Littafin na magana akan kadaita allah shi kadai, wajan bautamasa da sunayansa da siffofinsa ,da nau ukan shirka da allah , kuma tauhidi sharadhine na zaman Lafiya da shiriya ,da saukan albarkan allah ,kuma shine farkon abinda akekira gareshi ,kuma dalilinsa allah ya aiko manzonni da littaffansa.
Malan yayi bayanine akan alamomin jinin ciwon mata dakuma wasu hukumce hukumcan jinin ciwo da kuma yadda ake bam banta jinin ciwo dana haila. Da wasu hukumce hukumne masu alaka akan jinin ciwon mata wanda wajibine gakowace mace musulma ta sansu.
Malan yayi bayanine akan hukuncin maziyyi da kuma ban banci tsakaninshi da mayiyyi da waddiyyi da kuma bayani akan cewa najasane kuma wajibine wankeshi da kuma cewa yana wajabta alwallah da kuma bai wajabta wanka amma doline awankeshi da ruwa dakuma wasu hukumce hukumce masu alaka dashi wanda wajibine musulmi ya sansu.
Malan yayi bayanine akan hukumcin yin wanka aranar juma a dakuma cewa yin haka mustahabbine ga kowane musulmi kafin yaje juma a dakuma yin ado a ranar, dakuma wasu bayanai akan wankar ranar juma a wadanda wajibine musulmi yasansu domin mahimmancinsu.
Yana bayanine akan hukuncinsa da haram cinyin mauludin nabiyyi(s.a.w) da kinyinsa dakum nisantar aiykatashi da bayanin hatsarinda ke cikinsa da masuyinsa dakuma bayanin alakar yan shia da sufaye dakuma kaidin da sukeyiwa musulmai da musulinci da kuma sanin hakikanin sufaye.