• LINK

    Wannan aiki ne na musamman domin koyarda hukunce-hukuncen musulunci da harsuna da dama na duniya, domin watsawa da yaxa ingantaccen koyarwan musulunci tsakanin musulmai, wannan aiki ya qunshi littafi mai xauke da hotuna Wanda yake qunshe da babuka biyar, wato tsarki, sallah, azumi, zakka da hajji. Littafin yana qunshe da sharhi Wanda ke bayani da dalilai domin sauqaqawa ga makaranci. Hakanan yana xauke da bidiyo Wanda ke bayanin waxancan babuka guda biyar a aikace , bugu da qari ga DVD da dai sauran hanyoyin yaxa ilimi na zamani

  • LINK

    Manufar wannan minbari na duniya shine isarwa tare da ya’da usullan karantarwan musulunci, ta hanyar samarda littafi da ya ‘kunshi ‘bangarori biyar : fagen imani, fagen zamantakewa, fagen ya’da da’awa , fagen suluki, fagen ibada, da fagen munasabobi Za’a gabatar da wa’dannan ‘bangarori ne a sigar shirye-shirye na talabijin da rediyo, tare da ya’da su ta kafar yanar gizo da kafafen ya’da labarai na zamani. Haka nan za’a watsa su ta hanyar CD da dai wasu hanyoyin, kamar yadda dai za’a ya’da wa’dannan hu’dubobi da darussa ta hanyar gidajen tibi da rediyo da harsuna daban-daban

ra ayinka nada mahimmanci