Mawallafin littafin ya ambaci wadansu gimshikai guda shida, kuma ya yi bayanin abinda ya shafi hakkin Allah akan bayinsa da kuma cewar shi Allah ya umarce su ne da kadaitashi, kuma ya hana su su rarraba ya umarce su da hadin kai, kuma ya maida martini ga rudanin da makiya musulunci suke kawowa.
Laccace da ta kunshi falalar Madina da kuma falalar masallacin Ma’aikin Allah , da kuma ladubban zama a cikinta, da hukunce-hukuncen ziyar da ma ladubbanta.
SIFAR SALLAR ANNABI SAW: a cikin allo na harshen Hausa wanda aka zana bayanin sifar sallah, Tanadar shehun Malami Dr. Haisam Sarhan, an bada bayani akan sifar sallar Annabi SAW a takaice, tun daga kabbarar harama har zuwa sallamewa, kamar kana ganinta, tare da kawo fotunan sallah a aikace, wadanda suke karin bayani.
SIFAR ALWALA DA TAIMAMA DA WANKA: a cikin allo na harshen Hausa wanda aka zano bayanansu, Tanadar shehun Malami Dr. Haisam Sarhan, an bada bayani akan sifar alwala da taimama da wankan Annabi SAW, tare da kawo fotunan da suke karin bayani.