنَا غِلّا لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوف رَّحِيمٌ١٠﴾

Ma'ana:“Kuma wadanda suka zo bayan su suna cewa (Ya) Ubangijinmu ka gafarta mana da yan'uwan mu da suka rigamu imani, kuma karka sanya damuwa a zukatan mu na wadanda suka yi Imani, (Ya) Ubangiji lalle kai mai tausayi ne mai jin kai". [Hashr: 20].

**** **** ****

FASALI

Kuma muna bada gaskiya da ranar karshe shi ne ranar alkiyama wanda babu wani yini bayan sa, lokacin da za'a tayar da mutane araye domin tabbata a cikin gidan ni'ima ko gidan azaba mai radadi.

Muna bada gaskiya da tashi bayan mutuwa, kuma shi ne lokacin Allah yake rayar da matattu a lokacin da Mala'ika Israfil zai yi busa ta biyu a cikinj kaho “Sai ya yi busa a cikin kaho saboda haka sai duk wanda ke cikin sammai da kassai yam utu sai dai wanda Allah ya so, sa'annan ayi busa ta biyu sai ka ga mutane tsaye suna kallo". [Zumar: 68].

﴿وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَصَعِقَ مَن فِي ٱلسَّمَوَتِ وَمَن فِي ٱلأَرضِ إِلَّا مَن شَاءَ ٱللَّهُ ثُمَّ نُفِخَ فِيهِ أُخرَى فَإِذَا هُم قِيَام يَنظُرُونَ٦٨﴾

Sai duk wanda ke cikin kabari su tsaya a gaban Ubangijin halittu maigirma da daukaka suna huntaye ba takalma, tsirara ba tufafi, da loba babu kaciya “Kamar yadda muka fara halittar su zamu maida su, alkawali ne akan mu lalle mu masu aikatawa ne". [Anbiya'i: 104].

﴿ كَمَا بَدَأنَا أَوَّلَ خَلق نُّعِيدُهُ وَعدًا عَلَينَا إِنَّا كُنَّا فَعِلِينَ١٠٤﴾

Kuma mun bada gaskiya da littafin da aka rubuta ayukka wanda za'a bayar da shi ta hannun dama ko ta baya a hagu “Duk wanda aka ba shi da hannun dama, da sannu zai samu saukakken hisabi, zai koma ga iyalansa yana mai jin dadi, kuma duk wanda aka ba shi littafinsa ta bayan shi, to da sannu zai ambaci mummunar azaba, kuma zai shiga wutar sa'ira (wacce ake rurutata).[Inshikak: 7-12].

﴿فَأَمَّا مَن أُوتِيَ كِتَبَهُ بِيَمِينِهِ٧ فَسَوفَ يُحَاسَبُ حِسَابا يَسِيرا٨ وَيَنقَلِبُ إِلَى أَهلِهِ مَسرُورا٩ وَأَمَّا مَن أُوتِيَ كِتَبَهُ وَرَاءَ ظَهرِهِ١٠ فَسَوفَ يَدعُواْ ثُبُورا١١ وَيَصلَى سَعِيرًا١٢﴾

(da kuma fadinsa mai girma da daukaka):

﴿وَكُلَّ إِنسَنٍ أَلزَمنَهُ طَئِرَهُ فِي عُنُقِهِ وَنُخرِجُ لَهُ يَومَ ٱلقِيَمَةِ كِتَبا يَلقَىهُ مَنشُورًا١٣ ٱقرَأ كِتَبَكَ كَفَى بِنَفسِكَ ٱليَومَ عَلَيكَ حَسِيبا١٤﴾

Ma'ana: “Kuma kowanne mutum mun rataya masa littafinsa a wuyansa, sai mu fitar da su a ranar kiyama muna masu raba masu, ka karanta littafinka ka isa ka yi wa kanka hisabi (dakanka)". [Isra'il: 13-14].

Kuma muna bada gaskiya da cewa akwai ma'auni wanda za'a yi awo da shi (aranar alkiyama) kuma baza'a zalunci kowanne mutum ba “To duk wanda ya aikata aiki misalin zarra na alheri zai gan shii, kuma duk wanda ya aikata sharri misalin zarra zai gan shi". [Zilzal: 7-8].

﴿فَمَن يَعمَل مِثقَالَ ذَرَّةٍ خَيرا يَرَهُ٧ وَمَن يَعمَل مِثقَالَ ذَرَّة شَرّا يَرَهُ٨﴾

Da kuma fainsa:

﴿فَمَن ثَقُلَت مَوَزِينُهُ فَأُوْلَئِكَ هُمُ ٱلمُفلِحُونَ١٠٢ وَمَن خَفَّت مَوَزِينُهُ فَأُوْلَئِكَ ٱلَّذِينَ خَسِرُواْ أَنفُسَهُم فِي جَهَنَّمَ خَلِدُونَ١٠٣ تَلفَحُ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ وَهُم فِيهَا كَلِحُونَ١٠٤﴾

Ma'ana: “To duk wanda ma'auninsa ya yi nauyi to yana daga cikin wadanda suke sun rabauta. Kuma duk wanda ma'auninsa ya saukaka (ba shi da nauyi) to yana daga cikin wadanda suka yi a sarar kawunan su a cikin (wutar) jahannama suna masu dauwama. Wuta tana kwaye fuskokinsu kuma su a cikinta kwarangwal suke". [Muminun: 102-103].

Da kuma fadinsa:

﴿مَن جَاءَ بِٱلحَسَنَةِ فَلَهُ عَشرُ أَمثَالِهَا وَمَن جَاءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجزَى إِلَّا مِثلَهَا وَهُم لَا يُظلَمُونَ١٦٠﴾

Ma'ana: “Kuma duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki (guda) daya to yana da kwantankwacinta goma, kuma duk wanda ya zo da mummuna (guda) daya babu to ba za'a sakanka masa ba sai da irin abinda ya aikata, kuma su (bayi) ba za'a taba zaluntar su ba". [An'am: 160].

Kuma muna bada gaskiya da cewa akwai ceto babba mai girman gaske wanda Manzon Allah ﷺ‬, zai nema daga wurin Allah ta'ala da izinin Sa domin ya yi hukunci a tsakanin bayin sa, hakanko zai farune a lokacin da suke cikin damuwa da bakin ciki da basu iya jurewa akan su, sai su je wurin (Annabi) Adam sa'annan su je wurin (Annabi) Nuhu sa'anna (Annabi) Ibrahim sa'annan (Annabi) Musa sa'annan (Annabi) Isah har daga karshe suje wurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Kuma muna bada gaskiya da ceton wanda ya shiga wuta daga cikin muminai cewa za'a fito da shi, kuma shi ma wannan ya shafi Annabi da kuma wasu daga cikin Annabawa da muminnai da kuma mala'iku. Tare da cewa Allah ta'ala zai fitar da wasu mutane muminnai daga wuta da rahmar sa.

Kuma muna bada gaskiya game da tabkin Manzon Allahr, ruwansa ya fi madara (nono) fari, kuma ya fi zuma zaki yana da kamshi fiye da almiski, tsawonsa tafiyar wata gudace fadinsa ma tafiyar wata gudace, kofunansa kamar taurarin sama suke wajan kyawon (haske) da kuma yawa, muminai daga cikin al'ummar sa za gangara tafkin duk wanda ya sha bai zai sake jin kishi ba har abada.

Kuma muna bada gaskiya da Siradi wanda aka shimfida shi akan jahannama, mutane zasu dinga wucewa ta kanshi akan gwargwadon ayukkansu, na farkonsu zai wuce kamar walkiya, sa'annan wani kamar iska, sa'annan wani kamar tashin tsuntsu, wasu kuma da kafafunsu za su wuce, kuma Annabi ﷺ‬ yana nan tsaye yana rokon Allah: (Ya) Ubangiji ka tseratar". Har dai ayyukkan bayi su kasa, sai a samu wanda yake jan-gindi, kuma a bakin gabar sirati akwai kungiyoyi masu wulgowa, za su kuma kama duk wanda aka yi musu umarni da su da su kama, kuma su bar wanda zai tsira kuma su wulga wanda zai shiga wuta.

Kuma muna bada gaskiya da duk abinda ya zo a cikin littafin Allah mai girma da daukaka da Sunnar Manzonsa rna daga labarai na abinda ya shafi yinin karshe da wahalhalun dake ciki, Allah ya taimake mu akan su ya kuma sawwake mana domin ni'imarsa da darajar sa.

Kuma muna bada gaskiya da ceton Annabi ﷺ‬ ga 'yan aljanna da su shigeta, wannan kadai ga Annabi ﷺ‬ ne.

Kuma muna bada gaskiya da kusancin aljannah da wuta, aljannah gidan ni'ima ce Allah ta'ala ya tanadar da ita ga muminai masu kiyayewa dokokin Allah, a cikin ta akwai ni'ima na irin abinda ido bai taba gani ba, kunne kuma bai taba ji ba, haka zuciya bata taba nasawa ba, rai bai san abinda Allah ya tanadar masa ba na abinda ke faranta rai. Wuta kuma gidan azaba wacce Allah ya tanadata ga kafirai azzalumai akwai azaba da wulakanci acikinta na abinda zuciya bata iya kwatantawaba. “Lalle mu mun yi tanadin wata wuta ga azzalumai wadda shamakunta sun kewayesu, kuma idan suka nemi agaji za'a agaza musu da wani ruwa (maizafi) kamar dabzar mai, yana soye fuskokinsu, tir da abin shan su, kuma wutar ta yi munin zama mahutarsu". [Kahf: 29].

﴿ إِنَّا أَعتَدنَا لِلظَّلِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِم سُرَادِقُهَا وَإِن يَستَغِيثُواْ يُغَاثُواْ بِمَاء كَٱلمُهلِ يَشوِي ٱلوُجُوهَ بِئسَ ٱلشَّرَابُ وَسَاءَت مُرتَفَقًا٢٩﴾

Kuma suna nan ahaka yanzu ba su karewa har abada “duk wanda yayi imani da Allah kuma ya yi aiki na kwarai za'a shigar da shi aljannah wace koramu ke gudana a karkashin ta, hakika Allah ya kyautata masa zai arzikinsa". [Talak: 11].

﴿رَّسُولا يَتلُواْ عَلَيكُم ءَايَتِ ٱللَّهِ مُبَيِّنَت لِّيُخرِجَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّلِحَتِ مِنَ ٱلظُّلُمَتِ إِلَى ٱلنُّورِ وَمَن يُؤمِن بِٱللَّهِ وَيَعمَل صَلِحا يُدخِلهُ جَنَّت تَجرِي مِن تَحتِهَا ٱلأَنهَرُ خَلِدِينَ فِيهَا أَبَدا قَد أَحسَنَ ٱللَّهُ لَهُ رِزقًا١١﴾

“Allah ya tsine wa kafirai kuma ya tanadar masu wutar sa'ira. Suna masu dawwama acikinta har abada, ba su da majibinta ko mataimaka. A ranar da za'a juya fuskokinsu a cikin wuta za su ta fadin cewa kaicon mu inama ace mun bi Allah kuma mun bi Manzo (nsa)". [Ahzab: 64-66].

﴿إِنَّ ٱللَّهَ لَعَنَ ٱلكَفِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُم سَعِيرًا٦٤ خَلِدِينَ فِيهَا أَبَدا لَّا يَجِدُونَ وَلِيّا وَلَا نَصِيرا٦٥ يَومَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُم فِي ٱلنَّارِ يَقُولُونَ يَلَيتَنَا أَطَعنَا ٱللَّهَ وَأَطَعنَا ٱلرَّسُولَا٦٦﴾

Kuma muna tabbatar da aljannah ga duk wanda littafin Allah (Alkur'ani) ya tabbatar masa ko Sunnar Manzo ﷺ‬ da sunansa ko a siffance.

Daga cikin wadanda aka tabbatar da sunayansu akwai Abubakar Siddik da Umar da Usman da Aliyu da makamantansu wadanda Manzon Allah ﷺ‬ ya tabbatar.

Daga cikin wadanda aka siffanta da tabbatar musu akwai muminai da masu tsoron Allah.

Kuma muna tabbatar da wuta ga duk wanda littafin Allah (Alkur'ani) ko Manzo ﷺ‬ ya tabbatar da sunansa ko a siffance.

Daga cikin wadanda aka tabbatar da sunayansu a wuta akwai Abi lahab da Amru dan Luhai mutumin Khuza'a da makamantan su.

Daga cikin wadanda aka tabbatar da cewar su 'yan wutane ta hanyar siffantawa akwai dukkan kafirai ko mushirikai masu babbar shirka ko munafirci.

Kuma muna bada gaskiiya da fitinar kabari, ita ce kuwa tambayoyi game da Ubangiji da Addini da Annabi ﷺ‬ a cikin kabari, “Sai Allah ya tabbatar da wanda suka yi imani da fadin zance tabbatance acikin rayuwar duniya da lahira". [Ibrahim: 27].

﴿يُثَبِّتُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱلقَولِ ٱلثَّابِتِ فِي ٱلحَيَوةِ ٱلدُّنيَا وَفِي ٱلأخِرَةِ ٢٧﴾

Lokacin amsa tambaya sai mumini ya ce Ubangiji na shine Allah, kuma addini na shi ne musulunci, kuma Annabi na shi ne Muhammadr. Amma kafiri da munafiki sai suce ban saniba na ji mutane suna fadin haka sai na fada.

Kuma muna bada gaskiya da cewa akwai jindadi a kabari ga muminai “Wadanda Mala'iku suka karbi rayukan su suna masu tsarki na imani, suna ce dasu aminci ya tabbata a gare ku, ku shiga aljannah saboda abinda kuka aikata". [Nahl: 32].

﴿ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىهُمُ ٱلمَلَئِكَةُ طَيِّبِينَ يَقُولُونَ سَلَمٌ عَلَيكُمُ ٱدخُلُواْ ٱلجَنَّةَ بِمَا كُنتُم تَعمَلُونَ٣٢﴾

Kuma muna bada gaskiya da cewa akwai azabar kabari ga azzalumai kafirai “Da zaka lokacin da azzalumai suke cikin magagin mutuwa kuma Mala'iku sun shinfida hannuwansu suna cewa ku fito da kanku, a yau za'a sakanka muku da mummunar azaba akan abinda kuka kasance kuna fadi ga Allah na karya kuma kuka kasance masu girman kai ga ayoyin Sa". [An'am: 93].

﴿وَمَن أَظلَمُ مِمَّنِ ٱفتَرَى عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَو قَالَ أُوحِيَ إِلَيَّ وَلَم يُوحَ إِلَيهِ شَيء وَمَن قَالَ سَأُنزِلُ مِثلَ مَا أَنزَلَ ٱللَّهُ وَلَو تَرَى إِذِ ٱلظَّلِمُونَ فِي غَمَرَتِ ٱلمَوتِ وَٱلمَلَئِكَةُ بَاسِطُواْ أَيدِيهِم أَخرِجُواْ أَنفُسَكُمُ ٱليَومَ تُجزَونَ عَذَابَ ٱلهُونِ بِمَا كُنتُم تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ غَيرَ ٱلحَقِّ وَكُنتُم عَن ءَايَتِهِ تَستَكبِرُونَ٩٣﴾

Kuma hadissai sanannu da suka tabbatar da haka suna da yawa, saboda haka ya zama wajibi ga mumini ya yi imani da duk abinda ya zo daga cikin Alkur'ani mai girma da Hadissai game da lamarin da ya shafi gaibi kuma kada yace sun ci karo da abinda ya gani a duniya, domin babban banbancin dake tsakaninsu. Allah ya taimakemu.

***** **** ****

FASALI

Kuma muna bada gaskiya da kaddara ta alheri ko ta sharri ita ce kuwa kaddarawar da Allah ya yi ga dukkan abubuwa da za su kasance a daidai yadda ilimin Allah ya rigaye kuma hikimarsa ta tabbatar.

Imani da kaddara yana da matakai guda hudu:

1. MatakiNa Farko: Ilimi, muna bada gaskiya da cewa Allah ta'ala yana da cikakken sani akan komai na abinda ya kasance, da ya yake kasancewa, da kuma yadda zai kasance kuma sanin Sa tabbatacce ne har abada, baya canza iliminsa akansa domin jahiltarsa ko mantuwa ba sa riskarsa bayan ilimi.

2. Mataki Na Biyu: Rubutu, mun yi imani da cewa Allah ya rubuta duk abinda zai kasance har zuwa tashin kiyama a cikin lauhul mahfuz “Shin baka sani ba cewa Allah yana sane da duk abinda ke sammai da kasa, lalle wannan yana cikin littafi, kuma haka ga Allah abu ne mai sauki". [Hajj: 70].

﴿أَلَم تَعلَم أَنَّ ٱللَّهَ يَعلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَاءِ وَٱلأَرضِ إِنَّ ذَلِكَ فِي كِتَبٍ إِنَّ ذَلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِير٧٠﴾

3. Mataki Na Uku: Mashi'ah (Ganin dama), muna bada gaskiya da cewa Allah ta'ala da ganin damar sa ne duk abinda ya kasance a sammai da kassai, duk wani abu ba ya kasancewa idan Allah bai ga damar kasancewar sa ba.

4. Mataki Na Hudu: Halitta, muna bada gaskiya da cewa Allah ta'ala shi ne “Ya halicci dukkan komai, kuma shi akan dukkan komai mai kula ne, makulan sammai da kassai su na hannunsa".[Zumar: 62-63].

﴿ٱللَّهُ خَلِقُ كُلِّ شَيء وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيء وَكِيل٦٢ لَّهُ مَقَالِيدُ ٱلسَّمَوَتِ وَٱلأَرضِ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بَِايَتِ ٱللَّهِ أُوْلَئِكَ هُمُ ٱلخَسِرُونَ٦٣﴾

Wadannan matakan guda hudu sun tattara duk abun da zai kasance tun daga wurin Allah kansa har zuwa ga bayinsa, duk abinda bawa zai fada na zance ko ayyuka ko burin su to abune sananne a wurin Allah kuma rubutacce a wurinsa. Allah ta'ala shi ne ya so da haka kuma ya halitta shi. “Duk wanda ya so daga cikin ku ya tsayu, babu wanda zai so wani abu face idan Allah ya so (shi) da faruwa sa'annan ya faru". [Takwir: 28-29].

﴿لِمَن شَاءَ مِنكُم أَن يَستَقِيمَ٢٨ وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلعَلَمِينَ٢٩﴾

“Kuma da Ubangiji ya so da ba su yaki juna ba, amma Allah ke aikata abinda ya ga dama". [Bakara: 253].

﴿ وَلَو شَاءَ ٱللَّهُ مَا ٱقتَتَلُواْ وَلَكِنَّ ٱللَّهَ يَفعَلُ مَا يُرِيدُ٢٥٣﴾

“Da Allah ya ga dama da basu aikata ba, bar su da abinda suke kirkira". [An'am: 112].

﴿ وَلَو شَاءَ رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُ فَذَرهُم وَمَا يَفتَرُونَ١١٢﴾

Saidai mun yi imani tare haka Allah ta'ala ya baiwa bayi zabi da iko akan aikata ayyuka kuma dalilin akan haka shi ne:

1. Na daya fadin Allah ta'ala:

﴿ فَأتُواْ حَرثَكُم أَنَّى شِئتُمَ٢٢٣﴾

Ma'ana: “Ku zo ga iyalanku ta inda ku ka so". [Bakara: 223].

﴿وَلَو أَرَادُواْ ٱلخُرُوجَ لَأَعَدُّواْ لَهُ عُدَّة ٤٦﴾

Ma'ana:“Kuma da sun yi nufin fita yaki da sun yi masi tanadi matukar tanadi". [Tauba: 46]. Sai ya tabbatar wa bayinsa da zuwa (a yar Bakarah) mashi'ah (ganin dama) da kuma tattali da nufinsa.

2. Na biyu fuskantar da umarni da kuma hani zuwa ga bawa, da basu da zabi da iko da wannan ya kasance abun tilastawa ne naabinda ba zasu iya aikata shi ba, hakan kuma abune da hikimar Allah da rahamarsa bata yarda da shi ba, da kuma tabbataccan bayaninsa na gaskiya a fadinsa mai girma da daukka:

﴿لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفسًا إِلَّا وُسعَهَاَ٢٨٦﴾

Ma'ana: “Allah baya tilastawa rai abunda zata iya". [Bakara: 286].

3. Na uku; Yabo: ga wanda ya kyautata da kuma zargi ga wanda ya munana tare da tabbatar da sakamakon abinda kowannen ya cancanta, da badun aiki ya kasance da zabin bawa da kuma nufinsa ba da duk yabon masu kyautatawa ya zama wasa, kuma ukubar wanda ya munana ta zama zalinci kenan, kuma Allah tsarkakakke ne daga wasa da zalunci.

4. Na hudu lalle Allah ta'ala ya aiko manzanni “Masu bushara (da aljanna ga dukkan wadanda suka bi Allah da Manzanshi), kuma masu gargadi (da azaba ga dukkan wadanda suka sabawa Allah da Manzanshi), domin kada ya kasance mutane suna da wata hujja ga Allah bayan aiko Manzanni".

﴿رُّسُلا مُّبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى ٱللَّهِ حُجَّةُ ١٦٥﴾

[Nisa'i: 165]. da aikin bawa bai kasance da nufinsa da kuma ikon sa ba, da kafa hujja da manzanni ya zama wani abu mara tasiri.

5. Na biyar lalle dukkan kowane mai aiki yana sane da abunda yake aikatawa da wanda yake bari ba tare da an tilastawa mishi ba, kuma yana tashi yana kuma zama yana shiga sannan yana fita yana tafiya kuma yana barin tafiya gwargwadon nufinsa (yadda yake so), kuma ba tunani akwai wani da yake tilastashi akan haka, sai dai yana bambamce abun da yake aikatawa na zabinsa da kuma wanda aka tilastawa masa, game da abun da yake hakkin Allah.

Kuma muna fahimtar cewa babu hujja ga mai aikata laifi da ikon Allah, domin laifi ana gabatar da shi akan zabinsa, ba tare da ya san cewa Allah ta'ala ya kaddara ba sai bayan ya auku “Kuma rai ba ta san abun da zata aikata gobe ba". [Lukman: 34].

﴿ وَمَا تَدرِي نَفس مَّاذَا تَكسِبُ غَدا ٣٤﴾

To ta yaya hujja zata kasance ingantacciya bayan lokacin da wanda aka kafa wa hujja bai san hujjab alokacin da yake afkawa abinda yake bada hanzari akai, hakika Allah ta'ala ya bata hujjar da suka gabatar “Da sannu wadanda suka yi shirka za su ce da Allah ya so da ba mu yi shirka ba da mu da iyayen mu, kuma da bai haramta mana komai, da haka wadanda suka rigasu fadi suka dandani azaba, kace in kuna da wani ilimi ku fitar mana da shi, babu abun da ku ke bi sai zato kuma alhalin ku kuna kutse-kutse". [An'am: 148].

﴿سَيَقُولُ ٱلَّذِينَ أَشرَكُواْ لَو شَاءَ ٱللَّهُ مَا أَشرَكنَا وَلَا ءَابَاؤُنَا وَلَا حَرَّمنَا مِن شَيء كَذَلِكَ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبلِهِم حَتَّى ذَاقُواْ بَأسَنَا قُل هَل عِندَكُم مِّن عِلم فَتُخرِجُوهُ لَنَا إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِن أَنتُم إِلَّا تَخرُصُونَ١٤٨﴾

Kuma muna fada wa mai laifi da yake kafa hujja da kaddara: don me ba ka gabatar da biyayya ga Allah ba cewa shi ya kaddara akan haka, domin ba bu banbanci tsakanin laifi da biyayya tare da jahilci akan wanda aka kadarta masa kafin ya aikata aikin?, da kuma a lokacin da Annabi ﷺ‬ ya ba Sahabbai labarin cewa lalle an rubuta wa kowa mazauninsa a aljanna da wuta, sai su ka ce: Shin ba zamu dogara da hakan ba, kuma mu bar aiki?. Sai ya ce, A'a ku yi aiki domin kowa za'a saukakamasa abinda aka halicce shi dominsa.

Kuma muna fada wa mai kafa hujja da kaddara cewa: da zaka yi nufin tafiya zuwa Makkah sai aka ce tana da hanya biyu daya hanyar ba ta da aminci akwai tsoro da wahala, ta biyun kuwa tana da aminci da sauki, to hakika kai za ka bi dayar kuma ba zaka ce an kaddara ta akai na ba, da kuma za ka yi hakan to da mutane za su dauka cewa kai mahaukaci ne.

Kuma muna cewa: da za'a bijiro maka da wasu tsari guda biyu daya akwai martaba mai girma, lalle da sannu zaka dauke ta ka bar mai nakasun, to yaya zaka zabar wa kanka a aikin lahira ya zama kasakantatta, sa'anna ka kafa hujja da kaddara?.

Kuma muna cewa idan ka samu rashin lafiya a jiki aka nemi likita domin samun lafiya, kuma za ka yi hakuri da duk zafin ciwon tare da kana karbar magani, to me yasa ba zaka aikata haka ba wajan rashin lafiyar zuciyar ka da aikata laifi?.

Kuma muna bada gaskiya da cewa ba'a jingina sharri ga Allah ta'ala, domin cikar rahamarsa da hikimarsa. Annabi ﷺ‬ ya ce: “kuma sharri ba ya gare ka". [Muslim].

Sai ya kore sharri ga dukkan hukuncin Allah har abada, domin yin haka ya kauce wa rahamarsa da hikimarsa, saidai sharri yana kasancewa ga abinda ya zartar domin fadin Annabi ﷺ‬ a cikin addu'ar kunuti da ya koya wa Alhassan t“Allah ka tsare ni daga sharrin abinda ka zartar". tare da ya jingina sharri ga abun da ya zartar, shi sharri yana ga abinda ake zartarwa sai dai sharri ne a mahalin sa ta wata fuskar alheri kuma ta wata fuskar, ko sharri a mahallinsa kuma alheri ta wata fuskar daban.

Cikin kasa: yana tabbata ne daga rashin lafiya, talauci da tsoran sharri, sai dai ya kasance wanin su alheri ne a wani mahallin, Allah ta'ala ya ce “Barna ta bayyana a cikin kasa da kogi domin abin da hannayan mutane suka aikata don mu dandana musu azaba game da abinda suka aikata, tsammani zasu dawo (kan hanya)". [Rum: 41].

﴿ظَهَرَ ٱلفَسَادُ فِي ٱلبَرِّ وَٱلبَحرِ بِمَا كَسَبَت أَيدِي ٱلنَّاسِ لِيُذِيقَهُم بَعضَ ٱلَّذِي عَمِلُواْ لَعَلَّهُم يَرجِعُونَ٤١﴾

Yanke hannun barawo da jefe mazinaci suna ganin cewa sharri ne, amma alheri ne ta wata fuskar a gare su, fuskar da haka zai zama kaffara a garesu domin ba za su hada masu azabar duniya da ta lahira ba, kuma hakan alhere ne.

A wannan mahalli tare da cewa kiyayewa ne ga dukiya da mutuncin su da kuma dangin su.

FASALI

Wannan akida mai daraja wacce ta kunshi wanan tushe mai girma, yana kuma fa'idantar da dukkan wanda ya kudurcesu fa'idoji masu tarin yawa kuma masu daraja.

To shi Imani da Allah da kuma sunayansa kyawawa da siffofinsa madaukaka, zai amfanar da bawa son Allah da kuma girmama shi wadanda za su say a tsayu wurin bin umarnin Allah da kuma hanuwa ga abinda ya hana, yin abinda Allah madaukakin sarki ya yi umarni da kuma nisantar abinda ya hana yana samarwa bawa samun cikakken kwanciyar hankali a duniya da lahira ga mutum shi kadai ko ga al'umma, “Duk wanda ya aikata (aiki) na kwarai na miji ko mace kuma alhali yana mumini to hakika za mu rayar da shi rayuwa daddada, kuma za mu sakanka musu da mafi kyawun abinda suka kasance suna aikatawa". (Nahl: 98).

﴿مَن عَمِلَ صَلِحا مِّن ذَكَرٍ أَو أُنثَى وَهُوَ مُؤمِن فَلَنُحيِيَنَّهُ حَيَوة طَيِّبَة وَلَنَجزِيَنَّهُم أَجرَهُم بِأَحسَنِ مَا كَانُواْ يَعمَلُونَ٩٧﴾

Kuma yana daga cikin fa'idojin Imani da mala'iku:

Na Farko: Sanin girman wanda ya halicce su mai girma da daukaka da kuma karfin ikonsa.

Na Biyu: Godewa Allah madaukakin sarki akan yadda yake kula da bayinsa, ta yadda ya wakilta musu daga wadannan mala'iku wadanda suke kiyayesu da kuma rubuta ayyukan su da wanin haka na abubuwan da suke alheri ne a gare su.

Na Uku: Son su mala'ikun akan abinda suka tsayu da shi na bautawa Allah madaukakin sarki ta fuska mafi cika da kuma yadda suke nemawa muminai gafarar Allah.

Yana kuma daga cikin fa'idojin Imani da littattafai:

Na Farko: Sanin rahamar Allah madaukakin sarki da kuma kuda da bayinsa, ta yadda ya saukarwa kowacce al'umma littafin da zai shiryar da su.

Na Biyu: Bayyanar hikimar Allah madaukakin sarki, ta yadda ya shar'anta a cikin wadannan littattafai kowacce al'umma abunda ya yi daidai da ita, kuma ya kasance cika makon wadannan littattafai shi ne Alkur'ani mai girma wanda ya yi daidai da dukkanin jama'a a kowanne zamani kuma a kowanne gari har zuwa ranar tashin alkiya.

Na Uku: Godewa ni'imar Allah akan haka.

**** **** ****

Yana daga cikin fa'idojin Imani da Manzanni:

Na Farko: Sanin rahamar Allah madaukakin sarki da kuma kulawarsa da bayi, ta yadda ya aiko musu da wadannan Manzanni masu karamci domin shiryarwa da kuma fadakarwa.

Na Biyu: Godewa Allah madaukakin sarki akan wannan babbar ni'imah.

Na Uku: Son wdannan Manzanni da kuma girmamasu kana da yabonsu akan abinda ya dace da su, domin su Manzanni ne na Allah kuma kebantattun bayinsa ne, sun tsaya domin Allah suna bauta masa kuma suna isar da manzancinsa suna kuma yin nasiha ga bayinsa da kuma hakuri da cutar da su da su bayin suke yi.

Yana daga cikin fa'idojin Imani da ranar lahira:

Na Farko: Kwadayi akan bautawa Allah domin samun lada a wannan rana, da kuma nesa da sabawa Allah domin gudun azaba a wannan rana.

Na Biyu: Lallashin mumini akan abinda zai rasa anan duniya na ni'ima da jindadinta saboda abinda yake kwadayinsa na ni'imomin lahira da kuma ladan.

Daga cikin fa'idojin Imani da kaddara:

Na Daya: Dogaro ga Allah madaukakin sarki lokacin aikata duk abinda yake shi sababi ne, domin shi sababi da abinda yake sabbabawa yana faruwa da hukuncin Allah da kuma kaddarawarsa.

Na Biyu: Kwanciyar hankali da samun natsuwar zuciya, domin a duk lokacin da kasan hakan na faruwa ne da hukuncin Allah kuma abin ki sai ya kasance ba makawa saii hankali ya kwanta kuma zuciya ta natsu, sai iyar da hukuncin Ubangiji, babu wani mutum da zai sami daddadar rayuwa da kuma kwanciyar hankali kuma natsuwarsa ta karfafa kamar wanda ya yi Imani da kaddara.

Na Uku: Yadda mutum zai nisanci yin mamakin kansa alokacin da ya sami abinda yake so, domin faruwar hakan ni'ima ce daga wurin Allah na abinda ya kaddara na sabubabban samun nasara, to sai ya godewa Allah madaukakin sarki akan haka, ya kuma bar ganin ya burge.

Na Hudu: Nisantar da damuwa da kaduwa a lokacin da ka rasa abinda kake so, ko abinda baka so ya faru, domin hakan da hukuncin Allah madaukakin sarki ne wanda yake shi ke da mulkin sammai da kassai, kuma hakan zai kasance ba makawa, sai ya yi hakuri akan hakan ya kuma kaunaci lada, akan hakane Allah madaukakin sarki yake nuni da fadinsa:

﴿مَا أَصَابَ مِن مُّصِيبَة فِي ٱلأَرضِ وَلَا فِي أَنفُسِكُم إِلَّا فِي كِتَب مِّن قَبلِ أَن نَّبرَأَهَا إِنَّ ذَلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِير٢٢ لِّكَيلَا تَأسَواْ عَلَى مَا فَاتَكُم وَلَا تَفرَحُواْ بِمَا ءَاتَىكُم وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُختَال فَخُورٍ٢٣﴾

Ma'ana:“Babu wata masifa da zata faru a bayan kasa ko akarankanku face tana cikin littafi (lauhul mahfuz a rubuce) tun kafin mu halicceta, lalle hakan a wurin Allah mai sauki ne. Domin kada ku yi bakin ciki akan abinda ya wuce muku (na alheri da ba ku samu ba) kuma kada ku yi farinciki akan abinda ya zaike muku ( ya baku), kuma Allah baya son dukkan mai takama kuma yawan alfahari". (Hadid: 22-23).

To muna rokon Allah da ya tabbatar da mu akan wannan akidar, kuma ya tabbatar mana da fa'idojinta, kuma ya kara mana daga falalarsa, kuma kada ya karkatar da zukatammu bayan ya shiryar da mu, kuma (muna rokonsa) da ya yi mana baiwa ta rahama daga wurinsa, lalle shine mai yawan baiwa, kuma dukkan godiya ta tabbata ga Allah.

Kuma Allah ya yi dadin tsira ga Annabimmu (Annabi) Muhammad da alayansa da kuma sahabbansa da kuma masu bin su da kyautatawa.

Wanda ya rubuta.

Muhammad Salih Al'uthaimin,

30 Shawwal, 1404H

(29/17/1984).

kafofi:

Nau'uka na ilmi: