Rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama A Lokacin Aikin Hajji

Download
karubuta zuwaga shugaba wannan shafi

karin bayani

 Rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama  A Lokaci Aikin Hajji

Wallafar:

Faisal Xan Ali Al-Ba’dani

Fassarar:

Muhammad Mansur Ibrahim

Da

Aliyu Rufa’i Gusau

Bugawa da Yaxawar

Cibiyar Ahlulbaiti da Sahabbai Ta Najeriya

 Ja Makafi

SB =Sahihul –Bukhari

SM= Sahihu Muslim

MA=Mustadrak al Hakim

SA=Sahhahahu al Albani (Malam Albani ya inganta shi)

DA=Dha’afahu Albani (Malam Albani ya raunana shi)

HA=Hassanahu Albani (Malam Albani ya yi hukunci da kyawonsa)

ZM=Zadul Ma’ad

SN=Siratun Nabiyyi

FB=Fathul Bari

TA=Tuhfatul Ahwazi

AM=Aunul- Ma’abud

JT=Jami’ut Tirmidhi

JS=al Jami’us-Sagir

HW=Hajjatul Wada’i

SA= Shara’iul Imani

MM=al Misbahul Munir

MS=Madarijus-Salikin

MA=Mu’ujamul-Ausax

MS=Mukhtasarus-Sirah

SS=Sharhus-Sunan

RN=al Riyadun-Nadira

SN=Sharhun-Nawawi ala Muslim

JA=Jami’ul Ahkam

SD=Sunanud Darimi

MA=Mukhtasaru Ad’dhiya’i

MZB=Mukhtasaru Zawa’idil-Bazzar

MKK=al Mu’jamul-Kabir na Kurxnbi

SKB=al Sunanul –Kubura, Baihaki

MZH=Mu’jamuz –Zawa’id na Haisami

SIM=Sunanu Ibni Majah

SAD=Sunanu Abi Dawud

HIK=Hashiyatu Ibnil Kayyim

SIH=Sahihu Ibni Hibban

SNI=Sunanun Nisa’i

HAD=Hassanahu Arna’uxi (Malam Shu’aibu Arna’ux ya yi hukunci da kyawonsa)

TIK=Tafsiru Ibni Kasir

SSM=Sunanu Sa’id bin Mansur

KKH=Kashful –Khafa’a na Ijluni

SIA=Sahhaha Isnadahu al Albani (Malam Albani ya yanke hukunci isnadinsa ya na da kyau)

TJU==Takhriju Jami’il Usul

NFK=al Nisa’i Fil Kubra

FWM=al Faqihun Wal Mutafaqqih

IUD=Ihya’u Ulumid –Din

MSH=Mukhtasar as Shama’il

MAR=Musnad Abdir Razzaq

JUMH=Jami’ul Ulumi Wal Hikam

SMLN=Sharhu Muslim Lin Nawawi

ANWA=Akhlaqun – Nabiyyi Wa Adabuhu

MIAS=Musannafu Ibni Abi Shaibah

 GABATARWAR MASU FASSARA

Daga

Muhammad Mansur Ibrahim

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa baki xaya. Bayan haka:

Sanin rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na daga cikin mafi muhimmancin abinda ya kamata musulmi su mai da hankali gare shi. Musamman kuma idan ya kasance wannan yana da alaqa da ayyukan ibada waxanda Allah ya aiko annabin nasa don ya koya mana su. Aikin Hajji kuwa na daga cikin mafi girman rukunan musulunci waxanda ke buqatar jagora, masani. Babu masani kuwa daga bil adama wanda ya kai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Game da mawallafin wannan littafi Sheikh Faisal bin Ali, na san shi tun da daxewa a matsayin marubuci mai kaifin alqalami. Rubuce rubucensa a mujallar nan ta Al Bayan na daga cikin abinda ya sa mata farin jini a duniyar musulmi. Haxuwa da nayi da shi a taron masu wa’azin Africa a qasar Togo a 1995 da kuma wanda ya biyo bayansa a 1997 a qasar Ghana ta bani damar qara saninsa, sannan kuma yai mun karimcin da dama daga cikin wallafe wallafensa. Ba zan voye ma mai karatu ba cewa, na amfana da littattafan nasa matuqa. Amma a haqiqanin gaskiya ban tava ganin ya samu muwafaqa a rubutunsa ba sama da wacce ya samu a wannan littafin nasa, da kuma takwaransa mai taken “Rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin azumi”. Wannan shi ya sa nayi gaggawar gayyatar xan uwa Mal. Aliyu Rufa’i don mu haxa kai wajen mayar da shi zuwa harshenmu na Hausa saboda amfanin jama’armu, musamman kuma mahajjata waxanda, na tabbata zai taimaka masu matuqa wajen inganta Aikin Hajjinsu.

Salon da muka xauka a wannan aiki shi ne irin salon da masu buga wannan littafin (Cibiyar Ahlul Baiti Da Sahabbai) suka zava, wanda ya qunshi isar da saqon mai littafi cikakkiyar isarwa ba tare da canza masa magana ko ra’ayi ba. Amma kuma a samar da hanya mafi kyau wadda mai karatu zai fi fahimtar bayanin mawallafin bisa ga la’akari da nasa harshe. Wannan ya kan samar da wani taqaitaccen ‘yanci ga mai fassara amma ba tare da wuce iyaka ba. Misali, mai karatu zai lura da tsawaitawa a wasu wurare a cikin wannan littafi, da maimaita bayanai a wurare da dama. A wajen kawo hadissai kuma zai ga an kawo riwayoyi da dama a waje xaya waxanda daga qarshe ma’anarsu xaya ce, ba kuma tare da an taqaita akan xaya daga cikinsu ba. Mun so mu canza duka waxannan, amma ba ya cikin haqqinmu. Sai dai a cikin amincewar mawallafin wataqila nan gaba mu taqaita littafin gaba xaya.

Fassara wannan littafin zuwa harshen Hausa wata ‘yar gudunmawa ce daga vangarenmu don taimaka ma wovvasa da yekuwar da ake yi ta wayar da kan Musulmi akan koma ma sunnar Annabinmu Sallallahu Alaihi Wasallama da kauce ma sababbin abubuwa da suka vullo a cikin addini. Aikin da Mujaddadi Xan Fodiyo Allah ya jiqansa ya aza harsashinsa a qasar Hausa tun kimanin qarnuka biyu da suka wuce.

Tukuicin da muke nema ga waxanda aikin ya amfana shi ne su yi mana kyakkyawar addu’a ta samun alherin wannan aiki a lahira. Waxanda kuma aikin bai gamsar da su ba, su yi mana uzuri, domin aikin ya xan siffaitu da gaggawa fiye da yadda aka saba. Ga kuma gwamatson ayyuka waxanda muke neman taimakon Allah wajen kammala su.

Muna godiya ga Allah bisa samun damar haxa wannan aiki. Sannan dole ne mu yi godiya ga dukkan waxanda suka taimaka wajen kammala wannan aiki da waxanda suka ba da agaji wajen gyara kurakuran da ke cikinsa.

Daga vangarena kuma, dole ne in yaba ma Mal. Aliyu Rufa’i bisa ga namijin qoqarin da ya yi wanda ya zarce nawa nesa ba kusa ba a wannan aiki. Allah ya karva mana baki xaya.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen talikkai, Muhammadu xan Abdullahi, da iyalansa, da sahabbansa da mabiyan tafarkinsa akan gaskiya.

 A Misfala, ta birnin Makka

 Daren Assabar 06 ga Zul Hajji 1428

 GABATARWAR MAWALLAFI

 Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa baki xaya. Bayan haka:

 Tabbas Allah Ta’ala ya hori bayinsa da koyi da Annabinsa Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama a in da buwayayyen Sarkin ya ce:

“Kuma abin da Manzo ya zo maku da shi, to ku kama shi. Kuma abin da ya hane ku, to ku bar shi” (59:7)

 Haka kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya zavar wa musulmi koyarwa da karantarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a matsayin mafi nagarta da ingancin abin da za su bi. Allah Ta’ala ya ce:

“Lalle abin koyi mai Kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasance yana fatar (Samun rahamar) Allah da Ranar Lahira, Kuma ya ambaci Allah da yawa” (33:21)

 Bayan haka kuma, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya bayar da tabbacin cewa ba wani abu da ke nuna mutum na son Allah, kamar a gan shi yana koyi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Allah maxaukaki ya ce:

“Ka ce: “Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku” (3:31).

A wata ayar kuma fiyayyen Sarkin Ya Bayyana cewa yin biyayya ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta hanyar koyi da ayyukansa, shi ne xa’a a gare shi. Subhanahu Wa Ta’ala Yace:

“Duk wanda ya yi xa’a ga Manzon, to haqiqa ya yi xa’a ga Allah, kuma wanda ya juya baya, to ba Mu aike ka ba don ka zama mai tsaro a kansu” (4:81).

 Kafin wannan aya kuma, a cikin dai wannan sura, Allah ta’ala Ya faxi irin Sakamakon alherin da zai yi wa duk wanda ya bi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sau da qafa, a cikin horo da haninsa. Ya ce:

“Kuma duk waxanda suka yi xa’a ga Allah da Manzonsa, to waxannan suna tare da waxanda Allah Ya yi Ni’ima a kansu, daga cikin annabawa da masu yawan gaskatawa da masu shahada, da Salihai. Kuma Waxannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya” (4:69).

 Na’am. Gaba xayan waxannan ayoyi da suka gabata na nuna wajabcin Kwaikwayo da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne a cikin ayyukan Ibada. Aikin Hajji kuwa na xaya daga cikin ibadodin musulunci, wanda kuma koyi da manzon a cikinsa na da matuqar sauqi. Saboda Shehunan Malamai, da xalibai masu qwazo da hazaqa a yau, sun himmatu matuqa ga yin aikace – aikace, don fitowa da hukunce – hukuncen wannan ibada ta Hajji a fili. Tare da bayanin abubuwan da ke inganta ta ko vata ta. Wannan qoqari nasu kuwa ya taka muhimmiyar rawa a wannan fage. Domin ya cika wani wagagen gurbi, a cikin wannan sha’ani. Ta hanyar yaxa ilimi da warware zare da abawar wannan babban ginshiqi na addini.

 Sai dai duk da haka, akwai wani vangare da malaman ba su tavo ba. Tattare da irin muhimmancin da yake da shi. Wanda hakan ke sa lalle a kula da shi. Wannan vangare kuwa shi ne: Rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin Aikin Hajji. Babu wanda ya ce komai a wannan sashe har yau.

 Kuma ko shakka babu gabatar da wani aiki a kan wannan vangare na da matuqar muhimmanci, musamman idan aka yi la’akari da waxannan abubuwa kamar haka:

·   Yin nazarin qwaqwaf a rubuce a wannan fage, tare da aiwatar da shi, bayan ya zauna daram a qwaqwalen musulmi, zai taimaka matuqa ga raya wannan sashe na hikimomin da ke qunshe a cikin Aikin Hajji, da fitowa fili da manufofin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke da su a cikin wajabta wannan ibada. Tare da fitowa da irin tsabar narkewar da gaba xayan al’umma ke yi a gaban Allah Subhanahu Wa Ta’ala a matsayin bayi a wannan lokaci.

·   Wannan aiki zai shafe rashin masaniyar da, da yawa daga cikin musulmi ke da, game da irin yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke gudanar da rayuwarsa a wannan lokaci na Aikin Hajji. Wanda hakan ta sa ba su damu da neman sanin ta ba. Kullum abin da kawai suke qoqarin naqalta shi ne hukunce – hukuncen ibadar kawai.

·   Haka kuma Aikin zai qara wa xalibai ilimi. Musamman waxanda ke nazarin Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin kuwa mafi yawansu na da qishirwar wannan sashe, balle su xabbaqa shi. Tattare da sha’awar da suke da ita a kan Sunna.

·   Wannan aiki zai fito da wani sanfuri ne na daban na rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama saboda a irin wannan lokaci na Aikin Hajji mutum ya kan sadu da mutane daban – daban, waxanda idan ba irin wannan lokaci ba, sai dai ya ji labarinsu. Amma ba zai gansu ba balle ya yi hulxa da su.

·   A wannan lokaci na Aikin Hajji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kan kasance tare da gaba xayan matansa da wasu masu rauni daga cikin iyalin gidansa da danginsa. Hakan kan zama wani madubi na kyawawan halayensa da hulxarsa da su, a cikin wata siga da ba ta tava faruwa ba.

A dunqule, wannan aiki na nufin bayar da cikakken hoto ne a kan yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke rayuwa a lokacin Aikin Hajji. Da fatar hakan zai taimaka wa masu qoqarin koyi da shi Sallallahu Alaihi Wasallama da tafiya a kan tafarkinsa.

 Kamar yadda na faxa a baya, an yi aikace – aikace da yawa a kan yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Ya gudanar da Aikin Hajji. Saboda haka ba zan kutsa kai sosai a wannan sashe ba. Amma dai zan riqa xan yin nuni da ishara zuwa ga wasu sassa masu kama da haka. Tare da mayar da hankali kacokwan ga sassan da ba su ba.

 Na yi qoqarin taqaita wannan aiki a cikin babuka guda uku, don ya yi sauqin fahimta ga masu karatu. Kuma wasu sassa ne kawai na kalla daga cikin sassan rayuwar Manzon a wannan lokaci. Domin yana da wuya a iya haxa gaba xayan yanayin rayuwar tasa Sallallahu Alaihi Wasallama ta lokacin a cikin aiki xaya.

 Babi na xaya, ya yi magana ne a kan Rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Tsakaninsa da Ubangijinsa a lokacin Aikin Hajji. Na biyu kuma, tsakaninsa da al’ummarsa. A yayin da babi na uku, ya kula da rayuwar tasa Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin, tsakaninsa da iyalinsa.

 A qarshe ina rokon Allah albarkacin kyawawan sunayensa da maxaukakan siffofinsa, yadda ya nufi aka wallafa wannan littafi da rahamarsa da jinqansa, ya sa shi mai amfani ga mahajjata da masu Aikin Umra. Ya kuma zama wata garkuwa ga masu koyi da Shugaban manzanni, Sannan ya zama karvavve a wurinsa, a matsayinsa na mai karva du’a’i Subhanahu Wa Ta’ala.

 A qarshen qarashewa kuma, ba zan dasa aya ba, sai na yi godiya ga duk wanda ke da hannu a cikin fitowar wannan littafi. Ina fatar Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya saka masu da mafificin alherinsa.

 Allah ka daxa aminci ga bawanka kuma manzonka da alayensa da sahabbansa baki xaya.

 BABI NA XAYA

 1.0 Rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Tsakaninsa da Ubangijinsa a Lokacin Aikin Hajji

 Wannan babi zai yi magana ne a kan irin yadda Annabi, Sallallahu Alaihi Wasallama ke gudanar da rayuwarsa, tsakaninsa da Ubangijinsa a lokacin da yake garin Makka da sauran wuraren ibada, don gudanar da Aikin Hajji, ta hanyar tabbatar da kaxaituwar Allah, da girman ibadodinsa, da raba gari da mushrikai, da yawaita qanqan da kai ga Allah, da kuma tsayawa ga iyakokinsa, da sauransu.

 1.0.1 Simfixa

Yawan kusanci da Allah Maxaukakin Sarki da danqon zumunci tsakanin bawa da Ubangijinsa, su ne dukiya kuma hannun jarin bayin Allah na qwarai. Shi kuwa lokacin Aikin Hajji na xaya daga cikin lokutan da ke cike da amon taqawa da tsoron Allah. Kuma babbar makaranta ce da babu komai a cikinta sai tsabar bauta. Lokaci ne da danqon zumuncin da ke tsakanin Allah Subhanahu Wa Ta’ala da bayinsa ke qara qarfi, har ya tasar wa zama kwangiri qarfen jirgi.

Haka kuma a wannan lokaci ne zuciyar xan Adam ke sabawa da cirata daga wata bauta zuwa ga wata, nan take ba tare da yankewa ko hutawa ba. Ta yadda tsoron Allah da qanqan da kai gare shi, za su tarwatsa rundunar shexan da ke cikin zuciyarsa.

Duk da kasancewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne wanda ya fi kowa bauta ga Allah, da kusanci da gwamatsarsa, ibadarsa ta Aikin Hajji makaranta ce. Domin yawan ibadar tasa ya qaru matuqa a lokacin, ta fuskoki daban-daban: ya karantar da alhazzai ya kuma yi masu jagora. Ya kula da matansa ya kuma zame masu gata. Ya yi haquri kyakkyawa da sauran mutanen gidansa da ke tare da shi a lokacin, ya kuma kyautata masu iyakar kyautatawa.

 Amma kuma duk wannan nauyi, bai sa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya xaga qafa da minti xaya ba, daga neman fada wurin Ubangijinsa, ta hanyar narkewa a matsayinsa na bawansa.

 Ba zamu ce mu qididdige yanaye-yanayen da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qanqan da kansa ga Ubangijinsa a wannan Lokaci, ya miqa wuya gare shi matuqar miqawa ba, anan dai zamu taqaita ne kawai a kan mafi muhimmanci daga cikinsu.

 1.1 Ban Ruwan Itaciyar tauhidi

 Shayar da itaciyar tauhidi da musulmi suka zo da ita tana a dashe cikin zukatansu ruwa, don ta yi kyau ta barbaje, na daga cikin abubuwa muhimmai da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi a lokacin Aikin Hajji. Yana kuma yin haka ne saboda tabbatar da ganin Aikin Hajjin kowa ya kasance don Allah kawai. Saboda cewa Sarkin Ya yi:

“Kuma ku cika Hajji da Umra domin Allah”. (2:196)

 Ayar na nufin kada a yi Aikin Hajji da wata manufa ba Allah ba. Sannan kuma a yi shi da kyau. Kamar yadda shari’a ta tanada (TKR:90).

 Duk wanda ya kalli Aikin Hajjin ma’aiki da idon basira, zai ga haka.

 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan yi qoqarin tabbatar da wannan manufa a qashin kansa, ta waxannan hanyoyi:

i) Talbiyyah (Faxar Labbaikallahumma..):

 Talbiyyah shishshike ce daga cikin shika-shikan Aikin Hajji (SIUH:2627,2629) kuma ta qunshi kaxaita Allah Subhanahu Wa Ta’ala da aiki (Hajji); shi kaxai ba tare da kowa ba. Kamar yadda ya zo a cikin hadisin da jabiru Allah ya yarda da shi ya riwaito, cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan fara Aikin Hajji da shelanta kalmar tauhidi. “Mun karva kiranka ya Ubangiji, mun karva, ba ka da abokin tarayya, mun yarda. Ka cancanci godiya, kuma da ni’ima da mulki duka naka ne. ba ka da abokin tarayya”. (SM:1218)

Waxannan kalmomi ne Annabi ke faxa a matsayin talbiyya, amma a cikin harshensa na larabci. Kuma xan Umar Allah ya yarda da su ya ce: “Iyakar abin da yake faxa kenan ba ragi ba qari”. (SB:5915/SM:1184). Amma kuma Abu Hurairata Allah ya yarda da shi ya ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kan ce a cikin talbiyya: “Mun karva kiranka ya Ubangijin gaskiya, mun karva” (SIM:2920/SA:2362).

ii) Ikhlasi:

 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na iyakar qoqarinsa na ganin Aikin Hajjinsa ya zama tsarkakakke. Yana kuma yawaita roqon Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya taimake shi a kan nisantar riya a cikin aikin. Kamar yadda Anas Allah ya yarda da shi ya riwaito cewa, Manzon Allah ya kan riqa cewa: “Ya Ubangiji ka nufa mu yi Hajji wanda ba riya ba fankama a cikinsa” (SIM:2890/HF: 3/446/SA;2617).

 Bayan wannan du’ai kuma ya kan karanta surori biyu a cikin raka’o’in nan biyu da a kan yi bayan xawafi. Wato ‘Suratul- Kafiruna” da “Suratul – ikhlasi” (Qulhuwallahu Ahad) kamar yadda Jabir Allah ya yarda da shi ya riwaito cewa: “Annabi ya kan karanta Surorin tauhidi biyu a cikin raka’o’in (xawafi). (SAD: 1909/SA: 689) A wata riwaya kuma ya ce: “Annabi ya kan karanta Surorin Ikhlasi a cikin raka’o’in xawafi: Qul ya Ayyuhal Kafiruna, da qul Huwallahu Ahad” (JT: 869/SA: 689).

 Bayan waxannan abubuwa guda biyu kuma, akwai wurare biyu muhimmai da a lokacin Aikin Hajji babu abin da ake yi wajensu sai addu’o’i. To shi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama duk du’a’in da zai yi a wurin ya shafi kaxaita Allah ne (Tauhidi). Wuraren kuwa su ne:

i) Safa da Marwa:

 Jabir Allah ya yarda da shi ya ruwaito cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan fara hawa kan dutsen safa har sai ya tsinkayi xakin Ka’aba, Sannan ya fuskanci alqibla, ya kaxaita Allah, ya kuma yi kabbara ya ce: “Babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, shi kaxai ba ya da abokin tarayya. Mulki da godiya duka nasa ne. Kuma shi mai iko ne a kan dukkan komai. Babu wani Ubangiji sai Allah shi kaxai… Haka zai faxi har sau uku, Sannan ya isa Marwa, ya hau kan dutsen ya yi kamar yadda ya yi a kan na Safa…” (SM:1218)

ii) Filin Arafa:

 Ya zo a cikin wani hadisi cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yana cewa: “Mafi alherin du’a’in da mutun zai yi Ranar Arafa, kuma mafi alherin abin da Ni da sauran Annabawan da suka gabace ni kan faxa shi ne: Babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, shi kaxai ba ya da abokin tarayya. Mulki da godiya duka nasa ne, kuma shi mai iko ne a kan dukkan komai” (JT: 3585/HA: 2837) Haka kuma Amru xan Shu’aibu ya riwaito daga mahaifinsa, daga kakansa cewa “Mafi yawan du’a’in da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi a Ranar Arafa shi ne ‘La’illaha Illal Lah…’” Wani lokacin kuma ya kan qara da cewa “Bi Yadihil Khairu” (MA: 6961).

 1.0.2 Hannunka Mai Sanda

 Abin takaici a yau, duk wanda ya dubi yadda mafi yawan musulmi ke gudanar da rayuwarsu ta Aikin Hajji zai ga maqare take da bidi’o’i da canfe-canfe da ayyukan shirka irin waxanda mamakonsu ya kai wa mutane da yawa ga hanci.

 Saboda haka muke kira da babbabr murya ga malamai da masu wa’azi, musamman waxanda ke a wannan babban wuri mai alfarma da su sani wajibi ne a kansu, su karantar da mahajjata tushen addini. Su yi masu cikakken bayani, filla-filla a kan tantagaryar tauhidi, kamar yadda gaba xayan manzanni suka zo da shi. Tare da yi masu kashedi da hani daga Babbar shirka da Qarama, da kuma dukkan abin da yake vata ne.

 Wannan ita ce koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, tun da ya gabatar da sha’anin Tauhidi tare da farawa da shi kafin ko wace irin ibada ta motsa jiki. Babban abin da ke tabbatar mana da wannan shi ne: A lokacin da Manzon Sallallahu Alaihi Wasallama ya aiki Mu’azu Allah ya yarda da shi zuwa Yaman don yaxa Addinin Musulunci sai ya ce masa: “Ka fara kiran su zuwa ga, shedar babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, kuma ni Manzon Allah ne. Idan sun yarda da haka, sai ka sanar da su cewa, to Allah Ya wajabta Salloli biyar a kansu ko wace rana. Idan sun yarda da haka, sai kuma ka gaya masu cewa, to kuma, Allah ya wajabta masu fitar da zakka daga cikin dukiyarsu, wadda za a karva daga hannun mawadata daga cikinsu, a mayar ma talakkawansu” (SB”1395)

 A kan haka, babu abin da ya fi dacewa da xan’uwa mahajjaci, kamar tabbatar da amon Tauhidi a cikin zuciyarsa, tare da qoqarin isar da saqon ga sauran ‘yan uwansa mahajjata.

 1.2 Darajanta Wuraren Ibada:

 Allah Ta’ala ya kwaxaitar da bayinsa a kan girmama ibadodin da ya yi umurni da su. Haka kuma da wuraren da ake gudanar da su. Su ma kada a wulaqanta su, don su ne alamomin addininsa (Q, JLAQ:2/37, 6/37, 12/180).

 Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya nufi waxannan abubuwa da kasancewa ginshiqan taqawa. Kuma ta hanyarsu ne musulmi ke karva sunan bayin Allah. Don ta hanyarsu ne su ke bauta masa. Haka kuma su ne dalilin samun ladarsa da alherinsa a lokacin da aka sami haxuwa da shi. Saboda haka ne Ya hori bayinsa da girmama su, Ya ce:

“Wancan ne, kuma duk wanda ya girmama (wuraren) bautar Allah, to lalle ne ita (girmamawar) tana daga ayyukan xa’a na zukata” (22:32).

Haka kuma a wani hadisi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na isar da wannan saqo na Ubangijinsa, na girmama waxannan abubuwa. Ya ce:

“Ka nisanci duk abin da Allah Ya haramta, sai ka zama mafi bauta daga cikin mutane” (JT:2305/HA: 1876).

Bayan wannan kuma, sai Buwayayyen Sarki Ya yi hani da a wulaqanta ibadodinsa da wuraren da ake gudanar da su, bayan Ya yi umurni da girmama su. Ya ce, kada a keta rigar mutuncinsu. Ya ce, a game da Haramin Makka:

 “Kuma duk wanda ya yi nufin kawar da gaskiya a cikinsa da zalunci za mu xanxana masa wata azaba mai raxaxi” (22:25)

A wata ayar kuma Ya ce:

 “Waxancan iyakokin Allah ne, saboda haka kada ku qetare su. Kuma duk wanda ya qetare iyakokin Allah To, waxannan su ne azzalumai” (2:229)

A wata ayar kuma Ya ce Subhanahu Wa Ta’ala:

“Kuma Duk wanda ya sava wa Allah da Manzonsa, kuma ya qetare iyakokinsa, zai shigar da shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azaba mai wulaqantarwa” (4:14)

 Girmama ibadodi shi ne aikata abinda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce a aikata, kamar kuma yadda Ya ce, tare da nisantar abin da Ya ce a nisanta.

 Manzon Allah, Almustafa Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne farkon wanda ya fahimci abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke nufi da waxannan ayoyi. Sannan sauran musulmi masu gani da hasken Allah, suka rufa masa baya. Limamin annabawa, shugaban halitta baki xaya, shi ne kuma ya fi duk wani mai tsoron Allah Ta’ala girmama ibadodinsa ta hanyar xaukaka alqadarinsu, tare da yin kaffa-kaffa da nisantar duk wani abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta. Kuma shi ne yafi kowa daga cikinsu xaure hannu da qafarsa don nisantar iyakokinsa a cikin rayuwarsa baki xaya.

 Lokacin Aikin Hajji kuwa, wata dama ce da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke amfani da ita ya yi fadanci a wurin Allah Subhanahu Wa Ta’ala fai da voye. Ta hanyar girmama ibadodi da wuraren yin su da nisantar haramce –haramce. Ya kan kuma yi haka ne ta fuskoki da dama da suka haxa da:

 a) Tsafta:

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan Lokaci na Hajji ya kan yi cikakkar tsafta, ta hanyar yin wanka kafin ya xaura Harami. Sannan kuma ya tsefe gashin kansa ya kuma shafe shi da mai don samun tabbacin kulawa da kiwon lafiya. Kuma domin kada gashin ya zama tunbutsai, balle qwarqwata ta sami mafaka a cikinsa. Sannan kuma sai ya nemi turaren da ya fi ko wane qanshi ya shafa.

Zaidu xan Sabitu Allah ya yarda da shi na cewa a wani hadisi nasa: “Na ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kimtsa ya yi wanka don kama Aikin Hajji” (JT: 830/SA: 664). Haka kuma Ibnu Umar Allah ya yarda da su na cewa a wani hadisi: “Na ji cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana kama Aikin Hajji bayan da ya tsaftace gashin kansa da kyau” (SB:1540) Haka kuma sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda na cewa a wani hadisi: “Ni kan shafa wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama turare mafi qanshi kafin ya xaura Harami “(SM:1189/SD:1801). A wata riwaya kuma ta ce Allah ya yarda da shi: “Ni kan shafa wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama mafi qanshin turaren da yake da shi, har sai na ga gashin kansa da na gemunsa sun fara walqiya” (SB:5923).

b) Hidimar Hadaya:

 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan yi tsaye haiqan ga hidimar raqumman da zai yi Hadaya da su da kansa. Ta hanyar gargaxa su daga Zul-hulaifa, a matsayinsu na abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya hukunta a gudanar da wata ibada ta Hajji da su. Kamar inda Ya ce:

“Kuma raquman, Mun sanya su a gare ku (wata hanya) ta ibadodin Allah” (22:36).

 Bayan wannan kuma, shi da kansa ne Sallallahu Alaihi Wasallama kan tsattsaga tozayen waxannan raquma, jini ya darara a jikinsu, tare da rataya masu takalma a wuya, duk da hannunnsa mai tsarki Sallallahu Alaihi Wasallama don a iya banbancewa tsakaninsu da waxanda ba na hadaya ba.

 Xan Abbas Allah ya yarda da su ya tabbatar da wannan magana a cikin wani hadisi, inda ya ce: “Qarewar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Sallar Azzahar a Zul-hulaifa ke da wuya sai ya ce a kawo masa raqumarsa, ya tsattsage shafin tozonta na dama, jini ya tsiyayo, ya kuma rataya mata takalma biyu a wuya” (SM:1243).

 Malam Ibnu kathir ya ce: “Wannan hadisi na nuna mana cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne da kansa ya tsattsage tozon wannan taguwa tasa, ya kuma rataya mata takalman da hannunsa mai alfarma. Amma sauran raquman hadayar, wakiltawa ya yi aka yi masu irin wannnan hidima” (SN:4/228) Abin da kuma ke tabbatar da wannan sharhi na ibnu kathir shi ne wata riwaya da ta zo a kan sha’anin hadayar, wadda ke cewa:

“Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi umurni da a tsattsage shafin tozon raqumansa na Hadaya na dama” (SIM:2609).

 Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya karrama raquman hadayar, ta hanyar hana duk wanda ke da hali hawansu. Kamar yadda hadisin Jabiru Allah ya yarda da shi ke tabbatarwa cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda rashin wata mazauxa ta tilasta shi hawan raqumin hadaya, to ya hau shi cikin ladabi da girmamawa. Kuma da zarar ya sami wanda aka tanada don jigila, to ya sauka daga kan na hadaya” (SM:1324).

c) Lizimtar Talbiyyah:

 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan tsare talbiyyah ba qyaqqyaftawa, da zarar ya fara gudanar da Aikin Hajji, har zuwa lokacin da zai jefi Aqabah a ranar sallah. Kamar yadda ya zo a cikin hadisin xan Abbas Allah ya yarda da su cewa: “Haqiqa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan lizimci talbiyyah har sai ya jefi Aqabah, Sannan ya saurara”. (SIM:3040/SA:2464). Haka kuma Xan Mas’ud Allah ya yarda da shi ya tabbatar da wannan magana a cikin wani hadisi da yake cewa: “Ina rantsuwa da wanda ya aiko Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama da gaskiya, na fita tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga Mina zuwa Arafat amma bai daina talbiyyah ba har sai da ya jefi Aqaba, sai dai ya kan sassaqa ta da Hailala (Faxar La’ilaha Illallahu) da Kabbara (Faxar Allahu Akbar) (MH:1/461/SIM:2806).

 Haka kuma wannan Talbiyyah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke lizimta a wannan lokaci, ba cikin zuciya yake yinta ba. A’a, ya kan xaga muryarsa ne, har duk wanda ke tare da shi daga cikin sahabbansa Allah ya yarda da su ya ji. Kamar yadda xan umar Allah ya yarda da su ya tabbatar a cikin wani hadisi cewa: “Na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana buxe Aikin Hajji da “Labbaika.. ” bayan ya tsaftace gashin kansa”. (SB:5915/SM:1184) Haka shi ma hadisin xan Abbas Allah ya yarda da su na tabbatar da haka, inda ya ce: Haqiqa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Lalle Jibrilu ya zo mani, ya kuma umurce ni da shelanta Talbiya” (M.A:2950). Haka kuma manzon ya umurci Sahabbai da su ma su shelanta ta, kamar yadda Jibrilun ya umurce shi da umurtar su a wata riwayar (M.A:8314/B:5/42).

 Daga nan sai suka xunguma baki xaya, suna Talbiyya bayyane. Kamar yadda baban Sa’idu Allah ya yarda da shi ya tabbatar a wani hadisi cewa: “Mun fita tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama muna ta kururutawa da Aikin Hajji (yana nufin Talbiyya). (SM:1247).

d) Girmama garin Makka:

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan girmama garin Makka, ta hanyar yin wanka kafin ya shige shi don gudanar da Aikin Hajji. Ya kan yi haka ne don ya kawar da qurar da ya xauko a hanya. Idan kuma ya shiga masallacin Ka’aba sai ya fara gabatar da xawafi. Kamar yadda Nafi’u ya riwaito cewa Xan Umar ba ya shiga garin makka kai tsaye don gudanar da Aikin Hajji har sai ya yada zango ya kwana a Zu-Xuwa. Idan gari ya waye kuma sai ya yi wanka, ya kuma jira sai rana ta yi Sannan ya shiga. An kuma riwaito cewa haka Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi (SM:1259).

 Haka kuma hadisin Sayyidah Aisha Allah ya qara mata yarda na tabbatar da haka, inda ta ce: “Farkon abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi bayan ya iso Makka shi ne alwalla, Sannan ya yi xawafi” (SB:1615).

e) Girmama Hajarul – Aswad:

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan yi fadanci ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala a wannan lokaci, ta hanyar karrama hajarul –Aswad da xaukaka alqadarinsa. Ya kan rungume shi, ya sumbance shi, ya yi sujada kan shi, ya kuma fashe da kuka. Haka kuma ya kan sumbanci kwanar Ka’aba mai suna Ruknul – Yamani. Kamar yadda ya zo daga Suwaidu xan Gafala, wanda ya ce: “Na ga Umar Allah ya yarda da shi ya sumbanci al-hajaru, ya kuma rungume shi. Sannan ya ce: na ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne yana girmama ka matuqa” (SM:1271) Haka kuma xan Abbas Allah ya yarda da su ya ce:

“Haqiqa Umar xan Haxxabi Allah ya yarda da shi ya kafe a wurin Rukuni, yana cewa: “Wallahi na san cewa kai dutse ne, ba kuma don na ga masoyina Sallallahu Alaihi Wasallama ya sumbance ka, ya rungume ka ba, da ban rungume ka na sumbance ka ba” (MA: 131).

Haka kuma an samo daga xan Abbas xin, ya ce: Na ga Umar Allah ya yarda da shi ya sumbanci Rukuni, ya kuma yi sujada a kansa. Sannan ya ce: Na ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Ya yi haka, shi ya sa na yi” (MD: 1/215-216/skb: 5/74).

 Haka kuma Jabir Allah ya yarda da shi ya riwaito cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fara ne da hajaru, ya sumbance shi. Nan take kuma idanunsa suka vare da hawaye, ya rinqa kuka”. (SUB: 5/74) Haka kuma an samo daga xan umar Allah ya yarda da su wanda ya ce: “Babu abin da ke hana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sumbantar Rukuni da Hajaru, a duk Lokacin da ya yi xawafi” (SAD:1876/SA:16652).

f) Sallah a Bayan Maqamu da Fara Sa’ayi a Safa:

 Haka kuma a duk lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qare xawafi ya sumbanci Rukuni da Hajaru ya kan yi nafila bayan Maqamu Ibrahim. Idan ya zo wurin Sa’ayi kuma ya kan fara ne da dutsen Safa, ya tsaya a kansa ya ambaci Allah ya kuma yi du’a’i. Kamar yadda ya zo a cikin dogon hadisin nan na Jabir Allah ya yarda da shi inda ya ce: “Sannan sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya wuce zuwa wurin Maqamu Ibrahim ya karanta: “Kuma ku riqi wurin Sallah daga Maqamu Ibrahim” (2:125). Yana karanta haka ne, daidai lokacin da Maqamu xin ke tsakaninsa da Ka’aba.

Daga nan kuma sai ya fita ta qofar da ya shigo ya nufi Safa. Da ya yo kusa da dutsen sai ya karanta: “Lalle ne Safa da Marwa na daga cikin wuraren Ibadar Allah” (2:158) sai kuma ya ce: To zan fara ne da abin da Allah Ya fara ambata (Wato Safa). Sai ya hau kan dutsen Safa; can sama sosai har sai ya tsinkayi xakin Ka’aba. Sannan ya fuskanci alqibla ya kaxaita Allah ya kuma girmama shi; ya ce: babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, shi kaxai; ba ya da abokin tarayya. Mulki da godiya duka nasa ne. Kuma shi mai iko ne a kan komai. Babu wanda ya cancanci bauta sai shi kaxai. Ya cika alqawarinsa, ya kuma taimaki bawansa. Kuma shi ne wanda Ya qasqantar da rundunonin kafirai shi kaxai. Daga nan kuma sai ya yi du’a’i, ya kuma sake maimaita haka sau biyu. Sannan ya sauka ya nufi Marwa. A nan kuma zai yi kamar yadda ya yi a kan Safa” (SM:1218).

 A wata riwaya kuma ya ce: “Kuma ku riqi wurin sallah daga Maqamu Ibrahim” (2:125). Daga nan sai ya yi nafila raka’a biyu. Yana mai sa Maqamu xin tsakaninsa da xakin Ka’aba” (JT: 856/SA: 679).

g) Tsayuwa a Mash’arul-Haram:

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan girmama wurin nan da ake kira Mash’arul Haram, ta hanyar tsayuwa wurin ta wani dogon lokaci. Yana kuwa yin haka ne don tabbatar da umurnin Allah Ta’ala da ya ce:

“Babu laifi a kanku ga ku nemi falala daga Ubangijinku. Sannan idan kun sauko daga Arafat, ku yi ta ambatar Allah a wurin Mash’arul Haram. Kuma ku tuna shi kamar shiriyar da ya yi muku, kuma lalle ne kun kasance, a gabaninsa, haqiqa, daga vatattu” (2:198).

 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan ya da zango ne a wannan wuri yana ambato da tuna ni’imomin Ubangijinsa, da fakewa wurinsa ta hanyar zubewa yana fadanci a gabansa. Jabiru Allah ya yarda da shi ya siffanta wannan yanayi da cewa: “Da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya qare sallar safe, bayan hudowar al-fijiri da kiran salla da tayar da iqama. Sai ya hau Mash’arul Haram. Ya tsaya wurin ya fuskanci alqibla, ya yi du’a’i, ya yi kabbarori da Hailaloli da Tashahhudodi. Bai gushe ba yana tsaye har sai da gari ya waye garas. Amma bai bari rana ta vullo ba, ya bar wurin” (SM:1217).

 h) Sanya Turare Don Ziyartar Ka’aba:

 Kafin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tafi ziyarar xakin Ka’aba daga Mina, bayan ya gama tahalluli na farko (gama ayyukan ranar sallah) ya kan shafa turare mai qanshi don girmamawa ga wannan xaki a matsayinsa na wurin da ake bautar Allah.

 Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ta tabbatar da wannan magana a cikin wani hadisi, da tace: “Na shafa wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama turare daga Mina kafin ya tafi ziyarar xakin Ka’aba” (SIKH:2934/SIH:3881).

 i) Girmama Wuri Da Lokacin Aikin Hajji.

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na matuqar girmama gaba xayan lokacin da ake gudanar da Aikin Hajji a cikinsa, da kuma wurin da ake yinsa; wato garin Makka. Abin bai tsaya kansa ba kawai Sallallahu Alaihi Wasallama sai da ya tabbatar da wannan girma nasu a cikin zukatan Musulmi, da ya ce: “Haqiqa jinainanku da dukiyoyinku haramun ne ga junanku, kamar yadda wannan yini naku yake da alfarma. Musamman kuma a cikin wannan wata naku mai alfarma, a cikin kuma wannan gari naku mai alfarma” (SM:1218) kamar kuma yadda a wani wurin yake cewa Sallallahu Alaihi Wasallama: “Haqiqa mafi girman kwanuka a wurin Allah Ta’ala shi ne Ranar Babbar Sallah kuma Ranar Layya” (SAD:1765/SA:1552) A wani wurin kuma yake cewa Sallallahu Alaihi Wasallama: “Ranar Arafa da ranar sallah (Babba) da kwanaki uku bayanta duk, ranaku ne na shagali (cin abinci da shan abin sha) da ambaton Allah Ta’ala” 9JT:773/SA:620).

 Bayan waxannan tamburra da Almusdafa Sallallahu Alaihi Wasallama ya buga ma wannan lokaci da waxannan kwanuka sai kuma ya faxa wa musulmi irin gajiyar da za mu samu idan muka kiyaye alfarmar wannan lokaci. Kamar yadda ya gaya mana xin nan! Kada mu kuskura mu keta rigar mutuncinsu. Ya ce Sallallahu Alaihi Wasallama: “Duk Aikin Hajjin da aka yi shi ba tare da an ci waxannan iyakoki (da ya shata ba), to ba ya da wani sakamako sai aljanna” (SB: 1773/SM:1349) Ya kuma qara da cewa: “Duk wanda ya ziyarci wannan xaki (ya yi Aikin Hajji) bai yi wata alfasha ko fasiqanci ba, to zai dawo gida sumul kamar yadda mahaifiyarsa ta haife shi, ba ya da zunubi ko xaya” (SB:1819). Wannan Magana kuwa sharhi ne manzo Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi da qara tabbatar da faxar Allah Subhanahu Wa Ta’ala cewa:

“Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar Hajji a cikinsu, (ya sani) babu jima’i kuma babu fasiqanci, kuma babu jayayya a cikin Hajji. Kuma abin da kuka aikata na alheri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To mafi alherin guzuri yin taqawa. Kuma ku bi ni da taqawa, ya ma’abuta hankula” (2:197).

1.2.1. Hannunka Mai Sanda:

 Duk wanda ya dubi irin yadda mafi yawan musulmi ke gudanar da Aikin Hajji a yau, zai ga ya sha banban da wannan karantarwa ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Babu abin da irin waxannan mahajjata ke yi sai keta alfarmar aikin na Hajji, ta hanyar qetare iyakokin Allah Subhanahu Wa Ta’ala da tozarta ayyukan Hajji da tabbatar da cewa ba su san girman Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba, balle su ba shi matsayin da ya cancance shi. Hakan sai ta sa maganar da Malam Ibnul-Qayyim Rahimahullahu ya yi ta yi dai-dai da su, da ya ce: “Duk wanda rashin ganin girman Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya sa ya sava masa, ta hanyar yin biris da horace-horacensa da aikata abubuwan da ya hana, da tozarta haqqoqinsa, da yin ko oho da ambatonsa, da kakkave zuciya daga tunaninsa. Aka wayi gari ya fifita son zuciyarsa a kan neman yardar Allah, kuma biyayya ga wani abokin halitta ta fi muhimmanci gare shi bisa ga xa’ar Allah. Wanda duk yake haka, bai girmama Allah yadda ya dace da shi ba. Allah kuwa Ya wadatu daga zuciyar irin wannan mutum da Aikinsa da iliminsa da dukiyarsa. Wanda ba haka ba kuwa shi ne na gaba – gaba a wurinsa, saboda muhimmancinsa” (JK:98).

 Saboda tsere wa irin wannan haxari ne muke kira ga ‘yan’uwa mahajjata, da babbar murya, da cewa su ji tsoron Allah. Su kuma yi koyi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin girmama ibadodi da wuraren yin su, tare da nisantar iyakokin Allah. Da gudanar da Aikin Hajji kamar yadda shari’ah ta tanada. Su kuma yi gargaxi ga ‘yan uwanmu alhazai da tsare gaskiya. Su yi haquri da abin da hakan zai haifar. Wannan shi ne wajibi.

 1.3 Shelanta Raba Gari da Mushrikai:

 Musulunci da shirka kishiyoyin juna ne da, basu ga maciji. Kuma dole ne xayansu ya kau kafin xaya ya samu gindin zama. Kamar dai dare ne da rana, ko kaskon Rana da na wata, waxanda haskensu ba ya tava haxuwa a lokaci xaya. Saboda haka farkon abin da musulmi suka fara yi a Makka bayan Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya mallaka masu ita shi ne, kawar da duk wani abu da ke da alaqa da shirka ko masosonta, tare da turmuje gurabun bautar gumaka.

 Kai! Saboda muhimmancin da wannan al’amari yake da shi, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai tsaya wata-wata ba; nan take, shigarsa harabar masallacin Harami ke da wuya, ya fara sa sandarsa mai alfarma yana zungurar gumakan da ke kewaye da xakin Ka’aba yana karanta wannan ayar:

“Kuma ka ce, “gaskiya ta zo, kuma qarya ta lalace..” (17:81)

 Da kuma:

“Ka ce, “gaskiya ta zo, kuma qarya ba ta iya fara (kome) kuma ba ta iya mayarwa” (34:49) (SB:4287).

 Bayan wannan kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya qi shiga cikin xakin Ka’aba ya ce, sai an yo waje da gaba xayan gumakan da ke ciki. Kamar yadda xan Abbas Allah ya yarda da su ya ce: “Da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya iso, sai ya cije; ya qi shiga cikin xakin Ka’aba tunda akwai gumaka a cikinsa. Ya yi umurni da a fitar da su, Sannan ya shiga” (SB:1601).

 Haka kuma a lokacin da Allah Ta’ala Ya saukar da ayar nan da ke cewa:

“Ya ku waxanda suka yi imani! Abin sani kawai, mushrikai najasa ne, saboda haka kada su kusanci masallaci mai alfarma bayan shekararsu wannan.: (9:28).

 Saukar wannan aya ke da wuya, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan karon ma, bai yi wata-wata ba; nan da nan ya umurci wakilinsa Abubakar Allah ya yarda da shi da ya shelanta wannan saqo na Allah Subhanahu Wa Ta’ala a birnin Makka cewa, kada duk wani mai shirka ya sake zuwa Aikin Hajji daga wannan shekara ta tara. (SB:369/SM:1347/SN:2958).

 A irin wannan lokaci na Aikin Hajji ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke daxa tabbatar wa duniya da cewa ya raba gari da mushrikai. Ya kan yi haka ne ta hanyar sava masu a cikin gaba xayan ayyukan Hajji, tare da gudanar da su a kan tafarkin Annabi Ibrahim Alaihis Salam. Wannan al’amari ya kai mashafar turare a lokacin da ya faxa wa mutane cewa: “Koyarwarmu ta sava wa koyarwarsu” (SB:5/125/MH:2/403) Haka kuma wannan bara’a da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa mushrikai ta qara tabbata da fitowa fili, a lokacin da ya shelanta yin bankwana da duk wani aiki da ke da alaqa da su. Ya faxi haka ne a huxubar da ya yi a filin Arafat, cewa: “Ku saurara, daga yau na kashe maganar duk wani abu na Jahiliyya; kuma duk jinainan da aka zubar da rayukan da aka kashe a zamanin jahiliyyah to, kada a sake maganarsu. Jini na farko da za a qyale kuwa shine na xan’uwanmu xan Rabi’ata xan harisu, wanda qabilar Huzailu ta kashe ana renonsa a bani Sa’ad. To, na kashe wannan magana. Haka duk wani bashi na riba da ake bi, a jahiliyyah, na kashe maganarsa. Kuma zan soma da ribar gidanmu ta baffana Abbas xan Abdul Muxxalib, ita ma wannan magana na kashe ta kwata-kwata” (SM:1218).

 Haka kuma wannan raba tafiya da mushrikai ya daxa fitowa fili, a lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana wa musulmi kasancewar addinin da ya zo da shi, da na annabawan da suka gabace shi xaya ne. Wanda kuma ya yi ban hannun makaho da abin da mushrikai suke a kai. Ya yi haka ne ta hanyar aika xan Mirba’u Allah ya yarda da shi zuwa ga mutane, a lokacin da suke tsayuwar Arafa, cewa ya gaya masu: “Ku tsaya a kan abin da muka karantar da ku na Aikin Hajji, haka Annabi Ibrahimu ya yi” (SIM:3011/SA:2438).

 Daga nan kuma sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qara daddale wannan saqo a zukatan musulmi, ta hanyar bayyana masu daxaxxe kuma ingantaccen tarihin da suke da shi a cikin wannan ibada ta Hajji, wadda suka gada daga Annabawa kuma shugabanni masu kaxaita Allah. Ya kuwa yi haka ne ta hanyar labarta masu wani yanki na Hajjin wasu daga cikin Annabawan, a lokuta daban-daban. Misali, wani lokaci a cikin Aikin Hajjinsa Sallallahu Alaihi Wasallama yana tare da sahabbai, sai suka shige ta wani kware da ake kira “Wadil-Azraq”. Sai ya tambaye su: “Wane kware ne wannan?” Suka karva masa da cewa: “Wannan kwaren Azraqu ne. “Sai ya ce: “Kamar ina ganin annabi Musa Alaihis Salam a nan sadda ya gangaro daga dutsen nan yana xaga muryarsa zuwa ga Allah, yana “Talbiyyah”.

 Daga nan kuma suka iso wurin dutsen Harsha, sai ya sake tambayarsu: “Wane dutse ne wannan?” suka amsa masa da cewa: “Dutsen Harsha ne”. Sai ya ce: “Kamar ina ganin annabi Yunusa xan Matta Alaihis Salam a kan wata taguwa ja mai qiba-qiba, yana sanye da jabbar gashin raqumi. Yana riqe da akalar taguwarsa. Shi ma kamar ga shi nan ina ganinsa yana talbiyyah (SM:166).

 A wani wurin kuma Sallallahu Alaihi Wasallama yake cewa: “Ina rantsuwa da Sarkin da rayuwata take hannunsa, ko annabi Isah xan maryamu kaxan ya rage ya yi harama da Hajji ko Umra daga Fajjur-Rauhan, ko ya haxa su baki xaya (Qirani) (SM:1252). Haka kuma an riwaito cewa Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Akwai qabarin annabi saba’in a cikin masallacin khaif”. (MK:13525/MZB:813/MZH:3/297/DA:4020).

 A taqaice dai, abubuwan da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sava wa mushrikai a cikinsu a Aikin Hajji suna da yawa. Ga wasu daga cikinsu:

 i) Kaxaita Allah da Ibada:

 A duk lokacin da mushrikai ke gudanar da Aikin Hajjinsu irin na Jahiliyyah, sukan yi wani abu mai kama da talbiyyah, inda suke haxa Allah da gumakansu (shirka) suna cewa bayan sun sheda Allah ba ya da abokin tarayya: “---Sai fa abokin nan da kake da shi. Wanda kuma shi da abin da ya mallaka duk naka ne”. Shi kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ya zo nasa Aikin Hajjin sai ya kaxaita Allah da wannan ibada. Ya yi watsi da shirka bayan bayansa (SM:1185).

 ii) Tsayuwar Arafat:

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya zavi tsayawa a Arafat tare da mutane. Savanin abin da kafiran Quraishawa suka al’adanta na tsayawa a Muzdalifa, suna cewa: Mu ba mu gangarowa sai daga Harami (domin ita Arafat a wajen Haramin Makka ta ke). (SB:1665/SM:1219).

 iii) Tsayawa a Arafat Har Faxuwar Rana:

 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya baro Arafat ne bayan faxuwar rana, ya kuma bar Muszdalifa kafin hudowarta. Savanin abin da mushrikai suka al’adanta na baro Arafat kafin faxuwar rana da barin Muzdalifa bayan ta fito (Su kam Quraishawa mun faxi cewa, ko Arafat xin ba su isa). Kamar yadda hadisin Miswaru xan Makhramata Allah ya yarda da shi ya tabbatar, da ya ce: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi mana huxuba a Arafat. Ya yi yabo ga Allah bayan ya gode masa, Sannan ya ce: “Bayan haka, Mushrikai, ma’abuta bautar gumaka sukan bar wannan wuri kafin rana ta gama faxuwa, a daidai lokacin da take kasancewa a kan duwatsu kamar rawunna a kanun mazaje. To koyarwarmu ta sava wa tasu. Sannan kuma sun kasance suna barin Mash’arul – Harami yayin da rana take hudowa a kan duwatsu kamar an naxa rawunna a kanun mazaje. To koyarwarmu ta sava wa tasu” (SB:5/125/MH:2/304/MK:20/24).

 Haka kuma hadisin Amru xan Maimun ya tabbatar da haka, inda ya ce: “Mun yi Aikin Hajji tare da Umaru xan Haxxabi. Da lokacin da ya kamata mu bar Muzdalifa ya yi, sai ya ce: “Haqiqa mushrikai sun kasance suna cewa, rana ta haska dutsen Sabiru sai mu gaggauta. Wato ba su barin wurin nan sai rana ta hudo. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sava masu, ya bar wurin kafin ranar ta hudo”. (SB:1684/SIM:3022).

 iv) Aikin Umra A Lokacin Hajji:

 Bayan qare Aikin Hajji sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi iznin yin Umra ga Sayyida aisha Allah ya qara mata yarda, savanin abin da mushrikai suka saba da shi. Su a wurinsu Aikin Umra ba ya halalta sai cikin watan Safar kamar yadda xan Abbas Allah ya yarda da su ya ce: “Wallahi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai bada damar yin Umra ga Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ba, a cikin watan Zul-Hajji sai don ya kai qarshen abin da mushrikai suka saba da shi. Domin kuwa Quraishawan wannan yanki, da waxanda ke irin addininsu, na cewa: “Aikin Umra ba ya halalta sai lokacin da gashin raqumma ya tose, miyakun da ke kuturinsu suka warke, kuma watan Safar ya kama; su kan ce, Aikin Umra haramun ne kafin watan Zul-Hajji da Muharram su yi bankwana.” (SAD:1987/HA:175).

v) Raya Wuraren Shirka Da Tauhidi:

 Wata hanya kuma da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kan bi don tabbatar da sava wa mushrikai a lokacin Aikin Hajji ita ce Raya Wuraren shirkarsu don ya turmuza hancin maqiya Allah.

 Ya kan yi haka ne ta biyar wuraren da suka tava kafa tutar kafirci da qiyayya ga Allah da Manzonsa, har ta filfila, ya maye gurbinta da tutar Musulunci. A kan wannan tafarki ne ya ce a Mina: “Gobe za mu sauka a khaifu ta bani kinanata. Wurin da suka sha Billahillazin kafirci (Yana nufin wurin da ake kira al-Muhassab) A wurin ne Quraishawa da Bani kinanata suka haxe wa ‘yan gidan Hashimu kai (dangin Manzon Allah) a kan cewa: Ba za su sake aure daga cikinsu ba ko ciniki da su, har sai sun miqa masu ni (Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama) (SB:1590) Amma kuma Allah bai cika masu wannan guri ba; sai Ya mayar masu da baqar anniyarsu. Suka koma suna tavavvi. Allah Ya taimaki Annabinsa Sallallahu Alaihi Wasallama Ya kuma xaukaka kalmarsa, Ya qara qarfafa addininsa”.

 Malam Ibnul–Qayyim na cewa: “Wannan dama ita ce al’adarsa Sallallahu Alaihi Wasallama, ya maye gurbin duhun shirka da hasken Tauhidi. Kamar yadda ya umurci a gina masallacin Xa’ifa a daidai gurbin Lata da Uzza” (ZM:2/194-195/SN:4/408).

 Wannan sunnah ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta sava wa mushrikai a cikin ayyukan Hajji ba ta taqaita a kansa ba kawai, har ma sahabbansa yake umurta da haka, a lokutan da abin ya sha kansa. Kamar yadda ya umurci waxanda ba Quraishawa ba da yin ihrami savanin yadda Quraishawa kan yi. Wato su a wurinsu ba a xawafi sai da tufafin Quraishawa, don haka wanda ba Baquraishe ba ko dai ya ari tufafi daga wurinsu, ko ya xauka haya, ko kuma ya yi xawafinsa tsirara. Sai Manzon Allah ya canza wannan baki xaya (FB:3/565).

 Saboda a sava wa wannan bidi’a, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa a yi shela wa mutane a shekara ta tara bayan hijira cewa: “Lokacin Aikin Hajji ya kama. Amma kada wanda ya sake yin xawafi tsirara” (SB:1622) haka kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci wasu daga cikin sahabbansa da ba su zo da niyyar Hajjin Tamattu’i ba, su yi Umrarsu da Hajjinsu savanin yadda mushrikai suka al’adanta. Domin su a wurinsu yin Aikin Umra a cikin watannin Hajji shi ne fajirci mafi girma (SB:7230). Haka kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci Ansaru Allah ya yarda da su da yin sa’ayi tsakaninn Safa da Marwa, inda ya ce: “Kuyi Sa’ayi don haqiqa Allah Ya wajabta Sa’ayi a kanku” (SIKH:2764). Wannan kuwa (Sa’ayi) ya sava wa abin da mushrikai suka al-adanta a zamanin jahiliyyah, na qin yin sa’ayin don suna ganin bai halalta ba. Rashin tafiyar ma a tsakanin Safa da Marwa wata ibada ce da suke fatar samun kusanci ga gumakansu da ita. Kamar yadda Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ta bayyana wa Urwatu xan Zubairu, a lokacin da ya ce mata: “Ina jin da zan qi yin sa’ayi a tsakanin Safa da Marwa babu wani laifi a kai na”. Ta ce masa: “Don me ka ce haka?” yace, don Allah Buwayayyen Sarki Ya ce: “Lalle ne Safa da Marwa suna daga wuraren ibadar Allah, to, wanda ya yi Hajjin xaki ko kuwa ya yi Umra, to babu laifi a kansa ga ya yi xawafi (Sa’ayi) a gare su” (S:158) Sai ta ce: “Da Allah na nufin yadda kake nufin nan, da cewa zai yi: “Babu laifi a kansa idan bai yi xawafi gare su ba”. Ka sani wannan aya ta sauka ne a kan wasu mutane daga cikin Ansaru waxanda kan fara Hajjinsu a kan Manata. Amma ba ya halatta gare su su yi sa’ayi tsakanin Safa da Marwa.

 To a lokacin da suka zo don gudanar da Aikin Hajji tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai suka faxa masa haka, sai Allah Ta’ala Ya saukar da wannan aya. To ka sani, wallahi Allah ba zai cika Hajjin duk wanda bai yi sa’ayi tsakanin Safa da Marwa ba” (SB:1643/SM:1277).

 Saboda ire-iren waxannan abubuwa ne ma, Malam Ibnul-Qayyim Rahimahullahu ke cewa: “Shari’ar Musulunci ta ginu ne, musamman Aikin Hajji a kan manufar sava wa mushrikai”. (HIQ:5/146).

  1.3.1 Hannunka Mai Sanda:

 Da Wannan matashiya muke bushara, wata bayan wata ga duk wanda ya yi qoqarin kwaikwayon Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin wannan maxaukakiyar koyarwa. Ya rinqa yin kaffa –kaffa da faxawa cikin wani abu na addinin mushrikai. Ba a lokacin Aikin Hajji kawai ba a’a, a cikin rayuwarsa baki xaya. Ta hanyar nisantar duk wani abu da ya kevance su. Domin kuwa; “Duk wanda ya yi kama da mutane to yana daga cikinsu” (SAD:4031/S,HA:3401) Kuma: “Mutum na tashi ranar alqiyama tare da wanda yake so” (MH:3/19/SB:6169/3688).

  1.4 Zuba, fadanci da Addu’a:

 Wata hanya kuma da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke qara inganta alaqar da ke tsakaninsa da Ubangijinsa a lokacin Aikin Hajji, ita ce yawan zuba gaban Allah da yin fadanci da addu’a zuwa gare shi.

 Roqon Allah abu ne mai matuqar girma da muhimmanci. Domin ana yin sa ne ta hanyar qanqan da kai matuqa, da nuna tsananin buqata zuwa ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala tare da marairaice masa. (F.B:11/98) Saboda waxannan martabobi ne da addu’a ta tara Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana cewa ba wani abu ne tantagaryar ibada ba illa addu’a. inda ya ce: “Addu’a ita ce ibada” (JT:2969/SA:1590).

 Wato yana nufin addu’a ita ce rukuni mafi girma da xaukaka cikin abubuwan da suka haxu suka qarvi sunan “Ibada”. Saboda a cikinta ne, ita addu’a, ake tsananin komawa da fuskantar Allah Subhanahu Wa Ta’ala tare da mantawa da kau da kai daga duk wanda ba shi ba (TA:9/220/AM:4/352) Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayar da labarin cewa: “Babu wani abu da ke da girma a wurin Allah kamar addu’a” (SIH:870).

 To a lokacin Aikin Hajji fa ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke ware gaba ya yi babbar kandama daga cikin wannan kogi na fadanci a wurin Allah Subhanahu Wa Ta’ala. Ta hanyar yawan roqon Allah Ubangijinsa a lokacin xawafi (SAD:1892/HA:1666) da lokacin tsayuwa a kan dutsen Safa da na Marwa. Babu ma inda yake tsawaita du’a’i da zuba gaban Allah kamar Ranar Arafa. A nan ne ya kan bayyana firgice a kan taguwarsa xage da hannayensa dai dai da qirjinsa, kamar yadda musaki yake yi idan yana baran abinci. Haka kuma a Muzdalifa, a Mash’arul – Harami, ya kan tsawaita fadanci da qanqan da kai ga Allah, tun daga lokacin da ya yi sallar safiya a lokacinta na farko, har zuwa gari ya waye tangaram, kafin rana ta fito. (SM:1218). Haka kuma ya kan fuskanci alqibla, a tsawon kwanaki uku bayan ranar sallah, bayan qare jifa biyu na farko, ya yi tsaye, tsayi kuwa mai tsawon gaske yana addu’a da hannayensa xage a sama. (SB:1751) Malam Ibnul-Qayyim ya ce: “Annabi ya kan daxe a tsaye a irin wannan lokaci, gwargwadon yadda mai karatun Surar Baqara har ya qare zai yi” (ZM:2/285). Vangaren abin da ya shafi roqon Allah kenan, kamar yadda riwayoyi suka zo da shi.

 Fuskar abin da ya shafi tsabar yabo kuma da ambato (Zikiri) zuwa ga Allah, ba a ko maganarsa. Babu wani lokaci, daidai da minti xaya da harshen Manzon Allah ya motsa ba tare da ya ambaci Allah ya kuma yi yabo gare shi ba. Wannan kuwa tun daga lokacin da ya baro garin Madina har zuwa lokacin da ya koma mata; bayan qare Aikin Hajjin. Annabi kan zuba wannan yabo ne ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba qyaqqyautawa ta hanyar zaven nagartattun kalmomi na kambamawa da ciccivawa, waxanda suka dace da zatin Allah mai alfarma. Ya gabatar da su zuwa gare shi Subhanahu Wa Ta’ala a cikin Sigar Talbiyyah (Faxar Labbaikallahumma Labbaika) da kabbara (Faxar Allahu Akbar) da tasbihi (Faxar Subhanallahi) da Tauhidi (Faxar La’ilaha Illallahu), a cikin ko wane irin hali yake; bisa wata dabba ko yana tafiya da qafafunsa da sauran rayuwarsa ta lokacin Aikin Hajji gaba xaya. Duk wanda ya bi diddigin yadda Sallallahu Alaihi Wasallama ya gudanar da Aikin Hajjinsa zai tabbatar da haka.

 (SB:1544/1550,1750,1751,1797/SM:1218/JT:3585/HA:2837).

 A nan yana da matuqar muhimmanci musulmi mu san cewa kaxan ne daga cikin sigogin addu’o’in da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi wa kwanakin Aikin Hajji ado da su masu riwaya suka riwaito. Domin kuwa irin wannan yawan zuba da yabo da fadanci, a kan gudanar da su ne a asirce tsakanin bawa da Ubangijinsa. Kuma kowa ya kan yi ne gwargwadon buqatarsa. Sai dai Manzon ya bayyana wani abu daga ciki don al’ummarsa ta yi koyi da shi. Kamar yadda Jabir Allah ya yarda da shi ya ba mu labari a cikin wani hadisi nasa cewa,: “Daga nan kuma sai Sallallahu Alaihi Wasallama ya karanta:

“Kuma ku riqi wurin sallah daga maqamu Ibrahim” (2:125)

Ya kuma xaga muryarsa sosai don mutane su ji.” (SN:2961/SA:2771)

 Wannan koyarwa ta Almusxafa Sallallahu Alaihi Wasallama na tabbatar da cewa, babu wani abu da ke da muhimmanci a lokacin Aikin Hajji kamar ambaton Allah Subhanahu Wa Ta’ala kamar yadda ake iya tsinkayo haka a cikin ayoyin alqur’ani da ke cewa;

“To, idan kun qare ayyukan Hajji; sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubannenku, ko kuwa mafi tsanani ga ambato. To, daga cikin mutane akwai wanda ke cewa, “Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya! kuma ba ya da wani rabo a lahira. Kuma daga cikinsu akwai wanda yake cewa; “Ya Ubangijinmu! Ka ba mu mai kyau a duniya da mai kyau a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta. Waxannan suna da rabo daga abin da suka sana’anta; kuma Allah Mai gaggawar sakamako ne. Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanukka qididdigaggu…” (2:200-203).

A wani wurin kuma Ya ce:

“Domin Su halarci abubuwan amfani a gare su, kuma su ambaci sunan Allah a cikin ‘yan kwanuka sanannu; saboda abin da Ya azurta su da shi daga dabbobin jin daxi.” (22:28).

Kai! Da za a bugi qirji a ce, an shar’anta ayyukan Hajji ne gaba xaya don kawai hakan ta zama wata wasila ta tuna Allah, da anbatonsa, ba a yi kuskure ba. Saboda hadisin Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda wanda ta karvo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: “Haqiqa an shar’anta yin xawafi ga xakin Ka’aba ne, da sa’ayi tsakanin Safa da Marwa da Jifa, don tabbatar da tuna Allah Subhanahu Wa Ta’ala da ambatonsa (JT:902/MH:1/459/JS:2589/ HAD:1505/ DA:2056) Haka kuma hadisin Nusaibatu Allah ya qara mata yarda shi ma ya tabbatar da haka, inda ya ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ranar salla da ranaku uku bayanta ranaku ne na ci da sha da ambaton Allah” (SM:1141).

  1.4.1. Hannunka Mai Sanda:

 Wannan ke nan. Wani abu kuma da ya kamata a kula da shi a nan shi ne, duk adduo’i da aka riwaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci na Aikin Hajji, addu’o’i ne gama gari, wato kundumau, waxanda suka haxa ko wane musulmi, ta hanyar amfani da lamirin jam’i. Kamar cewar da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a gaban Rukunul – Yamani: “Ya Ubangijinmu ka sa mu yi kyakkyawan rayuwa a duniya haka kuma a lahira. Ka kuma tsare mu daga azabar wauta” (SAD:1892/NA:1666).

 Ke nan mutum ba zai yi muwafaqa da sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba, a wannan fage sai ya yawaita zuba tare da qanqan da kai da fadanci ga Allah, tare da bayyana tsananin buqatuwa zuwa gare shi, da kuma narkewa a gabansa ta hanyar mayar da zikirin sa nunfashi da buxe gaba xayan qofofin zuciya dominsa, da kuma yin addu’o’i masu xauke da lamirin jam’i da kuma suke haxa duniya da lahira. Ba kuma tare da vata lokaci ba a kan abin da ba ya da wani amfani, ko kuma yin roqon cikin siga maras nagarta (TIK: 1/559).

 1.5 Fushi Saboda Allah:

Yin fushi saboda Allah Ta’ala, tare da tsayawa nesa ga iyakokinsa shi ne ke nuna inganci da nagartar imanin bawa, da cikar sa wanda ya karva sunan “Bawan Allah”.

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa gaba xayan mutane fintinkau a fagen tsoron Allah da yin fushi saboda shi da sanin iyakokinsa. Hakan na matuqar bayyana a rayuwarsa ta Aikin Hajji ta hanyoyi da dama, da suka haxa da:

i) Yini a Zul-Hulaifa:

Sahabban da ke tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan Aikin Hajji na sauraren ya jagorance su bayan qare sallar Subahin, su bar Zul-hulaifa. Sai kawai ya ci gaba da zama a wurin, ya kuma jira sauran mahajjatan da ke son shiga cikin tawagarsa.

 Abin ya ba sahabbai mamaki. Ba su sani ba ashe, Ubangijinsa ne Mai girma da xaukaka Ya umurce shi da haka. Kamar yadda hadisin xan Abbas Allah ya yarda da su ke tabbatarwa, da ya ce: “Na ji Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa a kwaren Aqiqu: “Wani manzo ya zo wurina a daren jiya daga wurin Ubangijina ya ce mani: ‘Ka yi salla a wannan kware mai albarka ka kuma ce: Hajji ne tare da Umra.” (SB:1534).

Wannan lamari ya faru ne, a zance mafi karvuwa, bayan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tashi daga Madina ranar asabar, bayan da ya sallaci azahar a Madinar (raka’a huxu) kuma bai bar Zul-huhaifa xin ba sai ranar lahadi, bayan da ya sallaci azahar (raka’a biyu) (SN:4/315-218/ZM:2/102-106) Wannan shi ne abin da tarihi ya tabbatar.

Malam ibnu Kathir ya ce: “Wannan tarihi na nuna cewa waccan salla ta gaba, da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, an umurce shi da tsayawa har ya sallata, ita ce sallar azahar ta ranar Lahadi. Domin ko banza saqon a cikin dare ya zo masa ranar assabar. Shi kuma ya labarta wa sahabbansa bayan sallar Subahin ta ranar lahadi. Ka ga batun wata salla gabansu a lokacin sai ta azaharin ranar. Sai aka umurce shi tsayawa har ya sallace ta a wurin” (SN:4/222).

 Ko shakka babu qarfin imani kawai ke sa a shanye irin wahalar da ke cikin irin wannan jira, a irin wannan wuri. Musamman ga wanda ke da dubban mutane irin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Amma wannan bai hana shi biyar umurnin Ubangijinsa ba Subhanahu Wa Ta’ala.

 ii) Qara wa Sahabbai haske:

Saurarawar da wasu sahabbai suka yi bayan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurce su da aje Haraminsu da komawa ga rayuwarsu ta yau da kullum su xauki Aikin Hajjin da suka zo yi matsayin Umra tun da suna cikin waxanda Allah bai sa suka zo da dabbobin hadaya ba ta xan sosa ransa.

Shi kam, tunda da dabbar hadayarsa a hannu ta ke Sallallahu Alaihi Wasallama bai aje haramin ba. Ganin haka sai waxannan sahabbai suka xauka cewa, umurnin nasa ba ya nufin wajabci. Sai dai yana gaya masu ne hakan ta halalta da za su yi. Har aka sami wani daga cikinsu na bayyana wannan fahimta tasu, tare da dalilinsu na zavar ci gaba da zama da Haramin a xaure, yana mai cewa: “Bamu son mu halarci Arafa da sauran janaba a jikinmu!”. Nan take sai fushin Manzon Allah ya bayyana, saboda an yi jinkirin yin biyayya ga umurninsa, har kuma ma da kafa wata hujja, alhali kuma shi Manzon Allah ne.

Yana tashi a fusace bai tsaya ko’ina ba sai wurin Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda. Ganinsa cikin wannan hali, sai ta ce: “Wa ya tava ka ya Manzon Allah? Ko waye, shi da Allah” Sai ya karva mata da cewa: “Ba ki ji yadda nake fama da mutane ba. Ina ba su umurni, suna kokwanto? Da na fuskanci baya ba zan zo da hadaya ba. Sai in aje Haramina tare da su” (SM;1211).

Daga nan kuma bai tsaya wata-wata ba sai ya juya, ya tsaya wurin da mutanen suke ya qara masu haske da cewa: Dukanku kun san na fi ku tsoron Allah da gaskiya da biyayya. Ba don da hadayata a hannu ba wallahi da na aje Harami yadda ya kamata ku aje. Saboda haka kowannenku ya je ya aje Haraminsa” (SB:7367/SM:1216).

Nan da nan sai suka miqa wuya, suka yi kamar yadda Ya ce.

ii) Safiyya Allah ya qara mata yarda Za Ta Kawo Jinkiri

A qoqarin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na bayyana rashin jin daxinsa idan ba a dace da umurnin Allah ba, a cikin wani aiki na Hajji, sayyida Safiyya Allah ya yarda da ita ta yi wanki daren ranar rabon layya. Ranar da alhazzai za su bar Mina zuwa Makka. Aka kuma yi sa’a cewa uwar muminan ta rigaya ta gabatar da xawafi (na ifala) tun a ranar salla. To da Almusxafa Sallallahu Alaihi Wasallama ya ji cewa, mai xakinsa tana wanki sai ransa ya sosu har ya ce, “Shin Safiyya za ta tsayar da mu ne?” (SB;1772).

Ka kuwa san hana dubban mahajjata motsawa a irin wannan hali abu ne mai matuqar wuya. Amma dai Allah ya kiyaye. Hakan ba ta faru ba. Amma mu duba jinqayin Manzon Allah da kulawarsa ga iyalansa da sauran al’ummarsa. Sallallahu Alaihi Wasallama.

 1.5.1 Hannunka Mai Sanda:

A kan haka, yana da kyau ga ko wane musulmi ya kasance mai koyi da Shugaban halitta Sallallahu Alaihi Wasallama ta hanyar kasancewa daga cikin waxanda ke fushi idan an yi wa Allah ba daidai ba, tare da nisantar iyakokinsa, da tsayawa kan umurninsa; ba tare da savawa ba. Domin sava masa tafarki ne na faxawa cikin fitina da halaka kamar yadda Maxaukakin Sarkin da Ya ce:

“To waxanda suke savawa daga umurninsa, su yi saunar wata fitina ta same su, ko kuwa wata azaba mai raxaxi ta same su”. (24:63).

 Duk wanda ke son tsira, to ya yi koyi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Ya kuma bi umurninsa, kamar yadda yake cewa: “Duk abin da na hane ku da shi, ku nisance shi. Abin da kuma na umurce ku da shi, ku zo da shi gwargwadon ikonku. Ku sani abin da ya halakar da waxanda suka zo gabanku, shi ne yawan tambayoyinsu da sava wa annabawansu” (SB:7288/SM:1337).

 Ya kuma saurari gargaxi nan da gogaggen sahabin nan masani, wato Abdullahi xan Mas’udu Allah ya yarda da shi ya yi wa musulmi, da kunnuwan basira. Inda ya ce: “Idan ka ji Allah Ya ce: “Ya ku waxanda suka yi imani… To, ka kasa kunnuwanka da kyau, domin alheri ne za’a horonka da shi, ko a hane ka daga wani sharri” (SSM:848).

 To muna kira ga musulmi, kada su yi biris da wannan faxakarwa. Domin kuwa hakan na kai mutun ga tavewa da rashin arziqi.

 1.6 Tsoron Allah da Natsuwa:

 Ana iya fahimtar kamalar zuciyar mutum, da ma’aunin abinda ke cikinta na tsoron Allah, ta hanyar la’akari da natsuwa da tsanakin gavvan jikinsa. Domin kuwa da ma labarin zuciya a kan tambayi fuska ne kamar yadda masu hikima suka ce (FB:2/264).

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya haxa tsoron Allah tare da natsuwa a lokacin Aikin Hajjinsa. Ko da yaushe hankalinsa yana gare shi, lizzamin zuciyarsa na cikin tafin hannunsa. Bai tava shagalta ba daga abin da yake yi na ibada (Hajji); yana nan zube gaban Ubangijinsa, zuciyarsa na kuka, idanunsa na ambaliyar hawaye, qassansa sun yi sanyi yana fadanci. Tare da tsananta tsayuwa da xaukaka hannayensa zuwa sama a daidai lokacin. (SB:1751/SM:1218).

 Nassosa da dama, na tabbatar da haka, da suka haxa da, maganar Jabiru Allah ya yarda da shi in da yake siffanta yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke xawafi, da cewa: “Sai ya fara da Hajarul Aswad, ya sumbance shi, idanunsa su ka vare da hawaye. Sannan ya yi sassaka sau uku, ya kuma yi tattaki sau huxu. Har dai ya qare. Bayan kuma ya qaren, ya sake dawowa ya sunbaci hajaru xin, ya xora hannayensa a kansa, ya shafi fuskarsa da su” (SKB:5/47/SN;4/317).

 Haka kuma abin da Salimu xan umar Allah ya yarda da su ya riwaito, na tabbatar da haka, cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan jefi jamra ta farko. Sannan ya xan saurara. Sai kuma ya miqe tsaye na lokaci mai tsawo, yana fuskantar alqibla. A nan ne zai yi du’a’i hannayensa na xage a sama. Sannan ya matsa ya jefi Jamrar tsakiya. Sai kuma ya xan karkata hagu kaxan dabra da wani kware da ke wurin. Ya xaga hannayensa sama, yana fuskance da alqibla yana addu’a. Sannan ya matsa ya jefi Jamra ta qarshe, daga cikin kwaren. Ba zai tsaya a nan ba. Kuma xan umar Allah ya yarda da su xin haka yake aikatawa, tare kuma da kafa hujja da cewa: “Haka na ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na yi” (SB:1751,1753/ZM:2/286).

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance a duk tsawon wannan ibada ta Hajji cikin natsuwar gavvai. Duk Aikin da zai gudanar yana gudanar da shi ne cikin natsuwa da tsanaki. Jabiru Allah ya yarda da shi na cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sauko cikin natsuwa” (SN:3024/SA:2827) kuma falalu xan Abbas Allah ya yarda da su na cewa: “Lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sauko ya kasance cikin natsuwa, har ya iso Muzdalifa” (M.A:1816) haka kuma Abdullahi xan Abbas Allah ya yarda da su na cewa: “Mun tausa tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ranar Arafa. Sai (Annabi) ya ji wata irin yaya, da amon dukan raqumi masu tsanani. Sai ya nuna su da sandarsa ya ce: “Ya ku mutane ina horonku da natsuwa, ku sani ba gaggawa ce xa’a ba’ (SB:1617/FB:3/522).

  1.6.1 Hannunka Mai Sanda:

 Abin da ya kyautu ga ko wane musulmi, musamman wanda ya sami kansa a qasa mai tsarki don gudanar da ibadar Aikin Hajji shi ne riqo da koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Ta hanyar xaura gyafton natsuwa da yafa mayafin tsanaki da gudanar da ibadarsa cikin ruwan sanyi da barin ibadar ta kama jikinsa. Ta haka sai Allah ya yi masa Katangar dutse tsakaninsa da kowa ce irin varna.

 Yana kuma da matuqar kyau, mutum ya riqi Aikin Hajjinsa wani abin jin daxi da nishaxi da samun natsuwa a zuci. Ta hanyar nisantatr xabi’ar mutanen jahiliyyah. Waxanda ke ganin nawar su qare Aikin Hajjinsu, don ya zamar masu qargage, suna Aikin, bugawar zuciyarsu na cewa: “Ya Ubangiji ka raba mu da wannan baqar jaraba. Maimakon a sami suna cewa: Allah ya maimata mana”.

 1.7 Yawaita Ayyukan Alkhairi:

 Allah maxaukkain Sarki Ya kwadaitar da bayinsa a kan riqon “Taqawa” a matsayin guzurinsu na zuwa lahira. Kuma kar su yarda su yi raggon kaya a fagen ayyukan alheri, balle su zama kurar baya. Mai duka Ya ce:

“Kuma ku yi guzuri. To mafi alherin guzuri shi ne yin taqawa. Kuma ku bi Ni da taqawa, ya ma‘abuta hankula”(2:197).

A wata ayar kuma Ya ce:

“Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga wurin Ubangijinku da wata Aljanna wadda faxinta (dai-dai) da sammai da qasa ne. An yi tattalinta domin masu taqawa” (3:133).

 Da wannan umurni ne na Allah Subhanahu Wa Ta’ala Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tsare yawaita Ayyukan alheri a lokacin Aikin Hajji, kamar yadda ya saba. Wani abun ban sha’awa ma, duk bai fi kasancewarsa Sallallahu Alaihi Wasallama ba, a mafi yawan lokuta shi ke gudanar da waxannan ayyukka na alheri da kansa ba ya waqilta kowa. Sun kuma haxa da:

 i) Kula Da Aikata Mustahabban Hajji:

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya himmatu qwarai da gaske, tare da bayar da cikakkiyar kulawa da mustahabban Hajji, ta hanyar aikata su a matsayinsu na ayyukan alheri.

 Mun ji irin yadda ya fara gabatar da wanka kafin ya xaura Harami Sallallahu Alaihi Wasallama (JT:830/SA:664). Ya kuma shafa turare mafi qanshi a farkon ibadar da qarshenta (SB:1539) Ya kuma tsallake shafin tozon hadayarsa na dama, tare da rataya mata takalma a wuya (SB:1544,1697). Haka kuma ya tsare talbiyya har zuwa lokacin da ya yi jifa ta qarshe (SB:1544,1573/SM;11840). Ya kuma fara yin xawafi ga xakin Ka’aba (SB:1615) tare da yin sassaka a cikin shuxi uku na farkonsa (SB:616) Ya kuma rungumi Rukunai guda biyu (SB:1699/ SM:1218/ MA:4686) Sannan ya yi nafila raka’a biyu bayan muqamu Ibrahim (JT:856/SA:679) Ya kuma yi xawafi tsakanin Safa da Marwa tare da yin Sauri mai tsanani a tsakiyar kwaren (SM:1218,1261). Ya kan kuma ambaci Allah a lokacin da yake rungumar Rukunai guda biyu, ko jifa (SB:1751/SM:1218). Da kuma wasu sunnoni da mustahabbai da dama.

ii) Saurarawa A Muzdalifa:

 Wani aikin kuma na laheri da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a wannan lokaci, shi ne saurarawa a Muzdalifa, ba tare da ya baro ta ba, har gari ya waye tangaram, amma rana ba ta kai ga fitowa ba. Tattare da kuwa, da zai baro ta, ya sauko kafin wannan lokaci, bai sava ba. Amma ya tsaya don tausaya wa masu rauni daga cikin tawagarsa (SB:1680/SM:123).

 iii) Yawaita Dabbobin Hadaya (Raquma Xari):

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yanka raquma xari a matsayin hadaya, tattare da cewa kashi xaya bisa bakwai na raquma xaya ko saniya ko wata ‘yar qaramar dabba ta isar masa. (SB:1718;1688/ HW:139/ZM:2/221).

 Wani abin da ya kamata a yi la’akari da shi a nan shi ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya gudanar da gaba xayan ayyukan Hajji ne da kansa, ba tare da ya wakilta wani ba. Ko da kuwa aikin, irin wanda wani ke iya isar ma wani ne. Sai fa idan ba makawa ga yin hakan. Misali, ya wakilta Sayyidina Ali Allah ya yarda da shi ya soke sauran raquman hadayarsa, bayan ya soke sittin da uku da hannunsa mai alfarma (SIM:3074/SA:2494). Duk da yake cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya rava Sayyidina Alin ne a cikin hadayar; wato su biyu ke da ita (SB:2506/SM:1218). Ka ga bisa wannan, babu wakilci kenan.

 Amma kuma muna fatar a lura. Wannan magana ba ta haxa da amfani da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi da wasu sahabbai ba, a matsayin masu hidima da agaji, suka gudanar da wasu abubuwa na Hajjin a madadinsa. Kamar: Tsattage tozayen dabbobin hadaya (SIM:2609) da kafa masa tanti a Namrata (SM:1218) da tsinto masa tsakwankwani a Muzdalifa (SIM:3029/SA:2455) da kula da dabbarsa ta hawa (SA:27290/MZ:3/261) da wasu abubuwa masu kama da wannan. Dalili kuwa shi ne gaba xayan waxannan ayyuka ko dai su kasance ba cikin jerin ayyukan ibadar Hajji ba ko kuma da ma ba ayyukansa ne na kai tsaye ba.

 A taqaice, duk wanda ya kalli Aikin Hajjin manzo Sallallahu Alaihi Wasallama da kyau, zai ga irin yadda yake yin tsaye tsayin alif ya gudanar da ko wace ibada a cikin siga mafi cika da kamala. Da zaven ayyukan da aka bayyana cewa su ne mafifita, ya fita batun masu matsakaiciya ko qanqanuwar daraja. Sai fa inda abin ya gagari kundila, wata maslaha ta kunno kai. Nan kam ba yadda zai yi. Sai ya sha yadda aka dama. Kamar yadda ya yi xawafi ga xakin Ka’aba da sa’ayi tsakanin Safa da Marwa yana kan dabba, bisa lalura (SB:1608/MA:3492,14/415). Haka kuma ya sumbanci hajarul Aswadi da sanda (SB:1715/SM:1218/AN:1/347) saboda irin yadda mutane suka rufe shi. Shi kuma yana farin ciki da haka. Musamman don su sami damar yin fatawa gare shi da xaukar karatu da koyon Aikin Hajji.

  1.7.1 Hannunka Mai Sanda:

 Da wannan muke kira ga ko wane mahajjaci, da ya sha xamarar gwagwarmaya don ganin ya yi zara a lokacin Aikin Hajji, a fagen ayyukan alheri, da yawaita neman kusanta ga Allah. Domin yana cikin wasu kwanaki mafiya alheri a cikin kwanakin duniya.

 Lokacin Aikin Hajji, lokaci ne na nuna tsoron Allah da biyayya gare shi, da fadanci da ambaton shi Subhanahu Wa Ta’ala. Babu wani abu daga cikin ayyukan bayi a irin wannan lokaci, da ma wanda ba shi ba, da ke isa wurin sa Subhanahu Wa Ta’ala baya ga “taqawa” (22:37). Ba kuma siffar jikin mutum yake la’akari da ita ba ko dukiyarsa. Ko alama, yana la’akari ne da tsarkin zuciya da nagartar ayyuka (SM;2564).

 Saboda haka yana da matuqar kyau Alhaji, ya zare dantse, ya tsaya tsayin daka; ba da wata kasala ko ragganci ba, ya ribanci waxannan kwanuka. Domin wata qila, ba zai sake samun damar dawowa ba. Kuma ya tuna a nan duniya ake aiki, Lahira kuwa sai hisabi. Duk wanda ya yi aiki na qwarai ya tsira ya kuma samu babban rabo. Wanda kuma ya yi kwance da siddi, ya miqa kafa, ya shiga uku ya lalace. Kuma ya sani Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda bai tavuka wa kansa wani abu ba, dangantakarsa ba za ta cece shi ba’ (SM:2699).

  1.8 Bugi sa Bugi Taiki:

 Mafificin al’amari duk, shi ne wanda aka yi sese – sese, wato tsaka-tsaka a cikinsa. Duk wanda ya kwasa ya tausa gabas mai nisa, ya fita batun yamma. Ko ya kwasa ya tausa yamma mai nisa ya fita batun gabas, bai kyauta ba, matuqar gaba xayan nahiyoyin na da buqata da shi. Ko shi yana da buqata da su. Kuma wannan shi ne abin da nagartacciyar Shari’a; ta musulunci ta zo da shi. Saboda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “Ina horonku da shiriya matsakaiciya (har sau uku) domin kuwa duk wanda ya yi wa addini kwasar karan mahaukacciya, sai ya niqe shi”. (MA:19786).

 A Lokacin Aikin Hajji, Almusdafa Sallallahu Alaihi Wasallama na tsananin bayyana kyaukyawar xabi’ar nan tasa, ta daidaito, da guje wa kasawa ko wuce wuri, ta hanyar karkata ga wani vangare da qyale wani. A nan, za mu yi magana ne a kan wasu abubuwa guda biyu da suka shafi rayuwarsa Sallallahu Alaihi Wasallama tsakaninsa da Ubangijinsa a wannan lokaci.

 i) Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallama) Da Alaqar da ke Tsakaninsa da Al’ummarsa da Kuma Ubangijinsa:

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya raba qafa, ta hanyar dagewa a kan kula da alaqar da ke tsakaninsa da Ubangijinsa; bai bari wannan alaqa ta yi rauni ba ko kaxan. Hasali ma kullum sai daxa bunqasa ta yake yi (SB:1715/SM:1218). A lokaci xaya kuma, bai manta da al’ummarsa ba ko iyalinsa. tsaye yake haiqan a kan karantar da su al’amurran addini da na duniya. Musamman abin da ya shafi Aikin Hajji. Tare kuma da ba da kyakkyawan misali. Haka kuma yana tsare da haqqoqan matansa, ta fusakar kula, takalifi, da bayar da kariya. Da kuma nuna so da qauna ga sauran iyalin gidansa Sallallahu Alaihi Wasallama (SB:305,1556/SM:1218).

 ii) Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallama) Da Alaqar da ke Tsakaninsa da Ruhinsa da Kuma Gangar Jikinsa:

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci da yanayi na kaxawar iskar imani da tsoron Allah ya kai qololuwar mataki. Wanda hakan kan sa mutane da yawa saka wa Ruhinsu da gangar jikinsu rigunan Bora da Mowa, ta hanyar karkata da mayar da hankali ga xaya, tare da yin ko oho da xaya. Shi kam Sallallahu Alaihi Wasallama ya daidaita kafaxunsu ne, ta hanyar ba wa ko wane daga cikinsu cikakken haqqinsa, ba tare da kasawa ko wuce wuri ba.

 Ta tabbata cewa hawan da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ranar takwas ga watan Hajji, zuwa Mina, ya kusanci Arafa, na da alaqa da tsananin kular da yake da ita, da haqqin gangar jikinsa (SAD:1911/ SA:1682/ SM:3004,3074/ SA:2433,2494). Domin hakan zata ba shi damar yin bacci a daren Arafa. Kamar kuma yadda ya yi a daren Muzdalifa (SM:1218) ya kuma ci abinci ranar Arafa (SB :1658) ya kuma fake wa rana a cikin wata bukka da aka kafa masa tun kafin wannan rana (SM;1218). Haka kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya sarara daga sallolin nafilar da ya kan yi kafin magariba da Isha’i da bayansu, a wannan dare, ya nemi wuri ya yi kwanciya abinsa (SB:1673/ZM:2/247).

 Haka kuma ta tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya hau kan taguwarsa daidai lokacin da yake kai wa da komowa tsakanin “Masha’ir”, wuraren ibadar Hajji (SB;1666/SM:1218) da kuma daidai lokacin da yake gudanar da wasu ibadodi na Hajji, kamar: xawafi, Sa’ayi, da Jifar Jamra. (SB;1607/SM:1283,12970 Haka kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya nemi hadimi, don rage masa ayyuka (SM:1313/ MA:27290). Ba kuwa don komai ba, sai kawai don ya ba jikinsa haqqinsa. Ta yadda zai qarfafa, har ya lamunce ma gudanar da manya-manyan abubuwa na ibada, da suka haxa da kamar du’a’i da fadanci a wurin Allah a cikin cikakkiyar Sifa. Da gudanar da sauran Ayyukan Hajji cikin cikakakkiyar natsuwa da sadaukar da zuciya, da qanqantar da kai da zubewa gaban Buwayayyen Sarki duk, idan ya isa waxannan manya-manyan wurare Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Wataqila, babban abin da ke iya tabbatarwa tare da qara fitowa fili da, irin wannan adalci, daidaito da bugi sa bugi taiki da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi tsakanin haqqin ruhi da na gangar jikinsa a wannan lokaci, shi ne hadisin ummul Hussain Allah ya yarda da ita da ta ce: “Na yi Aikin Hajji tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin Hajjinsa na bankwana. Sai na gan shi, a daidai lokacin da yake jifar Jamrar qarshe. Da ya qare kuma da Bilalu da Usamatu Allah ya yarda da su xayansu na janye da lizzamin taguwar, xaya kuma ya na yi masa lema daga zafin rana, da tufafinsa. Ta ce; sai Manzon Allah ya yi jawabi mai yawa. Har aka kai inda na ji yana cewa; “Da Allah zai sa wani bawa, baqar fata kuma mai qirarrun gavovi ya Shugabance ku, to ku saurare shi, ku kuma yi masa xa’a matuqar yana jagorancin ku ne da littafen Allah Ta’ala” (SM;1298).

 Wannan baiwar Allah ta riwaito abubuwa da dama, daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a kan abin da ya shafi: Jifa, da gudanar da wasu ibadu a kan taguwa, da fake wa rana, da tafiya cikin natsuwa, da hidimar da wasu sahabbai suka riqa yi masa Allah ya yarda da su da kuma wa’azi da gargaxi da ya yi tsaye ga yi wa mutane a lokacin.

  1.8.1 Hannunka Mai Sanda:

 da wannan muke kira ga duk musulmi da ke son haqarsa ta cimma ruwa, musamman a cikin ibadar Hajji, da cewa lalle ne ya qanqame sunnar ma’aiki ba ji ba gani. Ya kuma tuna da tunatarwar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi masa, da duk wanda ke tare da shi a kan wannan tafarki na musulunci, cewa: “Haqiqa addini abu ne mai sauqi. Babu kuma wanda zai xauke shi da zafi face ya niqa shi. Saboda haka ku dai sassauta, amma kuma kar ku rafashe. Tabbas kuna tare da nasara. Amma ku riqa rage wa al’amurra kaifi ta hanyar yin su tun da sassafe, ko da maraice, ko da dare (yana nufin muyi aiki a lokacin da muke da kuzarin yin sa) (SB:39).

 Ka sani yin biris da wannan koyarwa ta Almusxafa Sallallahu Alaihi Wasallama halaka ne. Kuma ya tabbaatar maka da haka tare da yi maka hannunka mai sanda Sallallahu Alaihi Wasallama inda ya ce ma ka: “Duk wanda ya qyamaci sunnata, ba ni ba shi” (SB:5023). Duk abin da za ka yi na addini, to ka yi shi tsaka – tsaka; ba tare da ka kallafa wa kanka abin da Allah bai kallafa maka ba. Ka zama mai tsakaitawa da daidaitawa. Domin ta haka ne kawai zaka sa ranka sha’awa da kwaxayin bautar Allah Ta’ala. Domin kuwa: “ duk dabbar da aka xora wa abin da ya fi qarfinta na kaya, to ba ta isa wurin da ake so, kuma qashin bayanta zai tashi aiki” (SI:3885/KKH:2339).

  1.9 Gudun Duniya:

 Zuciyar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ko da yaushe cike take fal da bege da shauqin Ubangijinsa Mai girma da Xaukaka. A sakamakon haka duk wani abu da ba ya da amfani a lahira, to, ba ya cikin lissafinsa balle ya yi hidima akan sa. A guje yake har kullum a kan qafafunsa, da nufin yi wa duniya fintinkau, ba kuwa don ta buwaye shi tarawa ba. A duk lokacin da ta shigo hannunsa, ba zai yi wata – wata ba Sallallahu Alaihi Wasallama zai rabe ta ne wa bayin Allah ta fuskoki daban – daban. Ba tare da ya ajiye wani abu don kansa ko iyalinsa ba, wai don gobe. Wani mai hikima ya siffanta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa: “Shi ne wanda ya fi kowa gudun duniya daga cikin mutane” (MA:17773).

 Yanayi da Sigogin yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa duniya adabo, na da matuqar yawa da qayatarwa. Amma daga cikinsu akwai:

a) Roqon Allah:

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance a tsawon rayuwarsa ya kan roqi Allah Ubangijinsa agaji da tsari daga tara abin duniya, da cewa: Ya Ubangiji! ka wadata Muhammadu da danginsa da abin da za su ci kawai" (SB: 6460) A wata riwaya kuma cewa yake yi: "Ya Ubangiji! ka sa arziqin Muhammadu da danginsa na rufin asiri kawai" (SM: 1055)

b) Haquri

 Wata hanyar kuma da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan bi ya guje ma duniya, ita ce ta haquri. Da yawa Sallallahu Alaihi Wasallama kan shafe tsawon wuni lahe da cikinsa, yunwa na cinsa babu kuma yadda zai yi don ba ya da ko qwayar dabino da zai jefa ciki. Kamar yadda Umar Allah ya yarda da shi ya ce: "Haqiqa na ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama lahe da ciki saboda yunwa, tsawon wuni ba tare da ya sami wani xan busasshen dabino da zai jefa ciki ba" (SM: 2978/B/127)

 Haka kuma, saboda tsananin haquri da al'amarin duniya, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kan kwashe tsawon kwanaki uku da 'yar wainar alkama a ciki, wadda da ita da rashin ta banbancinsu kaxan ne. Kamar yadda hadisin Aisha Allah ya qara mata yarda ke tabbatarwa, da ta ce: "Har Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wafati babu lokacin da aka jera kwana uku shi da iyalansa na cin wainar alkama har su qoshi" (SM: 2970) A wata riwaya kuma aka ce, cewa ta yi: "Babu lokacin da iyalin gidan Muhammadu suka jera kwana uku suna cin wainar alkama da miya har su qoshi" (SB: 4538).

 Haka kuma a lokacin Aikin Hajji ta bayyana iyakar zarafi cewa dai, hankalin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya karkata ne ga al'amarin lahira. Domin kuwa abin da aka ji yana furtawa a lokacin da ya tsaya a Arafa shi ne: "Mun karva kiranka ya Ubangiji, mun karva, mun kuma sakankance da cewa sakamakon alherin da za a samu a lahira shi ne alheri na haqiqa" (SIKH: 2831/HA: 5058) ko "Mun karva kira, haqiqa rayuwar lahira ita ce rayuwa" (MIAS: 3/2/44/SU: 5/45)

Bayan wannan kuma, waxanda suka shedi Aikin Hajji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sun bayyana sigogi da yanaye-yanayen gudun duniyarsa a wannan lokaci, ta fuskoki da dama, da qididdige su ba zai yiwu ba. Amma dai mafi fitowa fili daga cikin su sun haxa da cewa:

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gudanar da Aikin Hajjinsa a kan wani abin hawa da wata ‘yar shimfixa a kansa da farashinta bai kai dirhami huxu ba. Ko kuma iyakarsa ke nan (SIM: 2890/SA: 3337). Malam Ibnul Qayyim ya tabbatar da wannan magana da cewa: Hajjin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance a kan wani sirdi qeqasasshe da babu wasu shimfixu ko kilisai ko dardumai a kan sa" (SM: 2/169)

Haka kuma aminin Manzon Allah, Ibnu Umar Allah ya yarda da shi ya tuna irin wannan hali na gudun duniya da manzon ya gudanar da Hajji a cikinsa, bayan shekaru masu yawa, a daidai lokacin da wasu mutane daga Yaman suka yo ayari don gudanar da Aikin Hajji suka kuma shuxe ta gaban sa, sai ya kalli siriddan raqumansu, ya gan su huntaye qeqasasshi. Kuma akalolinsu na wani bussashen gashin raquma ne da aka tufqa. Sai ya kayar da baki ya ce: "Duk wanda ke son ya ga ayarin da suka fi ko wane ayari bana, yin kama da ayarin Manzon Allah da sahabbansa, a lokacin da suka zo Hajjin bankana, to ya kalli wannan ayari" (SAD: 4144/SIA: 3491/MA: 6061/AM: 10/117/MM: 1/167).

Haka kuma, wani abin da ke tabbatar da gudun duniyarsa Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne rashin damuwa, da zowa wannan ibada a kan taguwar nan tasa, da ke jefa qafa. Wadda kuma yake xaukar kaya da guzurinsa a kanta, bai damu da sai ya hau raqumin alfarma ba kamar yadda hadisin Sumamatu ke cewa: "Anas ya zo Aikin Hajji a kan raquma. Kuma bai kasance marowaci ba. Ya kuma bayar da labarin cewa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo shi ma, Aikin Hajji a kan taguwar nan tasa da ke jefa qafa" (SB: 1517/ HA: 2373/ SIM: 2933).

Haka kuma an riwaito cewa, saboda tsananin rashin xaukar duniya wani abu har Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya goya Usamatu xan Zaidu Allah ya yarda da shi a kan wannan taguwa tasa daga Arafa zuwa Muzdalifa. Ya kuma goya Falalu xan Abbas Allah ya yarda da su daga Muzdalifa zuwa Mina (SB: 1544)

Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava banbanta kansa da sauran mutane a cikin wani abu ba a wannan lokacin na Aikin Hajji. Babban abin da ke tabbatar da wannan shi ne riwayar da ke cewa: " Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo wurin masu shayar da alhazai ruwa, ya nemi a ba shi shi ma ya sha. Sai Abbas, saboda girmamawa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce da Falalu: Tafi wurin Mahaifiyarka ka samo wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wani ruwa ya sha" Sai Manzo ya ce: “Ku dai ba ni wannan” sai Abbas xin ya karva masa da cewa: "Ya Manzon Allah wannan fa mutane na saka hannayensu a ciki. Annabi dai ya nace ya na mai cewa: “Ba komai. Ku dai ba ni shi a haka, na sha". To haka kuwa aka yi. (SB: 1636) A wata riwaya kuma aka ce, da aka ce masa: A'a ya Manzon Allah bari mu sa a kawo maka wani ruwa na musamman daga gida. Sai ya ce: "Ba ni da buqata da shi, Ku dai ba ni wannan da mutane ke sha" (MA: 1814).

Wani abin kuma, shi ne raquma xari da ya yi hadaya da su Sallallahu Alaihi Wasallama (SB: 1718). Ka sani duk wanda ke son duniya, ba zai iya fitar da fiye da abinda aka wajabta masa ya bayar sadaqa ba.

Wani abin kuma da ke tabbatar da irin wannan karamci na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci, shi ne yanka dabbobin layya bayan ya yi waccan qasaitacciyar hadaya (SM: 3180/HW: 123,301--) tattare da cewa, idan mahajjaci ya yi hadaya, ba dole ne akansa ya yi layya ba.

Bayan wannan kuma ya yi sadaqa da su, ta hanyar ciyar da su ranar takwas ga watan Hajji. Inda ya sa hannunsa mai albarka ya soke raquma bakwai, ba tare da ya zauna don ya huta ba (SB: 1551) duk kuma ya yi sadaka da su bayan kuma ya umurci Sayyidina Ali Allah ya yarda da shi da ya rarrabe raquman nan xari da ya yi hadaya da su, a ranar salla, gaba xaya. Duk ya rabe wa musakai bai rage komai ba daga ciki. (SM: 1317)

Haka kuma an riwaito cewa wata sadaqar ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ke raba wa mutane da hannunsa, ba ya sa kowa. Domin kuwa an gan shi a ranar salla ya nufi wani xan garken dabbobi. Ya kuma ci gaba da hidimar rabonsa (SM: 3/30). Yana cikin haka sai ga wasu samari su biyu sun kawo jiki suka kuma nemi ya raba da su, sai ya xago fuskarsa Sallallahu Alaihi Wasallama ya kuma mayar da ita, da yake ya fahimci cewa su, majiya qarfi ne. Sai ya ce masu: "In dai kuna so ina iya baku. Amma ku sani duk wanda ya kasance mawadaci ko majiyi qarfi da ke iya nema wa kansa, to ba ya da rabo a cikinta" (SAD: 1633/SA: 1438).

Haka kuma daga cikin abin da ke bayyana mana cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai xauki duniya bakin komai ba akwai tawali’un da ya nuna a lokacin da ya yanke dabbarsa ta layya, a Hajjinsa na bankwana, sai ya ce wa Saubanu: "Gyara naman nan" Saubanu ya ce: "Sai na gyara naman. Annabi kuwa bai gushe ba yana cinsa har ya isa Madina" A wata riwaya kuma ya ce: "Ban gushe ba ina xebo masa shi yana ci har ya isa Madina" (SM: 1973)

 1.9.1 Hannunka Mai Sanda:

Wannan ya ishi duk mai hankali gane cewa duniya da qawace-qawacenta abun gudu ne. Kuma ba ya kamata ga duk musulmi ya yarda ya zama xan duniya balle bawanta. Domin ita gida ce na qasqanci da wulaqanci. Kuma gishirin roqo ce, ana cikin kaxi yake qarewa.

Duniya "Gida ce ga wanda ba ya da gida, kuma dukiya ce ga wanda ba ya da dukiya, kuma babu mai tara ta sai marar hankali. (MA: 24464| MZ: 10 | 288 | 51: 10637). Wannan ko shakka babu haka yake. Domin inda duniya gidan arziki ce, to da kuwa Allah Ta’ala ya zavar wa masoyansa kuma zavavvu daga cikin halittarsa.

Saboda haka xan’uwa kada ka amince ma ta. Kuma kaji tsoron jin daxinta. Don fitina ne kawai. Kuma nan take ta ke gushewa.

 To, yanzu kam dai alhamdu lillahi. Ga shi mun tsakuro maka wani sashe na sigogi da yanaye-yanayen da za su haska maka, yadda alaqar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta kasance tsakaninsa da Ubangijinsa a lokacin Hajji. A ciki ka ga yadda Sallallahu Alaihi Wasallama yake zubewa da qan-qan da kai ga Ubangijinsa, tattare da irin xinbin ayyukan da ke gaban sa a wannan lokaci.

 To tunda kuwa har Allah cikin ikonsa Ya sa yau ga wannan dama a hannunka, ta kusanta ga Ubangiji, saboda samun kanka da ka yi a cikin wannan yanayi, wanda cikinsa da wajensa ayyukan xa’a ga Allah ne, wato Aikin Hajji, ga ka ga xakin Allah. Kuma kana da laifuka a wurinsa. Waxanda ka yi ta hanyar kasawa a cikin wasu ayyuka na wajibi, da yin ko-oho da wasu wajiban, tare da kasala a fagen xa’a. Ka daxe kana yin yadda kake so. Kamar dai yadda wata faxa ta Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa: "Ko wane xan Adamu mai kuskure ne. Amma mafi alheri daga cikin masu kuskure su ne masu tuba" (SIM: 4251)

 To a nan, kamata ya yi ka yi koyi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama don ka zama daga cikin zavavvun bayinsa. Hakan kuwa na iya tabbata ne idan ka zare dantse ka cika wannan lokaci da kake ciki da bauta ga Ubangijin har Ya ga kana gaggawa da son tsere wa takwarorinka a fagen neman yardarsa, da nisantar sava masa, nan take zai kusantar da kai zuwa gare shi. Ya sa ka cikin layin masoya kuma yardaddun bayi a wurinsa. Har kuma qarshe ka zama xaya daga cikin waxanda ya kewaye da tsarinsa. Kamar yadda faxarsa Sallallahu Alaihi Wasallama ke tabbatarwa, a cikin hadisin nan da ya karvo daga ubangijinsa cewa: “Babu wani abu da bawa zai sami kusanta zuwa gare ni ta hanyarsa kamar abin da na farlanta a kansa. Kuma bawana ba zai gushe ba yana nafiloli, har a wayi gari na so shi. Idan kuwa na so shi, to zan zama ganinsa, wanda yake gani da shi. Da Hannunsa, wanda yake xauka da shi. Da qafarsa wadda yake tafiya da ita. Idan kuma ya roqe Ni tabbas zan ba shi. Idan kuma ya nemi tsari tabbas zan tsare shi” (SB: 6502)

  

 BABI NA BIYU

 2.0 Rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Tsakaninsa Da Al’ummarsa A Lokacin Aikin Hajji

 Wannan Babi kuma, zai qunshi bayani ne a kan yadda rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta kasance tsakaninsa da al’ummarsa a wannan lokaci na Aikin Hajji. Hakan zata kasance ne ta hanyar biyar diddigin yadda ya rinqa qoqarin kyautatawa da inganta alaqa tsakaninsa da sahabbansa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai saki al’ummarsa ba, ga igiyar ruwa. Ya kula da su matuqa, ta hanyar karantar da su, yi masu wa’azi da gargaxi da kuma haquri da su da zamar masu kyakkyawan abin koyi da sauransu.

 2.0.1 Shimfixa

 Akwai mamaki matuqa ganin irin yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci na Aikin Hajji ya sanya rigar malami mai karantarwa, ya kuma yi tsaye kamar haure yana yi wa al’ummarsa darasi tare kuma da yi masu jagora duk a lokaci xaya. Kuma babu wani abu da zai gabatarwa gare su ta waxannan vangarori biyu, face ya kasance abu ne mafifici kuma gangariya. Irin wanda, da za a buqaci mutum a matsayinsa na xan kallo, da ya maimaita shi, ko shakka babu ba zai iya ba.

 Amma kuma a dunqule, gaba xaya waxannan abubuwa na daxa fitowa ne da irin girman daraja da xaukaka, waxanda ya kevanta da su Sallallahu Alaihi Wasallama. Abubuwan kuwa sun haxa da:

 2.1 Karantarwa

 Asalatan, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya aiko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne domin ya kasance “Mai karantarwa ga mutane tare da sawwaqe masu al’amurra” (SM: 1478). Ya kuwa kai magaryar tuqewa ga karva wannan suna. Kamar yadda gwanin zana hoto cikin bayani ya siffanta shi da cewa: “Ban tava ganin wani malami kafin Manzon Allah, ko bayansa ba, da ya fi shi naqaltar asirin karantarwa” (SM: 537).

 Ko shakka babu, duk wanda ya yi wa Hajjin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kallon tsaf, zai tabbatar da gaskiyar wannan magana ta Mu’awiyya xan Hakamu Al-Sulami Allah ya yarda da shi. Domin kuwa kafin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kama hanyarsa ta zuwa Aikin Hajji, sai da ya sa aka yi shela cewa, to ga shi fa ya yi azamar fita. Ya kuwa yi haka ne domin duk mai shirin tafiya ya kimtsa.

 Wannan kuma bai isa ba. Bayan ya fita daga Madina Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya yada zango a Zul hulaifa don jiran waxanda ba su shirya ba (SB: 1551). Da haka sai mutane masu ximbin yawa suka yi ta tururuwa zuwa garin Madina. Suna zarcewa wurinsa ba wata qyaqqyaftawa, da nufin ya jagorance su ga wannan Ibada, suna biye da sawunsa a cikin komai (sad: 1905/sa:1676) da haka sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sami haxuwa da mutane daban-daban, ya jagorance su tsawon kwanakin Aikin Hajji (SM: 1187,1218,1278). Ga su ga shi, ba wanda ake kora ko tsangwama, ko wani abu mai kama da haka (SM: 1274/MA: 2842) balle a nisanta shi daga gare shi (SM: 3035/SA: 2461).

 A tsawon wannan lokaci, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi matuqar qoqari, da kwaxayin ganin ya isar da gaba xayan saqon da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya aiko shi da shi ta wannan fuska. Domin yana ji a jikinsa cewa, wataqila wannan ita ce babbar haxuwa ta qarshe da zai yi al’ummarsa. Saboda ya yi amfani da wannan dama a matsayin hujja a kan kowa. Ta hanyar jawo hankalin su da zaburar da su, tare da sa masu sha’awar sauraren duk abin da zai faxa masu. Yana yi yana canza salo wajen gabatar da jawabi, yana kuma amfani da wasu hanyoyi na karantarwa, don kada su qosa. Ya kuma umurce su da su dubi irin yadda yake gudunar da ibadodin Hajji. Don abu ne mai yiwuwa matuqa rai ya yi halinsa kafin baxi (SM: 1297)

 Wani abu kuma ma, da zai qara tabbatar maka da cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai xauki wannan al’amari da wasa ba ko kaxan, shi ne tanadin wani mutum da ya yi na musamman, wanda zai riqa hana mutane magana ko wata sumuiniya a lokacin da yake bayar da karatu (SM: 3024/SA: 2450) kamar yadda Jarir Allah ya yarda da shi ke cewa a cikin wani hadisi: “Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce mani, a lokacin Hajjinsa na bankwana: “Hana mutane magana ka umurce su da su saurara”. Sannan sai Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masu: “Kada ku kuskura ku koma kafirai, sashenku na saran wuyan sashe bayan na cika” (SB: 121). Haka kuma a wani hadisin, Bilal Allah ya yarda da shi ya ce: "Annabi ya ce mani, a ranar da aka taru: 'Ya kai Bilal gaya wa mutane kowa ya saurara, a yi shiru.." (SIM: 3024/SA: 2450).

 Wani abin kuma da ke tabbatar da muhimancin wannan al'amari a idon Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne, neman mutane su sheda cewa ya isar da saqon Allah zuwa gare su. Domin da yawa zaka ji idan ya qare magana da su ya dasa aya, sai ya ce: "Ko na isar da saqon?". Sai mutane su karva gaba xaya: 'Mun sheda ka isar da saqo ya Manzon Allah. Ka kuma xaure shi da igiyar arziki gindin magarya" (SB: 1741/ MA: 20695/ SM:1218)

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai tsaya nan ba, saboda tsananin son da yake yi, na ganin duk abin da zai faxa na saqon Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya isa kunnensu, sai bai wadata da tasa muryar kaxai ba, a lokacin da yake yi wa mutane huxuba a Arafat Sallallahu Alaihi Wasallama sai da ya umurci Rabi'atu xan Umayyah da ya tsaya bayansa, yana xaga murya sosai qwarai yana maimaita duk abin da ya faxi Sallallahu Alaihi Wasallama don mutanen da ke nesa su ji (SN:4/42). Haka kuma har wayau, a Arafat xin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi amfani da wani mutum, shi ma da ke isar da wasu saqonnin daga gare shi zuwa ga mutane (SA: 1949/SA:1717). A Minna kuma ya sa Ali Allah ya yarda da shi yana maimaita wa mutane abin da ya faxa. A lokacin duk wurin ya cika maqil da mutane, wasu na zaune, wasu na tsaye (SAD: 1956/SA:1723).

 Bayan haka kuma, a nan Minna, da can Arafat, ya kan zavi wasu mutane, ya tura su wuraren da alhazzai ke zazzaune. Su isar da wasu saqonnnin gare su, daga gare shi Sallallahu Alaihi Wasallama (JT: 883/SA: 700/MA: 10664/IKH: 2960).

 Haka kuma an riwaito cewa, da yawa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan sa raha a cikin karantarwarsa a wannan lokaci. Kamar yadda hadisin xan Abbas Allah ya yarda da su ke tabbatarwa, wanda ya ce: "Mun sami Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama mu ‘yan yaran gidan Abdul Muxxalabi, muna a kan raqumanmu. Sai ya zazzagaya mu, yana daddafa qafafunmu yana cewa: 'ya’yana kada dai ku jefi Jamrah sai rana ta hudo" (SIM: 3025/SA: 2451).

 Haka kuma wannan karantarwa ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ta taqaita ga lafiyayyu da manyan mutane ba kawai, ko alama. Ya karantar da har marasa lafiya, ya kuma samar wa masu rauni mafita. Misalin wannan shi ne cewar da ya yi wa Dhuba’atu Allah ya yarda da ita: "Ba komai, kina iya Aikin Hajjin. Amma ki sharxanta wadatuwa da in da kika tsaya idan rashin lafiyar ta tsananta (SM:1207). Ya gaya mata haka ne a lokacin da ta koka masa cewa: "Ya Manzon Allah, ga shi ina son in yi Aikin Hajji, amma ba ni da cikkakkiyar lafiya". Haka kuma Ummu Salmah Allah ya yarda da ita, ita ma ta koka masa rashin lafiya. Sai ya ce mata: "kina iya yin xawafi a bayan mutane, kuma kina kan wani abu". Kamar kuma yadda aka riwaito cewa ya ce wa mata da raunana, su tafi tun cikin dare. (SB:464/ 1679/SN: 3034/HA: 2840)

 Kai! Karantarwa ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci, ta haxa har da matasa da qananan yara. Domin ta tabbata cewa xan Abbas Allah ya yarda da su na bisa abin hawansa ranar jifar Aqabah, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurce shi ya sauka ya tsinto masa tsakuwa. Xan Abbas ya ce: "Sai kuwa na tsinto masa tsakuwa daidai jifa, da na bashi sai ya saka su a hannunsa, ya kuma rinqa faxar kwatankwacin waxannan" (SNI: 3059/SA: 2865). Haka kuma cewar da ya yi wa matasan Banu Abdil Muxxalabi: "Kada dai ku yi jifa sai rana ta fito" (SAD: 1940/SA:1710) ita ma ta tabbatar da haka.

 Haka kuma wannan karantarwa tasa Sallallahu Alaihi Wasallama ba ta tsaya ga zuba ilimi kawai ba. A’a, har bayani ya kan yi a kan matsayin wasu ayyuka. Kamar yadda ya bayyana hikimar da ke cikin shar’anta wasu ibadu na Aikin Hajji, da cewa: "Haqiqa an ce ne a yi xawafi wa xakin Ka’aba, a kuma yi sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, a kuma jefi shexan, don a tuna Allah" (SAd: 1777/JT: 902/TJU: 1505)

 Wata hanya kuma, da wani salo da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi amfani da su a wajen karantarwarsa ga al'ummarsa, don ya qara masu qwarin guiwa, su ne bayyana masu martabobi da darajojin wasu ayyuka, da kuma falalar da suke qunshe da ita. Misalin wannan shi ne, gaya masu da ya yi cewa: "Mafi alherin du’a’i shi ne wanda ake yi a ranar Arafa. Kuma mafificin abin da ni da annabawan da suka gabace ni, muka faxa a wannan wurin a matsayin addu'a shi ne: La Ilaha Illal-Lahu Wahdahu La Sharika Lahu, Lahul Mulku Walahul Hamdu, Wa Huwa Ala kulli Shai’in Qadir (JT: 3585/HA: 2837) da kuma cewar da ya yi:" Shafar Hajarul Aswad da Rukunul Yamani na shafe zunubbai shafewa" (SIKH: 2729/SIH: 3698) da kuma cewar da ya yi: "Duk wanda ya yi xawafi ga xakin Ka’aba ya kuma yi sallah raka’a biyu, Allah zai ba shi lada kamar ta wanda ya 'yanta bawa" (SIM: 2956/SA: 2393) Haka kuma an tambaye shi cewa: "wane Hajji ne mafi karvuwa a wani Allah? Sai ya karva da cewa: "Shi ne wanda aka cika shi da talbiyyah, aka kuma yanka hadaya" (JT: 827/SA: 661)

 Wannan ke nan. An kuma riwaito cewa wani Ba'ansare ya tambayi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a Mina ya gaya masa falalar da ke cikin wasu ayyuka na Hajji sai Sallallahu Alaihi Wasallama ya karva masa da cewa: "Fitowarka daga gidanka don ka ziyarci xakin Allah, Allah zai rubuta maka lada, Ya kuma shafe maka zunubi xaya-xaya ko wane, daidai yawan takawar da zaka yi a Arafa. Ka sani Allah Ta'ala na saukowa zuwa sararin sama, Ya yi wa mala’iku alfahari cewa, “Waxancan bayiNa ne, sun zo daga wurare masu nisa, kuma gashin kansu ya mummurje. Jikinsu kuma ya yi qutuq-qutuq. Ba kuma don komai ba, sai kawai don suna fatar haxuwa da rahamata, suna tsoron azabata, kuma ba su tava sa Ni a ido ba. To ya kuke gani da a ce sun tava yin tozali da ni?”

 Annabi ya ci gaba da gaya masa: "Anan, da a ce zunubanka sun yi yawan Hamada, ko yawan kwanakin duniya, ko yawan abin da sama'u ke zubarwa na ruwa, Allah zai wanke su, ka koma tas. Shi kuma aske gashin kanka da za ka yi, kana da lada xaya a kan ko wane gashin da ya faxi daga gare ka. To kuma da zarar ka qarqare xawafin xakin Ka’aba, da kai da jinjirin da aka haifa yau duk xaya, ba ka da zunubi ko xaya a kanka" (MAR: 8830/MA: 2320/HA: 1360/SM:1348/JT:3585/HA: 2837)

 Kamar yadda muka faxa a baya, ba karantarwa kawai ba, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi matuqar kwaxaitar da al’ummarsa tsayawa tsayin daka ga ganin sun cika mudun ibadarsu ta Hajji. Ya kuma yi haka ne ta hanyar yi masu bushara da kyakkyawan sakamakon da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi masu tanadi, sanadiyyar wasu ayyuka da suka riga suka gudanar na ibadar. Kamar cewar da Bilal Allah ya yarda da shi ya yi "Haqiqa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce mana, a safiyar taro: "Haqiqa Allah Ya albarkaci taron nan naku, Ya kuwa yi maku baiwa ta hanyar damqa masu laifi daga cikinku a hannun masu kyautatawa daga cikinku. Ya kuma sha alwashin ba masu kyautatawar duk abin da suka roqe shi abin da duk suka roqa. Maganar ta qare sai ku zabura da qarfin Allah" (SIM: 3024/SA: 2450).

 A gaba xayan wannan lokaci, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi mayar da hankali, a cikin wannan karantarwa tasa, a kan waxansu muhimman abubuwa, da suka haxa da:

i) Hukunce-Hukuncen Aikin Hajji:

 A qoqarinsa na karantar da al’ummarsa da wayar masu da kai, a kan hukuncen-hukucen Aikin Hajji, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan haxa hancin magana ne da aiki. Bai jira ranar takwas ga watan Hajji ta kama ba, sai ya tara mutane ya yi masu huxuba, inda kuma ya bayyana masu abubuwan dake wajaba a kansu a ibadodin Hajji (MN: 1/632/SA: 4774) Sannan kuma ya jagorance su ga ko wace ibada, yana kuma tafe yana bayyana masu hukunce - hukuncenta (SM: 1218/JT: 835/H: 702/ SAD:1959/ SA: 1724)

ii) Rukunnan Musulunci:

 Haka kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya kula matuqa da Rukunnan Musulunci, ta hanyar yin bayani a kansu. Kamar cewar da ya yi a cikin wata huxaba a wannan lokaci na Hajji: "Ku ji tsoron Ubangiji, Ku kuma tsare sallolinnan guda biyar. Idan watan Ramadan ya kama kuma, ku azumce shi. Da kuma zarar lokaci ya yi, to ku fitar da zakka daga cikin dukiyoyinku. Ku kuma yi xa'a ga shugabanninku. Idan kun yi haka zaku samu shiga aljannar Ubangijiku" (JT: 616/SA: 512/MA: 15883).

iii) Yaqar Shirka da Kaba’irai:

 Sai kuma shirka, daidai da qyaftawar idaniya, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai xaga mata qafa ba a wannan lokaci. Haka kuma bai bari wasu manya-manyan haramtaccin abubuwa suka nunfasa ba, irin waxanda shari'o’i suka yi ittifaqi a kan haramacinsu. Kamar zubar da jini, tava dukiya ko mutunci. Ya yaqi gaba xayansu, inda ya ce: "ku sani haqiqa jininku da dukiyoyinku da mutuncinku tava su, haramun ne a tsakaninku, kamar yadda keta alfarmar wannan yini da wannan wata naku, a cikin kuma wannan garinku yake haramun" (SB: 67) A wata maganar kuma yace: "ku nisanci wasu abubuwa guda huxu: i)kada ku haxa Allah da wani a cikin bauta, ii)kada kuma ku kashe wata rayuwa, wadda Allah Ya haramta ba tare da wani dalili na shari'a ba, iii)kada kuma ku yi sata, iv) kuma kada ku yi zina (MA: 18989).

iv) Hukunce-Hukuncen Shari'a:

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kula da bayanin wasu hukuncen-hukuncen, da suka shafi wasu shari'o’i. Kamar bayanin da ya yi na yadda ake yi wa mai harama da Hajji wanka, idan ya rasu a lokacin, da kuma yadda za a yi masa likkafani. Kamar yadda xan Abbas Allah ya yarda da su ya tabbatar a cikin wani hadisi, da ya ce: "Wani mutum, na tsaye a Arafa, sai kawai ya faxo daga kan abun hawansa. Dabbar kuma ta taka wuyansa, ya mutu nan take. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: "Ku yi masa wanka da ruwa da magarya. Ku kuma sa masa tufafi biyu, a matsayin likkafani. Anan kada ku shafa masa turare. Kada kuma ku rufe kansa da ani abu, domin kuwa za a tayar da shi ranar qiyama yana talbiyya" (SB: 1267).

 2.1.1 Hannunka Mai Sanda:

 Lalle wajibi ne mu yi hattara, domin an wayi gari jahilci ya yi ma wannan al'umma katutu a zuciya. Yana kaxa molaye da garayunsu, zuciya da hankulan mafi yawan matasa na kaxawa. Aka wayi gari sun manta wani yanki mai yawa na abin da suka gada na ilimi, har addini ma na nema ya rinjaye su, saboda sun jahilce shi.

 Eh, tabbas! Sun jahilici abin da bai kamata a ce sun jahilta ba, sun kuma manta abin da bai kamata a ce sun manta ba, da yawa ba su san gabas a ke fuskanta idan za a yi salla ba. Balle daxa sauran qa’idojin musulunci su ba maganarsu ake yi ba. Kai! Suna kawai yin addinin ne don sun gada. Wasu kuma don yana ba su sha'awa. Wasu kuma don kada tarihinsu ya vace. Ba don sun fahimci shi ne addini mafifici ba, balle su aiwatar da shi tare da riqo da shi yadda Allah Ya ce.

 Kuma mu sani wannan hali ne fa, ya ba shexanun duniya damar baje kolinsu da yaxa varnace-varnacensu a tsakanin jama'a. Ta hanyar gabatar da su a cikin wata siga mai yaudarar hankali, da ke sa a za ci cewa duhu haske ne, abin qi kuma ma'arufi ne. Ta haka sai qarfin varna da kuzarin yaxuwarta suka rinjayi gaskiya da shiriya.

Da wannan 'yar qwarya-qwaryar matashiya muke kira ga ma'abuta ilimi da cewa, su yi amfani da damar da suke da ita, ta haxuwa da miliyoyin mutane. Waxanda ke zuwa qasa mai tasrki ko wace shekara don gudanar da Aikin Hajji. Su yi amfani da wannan dama su karantar da al'umma tuwasun addini, da fiqihunsa da hukuncen-hukuncensa. Tare da fahimtar da su cewa ba su da wani girma wanda ya fi na kasancewarsu musulmi. Da kuma kimsa masu sha'awa da kwaxayin yaxa addinin da aiki da shi, da kare mutuncinsa.

 Ko shakka babu wannan aiki wajibi ne a kan duk wani almajiri, ba malamai kawai ba. Matuqar dai Allah Ya hore masa zalaqa da fasaha, Ya kuma kawo shi qasar Makka a irin wannan lokaci na Aikin Hajji. Haka kawai za a yi a kawar da jahilci daga cikin wannan al’umma, a taqaita yaxuwar duhunsa, a kuma share wa haskensa wurin zama.

 2.2 Bayar da Fatawa:

 Bayar da fatawa na xaya daga cikin muhimman abubuwan da rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama tsakaninsa da al'ummarsa, ta qunsa a lokacin Aikin Hajji. Ya kan yi haka ne ta hanyar wayar masu da kai a kan abubuwan ibada da suka shige masu duhu, da kuma amsa tambayoyinsu da tattaunawa a kan waxansu hasashe hasashe nasu.

 Fatawoyin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayar a wannan lokaci na Hajji suna da yawa matuqa. Amma dai ana jin mafi shahara daga cikin su sun haxa da, wadda ya ba wata mata Bakhas'ama, wadda ta ce masa: "Ya Manzon Allah, mahaifina ya tsufa matuqa kuma ga shi Allah bai sa ya xauke farillar Hajji ba. Kuma a halin yanzu abun na da wuya gare shi, domin ko raqumi ba ya iya hawa, ya za a yi? Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya karva mata da cewa: "Kina iya yin Aikin Hajji a madadinsa mana"(SM: 1335). Haka kuma amsar da yake ba duk wanda ya tambaye shi matsayin jinkirtawa ko gaggautawa da ayyukan ranar salla babba, da cewa: "Kana iya yi ba laifi" (SB: 83) na daga cikin shahararun fatawowin nasa Sallallahu Alaihi Wasallama

 Akwai abubuwa da dama da ya kamata a yi la'akari da su, dangane da fatawowin nasa Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci, da mafi bayyana daga cikin suka haxa da:

a- Fitowa fili da tsayawa don mutane su sami ganinsa har su yi masa tambayoyi a kan wasu abubuwa. Kamar yadda hadisin Jabir Allah ya yarda da shi ke tabbatarwa. Inda ya ce: "Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi xawafi ga xakin Ka’aba, a lokacin Hajji na bankwana, Yana haye da taguwarsa, Yana kuma sunbantar Hajarul Aswadi ta hanyar amfani da sandarsa. Ya kuma yi haka ne don mutane su sami ganinsa, su kuma matso suyi masa tambayoyi. Nan take kuwa sai mutane suka kewaye shi" (SM: 1273) Haka kuma Abdullahi xan Amiru na cewa a wani hadisi: "Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tsaya a Mina a lokacin Hajjinsa na bankwana, don mutane su yi masa tambayoyi…" (SB: 1736/SM: 1306) Haka kuma a wani hadisin xan Abbas Allah ya yarda da su na cewa: "Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya taka burki yana ba wa mutane fatawa" (SB: 6228)

b- Haka kuma a cikin waxannan fatawoyi da yake bayarwa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan sasauta tare da ba wa masu wasu uzurora amsoshi masu sauqi. Abubuwan da ke iya tabbatar da haka suna da yawa. Misali, hadisin Aisha Allah ya qara mata yarda inda take cewa: "Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya shiga wurin Dhuba'atu 'yar Zubairu xan Abdul Muxxalabi, sai tace Ya Manzon Allah, haqiqa ina son in yi Aikin Hajji, amma ba ni jin sosai. Ya ke Nan?” Sai ya ce mata: "Kina iya yin Aikin amma ki sharxanta taqaitawa duk inda rashin lafiyar ta rutse ki" (SM: 1207)

 Bayan wannan hadisi kuma akwai wani, mai tsawo na Jabiru Allah ya yarda da shi wanda a cikinsa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa: "Da na fuskanci in da nab a baya da ban zo da hadaya ba, na sanya Hajjina ya zama Umra. To duk wanda bai zo da abin yin hadaya ba daga cikinku, ya ajiye Haraminsa, ya mayar da Hajjinsa Umra. Sai Suraqatu xan Maliku xan Ju’ushumu ya tashi ya ce "Ya Manzon Allah, wannan rangwame bana kaxai aka yi mana shi ko har abada? Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya saqa xan yatsansa xaya cikin wani, ya ce: "Ba bana kawai ba. An halalta haxa Hajji ne da Umra har abada" (SM: 1217) ya faxa ya sake maitawa.

 Haka kuma Abdullahi xan Amru Allah ya yarda da su ya faxa a wani hadisi cewa: na ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na huxuba ranar layya. Sai wani mutun ya tashi ya ce: “Ya Manzon Allah, ni a zatona abu kaza ake yi kafin kaza. Yana qarewa kuma sai wani ya tashi shi ma ya ce: Ni ma dai Manzon Allah, na zaci sai an yi kaza ne kafin a yi kaza. Saboda haka nayi aski kafin in yi hadaya. Sai kuma da na soke hadayar tawa ne, sannan na yi jifa" Haka dai aka ta yi masa. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce "Ba komai yayi daidai " kai! babu wata tambaya da aka yi masa a wannan rana face ya karva da cewa: Ya yi daidai ba wata matsala" (SB: 1736)

 Haka kuma xan umar Allah ya yarda da su ya riwaito cewa "Abbas xan Abdul Muxxalabi ya nemi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa izini ya ci gaba da kwana a garin Makka tsawon kwanakin da ya kamata ya yi Mina, saboda shayar da alhazai ruwa da yake yi. Ya kuma yi masa izinin" (SB: 1634). Sai kuma hadisin Adiyyu Allah ya yarda da shi inda ya ce: "Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi rangwame ga masu kiwon raquma su kwana xaure da niyya: Su yi jifa ranar suka. Sannan su haxa jifar kwana biyu na bayan ranar suka, su yi su haxe cikin xayansu" (JT: 955/SA: 763)

c- Bayan wannan kuma, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance yana matuqar so da qoqarin ganin ya gamsar da wanda ya yi masa wata fatawa. Wannan ma abin lura ne.

 Misali, wani mutum ya ce masa: "Ya Manzon Allah, ko da musulunci ya bayyana mahaifina ya tsufa matuqa, ba ya iya hawan taguwarsa. Ko ina iya yin Aikin Hajji madadinsa? Sai Almustafa Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: "Eh! Me zai hana kuwa. Yanzu kana ganin da bashi ne ake bin sa idan ka biya masa bai biyatu ba?" Mutumin ya ce “tabbas ya biyatu” sai Annabi ya ce "Jeka ka yi wa mahaifinka Aikin Hajji ka ji! (MA: 1812)

d- Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mai matuqar haquri da masu yi masa tambayoyi. Yana jure wa duk wani abu da ba daidai ba da ka iya biyowa daga gare su, ta hanyar tausayawa da yi masu jinqayi a magance. Abubuwan da ke tabbatar da wannan Magana suna da yawa qwarai. Amma daga cikinsu akwai hadisin Jabir Allah ya yarda da shi mai tsawo, wanda a cikin sa yake cewa: "Sannan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya hau taguwarsa, ya tsaya da ita sosai a cikin sarari. Na duba iyakar ganina a gabansa Sallallahu Alaihi Wasallama na ga mutane gasu nan birjik, ba masoka tsintsiya damansa da hagunsa haka. Haka kuma bayansa" (SM: 1213) Amma bai tava qosawa da ko xayansu ba.

 Haka kuma xan Abbas Allah ya yarda da su ya ce a wani hadisi nasa: "Wata rana mutane suka yayyave Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama suna cewa: La! Ga Muhammadu, ga Muhammadu har sai da mata tsoffi daga cikin gidaje, su ma suka fito don su gan shi. Xan Abbas ya ce: "Ka san ba dama a kori mutane don sun taru wurin Manzon Allah, don bai yarda da haka ba. Da dai al'amarin ya yi qamari, sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya haye taguwarsa. Amma kuma dai duk da haka tafiya qasan ta fi sauqi gare shi. Don mutane ba su fasa abin da suke yi ba" (SM: 1264)

 A wata riwayar kuma Allah ya yarda da shi ya ce "Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi sa'ayi tsakanin Safa da Marwa a kan taguwarsa. Amma a sani wannan ba sunna ba ne. A'a ya yi haka ne saboda yadda za a yi mutane da ke rufe shi, don su ji abin da yake faxa, su kuma ga inda yake. Kuma ba yadda za a yi hannayensu su kai gare shi" (MA: 2842) Akwai kuma hadisin Qudamatu al Amiri Allah ya yarda da shi wanda ya ce: "Na ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya na jifar Jamra a ranar suka daga kan taguwarsa ja. Kuma ba a tsangwamar kowa daga gare shi, balle kora ko duka" (SIM: 3035/SA: 2461)

e- Haka kuma waxannan fatawowi na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sun fi kasancewa a kan abin da ya shafi Aikin Hajji. Kamar amsar da ya ba Asma'u 'yar Abubakar Allah ya yarda da su lokacin da ta haifu, a daidai kuma lokacin tana Zul-khulaifa. Sai ta aika masa, tana tambayar yadda za ta yi. Shi kuma ya ce a gaya mata cewa: "Ba komai, sai ta yi wanka ta kuma yi kirshe da wani tufa, ta xauki Harama. (SM: 1218) Akwai kuma wani lokaci da ya umarci sahabbansa Allah Ya yarda da su su aje Harami. Suka tambaye shi, "Ya Manzon Allah, wace irin ajiyewa za mu yi masa" Shi kuma ya karva masu da cewa: "Ajiyewa ta gaba xaya" (SB: 3832).

 Bayan wannan kuma, Ausu ax-Xa’i Allah ya yarda da shi ya tambayi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa: "Ya Manzon Allah, Ni na zo ne daga wurin dutsen Xayyi’u. Saboda nisansa, kafin in iso nan taguwata ta yi matuqar gajiya. Ni ma na sha baqar wuya. Domin kuwa, wallahi babu wani tudun yashi ko dutse da ban hau ba. To, yanzu shin na samu Aikin Hajji?" sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya karva masa da cewa: "Duk wanda ya halarci wannan salla tamu, ya kuma tsaya tare da mu a Arafa, har lokacin da muka bar ta. Bayan kuma ya riga ya yi wata tsayuwar a Arafa xin kafin yau ta tsawon yini da kwana. To ya kammala Hajjinsa, kuma tsaftarsa ta cika" (JT: 891/SA: 707).

f- Bayan waxannan fatawowi kuma, da suka kevanci Aikin Hajji. Ta tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayar da wasu fatawowin wa mutane a lokacin, waxanda ba su shafi Aikin na Hajji ba, amma dai qalilan ne.

 Daga cikinsu akwai abin da ya zo cikin wani hadisi na Jabiru Allah ya yarda da shi inda yake cewa, Suraqatu xan Maliku ya ce wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wani lokaci: "Ya Manzon Allah, muna so ka yi mana bayanin addininmu, kuma ka fexe mana biri har wutsiya kamar yadda za ka yi wa wanda aka haifa yau bayaninsa. Ka gaya mana matsayin abin da za mu aikata yau. Shin abu ne da har alqaluman da aka rubuta shi da su sun bushe, kuma yau da gobe sun buga masa hatimin abadiyya, ko ko yanzu ne za a buxa masa shafi a cikin kundin qaddarorin rayuwa?" sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya karva masa da cewa: "A'a abu dai ne da siffofin da ka faxa na farko suka tabbata a kansa". Sai Suraqatu ya qara da cewa: "To tunda haka ne me ye amfanin aikin da za mu yi?" Manzon Allah, ya amsa masa har wa yau da cewa: "Ku dai yi aikin, kowa Allah Yana sawwaqe masa ne abin da Ya halicce shi dominsa. " (MA: 14116)

 Sai kuma hadisin Abu Qatadata Allah ya yarda da shi wanda ya ce: "Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita don gudanar da Aikin Hajji. Mu ma kuma mun fita tare da shi don haka---" Sai Abu Qatadata ya bayar da labarin yadda ya farauci jakin daji a cikin wannan hali. Kuma har waxanda ke tare da shi suke ci naman. Alhali kuwa suna xauke da alfarmar harama da Aikin Hajji a wuyansu. Ya ci gaba da cewa: "Sai suka farga, suka ce: To ya ke nan ga shi mun ci naman da aka haramta, alhali kuma muna cikin harama da Hajji?! Sai kuma suka xauki sauran naman suka nufi wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Da isarsu, suka ce masa: Ya Manzon Allah, muna cikin harama da Hajji, amma ba da abu Qatadata ba, Sai ga garken raquman daji. Abu Qatadata kuwa ya kai masu farmaki ya kashe jakin da ke tare da su. Mu kuwa muka sami wuri muka sha gara. Sai muka farga da cewa muna fa cikin harama da Hajji ne kuma ga shi mun ci naman da aka farauta ga ma sauransa nan da muka yo guzuri" Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masu: "Akwai wani daga cikin ku, masu harama, da ya bayar da wata gudunmawa a cikin farautar naman? suka ce masa: ko alama. Sai ya ce: "To ku je ku iyar da cinye saura " (SM: 1196)

g- Wani abun kuma shi ne, a lokacin amsa tambayoyi da bayar da fatawowi, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi amfani da salo iri daban-daban, gwargwadon yanayi. A inda mafin yawa ya kan yi la'akari da mai tambayar. Sai ya ba shi amsa kai tsaye (SB: 83/MA 1812). Misalin wannan shi ne, amsar da ya ba wa yarinyar nan Bakhas’ama, wadda ta ce masa: "Ya Manzon Allah, ko da Allah Ta'ala Ya wajabta Aikin Hajji a kan bayinsa, mahaifina ya tsufa matuqa. Ko raqumi ba ya iya hawa. Ko na iya tsayawa a madadinsa? Sai ya ce : "Eh" (SB: 1513) Bai daxa ba, bai qara ba.

 Wannan ke nan. A wani lokacin kuma ya kan yi cikakken bayani. Har ma ya isar da fatawar ga sauran mutane. Kamar yadda ya zo cikin hadisin Abdurrahmani xan Ya'amar. Wanda ya ce: "Wasu mutane daga Najadu sun zo wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin yana Arafa, suka yi masa wata tambaya. Sai ya umurci wani mai shela da cewa ya gaya wa mutane: Ba komai ne Hajji ba sai tsayuwar Arafa".

h- Bayan wannan kuma, wani lokacin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi wa fatawarsa kwalliya da kwaxaitar da mai tambaya, tare da qarfafa masa guiwa a kan aikata wani aiki. Misalin wannan shi ne, amsar da ya ba wa wata mata a Rauha'u, wadda ta zo masa da wani yaro ta tambaye shi, ko akwai buqatar shi ma ya yi Hajji? Sai ya karva mata Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa: "Eh, akwai. Amma ladar taki ce" (SM: 1336)

i- Haka kuma babu wani wuri da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya keve a wannan lokaci, da sai nan ne zai karva tambayoyin mutane. Duk inda ta faxi rataya, Ya bayar da fatawa ga alhazai a Madina (SB"1736/SM: 1306). Ya bayar a Zul-khulaifa a lokacin xaukar Harami (SM: 1218). Ya bayar a Arafa (JT: 889) da Muzdalifa (JT: 891/SA: 707) da Mina (SB: 83) da kuma ma har lokacin da yake kaiwa da komowa tsakanin ibadodi da wurarensu (SM: 1273) da kuma a kan hanyarsa ta dawowa Madina (SM: 1336)

 2.21 Hannunka Mai Sanda

 Duk da yake malamai a wannan zamani namu, suna iyakar qoqarinsu wajen ganin sun maye gurbin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta wannan hauji amma da sauran rina a kaba.

 Dalili kuwa shi ne, za ka ga ximbin mutane a lokacin Aikin Hajji, suna faganniyar samun wanda zai warware masu wata matsala da ta shige masu duhu ko ya qara masu haske a kan waxansu hasashe-hasashen da suke da su a kan wasu abubuwa. Wanda a qarshe, rashin tsayayyu, wadatattu kuma ingantattun malamai, waxanda suka san harsunansu sai ya sa su faxa hannun “muna-malamai". Sai ka ji abin ba daxi, wanda ko shakka babu, duk wanda ke tsoron Allah, da fatar ganin kyautatuwar al'amarin musulmi, ya san akwai buqutar yi wa wannan al'amari gyaran fuska. Ta hanyar tanadar qwararrun malamai, da ke jin harsuna daban-daban waxanda za a rarraba wurare da kafafe daban-daban, don tambayoyin mahajjata, tare da wayar masu da kai.

 Ta wannan hanya ne kawai, za a sami nasarar jefe tsuntsu biyu da dutse xaya, kuma a lokaci xaya. Farko za a kori jahilci kora ta har abada. Na biyu kuma a kawo qarshen yamutsa hazon da waxanda ba malamai ba ke yi.

 Bayan wannan kuma, wajibi ne a wayar wa mahajjata da kansu, a kan cewa lalle ne, su san wanda za su fuskanta da matsalolinsu na addini. Dole ne su tabbatar da cancantar duk wanda za su tambaya, ta fuskar iliminsa da fahimtarsa ga addini. Su kuma san cewa, idan suka tambayi wanda bai cika waxannan siffofi ba, Allah zai caje su.

 A hannu xaya kuma yana wajaba a faxakar da mutane a nuna masu irin haxarin da ke tattare da bayar da fatawa ba tare da an qoshi da ilimi ba. Wato dole ne duk wanda zai karva tambayar addini, ya kasance ya ilmantu. Kuma ya sha fannona da dama. Domin kuwa kutsa kai cikin dajin bayar da fatawa, da xan ilimi cikin cokali, shi ke sa a yi wa Allah da Manzonsa qiren qarya. Allah Subhanahu Wa Ta’ala kuwa na cewa:

"Ka ce: Abin sani kawai, Ubangijina Ya hana abubuwan alfasha, abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya vuya, zunubi da raba kan jama'a ba da wani haqqi ba, kuma da ku yi shirka da Allah, ga abin da bai saukar da wani dalili ba gare shi, kuma da ku faxi abin da ba ku sani ba, ga Allah" (7:33)

 Bayan wannan kuma, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ja kunnenmu a kan wannan lamari, inda yake cewa: "Yi mani qarya ba xaya yake da yi wa wani mutum qarya ba. Duk wanda ya yi mani qarya da gangan, to ya yanki tikitin shiga wuta da kansa" (SB: 1291)

 2.3 Gargaxi da Tunatarwa

 Gargaxi da tunatarwa na xaya daga cikin ayyukan nagartattun bayin Allah. Kuma su ne makaman masu da'awa da kira zuwa ga addininSa. Kuma abubuwa ne da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya umurci manya-manyan manzanni da su. Kamar inda Yake cewa Annabi Musa Alaihis Salam:

 "Ka fitar da mutanenka daga duhu zuwa ga haske. Ka kuma tuna masu da kwanukan (masifun) Allah" (14:5)

Ya kuma ce ma shugaban manzanni:

 “Saboda haka ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai" (88:12)

 Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi wannan umurni ne ga waxannan Annabawa nasa, saboda kasancewar wa'azi wata hanya xaya-xaya da, ake iya bi a yaqi zuciyar mutane da fatar baki. A kuma motsa hankalinsa. Har a ci qarfin shexanin da ke kansu, a raba su da qasqanci da gafala.

 Tabbas wannan shi ne abin da wa'azi ke samarwa. Saboda yana niqa zuciya ne, ya haskaka ta, ya yi mata wankan tsabal-tsabal ta hanyar yaye duk wata yana da ta hana ta ganin gaskiya, da gusar da duk wata tsatsa da ta yi mata katutu. Ta yadda ma'abucinta zai wayi gari yana jin danshin girman Ubangijinsa cikinta, da xaura azamar biyar umurninsa da nisantar hane-hanensa.

 Saboda waxannan martabobi da darajoji da wa'azi ya tara, ya sa kowa ma na da buqata da shi. Ba sai masu laifi ba. Sai dai kuma kash! Ko an yi shi ba kowa ne ke rabauta da amfani da shi ba. Sai wanda ya kasance asalatan, mai tsoron Allah da kauce ma fushinSa. Kamar yadda Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

"Saboda haka ka tunatar, idan tunatarwa za ta yi amfani. Wanda yake tsoron (Allah) zai tuna" (87:9,10)

A wata yar kuma Ya ce:

 "Kuma ka tunatar, domin tunatarwa tana amfanin muminai" (51:55)

 Bisa waxannan dalilai ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mai matuqar kula da bayar da muhimmanci ga gargaxi da faxakarwa. Wanda kuma ta hanyarsu ne ya shiryar da al’ummarsa zuwa ga tafarkin alheri. Tare da dasa son aiwatar da shi a cikin birnin rayuwarsu. Ya kuma hane su aikata sharri, tare da tsoratar da su, da nuna masu mummunar aqibarsa.

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sami wannan nasara ne, sakamakon kirdadon lokaci da yanayin da ya dace ya yi wa sahabbansa gargaxi a cikinsu. Yin haka ya zama wajibi gare shi, don gudun su gundura da abinda yake cika su da shi (SB: 70) Bayan wannan kuma wa'azin da yake yi masu, wani irin wa'azi ne da ke cike da hikima da fasaha, da girgiza zukata tare kuma da sa idanu su zubar da hawaye (JT: 26/SA: 2157). Xaukar wannan mataki da biyar wannan salo ga Ma’aiki wajibi ne. Ko banza wa'azi na xaya daga cikin muhimman abubuwan da Allah Ta'ala Ya aiko shi da su. Kamar yadda shi Subhanahu Wa Ta’ala da kansa Yake faxa: "Ku sani misalina da na saqon da Allah Ya aiko ni da shi, shi ne: Kamar wani mutum ne da ya zo ya sami wasu mutane, ya ce masu: Ya ku mutane, haqiqa na ga wata runduna da qwayar idona sun taso maku. Sai wasu daga cikinsu suka saurare shi da kyau. Suka kuma sulale cikin dare, suka tsira. Saura kuma suka qaryata shi, suka kwana a wurin. Qarshe rudunar can ta yi masu sammako, ta dira a kansu ta xaixaita su. To wannan shi ne misalin wanda ya yi mani xa'a daga cikinku, ya kuma yi riqo da abinda na zo da shi. Da kuma misalin wanda ya sava mani ya kuma qaryata abin da na zo da shi na gaskiya" (SB: 7283)

 Wannan ke nan. A lokacin Aikin Hajji kuma, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mai yawan yi wa mutane gargaxi da tunatarwa. Idan kuma aka kalli yadda hakan ta gudana, za a ga wasu muhimman abubuwa kamar haka:

• Ya kan gudanar da wannan tunatarwa kusan ko wane lokaci, kuma a ko wane wuri Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin ta tabbata, kamar yadda muka faxa a baya, ya yi wa mutane gargaxi a Arafata. Wanda ya yi tsananin ratsa zukatansu (SM: 1218/MA: 6173) da kuma lokacin da yake kaiwa da komowa tsakanin ibadodi da wuraren gudanar da su (SB: 1671/MA: 2264) Ya kuma yi masu a Mina, ranar suka (SB:1741, 4403, 4406, 5550) da kuma gaba xayan tsawon ranakkun Tashriq (kwanaki uku na bayan sallar layya) "(MA: 20695) da kuma kan hanyarsa ta dawowa Madina (NFK: 8464/SN:4/416). Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya xauki irin wannan mataki ne, don kada dama ta wuce shi. Ta kasancewar zukatan mutane a irin wannan lokaci na Hajji a buxe, kuma shirye da saurare da karvar wa'azi da tunatarwa.

• Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan washe zukatan mutane, ta hanyar kama zaren hankalinsu da qulla shi da wata matashiya don abin da zai faxa, ya sami gidin zama na dindindin a ciki. Kamar haxubar da ya yi wa mutane a ranar salla, wadda yake cewa: "Shin ko kun san ko wace rana ce yau?” Sai abin ya ba sahabbai mamaki, a'a! suka dai ce masa: “Allah da manzo ne suka sani fiye da kowa. Mai bayar da labarin ya ce: "Sai kuma ya yi shuru har muka yi tsammani ko zai sake wa ranar suna ne. Sai kuma muka ji ya ce: "Ashe ba ranar salla ce ba?” Muka karva masa cewa: “Lalle ita ce. Sai kuma ya ce: "To wane wata ne muke ciki? Muka ce masa: Allah da Manzonsa ne suka sani fiye da kowa. “Sai kuma ya yi kawaici, har muka yi zaton shi ma zai sake masa suna ne. A qarshe kuma sai ya ce:"Ashe ba Zul-hajji ba ne?” Muka ce: “lalle shi ne”. Sai ya sake cewa: "To ko kun san ko wane gari ne wannan?” Muka sake ce masa: Allah da Manzonsa ne suka sani fiye da kowa. Kuma ya sake yai yin kawaici. Har shi ma muka yi zaton ko zai sake masa suna ne. Can sai muka ji ya ce: "Ashe ba garin nan ne ba mai alfarma?" Muka ce “Tabbas shi ne”. Daga nan kuma sai ya ce: "To, ku sani haqiqa jinainanku da dukiyoyinku da mutuncinku sun haramta tsakaninku, wa ku wa ku. Kamar yadda keta alfarmar wannan yini da wannan wata da wannan gari naku su ke haramun har ranar da za ku haxu da ubangjinku" (SB: 1741).

Sai kuma lokacin da aka tamabaye shi a kan matsayin jinkirtawa ko gaggauta wasu ayyuka a ranar salla. Sai bai wadatu da karva tambayar da cewa: "Ba komai, ba komai ba" sai ya qara xaure mata gindin zama a zuciyar mai tambayar da masu sauraren da cewa: "Sai fa muminin da ya ci mutuncin xan'uwansa a kan zalunci. Wannan kam, ya yi illa ya kuma halaka" (SAD: 2015/SA: 1775)

• Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan maimaita gargaxi kan abu xaya, a wurare da dama. Kamar yadda ya yi ta maimaitawa da nanata haramcin jinainai da dukiyoyi da mutunci, a ranar Arafa (SM: 1218/SU: 4002) da ranar layya (SB: 67) da tsawon kwanukwan Tashirq (MA: 20695).

Kai, da yawa ma ya kan maimaita gargaxi kan abu xaya a wuri xaya fiye kuma da sau xaya. Kamar gargaxin can da ya yi a cikin hadisin xan Abbas Allah ya yarda da su a kan haramcin jinainai da dukiyoyi da mutunci daidai da haramcin keta alfarmar yini da wata da garin Makka masu girma, hadisin da muka rawaito yanzu ba da daxewa ba (88:1739)

 • Bayan wannan kuma, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bawan Allah ne mai faxi da cikawa. Maganarsa da wa'azinsa ba su tava savawa da aikinsa ba. Babu wani abu na alheri da zai yi wa mutane gargaxi da shi face ya riga su aikata shi. Kamar yadda kuma yake fin su yin nesa-nesa da duk wani abin qi, da ya hane su da aikatawa.

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mafi tsoron Allah daga cikin bayin Allah, mafi kuma gaskiya da xa'a gare shi Sallallahu Alaihi Wasallama.

• Haka kuma ta tabbata, a duk lokacin da Annabi zai tunatar da mutane a kan wani abu, to ya kan yi amfani da kalmomi masu sauqin fahimta da ganewa. Ba ya kuma tsanantawa a ciki. Duk huxubar da zai yi za ta kasance a cikin salo sassauqa kuma karvavve, mai armashi da kwarjini, ta fuskar kalmomi da ma'ana. Haka kuma salon ba zai kasa zama miqaqqe ba.

• Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan mayar da hankali ne matuqa a lokacin gargaxinsa a kan manyan ginshiqan addini. Waxanda samun tsira ga bayi ya rataya a kansu. Saboda kasancewarsu sanadin kyautatawar addini da nagartar duniyarsu. Haka kuma ba za ka same shi yana tayar da hankalin mutane ko yawo da shi, ba gaira ba sabat ba.

• Wani abun kuma shi ne, ta tabbata cewa, wani lokaci Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya kan wadatu gargaxi da ya fito daga bakinsa kawai ya shiga kunnuwan wasu mutane ba. A'a, ya kan yi tsaye haiqan a irin wannan lokaci sai saqon ya isa kunnen kowa ko mafi yawa. Kamar yadda ta faru a hadisin Bashiru xan Suhaimu Allah ya yarda da shi, sahabin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurta da yi wa mutane shela da cewa: "Babu wanda ke shiga aljanna sai mumini----" (314KK : 2960) kuma kada ya saurara da shelanta wannan gargaxi duk tsawon kwanakin da z'a a kwashe a Mina.

• Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai taqaita a kan yi wa mutane wa'azin tsoratarwa kawai ba. Ko alama, Ya kan haxa da kwaxaitar da su da aikata ayyukan lada, ta hanyar yi masu bushara. Misalin wannan shine, cewar da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: "Duk wanda ya yi Aikin Hajji saboda Allah, ba tare da ya yi wata alfasha ko mugun aiki a lokacin ba, to zai koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi" (SB: 1521) da kuma cewar da ya yi wa mutane, safiyar da aka taru: "Haqiqa Allah Ya albarkaci taron nan naku, Ya kuwa yi maku baiwa a cikinku ta hanyar damqa masu munanan aiki daga cikinku a hannun masu kyautata shi.Ya kuma sha alwashin bai wa masu kyautawar duk abin da suka nema. Magana ta qare. Sai ku cirata da qarfin Allah" (SIM: 3024/ SA: 2450)

• Haka kuma kamar yadda ya gabata. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance yana yi wa wa'azinsa ado da aiki na qashin kansa. Misali shi ne sassakar da ya yi a lokacin da ya kawo daidai kwaren nan da ake kira 'Wadi Muhassar". Wato wurin da fushin Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya sauka a kan Abrahata da rundunarsa ta giwaye. Kamar yadda hadisin Ali Allah ya yarda da shi ke tabbatarwa, inda ya ce: "Sai kuma Annabi ya sauko, har ya iso wurin "Wadi Muhasshar". Nan take sai ya yi wa taguwarsa qaimi ta zabura ta qetare kwaren da sauri. Sannan ya taka burki, kuma ya tafi a hankali. (JT: 885/HA 702)

Bayan waxannan sigogi kuma na wa'azin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci. Idan aka yi wa gargaxin nasa da tunatarwa kallo na gaba xaya, to za a ga cewa ya qunshi wasu muhimman abubuwa mabanbanta da suka haxa da:

i) Gudun Duniya

 Ya kasance yana kwaxaitar da mutane a kan gudun duniya. Kamar ce masu da ya yi, gab da faxuwar rana a filin Arafa: "Ya ku mutane, ku sani babu wani abu da ya rage maku na duniya, idan aka yi la'akari da abin da ya riga ya wuce, Sai kamar abin da ya rage wa yinin nan naku kafin ranarsa ta faxi, idan aka kalli abin da ya wuce daga safiya zuwa yanzu" (MA: 6173).

ii) Tsoron Allah

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan ja hankalin mutane a kan kasancewa masu tsoron Allah. Tare da nuna masu abubuwan da ke sa mutum ya sami sakamakon shiga aljanna. A inda yake cewa: “ku ji tsoron Ubangijinku, ku kuma sallaci sallolin nan biyar. Idan kuma watan Ramalana ya zo ku adonta shi da azumi. Ku kuma fitar da zakka daga cikin dukiyoyinku. Sai ku sami shiga aljannar Ubangjinku. (JT: 616/HA: 502)

iii) Laifin Wani…:

 Haka kuma ya kan yi wa mutane bayanin cewa laifin wani ba ya shafuwar wani. Idan an haxu gaban Allah Subhanahu Wa Ta’ala gobe qiyama kowa tasa ta fishshe shi, ba wanda za’a tambaya abin da ba shi ya aikata shi ba. Ya tabbatar masu da haka ne kuwa da faxarsa Sallallahu Alaihi Wasallama: "Ku saurara, duk wanda ya yi wata zamba a kansa zata qare. Ba a kama xa da laifin mahaifinsa ko a kama mahaifi da laifin xansa, ko alama" (SIM: 2669/SA: 2160)

iv) Kyawawan Xabi'u:

 Bayan wannan kuma, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan kwaxaitar da mutane a kan riqo da kyawawan xabi'u da ayyukan alheri, da nisantar fasiqanci da savo. Musamman a lokacin gudanar da Aikin Hajji. Yana kuma kashedinsu da shagaltuwa da duk wani abu maras amfanin yau balle na gobe. Kamar inda yake cewa: "Duk wanda ya ziyarci wannan xaki, ba kuma tare da ya aikata wata alfasha ko wani fasiqanci ba. To, zai dawo gida kamar yadda mahaifiyarsa ta haife shi" (SB: 1819).

 Da kuma faxarsa Sallallahu Alaihi Wasallama: "Gaggawa da sassaka a kan dawakai ko raquma ba shi ne xa'a ba" (SB: 1617/MA: 2264) Da kuma cewar da ya yi a lokacin da aka tamabaye shi, a kan abin da xa'a take nufi? Sai ya qara da cewa: "Ita ce: "Sadaqar abin ci da kyakkyawar magana "(MH: 1/658/MZ: 3/207/HA: 2819)

v) Sassaftawa:

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi wa mutane gargaxi da nisantar wuce wuri a cikin al'amarin addini, tare da nuna masu sassaftawa ita ce mafi dacewa. Kamar inda ya ke cewa: "Ya ku mutane, ina maku kashedi da wuce wuri a cikin addini, ku sani babu abin da ya halakar da waxanda suka zo gabaninku sai wuce wuri da suke yi a cikin addini" (SIM: 3029/SA: 2455)

vi) Biyayya Ga Uwaye:

 Haka kuma ya kan yi wa mutane wasicci da yi wa uwaye biyayya, da kuma sada zumunta. A kan haka ne yake cewa, a lokacin da ya yi wa mutane huxuba a Mina, a Hajjinsa na bankwana: "Ka yi biyayya ga mahaifiyarka da mahaifinka. Sannan ka kyautata wa 'yar uwarka mace kafin xan uwanka namiji. Sannan ka bi qannenka xaya bayan xaya, qane na bi ma wa" (MK: 484/M: 1389/HA: 1400)

vii) Jinqayin Masu Rauni:

 Ya kan kuma yi wasicci Sallallahu Alaihi Wasallama da jinqayi da tausaya wa masu rauni daga cikin al'umma, kamar mata da Barori (Bayi). Ya kan so a kyautata masu matuqa. A kan haka yake cewa: "Ku ji tsoron Allah a cikin sha'anin mata. Don Allah ku tausaya masu. Ku tuna cewa fa kun raba su da uwayensu bisa alqawarin amana tsakanin ku da Allah. Kuka kuma kusance su da sunan Allah" (SM: 1218) A wata riwaya kuma ya ce: "Ku saurara! Don Allah ku tsare yi wa mata alheri, domin su mataimaka ne a gare ku" (JT: 3087/HA: 2464) A wani hadisin kuma ya ce: "Ku tausaya wa bayinku! Ku tausaya wa bayinku!! Ku tausaya wa bayinku!!! Idan za ku ba su abin ci, ku ba su irin wanda kuke ci, Sutura kuma, ku yi masu irin wadda kuke sakawa. Idan kuma sun yi wani babban laifi, da kuke jin ba za ku iya gafarta masu ba. To ku fansar da su, a matsayin bayin Allah irinku. Amma! Kada ku azabtar da su" (MA: 1640/ SB: 30/ SM: 1661).

viii) Amana:

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan kwaxaitar da mutane a kan tabbatar da wanzuwar amana tsakaninsu da mutane 'yan uwansu da kuma tsakaninsu da Ubangijinsu. Ta hanyar bari da nisantar cutar da kowa. Da kuma qaurace wa duk wani abin da ya karva sunan "Savon Allah". Kamar inda yake cewa: "Ku bari in gaya maku ko wa ye mumini: Shi ne wanda mutane ke iya ba wa amanar dukiyarsu da rayuwarsu. Shi kuma musulmi, shi ne wanda mutane suka tsira daga sharrin harshensa da hannunsa. Shi kuwa mujahidi, shi ne wanda ya yaqi zuciyarsa ta yi wa Allah xa'a. Shi kuwa muhajiri, shi ne wanda ya qaurce wa ayyuka na zunubi da savo" (SIM: 3936/SA: 3179/SIM: 4862)

iv) Isar Da Saqonsa

 Haka kuma Sallallahu Alaihi Wasallama kan kwaxaitar da mutane a kan kama masa sha'ananin isar da saqon Allah, tare kuma da yi masu kashedi da yi masa qarya. Kamar cewar da ya yi: " Allah Ya yi albarka ga duk mutumin da ya ji wata kalma daga gare ni, ya kuma kama mani ga yaxa ta. Domin abu ne mai yiwuwa qwarai wanda ya ji ta daga bakinsa ya fi shi fahimtar maqasudinta" (SIM: 3056/SA: 2480)

D) Dagewa

 Wani abin kuma da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan kwaxaitar a kansa shi ne dagewa da nacewa a kan zubewa da qasqantar da kai ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala a cikin du’a’i da fadanci. Tare da tsananta fatar samun gafara, da dacewa da rahamarsa. Abin da ke tabbatar da wannan shi ne cewar da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: "Babu wata rana da Allah ke gafartawa da gaggawar 'yanta bawa daga shiga wuta kamar ranar Arafa. Domin ya kan matso kusa da su a ranar yana yi wa mala’iku alfahari da su, yana cewa: Waxannan bayi nawa ba su da sauran wata buqata daga yau" (SIM: 1348).

 2.3.1 Hannunka Mai Sanda

 Abin da ban mamaki. Idan dai har Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai dage irin haka, yana yi wa irin su Abubakar da Umar Allah ya yarda da su gargaxi da tunatarwa, da kuma sauran sahabban da aka yi wa bushara da aljanna. Da waxanda suka halarci yaqin Badar da ma’abota "Shajara", da sauran sahabai masu girma. To babu ko wanda ya wuce a yi masa wa'azi da gargaxi.

 Ka tuna irin matsayin da waxannan mutane su ke da shi, na kasancewarsu zavavvu a cikin wannan al'umma, kuma mutane mafiya xa'a da ilimi mai zurfi fai da voye. Kuma mafiya sassafci da gaskiyar zance, da nacewa a kan shiriya, da kyawawan halaye. Qari kan kasancewarsu waxanda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya zavar wa Annabinsa Sallallahu Alaihi Wasallama a matsayin abokai kuma mataimaka a kan tabbatarwa da yaxa addininsa. Amma tattare da haka Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya bi su da irin wannan ruwan harsashen wa'azi, mai girgiza zukata da tayar da hankali da valle ganxon tafkin idanu. Har kuma ma ya qara da sa wani, don ya jiyar da wanda bai ji ba daga cikinsu. Kai ka san girman wannan al'amari ya kai. (HA: 1/ 305/ JA: 1/60)

 Ko shakka babu buqatar da muke da ita da irin wannan wa'azi a lokacin Aikin Hajji, a wannan zamani namu ba ta misaltuwa. Musamman da yake mantuwa da rafkana da savo da jahilci sun yi mana katutu. Kuma sha'awowi da shubuhohi sun yi mana riga da wando har da ma rawani.

 Da za a buxa baki, bayan la'akari da waxannan abubuwa a ce, ko abinci da abin sha ba mu buqata kamar yadda muke buqatar irin wannan gargaxi, ba a yi kuskure ba. Domin ko shakka babu ruwan ya kai wa kowa ga hanci.

 Da kuma wannan, muke kira ga duk wanda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya hore wa ikon iya yin wa'azi da tunatarwa, da ya yi qoqarin amfani da wannan dama ta haxuwar mutane a Makka. Ya isar da saqon Allah da Manzonsa. Ko Allah na sa mutane su farka daga wannan irin barci da suke yi wanda ya kai ga minshari. Ta haka sai imaninsu ya qara qarfi. Su koma ga Allah, su narke a cikin yi masa xa'a. Su kuma waxanda suka farkar da su xin su sami ladar aikin nasu.

 2.4 Xa'a Da Xayanta Makama

 Abu na huxu kuma da rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama tsakaninsa da al’ummarsa a lokacin Aikin Hajji ta qunsa shi ne karantar da su xa'a da biyar koyarwarsa ko ba su san dalili ba, tare kuma da xayanta makamar addininsu. Ta yadda duk abin da ba ta hanyarsa ya zo masu ba to ba da shi ba.

 Musulunci kamar yadda ya kamata a ce an sani, qanqantar da kai ne da miqa wuya ga Allah shi xaya, tare da karvar duk abin da Manzonsa Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo da shi. Kuma mutum ba zai zama cikakken musulmi ba face ya sallama rayuwarsa ga duk abin da wahayi ya zo da shi gaba xayan sallamawa. (80:201) kamar yadda Allah Ta'ala Ya ce:

"To, a'a ina rantsuwa da Ubangijinka ba za su yi imani ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sava a tsakaninsu, sa'an nan kuma ba su sami wani qunci a cikin zukatansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamawa" (4: 65)

 Shi kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce a wani hadisi: "Xayanku ba zai zama mai cikakken imani ba, har sai zuciyarsa ta kasance mai bin abin da na zo da shi" (85: 104/ JUWH: 2/393-394) Haka kuma Imamu Shafi’i na cewa: "kan musulmi ya haxu a kan cewa ba ya halalta ga duk wanda Sunna ta bayyana gare shi, ya bar ta ya kama zancen wani mutum" (MS: 2/335).

 Shi kuwa lokacin Aikin Hajji shi ne qarshen wurin da miqa wuya ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke bayyana. Kuma wata makaranta ce da ake koyon yadda ake narkewa da sallamawa. A irin wannan hali ne kuwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya reni sahabbansa a kan xayanta shi a matsayin matusgin makamar addininsu. Ya kuma dasa wajabcin koyi da shi, a cikin daxin rai, a zukatansu. Jabir Allah ya yarda da shi na cewa, a qoqarinsa tabbatar da wannan magana, da kawo mana hoto cikin bayani a kan irin wannan hali, ga abin da ya cen: "Muna dai tare da Manzon Allah, alqur’ani kuma na sauka, shi ne kuma mafi sanin ma'anarsa. Saboda haka duk abin da ya aikata, shi za mu aikata" (SM: 1218) Tirqashi ka ji maza.

 Ko shakka babu kwalliyar wannan tarbiyya da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa sahabbai ta biya kuxin sabulu. Bari ka ji:

 Wani lokaci Umarul-Faruku Allah ya yarda da shi ya zo ya sumbaci Hajarul Aswadi. Sai kawai aka ji ya ce: "A sane nake da cewa kai dutse ne, ba ka da wani amfani balle wata cuta da kake iya yi wa wani. Kuma ba don na ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sumbance ka ba da ban sumbance kan ba ni ma" (SB: 1597). Da kuma cewar da ya yi: "Kamata ya yi a ce mun daina takawa da qarfi, da xaga kafaxu lokacin xawafi, da kware su. Tunda Allah Ya riga ya tabbatar da addininsa, Ya kuma turmuza hancin kafirai da kafirci. Amma tunda mun kasance muna aikata haka tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da yake raye, ba za mu daina ba har tamu ta riske mu" (BAD: 1888/ SHA: 1662/ SB: 1605/ SM 1266, 1218/ SB: 1604/ ZM: 2/225. A wata riwaya kuma aka ce, cewa ya yi: "Wallahi ba za mu fasa abin da muka saba yi ba tare da shi---" (SIM: 2952/SA: 2390).

 Shi ma sahabi Ali Allah ya yarda da shi ya taka irin wannan rawa, ko ma wadda ta fita qarfi. Domin kuwa sahabi Usmanu Allah ya yarda da shi na halifa amma Ali ya sava da shi, ya yi gabas shi kuma yana yamma, a kan al'amarin haxa hancin Umra da Aikin Hajji "al-Mut’a" Ali Allah ya yarda da shi ya san halifa Usman na qyamar haka. Har ma ya hana mutane yi. Amma gogan naka sai ya xaura Haraminsa a kan haka. Har ma da, faxa a cikin talbiyyarsa: "Ya Ubangiji na xaura niyyar gudanar da Hajji da Umra tare" Sai kuwa halifa Usmanu Allah ya yarda da shi ya zare masa ido. Ya ce: "Ashe ban hana haka ba, kuma za ka yi? Sai shi kuwa ya karva masa da cewa: "Babu wanda ya isa ya sa in bar sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama" (SB: 1563/ SN: 2724/ SA: 2552).

 Haka shi ma Abdullahi xan umar Allah ya yarda da su ba a bar shi a baya ba a wannan fage. Domin kuwa duk lokacin da zai sumbaci Hajarul Aswadi, za ka ji yana cewa a farkon fara xawafi: "Ya Ubangiji muna wannan aiki ne saboda mun yi imani da kai, mun kuma gaskata littafinka, mun kuma qanqame sunnar Annabinka Sallallahu Alaihi Wasallama" (MA: 5843/MZ: 3/240). Kuma babu wani lokaci da zai yi xawafi ba tare da ya je ya sumbanci Hajarul Aswadi ba ta ko wane hali, tun lokacin da ya ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sumbance shi." (SB: 1606/SM: 1268).

 Malam Mujahidu ya ce: "Wallahi akwai lokacin da na gan shi (xan Umar) ya yi gumurzu har hancinsa ya vare da jini don ya kai ga Hajarul aswadi" (SK: 5/87).

 Wani lokaci kuma an yi masa tambaya a kan matsayin sumbantar baqin dutsen. Sai ya ce: "Ni dai na ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na sunbantarsa ne kawai. Ni kuma na wajabta wa kaina." Sai mai tambayar ya ce: "Har da idan yawan mutane da ke nan ya fi qarfinka?" Shi kuma ya karva masa da cewa: "Wannan tambaya taka ta tsaya Yaman. Tun da dai na ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, ai magana ta qare" (SB: 1611)

 Wani mutun kuma ya tava tambayarsa a kan matsayin haxa hancin Umra da na Hajji, sai ya karva masa da cewa "Yin haka halas ne" Sai mai tambayar yace: "Amma ai mahaifinka ya hana yin haka". Shi kuma Allah ya yarda da shi ya mayar masa da martani da cewa: "To tafi na ji mahaifina ya hana yin haka. Amma ai ta tabbata cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya aikata haka. To, Umurnin mahaifina ya kamata a bi ko sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama?" Mai tambayar ya rufe da cewa: "A'a, umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama za a bi" sai xan Umar ya qara da daddale masa batun da cewa: "To ta tabbata Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya aikata haka, don ka sani (JT: 324/SA: 658).

 Haka kuma an sami wani mutum ya ce wa Abdullahi xan Umar xin Allah ya yarda da shi: "Xan Abbas na da ra'ayin cewa, ba a fara xawafi sai an isa "al-mauqif" sai ya karva masa da cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi Aikin Hajji kuma ya yi xawafi wa xakin Ka’aba, ya kuma fara shi tun bai kawo wurin ba. To sunnarsa za mu bi ko maganar xan Abbas, tsakaninka da Allah?" (SM: 1233)

 Shi ma xan Abbas xin Allah ya yarda da shi a matsayinsa na limamin malaman wannan al'umma, duk da wannan abu da ya gudana tsakaninsu da xan Umar, tarihi ya tabbatar da ba a bar shi a baya ba a fagen raya sunnar Manzon Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin wata rana ya ga Mu'awiya Allah ya yarda da shi na sumbantar gaba xayan rukunnan Ka’aba. Sai ya ce masa: "Don me kake sunbantar waxannan rukunai guda biyu, alhali kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai sunbance su ba?" Sai Ma'awiyya ya karva masa da cewa: "Ai babu wani abu a jikin Ka’abar nan da ya kamata a qyale." Sai shi kuma ya mayar masa da martani da cewa:

 "Lalle abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah" (33:21)

 Haka kuma xan Abbas na ganin halaccin haxa hancin Hajji da Umra. To sai aka ce masa, to amma fa Abubakar da Umar ba su yi haka ba. Sai ya mayar da martani da cewa: wallahi ina kyautata zaton wuta Allah zai watsa ku. Ina gaya maku abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi kuna kawo mani zancen Abubakar da umar!" (MA: 2277/ FWM: 280)

 Wannan ke nan. Tarbiyyar kuma da Annabi ya ba sahabbai a cikin wannan siga, a wannan lokaci na Aikin Hajji a kan su kasance masu xa'a da tsayawa ga abin da nassin Alqur'ani da na hadisi suka umurce su kawai, cike take da muhimman abubuwa da suke yi mata kwalliya da suka haxa da:

1.  Jawo hankalin alhazai, a kan su kula da abubuwan da yake faxi, kuma su yi koyi da shi a cikin ayyukansu na Hajji. Ya yi musu irin wannan jan hankalin a wurare da dama. Yana kuma yi yana yi wa wasiccin nasa dabaibayi a cikin qwaqwalensu, ta hanyar tuna masu cewa, to fa abu ne mai yiwuwa wannan Hajji ya zama na qarshe gare shi. Ya kan ce masu: "Ina ba ku shawara da ku kwaikwayi Aikin Hajji daga gareni tun yanzu. Domin ban sani ba ko wataqila ba zan sake yin Aikin Hajji ba, bayan wannan" (SM: 1297/ SIM: 3033/ SA: 2449/ MA: 14943).

2.  Kwaxaitar da mutane, a cikin huxubarsa ta ranar Arafa da ya yi a kan riqo da littafin Allah. Domin shi ne kawai zai zame masu garkuwa da kariya daga sakin hanya da faxawa rami. Ga abin da yake cewa: "Haqiqa kuma na bar maku wani abin da har abada ba zaku vace ba bayan na cika matuqar kuna riqe da shi, shi ne littafin Allah (SM: 1218).

3.  Haka kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya gargaxi al'ummarsa, da su nisanci biyar son zuciya da qage-qage a cikin addini. Ya faxi abin da ke tabbatar da haka ne, yana tsaye a kan taguwarsa a ranar Arafa, da cewa: "Ku sani ni ne wanda zai shiga gaba ku bi gobe qiyama, mu tasar wa tafkin al-kausara. Ina alfahari da kun fi ko wace al'umma yawa. Dan Allah kada ku ba ni kunya. Ku sani zan nemi ceton wasu mutane, za a kuma yi qoqarin ware wasu bara gurbi daga ga reni. Don idan na ce: "Ya Ubangiji ka jiqan al'ummata, ka ba ni cetonsu. Sai ya ce: "Al'ummarka?! Hala baka san abin da suka tsira bayan ka cika ba" (SIM: 3057/SA: 2481)

4.  Koya wa sahabbansa Allah ya yarda da shi ibadodin Hajji a aikace. Tare da yi masu kashedi da wuce iyaka. Kamar yadda hadisin xan Abbas Allah ya yarda da su ya tabbatar. Inda ya ce, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa, a ranar jifa da safe yana kan taguwarsa: "Tsinto mani tsakwankwani" Ya ce: sai ya rinqa wasa da su a hannuwansa yana cewa: "kada ku wuce irin waxannan idan za ku yi jifa" Sannan kuma ya ce: "Ya ku mutane ina yi maku kashedi da wuce wuri a cikin addini. Ku sani shi ya halakar da waxanda suka zo gabanin ku" (SIM: 3029/SA: 2455).

5.  Goyawar da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa masoyinsa Usamatu da xan amminsa Falalu, lokacin da zai gudanar da wasu ibadodi, ita ma alama ce ta yana son ya xayanta makamar addininsu Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin kuwa ya janyo su kusa da shi ne don su ga yadda ya gudanar da waxannan ibadodi, su ma su yi haka. Su kuma riwaito wa mutane abin da suka gani, don al'amarin ya tafi bai xaya. Saboda tabbacin haka ne ma da mutane ke da shi, da suka ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya lizimci Usamatu ranar Arafa, sai suka ce: “Xan uwan namu Usamatu zai gaya mana yadda Annabi ya gudanar da komai". Da kuma suka ga ya lizimci Falalu, a tsakanin Muzdalifa da Mina, sai shi ma suka ce: "Ashe Falalu zai gaya mana duk yadda aka yi" (MA: 21861)

Ni kuwa a wurina, babban abin da ke tabbatar da gurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na kasancewar sahabbansa Allah ya yarda da su ba su karvar ayyukan ibada daga kowa sai shi. Har kuma ya yi qoqarin xora su a kan wannan turba, shi ne tilasta wa waxanda ba su zo da abin yin hadaya ba ajiye Harami. Tattare kuwa da cewa su ne mafi yawa. Har kuma ma uzuri sai da suka kawo, da cewa; Ke nan za mu isa Arafata muna da sauran janaba a jikinmu (suna nufin zasu kusanci matansu a wannan tsakanin. Suna ganin kuwa hakan ya keta alfarmar ibadar da suka zo yi) (SM: 1216).

 Dalili kuwa shi ne, ganin Sallallahu Alaihi Wasallama ya halasta wa duk wanda ba ya da hadaya a hannu ya ajiye Harami, ya kusanci iyali. Kamar yadda hadisin Abbas Allah ya yarda da shi ke cewa: "Annabi na qare sallar subahi sai ya ce: duk wanda ke da sha'awar mayar da Hajjinsa Umra ya samu ya yi hakan" (SM: 1240) ka ga ya ba su zavi ke nan. Shi kuwa Jabir Allah ya yarda da shi ya ce a nasa hadisin: "Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa sahabbansa izinin mayar da Hajjinsu Umra. Su tafi kawai su yi xawafi ga Ka’aba, su yi saisaye (aski), su kuma ajiye harami. Amma ban da wanda ke da hadayarsa a hannu" (SB: 1785) kuma har wayau cewar da Jabir xin Allah ya yarda da shi ya yi: "Ba su zaci yana nufin lalle ne ba. Illa dai ya halasta masu iyalin ne nan kawai"

 To fa ai, da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ji wannan magana, ya kuma fahimci cewa, wanda ya yi ta xin, ya yi ta ne saboda abin da suka riga suka karva daga mushrikai, na rashin halaccin haxa Umra da Hajji, ko gudanar da Umra a cikin watannin hajji, kuma wai yin haka babban fajirci ne a wurinsu (SB: 1564). To sai ya janye maganar zavi, ya tilasta wa gaba xayan sahabban ajiye haramin don ya tabbatar masu da cewa gare shi kawai ne za su karvi qa’idojin addini, su kuwa suka yi masa xa'a suka ajiye (SB: 7367/SM: 1216).

 2.4.1 Hannunka Mai Sanda

 Duk wanda ya kalli halaye da yanayin mutane a duniyar musulunci ta yau, zai ga irin yadda rashin tsayawa a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama qeqe da qeqe, ya haifar da yawaitar yaxuwar bidi'o’i da varnace-varnace, a cikin wata irin siffa mai tayar da hankali. Haka abin yake har a cikin Aikin Hajji. Dole ne kuwa kafin a ceto al'umma daga wannan hali sai an xora ta a kan tafarkin xayanta makama da matusgar addininta. Ta hanyar riqon Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da sunnarsa, su kaxai abin koyi. A kuma samar da rundunar malamai ta musamman, wadda za ta tsaya a kan wannan aiki ba dare ba rana, musamman a lokacin Aikin Hajji. Saboda kasancewarsa wata muhimmiyar dama, da ake iya amfani da ita, a yi wa musulmi ganxo a kan wannan manufa.

 Da wannan kuma muke kira ga duk wanda ke fatar samun tsira a duniya da lahira, da ya yi wa kansa da qafafunsa dabaibayi, da farko, a kan bin koyarwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sau da qafa. Ya kuma xaura wannan niyya tun daga wannan Hajji nasa. Domin kuma koyi da Almusxafa Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne matuqar abin da zai sa aikin mutum ya zama karvavve a wurin Allah. Kuma shi ne sharaxi na farko ga samun shiga aljanna, da kuvuce ma wuta. Kamar yadda nassosa da dama ke tabbatarwa. Kamar inda Sallallahu Alaihi Wasallama yake cewa: "duk wanda ya aikata wani aiki da ba mu muka koya masa ba, to ya yi aikin baban giwa" (SB: 1718). Da kuma inda yake cewa: "Kowa zai shiga aljanna daga cikin al'ummata, sai wanda ba ya so". Sai sahabbai suka yi mamaki suka ce masa: "Ya Manzon Allah, yanzu ashe akwai wanda ba ya son shiga aljanna? "Ya karva masu da cewa: "Qwarai kuwa. Ai duk wanda ya bi ni sau da qafa, ya nuna yana son shiga ke nan. Wanda duk kuwa ya kuskure ya sava mani, to ya ce ba ya son shiga aljanna ke nan" (SB: 7280).

 2.5 Haxa kan Al'umma

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi qoqari matuqa a lokacin Aikin Hajjin nasa, ya gina al'ummarsa a kan harsashen haxin kai da nisantar wariya da fitinu.

 Wannan kuma da ma, na xaya daga cikin muhimman manufofin addini musulunci, al'umma ta kasance tsintsiya maxaurinki xaya bangonta katangar qarfe. Saboda haka ne nassosa da dama na alqur’ani da hadisi suka zo suna umurtar bayin Allah da haxin kai da zama abu xaya. A lokaci xaya kuma su nisanci savani da raba gari da juna. Daga cikin nassosan akwai kamar faxar Allah Ta'ala.

"Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya, kuma kada ku rarraba" (3: 103)

Da kuma inda yake cewa:

“Kuma lalle ne wannan al’umma taku al’umma ce guda, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku bauta min.’ (23:52.

Da kuma inda Yake cewa:

“Kuma kada ku kasance daga cikin mushrikai. Waxanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance qungiya-qungiya, ko wace qungiya na farin ciki da abin da ke gare ta kawai”. (30:31,32).

 Sai kuma abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mumini da mumini kamar gini ne. sashensa ba ya yi sai da sashe” (SB:2446). Mai riwayar ya ce: Yana faxar haka sai ya sarqe yatsun hannayensa ya kuma jimqe su. A wani wurin kuma cewa Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Taimakon Allah na tare da jama’a” (JT:2166/ SA:1760).

 Da yake lokacin Aikin Hajji, lokaci ne da ke da yanayi irin na haxin kai a tsakanin mutane. Kuma wata gagarumar dama ce shi, ta tarkata hankalin al’umma wuri xaya, da lurar da ita sharrin da ke cikin rashin haxin kai, da zama cikin fitinu. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi wata-wata ba, sai ya mayar da hankali ga inganta wannan vangare ta hanyoyi da suka haxa da:

* Daidaita matsayin xaixaikun mutane. Da sanya tsoron Allah, ya zama dalili qwaya xaya rak, da zai iya fifita wani a kan wani. Ga abin da yake cewa: “Haqiqa Ubangijinku xaya ne, kuma kakanku xaya ne. Balarabe cikinsu bai fi bobawanku da komai ba. Kamar yadda baqar fata ba ya fin farar fata komai, sai idan ya fi shi tsoron Allah” (MA:23536/ MZ:3/266).

* Yi wa mutane umurni da yin xa’a da biyayya da nasiha ga shugabanninsu, matuqar suna jagorancinsu da littafin Allah Subhanahu Wa Ta’ala. Haka kuma ya umurce su da zama tare da jama’a. gaba xayan waxannan umurce-umurce biyu na cikin faxarsa Sallallahu Alaihi Wasallama: “Da za a shugabantar maku da baqin bawa kuma mai qirarrun gavovi, to ku yi masa xa’a da biyayya matuqar da littafin Allah ne yake jagorancinku” (SM:1298) da kuma cewar da yayi a khaifu ta Mina “Bai kamata zuciyar mumini ta ji qyashin wasu abubuwa guda uku ba: 1) Yin ko wane aiki don Allah kawai, ii) Yin nasiha ga shugabanni, da, iii) Lizimtar jama’a. Domin kuwa da su ne ake karva da’awowinsu” (SIM:3056/ SA:2480).

* Yi wa al’ummarsa kashedi da karva gayyatar shexan, a lokacin da ya kaxa gangar fitina tsakanin sashensu da sashe. Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ku sani haqiqa shexan ya yanke qaunar musulmi masallata za su sake bauta masa a cikin yankin nan na Larabawa. Amma ya fito da wani nau’i na yi masa bauta, ta hanyar zuga sashenku ya faxa wa sashe da faxa. To kar ku yarda (SM:2312/MA:20695).

 * Yi wa al’umma kashedi da qaga wani abu a cikin addini. Ya kuma faxa masu haka ne don kowa ya shiga taitayinsa. Ya ce: “Ku sani gobe qiyama zan ceci wasu mutane. Amma kuma za a ware wasu bara gurbi daga cikinsu. Ganin haka zan ce: ya Ubangiji ai su ma nawa ne, sai Ya karva mani da ce wa: “Ai ba ka san bidi’o’in da suka tsira bayanka ba (SIM:3057/ SA:2481).

 * Hana mutane kusantar duk wani abu da ke iya rarraba kan musulmi da haifar da fitina tsakaninsu, kamar abin da ya shafi yaqi. Ya yi masu wannan hani ne Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa: “Kada bayan na cika ku koma kamar kafirai sashenku ku girbe kanun sashe” (SB:121). Saboda ma muhimmancin wannan Magana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai faxe ta ba, sai da ya nemi a sanya jama’a su saurara.

 Bayan wannan hani na gaba xaya kuma, a wannan vangare, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci al’ummarsa da nisantar waxannan abubuwa, waxanda ga al’adarsu suna haifar da qiyayya ne da fitina da gaba wani lokacin ma har da yaqe – yaqe.

Abubuwan sun haxa da:

1.  Tozarta jini, dukiya ko mutuncin wani: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wannan hani ne a cikin wasu huxubobi guda uku da ya gabatar a Arafa, da ranar Layya da kuma Tsakanin Kwanukan Tashriq. Ga abin da ya ce: “Ku sani jinainanku da dukiyoyinku da mutucinku sun haramta a tsakaninku kamar yadda keta alfarmar wannan wuni, da wannan watan da wannan garin naku ya ke haramun” (SB:67/SM:1218/MA:20695).

2.  Zalunci: Ya kuma yi masu kashedi da zalunci Sallallahu Alaihi Wasallama, kamar cin dukiyar mutane ba tare da yardarsu ba, wato dai zamba da yaudara. Ga abin da ya ce masu: “Ku saurara in gaya maku abin da idan kun bi shi, za ku rayu: kar ku yi zalunci!, ku nisanci zalunci!! Ku xaure hannayenku daga zalunci!!! Ku sani dukiyar mutum musulmi ba ta halasta ga kowa sai da yardarsa” (MA:20695).

3.  Hana wasici ga mai gado: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya haramta wannan, da cewa: “Haqiqa Allah Ta’ala Ya raba gado da kansa Ya ba ko wane magadi haqqinsa. Ba a yin wasiyya da wani abu ga magadi” (JT:2218/SA:1721).

4.  Giba: Wato cin naman musulmi ko keta mutuncinsa, ba tare da wani dalili na shari’a ba. Ya yi wannan gargaxi da hani ne a kan wannan abu Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da aka tambaye shi matsayin jinkirtawa ko gaggauta wasu ayyuka a ranar salla, sai ya ce: “Babu laifi. Babu laifi!! Sai fa ga mutumin da ya ci nama ko mutuncin wani mutum musulmi. Wannnan kam azzalumi ne. shi kam idan ya aikata haka yana da laifi, ya kuma halaka” (SAD:2015/SA:1775).

* Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya gargaxi al’ummarsa a kan Dujjal. A inda ya ce masu: “Babu wani Annabi da Allah Ya aiko face ya yi wa al’ummarsa gargadi game da Dujjal. To ni ma ina yi maku gargaxi a kan sa. Haqiqa zai bayyana a cikinku. Amma duk irin yadda ya rikirkita ku ba za ku kasa gane shi ba. Domin shi alamominsa a bayyane su ke”. Mai riwayar ya ce, ya faxi haka har sau uku Sallallahu Alaihi Wasallama Sannan ya ci gaba da cewa: “Kun dai riga kun sani cewa, Ubangijinku ba mai ido xaya ne ba. to shi Dujjal ba ya da idon dama. Xayar kuma da ya ke da ita kamar mulmulalliyar qwayar dabino ce. Don haka sai ku yi hattara” (SB:4403).

 2.5.1 Hannunka Mai Sanda:

 Duk da wannan muhimmin tarihi na horo da gargaxi da haxin kai, da wannan al’umma tamu take da shi. An wayi gari yau wasu daga sassanta ba su ga maciji da juna. Miyagun fitinu sun ratsa jikinta ta ko ina, kamar yadda jini ke ratsa tsoka.

 Ashe ke nan kamata ya yi wannan al’umma tamu ta yi wa tafiyarta ado da waiwaye. Ta zama tsintsiya maxaurinki xaya. Ta qanqame addininta. Sai Allah ya dawo mata da qarfinta da martabarta.

 Wannan hanya kawai ce mafita. Domin kuwa tarihi ya tabbatar da cewa, ta haka ne zaren wannan al’umma ke rikixewa ya zama kwangirin qarfe. Ya gagari har maqeran asali, balle ‘yan walda. Da ikon Allah.

 Ko shakka babu lokacin Aikin Hajji na iya zama asasin wannan aiki. Domin kuwa jiki da zukatan miliyoyin mutane sun haxu qarqashin inuwa xaya. Tattare da banbancin da ke tsakaninsu na gari da harshe da jini da al’ada da matsayin ilimi da na wayewa da shekaru da arziqi da ma komai da komai in ban da wannan addinin da duk aka zo taron dominsa.

 Makama ta farko ta wannan juyin juya – hali, Allah Ya riga ya lamunce wa ko wane mahajjaci ita tun da ya ba shi ikon zowa Aikin Hajjin. A nan ne zai wanke zunubbansa gaba xaya. Ashe ke nan ko wane mahajjaci na iya shan alwashin daga rana mai kamar ta yau, da shekara mai kamar ta yau, shi da duk wani abu da ke da alaqa da jahiliyya fau-fau. Ya kuma yi tsaye, tsayin alif ya qarfafa alaqa da soyayyarsa da Allah Ubangijinsa. Ta hanyar son duk wanda Allah ke so, da qin duk wanda ba ya so, ko waye shi. Sannan kuma ya yi qoqarin aiwatar da wannan xabi’a tsakaninsa da alhazai ‘yan uwansa. Tare da kwaxaitar da su a kan kwaikwayonsa.

 Bayan wannan lokaci, kuma. Idan ya koma gida, kada ya bari wannan aqida da xabi’a su yi tsatsa. Ya dage a kan duk wani abu da ke iya sabunta su, a gaba xayan rayuwarsa ta yau da kullum. Ta hanyar taimakon musulmi ‘yan uwansa ta ko wane hali, tare da yi masu fatar duk abin da yake yi wa kansa fata na alheri. Ya kuma yi kaffa – kaffa da zurfafa a cikin yin hulxa da wanda ba musulmi ba.

 Duk alhajin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ba shi ikon aikata waxannan abubuwa da muka faxa, ko shakka babu ya yi nasara, ya kuma haye tudun mun tsira. Ya kuma bayar da gagarumar gudunmawa, ga haxuwar kan wannan al’umma da kyautatuwar al’amarinta.

 2.6 Nagartaccen Shugabanci da Kyakkyawar Mu’amala:

 Abu na gaba kuma da ya gudana tsakanin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da al’ummarsa, a wannan lokaci na Aikin Hajji shi ne, nagartaccen shugabanci da kyakkyawar mu’amala.

 Da ma Allah Ta’ala Ya qawata Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da kyawawan xabi’u da nagartattun halaye. Waxanda suka haxu suka ba shi damar iya kasancewa nagartaccen shugaba. Wanda zai iya gina nagartacciyar al’umma ta hanyar amfani da hikima da fasaha da shari’a.

 Fahimtar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a haka ne fa, da mutane suka yi, sai ya mamaye birnin zuciyarsu. Da labarin tafiyarsa zuwa Aikin Hajji ya yaxu ko’ina sai mutane da dama suka ji lalle sai sun yi Aikin Hajji a wannan shekara qarqashin jagorancinsa. Haka kuwa aka yi. Domin Allah ne kawai Ya san adadin mutanen da suka yi ibadar qarqashin tutarsa Sallallahu Alaihi Wasallama. Amma wasu malamai sun qaddara yawan nasu da, mutum dubu xari (M:572). Kuma gurin kowa daga cikinsu shi ne ya yi koyi da Annabin Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin ibadarsa ta Hajji (SM:1218).

 To fa ai, ba a qare Aikin Hajjin ba, sai da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya mamaye zukatansu, ya kuma yi wani irin tasiri a cikin rayuwarsu. Ta hanyar ba su tarbiyya mafi inganci, da yi masu wani irin gangariyar shugabanci, da ba a tava gani ba ko aka ji irinsa a tarihin duniya.

 Ko shakka babu, wannan taqaitaccen littafi, ba zai iya qunsar filla-filla ba, ko ya yi sharhi a kan wannan mu’amala dalla – dalla. A kan haka za mu taqaita kan wasu daga cikinsu, waxanda kuma muna da yaqinin za su iya bamu cikakken hoton yadda al’amurran suka kasance.

Bissimillahi:

 a) Farawa da Kai:

 Haqiqa Allah Maxaukakin Sarki Ya yi tir da bayinsa, waxanda ke horo da aikata alheri, amma su ba su aikatawa. Inda Ya ce:

“Ya ku waxanda suka yi imani! Don me kuke faxin abin da ba ku aikatawa? Ya girma ga zama abin qyama a wurin Allah, ku faxi abin da ba ku aikatawa” (61:2,3).

 To kasancewar da ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, halaye da xabi’biunsa na tafiya ne daidai da karantawar alqur’ani (SM:746). Sai ya zama babu wani abu da zai umurci al’ummarsa da aikatawa na alheri, face ya riga su aikata shi. Haka ma babu wani abu na sharri da zai hane su aikatawa face ya fi su nisantarsa. Wannan xabi’a tasa kuwa ta farawa da kai, na xaya daga cikin abubuwan da suka sa ya yi nasara a cikin aikinsa na koyarwa. Musamman a lokacin Aikin Hajji. Ga kaxan daga cikin yadda wannan al’amari ya kasance:

 A huxubarsa ta bankwana, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “ku saurara! Daga yau na kashe duk wata magana da ke da alaqa da tarihinmu na jahiliyya. Duk wani jini da ake bi bashi tun wannan lokaci na saryar da shi. Kuma jinin farko da nake shelanta saryarwa shi ne na xan’uwanmu xan Rabi’ata xan Harisu. Wanda Huzailu ta kashe, a daidai lokacin da ake renon sa a Bani Sa’ad. Haka kuma duk wata Riba da ake bi bashi tun wannan lokaci, ita ma na saryar da ita. Farkon kuwa ma wadda nake saryarwa ita ce tamu. Wato Ribar Abbas xan Abdul Muxallibi. Daga yau na saryar da ita” (SMl1218).

 Haka kuma a daidai lokacin da yake kwaxaitar da sahabbansa a kan kasancewa masu tsananin biyayya ga Allah, da qanqan da kai da zubewa a gabansa a wannan lokaci na Aikin Hajji (SB:1871,1710,1819). Sai ya kasance babu wanda ya kama qafarsa a wannan fage Sallallahu Alaihi Wasallama; domin shi ne wanda ya fi kowa daga cikinsu qanqan da kai ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala ta hanyar fadanci da tsoro da gurfanawa a gabansa a ko wane lokaci (SB:1751/SM:1218).

 Haka kuma, a daidai lokacin da yake karantar da su gudun duniya da kuma mayar da hankali ga tunanin lahira. Suna dubawa sai suka ga sirdin da ke kan taguwarsa a wannan lokaci na Aikin Hajji ba wani kayan gabas ne ba. Kai! Ko ga na yamma ma bai kai ba. Kuma da qyar ne ma shimfixar da ke kansa, zata yi dirhami huxu a farashi. (MA:6173/ SIM:2890/ SA:2337).

 Haka kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya hori sahabban nasa Allah ya yarda da su da nisantar gomotso da turereniya da rashin natsuwa a lokacin gudanar da ibadun Hajjin. A qarshe da suka mayar da hankali suka kalli yanayin tasa ibadar a lokacin, sai suka ga ya sauko cikin wata irin cikakkiyar natsuwa, da kamala, ba kuma tafiya irin ta masu batun zuci ba (JT:886/SA:708).

 Ko a lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masu bayanin kasancewar aski da saisaye a lokacin Hajji abu xaya ne, da shari’a ta yarda da ko wanensu. Amma kuma ya kwaxaitar da su a kan su zavi yin aski, har ma ya yi addu’a ga duk wanda ya yi shi (SB:1727,1728) ko kafin su farga, sai kawai suka ga kan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama twal twal twal ya yi aski abinsa. (SB:1729).

 Haka kuma da annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa sahabbansa kashedi da wuce wuri a cikin sha’anin addini. Har kuma ya umurce su da su yi amfani da ’yan tsakwankwani, daidai jifa irin ta hankali (SM:1282/SIM:3029/SA:2455). Sai ya kasance shi ma da irin wannan tsakuwar ya yi jifar kafin su (SM:1299).

 Wani babban abin da ya kamata a lura da shi a nan, saboda muhimmancinsa, shi ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya na sane, ya xaura xamarar ba sahabbai misalai a aikace, ba wai abu ne da ya faru kwaram ba. Babban abin da zai qara tabbatar maka da haka shi ne cewar da ya yi wa masu shayar da alhazzai ruwa; “Ba don gudun mutane su rinjaye ku ba, a cikin wannan shayarwa da na kama maku” (SM:1218).

 Irin wannan hali da xabi’a na daga cikin manyan abubuwan da suka sa mutane suka ji babu wanda suke so kamar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma saboda haka ne suka miqa wuya gare shi, ya zama abin koyinsu. Domin sun ga irin yadda yake gudanar da wani irin nagartaccen shugabanci, ta hanyar imani da aikata abin da yake horo da shi.

 To irin wannan hali ne na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kamata masu da’awa da yekuwar gyara halin jama’a su kwaikwaya. Don su suka fi dacewa da shi fiye da kowa. Su yi qoqari su zama nagartattun jagorori, a cikin gaba xayan ayyukansu. Musamman a lokacin Aikin Hajji. Ta hanyar kasancewa waxanda za su riga mutane aikata duk wani alheri da suka hore su da aikatawa. Kuma su fi kowa nisantar duk wani abin da suka hori mutane da nisanta, tare da fin kowa kaffa – kaffa da shi.

 b) Horo da Hani:

 Horo da aikata alheri da hani daga ko kusantar sharri, su ne qashin bayan addini, kuma babban Aikin da allah Ya aiko Manzanni don Gudanarwa. Haka kuma su ne gishirin ingantattar rayuwa da tafarkin samun tsira gobe qiyama. Da tsare su ne kuma ake samun xaukaka, har kuma qafafu su kama qasa.

 Da za a taru, a yi biris da wannan Aikin na Horo da Hani, lalle da shari’a ta zama labari, a nemi ma addinin kansa a rasa, jahilci ya kafa sansani, varna ta zama ruwan dare (IUD:2/306).

 To, kuma shi wannan aiki wajibi ne a kan duk wanda Allah Ya hore masa ikon yin sa. Idan kuma zai yi, to ya yi da gaske. Koda kuwa yana ganin kamar abin ba zai yi amfani ba. To ya sani, ai horo da hanin ne wajibi a kansa, ba sanya mutane su karva ba. Kamar dai yadda Allah Ta’ala Ya ce:

“Babu abin da yake a kan Manzo, sai iyarwa” (5:99).

 A wata ayar kuma ya ce wa Annabinsa Sallallahu Alaihi Wasallama:

“Lalle fa kai ba ka shiryar da wanda kake so, amma Allah shi ke shiryar da wanda Ya so---“ (28:56) SMLN:2/23/D:1/65).

 Ka ga abin da kawai Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya umurci Manzon da shi, shi ne “Horo” Ya ce:

“Kuma ka yi horo da alheri” (7:199).

 A wata ayar kuma Ya hore shi da “Hani” bayan horon. Inda yake bayyana wasu siffofi na Manzon. Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

“Rubutacce ne a wurinsu a cikin at-Taura da Linjila, yana horonsu da alheri, kuma yana Hana su daga abin qi” (7:157).

 A kan haka, duk wanda ya nazarci rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai same ta maqil da bayanan da yake yi ko da yaushe a kan alheri, da kwaxaitar da jama’a ga aikata shi, tare kuma da tona asirin sharri, da fitowa da shi fili, don kowa ya tantance shi, ya kuma guje shi. Irin wannan xabi’a tasa Sallallahu Alaihi Wasallama ta yi matuqar bayyana a lokacin Aikin Hajji. Domin kuwa ya faxakar da alhazzai a kan abubuwan da ibadarsu ta Hajji, ba ta inganta sai da shi. Wanda kuma sai ta haka ne addininsu zai kammala. Har su sami tsira a gaban Ubangijisu. Ya kuma tsoratar tare da yi masu kashedi daga duk abin da yake akasin wannan ne.

 Kusan mafi bayyanar abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya hori al’ummarsa da shi, da kuma wanda ya hane ta daga gare shi a wannan lokaci ya haxa da:

·   Yin hannunka mai sanda da ya yi wa wani mutum a lokacin da ya ji shi yana shelanta haramar Aikin Hajji don wani mutum, alhali shi bai tava yi ba. Wanda kuwa kansa ya fi cancanta ya yi wa kafin wani. Xan Abbas ne ya riwaito wannan a cikin wani hadisi nasa, inda ya ke cewa: “Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ji wani mutum na cewa: Na karva kiranka ya Ubangiji a madadin Shubrumata. Sai ya tambaye shi “Wane ne Shubrumata?” mutunin ya karva masa da cewa: Wani xan uwana ne. Sai Annabi ya sake tambayarsa da cewa, “to kai ka tava yin Aikin Hajji?” Ya ce, a’a. Sai Annabi ya hore shi da cewa: “To ka fara yi wa kanka, kafin ka yi wa Shubrumata” (SAD:1811/SA:1596).

·   Haka kuma yana daga cikin horace – horacensa Sallallahu Alaihi Wasallama tilasta wa waxanda ba su zo da hadaya daga cikin sahabbansa ba, su ajiye harami, su yi tamattu’i don su samu falalar haxa Umra da Hajji. Tare da rashin jin daxin haka da suka nuna don ganin kamar yin ifradi ya fi kai matuqa ga girmama xakin Allah. Annabi kuma ya nace akan matsayinsa, daga qarshe suka fahimci babu wata mafita sai su bi umurnin nasa. (SM:1211/ SB:7367/ SM:1216).

·   Haka kuma ya haxu da wani mutum, a daidai lokacin da yake xawafi ga Ka’aba Sallallahu Alaihi Wasallama. Mutumin ya xaure hannunsa ga jikin wani mutum, da wata igiya, yana jan sa. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa hannunsa mai albarka ya tsinka igiyar. Ya kuma hore shi da cewa: “Ka ja shi da hannunka ya fi” (SB:1620) tunda ba dabba ne ba.

·   Wani horon kuma da alheri da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci, shi ne hana abin qi da hannunsa. Mun dai riga mun sanar da kai labarin yadda Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana Falalu Allah ya yarda da shi sakewa ya kalli wasu ‘yan mata da suke wucewa (N:3/157) Jabir ne Allah ya yarda da shi ya kawo labarin a wani hadisi nasa mai, inda ya ce: “Sai kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tafi tare da Falalu xan Abbas. Ga shi kuwa Allah ya yi masa kyakkyawar siffa; ga shi dai fari ne santilo, ga kuma gashinsa liya-liya amma na gota shi, sai ga wasu ‘yan mata suna wucewa. Sai ko hankalin Falalu ya koma kansu ya qura masu ido. Da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya lura, sai ya sa hannunsa ya rufe fuskar Falalu. Sai ya koma yana kallonsu ta xaya vangaren. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sake komawa da hannunsa wancan vangaren ya yi masa shamaki” (SM:1218).

 Haka kuma ta sake faruwa tsakaninsu kamar yadda xan Abbas xin ya faxa a wani wuri cewa, wani lokaci ana tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma Falalu. Sai ga wata mata Bakhas’ama (‘yar qabilar Khas’am). Sai kuwa Falalu ya qura mata ido. Ita ma ta qura masa. Ganin haka sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kama kan Falalu ya juya fuskarsa zuwa wani vangare (SB:1855).

 Ka ji irin yaqin da Manzon Rahama Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ta famar yi don hana shaixan ya yi varna a tsakanin bayin Allah. Amma yau, a wannan zamani namu, ire-iren waxannan abubuwan qi sun yawaita a tsakanin alhazai. Wasu kuma suna faruwa ne a mafi yawan lokuta, sanadiyyar jahilci, ko qaramin sani. Ba don an yi nufin aikata su da gangan ba, ko don rashin tsarkin zuciya. Ashe ke nan da za a sami waxanda za su naqaltawa alhazzai hukunce – hukuncen shari’a cikin tsanaki da kwanciyar hankali, tare da kyautatawa, da an ce madalla.

 To amma kuma mu sani, duk yadda malamai da masu wa’azi suka take gidan wuta don tabbatar da wannan manufa, abin yana da wuya. Saboda irin yadda varnace - varnacen suka yawaita, da irin nauyin rashin masaniyar da alhazan ke da ita, da abin qwarai da ma’abutansa. Ya kamata kenan ko wane alhaji ya zama mai gargaxi da faxakarwa, da horo da alheri, da hani daga abin qi gwargwadon iko. Saboda tabbatarwa, da aiwatar da faxar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da ya ce: “Duk wanda ya ga wani abin qi daga cikinku, to ya hana shi da hannunsa. Idan bai iyawa, to ya sa harshensa. Idan kuma haka ma ba ta samuwa, to ya qyamaci abin da zuciyarsa. Wannan kuwa shi ne mafi raunin imani. (SB:2172/ SM:49).

 Da wannan kuma muke kira ga ko wane musulmi, da ya kasance mai nuna fushinsa a duk lokacin da aka shiga hurumin Allah. Ya kuma yi qoqari iyakar zarafi na ganin ya raya abin nan da aka nakkasa. Ya tuna Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: "Duk wanda ya kafa wani abu mai kyau a musulunci, to Allah zai ba shi ladar da ke ciki, da kuma irin wadda zai ba wanda duk ya yi aiki da wannan abin bayansa. Ba kuma tare da ladar tasu ta ragu da komai ba. Duk kuma wanda ya kafa wani abu maras kyau a musulunci. To shi ma, Allah zai ba shi zunubin da ke ciki, da kuma irin wanda zai ba wanda duk ya yi aiki da shi a bayansa. Ba kuma tare da zunubin nan nasu ya ragu da komai ba’ (SM:1017).

 c- Tawali’u:

 Tawali’u shi ne jagoran kyawawan xabi’u. Da shi ne kuma ake samun xaukaka a wurin Allah Subhanahu Wa Ta’ala da ma wurin mutane ‘yan adamu. Kamar yadda ya zo a hadisi cewa: “Babu lokacin da mutum zai yi tawali’u ga Allah, face Allah Ya xaga darajarsa”. (SM:2588) .

 Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya umurci Annabinsa Sallallahu Alaihi Wasallama da wannan xabi’a ta Tawali’u. inda ya ke ce masa:

“Kuma ka sassauta fikafikanka ga wanda ya bi ka daga cikin muminai”. (26:215)

 A nan Allah Subhanahu Wa Ta’ala Yana umurnin sa da ya zama mai tausayi ga muminai waxanda suka bi shi. Ya yi masu kamar yadda kaza ta ke yi wa ‘ya’yanta qanana a lokacin sanyi, ko idan za su yi barci, domin ta kare su daga cuta.

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya bi umurnin Allah, domin kuwa ya kasance mutum mai tsananin Tawali’u fiye da kowa daga cikin mutane. Yana yi wa kansa ko wace irin hidima. Ya kuma yi ta iyalinsa a gida. Ya kan kakkave takalminsa, ya xinke tufafinsa, ya tatsi akuyarsa, ya kuma xauki kayansa da kansa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan yi sallama ga qananan yara, har ma ya yi masu zantuka na raha da nishaxi. Ba ya kuma nuna fifikon kan sa duk da irin tarin xaukakar da Allah ya yi masa. Idan kuma aka gayyace shi zuwa ko wane irin al’amari zai halarta (SB:676,6072,6247). Har ma ya kan Siffanta kansa da cewa: “Ni ina cin abinci kamar yadda ko wane bawa ke ci. Ina kuma zama kamar yadda ko wannensu ke zaunawa” (SB:3683) Wani lokaci ma wata kuyanga za ta zo ta kama hannunsa, ya bi ta kamar raqumi. Har su je inda take nufi ya qwato mata haqqinta. (SB:6072)

Bayan wannan duka ya kan gargaxi al’ummarsa a kan cewa, kada su kuskura su kai shi a matsayin da ba nasa ba. Ya kan ce: “kada ku xaga ni kamar yadda Nasara (kiristoci) suka xaga xan Maryamu (Isah Alaihis Salamu). Ku sani ni bawan Allah ne. Don haka idan za ku ambace ni, to ku ce da ni: Bawan Allah kuma Manzonsa” (SB:3445).

 Wannan ke nan. A lokacin Aikin Hajji kuwa, nan ne tawali’un Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin lamarin jagorancinsa ga mutane, ya daxa fitowa fili, ta fuskokin da suka haxa da:

·   Hajjin da ya tafi Sallallahu Alaihi Wasallama a kan wani tsohon sirdi da shimfixar da ba zata yi dirhami huxu a farashinta ba, ta isa alama (SIM:2890/SA:2338.

·   Sai kuma qin yarda da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama a banbanta shi da sauran mutane. Ta hanyar kawo masa wani ruwan sha, na daban wanda mutane ba su sa hannayensu a ciki ba. Ba shakka wannan Tawali’u ne mai girma. A maimakon yarda da hakan can da bai yi ba, sai ya ce wa amminsa Abbas Allah ya yarda da shi: “ba ni da buqata da wani ruwa na daban. Ku dai bani wanda mutane ke sha, ni ma in sha daga cikinshi (MA:1814/ SB:1636).

·   Wani abin kuma da ke tabbatar da tawali’un Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da rashin xaukar kansa daban da mutane, shi ne tafiya tare da Usamatu xan Zaidu Allah ya yarda da shi kafaxa da kafaxa, akan abin hawa xaya daga Arafa zuwa Muzdalifa, kuma gaban kowa. Tattare da kasancewar Usamatu bawa ne (SB:1544)

·   Sai kuma tsayawa da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi tare da wata mata, tana yi masa tambayoyi, yana saurararta daki daki, tare kuma da ba ta amsa. Ba tare da la’akari da zamanta mace ba, balle hakan ta sa ya rinqa yi mata kallon hadarin kaji. (SM:1335). Wannan ma wani Tawali’u ne.

·   Bayan wannan kuma, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya shirya rayuwarsa, musamman a wannan lokaci na Aikin Hajji, irin yadda babu wanda ba zai iya kai wurinsa ba. Kuma da zarar mutum ya yi tozali da shi Sallallahu Alaihi Wasallama nan da nan zai kai qarshen matsalarsa, domin babu wasu dogarawa da ya ajiye masu yin iso ballantana su hana mutane ganinsa ko yin magana da shi. (SM:1274/ SM:3035/ SA:2461).

·   Sai kuma qin yarda da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama ya waqilta wani ya soke dabbobin hadayarsa a madadinsa, tattare da damar da yake da ita ta yin haka. Amma saboda Tawali’u, a maimakon haka sai ya soke guda sittin da uku daga cikin raquman da hannunsa mai albarka (SIM:3074/SA:2494).

Da wannan Tawali’u ne, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya mallakawa Annabinsa ragamar zukatan mutane, aka wayi gari ba wanda suke so da amincewa tamkarsa Sallallahu Alaihi Wasallama.

Wannan shi ne sirrin. Da kuma yau almajirai da malamai masu wa’azi, za su yi kwaikwayon wannan xabi’a ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kwalliya ta biya kuxin sabulu ko shakka babu, waxannan jinsunan mutane biyu, sun fi kowa cancanta da su yi koyi da wannan xabi’a. musamman a lokacin Aikin Hajji. Su qara qaimi wurin rarrashi da tausaya wa jama’a. musamman masu rauni da sarqaqun buqatu, da bobayi, domin irin wannan shi ne tawali’u mafi nagarta kamar yadda Abdullahi xan Mubarak Allah ya jiqansa ya bayyana, inda ya ce: “Mafi nagartar Tawali’u shi ne ka haxa kafaxarka da wanda bai kai qimarka a duniya ba, har ya fahimci cewa, baka xauki ni’imar da kake ciki ta duniya a wani abu da zai sa ka yi masa fankama ba” (IUD:3/342).

 Da zarar haka kuwa ta samu, to abin neman ya zo hannu. Domin mahajjata za su qaunaci masu yi masu gargaxi da faxakarwa. Su kuma sami aminci tsakaninsu da su. Wanda a qarshe hakan za ta sa su karvi duk abin da suke gaya masu, su kuma yi aiki da shi.

 d- Rahama da Jinqayi:

 Musulunci addini ne na rahama da jinqayi. Kuma shari’o’i da hukunce – hukuncensa gaba xaya an gina su ne, a kan harsashen tausayawa da taimaka wa mutane (RN:61). Saboda haka ba sai an yi wani dogon yunquri ba, don a tabbatar wa duniya da cewa, an aiko Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da saqon Rahama da Jinqayi. Ko banza kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya gama Magana da ya ce:-

“Kuma bamu aike ka ba face domin ka zama rahama ga talikkai” (21:107).

 Bayan wannan kuma, shi ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayar da labarin da kansa cewa: “Haqiqa an aiko ni ne, don in zama rahama ga mutane” (SM:2599). A wani wurin kuma ya ce: “Nine Muhammad, Annabin tuba, kuma Annabin Rahama” (SM:2300).

 A kan haka ne rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama tsakaninsa da mutane ta zama kamar yadda Ubangijinsa Ya siffanta shi:

“Mai Tausayi mai jinqayi” (9:128)

 Kuma a sakamakon haka ne, Rahama da tausayi da Jinqayinsa Sallallahu Alaihi Wasallama suka zama ruwan dare game duniya. Har aka wayi gari babu wani mahaluki daga cikin mutane, da ya kama qafarsa a wajen jinqayi ga mutane. Har sai da hakan ta sa wasu daga cikinsu bayar da shedar cewa, irin yadda yake tausayi da jinqayinsu, ko su ba za su iya yi wa kansu haka nan ba. Kamar yadda ya zo a cikin hadisin Umaimatu Allah ya qara mata yarda wadda ta ce: “Na yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama mubaya’a tare da wasu mata. Sai ya ce mana: “Na karvi mubaya’arku. Amma a kan abin da kuke iyawa”. Sai na ce masa: Allah da Manzonsa su ne mafiya Rahama da jinqayi gare mu, fiye da kanmu zuwa ga kanmu” (JT:159/SA:1300).

 Wani kuma daga cikin sahabbai ya siffanta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa: “Manzon Allah ya kasance mai rahama da Jinqayi gare mu, fiye da jinqayi da rahamar da muke yi wa kanmu” (JT:159/ SA:1300).

 Wani kuma daga cikin sahabbai ga siffanta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa: “Manzon Allah ya Kasance mai rahama da jinqayi” (SB:628). Wani kuma ya ce: “ban tava ganin mutum mai Rahama da jinqayi ga iyali ba kamar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama (SM:2316). A wata riwaya kuma aka ce cewa ya yi” … ga bayin Allah” (SN:151/76).

 Wannan irin Rahama da jinqayi na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa ga sahabbai da sauran mutane, ta sa su narkewa cikin kogin sonsa, da yin goggoriyo wurin ganin sun aiwatar da umurninsa Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan sakamako kuwa, ya taimaka masa matuqa ga samun sauqin jagorancinsu da xora su akan tafarki madaidaici.

 A lokacin Aikin Hajji, wannan Rahama da jinqayi na ma’aiki, a cikin jagorancinsa ga mutane, sun bayyana ta fuskoki da dama kamar:

 * Wajabta wa waxanda ba su zo da abin yin hadaya ba, daga cikin sahabbai, su aje Harami, cikakkar ajewa. Wanda hakan ke nufin suna iya zo wa iyalinsu, su kuma xaura tufafinsu na gida, su kuma shafa turare. Duk don sauqaqawa gare su. (SM:1213,2131).

 * Sai kuma haxa sallar azzahar da la’asar da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a Arafa (SM:1218). Da kuma jinkirta sallar magariba da ya yi a lokacin da ya sauka zuwa Muzdalifa (SB:136). Duk, saboda ya sauqaqa wa mutane. Ta hanyar rage masu yawan hawa da sauka daga kan ababen hawansu. Kuma hakan zata ba wa ko wane alhaji damar daidaita hankalin raquminsa ta hanyar aje kayansa kacokam a daidai wurin da zai kwana.

 * Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba masu rauni daga cikin alhazai damar baro muzdalifa tun a cikin dare, bayan wata ya faku. Wato su riga sauran mutane masu isasshen qarfi tasowa. Don hakan ta lamunce masu gudanar da wasu ayyuka na ranar layya kafin mutanen can su kwararo wuri ya cushe a rinqa goggoriyo da su (SB:1567).

 * Sai kuma rangwamen da ya yi wa mutane Sallallahu Alaihi Wasallama na gaggautawa ko jinkirta wasu ayyuka na ranar layya. Ta hanyar karva wa duk wanda ya tambaye shi a kan haka, da cewa: “Ku na iya yi, ba komai” (SB:83).

 * Haka kuma akwai wasu mutane da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi wa wani sassauci, Rahama da Jinqayi na musamman, saboda waxansu lalurori da suka kevantu da su. Kamar damar da ya ba Abbas Allah ya yarda da shi ya kwana a Makka, Sallallahu Alaihi Wasallama tsawon kwanukan da ya kamata a ce ya yi su a Mina. Saboda lalurar shayar da alhazzai ruwa (SB:1745). Da kuma iznin da ya yi wa wasu masu kiwon raquma da su haxe jifar kwana biyu, su yi ta gaba xaya, bayan ranar layya, a cikin xayan kwanakin (JT:968/ SA:764/ ZM:2/290).

 * Bayan wannan kuma sai, iznin da ya bayar Sallallahu Alaihi Wasallama na wani ya yi Aikin Hajji a madadin wani, wanda ibadar ta wajaba a kansa, amma jikinsa ba zai iya xaukar xawainiyar Hajjin ba. (SM:1335/ MA:1812).

 * Haka kuma, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama saboda Rahama da jinqayi ga mutane, ya kan bar abin da yake shi ne mafifici. Kamar gudanar da xawafi da sa’ayi da ya yi a kan taguwa da kuma sunbantar Hajarul Aswad da ya yi da sanda. (SM:2217).

 * Sai kuma tsananin tausayawa da kula da marasa lafiya da yake yi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci tare kuma da xora su a kan abin da yake shi ne mafi sauqi gare su a shari’a da al’ada (SB:4699,4753,5896).

 Ke nan duk wanda ke son haxuwa da rahamar Allah Ta’ala, musamman a lokacin Aikin Hajji, lokacin Rahama da Jinqayi, to lalle ne ya riqa tausaya wa masu rauni daga cikin mutane. Domin kuwa “Allah na yin rahamarsa ne kawai ga waxanda ke yin rahama ga mutane” (JT:1924/ SA:1569) kuma “Duk wanda ba ya jinqayi, ba ya samun a yi masa jinqayi” (SB:5997) Haka “Allah ba Ya jinqayin wanda ba ya jinqayin mutane” (SB:7376) “Waxanda kawai Allah ke yi wa rahama daga cikin bayinSa su ne masu yin rahama ga bayinSa” (SB:1584).

 A kan haka lalle ne, duk wanda ke fatar samun tsira gobe qiyama, ya ji tsoron kasancewa cikin sahun marasa tausayi da jinqayi. Domin kuwa da zarar haka ta faru, to rashin arziki ya tabbata a kansa. Domin “Babu wanda ake cire wa rahama daga cikin zuciyarsa sai tavavve” (JT:1923/ NA:1568).

 Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi mana kariya baki xaya. Amin.

 e- Baiwa:

 A duk lokacin da aka yi nasarar tarbiyyantar da rayuwa a kan gudun duniya, da taqaitawa a cikin jin daxinta, to ba za a gamu da wata wahala ko tangarxa ba, idan aka xaura niyyar yin baiwa da ita duniyar wa mutane. Da haka kuma sai a wayi gari an ga baya ga duk wata qiyayya da gaba da ke tsakanin masu baiwar da waxanda ake yi wa. A lokaci xaya kuma sai soyayya mai zurfi, da qauna su maye gurbinsu. Tabbas wannan shi ne abin da zai faru. Saboda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya gina rayuwar xan Adamu a kan son alheri da kyautatawa, tare da girmama duk wanda ke yi mata su, da saurararsa zuci da kunne. Tabbacin duk wannan Magana da muke yi, shi ne faxar Allah Subhanahu Wa Ta’ala:

“Ka tunkuxe cuta da abin da yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai qiyayya a tsakaninka da shi, kamar dai shi majivinci ne, masoyi”. (41:34).

A kan wannan tafarki, duk wanda ya kalli rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kuma yi nazarinta da kyau zai ga irin yadda Sallallahu Alaihi Wasallama ya haxa hancin gudun duniya da yawan baiwa a lokaci xaya. Domin kuwa a daidai lokacin da ake share tsawon wata uku ba a hasa wuta ba a gidansa, ba abin da yake ci shi da iyalinsa sai dabino, su yayyafa wa cikinsu ruwa (SB:2567). A daidai wannan lokaci kuma ya ke riqe da kamban kyauta da baiwa a cikin mutane (SB:6). Idan ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tashi yin kyauta, ya kan yi ta kashin fari ne. Kamar da xai bai san akwai wani abu mai suna talauci ba (SM:2312). Har an ma riwaito yana cewa: “Da zan mallaki zinari kamar tulin dutsin Uhudu, zan fi farin cikin kada bayan kwana uku, a iske wani abu ya rage hannuna daga cikinsa, sai fa abin da zan taimaki addini da shi”.

Ba wani abu ya sa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ke xaukar wannan mataki ba, sai kasancewar babu abin da ke cikin zuciyarsa sai Allah. Kuma lahira ita ce alqiblarsa. Duniya kuwa ba shi ba ta. Don haka, shi a wurinsa fiffiken sauro ya fi duniya da abin da ke cikinta.

 Da haka ne kuma a lokacin Aikin Hajji, baiwa da alherin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa ga mutane, a matsayinsa na jagoransu suka zama shafe zane. Saboda babu wani vangare na rayuwarsa a wannan lokaci da zaka kalla, face ka ga wata itaciya ta alherinsa, wadda sayyunta suka kama qasa, rassanta suka barbaje. Ta yadda yawan alqalami ba zai iya qididdige su ba. saboda haka za mu taqaita a kan kaxan daga cikin baiwa da karimcinsa a matsayin misali:-

·   Tumun fari Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi baiwa ta lokacinsa ga waxanda suka yi jinkirin fitowa daga garuruwansu don su tafi Aikin Hajji tare da shi. Wanda a sakamakon haka ya sadaukar da wuni xaya a Zul-Khulaifa yana jiransu (SB:1551/ SN:4/215,218/ ZM:2/102,106).

·   Sai kuma a lokacin gudanar da Hajjin, inda ya yawaita kyauta da sadaqa ta hanyar yankewa da soke raquma xari, ya kuma rarraba namansu, fatunsu har da qassansu ga mabuqata, duk a matsayin hadaya (SM:1317). Haka kuma ya yi wasu sadaqoqi a wurare da dama a cikin sigogi daban-daban (SM:1679/SAD:1633/SA:1437).

·   Wani Alherin kuma da ya yi ga mutane Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne sauraren mutane da biya masu buqatunsu, a duk lokacin da buqata ta taso, don kawai ya faranta masu rai (SB:1518/ MA:15972).

·   Bayan wannan kuma, sai karimcin da ya yi wa Usamatu xan Zaidu, da Falalu xan Abbas Allah ya yarda da su a lokacin da ya yi masu kuturi a kan taguwarsa, a daidai lokacin da ake kaiwa da komowa tsakanin Arafa da Muzdalifa da Mina (SB:1544).

·   Wata babbar baiwar kuma da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ita ce samar wa masu rauni mafita, da karantar da su, da sauqaqa masu al’amurra, ta hanyar xora su a kan abin da ya fi dacewa da sauqi gare su. Kusan babu wata huxuba da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a wannan lokaci face ka ji wannan jigo na sauqi ya fito a cikinta (SM:1218/SB:4853/SM:1207).

·   Bayan wannan kuma sai kwaxayin da Sallallahu Alaihi Wasallama ya nuna na ganin al’ummarsa ta tsira, ta hanyar samun Allah Ya karvi aikinsu gaba xaya. Hakan ce ta sa shi ya dage ga du’a’i da roqon gafarar Allah. Musamman a marecen ranar Arafa da kuma a Muzdalifa (MA:16207) kuma a duk lokacin da zai yi masu dua’i, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi gama gari ne, ta hanyar roqon Allah Ya gafarta masu baki xaya (MA:1592).

·   Abu na gaba kuma shi ne, alherin dagewa da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi na ganin saqon da ya zo da shi, ya isa kunnen kowa. Ta hanyar yawan nanatawa da maimaita abu xaya a lokacin da ake saurararsa duk. (JT:616/SA:512/MA:18989).

·   Wani abin alheri kuma da ya aiwatar ga al’ummarsa Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci, a matsayin baiwa, shi ne qoqarin nisantar da sahabbansa Allah ya yarda da su daga ko wace irin fitina, kamar yadda ya juya kan Falalu Allah ya yarda da shi a lokacin da ya ga ya qura wa wata budurwa bakhas’ama ido. Da amminsa Abbas Allah ya yarda da shi ya tambaye shi dalili, sai ya ce masa: “Na ga matashi ne da matashiya na qyaren juna. Ina tsoron kar shexan ya shiga a tsakaninsu” (JT:885/NA:702).

·   Sai kuma lokacin da wasu mutane daga cikin sahabban nasa su biyu, suka yi sallah a masaukansu. Sannan suka zo masallaci. Suka taras Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yana ba wa mutane sallar can da suka rigaya suka yi a gidajensu. Sai su kuma suka toge can qarshen masallacin, daga baya; ba su shiga aka yi sallar da su ba. saboda tsoron fitina da kashe wutarta, da aka sallame sallar, sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masu: “kada ku sake yin haka. Ko da kunyi salla a gidajenku, idan kuka iso masallaci kuka taras jama’a suna salla, to ku shiga a cikinsu ayi sallar da ku, tana matsayin nafila a gare ku” (JT:219/SA:181).

 Bisa wannan turba, babu abin da ya dace ga duk wanda ke son Allah Ya so shi, Ya kuma yi masa falala da rahama, sai ya yi koyi da halayen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta hanyar kyautata aikinsa, da yawaita baiwa da alheri ga mabuqata a lokacin Aikin Hajji, ta hanyar duk abin da Allah Ya hore masa na ilimi da duniya da qarfi da matsayi da makamantansu. Domin Allah Ta’ala na cewa:

“Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son masu kyautatawa” (2;195)

A wata ayar kuma Yana cewa:

“Shin alheri na da wani sakamako, ban da kyautatawa?” (55;60).

 Duk kuma wanda ke son Hajjinsa ya zama nagartacce kuma karvavve a wurin Allah, Ya kuma gafarta masa zunubansa, qarshe ya samu shiga aljanna, to ya yawaita ciyar da miskinai, ya kuma lizimci kyawawan halaye. Saboda hadisi ya zo cewa, wanda ya yi nagartaccen aikin Hajji, ba ya da wani sakamako sai aljanna” (SB:1773/SM:1342). Kuma ya fassara nagartaccen Aikin Hajji da cewa, “Ciyar da abinci da kyakkyawar magana”. (MH:1/658/HH:3/207/HA:2819).

 f) Haquri:

 Haquri shi ne abin da masu taqawa kan yi guzuri da shi. Masu kira zuwa ga addinin Allah kuma, shi ne abin da sukan riqa a matsayin sanadin nasara. Ta hanyarsa ne kuma al’amari ke kama qasa. Kuma wata taska ce shi, ta alheri wadda mai ita kan dafa dutse a sha romo. Da haquri ne kuma shugabanci kan karva sunansa. Har ya gudana a ci moriyarsa.

 Haquri ya haxa waxannan martabobi da darajoji ne, saboda kasancewarsa ruwan kashe zafin zuciya da taka mata burki lokacin da shexan ya kaxa mata tamburra. Wanda a qarshe hakan za ta tsirar da itaciyar soyayya da qauna tsakanin mutane, har su haxa hannu da qafa, su gina aljannar duniya. Su sami kwanciyar hankali, arziqi da wadata.

 Saboda wannan irin rawa da haquri ke takawa ne, ya zama mafi alherin abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke arzuta bawa da shi. Kamar yadda wani hadisi da ya zo daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, ya ce: “Duk wanda ya xaura niyyar mayar da haquri xabi’arsa, to Allah zai taimake shi a kan haka kuma babu wata kyauta da za ayi wa mutum a duniya, mafi zama alheri da yalwa kamar Allah Ya azurta shi da haquri” (SM:1053).

 Manya manyan mutane a duniya, masu hankali da kaifin basira irin su Umarul – Faruqu Allah ya yarda da shi sun fahimci wannan magana. Domin an riwaito yana cewa: “Mafi alherin abin da muka samu a rayuwa mun same shi ne ta hanyar haquri” (SB:1122). Shi kuwa Sayyidina Ali Allah ya yarda da shi cewa ya ke yi: “Haquri wani abin hawa ne da ba ya kasawa” (MS:2/158).

 Haquri a wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama abu ne da ake yi don neman yardar Allah Subhanahu Wa Ta’ala da xaukaka addininsa. Saboda haka ne shi ya qure maleji a fagen Haquri, ya turmuza hancin zuciyarsa da ransa, ta hanyar karkatar da su daga raki da raggon kaya, tare da xaure su gindin bishiyar dauriya da yarda da qaddara da hukuncin Allah komai xacinsu.

 A lokacin Aikin Hajji kuwa, a matsayinsa na wani nau’i na jihadi (SB:1861) Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya hore wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ikon haxa hancin wasu nau’uka uku na haquri a lokaci xaya. waxanda suka haxa da:

 i) Haqurin Ibada:

 Babu wani sahabi daga cikin sahabban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da ya kama qafarsa a fagen xa’a da biyayya ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala a wannan lokaci, balle ya wuce shi. Shi ne mafi dauriya da haquri a cikinsu wajen tsare abubuwa na wajibi da na mustahabbi, don qara samun fada da shiga a wurin Allah. Ko da yaushe Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi tsaye gadan-gadan, ya yi gaba da gaba, da Mahaliccinsa, ya faxi ya narke ya qasqantar da kansa a gabansa Subhanahu Wa Ta’ala don gudanar da ko wace irin ibada (SB:1544,1751/ SM:1217).

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne zaqaqurin zakara tsakanin sahabbai Allah ya yarda da su wanda shi kaxai ke cara idan ana zancen tsoron Allah tsabarsa, da aiwatar da hakan a rayuwa, tare da tsananin fushi idan an sava masa. Haka kuma, kamar yadda muka faxa a baya kaxan, shi ne mafi nesa-nesa da iyakokin Allah. Da duk wani abu da ke kai mutum ga kutsa huruminsa (SB:1772,6367).

 ii) Haqurin Jagoranci:

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya jagoranci al’ummarsa a wannan lokaci na Aikin Hajji, ba tare da kasawa ko qosawa balle fasawa ba. Duk wanda ya yi la’akari da irin nauyin da yake kansa Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci, na ayyuka masu yawa, da ta’amuli da mutane daban – daban, a cikin wani yanayi na daban, dole ya jinjina masa, don abin ya sha kan hankali.

 Ka riga ka san Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama mutum ne, kuma bawan Allah, da ke da tsananin kwaxayin tabbatar da cikar mutuntakarsa, ta hanyar qanqan da kai, da zubewa gaban Allah Subhanahu Wa Ta’ala da gudanar da ibadodin Aikin Hajjinsa a cikin siffa mafi cika da kamala. Na farko ke nan.

 Sannan kuma ga shi Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya xora masa nauyin jagorancin mutane, ta hanyar kula da su ciki da waje da tattara hankalinsu wuri xaya. Kai babu wani abu da ya shafe su, face Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya damqa kula da shi a hannunsa Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Shi ke da alhakin karantar da su, da shiryar da su, da tarbiyyantar da su, da xora su a kan tafarkin alheri, komai yawansu. Ta hanyar isar da saqon zuwa gare su, da yi masu bayanin hukunce – hukunce dalla – dalla ba tare da wata kasawa ba. Kuma su musulmin da ke tare da shi duk, sun san da haka. Kuma duk shi suka zura wa ido, babu wani abu da za su aikata sai irin wanda ya aikata, ko ya ce su aikata. Kai, da da hali, ko motsi wani daga cikinsu ba ya son ya yi sai irin yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, ko ya ce a yi. Na biyu ke nan.

 Ka ga wannan ma wani babban nauyi ne.

Bayan wannan kuma dubi irin yadda Aikin Hajji ke da wuyar Gudanarwa a wancan lokaci. saboda rashin ci gaban zamani irin na yau. Ga shi kuma ko a lokacin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi shekaru sittin da haihuwa. Ga kuma matansa guda tara, da mutane masu rauni daga cikin iyalin gidansa duk a tare da shi. Kuma shi ke da alhakin kula da su ta ko wane hali.

 Tirqashi wani kaya sai amale!

iii) Haquri da Jama’a

Allah Subhanahu Wa Ta’ala ne kawai ya san iyakar adadin mutanen da ke tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin Aikin Hajjinsa. Amma dai tabbataccen abu ne cewa, mutane ne da suka banbanta da juna. Wasunsu sun daxe a cikin musulunci, wasu kuwa yau suka shige shi ko jiya ko shekaranjiya. Wanda hakan dole ta haifar da kasancewar waxancan masu faffaxar masaniya da addinin kuma qaqqarfa. Waxannan kuwa tasu ba ta wuce sanin wasu farlu aini ba.

Haka kuma waxannan mutane sun fito ne daga garuruwa daban – daban, da qabilu daban – daban. Wasu matasa ne, wasu kuwa dattijai, wasu kuma matsakaita. Wasu mawadata ne, wasu kuma talakkawa. Wasu shugabannin jama’arsu, wasu kuwa mabiya. Wanda dole ne haka ta haifar da banbance – banbancen fahimta da riskuwar al’amurra, da na halaye da xabi’u, da na buqatu da lalurori da sauransu.

A dunqule kuma, akwai irin waxannan nau’uka, na masu rauni, da suka haxa da marasa lafiya da mata da qananan yara waxanda ke da buqatar kulawa ta musamman saboda irin halin da suke ciki.

Idan muka yi la’akari da irin wannan nauyi da kyau, da ya hau kan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci na Aikin Hajji, za mu fahimci irin girman haquri da ya wajaba a kansa, da irin wahalar da zai haxuwa da ita Sallallahu Alaihi Wasallama kafin ya yi nasarar jagorancin waxannan mutane. Domin kuwa ko shakka babu, tilas mai hawan ruwa ya yi babban masaki.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke nan. Kwaikwayo da shi kuma fagen Haquri abu ne da ke wuyan ko wane musulmi. Matuqar yana fatar karva sunan “Mumini” Domin kuwa ba komai ne imani ba face: Haquri da yafewa. (MA:19435) Kuma Allah Ta’ala na tare da masu haquri. Ya kuma yi alqawarin zai ba su cikkakar ladarsu ba tare da lissafi ba.

Alhazai musamman, lalle ne idan suna fatar gudanar da nagartaccen Hajji, to su xauki darasin haquri irin na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wajibi ne su lizimci xa’a, farko har qarshen ibadarsu. Su kuma yi kaffa-kaffa da savo, don kada su faxa tarkon shexan. Su kuma zama masu tsananin haquri da xaukar kwaramniyya. Tare da nisantar fushi da raki da yawan jinini. Su yi cuxanya da mutane, tare da daure wa cutarwar da za su yi masu, domin kuwa: “Mumini da ke cuxanya da mutane yana haquri da cutawarsu, ya fi girman lada bisa ga wanda ba ya cuxanya da su, balle ya daure wa cutawar tasu” (SIM:4032/SA:3257) kada su mayar da fuskokinsu a kullum xaure kamar huhun goro. Domin kuwa yin haka na tsananin takin saqa da kyakkyawan Haquri.

g- Tausayi:

 Akwai nassosa da dama kuma tabbatattu, da ke kara kaina suna bayanin falalar tausayi, da kwaxaitar da bayin Allah a kansa. Kamar cewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Haqiqa Allah na son tausayawa a cikin ko wane al’amari (SB:6024) da kuma cewarsa: “Babu wani abu da tausayi zai kasance a cikinsa face ya qawata shi. Ba kuma za’a zare shi daga wani abu ba, face abin ya munana” (SM:2594). Da kuma wata faxa tasa: “Duk wanda Allah bai yi wa tausayi ba, ba ya tare da alheri ko qyas” (SM:2592/SAD:4809).

 Tausayi ya samu irin wannan matsayi ne saboda kasancewarsa tubalin ginin hikima, da harsashen samar da ingantaccen aiki. Kuma shi ne asirin da ke sa a naqalci makamar addini (Fiqihu). Kuma wata alama ce shi, da ke tabbatar da cewa mai shi, yana da kyawawan halaye, kuma ya fi qarfin zuciyarsa.

 Tausayi na jawo wa mai shi, so da jinqayi da rahama daga wajen mutane, ta yadda kowa zai so ya kusance shi. Wanda a qarshe yake haifar da taimakon juna a tsakaninsu da zaman lafiya da lumana. Ya kawar da sharri, ya yayyafa wa wutar gaba da hassada ruwa.

 Tausayi na daga cikin kayan adon Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama wanda kowa bai kai gare shi ba. Ya fi kowa haquri da yafewa. Kamar yadda Allah Ta’ala Ya siffanta shi da cewa:

“Saboda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma da ka kasance mai fushi, mai kaushin zuciya, da sun watse daga gefenka. Sai ka yafe masu laifinsu, kuma ka nema masu gafara, kuma ka yi shawara da su a cikin (duk) al’amari” (3:159).

 Duk wanda ya yi hulxa da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbata ya aiwatar da abin nan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya umurce shi da shi. Har wani daga cikin sahabbansa Allah ya yarda da shi ke siffanta shi da cewa: “Ya kasance: “Mai Tausayi” (SB:628) A wata riwayar kuma aka ce cewa ya yi: “Mai sanyin hali”. (SM:674) Wani kuma daga cikinsu ya ce: “Ya kasance yana tausaya mana” (SB:2339/ SM:1548).

 A lokacin Aikin Hajji, Tausayin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa ga mutane, a matsayinsa na jagora, ya bayyana iyakar zarafi, ta fuskoki da dama, da suka haxa da;

 * Rashin tilasta wa mutane yin Talbiyya kamar yadda yake yi Sallallahu Alaihi Wasallama. A maimakon haka sai ya bar su da abubuwan da suke qarawa ko ragewa. (SM:1218/ SAD:1813/ SA:1598/ ZM:2/161). Kamar lokacin da suka baro Arafata, shi a wannan lokacin, talbiyya ce kawai a bakinsa Sallallahu Alaihi Wasallama. Amma wasu daga cikin mutane hailala suka riqe. Bai hana su ba. wasu kuma suka zilimci kabbara. Su ma bai hana su ba (SB:1659,1676,1687). Ka ga akwai tausayawa da sauqaqawa a nan.

 * Sai kuma rufe kansa da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama saboda zafin rana. Da hawa taguwa da ya yi a kan hanyarsa ta zuwa Aikin Hajji. Da kuma lokacin da yake safa da Marwa tsakanin wuraren ibadu da makamantan wannan. Duk waxannan abubuwa sun zama rahama ga mutane. Domin kuwa da ya yi wani abin da ba haka ba Sallallahu Alaihi Wasallama da dole haka mutane za su yi, komai wahalarsa.

 * Wannan ya haxa har da hawan taguwa da ya yi a lokacin gudanar da wasu ibadun na Hajji, kamar xawafi da Sa’ayi. Don kada mutane su yayyave shi, ta yadda hakan zata sa a tsangwame su. Ko har ma a kore su. Alhali shi kuwa ba ya son haka (SB:1666/SM:1218/JA:12/40/SM:1274).

 * Bayan wannan kuma sai sawwaqe wa mutane ganinsa da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama tsawon kwanakin Aikin Hajji. Don hakan ta ba su damar yin ido huxu da shi, su tambaye shi abin da ya shige masu duhu. Ta yadda ba za su haxu da wata wahala ba, a cikin yin koyi da shi, tun da ya riga ya fexe masu biri har wutsiya. Wannan ya haxa da wata tausayawa da ya yi masu Sallallahu Alaihi Wasallama ta rashin kallafa masu abin da ya fi qarfinsu. Daxa ta fuskar ayyukan Hajji ne na ibada, ko ta fuskar alaqar da ke tsakaninsu da shi, irin ta shugaba da mabiya. Babu fuskar da bai tausaya masu ba Sallallahu Alaihi Wasallama. Duk wanda ya nazarci tarihinsa musamman vangaren rayuwarsa ta Aikin Hajji zai tabbatar da haka (SAD:1905/SA:1676).

 * Sai kuma natsuwa da tsanaki, abubuwa guda biyu da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya lizimta a lokacin gudanar da ibadarsa ta Hajji. ya kuma hori mutane da haka. Saboda tausayinsu da yake yi. Da gudun kada rashin hakan ta jawo masa wahala ko fitina (SM: 1218/ SAD:1966/ HA:1729/JT: 886/SA: 703).

 * Sai kuma taqaita huxuba da ya yi ranar Arafa Sallallahu Alaihi Wasallama. Shi ma wani nau’i ne na tausayi ga mahajjata da ke saurarensa (SB:1560).

 * Bayan wannan kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai sake xawafin nafila ba tun da ya yi na qudumi, har sai da ya dawo daga Arafa. Haka kuma ya zauna a Mina tsawon kwanakin Tashriqi, ba tare da ya bar ta zuwa Harami ba, sai lokacin da ya tashi yin xawafin bankwana. Tattare da irin falala da matsayin da xawafi kuwa ke da shi. Wannan shi ne abin da ya inganta (SB:1545/ SN:4/334/ NW:124/ ZM:2/310,311/ SN:4/404). Wannan ya kai matuqa a cikin Tausayi.

 * Sai kuma kasancewarsa Sallallahu Alaihi Wasallama ko da yaushe, yana zaven abin da yake shi ne mafi sauqi ga jama’a. Kamar umurnin da ya ba waxanda ba su zo da abin yin hadaya ba daga cikin sahabbai Allah ya yarda da su cewa, su aje Harami. Da kuma haxe salla da ya yi a Arafa da Muzdalifa, da yin qasaru a Mina. Duk ya yi ne saboda tausayawa da sauqaqawa (SB:1656/SM:1218).

 * Bayan wannan kuma sai umurnin da ya ba sahabbansa Sallallahu Alaihi Wasallama na su soke hadayarsu a gida; ba sai a mayanka ba. Kamar yadda Jabir Allah ya yarda da shi ya riwaito daga gare shi, yana cewa: “Ni a nan na soke hadayata. Amma fa duk gaba xayan faxin garin Mina mayanka ce. Saboda haka ku soke hadayarku a gidajenku” (SM:1218). Da kuma iznin da ya yi wa mata, da su yi jifa kafin hudowar rana. Saboda la’akari da nauyin jikinsu, da gudun kada yawan mutane, ya wahalar da su har su takura” (SB:1679/ SAD:1942/ ZM:2/252/SN:4/363).

 * Wani Tausayi kuma da jinqayi da rahama da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya nuna wa al’ummarsa a wannan lokaci na Aikin Hajji, shi ne kwaxaitar da su a kan gaggauta komawa gida da zarar mutum ya kammala Aikinsa na Hajji. Ya yi haka ne saboda la’akari da yanayin tafiya, da kasancewarta wani yanki na azaba. Da kuma tausaya wa iyalinsu da ke can gida cikin kewa da begen dawowarsu. Sai ya ce: “Duk wanda ya kammala Aikin Hajjinsa daga cikinku, to ya gaggauta komawa wurin iyalinsa. Yin haka shi ne mafi lada” (MH:1/650/ SK:5/259/ HA:732).

 * Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi qoqarin ganin sahabbai Allah ya yarda da su na tausaya wa kansu da kansu. Abin da ke tabbatar da haka kuwa, ya haxa da, ganin da ya yi wa wani mutum ya janyo raqumarsa ta hadaya; shi kuma yana qasa. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa: “Kama ta ka hau” Sai ya karva masa da cewa: ta hadaya ce ya Manzon Allah. Suka yi haka har sau uku. Har dai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kai ga ce masa: “Ka faye gardama, na ce ka kama ta ka hau mana” (SB:1689). Bayan wannan kuma ya cewa sahabbai gaba xaya: “Ku hau kan dabbobinku na hadaya cikin tsanaki. Har ku cimma waxanda aka tanada musamman don hawa da xaukar kaya” (SIH:4016).

Sai kuma a wurin jifa da Sallallahu Alaihi Wasallama ya cewa mutane: “Ya ku mutane ku yi hattara kada waninku ya jefi wani, ko ya kashe shi. Idan zaku yi jifa, ku tsinto qananan tsakwankwani” (MA:16078/). Sai kuma gargaxin da ya yi wa Umar Allah ya yarda da shi da cewa: “Ya kai Umar, a matsayinka na mutum qaqqarfa, bai kamata ka yi goggoriyo da mutane wurin sumbuntar Hajrul Aswadi ba. Don kada ka cutar da masu qaramin qarfi. Idan ka sami kafa, ka isa ka rungume shi. Idan kuwa ba ka samu ba. to ka fuskance shi kawai, ka yi Hailala da Kabbara” (MA:190/SK:5/80).

 * Sai kuma rarrashin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi wa sahabbai saboda nuna masu tausayi, a kan wani abu da ba su fahimta ba. Kamar lokacin da ya umurce su da ajiye harami. Alhali kuwa su, ba su da ra’ayin haka. Saboda haka sai tankiya ta shiga ciki, bisa kuskure da rashin fahimta. Sai da ya rarrashe su de cewa: “Da na fuskanci in da aka fito, ba zan yi hadayar ba. Ku iya gane, ba don da ya kasance ina tare da dabbar hadayata ba, ai da ni ma babu abin da zai hana in ajiye haramin tare da ku” (SB:7230).

 Wato abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke son ce wa sahabbansa a nan, shi ne: “Da na san wannan al’amari zai takura ku haka, da ban zo tare da nawa dabbobin hadaya ba. Don mu yi aiki iri xaya. (SN:4/333).

 Haka kuma wani sahabi da ake kira Sa’adu xan Jusamatu Allah ya yarda da shi ya ba wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kyautar wani tsohon jaki. Amma ya qi karva. To don gudun haka ta sosa masa rai, sai Annabi ya rarrashe shi da cewa: “Bamu qi qarvar wannan kyauta taka ba, sai don kawai muna cikin Harami” (SB:1825/SM:1193).

 Haka kuma wannan ya haxa da abokan Abu qatadata Allah ya yarda da su, alhazan da suka ci farauta alhali suna cikin Harami. Duk da yake babu wani laifi gare su, tunda ba da hannunsu aka yi farautar ba. Amma duk da haka, kokwanto ya aure su. Da suka iso gaban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai magana ta qare cikin farin ciki da lumana. Domin tambayarsu ya yi: “ko akwai xaya daga cikinku wanda ya tare dabbar ko ya nune ta da wani makami? Suka ce: a’a. Sai ya ce masu: “ku iyar da canye sauran naman, ba komai”. A wata riwaya kuma cewa ya yi: “Ko kun riqo wani abu daga cikin naman?” Suka karva masa da cewa: Akwai qafa xaya da muka riqo. Sai ya karva ya kai baka” (SM:11296/ ZM:2/1652/304/ SIM:3093/ SA:2509).

 Wannan ke nan. To idan muka kalli zamaninmu na yau, zamu ga irin yadda alhazzai da yawan gaske ke fama da duhun kai game da hukunce – hukuncen Aikin Hajji. bayan ga kuma bobayi da masu rauni, da masu yawan shekaru da makamantansu a ciki. Kuma duk suna da buqata da wanda zai taimaka masu, ga jagoranci na gari, ta hanyar karantar da su, da yi masu nasiha, da sakin jiki dasu da xora su a kan tafarki madaidaici. Kai! Suna ma da buqata da wanda zai yi masu wata hidima da wani karimci, kamar irin yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a lokacinsa. Amma ina!

 Saboda haka yana da kyau gare ka, a matsayinka na alhaji, ka kyautata wa irin waxannan mutane, ka ja su a jika, ka tausaya masu.. idan zaka ba su shawara ko fatawa ka zavar masu mafi sauqi da dacewa da matsayinsu. Ka yi qoqari iyakar zarafi ka fi qarfin zuciyarka.

 Kada ka yi fushi da su ko kaxan, balle ka tsananta ko munana masu. Kai ko Magana zaka yi da su, kada ka kausasa murya. Domin alama ce ta rashin tausayi. Ya zo a cikin wani hadisi daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, cewa: “duk wanda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya raba da shi a xabi’ar tausayi to, haqiqa ya kwashe kasonsa na alheri. Duk kuwa wanda aka raba bai samu ba to, haqiqa ba sauran wani alheri da zai samu” (JT;2013/SA:1637).

 h- Sauran Al’amurra:

 Dangane da abin da ya shafi sigogi da yanayin shugabancin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ga mutane, a wannan lokaci na Aikin Hajji, akwai wasu abubuwa da dama da ya gudanar waxanda suka taimaka matuqa ga cin nasararsa. Abubuwan na iya taqaituwa a cikin waxannan ginshiqai:

i) Kyakkyawan Tsari:

 Tun a garin Mina, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yiwa Aikin Hajjinsa kyakkyawan tsari, ta hanyar kimtsa jama’a da aje kowa daga cikinsu wurin da ya dace da shi. A inda ya tsara su gwargwadon kusancinsu zuwa gare shi. Qarami na bi wa babba. Kamar dai yadda Abdurrahman xan Miswar ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gama yi wa mutane huxuba a Mina sai ya saukar da kowa inda ya dace da shi. Ya ce: “Muhajiruna su sauka a nan”. Sai ya nuna wani wuri dama ga alqibla ya ce: “Ansaru kuma a nan”. Ya nuna wani wuri hagu ga alqibla ya ce: “Sauran mutane su sauka a nan”. (SD:1951/SA:1719).

 A wata riwaya kuma aka ce: “Yana qare huxubarsa sai ya umurci Muhajiruna da su sauka a gaban masallaci, Ansaru kuma bayansa. Sannan ya saukar da sauran mutane (SAD:1957/SA:1724).

 Ka ji yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi. Amma a yau matsalolin da ke faruwa ga alhazzai a lokacin Aikin Hajji ba su da iyaka. Musamman na lokacin da suke gudanar da wasu ibadu. Ko idan za su bar wani wuri na ibada zuwa wani. sai ka ga ko wace jama’a na nuna son kai, da qoqarin halaka ‘yar uwarta. Duk tsarin da aka shata don cin nasarar ibadar, sai ka taras sun yi biris da shi, ko sun yi masa riqon sakainar kashi.

 Da ko wane alhaji zai yi qoqarin zama wani abin koyi ga sauran alhazai ‘yan uwansa ta hanyar yin kawaici, ya jinkirta da biyan buqatarsa, a lokacin da ta ci karo da wata maslaha ta sauran ‘yan uwansa alhazzai, to da musulmi sun ba duniya wani irin mamaki a fagen natsuwa, tsanaki da kyakkyawan Tsari.

ii) Kula da Hidimar Mutane:

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kula da hidimar mutane ainun, ya kuma qarfafa ta a wannan lokaci. Saboda tabbatar da ita ne ya yi wa amminsa Abbas iznin zama garin makka tsawon kwanakin da ya kamata ace ya yi a Mina don ya kula da Aikinsa na shayar da mutane ruwa. (SB:1734). Kuma a lokacin da ya zo Sallallahu Alaihi Wasallama ya sami masu wannan hidima sun yi kace – kace, suna ta aiki. Don ya qara masu qwarin guiwa, sai ya ce masu: “Ku dage ku yi ta yi, haqiqa kuna kan wani aiki na gari” (SB:1636).

 Sai godiya ga Allah. Domin kuwa irin wannan qwazo da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qarfafa, har yau bai gushe ba. Kullum masu sadaukar da qarfinsu da mafi yawan lokutansu ga hidimar alhazzai, da xora su a kan tafarki madaidaici, da kyautata masu, sai qara yawaita suke yi. Tattare da irin musgunawa da tsangwamar da suke haxuwa da ita wasu lokuta. Su ya kamata ayi ta fara’a da lale marhabin da su ko da yaushe. Amma duk wannan bata sa suka fasa ba. Alhamdu lillahi.

 Abin da ya kamaci ko wane alhaji shi ne, ya tuna faxar nan ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da yake cewa: “duk wanda bai gode wa mutane, to ko Allah ba ya gode wa”. Ta haka sai a gode da wannan aiki na alheri, ba tare da wata yankewa ba. Domin ko shakka babu godiyar zata qara masu kuzari da karsashi da nishaxi.

iii) Tsare Haqqoqa:

Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi matuqar kiyayewa da tsare haqqoqan mutane a wannan lokaci, don kada su tozarta. Misalin wannan shi ne: hana ummuna Aisha Allah ya qara mata yarda yin tsaye a gina masa xaki a Mina don ya shiga. Da ta xaura niyyar yin haka sai ya ce mata: “ba sai kin wahalar da kanki ba. Ai Mina gaba dayanta masauki ce tun ga waxanda suka gabace mu” (JT:881/ MH:1/638/ SN:4/398/ ZM:2/267).

Sai kuma qin kama wa masu hidimar shayar da alhazzai ruwan zamzam. Don tsoron kada haqqoqinsu su tozarta. Idan mutane suka rinjaye su. Sanadiyyar ganin har da shi Sallallahu Alaihi Wasallama cikin Aikin. Saboda kasancewar haka ya ce masu: “ba don tsoron kada mutane su takura ku ba, da na kama maku aikin nan. Har ma in xora taula a kafaxata” (SB:1636).

Wannan shi ne abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya koyar. Amma a yau, sai ga shi haqqoqan alhazzai, musamman masu xan qarfi daga cikinsu, na tozarta. Saboda buqatun wasu ‘yan tsiraru waxanda suka xauki duniya abin bauta. Haka kuwa na faruwa ne, saboda zaluntar alhazan da waxannan mutane ke yi ta fuskar rashin kula da hidimominsu, na masauki da zirga-zirgarsu; zowa da komawa.

Ba irin waxannan mutane kawai ba. wasu haqqoqan ma, na wasu alhazzan a hannun wasu alhazzai ‘yan uwansu ne, waxanda ba su fatar haxuwa da alherin Allah, suke tozarta. Ba tare da la’akari da alfarmar qarshe da suke kanta ba.

Saboda haka, wajibi ne a kan ko wane alhaji, ya yi qoqari iyakar zarafi, ya ga bai bi sawun waxannan mutane ba. ya yi gaggawa, matuqar yana da iko, ya kasance mai taimakon alhazai ‘yan’uwansa, ko da da kalmomin nasiha ne, da faxakarwa da bayar da agajin gaggawa.

iv) Kishin Gaskiya:

 Duk da kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama mai tsananin jinqayi da tausaya wa mutane. Ga kuma kunya marar misali (SB:3562/SM:2316).. hakan ba ta tava hana shi gaggawar bayyana abin da yake gaskiya, da yin jan ido ba idan an tava ta. Koda kuwa hakan zata sosa ran wanda suke tare. Dalilan da ke tabbatar da jaruntakarsa da namijin qoqari da jajancewarsa Sallallahu Alaihi Wasallama a kan duk abin da ya shafi gaskiya, suna da yawa matuqa. Ga kaxan daga ciki:

·   Xauki misalin karan tsayen da ya yi wa Falalu xan Abbas Allah ya yarda da su da hana shi ci gaba da kallon budurwar nan Bakhas’ama daya yi a kuma cikin dubu (SB:6228), wanda har hakan ta xauki hankalin amminsa Abbas Allah ya yarda da shi ya tambaye shi dalilin yin haka. Shi kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya karva masa da cewa: “Na ga hankalin saurayi da budurwa ne, ya kama hanyar shiga hannun shexan. Ban kuma san abin da zai faru ba (JT:885/HA:702).

·   Misali na gaba kuma shi ne, lokacin da matarsa Sallallahu Alaihi Wasallama safiyyah ta ga wanki. Ya zaci cewa ba ta yi xawafi ba ga xaki a ranar layya, ashe ta yi. Mun gabatar da tambayar da ya yi cewa, shin Safiyyah za ta riqe mu ne?

·   Sai kuma qin ba wa wasu sadaqa, tattare da cewa, sun roqe shi bisa dalilin cewa su majiya qarfi ne, da ke iya nema da guminsu (SAD:1633/SA:1438).

·   Ina jin babban misali a wannan vangare, duk bai fi bijire wa mafi yawa daga cikin sahabbansa Allah ya yarda da su da ya yi ba, waxanda ba su zo da dabbobin hadaya ba, ya qi ajiye Haraminsa duk da yake hakan tafi soyuwa ga reshi don zama abin koyinsu. Ya kuma gaya masu farar gaskiya garin da garin cewa: “Ku sani ni ba zan ajiye harami ba kamar yadda na umurce ku da ajewa. Saboda ni da hadayata a hannu” (SB:7367).

Saboda haka ya zama darasi ga ko wane musulmi, a gida da lokacin Aikin Hajji. Kada ya yarda son zuciyarsa ya hana shi bayanin abin da ya wajaba kansa na gaskiya da nasiha da faxakarwa, da horo da alheri da hani daga abin qi ko a gaban kowa. Domin kuwa kasa yin haka kasawa ce da rafashewa, ba kunya da kawaici ba. Domin kuwa Allah Ta’ala da kansa, ya faxi cewa ba ya jin nauyin faxar gaskiya.

 Saboda haka yin koyi da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne wajibi. Ya tabbata cewa: “Ya fi amaryar da ke cikin lalle kunya” (SB:3562) amma duk da haka, zo ka ga irin yadda yake fushi da xaukar mataki idan an tava Allah. Kamar yadda Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ta siffanta shi cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava xaga hannu ya bugi wani abu ba; ko matarsa ko hadiminsa. Sai fa idan an haxu ne a fagen jihadi. Haka kuma bai tava ko tunanin xaukar fansa, don an yi masa wani abu ba. Sai fa idan an yi wa wani hukunci na Allah karan tsaye. To nan kam zai yi fushi har ma ya xauki mataki, amma duk, saboda Allah maxaukakin Sarki” (SB:3560/SM:2328).

v) Rashin Gallaza Ma Wanda Ya Yi Kuskure:

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba mutum ne mai fushi da kaushin hali ba. Saboda haka ba ya gallaza wa wanda ya yi kuskure daga cikin sahabbansa Allah ya yarda da su. A maimakon haka, ya kan mayar da hankali ne, ga lurar da mutum idan ya fahimci ya jahilci abin ne ya kuma ci gaba da kula da shi har ya ga bai sake aikata kuskuren ba. haka zai zauna da shi, ko ‘yar fuska ba zai yi masa ba.

Misalin wannan shi ne, qin kula da qoqarin gano sahabin nan da ya mayar masa da magana da cewa: “Yanzu sai dai mu isa Arafa da sauran ruwan janaba a jikinmu? A maimakon haka ma sai kawai ya ci gaba da qoqarin lurar da su, tare da xora su a kan abin da yake shi ne mafifici, da kuma dacewa da su a lokacin. Yana mai cewa: “kun fi kowa sanin cewa, babu wanda ya kai ni tsoron Allah, da gaskiya da biyayya gare shi. To ya kamata ku lura da cewa, ba don na zo da dabbobin hadaya waxanda ba a yanke su sai lokacinsu ba, ai babu abin da zai hana in aje haramina kamar yadda ya kamata a ce kun aje. Yanzu kuma da na fuskanci abin da na ba baya ba zan zo da su ba don inyi Umra a tare da ku. (SB:7367).

·   Sai kuma rashin gallaza wa Falalu Allah ya yarda da shi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a kan waccan magana da mu ka faxa ta Bakhas’ama, da lokacin da kuma ya bi wasu ‘yan mata da ke gudu da kallo. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci bai yi wa xan’uwan nasa wata tsawa ko mugunyar magana ba. Sai dai kawai ya kama kansa a hankali Sallallahu Alaihi Wasallama ya xauke fuskarsa daga garesu. Tare kuma da ya maimaita hakan ba sau xaya ba. (SB:1513/SM:1218).

·   Bayan wannan kuma sai rashin tozarta mutanen nan biyu da suka yi salla a gidajen su. Basu yi sallah tare da mutane ba da suka zo masallaci. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya mayar da hankali ga lurar da su, tare da xauke masu nauyi, da kuma xora su a kan abin da ya fi dacewa da su aikata (JT:219/SA:181).

·   Wani misalin kuma mai qayatarwa shi ne, rashin musguna wa mutanen nan biyu da suka roqe shi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba su sadaqa, alhali kuwa su majiya qarfi ne, da ke iya ci da guminsu. A maimakon ma ya tozarta su Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya naxa su alqalai a kan matsalar. Wanda a qarshe, su da kansu suka haqura (SAD:1633/SA:1438).

 Ka kuwa san iyakar haquri da hikima ke nan.

 Wannan hali na Manzon Allah, ba ya zama xaya da na almajirai da malaman zamani. Waxanda fushi da miyagun kalamai su ne ado da kwalliyar nasiharsu, bayani kuma a wurinsu shi ne tozartawa da wofintar da mutane. Da sun harxe qafafu kuma, ko sun maqara makirifon cikin baki, ba abin da zaka ji yana fitowa bakinsu sai wautarwa da tura wa mutane haushi. Duk wannan wai da sunan karantarwa.

 A qarshe sai ka taras ba abin da za su qara wa mutane, illa ci gaba da aikata kurakuransu, da zama cikin vata. Kuma xaixaiku daga cikinsu, su yi ta da na sanin tambaya ko sauraren irin waxannan malamai da suka yi. Saboda sun tozarta su.

 To ka ga inda ma irin waxannan miyagun malamai, ba su tsoma bakinsu cikin al’amarin musulmi ba su da hakan ta fi zama alheri ga al’umma.

 Saboda gujewa irin wannan abu, wajibi ne duk wanda Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya ba shi ilimin addini, da damar haxa baki da jama’a, ya yi qoqari iyakar zarafi ya yi koyi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

vi) Tiryan – Tiryan:

 Wataqila, babban abin da ya taimaka wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ga cin nasara, a jagorancin da ya yi wa al’ummarsa a wannan lokaci na Aikin Hajji, duka bai fi kasancewar komai nasa tiryan – tairyan ya ke ba.

 Babu wani bayani da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai yi wa mutane, face ka taras da shi dalla – dalla, daki daki. Ya kan yi haka ne ta hanyar amfani da miqaqqen salo kuma sassauqa, mai armashi da kamsashi. Ta yadda jama’a ba za su qosa ba. Ko ana gabas suna yamma.

 Saboda haka sai gaba xayan mutanen da ke tare da shi, suka zama ala basiratin. Duk abinda suke buqata da gurin aiwatarwa ga shi ga fili sara. Kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne kawai makoma da makama, kuma shi ma ga shi gabansu ko da yaushe. Su kansu ibadodi na Aikin Hajji babu wadda aka voye masu. Ko aka kevance, sai wane da wane. Bayan kuma ga cikakken tsari kuma nagartacce, wanda akalarsa ke hannun mutum mafi nagarta da naqaltar jagoranci Sallallahu Alaihi Wasallama. Kai! Daidai da lokuta da wuraren ibadun an tantance su. Saboda haka kowa daga cikinsu ya san abin da ya kamata ya yi da wanda bai kamata ya yi ba.

 A kan haka kamata ya yi, a duk lokacin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya shugabantar da mutum ga wani abu da ya shafi Aikin Hajji, ta hanyar hulxa da alhazai, to ya riqa yi masu bayanin komai dalla dalla, yadda za su gane abin da yake nufi cikin sauqi.

vii) Nuna wa Mutane Qauna:

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mutum mai sauqin kai, mai marhaba da mutane, tare da yi masu shimfixar fuska, mai yalwantaccen qirji. Mutum ne da ba a tava ganin xan Adamu mai xabi’ar murmushi kamarsa ba. Ko Magana yake yi da sahabbansa, zai yi ta ne cikin wani irin nishaxi da fara’a tare kuma da sa raha a cikin maganganunsa, ta yadda farin ciki zai cika zukatansu (MSH:200,205/ ANWA:180,182,207).

 Misalin da ke tabbatar da irin qauna da so da rahar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya nuna wa mutane, tare da jawo su a jiki, a lokacin Aikin Hajji, shi ne abin da xan Abbas Allah ya yarda da su ya riwaito cewa: “Mun gabatar wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ‘yan qananan yaran ‘yan gidan Abdul Muxxalabi, muna kan wasu jajayen raquma. Sai ya shiga daddafa qaqafunsu yana cewa: “Ya ku ‘yan uwana kada fa ku yi jifa sai rana ta vullo” (SIM:3025/SA:2451).

 Saboda haka yana da matuqar kyau, a duk lokacin da ka haxu da mutane a lokacin Aikin Hajji, ka yi masu kyakkyawar gaisuwa cikin fara’a da nashaxi, da sakin fuska. Idan kuma wata Magana ta haxa ku, to su ji kalmominka kamar farar waina a ruwan zuma. Idan wani aiki ne kuma, ka yi shi cikin tsanaki da natsuwa. Da haka sai ka sami karvuwa gare su, har su amince da kai. Ka kuma sami wata irin lada a wurin Allah, wadda ba ta misaltuwa.

viii) Kamun kai da Kawaici:

 Kamar a ko wane lokaci na rayuwarsa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mutum mai kamun kai da kawaici da kamala, da kwarjini ciki da waje a lokacin Aikin Hajjinsa. Ta yadda babu wanda ya kama qafarsa a fagen tsafta da cika fuska. Ga dai gashin kansa nan Sallallahu Alaihi Wasallama ya tsaftace shi, ya kuma shafe shi da mai, mai qamshi (SB:4398). Kamar yadda kuma bai fara Aikin na Hajji ba, sai da ya shafa wani irin turare mai qamshi (SM:1189/ SD:1801). Ya kuma yi wanka a lokacin (JT:830/ SA:664) da kuma kafin ya shiga garin Makka (SM:1259).

 Bayan wannan kuma, a wannan lokaci, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mai kawaici da kwarjini. Ta hanyar nisantar duk wata Magana ko wani motsi, da bai dace ba (SN:3024/ SA:2827/ MA:1816). A sakamakon haka, sai mutane suka qara so da girmama shi, tare da shaya masa.

 Xaya daga cikin abubuwan da ke tabbatar da wannan magana, shi ne hadisin nan na harisu xan Amiru as-Sahmi Allah ya yarda da shi wanda yace: “Na ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da yake a Mina da Arafa, mutane sun kewaye shi ta ko ina. Duk qungiyar Larabawan da ta zo ta gan shi, ba za ta wuce ba sai gaba xayansu, sun ce: “kai wannan irin fuska mai hasken albarka fa! Suna ta farin ciki da wannan annuri nasa da suka yi tozali da shi (SAD:1742/HA:1532).

 2.6.1 Hannunka Mai Sanda:

 Saboda haka yana da matuqar kyau, musulmi ya kula da yanayin suturarsa. Kada ya yi banzar shiga. Ya kuma zama mai kamun kai daga yawaita wasa da barkwanci, tare da samun raha da nashaxi a cikin mu’amalarsa da mutane. Idan ya kiyaye waxannan, to mutane za su yi sha’awar haxa harka da shi, su kuma saurari duk abin da zai gaya masu a matsayin ilimi, har ma su kwaikwayi xabi’unsa.

 Kaxan kenan daga cikin abubuwa na kamala, waxanda suka bayyana ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin Aikin Hajji, da mu’amalarsa da mutane, a matsayin jagoransu. Kuma ta hanyarsu ne ya sami nasarar huda zukatan jama’a, har suka qaunace shi, suka kuma amince da shi. A matsayin wanda komai ya umurce su da shi za su aikata cikin gaggawa, har ma da goggoriyo. Haka kuma za su yi idan ya hane su wani abu. Wannan xa’a kuma, sun yi masa ita ne, cikin daxin rai da yarda da kwaxayin lada da tsarkin niyya.

To sai waxanda ke son musulmi su riqe su da hannu biyu a matsayin malamai kuma shugabanni, su auna xabi’unsu da halayensu, a kan ma’aunin waxannan xabi’u da halaye na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama su ga irin banbanci da ke tsakani. Su kuma sani, babu yadda za’a yi wanda bai siffantu da waxannan halaye na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya samu karvuwa a farfajiyar zukatan musulmi. Domin kuwa duk maso xan kwarai to dole ne ya auri isassa.

 BABI NA UKU

 3.0 Rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Tsakaninsa da Iyalinsa a Lokacin Aikin Hajji

 Wannan babi zai kalli yadda rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta kasance tsakaninsa da iyalinsa a wannan lokaci na Aikin Hajji. ta hanyar fitowa da yadda ya rungume su; mata da dangi da barwa, ba tare da nuna banbanci irin na son zuciya ba. Ya karantar da su hukunce – hukuncen Aikin Hajji, ya kuma koya masu a aikace, ta hanyar fita tare da su, da wasu abubuwa da dama.

  3.0.1 Shimfixa:

 Babu wani mahaluki a bayan qasa, ko shi waye, da ya kama qafar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a fagen kula da makusanta, tare da nuna so da qauna da kuma alheri da jinqayi zuwa gare shi. Waxanda suka rayu, suka kuma yi cuxanya da shi Sallallahu Alaihi Wasallama sun shedi haka. Har wani daga cikinsu ya siffanta shi Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa ya kasance: “Mafi kyautatawa da sadar da zumuta daga cikin mutane” (SM:1072/SB:3818,4954,5990).

 Babban abin alherin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sadar da zumuncin da ke tsakaninsa da makusantansa da shi, shi ne kiran su zuwa ga alheri. Da dagewa kai da fata, ga ganin sun kuvuta daga shiga wuta. Babban misalin wannan, shi ne: hawan dutsen Safa da ya yi a Makka, ya rinqa yi masu wa’azi, yana lurar da su irin haxarin da ke tattare da shirka. Yana cewa: “Ya ke Faximatu ‘yar Muhammadu, Ya ke Safiyyatu ‘yar Abdul Muxxallabi. Ya ku bani Abdul Muxxallabi. Ku sani ba ni iya shiga tsakaninku da Allah gobe qiyama. Amma idan abin duniya ne, duk abin da na mallaka naku ne. Ku roqa in ba ku” (SM:205) da kuma lokacin da mutuwa ta halarto amminsa Abu-xalib, inda ya ce masa Sallallahu Alaihi Wasallama: “Ya kai ammina! Yi qoqari ka ce La’ilaha Illal-lahu. Ka sani ita ce kawai kalmar da zan iya ceton ka da ita a wurin Allah” (SB:3884).

 Wannan a jumlace ke nan. To a lokacin Aiki Hajji, karimci da xa’a, kyautatawa da sadar da zumuncin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa ga iyalinsa, abubuwa ne da suka bayyana ta fuskoki da dama.

 Amma kafin mu fara kawo kaxan daga cikinsu xaya bayan xaya, ya kamata a lura da cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai ware iyalinsa, ya ba su wata kulawa ta daban, wadda bai ba sauran mutane ba. sai fa a vangaroran rayuwa, waxanda ba makawa ga yin haka a cikinsu. Amma baya ga wannan, babu wata kulawa da zai yi wa mutanen gidansa Sallallahu Alaihi Wasallama face sai ya yi wa sauran al’umma irinta.

 Kai!, irin shaquwar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi da iyalinsa, da irin kulawar da yake yi da su a wannan lokaci fiye da sauran mutane ta sa mafi yawan bayanai kan hukunce-hukuncen Aikin Hajji daga bakinsu aka riwaito su. Duk wanda ya yi nazarin sha’anin Aikin Hajji zai tabbatar da haka.

 Ina jin mafi bayyana daga cikin yanayin yadda rayuwarsa Sallallahu Alaihi Wasallama ta gudana tsakaninsa da iyalinsa a wannan lokaci zasu iya taqaituwa kamar haka:

  3.1 Manzon Allah Ya Karantar Da Iyalansa:

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kula matuqa da karantar da iyalinsa hukunce – hukuncen Aikin Hajji. Domin su sami sukunin gabatar da nagartacciyar ibada kuma karvavviya.

 Misalin wannan shi ne abin da yazo a cikin hadisin uwar muminai Ummu Salamata Allah ya qara mata yarda wadda ta ce; “Na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: Ya ku iyalin gidan Muhammadu ku xaura niyyar gudanar da Umra tare da Hajji” (MA:2659/ SIH:3922).

 Sai kuma cewar daya yi wa Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda a lokacin da ta ga wanki, kafin ta yi xawafi ga xaki: “Kina iya aikata duk abin da alhazzai ke aikatawa amma, kada ki yi xawafi ga xaki” (SM:1211). Da kuma abin da ya ce wa qannensa matasan ‘yan gidan Abdul Muxxalabi: “kada ku yi jifa har sai rana ta fito” (JT:893).

 Wannan karantarwa kuma, ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ga iyalinsa, ba ta taqaita a kan faxa masu makamar al’amurran ibada ba. A’a, har tattaunawa ya kan yi da su, ya kuma saurari tanbayoyinsu, ya karva masu. Kamar yadda Sayyida Hafsatu Allah ya yarda da ita ke cewa a cikin wani hadisi: “Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurce mu; matansa, mu aje harami a shekarar Hajjin ban kwana. Sai nace masa: To kai fa? me zai hana ka ajiye? Sai ya ce: ‘kin manta bayan na shirya gashin kaina, sai da na yi wa dabbobin hadayata layar takalmi? Ai tun da nazo da hadaya ba damar in ajiye sai hadayar ta kai lokacinta”. (SB:4398). A wata riwaya kuma aka ce, cewa ta yi: “Me ya sa za mu aje Harami bayan Umra alhali kai baka ajiye naka ba? “(SM:1228). Sai kuma hadisin Sayyidina Ali Allah ya yarda da shi wanda ya ce: ‘Abbas Allah ya yarda da su ya ce: Ya Manzon Allah don me ka naxe wuyan xan amminka haka? Sai ya karva masa Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa: “na ga shexan ne ya shiga tsakanin saurayi da budurwa. Ban kuma san yadda za a kwashe ba (JT:885/HA:702).

 Wannan kenan. Amma ka ga a wannan zamani namu, maimakon ayi koyi da Manzon Allah ta wannan fanni sai aka bar guguwar jahilci na ta xaukar hankalin mutane da dama. Saboda kasancewar ‘yan tsiraru ne daga cikin magidanta ke kula da karantar da iyalinsu hukunce-hukuncen abubuwa kafin lokacin aikata su ya riske su. Kada kayi maganar wayar masu da kai a kan hikimomi da asirran da ke qunshe a cikin ibadodin Aikin Hajji. Ko shakka babu wannan abin baqin ciki ne ga al’ummar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

 Saboda haka, wajibi ne ko wane musulmi ya yi qoqarin zama cikin sahun masu koyi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan fage. Don hakan ta xaukaka darajarsa gaban Ubangijinsa, tare da lissafa shi daga cikin mutanen arziki. Kamar dai yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ma fi alheri daga cikinku, shi ne wanda ya fi kowa sadar da alheri ga iyalinsa. Ni kuwa ni ne shafe zane, a cikinku, a fagen sadar da alheri ga iyali” (JT:3895/SA:3058).

 Lalle ne duk musulmin qwarai ya kula da wannan aiki da kyau. Domin kuwa shi Allah Ta’ala Ya xora wa alhakin kula da iyalinsa, zai kuma tambaye shi gobe qiyama a game da su. Kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “ko wane mutun makiyayi ne, kuma Allah zai tambaye shi, a kan abin da aka ba shi kiyo… Namiji shi ne makiyayin iyalinsa kuma za a tambaye shi a kansu” (SB:2553).

 Bayan wannan kuma, sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya buga kyakkyawan misalin yadda ya kamata a kula da wannan aiki. Ta hanyar fara karantar da iyalinsa na kusa kafin ya iso ga sauran mutane. Ya kuwa yi haka ne Sallallahu Alaihi Wasallama saboda biyar umurnin Ubangijinsa mai girma da xaukaka wanda Ya ce masa:

 “Kuma ka yi gargaxi ga danginka mafiya kusanci” (26:214).

 3.2 Kuma Ya Tarbiyyantar da Su:

 Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi matuqar qoqarin ganin ya tarbiyyantar da iyalinsa a kan ibadodin Aikin Hajji. Ta hanyar shagaltar da su da wasu ayyukan ibadar tun kafin a fito don gudanar da ita. Kamar yadda Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ke cewa; “Ni ce wadda Annabi ya sa ta xaura wa dabbobin hadayarsa layun takalma, tun kafin ya xaura harama” (SB:2553).

 Tunda kuwa haka ne, babu abin da ya kamaci ko wane alhaji, irin ya yi koyi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta hanyar shagaltar da kansa da iyalinsa da waxansu ayyuka na share fagen Aikin Hajji tun lokacin bai yi ba, ko a isa wuraren ibadun. Domin hakan zai sa zukatansu zama faxake da al’amarin.

 Ba wannan kawai ba, yana da kyau matuqa ma, ya bayyana masu manufofin ibadar tare da laqanta masu makamar hukunce – hukuncenta da faxakar da su a kan lada da falalar da ibadar ta qunsa. Ta yadda hakan za ta sa su kula da ladubban ibadu, da shirya ma wahalhalun dake ciki, da tanadin duk abubuwan da za su taimaka masu a kan cin nasarar gudanar da aikin, tun kafin ranar tafiya.

 Ko shakka babu, idan haka ta samu, to an gama kama hanyar gudanar da nagartaccen Aikin Hajji kuma karvavve.

  3.3 Ya Kuma Kuvutar da Su:

Allah Ta’ala ya wajabta Aikin Hajji a kan duk wanda ke da iko daga cikin bayinsa. Ya ce:

“Kuma akwai Hajjin Xakin domin Allah a kan mutane, ga wanda ya sami ikon zuwa gare shi” (3:97).

 Saboda haka babu wani musulmi na qwarai, da ke da hali, face yana jin cewa akwai wani wajibi a kansa wanda har abada hankalinsa ba zai kwanta ba idan bai ji ya kuvuta daga gare shi.

 Duk wanda ya nazarci tarihin rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci na Aikin Hajji, zai ga irin yadda ya himmatu a kan ganin ya agaza wa iyalinsa sun kuvuta daga wannan nauyi, ta hanyar xauke shi. Abubuwan da ke tabbatar da wannan Magana suna da yawa. Ga kaxan daga cikinsu:

·   Saboda tabbatar da wannan manufa ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, da ya xaura niyyar zuwa Aikin Hajji bai bar ko xaya daga cikin matansa a gida ba. (ISAD:1722/ SA;1515/ ZM:2/106/ SN:4222). Haka kuma bai bar mai rauni daga cikin mutanen gidan nasa ba Sallallahu Alaihi Wasallama (SB 1678,1680/SM:1293).

·   Bayan wannan fita kuma, da Aikin Hajjin ya kawo jiki, sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya miqe tsaye kuma, ga ganin babu wanda wani abu ya hana shi gudanar da ibadar, har da kuwa marasa lafiya daga cikinsu, bai qyale ba. Misalin wannan shi ne shiga wurin ‘yar amminsa da ya yi Dhuba’atu ‘yar Zubairu Raliyallahu Anha da bai ganta cikin shirye – shiryen kama ibadar ba. Ashe ba ta lafiya. Da ya shiga wurin ta sai ya ce mata: “Ya ke ‘yar uwata, me zai hana ki gudanar da Aikin Hajji? Sai ta karva masa da cewa: “ai ba na jin sarai” Sai ya ce mata: “A’aha tashi ki xaura harama. Amma ki qudurta cewa duk inda kika kasa, za ki dakata a nan” (SB:5089/SIM:2936/SA:2375).

Amma abin mamaki duk da wannan koyarwa ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, sai yau, ka ga mata da yawa masu sauran jini a jika suna qin gudanar da aikin Hajji, tattare da kuwa suna iyawa. Ba su da wata hujja da zasu kafa akan haka.

 Saboda haka, abin da ya kamaci duk wanda Allah cikin rahamarsa ya hore masa, shi ne ya yi koyi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta hanyar yin gaggawar kama hannun irin waxannan bayin Allah da ke tare da shi, ya yi tsaye ya ga ya kai su. Domin kuwa ba a san abin da yau da gobe za su haifar ba. Wuri na qurewa, dama na kubcewa. Duniya kuwa kamar hawainiya ce sarkin rikixa. A kan haka ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya zaburar da al'umma, tare da jan hankalinmu a kan gaggauta gudanar da Aikin Hajji. Inda yake cewa: "duk wanda Allah Ya ba shi halin zuwa Hajji, to ya gaggauta. Domin rashin lafiya kan iya riskarsa, ko vacewar abin hawa, ko wasu buqatu" (SIM:2883/NA:2331) A wata riwaya kuma ya ce: "ku gaggauta gudanar da aikin Hajji. Domin xayanku bai san lalurar da ka iya vijiro masa ba." (MA:2868).

 Kuma ka tuna ya kai musulmi, duk wahalar da zaka yi ta wannan fuska, ba zata tafi a banza ba. Allah zai saka maka da lada mai yawa. Kamar yadda hadisin matar nan da ta zo wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da qaramin yaro yake nunawa. Domin ta tambaye shi cewa: "ko Aikin Hajji ya na wajaba a kan wannan yaro? "Shi kuma Sallallahu Alaihi Wasallama ya karva mata da cewa: "Eh, Amma ke ki ke da lada" (SM:1336).

 Ladar da magidanci zai samu idan ya tafi da iyalinsa ta fi ta wannan mata. Saboda ya taimaka masu sun kuvuta daga wani nauyin wajibin da yake akan su. Waccan mata kuma, dama Aikin Hajjin bai wajaba kan yaronta ba.

 3.4 Kuma Ya Zaburar da Su:

Annnabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance a wannan lokaci, yana zaburar da iyalinsa a kan Aikin xa’a tare da qarfafa masu guiwa a kan guzurin Aikin alheri. Misalin wannan shi ne; lokacin da ya taras da danginsa na wajen Abdul Muxxalabi, na jawo ruwa daga cikin rijiyar zamzam, suna shayar da mutane. sai ya zaburar da su da cewa: “Ku dai dage ya ku Banu Abdul Muxxalabi. Ku dage. Ba don tsoron mutane su rinjaye ku ba, da na kama maku” (SIM:1218) A wata riwaya kuma aka ce, cewa musu ya yi: “Ku dai dage. Aikin nan da kuke yi tabbas mai kyau ne. Ba don tsoron mutane su rinjaye ku ba, da na kama maku, har ma in xauki taula a wuyana” (SB:1636).

 Ba wannan kawai ba. Don tsananin zaburarwa da qarfafa guiwa, har dama ya bai wa amminsa Abbas Allah ya yarda da shi ta ci gaba da kasancewa a garin Makka tsawon kwanakin da ya kamata ya yi a Mina. Don kawai kada wannan Aikin alheri ya wuce shi, shayar da alhazan kuma ya gamu da tangarxa. (SB:1745).

 Ka ga wannan koyarwa ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na nuna mana cewa, Lokacin Aikin Hajji wani lokaci ne da ke buxe qofofin saka jarin alheri da kyautata wa musakai da masu qaramin qarfi. Ko banza kuwa duk sadda ka zo zaka same su can birjik kamar janfa a Jos.

 Saboda haka dama ce samamma ga duk wanda ke son ayyukansa na alheri su rivanya, ma’auninsa ya nauyaya albarkacin waninsa. Ga wuri nan ga kuma waina. Sai ya sha xamarar taimakon baqin Allah, da tarbiyyantar da mutanen gidansa a kan yawaita ayyukan da ke kusantar da su ga Ubangijinsu. Ya nuna masu alheri, tare da sawwaqe masu hanyar aikata shi. Ya kuma qarfafa masu guwayu a kan kyautata ma mabuqata. Domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “duk wanda ya yi kira zuwa ga wani aiki na shiriya, to Allah zai ba shi irin ladar da zai ba duk wanda ya karva kiran nasa, ba kuma tare da an tauye masu ladar tasu da komai ba.” (SM:2674) Haka kuma an riwaito ya ce: “Duk wanda ya yi nuni ga wani abu na alheri, yana da irin ladar wanda ya aikata shi” (SM:1893) (JT:2670/HAS:2151).

 Wannan shi ne abin da ya kamaci ko wane musulmi. Ka da ka kuskura ka koya wa iyalinka varna da vata. Ko ka yi masu wasiyya da aikata wani abin da babu lada cikinsa sai zunubi. Ko ka sauqaqa masu hanyar aikata wani abin qi. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi hani daga haka; inda ya ce: “Duk wanda ya yi kira zuwa ga wani aiki na vata, za a ba shi zunubi daidai da na wanda ya karva kiran nasa, ba tare da an tauye zunubin nasu da komai ba” (SM:2674).

  3.5 Ya Kuma Nemi Gudunmawarsu:

 Wani abin kuma shi ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya nemi gudunmawar iyalinsa Allah ya yarda da su ta hanyar aiki da su tare da wakilta su ga waxansu al’amurra.

 Abubuwan da ke tabbatar da haka sun haxa da:

·   Ba wa matarsa Aisha Allah ya qara mata yarda umurnin tumqa igiyoyin da za a rataya wa dabbobinsa na hadaya, ta hanyar amfani da wani gashin raqumi da ke wurinta tun a Madina, kafin a xauki harami (SB:1696,1704,1705).

·   Sai kuma umurnin da ya bai wa xan Abbas Allah ya yarda da su a wayewar garin jifar Aqaba, yana kan taguwarsa Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa: “Tsinto mani ‘yan tsakwankwani” Xan Abbas ya ce; “Sai kuwa na tsinto masa guda bakwai daidai jifa” (SIM:3029/SA:2455).

·   Haka kuma umurnin Sayyidina Ali Allah ya yarda da shi da iyar da soqe raquman da suka rage na hadayarsa Sallallahu Alaihi Wasallama, da kuma yin sadaqa da namansu da sauran amfaninsu na daga cikin irin wannan neman gudunmawa. (SB:1718,2299/SM:1317).

·   Sai kuma neman gudummawar ‘ya’yan amminsa da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama, a lokacin da ya same su suna shayar da mutane ruwan zamzam. Ya ce wa Amminsa Abbas Allah ya yarda da shi: “Ni ma ba ni in sha. Ya kuwa ba shi ya sha’ (SB:1635) Hadisin xan Abbas xin Allah ya yarda da shi kuma na qara tabbatar da wannan Magana. Inda ya ce: “na bai wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ruwan zamzam, ya sha a lokacin da yake tsaye” (1637:SB).

·   Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya nemi gudummawar Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ta shafa masa wani irin turaren indiya mai daxin qanshi, da irin nasu na larabawa (al-Miski) a jikinsa da kuma kansa don shirin xaukar harami. Kuma waxannan turaruka, kamar yadda ta bayyana da kanta su ne mafi qanshin abin da ake iya samu a wancan lokaci. (SB:1754/SB:5930/SM:1189).

·   Wannan koyarwa ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta isa hujja a kan wanda ke neman gudummawar wasu mutane manisanta, ga irin waxannan ayyuka alhali ga makusantansa kamar bakin tsintsiya.

·   Ba Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama kawai ba, har annabawan da suka gabace shi, wannan ita ce sunnarsu, ina nufin neman gudunmawar makusanta, ga irin waxannan abubuwa muhimmai. Dubi irin yadda Annabi Musa Alaihis Salam ya roqi Ubangijinsa da cewa:

“Kuma ka sanya mani wani mataimaki daga mutanena. Haruna xan uwana. Ka qarfafa halittata da shi. Kuma ka shigar da shi a cikin al’amarina. Domin mu tsarkake Ka da yawa. Kuma mu tuna Ka da yawa”. (20:29-34)

 Kuma dubi irin yadda Annabi Luxu Alaihis Salam ya yi gurin samun makusanta, don su kama masa yaqi da mutanensa, lokacin da cutawarsu ta kai masa mashafar turare. Ga abin da Allah Ya labarto mana akansa:

“Ya ce: “Ina ma dai ina da wani qarfi game da ku, ko kuma ina da goyon baya daga wani yanki mai qarfi!”. (11:8).

 Annabi Luxu ya faxi haka ne saboda ba shi da dangi a cikin mutanen. Wannan shi ke nuna mana muhimmancin makusanta, musamman idan suka gamsu da kiran malami ko shugaba mai shiryar da mutane. Taimakonsu zai zamo mai qarfi da qarfafawa a gare shi. Wanda ko duk ya yi biris da makusantansa, ya haramta masu samun albarkar wani aiki na alheri, ta hanyar saka hannayensu ciki, zai sami kansa shi kaxai ke nan. Hannu xaya ko ba ya xaukar jinka.

  3.6 Kuma Ya Ba Su Kariya:

 Karakainar fitinu wani abu ne da ke dugunzuma zukata ya tayar da hankulla. Duk kuwa wurin da aka sami haxuwar mutane da yawa, musamman maza da mata, to shexan ya sami wurin girka dumarsa don tayar da fitina. Musamman irin wadda mata ke haifawa.

 Saboda haka ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, a wannan lokaci na Aikin Hajji, ya yi tsaye tsayin daka a kan ganin ya ba wa iyalinsa cikakkiyar kariya daga irin wannna fitina. Kada ta fara, kada kuma su faxa mata.

 Babban abin da ke tabbatar da haka shi ne juya kan Falalu xan Abbas Allah ya yarda da su daya yi Sallallahu Alaihi Wasallama don xaukar hankalinsa da wata budurwa Bakhas’ama ta yi. Ya kuwa yi haka ne don ya kuvutar da su, tare da ba su kariya daga sharrin shexan, kada ya kunna wa zukatansu wuta. Kamar yadda ya zo a cikin hadisin Ali Allah ya yarda da shi wanda ya ce: “Abbas, da ya ga haka, sai ya ce: ya Manzon Allah me ya sa ka naxe wuyan qaninka? Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa, ai na ga saurayi ne da budurwa sun kama hanyar shiga hannun shexan. Ina tsoron abin da zai iya faruwa ga resu” (JT:885/HA:702). A wata riwaya kuma aka ce cewa ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama: “Na ga saurayi ne matashi, da budurwa matashiya suna qyaran juna. Sai na ba su kariya daga sharrin shexan” (MA:564).

·   Sai kuma umurnin da ya ba wa matansa Sallallahu Alaihi Wasallama na yin lulluvi su rufe fuskokinsu a lokacin duk da maza suka tinkaro su. Wannan kuwa tattare da kasancewarsu, (Matan nasa) haramun ne ga mazajen. Sai idan sun wuce su, Sannan su buxe fuskokin nasu (SAD:1833).

·   Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci matansa da su nisanci sassarqewa da maza a lokacin xawafi. Tattare kuwa da kasancewar haka ake xawafin maza da mata kuma haka su matan nasa Allah ya yarda da su suke yi. Abin da ke tabbatar da wannan kuwa, shi ne, lokacin da Ummu Salamata Allah ya yarda da ita ta koka masa cewa ba ta jin sosai. Sai ya ce mata: “To ki yi xawafi bayan sahu mana, kina kuma bisa abun hawa”. (SB:1619). A wata riwaya kuma aka ce, ce mata ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama: “Bari sai an tayar da sallar subahin sai ki hau kan raquminki ki yi xawafi, a daidai lokacin da mutane ke sallah. Haka kuwa ta yi. Ba ta yi sallar subahin xin ba ita har sai da ta qare xawafin” (SB:1626).

Haka kuma hadisin Malamin nan xan Juraiju na qara fitowa da wana mas’ala fili. Domin cewa ya yi: Malam ‘Axa’u ya bani labari cewa: Malam xan Hishamu ya hana mata gudanar da xawafi tare da mazaje lokaci xaya. sai Malam Axa’un ya ce masa don me zaka hana su, alhali kuwa ta tabbata cewa tare da maza ne matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama suka gudanar da xawafi?. Juraiju ya ce: Sai ni kuma nace masa: kana nufin bayan an wajabta masu hijabi ko kafinsa?. Sai Axa’un ya karva da cewa: Eh, tsakani na da Allah bayan wajabta masu hijabi ne. Juraiju ya ce sai na sake ce masa: To kana nufin suna sassarqewa da maza ne a lokacin xawafin? Sai ya karva da cewa: A’a ba sassarqewa da maza suke yi ba. Domin Aisha Allah ya qara mata yarda kan yi xawafi ne nesa ga maza. Akwai ma lokacin da wata mata ta ce mata: ranki ya daxe uwar muminai mu je mana mu sumbanci Hajrul –Aswad. Sai ta ce mata: Ko kusa ni kam ba zan je ba.

 Abin da dai ya tabbata inji shi, shi ne su matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sun kasance sukan fita ne a cikin dare, tare da vatar da kama da sawu. Su tafi su gabatar da xawafinsu, daidai lokacin da wasu maza kan yi. Illa dai idan sun iso masallacin sukan saurara ne, har sai an fitar da mazan tukuna.

 Ya ce kuma, ko lokacin da mukan tafi wurin Aisha Allah ya qara mata yarda ni da Ubaidatu xan Ummaru a lokacin da take kusa da Subairu mukan taras da ita ne cikin wata bukka, irin ta mutanen Turkiyya, wadda kuma ta ke da labule. Amma dai na hange ta sanye da wani mayafi na qasar waje (SB:1617).

A wata riwaya kuma cewa ya yi: “Na ga wani mayafi mai fatsi – fatsi a kanta, a lokacin ina yaro qarami” (MAR:9018).

Bayan wannan ma, ana iya fahimtar wannan hani na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ga matan nasa, daga cewar da Aisha Allah ya qara mata yarda ta yi ma wata baiwarta, da ta yi xawafi ga xaki har sau bakwai, ta kuma sumbanci Rukuni sau biyu. A wata riwaya sau uku. Sayyida Aisha ta ce mata: “Allah ba zai baki ladar komai ba! Allah ba zai ba ki ladar komai ba. tunda sai da kika yi gogayya da maza tukuna. Ai kamata ya yi ki yi kabbara kawai ki wuce” (SK:5/81).

 Sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ta yi wa wannan mata haka ne, saboda ba ya yiwuwa, a matsayinta ita, na matar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta ga ana yin wani abu da ya hana, ba tare da ta yi Magana ba. Ko ta hana wani abu da aka aikata a gabansa bai ce uffan ba. Duk wannan ba ya yiwuwa gare ta Allah ya yarda da ita.

Wani abin kuma shi ne rashin shari’antar wa matan sassaka a xawafin xaki, da sa’ayi mai tsanani a daidai tsakiyar al-Masil tsanaknin Safa da Marwa da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin hakan za ta ba su kariya daga motsa jikinsu sosai don kar su xauki hankali. Abin dake tabbatar da wannan shi ne zancen Aisha Allah ya qara mata yarda da ta ce: “Ya ku taron mata, ku sani Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai shar’anta maku sassaka a lokacin xawafi ga xaki ba. Ku yi koyi da mu” (SK:5/84) a wata riwaya kuma aka ce cewa ta yi: “Ashe ba mu ne ya kamata ku yi koyi da mu ba? To ku sani, ba a shar’anta maku sassaka a xawafi, ko tsakanin Safa da Marwa” (MIAS;12951).

·   Bayan wannan kuma sai jan hakalin matan nasa Sallallahu Alaihi Wasallama da yayi tare da xora su kan tafarkin zama cikin gida ba tare da fita ba, bayan qare Aikin Hajji. Haka kuwa ta tabbata ne a cikin wata magana da ya yi da su a Hajjinsa na bankwana in da ya ce: “Daga yanzu kuma ko waccenku ta lizimci xakinta” (SAD:1721/SA:1515).

Wannan shi ne matakin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya xauka don kuvutar da iyalinsa daga faxawa cikin fitina.

 Amma sai ga shi yau, saboda kantar jahilci a qwaqwalen mutane lokacin Aikin Hajji ya zama wata dama ga masu raunin imani da qarancin haquri, ta aikata wasu miyagun abubuwa. Saboda haka ya zama wajibi ga duk wanda ke tsoron Allah, ya kula da iyalin gidansa ta hanyar kuvutar da su daga faxawa hannun mutane waxanda basu jin kunyar Allah Subhanahu Wa Ta’ala.

Yin haka wajibi ne musamman a cikin wannan gari mai alfarma. Ayi hanquri matuqa a ba Allah Subhanahu Wa Ta’ala matsayin da ya dace da shi. Koda kuwa haka za ta sa, wasu mustahabbai daga ibadodin Aikin Hajjin, waxanda suka kevanta da wasu wurare da lokuta, su faxi. Babu wani laifi idan sun faxi. Babu laifi, domin kuwa a shari'a varna ake fara kawarwa ta ko wane hali, kafin a yi qoqarin jawo amfani ko wane iri ne.

Bayan wannan kuma, tsare wannan aiki ga magabaci a cikin iyalansa, kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi na qara sa muradinsa na kula da kiyon da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya bashi ya qara cika. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: "Babu wani bawa da Allah zai damqa masa kula da wata jama’a, ya ha’ince su (ta hanyar rashin kula da su da kyau kamar yadda ya kamata) har ranar mutuwarsa ta zo, face Allah Ya haramta masa shiga aljanna" (SM: 142)

 3.7 Ya Yi Masu Gargaxi

 Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mai tsananin son ganin ya tsarkake iyalinsa daga ko wane irin savo da varna da abubuwan qi. Saboda haka yake tsaye haiqan ga yi masu gargaxi, da kuma hana su aikata laifuka, da hannunsa. Da zarar ya ga wani daga cikinsu ya kama hanyar shiga hannun shexan, nan take ne Annabi Subhanahu Wa Ta’ala zai kevo shi ya dawo da shi kan hanya.

 Misalin wannan shi ne abin da ya gudana tsakaninsa da falalu xan Abbas a lokacin da ya qura wa budurwar nan Bakhas’ama ido. Wadda ta zo domin ta yi fatawa ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Da ganin haka kuwa sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya shiga tsakani, ya hana shi sake kallon ta, a aikace.

 Da kuma dai har wa yau, abin da ya faru tsakaninsa da shi Falalun Allah ya yarda da shi na hana shi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ci gaba da kallon wasu ‘yan mata da ke kaiwa da komowa (SM: 1218)

 Wani gargaxin da hani kuma, a cikin wata irin sura mai hikima da ya yi wa iyalin nasa Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne buga misali da ya yi da su, da nufin mutane su xauki darasi daga gare su. Ya yi wannan ne a cikin wata huxuba da yayi wa mutane a filin Arafa. Inda yake cewa: “Ku saurara! Daga yau na kashe duk wata magana ta jahiliyya. Duk wani jini da ake bi bashi tun a wancan lokaci na saryar da shi. Farkon kuwa, jinin da na kashe maganarsa, shi ne jinin xan uwana xan Rabiata wanda Huzailu ta kashe, daidai lokacin da ake shayar da shi a bani Sa’ad. Kuma farkon ribar da zan saryarwa, ita ce ribarmu, ta wajen Abbas xan Abdul Muxxalabi. Daga yau ba wannan Magana, na kashe ta. Kuma ta mutu mututus”.

 Allahu Akbar, ka ji maza. Amma sai gashi a yau ana ji ana gani, abubuwan da suka yi hannun riga da koyarwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na ta faruwa a cikin iyali, babu mai cewa qala daga cikin magabatanmu. Tattare kuma da ana cikin lokacin gudanar da Aikin Hajji.

 Babu ruwan kowa, koda kuwa cikin waxannan abubuwan da ke faruwa akwai abin da ke iya vata Aikin Hajjin nasu, ko ya yi masa tasgaro.

 A gaban idon irin waxannan uwayen gidaje, mata daga cikin iyalin nasu, ke kwave-kwave irin waxanda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya qi kamar, tsiraici da fasiqanci, da cuxanya da mazajen da ba halas a gare su ba, da sauran su.

 To, fa ya kamata a faxakar, Allah Subhanahu Wa Ta’ala na yin rahamarSa ne ga bawan da ya tsare kansa kamar yadda Ya wajabta masa. Ta hanyar kare iyalinsa daga faxawa tarkon shexan, ta fuskar aikata miyagun ayyuka. Ya kuma dage kai da fata a kan horonsu da aikata alheri da nisantar sharri ko wani iri ne.

 3.8 Annabi Ya Tausaya Masu

 A wannan lokaci na Aikin Hajji, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mai matuqar tausayawa iyalinsa baki xaya. Tare kuma da mayar da hankali da kusantar da masu rauni daga cikinsu. Ya kan zavar masu abu mai sauqi a duk lokacin da buqatar hakan ta kama. Tare da bayar da fifiko ga wanda buqata ta yi wa zoba, ta hanyar nema masa mafificiyar mafita.

 Akwai dalilai da dama da ke iya tabbatar da wannan magana. Amma ga kaxan da ga cikin su:

• Zavar wa matansa Sallallahu Alaihi Wasallama yanayi mafi sauqi daya ya yi a lokacin Hajji ta hanyar umurninsu da aje Harami. Kamar yadda hadisin Sayyida Hafsatu Allah ya yarda da ita ke tabbatarwa, cewa: “Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci matansa da aje Harami a lokacin Hajjin bankwana” (SDB:4398)

• Sai kuma ware masu rauni daga cikin iyalin nasa da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da za a bar muzdalifa, ya turo su kafin kowa. Kamar yadda ya zo a cikin hadisin Falalu xan Abbas Allah ya yarda da su wanda ya ce: “Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci masu rauni daga cikin banu Hashim da su baro tun cikin dare, kafin sauran mutane” (SM: 3034/SHA: 2340/SB: 1678).

• Bayan wannan kuma sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ta ce: “Da muka isa muzdalifa, sai uwar muminai Saudatu Allah ya yarda da ita ta nemi iznin annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan ta gabata kafin sauran mutane su danno. Saboda kasancewarta mace mai nauyin jiki. Sai ya bata dama Sallallahu Alaihi Wasallama ta xan riga sauran jama’a tasowa. Mu kuwa, muka jira har sai da gari ya waye. Sannan muka taso tare da shi” (SB: 1681). Sai kuma hadisin Sauban, wanda ya ce: ya shiga wurin uwar muminai Ummu Habiba Allah ya yarda da ita bayan ta qaraso, sai ta ba shi labarin cewa ai, annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya haxa ta da wasu ne suka taso tun da dare kafin sauran mutane” (SM: 1272)

• Sai kuma umurcin da ya ba matarsa Sallallahu Alaihi Wasallama wato: Ummu Salama Allah ya yarda da ita a lokacin da ta koka masa cewa fa ita, tana jin jiki. Sai ya ce mata: “To ai kiyi naki xawafin nesa ga mutane kuma a kan abin hawa (SB: 464).

• Haka kuma ya ba amminsa Abbas xan Abdul Muxxalabi Allah ya yarda da shi izinin ci gaba da kasancewa a garin makka tsawon kwanaki da ya kamata a ce ya yi a mina. Domin hakan ta ba shi damar shayar da mutane ruwa cikin sauqi” (SB: 1634)

 Duk da yake alhazzan da ke tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci, yawansu bai taka kara ya karya ba, idan aka yi la’akari da irin xinbin mutane da ke zuwa Aikin Hajji a yau, amma kuma dluk da haka su ne mafiya qarfin imani da xaukaka da natsuwa a cikin wannan al’umma. Amma kuma tattare da waxannan siffofin annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tausaya wa iyalinsa daga cikinsu ya yi masu irin wannan sassafci.

 To idan kuwa har Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai yi haka a wancan lokaci, lalle kuwa buqatar da masu manyan shekaru da mata da qananan yara su ke da ita zuwa ga tunatarwa da sawwaqa al’amurra, a wannan zamani namu ta zarce ta waxancan. Domin matsayin ba xaya ba. Kuma ko shakka babu ya kamata a kula da su matuqa.

 Domin kuwa qaruwar yawan alhazzai a wannan zamani bai daxa su da komai ba, sai qaruwar jahilci, domin mafi yawansu imani da tsoron Allansu bai taka kara ya karya ba balle a yi zaton samun wani tausayi daga gare su zuwa ga takwarorinsu alhazai.

 Saboda haka yana da kyau matuqa mutum ya kula da iyalinsa. Ta hanyar sauqaqa masu al’amurra ko da yaushe, da zavar masu abin da ya fi dacewa da su a fagen hukunce hukuncen shari’a da a dokokinta. Domin kuwa haka shi ne mafi alheri ga mutum, da qara bunqasa rumbum ladarsa.

 3.9 Sannan Ya Nuna Haquri da su

 Bayar da misalai waxanda za su iya tabbatar da kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama mai haquri da iyalinsa a wannan lokaci na Aikin Hajji abu ne da ba sai an kai ruwa rana ba, ko sai an wani dogon tunani ko zuzzurfan batun zuci. Dalili kuwa, ba su da wani malami kuma a lokaci xaya mai kula da al’amurransu sai shi.

 Ka kuwa san duk wanda irin wannan nauyi ya hau kansa dole ne ya zama damo sarkin haquri; Ko kuma a yi ba tulu ba ruwan daxi. Musamman idan aka yi la’akari da kasancewar akwai masu manyan shekaru da nauyin jimi a cikin iyalin nasa Sallallahu Alaihi Wasallama kamar uwar muminai Saudatu (SB: 1681). Akwai kuma marasa lafiya, da ke fama da laulayi kamar Dhuba’atu (SB: 5089) da kuma Salmatu (SB; 464) Akwai kuma mata da yawa kamar ‘yarsa Faximatu (SM: 1218). Ga kuma gaba xayan sauran matansa Sallallahu Alaihi Wasallama (ZM: 2./106/SN: 4/222). Ga kuma matasan ‘yan gidan Abdul Muxxalabi da ‘yan gidan Hashimu (MA: 3013).

 Kai ka san duk wanda bai kai gwarzo a fagen haquri ba, ba zai iya rungume wannan taron jama’a ba. Amma sai ga shi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya iya da su ta hanyar wani irin haquri da dauriya irin waxanda ba a tava gani ba. A lokaci xaya shi ne malaminsu, jagoransu (SM: 1211/MA: 26590) Shi ne kuma inuwarsu wurin hutawa, kuma uwa mai maganin kukan xanta (SB: 4398, 1678). Shi ne mai sa ido akan su a cikin tausayawa da kyautatawa. (SB: 1788/SM: 1211) Shi ne kuma mai xebe masu kewa a cikin raha da nashaxi (SA: 2507) da kiyaye haqqoqansu daga tozarta (SB: 1636). Shi ne kuma mai qarfafa guiwarsu a kan aikata ayyukan alheri (SM: 1218).

 Da waxannan siffofi ne da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya haxa, ya ci nasarar jagorancin wannan tawaga ta iyalansa a cikin hikima da basira da nuna qwarewa a fagen tarbiyya da dashen zukatan alheri duk, a cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Ba tare da da xai rana an ji wani ya koka da shi ba daga cikinsu.

 Wai!....ina ma dai ace tarihi zai maimaita kansa? A samu wani nagartaccen shugaba ya kwatanta irin waxannan halaye da xabi’u na Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama, waxanda ya bar mana a cikin tarihi. Waxanda kuma sai mutum mai cikakkiyar himma da tsarkin zuciya ke iya aiwatarwa.

Ko shakka babu haquri da iyali wani aiki ne mai matuqar wuya da girma, da sai waxanda Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya zava daga cikin mazaje ke iya xauka. Domin kuwa ga al’ada ido ya raina wanda yake gani kullum. Saboda haka lalle ne sai mutun ya qara dauriya da haquri, kafin ya iya gudanar da jagoranci yadda ya kamata, kwalliya ta biya kuxin sabulu. Masamman irin lokacin Aikin Hajji, wanda kamar kogi da ruwa yake keta shi sai an shirya.

Saboda haka, lalle ne duk wanda ke son lada da tsira gobe qiyama, ya koya ma rayuwarsa haquri na gaske, tsakaninsa da iyalinsa da sauran makusanta. Ta haka sai ya karva sunan shugaba, kuma alkadarinsa ya xaukaka. Kamar yadda Allah Subhanahu Wata’ala Ya ce:

“Kuma mun sanya shugabanni daga cikin su, suna shiyarwa da umurninmu, a lokacin da suka yi haquri kuma sun kasance suna yin yaqini da ayoyinmu (32: 24)

Bayan wannan kuma, da haquri ne ake samun qauna da so daga wurin Allah har ma da agaji. Kamar yadda Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

 “Kuma Allah Yana son masu haquri” (3: 153)

A wata ayar kuma Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

“Lalle ne Allah na tare da masu haquri “ (2: 153)

To ba a wurin Allah Subhanahu Wa Ta’ala kawai ba, duk da mutane, suna matuqar son mutum mai haquri, suna kuma yarda da jagorancinsa.

 3.10 Manzon Allah Yana Rarrashin Iyalinsa

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na matuqar ji da iyalansa kamar yadda uwa ta ke ji da xan qaramin xanta, ko fiye da haka. Shi ya sa ba ya qaunar ganin abin da zai cuta masu. Ba abin da yake qoqarin yi Sallallahu Alaihi Wasallama ko da yaushe, sai ya yi abin da zai daxaxa masu rayuwa, matuqar hakan ba zai sava wa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba.

Ya kan xauki wannan mataki ne Sallallahu Alaihi Wasallama idan abu ya wakana savanin yadda xaya daga cikin iyalan nasa ke fata. A nan sai ya sanya rarrashi da lele a matsayin wata hanya ta magance al’amarin.

Haka Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance da iyalansa musamman a lokacin Aikin Hajji. Misalin wannan shi ne lokacin da matarsa, sayyida Aisha Allah ya qara mata yarda ta shiga wani hali na damuwa. Inda ya same ta tana kuka. Saboda an hana ta haxa haramai biyu (na Hajji da na Umra) kamar yadda sauran matansa suka yi, saboda wanki da ya kama ta. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ganin haka, ya shiga rarrashin ta yana cewa: haba yi haquri! Wannan ba zai cuce ki da komai ba. Abu ne da Allah Ya hukunta ga bayinsa mata, ba ke kaxai ba. Ki wadatu da Hajjinki, ya ishe ki. Sai Allah ya ba ki ladar Umra saboda niyyarki” (SB: 1788/SM: 1211).

Amma ina! Aisha Allah ya yarda da ita sai ta kafe saboda quruciya, tana mai cewa: “Ya Manzon Allah, ba komai ke damu na ba, sai in na tuna ‘yan ‘uwana (tana nufin abokan zamanta, sauran matan manzon Allah) duk za su koma gida, da Hajji da Umra. Ni ko Hajji kawai zan koma da shi. Jin haka fa sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fahimci lalle Aisha Allah ya yarda da ita ba ta xauki wannan matsala da sauqi ba. Don haka sai ya umurci yayanta Abdullahi xan Abubakar Allah ya yarda da shi da ya tafi da ita a can kan iyakar haramin Makka a wani wuri da ake kira “Tan’im” don ta sabunta haramarta da Umra. Shi kenan sai a huta” (SB: 1561/SM: 1211/SAD: 1782).

A wata riwaya kuma aka ce, ce mata ya yi “Dawafin nan naki na Hajji ya haxa har da Umra” amma ta kasa fahimta. A qarshe sai ya haxa ta da yayanta don ta yo sabuwar haramar Umra” (SM: 1211)

Allahu Akbar! Ka ji irin yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ke yi da iyalinsa. Amma mafi yawan mutane a wannan zamani ko dai ka sami sun wuce wurin. Ta yadda har iyalin nasu sun sukur-kurce. Ko kuma sun kasa, matuqar kasawa. A taqaice dai magidanta sun rabu zuwa qungiyoyi biyu:

Qungiya ta farko, ita ce ta magidantan da suka fifita buqatun iyalansu a kan dokokin Allah Ta’ala. Sai aka wayi gari iyalan nasu suna keta dokokin Allah, da biyar son zuciya.

Qungiya ta biyu kuwa, ita ce ta magidantan da, saboda tsananin rashin sanin girman Allah da dokokinsa, suke zamar wa iyalansu kamar dodanni. Su ne kullum xaure da fuska tanke da mara. A littafin rayuwarsu babu babin sassafci balle na ba ni gishiri in ba ka manda (Ina nufin musayar ra’ayi da neman fahimtar juna). Babu wani abu da ke sa su xan tattauna da iyalansu, balle har su xan shawarce su ko da wata rana. Ko su xan yi raha da su, ko rarrashi da lele. Babu abin da ke tsakaninsu, sai bayar da umurni ko hani, cikin kakkausar murya kamar sojoji, ba wata saurarawa ko nisawa balle karvar uzuri.

Alhali kuwa addinin Allah, abu ne da ke son tsakaitawa, kada a wuce wuri kar kuma a kasa. Yana kuma matuqar kwaxaitarwa da kira zuwa ga kula da iyali da rarrashinsu a inda hakan ya cancanta. Matuqar haka ba za ta kai ga sava wa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba. To abu ne mai kyau, da kuma ya kamata ko wane musulmi ya tsare idan yana fatar samun tsira da babban rabo.

 3.11 Yana Kuma Girmama Iyalansa

Wani abu kuma, da ke da alaqa da rarrashi da lele shi ne girmamawa. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance a wannan lokaci na Aikin Hajji yana kyakkyawar mu’amala da iyalinsa, ta hanyar amfani da kyawawan kalamai kuma daxaxa tsakaninsa da su.

Yana yin haka ne kuwa don ya nuna masu irin yadda yake qaunarsu. Har ya kan saki fuska sosai da qananan yara daga cikinsu, yana jan su a jikinsa.

Bayan wannan kuma ya kan bar wani abinda ya yi azama saboda su. Kamar yadda Jabir Allah ya yarda da shi ya faxa yana siffanta matsayin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da ya yi harama da Hajji. Amma Aisha Allah ya qara mata yarda ta yi harama da Umra. Ga abin da Jabir xin ke cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama mutum ne mai sauqin kai. Shi ya sa da Aisha Allah ya qara mata yarda ta yi yamma lokacin da ya yi gabas sai ya dawo ya bi ta” (SM: 1213).

Wannan ta fuskar Aikin ke nan. Ta fuskar kalamai kuma idan zai Magana da iyalin nasa ya kan zavo gangariyan kalmomi kuma daxaxa.

Dubi abin da yake cewa ‘yar kawunsa Zubairu wato Dhuba’atu Allah ya yarda da ita: “Haba dai Dhuba’ah, me zai hana ki Hajji?” (SM: 2936/ SA: 2375) Da kuma irin kalaman tausayawa da rarrashi da ya gaya wa mai xakinsa Aisha Allah ya qara mata yarda a lokacin da ya tarar tana kuka don wanki da ya kamata ta (SB: 1560). Haka ma daddafa qafafun samarin ‘yan gidan Abdul Muxxalabi da ya yi suna kan jajayen ababen hawansu, yana ce masu “Yan samari, kada dai a yi jifa sai rana ta hudo. Kun ji?” (SIM: 3025/SA: 2451) kamar dai yadda xan Abbas Allah ya yarda da su ya riwaito. A wata riwaya kuma ya ce: “Sai ga wata qungiya ta masu rauni daga cikin ‘yan gidan Hashimu sun zo a kan jajayen ababen hawansu. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya rinqa daddafa qafafunsu yana cewa: “Ya ku ‘ya’yana ku gangara. Amma dai kada ku yi jifa sai rana ta fito. Kun ji? (MA: 2507)

Wata riwayar kuma ta ce cewa masu ya yi: “Ya ku ‘ya’yan xan uwana, ya ku ‘yan gidan Hashimu, ku yi gaggawa ku isa kafin mutane su yi yawa. Amma kada xayanku ya jefi Aqaba.

Duba irin yadda wasu mahajjata ke yin biris da waxannan kyawawan xabi’u na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da suke mu’amala da iyalansu lokacin Aikin Hajji. Ta yadda wasu iyalin ba abin da zai rage a tunaninsu idan sun dawo gida daga qasa mai tsarki a matsayin guzuri na mu’amalar da ta gudana tsakaninsu da magidantansu, sai miyagun kalamai da munanan xabi’u na tozartawa da musgunawa da gori da cin fuska. Kai da dai abubuwa barkatai marasa daxin faxi, da suka haxu da su. Wasu ma har zargin iyalansu su kan yi a wannan lokaci mai alfarma.

Saboda haka, wajibi ne ga duk musulmin kirki, ya yi iyakar qoqarinsa, ya ga bai kasance xaya daga cikin irin waxannan mutane ba. Domin kuwa hakan za ta sa iyalansa su qyamace shi, kuma Hajjinsa ya sami tasgaro, ta hanyar kasancewa da zai yi nesa ga rahama da gafarar Allah Subhanahu Wa Ta’ala a sanadiyyar haka.

 3.12 Manzon Allah Yana Kyautata Ma Su

Fuskokin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kyautata wa iyalinsa da su, suna da yawa matuqa. Ta yadda da mutum zai kalli gaba xayan yadda rayuwa tsakaninsu ta kasance, zai iya cewa dukkanta kyautatawa ce. Domin kuwa babu wani vangare na rayuwar iyalinsa da bai bayar masu da gagarumar gudunmawa ba. Mafi bayyana daga cikin waxannan vargarori sun haxa da:

• Yin tsaye da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama a kan ganin ko wane daga cikin iyalin nasa ya sauke faralin Aikin Hajji. Ta hanyar gamsar da su har wanda bai da niyya daga cikinsu. Qissar Dhuba’atu da ta gabata ta isa misali a nan. Mu tuna cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tafi wurinta, lokacin da ya ji shiru. Ya ce mata: “Ko kina da niyyar xauke faralin Hajji?” ta karva masa da cewa: “Tabbas ina da amma dai ba ni jin sosai” Sai shi kuma ya ce ma ta “Kina iya fita zuwa Aikin, sai dai kawai za ki sharxanta ajiye harami inda kika kasa, sai ki ce: “Ya Ubangiji zan ajiye haramina a duk inda na kasa” (SB: 5089/ SM: 1207)

• Sai kuma tattara gaba xayan matansa da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tafi tare da su. Don su sami sukunin xauke faralin (SN: 4/222). Wannan kuwa matuqar adalci ke nan. Domin kuwa da ya so sai ya tafi da xaya daga cikinsu, ta hanyar zavin wadda ya ke so yaje da ita ko kuma yin quri’a a tsakaninsu.

• Sai kuma goya xan amininsa, Falalu da ya yi daga muzdalifa zuwa Mina Sallallahu Alaihi Wasallama (SB: 1544).

• Bayan wannan kuma, sai xauke wa matansa nauyin hadaya da ya yi ta hanyar yanka masu shanu, ba tare da ma sun roqe shi ba” (SB: 1709)

Irin wannan kyautatawa wani babban ginshiqi ce da ke nuna kamalar mutum. Kamar yadda shi da kansa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa cewa: “Mafifici daga cikin ku shi ne wanda ya tsere ma kowa a fagen kyautata wa iyali. Ni kuma ni ne shafe zancenku a wannan fage” (JT: 3895/SA: 3057)

Abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke nufi da wannan magana shi ne, duk da kasancewar hanyoyin kyautata wa iyali ba su da iyaka, to kyautata masu ta fuskar xora su akan abin da za su sami kusanci ga Allah da yardarsa shi ne mafifici. Saboda haka ne ma Allah Ta’ala ya umurce shi da ya soma kiransu zuwa gare shi kafin kowa, a in da maxaukakin Sarki ya ce:

“Kuma ka yi gargaxi ga danginka mafiya kusanci” (26: 214).

Ko shakka babu waxannan mutane, su suka fi cancanta da kyautatawar da mutum zai yi, ta duniya da lahira. Saboda haka yana da matuqar kyau mu kiyaye, mu kuma aikata don mu sami lada mai yawa a wurin Allah, kuma bayanmu ta yi albarka.

 3.13 Manzon Allah Yana Kariyar Mutuncinsu

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci na Aikin Hajji, ya kare mutunci da haqqoqin iyalansa iyakar zarafi, tsakaninsa da su, da kuma tsakaninsu da sauran mutane.

Babban misali a nan kuwa shi ne hadisin xan Abbas Allah ya yarda da su wanda ya ce: “Annabi ya yi xawafi ga xaki, Sannan ya sumbanci Hajarul-aswadi, ta hanyar amfani da sandarsa. Sannan ya zo inda ake shayar da mutane ruwan zamzam. Aikin da ‘ya’yan amminsa ke gudanarwa. Sai ya ce masu: Ku ba ni, ni ma in sha” Sai kuwa suka miqo masa gugar ya sha. Daga nan sai ya ce: Na yi nufin in kama maku wannan aiki na janyo ruwa daga rijiya. Amma ina gudun mutane su rinjayeku. Kuma kar su xauki hakan da na yi wani sashe na ayyukan Hajji” (SB: /MA: 2227).

Ka ga kenan kamata ya yi ga ko wane alhaji ya yi qoqarin la’akari da haqqoqan iyalansa. Kada ya yi wani abin da zai sa su tozarta ko su takura, matuqar yana fatar samun lada daga wurin Allah. To yin haka shi ya fi dacewa da shi.

Haka kuma kada ya bari su yi wani abu a karan kansu da zai zubar da mutuncinsu. Kada kuma ya bari wani daga waje ya zubar masu da shi.

Kaxan kenan daga cikin bayanin irin yadda rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta gudana tsakaninsa da iyalinsa a lokacin Aikin Hajji. Ba sauran abinda ya rage na uzuri yanzu, duk musulmin da ya karanta wannan littafi, ya kuma san girman iyalansa, a matsayinsu na mafi tsadar abin da ya mallaka sai kawai ya riqe su a wannan lokaci na Aikin Hajji kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya riqi nasa iyalin.

Da zarar haka ta samu, Nan take mutum zai fahimci amfanin abin, domin kuwa zai ji al’amurransa sun canza, kuma a qarshe ko shakka babu wannan zai qara masa qwarin guiwa ga koyi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama musamman a wannan fage na kula da haqqin iyali.

 Wajibi ne mutum ya kula da abin da zai gyara lahirar iyalinsa, ya kuvutar da su daga azabar Allah, wannan ya fi ya cika su da kayan alatu. A maimakon haka sai ya kula tare da kyautata tarbiyyarsu, da kuma nuna masu yadda zasu gudanar da ibadar Hajji yadda ya kamata, domin hakan zata taimaka ga gyaruwar halayensu.

Yana kuma da matuqar kyau mutun yayi kyakkyawar mu’amala da iyalin nasa fiye da yadda zai yi da mafi soyuwa ga reshi daga cikin abokansa. Domin haqqin iyalai ya fi na abokai nauyi.

 Saboda haka a dage, a kuma ji tsoron Allah. Don ayi gamo da katar da taimako da gudunmuwar Allah Subhanahu Wa Ta’ala.

 KAMMALAWA

Ina qara ninninka godiya, bayan wadda na yi wa Allah maxaukaki mai ni’ima da baiwa, ga duk wanda ya ba ni gudunmuwar wata shawara ko taimako ko wane iri ne a kan cin nasarar wannan aiki.

Wannan, wani xan qoqari ne kawai na yi, don share fagen fitowa da yadda rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta kasance a lokacin Aikin Hajji. Tattare da matsayina na ilimi da lokacin da nake da shi, ba su kai su yi wannan aiki ba. Amma duk da haka, ina fatar Allah Ubangijin baiwa ya yarda da wannan aiki, ya kuma karve shi. Ya sa ya amfani jama’a har su gudanar da Hajji nagartacce, karvavve, zunubbansu na abin gafartawa.

Kuma ina fatar a sani, wannan fage na da buqata da wasu manyan malamai su mayar da hankali a kansa, su ba shi isashshen lokaci da tunani. Wannan abu da na xan tsakuro ba komai ba ne, idan aka yi la’akari da wanda na baro.

Ina roqon Allah Ya samar da iko ga wanda zai yi wannan aiki daga cikin ma’abuta ilimi. Tabbas Shi Mai iko ne a kan dukkan komai, kuma shi ya fi kowa dacewa da jin kukan bawa.

Tsira da amincin Allah su qara tabbata akan shugabanmu Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, da duk wanda ya bi sawunsu, ya yi irin aikinsu har zuwa ranar sakamako.

 Alhamdu lillah.

Nau'uka na ilmi: