LITTAFIN TAMBAYOYIN KABARI GUDA UKU, da Ka'idodi guda hudu (ALKAWA'IDUL ARBA'U), da abubuwan da suke warware Musulunci (NAWAKIDUL ISLAM)

wallafawa :

The Publisher:

nau, i

LITTAFIN TAMBAYOYIN KABARI GUDA UKU, da Ka'idodi guda hudu (ALKAWA'IDUL ARBA'U), da abubuwan da suke warware Musulunci (NAWAKIDUL ISLAM): Littafi ne da harshen HAUSA wanda Dr. Haisam Sarhaan ya wallafa shi, kuma littafin ya kunshi: 1- TAMBAYOYIN KABARI GUDA UKU: Wannan karamin littafi ne mai daraja wanda ya kunshi ginshikan da suka wajaba Mutum ya sansu, wanda kuma sune za a masa tambayoyi akansu a cikin kabarinsa, da ambato nau'ukan ayyukan ibada; wadanda Allah Ta'alah ya yi umurni da su, da bayanin martabobin addini (Islam, Iyman, Ihsaan). 2- ALKAWA'IDUL ARBA'U: Karamin littafi ne takaitacce, da yake bayanin ka'idodin tauhidi da saninsu, da wasu daga cikin shubuhohin da Mushirkai suke makalewa a jikinsu, da yadda ake musu raddi. 3- ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI (Nawakidul Islam): Takaitaccen littafi ne, wanda Mawallafinsa a cikinsa ya ambaci wasu daga cikin mas'alolin da suka fi hatsari ga addinin Musulmi, tare kuma da girman hatsarinsu, saidai suna cikin abubuwan da suka fi yawan aukuwa, Kuma ya ambace su ne domin Musulmi ya kiyayi aukawa a cikinsu, kuma ya jiye wa kansa tsoronsu. Kuma Mawallafin ya sanya littafin cikin wani tsari mai ban kaye, ta fiskar sanya shi cikin jadwala, da rarraba shi daki-daki, Kuma ya ambaci muhimman manufofin addini, da dunkulallun ma'anoni, Kuma a bayan kammala kowane yanki na littafin, Mawallafin ya tsara tambayoyi da jarrabawan da suka ta'allaka da wannan babin, Kuma ya ambaci dukkan wadannan ne; ba tare da takaicewar da zata cire wasu fa'idodi ba, ko tsawaitawa mai gajiyarwa mai sanya kosawa.

Download
karubuta zuwaga shugaba wannan shafi

Nau'uka na ilmi: